Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TURKEN GIDA Part 1 by Janafty.txt
Chapter 71 of 103
Yau dai zaman gwanin daÉ—i ba faÉ—a ba bakar magana kowa ya binne abin da ke ran shi, Yaya Aina ce ta kalli Ma'u lokaci É—aya tana faÉ—in" Ke ko Ma'u dangin babanki na neman ki yanzu?
Sai ta yi shuru kafin ta ce" E. Muna waya da wasu daga ciki can kwanaki ma wata wacce da mamanta da babana uwar su É—aya uba É—aya ta zo wajena har ta yi kwanaki. Ni dai na daÉ—e ban je ba amman Alhaji ya ce in ya samu lokaci za mu je mu gan su."
Yaya Murja ta yi karaf ta ce" Ba dole su neme ta ba. Sun ji labarin ba ta wulakanta ba. Ta na da abin duniya."
Yaya Balki ke faÉ—in" To daman ai sai an san kana da amfani ake nemnka. Lokacin da suka san su za su wahala da ita ai ba su damu ba. Sai yanzu da suka san za su more ta. Ba komai abin da ta ke dashi ta yi musu ba shike nan ba."
Ni ko ina gefe na ce shiken nan kuwa. In kana da shi ka yi in baka dashi ne in baka yin ba matsala. Ita dai sai gyaÉ—a kai ta yi tana faÉ—in in sha Allahu.
Sallar la'asar ya tashe mu a wajen, bayan mun idar da sallah na shiga É—akin Gwaggo na gaida Baaba ta amsa kamar yadda ta saba amsa mini. Daga nan É—akin Mama na yi shigewata ina duba wayata su Firdausi ne a tsakar gida suna shara wasu na wanke wanke su Yaya Murja na baro su É—akin Gwaggo. Tun da su sun rigani zuwa karfe biyar Yaya Aina ta yi sallama ta wuce gida bayanta Yaya Balki tare suka fita da Zaituna ni ma sai na yi shirin tafiya har Ma'u na fadin ta É—auka sai dare zan tafi, da haka na so amman sai na tuna zan yi ma su Jidda kitso ba zan zauna jiran Yallabai ba.
"Tafiya zan yi. Na yi ma su jidda tsifa zan kama musu kai gobe makaranta."
Yaya Murja na gefe ta ce" Da kin zo da su Firdausi ta yi musu."
Sai na ce mata ban yi tunanin Firdausin za ta zo ba ne, ina shirin tafiya Munirra ta kirani a waya ta na tambayan muna asibitin ne ko gida? Sai na ce mata muna gida sai ta ce mini gata nan zuwa ita ta tsayar da ni na jirata har sai da ta zo na rakata falon Alhaji ta gaishe shi.
"Matar ƙanin Yallabai ne Alhaji"
"Allah ya yi mata albarka. Na gode.".
Har da kankana ta kawo masa Gwaggo na ta godiya, mun dawo ɗakin Mama sai ga su inna Mariya sun zo duba Alhaji ta ce Amina ce ta faɗa mata jiya shi ne ta ce bari ta zo ta duba shi, dalilin haka yasa na daɗe a gidan tun da sai bayan sun tafi tare ta ke da matan su Kawu Tasi'u, sannan ita Munnira ta ce min ba daɗewa za ta yi ba na fito rakata har bakin gida bayan ta yi sallama da su Gwaggo ta ke ce min.
"Ke na taɓa ki da alheri matar Yallaɓai. Kin ji Yaya Usman zai kara aure? Ban samu zarafin mgana ba ta cigaba da faɗin" To yanzu ma mganar da ake yi Anty Zabba na gidan su. "
Cikin nuna mamakin na ce"Wai har yanzu ba ta koma ba?
Munnira ta ce" Ina fa ta koma, a bakin Nasir na ji wannan satin mai shiga Yaya Usman É—in zai zo, na so kiran Anty Zabba sai na fasa kar ta ce ina da son jin gulma"
Ina mata dariya na ce" Wallahi haka za ta ce."
Munnira ta kama haɓa kafin ta ce" Shi ya sa ban kira ba. "
Na ce gwara hakan itama Munira ta na faÉ—in ba ta ji daÉ—i ba, koma mene da ta yi hakura ta zauna tunda matar na shi ba akanta za ta zauna ba.
"Uhm ke dai Munira Allah dai ya kyauta ya dai dai ta su."
Ta amsa min da Amin Amin daga nan muka yi sallama na koma cikin gida sai na ga Aneesa da wayata wai ana ta kirana ina dubawa sai na ga Yallaɓai ne da sauri na ɗaga kiran.
"Yallaɓai ka taho ne?
Cikin wani irin murya ya ce min" Sadiya ta congratulation."
Ina yar dariya na ce" Yallaɓai ka biya mini makka ne?
Shima dariyan ya yi kafin ya ce" In sha Allahu ina saka ran haka, amman dai yanzu ina so na faÉ—a miki ne an biya ni half payment na aikin nan namu na Rano."
Cikin murna na ce" Don Allah fa Yallaɓai"
"Allah Sadiya ta. Yanzu kuÉ—in suka shigo sun kuma kirani sun faÉ—a mini."
ÆŠakin Mama na faÉ—a ina faÉ—in" Alhamdulillah mun yi kuÉ—i"
Ya na yar dariya ya ce" In an yi mangariba zan fito sai na zo mu dawo tare"
Da haka muka yi sallama, muna gama wayar na yi hamdala ina jin daɗi Allah ma ji roƙon bayin shi.
Na ƙosa mangariba ta yi ma saboda murna, ina idar da sallar mangariba na shirya lokacin har Yaya Murja ta tara yayanta sun tafi gida ni da Ma'u kawai ne a gidan ita kuma tana tare da Baaba. Yallaɓai sai bayan isha'i ya zo, ya ƙara duba Alhaji sannan na yi musu sallama muka tafi gida.
Muna hanya ya kalle ni kafin ya ce" Yanzu da me zamu fara Hajiya ta?
Ina dariya na ce" Mu je gida mana Alhajina."
Sai muka kalli juna kafin mu kwashe da dariya, ni ko har ina dukan kafaɗansa kafin na ce" Ranka ya daɗe mai girma Tafida."
Shi dai ya na ta dariya ni kuma ina masa kirari
"Angon Sadiya Ɗan gatan Nene, uban Jidda da Maimuna. Allah ya ƙara ja zamanin Tafida mai girma Injiniyan gine gine, mai muƙamin zane zane takawar ka lafiya"
Ya na dariya ya ce" Me kike so Sadiya? Ina masa dariya na ce" Me kuwa na ke so? Yallaɓaina kaɗai na ke so."
Gira ya ɗaga min kafin ya ce" Kin yi kyakyawan zaɓi kuwa."
Muna tafe muna hira, har muka isa gida. Baby har ta yi barci, dole na tashe ta tana kuka tana komai na yi mata kitso, Yallaɓai na ta faɗan wai ban iya kitso ba ne na saka yarinya tana kuka.
Baki sake na kalle shi kafin na ce" Au ban iya ba ko?
Ya na kallona ya ce" To ni dai ban san lokacin da kika koyi kitso ki ka iya ba"
Sai kawai na yi banza da shi Jidda dai lafiyan lau muka yi kitson mu, sai bayan na gama mu su ne na ce su yi shirin kwanciya Baby daman Babanta ya lallasheta har ta yi barci. Wanka na sake yi na yi shirin kwanciya Tea na haÉ—a mana muka sha sannan muka zauna kassafa kuÉ—i, abu na farko kayan abinci na yi masa mgana sai kuma na ce ya ijiye kuÉ—in makaranta yara tun da sun kusa fara jarabaawa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.