Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TURKEN GIDA Part 1 by Janafty.txt
Chapter 95 of 103
Ganin ɗakunan su Nene cike da ƴayansu zuwa jikokinsu sai mu surukan gidan muka tsame kan mu zuwa ƙasa shashen su Jawahir ba ta nan ma tun safe an ce ta tafi can gidan kakaninta na bangaren uwa ita da Adnan. Da ni da Hauwa da Muniira muka zauna acan muna ta hira muna shewa. Muna ƙara ma junan mu sani kan abin da bamu sani ba. Muna mgana kan kayan gyara ne Munnira ke faɗin rabon ta da wani gyara tun haihuwan Mufeedan ta.
Cikin mamaki na kalleta kafin na ce" Ke kam Munnira me ya sa me ki? Mufeeda yanzu ai ta shekara uku ko Hauwa?
Na faɗa ina kallon Hauwa wacce kafin ma ta bani amsa Muniiran ta karɓe da faɗin" Shekaranta uku da wata biyu."
Jinjuna kai na yi kafin na ce" Ki ce waje duk ya yi tsatsa. Gaskiya ba ki kyauta ma Nasir ba."
Na faɗa ina hararanta ita kuma tana dariya kafin ta ce" Ke ni fa gani na ke yi duk ba sa wani yi asara ne. Kuma ni in dai ba shi zai ba da kuɗin a siya ba sai na ke ƙyashin fidda kuɗina na siya wallahi."
 Mamakin Munnira ya kamani daman har yanzu akwai mata masu tunani irin na Munnira? Ko dai ta yi ma kalmar gyaran mummunan fahimta kamar yadda wasu matan suka yi ma kalmar. Ban samu zarafin mgana ba Hauwa ta karɓe mganar da cewa" Haba Munnira ke da kan ki ma? Mata ai yanzu sun waye kowa ta san abin da za ta sha ya gyara ta ba wai kuma wanda zai zama cuta gare ta ba. Kuma kin manta hausawa na cewa in kana da kyau sai ka ƙara da wanka? Kina da yaƙinin tun gyaran da kika yi da haihuwan Mufeeda ya na nan a jikin ki? Haba ai yakamata dai ko yaya ne ki ɗan ƙara gyarawa ko dai baki sha komai ba yan kayan marmarin nan da za su ƙara miki cika da Ni'ima."
 Daga ni har Munnira baki muka saki muna kallon Hauwa. Sai da ta gama bayaninta ta ga irin kallon da muke yi mata sai ta ji kunya ta kauda kai tana faɗin" Me ya faru kuke kallona? Ko ba gaskiya na faɗa ba."
Ina ɓoye mirmishina na ce" Kin faɗi gaskiya Hauwa uwargida a gidan Mutaƙƙa shi ya sa har gobe bai kallon kowa sai ke ashe sirrin da kika riƙe kenan? To mu ma a ɗan gaya mana sirrin mana ko Muni?
Na faÉ—a ina kallon Munnira da ta kwashe da dariya har ta na bani hannu muna tafawa cikin dariya ta ce" Shegiya Hauwa ta zama yar gari. Maza gaya mana sirrin."
Hauwa na dariya ta ce" Shawarwarin ku ne fa, sannan daga Rano akan É—an aiko mini da gumba da sauran abin da ba za a rasa ba. Sai wacce Sadiya ta haÉ—a ni da ita na kan É—an siya mganin infection sai kaza in na samu kuÉ—i kuma Alhamdulillah ina ta ganin canji."
 "Allah Hauwan Mutaƙƙa ?
Na faÉ—a ina kallonta sai kawai ta É—aga mini kai. Tare muka saka dariya Munnira har ta na É—aga kafa saboda dariya kafin ta ce" Ke Sadiya yaushe Hauwa ta yi baki haka? Kuma abin É—anwaken zagaye ne? Hauwa kaÉ—ai kike so ta gyara ban da ni ko?
Ina ɗaga hannuna sama na ce" A'ah ita ta min mgana ta ce tana so saboda ranar tana gidana aka aiko min da saƙon. Sai ta ce min tana so sai na haɗa su kema in kina so ai ta kwana gidan sauƙi waya kawai za a yi mata."
Munnira sai ta gyara zama kafin ta ce" To wai kuma yana yi sosai?
Na kalleta ban yi mgana ba Hauwa ce ta ba ta amsa da cewa" To ai ke tunda kin riga kin saka wasi wasi ko kin siya ba zai yi miki aiki ba."
"Ko?
Haka ta ce tana kallon mu ni ko sai na gyara zama ina faÉ—in" Gaskiyan Hauwa. Kuma son kuÉ—i ne ba zai barki ki yi gyaran ba karki kashe kuÉ—i ko? Zauna Nasir ya samu wasu Æ´an kudaÉ—e ya nemi chanji lokacin za ki yi bayani ne."
Tana dariya ta ce" Haba. Ai ya yi ƙanƙanta da Mata biyu. Yallaɓai dai ke kan hanya daman ana ta cewa tunda Yaya Usman ya buɗe hanya Yallaɓan ki ne zai biyo baya."
 Wani kallo na yi mata sai ta kama dariya Hauwa na taya ta. Nuna ni take yi tana faɗin" Ta firgita ta. Kin gan fa Hauwa."
Ta faÉ—a tana nuna ni ture hannunta na yi ina faÉ—in" Firgitan me? A kaina za ta zauna? Allah ya kawo ta lafiya."
Hauwa da Munnira na ta danne dariya haushi ya kamani na ce" Wai dariyan na menene kuma? Ko kin ji labarin auren ne ni ban sani ba?
Da sauri Hauwa ta ce" A ina? Wallahi wasa ne kawai ba abin da muka ji."
Hararan su na yi domin na ga sun maida ni abin zolaya. Munnira ce ganin na haÉ—e rai ina faÉ—in" Ko za a mini kishiya sai an yi miki Munnira in sha Allahu."
Da karfi ta amsa da cewa" Wallahi ba Amin ba. Cab"
Ina mirmishi na ce" Au ashe ba daÉ—i? Sai ta marairai ce tana faÉ—in" Daga Wasa? To a bar mganar kawai."
 Ni kuma na ce sai an yi ta. Munnira uwar kishi ta ce ita fa ta tsani labarin kishiya. Ganin na na ce ina cewa Nasir sai ya yi aure nan kusa in sha Allahu Hauwa na taya ni sai kawai ta sauya mganar da cewa" Na ce ba ya mganar kayan gyaran can ɗin? Ina ga zan siya nawa nawa ne?
Ni da Hauwa har muna tafawa saboda dariya sai da na gama ja mata aji sannan na yi mata bayanim ingancin kayan gyara na Hajiya Surayya Halin yau.
Cikin mamaki Munnira ta ce" Da gaske suna da kyau? Ba su dai cutarwa ko?
Kai tsaye na ce" In da suna cutarwa da tuni sun cutar da ni. Ke Munnira ki cire wannan tunanin a ranki na matan da ba su san kansu ba. Yanzu mata sun fahimci muhimmamci gyara a jikinsu wanda ba zai zama cuta a gare su ba. Kin ga mganin infection ɗin nan yana da kyau duk bayan wattani uki mace ta riƙa shan shi. Saboda shi infection 90% na mata muna dashi sannan mu ke zuwa gidajen biki da suna muna mu'alama da banɗakuna mabambamta. Kin ga kowani lokaci za mu iya ɗauka sai mun dage da mgani sannan maganar gyara Munnira ba wanda zai cutar dake ba yar gumbar nan ta mata ɗan kazan nan na haɗin uwargida ba komai a cikinta sai itatuwan maganin da zai ƙara miki Ni'ima. Bayan nan za ki riƙa gyaran ki a cikin gida kayan marmarin nan ki riƙa shan su madara su rage kayan ganye da sauran su duk suma suna taimakama wajen dawo da ruwan jikin mu kin gani nan duk bayan wata uku sai na siya mganin infection na sha sannan na bi da kayan gyara bayan kuma ina yin nawa dubarun a cikin gida hatta fatata ban zauna ba bayan wani lokaci ina siyan mayukan gyaran jiki domin kaina da kuma Mijina. Ba kuma domin shi ɗin ba sai domin ka riƙe wannan martaban da Allah ya ba ka na ƴ'a mace. Sannan yana da kyau ka yi gyara domin ka farantama mijinka Munnira ba sai an kawo maka wata ka haukace ba. Wanda ko da watan ta zo sai dai ita ta yi gasa da ke ba dai ki yi da ita ba tunda komai ta zo ta iske ki kin san shi kuma kina yi saboda haka ki yi ma kanki faɗa ki gyara jikin ki da kanki saboda martaban ki Munnira"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.