Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TURKEN GIDA Part 1 by Janafty.txt
Chapter 7 of 103
"Ina wani yawa a aikin gidan nan Sadiya? Kawai daman kin saba da hutu shi ya sa kike kallon shi a matsayin aiki."
 Ni ko sai na yi mata mirmishi duk da maganar ta na sukan zuciyata amman sai na ɓoye hakan a saman fuskata. Kai na kaɗa kafin na ce"Hutun ne ya zo Anty Bahijja amman karki manta a baya nima na yi aikin."
Ta san magana na gaya mata shi ya sa ta yi mini wani kallo, ban bari ta samu damar magana ba na cigaba da faÉ—in" Kuma Anty Bahijja laifi ne in mace ta samu hutu ta huta a gidan mijinta? Kema fa kina da yar aikin nan sannan ki na fatan nan gaba in su Sulaihat suka yi aure suma su samu gidan da za su huta ko ba haka ba ne? Ba fa wanda ba ya son jin daÉ—in nan fa."
 Na faɗa ina kallonta saboda na ga kuma wata magana za ta ƙara faɗa mini, sai na ga ta juyar da kai ta na faɗin"Ba irin na ki ba Sadiya."
Ban yi magana na nima sai na kauda kaina ina É—an mirmishi, na rasa wani hutu suke hangomin a cikin wannan gidan? Sun manta a baya komai na gidana da mijina da Æ´aÆ´ana ni nake yi ma kaina? Saude ba ta fara zuwa mini aiki ba sai bayan mun tare a wannan sabon gidan amman gabaÉ—aya Æ´an'uwan Yusuf gani suke yi da kuÉ—in É—an'uwansu na ke walwali ina haskawa sannan na samu duniya ina ta jin daÉ—ina.
 Ban ƙara ce mata ƙala ba, amman ita sai faman kalle kallen falon take yi tana wani taɓe baƙi, ba yarinya ba ce tunda Yayar Yallaɓai ce, daga ita sai shi tana da manyan ƴaƴa amman ba taba aurarwa ba suna karatu ne.
Can ta ga ji da zaman mulkinta ta kalleni ta na faÉ—in" Su Jidda suna makaranta ko?
Sai na gyaÉ—a mata kai, kafin na yi magana ta rigani da cewa" Kuma sai satin nan ba ki kai su gidan Yaya Maimuna ba? Me ya sa ?
 Daman na san rashin zuwan su gidan Anty Maimuna sai ya zame min abin magana, zama na gyara kafin na fara faɗin" Ba su samu zuwa ba. Amman weekend ɗin nan in sha Allahu za su je."
 Anty Bahijja ta ƙara faɗin" Me ya sa na ke tambaya?
Kai tsaye na ce"Gidanmu muka yini ranar asabar, lahadi kuma na ce su tsaya saboda shiryen shiryem makaranta, su goge uniform da homework lokaci ya ƙure shi ya sa sai na ce bari su bari wannan satin da sun dawo makaranta ranar jumma'a zan tsa yar mai mashin ɗin su, sai ya kai su in sha Allahu."
 Miƙewa ta yi, lokaci ɗaya ta na rayata jakarta, kafin ta kalleni tana faɗin"Kina da ƙulafucin ƴa'ƴan Sadiya. To ki yi zuciya ki sake haihuwa mana. Amman ace kamar gidan Yusuf shi da ke son yara a ce ƴaƴa biyu kaɗai gare shi kamar ba shi da wani zaɓi, yanzu in muka ce ya ƙara aure sai ki ji haushin mu ko?
Ƙuramin ido ta yi saboda tana so ta ga yadda zan yi, sai ni kuma na nuna mata har yanzu ba ta gama sanin wacece Sadiya ba.
 Dariya na saki har ta na fidda sauti kafin na ce" Jin haushi kuma Anty Bahijja? Ai aure umarnin Allah ne shi ya ba su damar ƙarawa, wallahi tallahi na sha faɗa ma Yallaɓai in zai ƙara aure ya ƙara domin ni ba ni da matsala da ƙarin auransa tun da ba akaina za ta zauna ba, kuma ko ta zo sai dai ta zo a ta biyu kin ga kenan ko ya ya dai na ke na amsa sunan Turken gida. Haihuwa kuma ta Allah ce, in ya tsara min ƴa'ya biyu zan haifa shike nan, kuma ni ba zan yi ma Yallaɓaina baƙin cikin ya ƙara aure ya sake haihuwa ba, duk wani abu da ya fito daga tsatson Yusuf abin so ne a wajena."
 Kamar ba ta yarda da magana ta ba, domin sai ta ƙara kallona take yi, tana mirmishi, kallonta na yi domin har ta mirmishinta irin na Yallaɓaina ne. Ganin ta kama hanyar barin falon ya sa na miƙe na bi bayanta dai dai lokacin da na ji ta na faɗin"Ke fa kika tsaida haihuwan da kanki Sadiya kin ga ko, ko auran Yusuf ya ƙara bai yi miki rashin adalci ba."
Ina bin bayanta na yi mirmishi amman ban yi magana ba.
 Ni ce har haraban gida na rakata, ina ce mata"Ba ki zo da mota ba ne Anty Bahijja?
Kai tsaye ta ce" Tana waje."
Sai na gyaɗa kaina fulawowin gidan ta bi da kallo kafin ta ce" Fulawowin nan sun ƙara ma gidan nan kyau fa."
Na biye mata ina cewa" Sosai ni ko ma da farko ban so Yallaɓai ya saka su ba sai bayan sun fara girma sai na ga sun yi ma wajen aiki."
 Wani kallo ta yi min ta cikin likabinta da ta saki kafin ta ce"To gidan ki ne? Da sai kin zaɓi abin da zai saka ma gidan shi? Dariya na yi kafin na ce" Gidana ne mana Anty Bahijja, ko kwatance za a yi gidan Sadiya za a ce ko Maman su Jidda, kamar yadda kema a ke kwatancen gidan mijin ki da gidan Malama Bahijja."
Kallona ta yi ido cikin ido ni ko sai na waske ina dariya.
 Sai ta bige da yin mirmishi kafin ta ce"kin samu dai kan Yallaɓai ta bakin ki kina yadda kika ga dama, to tunda ya yi miki gida saura mota ko?
Ina riƙe baki na ce"Ni Sadiya? Ai ko kuɗin ya samu kuka ji zai siya mino mota hana shi za ku yi Anty Bahijja"
Kai tsaye Ta ce"Tabbas. Gwara ya yi aure shima ya tara zura'a kar ki manta a gidasu mata huɗu cif ne da kimanin ƴaƴa 21 ban da waɗanda suka rasu."
Ni ko da gayya na ce"Allah ya bashi kuÉ—in da zai wadatamu. Sannan sai ya yo auran miye a ciki?
 Anty Bahijja ta san halina ko Hajiya Maimuna ba na raga mawa, in suka faɗa min cuta zan faɗa musu mutuwa, duk da suna yayyen mijina, saboda suna da ƙananun maganganu sannan sun sakama rayuwata ido, a wasa ne za su yi ta faɗa minI magana
Nima ko a wasa na ke maida musu martani. Anty Zuwaira ce kaɗai ba haka a tsakanin mu saboda ita tana kama girmanta, da yake yar boko ce ga isa da gadara ba ta da ma lokacin tsayawa ƙananun maganganu. Har makaranta private nata na kanta gare ta, sannan ita ma ta kai matsayin Principal a wata makaranta ƴan mata ta cikin gari, sannan uwa uba mijinta a Mininsty of education reshen jihar kano ya ke aiki.
 Ban bar jikin get ba sai da Anty Bahijja ta shiga motar ta ta tafi, ina ɗaga mata hannu bayan na ce ta gaida su Suhailat, sannan na rufe get ɗin na koma cikin gida a falon da muka zauna na koma na sake zama.
Duk a cikin maganganun Anty Bahijja magana É—aya ta fi tsayamin a rai.
Wai da ta ce ni na tsaida haihuwa da kaina, tuni na ji kaina ya fara sarawa abin nan mai ɗaci ya tokaremin a cikin kirjina ya kasa wucewa, wani tuƙiƙi kawai na ke ji kamar zan shiɗe.
Har yau na kasa aminta da ba Yusuf ba ne ya je ya kwance min zani a kasuwa a gaban ƴan'uwan shi ba, tunda ya na da wani hali na faɗi ba a tambayeka ba, sai sai Ma'u ita ce abin zargina na biyu saboda tana auran yaron mai bi ma Mijin Anty Bahijja ma'ana suna aure a dangi ɗaya duk wasu maganganu da suke samu a kaina ta bakin Anty Bahijja ne, ko sunan Sadiya yar laushi da ke bakinta ko na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba daga baƙin Ma'u ne.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.