Tsofaffin Hausa Novels

Turken Gida Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: TURKEN GIDA Part 1 by Janafty.txt

Chapter 59 of 103

  Bangaren Yaya Murja ma ba ta sauya zani ba. Ko bayan auran ta in dai za ta zo gidan da abun arziƙin da za ta kawo ma Ma'u da Rahila har da Amina ni kuma sai ta ce ba ni da kunya. Ni ma da na gane ko gidan zan iya kirga zuwana, na fi zuwa gidan Yaya Aina ko Yaya Balki in ma fitan ya kamani kenan. Har a lokacin ba ni da wata kawa da zan iya nunawa amman Rahila da Ma'u suna da ƙawayen su. Barin ma Ma'u ƙawarta din nan Shema'u har lokacin suna tare su Gwaggo duk sun santa ta na zuwa nan gida itama Ma'un ta na zuwa gidan su saboda su haɗu da Ma'u su yi ta munafunci  har can dakata tare suke a makaranta. Ni dai kamar yadda ban son Ma'u itama Shema'u ban ƙaunarta domin gabaɗaya halin su ɗaya. Za mu haɗu sau goma a makaranta sannu ba ta haɗamu da Shema'u amman in ta zo gida tana mini fara'a kamar ta Allah. Na daɗe da yarda da mganar hausawa da suka ce sai hali yazo ɗaya ake abota. To akwai mugayen hallayar Shema'u da Ma'u da suke kamamceceniya.

 
****

  Mama  ta shiga madafi ta ga na ɗora miya tana tafasa ko ƙashin miyan ma da Muntari ya shigo da shi ban saka ba sannan ban ko ɗora tuwo ba. Ba ta yi mamaki ba sanin halina sai ta fito tana faɗin" Sadiya me take son zama ne ni Rukayya?

Gwaggo na zaune ta ce"Me ya faru hala?
Sai ta kaɗa kai tana nufar ɗakin mu kafin ta ce" Ba ta ko ɗora tuwo ba. Kuma miya na ta dahuwa ko ƙashin da muntari ya shigo da shi ba ta saka ba."
Lokacin ta É—aga labulen É—akin tana kwala min kira ina daga É—akin Hajiya har na fara barci.

"Ba ta fa a É—akin"

Hajiya hankalinta na wajen jin radiyonta ba ta ma jin su.  Gwaggo ce ta leƙo dakin Hajiya ta na kiran sunana na ji har gyara kwanciya na yi. Ban ankara ba sai ji na yi an ɗaka  mini duka a cinyata da sauri na miƙe ina sosa wajen sai na ga Mama tsaye a kaina tana huci.

Cikin tura baki na ce"Kai Mama a cinya fa kika dake ni."

"In ba ki tashi ba sai na mare ki a fuska yanzu."

Ina jin haka na yi saurin saukowa daga gadon saboda na san halinta tana da saurin hannu. Ina fitowa na ga har mangriba ta yi Gwaggo ta kalleni ta na faÉ—in" Sadiya ho. Ke ko koyi da Æ´an'uwanki ba kya yi. Su in dai suna da aiki akan lokaci suke gamawa."

Haushin aikin dake gabana ya sa ban ko yi ma Gwaggo magana Hajiya ce ta kashe radiyon ta na faɗin" Me ya faru ne? Ke Dubu ina kallabin ki? Sai a lokacin na taɓa kaina ba ɗankwali ina tura baki na koma na ɗauko a saman gadonta da ya saɓule na ɗaura na fito dai dai Hajiya na faɗin" Dare ya yi ina su Asma'u ne? Su kama mata su yi girkin tare.'

Jin haka sai na washe baki amman sai Mama ta ce" ƙyalata ta Hajiya. In na su aikin ne tana ɗaki kwance kauda kara ba za yi musu ba. Sai su ne za a ce su yi mata na ta aikin? Sai murnata ta koma ciki sai dai Hajiya ta sake ƙwatana da ta ce"Ita ai ba yanayin su ɗaya ba. Tun da sun fita zafin nama ai ba a zauna a zama ɗaya ba."

Jin haka yasa na miƙe da karsashina saboda na san in su Rahila suka dawo sai Hajiya ta yi musu mgana sun tayani. Icce na haɗa na ɗora Tuwo Mama na ta faɗan in ina girki har jajjage ita ke yi mini kawai na fito na ɗora ina jin ƙyashi na duba har wanke wanke da sharan tsakar gida da Amina ce ke yi sai da ta yi kafin ta fita sai ni da in dai ina da aiki sai ran kowa ya ɓaci ina cikin madafi ina tura baki amman raina fes domin na samu raran kuɗin cefane Alhajimu 2k ya ba ni kayan Miya kawai na siya kashi daman yaya Muntari ya kan tura ma kuɗi in dai za a yi miya ya siyo. Kuɗin cefane ke saka ni farinciki in ranar aikina ya zagayo amman bayan haka yini na ke yi cikin baƙin ciki sai na ji gabaɗaya duk na gaji kamar mahaukaciya haka nake komawa a irin yanayin ana takata sai na yi sati ina gaba da mutum.

  Ana kiran sallar mangariba su Rahila suka shigo. Gwaggo sai da ta yi musu faɗan da Alhaji ya shigo fa. Ma'u ce da yanayin mganarta ta ce" Mun taso da wuri Gwaggo rashin abun hawa ne."
Ina madafi ina talge da fitila a hannuna ba wuta. Na gama kenan na rufe na fito nepa suka kawo wuta. Miya ta isa kaɗi har na kwashe ƙashin ina fitowa Rahila ta kalleni yadda na yi kaca kaca kafin ta ce" Wai ke ba ki gama tuwon ba daman?

  Wani kallon tara saura kwata na yi mata na wuce ta. Ba domin ta matsa ba sai na bangajeta. Ma'u  wajen rijiya ta nufa bayan ta miƙa ma Amina Hijabinta ta kai mata cikin ɗaki wajen Hajiya na nufa ta miƙe tana kwashe tabarma tun da an kira mangariba raɗa na yi mata a kunne.

"Hajiya ga su Rahila nan."

Sai ta kalleni kafin ta juya ta na kallon Rahila wacce ke mgana da Ma'u.

"Rahila da Asma'u in kun yi sallah ku kama ma Dubu aikin nan ta gama kafin Sule ya shigo."
Rahila ta amsa da to amman Ma'u sai da ta kalleni nima na kalleta gwalo ta yi minibni kuma na ɗauke mata kai na koma kitchen. Gwara na kaɗa miyar da kaina na bar musu su ƙarisa tuwon. Sai da na kaɗa miyar na sauke sai na saka ruwan wanka ni kuma na je na yi alwala saboda ma ba na son mgana a ɗakin Hajiya na yi sallar mangariba na kuma yi zama na ƙarshenta dai Rahila da Ma'u suka ƙarisa tuwon Alhajinmu ya shigo gida bayan isha'i lokacin ina wanka a bayi daman ina ta Allah Allah na gama na fito kar ya dawo.

  Ina fitowa yana tsakar gida an baza masa tabarma. Na so na yi saɗaf na shige ɗaki amman hakan bai samu ba sai da ya ganni.

  "Dubu"

Dole na amsa ina kallon shi faɗa ya fara min na wankan dare wannan karon ma Hajiya ce ta fito ta ƙwace ni.

  "Sule ka ƙyale yarinyar nan. Yau fa a tsaye ta yini tana aiki har daren nan gwara ta yi wanka ko ta ji daɗin barci."

  Alhajinmu ya yi shuru amma Mama sai da ta ce" To ta riƙa yin aikin ta da wuri mana. Sadiya son jikinta har bani tsoro ya ke in ta yi aure ban san ya za ta yi ba "

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.