Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: RABO YA RANTSE.txt
Chapter 4 of 21
Sai da sadiÆ™ ya sanya su Safna suka kai Kayan abincin kitchen yasha ruwa sannan yace musu su tafi su kwanta dare yayi.
Sallama sukai masa suka nufi É—akunan kwanan su.
Falon yayi shuru daga sadiƙ sai Ammi ya gyara nutsuwar shi ya kalli Ammi sosai cikin sakewa dan Ammi bata alkunyar ɗan fari da Sadiƙ gaba ɗaya ta sake da ƴaƴanta yadda ba'a zato sabida sune sanyin idaniyarta Sune garkuwa a rayuwarta tun suna ƙananu take gwagwarmaya dasu Sabida suna ƙananu mahaifinsu ya rasu yabar mata su duka duka lokacin Sadiƙ baifi shekara goma sha biyar ba Aliyu sha Huɗu dan tsiransu da sadik shekara ɗaya ne Salma ce suke da ɗan tazara da Aliyu na kusan shekara Biyar ita lokacin tana shekara tara Bashir shekara bakwai Safna shekara huɗu sajeeda shekara Ɗaya haka Allah ya ɗauki ran mijin nata yabar mata waɗannan ƙananun ƴaƴa wannan tasa ta shaƙu da ƴaƴan nata taja su ajikinta fiye da ƙima.
"Ammi tun safe Aliyu ya kirani a waya wai Mami ta tashi tana ta zubar da Jini haka yace sunje asibiti a gigice hankalina ne yaƙi kwanciya shine na biyo jirgin dare nazo akan wannan batu"
SadiÆ™ ya faÉ—a cike da nutsuwa yana fuskantar Ammi wadda ta bada dukkan nutsuwarta a tare dashi.
"Nima bai gaya min ba sai a wajan masu aiki naji, Amman dan shishshigi har Æ´an cikin gidanku sun cika asibitin"
SadiÆ™ ya kawar da abin da Ammi tace dan har ga Allah baya jin daÉ—in yadda Ammi take wa Æ´an uwan mahaifin nasu.
"Ammi ni ina ganin kamata yayi kawai Aliyu ya ƙara aure, Dan wannn matsalar tayi yawa"
Ammi ta watsawa SadiÆ™ wani kallo.
"Haka ya aiko ka waje na kenan? saƙo ya baka?"
SadiÆ™ ya gigice dan yasan Halin Ammi inta botsare musu.
"Wallahi Ammi ko É—aya kawai dai ni tausayi yake bani ne kinga fa tare akai mana aure dashi yanzu haka Minal shekarun ta goma a duniya kinga shima in da Allah ya bashi da tuni yana da sama da Æ´aÆ´ana"
Ammi ta dube shi.
"Sadiƙ zaku ga kamar ina takurawa Babana ne akan Lamarin auren shi, Ko ɗaya ni tsorona kada ya auro matar da zata rabamu dashi Na san Baya son Mami ko kaɗan tsananin biyayya ce ta sa ya aureta Ni kuma na haɗa shi da Mami ne sabida Duk tsiya mahaifinmu ɗaya da Mahaifiyarta Kaga Mami tamu ce bamu da matsala da ita Kuma auren su zai ƙara ƙarfin zumuncin mu da mahaifiyarta"
Sadiƙ ya sunkuyar da kanshi a ƙasa Duk wannan fa ba Masalaha bace A zuciyar shi yake faɗin haka duba da yadda Ammi take Takura Aliyu akan abubuwa da dama ko lokacin auren su ma shi direct daya kawo sakina Ammi bata musa ba Amman shi Aliyu daya kawo wata Najuwa wadda sukai B.U.K tare da ita yace ita zai aura Fafur Ammi ta rufe ido tace bata yarda ya auri Najuwa ba, Haka yace yana son wata ƴar nan galadanci itama Ammi taƙi daga haka yay fushi yace shi yama fasa auren kwata kwata katsam Ammi taje gidan Yayarta dake fagge ta kawo masa babbar ƴarta Mami tace ala dole sai ya aureta Duk da ba wani sonta yake ba amman haka ya auri yarinyar.
"Ammi Wannan fa duk ba Mafita bace, Kowa yana son yayi aure dan ya haihu shima ya sami ɗansa na kanshi tunda Mami tana da matsala wajan ɗaukar ciki yakamata abar shi ya ƙara aure wataƙil Allah ya bashi rabon a jikin wata"
Ammi ta sunkuyar da kanta ƙasa kafin tace.
"Mami yarinya ce mai ladabi ka duba dukkan Mu babu wanda bata ganin darajar shi, uwa uba mahaifiyarta ma mace ce mai son zumunci, bana son ya auro wadda zata tarwatsa mana gidannan sannan yadda matan nan suke da wankakken ido ba kowacce bace zata aure shi dan Allah wata ma dan dukiyar shi zata aure shi, Muyi addu'a Allah ya bawa mami dan ita ce tamu Kome zata zama agidannan tamu ce ba bare ba"
SadiÆ™ yabi Ammi da kallo ya kasa fahimtar maganar Ammi kawai yadai fahimci Ammi tana tsoron kada Aliyu ya auro matar da yake sone tazo ta rabasu shiyasa ta aura masa mami sabida tasan baya son mami biyayyace yake mata sannan kuma bayan haka tasan kome mami zata zama ta tace tunda Æ´ar yayarta ce.
Sallama yayi mata ya nufi masaukin shi ya kwanta Cike da tunani kala kala sai da Asubahi suka haÉ—u da Aliyu a masallaci.
Cikin barkwancin da yake jan Ya sadiÆ™ dashi dan in kana son kaga Aliyu ya sake sosai to SadiÆ™ na wajen sabida shaÆ™uwar da sukai da SadiÆ™ Aliyu baya Æoye wa SadiÆ™ komai nashi kamar yadda Shima sadiÆ™ É—in baya É“oye masa tun asali basu da abokai awaje su biyu ne aminan juna wanda ko Ammi bata san wani sirrin nasu ba.
"Ah Babban yaya kaine agidan namu?"
Aliyu ya faÉ—a yana murmushi.
SadiÆ™ yace.
"Ba dole ka ganni ba tunda kai min waya hankalina bai kwanta ba wallahi yaya mamin?"
Aliyu yayi murmushin gefen baki haka suka jera zuwa sashin Ammi a falo sukai zaman shan baƙin shayi har wajan takwas suna tare da sadiƙ Aliyu ya miƙe yaje yay wanka ya dawo cikin shirin tafiya Bashir ya fito Musa ne ya kaisu airport Bayan sunyi sallama da Sadiƙ wanda zai je ya dubo mami sai ya wuce lagos shima..........
AUTA 09022260850
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
     Â
      *NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
           *004*
Baƙa ce sosai irin baƙin nan mai ɗaukar ido dan fuskarta har maiƙo take yi ga wasu ƙuraje da suka cika fuskar tata ƙananu Tana da Ƙananun ido marasa girma da gajeran hanci ba zaka sanya ta cikin Mata masu tsananin kyawu ba Bata da tsayi sosai ƴar ƙarama ce kamar zaka hureta ta faɗi sabida ƙanƙantarta sai dai daga samanta acike take dam haka zalika ƙasanta ma ta wajan hips ɗinta a cike yake dam amman tafarar ɗaya ba zaka hango hakan ba har sai ka ƙura mata ido Tana da wani irin jiki Wanda ake ce masa karuwan Jiki mai ɓoye halittar jikin mutum, Yanayin jikinta shiya ɓoye mata shekarunta wanda tana cikin shekaru Ashirin da huɗu da haihuwa amman in ka dube ta sai kace ƴar shekaru goma sha shidda zuwa sha bakwai ce, sabida ƙanƙantarta yawanci Ƙawayenta basa kiran sunanta sai dai suce mata bakwaini wannan suna In taji sun gaya mata shi faɗa ake da ita sosai sabida kowa yasanta bata barin kota kwana ƴar hayaniya ce FARHA kenan wadda sunan ta na Asali shine Fatimah Ƴar gidan Malam Abubakar Mai Bulo dake Ɗandago wanda jama'a kewa gidan laƙani da gidan Cida kai ko gidan yawa sabida tsabar yawan ƴaƴan babansu Malam Abubakar mai Bulo shine tasa kowa a gidan yake fafutukar abin da zai ci dan tuni Mahaifin nasu ya sallamawa kowa ce mace nauyin kanta ita da ƴaƴanta sabida tsabar yadda nauyi da rashi yayi masa yawa Mata uku ne agidan su Farha Babar su Hadiza Nada Ƴaƴa Goma Babar su Ruƙayyah nada ƴaƴa Goma babarsu farha nada Ƴaƴa Biyar Gaba ɗaya ƴaƴan gidan su ashirin da biyar ne cif.
Malam Abubakar mai bulo mutum ne mai son ya kyautatawa iyalinshi ada sanda yana dashi anji daɗi agidanshi dan wadatar sa ma ita ce ta saka ya tara mata har uku da ƴaƴa batare daya ji wata shakka ba, sai dai yau da gobe ga girma ga nauyi yasa abubuwan suka caɓe masa hakan tasa yaja tagumi ya zubawa matan sa ido yanzu haka suke buga buga dan asirinsu ya rufu wani bin inya sa mu yakan ƙoƙarin wajan yaga ya kawo gida mai girki ta sarrafa sai dai akan Shinkafa Rabin kwano ana iya bawa hammata iska acikin gidan Musamman da Farha wadda ita bataƙi tai dambe da ɗan ƙaramin yaro akan shinkafa loma ɗaya ba, in suna faɗa akan abinci agidan tamkar basu taɓa cin abincin ba haka suke cika gidan da hayaniyar su har maƙota sai sun shigo rabo ga matan ko wacce ba haƙuri daga ana faɗan kowacce ɗanta take tare wa Malam Abubakar mai bulo ( kawu ) mutum ne mai zafi manyan ƴaƴan sa da ike mata ne suna gama primary ya aurar dasu suma sauran ƴammatan sabida yadda zamani yazo ne da ƙyar aka shawo kanshi ya barsu suke karatun bokon waɗanda suke duk ƙannen farha ne Don ita farha ma ta kammala karatun ta a F.c.e kano inda ta sami diploma a ɓangaran mass communication kuma Cikin ikon Allah ta sami nasarar amsar result ɗinta wanda bata da wata matsala sabida tana da hazaƙa sosai, amman in kaga ƙannen farha sai ka rantse Yayinta ne.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.