Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: RABO YA RANTSE.txt
Chapter 19 of 21
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
           *16*
Tana zuwa gaban shi ta zube a ƙasa tana sakin marayan kuka, Hankalin shi a matiƙar tashe ya tsugunna a gabanta ya sanya hannun shi ya kamo Tattausan hannunta ya zuba mata Girman idanun shi batare daya ce mata ko mai ba sai binta yake da kallo kamar zai cinyeta ɗanya.
Kukan take Babu ƙaƙƙautawa Tuni Kan Aliyu ya fara juyawa in da abin da yafi tsana a duniya bai wuce kukan mace ba sabida tafarar ɗaya yake sanya masa Rauni.
Da ƙarfi ya damƙe hannunta wanda Hakan ya sanya ta sakin wata irin ƙara tana yarfe hannun sabida tun Dukan da umma tayi mata take zaton Hannun nata Ya sami targaɗe.
Kula da yayi hannun na mata zafi ya sanya shi ya sakar mata shi.
"Shiii Be quiet and let's talk"
Ya faɗa yana sakin numfashi mai ƙarfi.
Sannu a hankali take rage sautin kukan nata kamar yadda ya buƙata.
Muryarshi can ƙasan maƙoshi ya furta mata.
"What made you cry?"
Goge idanunta take da hannunta mai lafiya muryar ta a dashe ta soma yi masa magana.
"Kawu ne yace in baka aiko an É—aura min aure da kai gobe ba, zai ba dani sadaka"
Aliyu ya zare ido with full surprise.
Kafin yayi magana ta cigaba da cewa.
"Tun jiya umammu take dukana har targaÉ—e tai min"
Tana faÉ—in haka ta kuma fashe masa da kuka.
Yayi ƙasa da murya kamar mai raɗa Ya ƙara matsowa gaban ta a yadda yake a tsugunnen.
"Duka garin yaya akai haka? dama shi kawu ya sanni ne?"
Ƙunshe fuska tai Cikin jin kunya tace.
"Dan nace bazan auri Salim ba"
Cikin Tattausar Muryar shi yace.
"Dalilin ki? kodai kina sona ne kema?"
Ƙasa tai da kanta ta ɓoye fuskarta da hannunta wanda ya bashi tabbacin zargin dake zuciyarsa na ta bijirewa mahaifan tane akan shi.
Ya saki wani ƙasaitaccen Murmushi ya Leƙa fuskarta data ɓoye.
"Baki sanni ba Fatima, Ko sunana bani tunanin Kin sani bare anguwar mu bare sana'ata kawai tashi ɗaya ki bijirewa wanda da bakin ki kika ce tun kina ƙarama yake miki hidima Why are you doing this, Fatima?"
Ya faɗa mata hakan cike da mamakin ta tare da jinjina girman wauta da ƙuruciyarta.
Muryarta har zuwa lokacin bata Dawo daidai ba may be kukan data sha ne yayi Mata haka da muryar tata.
"Bawan Allah! Koda acikin Bukka kake rayuwa namun daji suna kewaye ka ni zan bika mu rayu tare, Ni dai na san ba zaka cutar dani ba, Kawu yace in baka aure ni ba zai bada ni sadaka kuma kai da bakin ka kace kana sona zaka aure ni"
Shuru Aliyu yayi gaba ɗaya ta gama kashe masa jiki da kalamanta wani irin tausayi yarinyar ta bashi amman daya tuna yadda tai jagora wajan ɓata sunan shi sai ya kawar da tausayin nata a zuciyar shi, Amman kuma mamakin yadda tace tana son shi batare data san koshi waye ba, abin ya bashi mamaki sau da dama yasha Cin karo da ƴammata su tare shi suce suna son shi wanda duk ba domin Allah bane sai dan kawai yana da kuɗi amman ita ta miƙa wiya ko sunan shi bata sani ba amman ta bashi dukkan zuciyarta.
"Kukan ya isa fatima, kawu É—in gobe yace?"
Da sauri ta É—aga kanta.
"So nake ki min magana da baki bana son magana da ka"
Ta fahimci yana da son a girmama shi.
"Eh haka yace"
Shuru ya kuma yi gaba É—aya kanshi ya É—auki zafi.
"Tom shikenan kice masa zan turo ƙanin mahaifina goben, Amman ni bani da abokai Kuma ni bazan zo wajan ɗaurin auren ba amman zan turo Waliyi na tare da sadaki hakan yayi?"
Ga mamakinsa sai yaga ta saki ranta har tana murmushi batare data tambayi ina zai kaita ba.
"Fatima baki tambayi ina zan kaiki ba inna aure ki?"
Fuskarta cikin farin ciki tace.
"Nina san ba zaka cutar dani ba"
Murmushi ya saki na dole dan ya ɗauki alƙawari mai wiyar cikawa.
"Tashi Muje a gyara maki hannun sai na maido ki gida"
Ta zaro ido wanda hakan ya ƙara fito da kyanta wanda ba kowa ne yake gane hakan ba.
"So kake ai gunduwa gunduwa dani agida"
Ya wani kashe mata ido É—aya.
"To niba mijin ki bane,Hurry up and let's go back"
Miƙewa tsaye yayi kafin ta tashi har yay tafiyar shi bin bayan shi tayi Allah yasa har suka je bakin layin basu ga kowa ba ya buɗe mata front seat ta shiga shi kuma ya shiga driver seat Lumshe idanu tai Sabida wani mahaukacin sanyin Ac tare da ƙamshi daya cika motar ita sai tace tunda take a rayuwa bata taɓa ganin mota mai kyan wannan mota ba, ( hhh to farha ai masu abu da abun sune da mai kamfanin madaki motors kike tare a rashin sani ) tafiya suke kamar ta kurame shi yana can duniyar tunanin dalar daya ɗaukowa kan shi ba gammo, ita kuma sanyi da ƙamshi da fargabar gida sun sa tai tsuku.
Jifa jifa yake É—aga wayarshi wanda duk maganar da yake bada hausa yake yiba da turanci yake yinta.
A daidai ƙofar Ɗan agundi Yayi parking ya kashe motar ya ɗauki face mask ya saka wadda ta lura kamar sakata ya zama ƙa'idar shi.
"Muje ko"
Daga haka ya sauka daga cikin Motar.
Yayi gaba tabi bayan shi gidan sarkin Ɗori Suka shiga kai tsaye ɗakin dake soron gidan ya shiga bayan ya tuɓe takalman shi Dattijo suka tarar a zaune yana shan shayi Suka gaisa dashi Aliyu yace.
"Na kawo ta Baba a duba hannun ta"
Dattijon ya aje Kofin shayin.
"Allah sarki yarinyar kace kenan? matso mugani jikata"
Aliyu yayi murmushi yana ayyana lallai ƙanƙantar Yarinyar tayi yawa.
Farha ta ƙarasa gaban Dattijon.
"Ki cire hijabin ki fito da hannun"
Da sauri Aliyu yace.
"A,a zata fito dashi a haka ai yana da hannu, Fatima fito dashi ta cikin hannun shi"
Tayi yadda yace É—in.
Addu'a Dattijon yayi Kafin ya cafki hannun da sauri yana Matsa shi.
"Wayyo Ummata Washhh zafi"
Ta faÉ—a tana cije bakin ta.
Kafin a gama Gyaran ta gama Jigata da gumi da hawaye.
Ana gamawa ta sunkuyar da kanta tana Kuka wiwi
Aliyu ya cire kuÉ—in da bai san adadin yawan suba ya aje wa Dattijon.
Godiya dattijon yayi tare da cewa.
"Wannan yarinyar taka akwai rigima bari na shiga daga ciki Allah ya bata lafiya.
Daga haka ya miƙe ya fita daga ɗakin.
"Ki shuru dare nayi, Ki tashi na kaiki gida"
Kukan take bata kula shi ba.
Ya miƙe tsaye ya nufi hanyar fita.
Da sauri ta miƙe agarin saurin ta take Hijabinta aiko ta faɗi ƙasa tim.
Cikin azama ya juyo ya É—agota.
"Kema gaki ƙarama kina sanya wannan abun yayta kayar dake"
Hijabin ne ya cukurkuÉ—e dole ya sanya hannu ya zare mata shi yana warware wa.
Farha tai saurin sanya hannu tana kare Jikinta sabida daga ita sai doguwar rigar atamfa wadda ta kama jikinta sosai Daga saman Ƙirjinta ya bullutso yayo sama dama duk ƙanƙantar ta Allah ya bata sama da ƙasa ba laifi kuma masu fusgar hankali.
Aliyu cikin mamakin Halittar Jikinta wadda ya kalla a rashin sani lokacin daze miƙo mata hijabin Ya bata Hijabin Ya fita daga ɗakin Har ya ƙarasa Cikin mota tana laƙai laƙan tafiya Haka ta shigo Cikin motar duk kunya ta gama kamata.
"Raguwa sarkin raki"
Ya faÉ—a batare daya kalleta ba yaja motar suka bar wajan, a wani haÉ—aÉ—É—an restaurant yay parking.
Ya juyo ya kalleta.
"Wait for me, I'm coming now"
Daga haka ya buÉ—e motar ya fita.
Minti kusan goma sai gashi nan da Ledoji Manya guda Biyu a hannunshi ya zaga Back Seat ya aje su.
Sannan ya dawo ya shiga motar ya zauna ya tayar da motar suka cigaba da tafiya idanunshi akan kwalta.
"Are you waiting for me? be patient"
Taji muryar shi acikin kunnenta ba tare daya kalle taba.
Har suka Ƙarasa bakin layin su.
Babu wanda yayi magana acikin su.
Ya kashe motar ya Fita ya kwaso ledojin Itama ta fito.
"Muje na rakaki"
Ya faɗa, tana gaba yana binta a baya har suka ƙarasa bakin Ƙofar gidan wanda yayi daidai da lokacin da kawu ya fito daga gidan.
Farha taja da baya ta koma bayan Aliyu cike da tsoro.
"Bawan Allah ga kawu nan na shiga uku"
Ga mamakinta sai taga ya tunkari kawu ba tare da wani tsoro ko fargaba ba.
Ba tada zaɓin daya wuce tabi bayan shi haka tabi bayan shi kamar kazar da ƙwai ya fashewa aciki.
Har ƙasa taga tsugunna yana gaida kawu.
Da gudu tayi cikin gida Kai tsaye É—aki ta nufa ta haye saman gado.
Jim kaɗan kawu ya shigo yana ƙwala mata kira.
Jiki na rawa ta fito ta tsugunna a gaban shi.
"Allah ya taimake ki, Gobe zasu zo a É—aura aure amman ki sani duk abin da ya faru dake kada ki nemi gidana"
Daga haka ya juya yabar wajan.
Tana shiga É—aki Zuhuriyya ta biyota da ledoji.
"Wai gashi inji wani a waje yace wai Allah ya baki lafiya"
Umma ko kallonta batai ba jiki a sanyaye ta É—ebe ledojin ta shige É—aki.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.