Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: RABO YA RANTSE.txt
Chapter 2 of 21
Bai tashi ba sai gab da magariba ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ya sanya jallabiya fara ƙal yay ɓarin turare mai kamshi sosai ya fita masallacin dake harabar gidan nasu yaɗan sami nutsuwa anan ya dinga Gaisawa da ma'aikatan gidan daga nan ya wuce part ɗin Ammi sai dai bai same ta ba wai tana asibiti cewar ƙannen shi ƴammata sajidah da safnah daya tarar suna kallo a parlo suma dawowar su daga makaranta kenan inda suke karatu a jami'ar bayero dake kano suna lavel 2
Cikin wata ƙaramar honda civic fara ya shiga
A hankali yajata yana driving kanshi bayan ya sanya p cap ya kare fuskarshi sabida gudun idanun jama'a Masu gadi suka hangame ƙaton gate ɗin gidan ya fita da motar dandazon matasan daya gani a ƙofar gidan ne ya bashi mamaki da gudu yaja motar yabar harabar gidan yana gudun kada su gane shine cikin motar.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarasa asibitin yay horn aka buɗe masa gate ɗin ya shiga cikin harabar asibitin yay parking motar ya fito gudu gudu sauri sauri ya shiga ɓangaran da aka kwantar da Mami matar shi Ya tura ƙofar ɗakin ya shiga ciki tana kwance har Lokacin ga ledojin ƙarin jinin da akai mata sun ƙare an cire Ammi zaune ita da Maman Mami sai ƙannen Mami ɗin duk sun yi tagumi Kallo guda zaka ma Maman Mami kaga suna yanayin kama da Ammi kasancewar yayarta ce Mahaifin su ɗaya.
ALIYU ya tsugunna ya gaida Maman Mami wadda ta amsa mai cikin kulawa tana mai tashi ta fita daga ɗakin Ammi data masa kallo ɗaya itama tabi bayan maman mami sauran ƙannen Mami miƙewa sukai suka fita ɗakin yayi saura daga ALIYU sai Mami dake kwance a saman gado.
*Idan kina buƙatar na tallata miki kayan siyarwar ki a ƙasan shafikan littafin nan kimin magana kai tsaye duk shafi 2 500 naira ne 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
     Â
      *NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
           *002*
Cikin sanyi jiki ALIYU ya ƙarasa Bakin gadon da Mami take kwance ya zauna a gefenta, Hannun shi mai taushi ya sanya ya tallafo kanta ya ɗora saman jikinshi ya zuba mata ido tsananin tausayinta ne yake ratsa masa cikin zuciyarshi wanda har yake huda dukkan sassan jikin shi.
Mami idanunta ta lumshe wanda ruwan hawaye ke ta firfitowa da gudu babu ƙaƙƙautawa a wannan karon raunin ta yafi na ko da yaushe bayyana wanda ganin hakan ya ƙara Razana Aliyu sosai ya firgita da yadda yaga ruwan hawayen dake fitowa daga idanun mami Sai dai tsabar kawai ci bai sanya ya bayyana wannan razana tasa a fili ba.
"Kiyi haƙuri Mami, wannan kukan bai da amfani"
Aliyu ya faÉ—a cikin tattausan lafazi.
Ta ɗago ƙwayar idanunta wadda tai jajir ta kalle shi tana mai ɗauko hannun nashi ta ɗora akan cikinta muryarta wadda ta dashe sabida tsabar kuka ita ke shiga cikin kunnen shi.
"Yayah Aliyu wannan karon ma cikina ya zube, cikin dana ƙwallafa raina akan shi cikin da nake mafarkin na haife shi....."
Sai ta kuma fashewa da kuka!
"Shitt!"
Ya É—ora yatsun sa a saman bakinta ya lumshe manyan idanun shi aran shi yana jin dama shima zai sami damar kukan daya koka dan yaji sanyi acikin zuciyar shi.
Muryar shi mai cike da taushi nagarta gami da haiba ita ke fita ƙasa ƙasa kamar yana yin raɗa, dama shi tun tuni bamai buɗe murya bane in zai yi magana.
"Mami ki shuru wannan kukan naki yana ƙara min zafi acikin zuciyata, Allah ne ya bamu ya kuma nufa bamai rayuwa bane shiyasa ya amsa mu duka haƙuri zamu yi"
YafaÉ—a cikin dakiya da jarumta.
Ƙofar aka turo da sauri Mami ta sauke kanta dake jikinshi ta gyara ɗaurin ɗankwalinta Maman ta ce.
Cikin alkunya ta ƙaraso Wajan su taja kujera ta zauna wanda Aliyu yay tsam ya miƙe yana sosa kanshi.
"Aliyu sai fa haƙuri mami taƙi kwantar da hankalin ta, Ni ina ganin wannan kukan kamar harda wauta sabida ba wanda ya isa ya tsaida Allah acikin dukkan al'amuran daya riga ya saukar"
Aliyu ya saki murmushin daya fi kuka ciwo.
"Mama ki barta tai kukan May be, zata ji relief acikin zuciyarta"
Yana faɗin hakan yayi saurin barin ɗakin Ya fita waje ya sami Ammi zaune a saman kujera tana ganin shi ta miƙe.
"Bara nayi musu sallama sai mu wuce"
Daga haka ta kama handle ɗin ƙofar ta shiga Maman Mami tana ta aikin rarrashin Mami Ammi tai musu sallama ta baro ɗakin.
Ƙannen Mami cike da ladabi sukai wa Aliyu sallama, Maman Mami har wajan Mota ta biyo Ammi suna ƙara tattaunawa wanda Maman Mami sai mita take na yadda Mami duk tabi ɗaga hankalin ta.
Ammi ta shiga motar wadda Aliyu ya buÉ—e mata Ta zauna sosai sannan shima ya shiga Bisimillah É—auke a bakin shi yaja motar yana É—agawa masu gadi hannu suka buÉ—e masa gate É—in ya cillah hancin motar shi titi.
Motar tayi shuru Ammi ce ta katse shurun nasu ta hanyar ce masa.
"Kadai ci abinci amman kafin ka tawo nan?"
Ya shafa kanshi kamar koda yaushe yace mata.
"A,a ina son sai nayi sallar isha'i sannan sai na É—an haÉ—a coffee In sha dan ina son gobe da sassafe zan je Abuja"
Ammi tai jimm kafin tace.
"Ya Kamata ku ƙara komawa wajan wannan Likitan Na ƙasar india akan matsalar ɓarewar cikin nan na Mami ni abinnan har tsoro yake bani ace daga ta samu ciki ana murna kuma sai aga ya ɓare ba wani dalili"
Ta cikin Madubi ya dubi fuskar Ammi wadda ta bayyana da damuwa ƙarara.
Cikin nutsuwa ya furta.
"Ammi babu wata dubara da za'ai akan abin da Allah ya ƙaddara bamai rayuwa bane, wannan rubutu ne tun asali haka Allah ya ƙaddara in muna da rabo Allah zai bamu"
Ammi tana jinjina wa Aliyu ta ɓangaran tawakkali bai taɓa dangana matsalar matar shi da wani abu ba ko wancan karon ma ita ta tilasta musu fita ƙasar india akan matsalar ɓarin da matar sa ke ta samu amman shi koda yaushe faɗin sa ɗaya shine Komai muƙaddari ne daga Allah.
"Shikenan Allah ya baka wani mai albarka ya kuma inganta"
Ammi ta faÉ—a a hankali.
Shima a ƙasan laɓɓansa ya amsa da.
"Amin"
Motar ta ɗauki shuru titin nasarawa gidan gwamna dama ya gaji haka har suka ƙaraso cikin gari babu wanda ya kuma magana acikinsu dama shi bamai yawan magana bane yawanci shurun sa yafi maganar shi yawa shiyasa wasu ke masa kallon Miskili.
A daidai ƙofar gidan shi yayi parking wasu matane cunkus wasu da goyo wasu ma sunyi bacci akan dakalin Ƙofar gidan Ammi takai duban ta ga matan.
"Kasan dai wannan duk jama'ar kace nidai taimaka ka shigar dani sai ka fito"
Yayi lallausan murmushi ya danna Horn masu gadi suka wangale masa ƙaton gate ɗin ya tura hancin motar shi zuwa harabar adana motocin gidan yayi parking da sauri ya fito ya buɗe wa Ammi motar ta fito ya take mata baya har zuwa part ɗinta.
A parlon ya tsugunna har ƙasa ya dube ta.
"Ammi zan fita na sallami matan waje ko kina buƙatar wani abu ne?"
Ammi taji wani irin farin ciki ya nunku acikin zuciyarta ciki da kulawa tace.
"A,a kaje Allah yayi maka albarka"
Ya miƙe bai koma part ɗin shiba ƙofar Gidan ya koma Da sauri matan suka miƙe suna gaishe dashi babu ƙyama bare nuna cewar shi mai kuɗi ne ya janyo kujerar roba fara ya zauna yana facing ɗin matan.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.