Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: RABO YA RANTSE.txt
Chapter 12 of 21
Ya koma ya zauna a saman kujerar da take facing É—in wadda Ammi take zaune akanta.
"Wannan wace irin magana kake Babana? yanzu ace kai kana a matsayin Mijinta ka kasa leƙawa ɗakinta har ka kwana ka wuni agidan amman baka san ko ta dawo ba ko bata dawo ba?"
Ya ɗaga butar shayin ya tsiyaya a kofi sai faman turiri yake yi da zafin da komai yake kurɓa yana lumshe ido zafin na ratsa mai ɓargon Jikinshi.
"Ammi kimin uziri jiya ban shigo ba sai 12 na dare bayan na gama meeting da mai girma gwamna na shiga gidan Radio mun gana da Ƴan jarida, yau kuma kinga shigowata kenan yanzun nan nai sallar isha'i sai yanzu na sami kaina duba ƙarfe kusan goma da wani abu"
Ya faɗa yana ƙara tsiyayar shayin.
"Kaga irin abin da nake nuna maka wannan shine yake ƙara sanyawa nake ƙaunar mami har raina, Sabida ba kowace mace bace zata jure auren irinku sam baka da lokacin kanka, Yarinyar nan bata taɓa ƙorafi ba wallahi bata taɓa kawomin, Ƙarar kaba Kaga Tana gadon asibiti haka fa ka tsallake ka tafi Abuja Bana jin ka dubo ta yanzu kamata yayi kaje ka duba lafiyarta sai ku tawo tare"
Ya lumshe idanu yana sauraran Ammi harta gama maganar tata.
"Ammi tun ina can na mata waya ta dawo tunda bata dawo ba a rabu da ita May be hutawa take, Nidai nasan duk wani haƙƙi ina ƙoƙarin saukewa"
Ammi tabi sa da kallo yana da kafiya duk abin da yace zeyi to baya fasawa.
"Dalilin haka Ammi nake son na ƙara aure Kin san Bahaushe yace mai Mata ɗaya Aminin gwauro, bada ban kin gayan bata nan ba ni kam bamma san bata dawo ba"
Ya faɗa yana murmushi dan tsokanar Ammi yayi da batun zai ƙara aure Aiko nan da nan ta haɗe girar sama data ƙasa.
"Idan ma sabida haihuwa kake son ƙara aure in ka kwantar da hankalin ka kwana nawa ne matarka ta sake samun wani, Tunda Zaku fita India a duba matsalar yawan ɓarewar Cikin nata, kuma nan ma na saka ana ta addu'a kayi haƙuri kada ka ƙara aure sabida ina tsoron matan wannan zamani ba kowace mace bace zata aure ka dan Allah wata ma Da burin ta wargaza gidannan zata shigo ita kuwa mami duk tsiya tamu ce matar Rufin asiri ce duk abin da kake mana bata taɓa ɗaga ido ta duba hakan da suffar baƙin Ciki ba ina burin Allah ya albarkace ka da samun zuri'a daga Mami sabida nagartarta"
Ya jinjina kai duk maganganun Ammi haka suke shima kanshi yana mamakin Mami sam bata da matsala Haƙurinta har yayi yawa tundaga kan Ƴan uwanshi Har zuwa kan Ma'aikatan gidan suna yabonta Duk yadda zai Buzance mata yayi mata masifa inta masa laifi bata ko duban sa haka Duk nacin sa wajan Buƙatar aure bata raki Bare Ta ƙosa.
"Ammi mai ƴa nima dama wasa nake ni yanzu Ɗayar ma Bani da lokacinta bare har Biyu, Ina naga Lokacin ma duba matar Ina nan dai ina addu'a Allah ya bamu ingantacce ƙarshan watan nan ma doctor yace za'a mata ɗaurin mahaifa wanda yace In sha Allah Da zarar an kwance Kuma mahaifarta zata iya ɗaukar Ciki"
Ammi ta washe baki cike da farin ciki tace.
"Allahu yasa Ya Rabbi ya nunan wannan rana, Babana a yanzu ba abin da zance wa Allah sai godiya duk wata ni'ima yayi Min ita Burina naga ÆŠanka Ko Æ´arka A duniya yadda na matsu da wannan burin ban matsu naga auren su Bashir ba, Wallahi bada ban sharrin matan wannan zamani ba dani dakai na zan Ƙara nema maka wani auren a karo na biyu ko Allah yasa a dace, To Ina tsoron Sharrin matan wannan zamani Kuma sannan Mami ba juya bace Æari ne kaÉ—ai matsalar ta shima Allah zai daidaita Gata Æ´ar uwarka ta jini gata da kyawu da biyayya Ni banga aibun taba Sabida haka ka Æ™ara damÆ™e matarka Koda wasa bana son ka kuma min maganar Æ™arin wani aure"
Aliyu yayi Murmushi ya rasa mai Yasa Amminsa ke masifar son Mami wata irin soyayya Ammi kewa Mami sosai, Sannan yana ganin tsoro a fuskar Ammi ƙarara duk sanda yace zai ƙara aure Kullum batun ta akan hakan shine tana tsoron sharrin matan wannan zamani amman mami ita tata ce tasan ba tada Matsala.
Ya miƙe yana zube dukkan hannayen shi cikin aljihun Farar shaddar Jikin shi "Ammi ni zan kwanta mu kwan lafiya"
Daga haka ya juya yabar ÆŠakin Ammi ta bishi da kallon tausayi Duk kawaicin sa wannan karon ya shiga damuwar Æarin Mami.
Koda ya koma ɗaki Shafa'i yayi ya kwanta ko kallon wayar shi da Mami ke faman Kira baiyi ba Daga ƙarshe ma kasheta yayi inta matsu dan kanta ta dawo shikam baze Je ba.
***********
Sukuku Farha ta miƙe yau har umma na ce mata ko ba zata aikin bane jiki ba ƙwari ta Shirya tai sallama da Umma ta fita Gabanta tun Jiya yake faɗuwa Haka ta ƙarasa Tashar tasu Md ya tareta da Murna yau har ɗakin yaɗa labarai ya rakata yana ƙara bata Hope akan Labarin da zata watsa a safiyar yau Ɗin.
Bayan sunyi sallama da Md ta duba doguwar takardar daya Miƙo mata sunan SA na gwamman a ɓangaran Matasa ne ya fita ɓaro ɓaro Jikin takardar.
Murya ta gyara bayan ta maƙala headphone tare da sanya ƴar ƙaramar loudspeaker a bakin ta
Cikin zaƙin Muryarta sautin maganarta ke Fita.
_Barkam mu da safiyar laraba ga labaran namu daki daki karku manta kuna tare da tauraruwar tasharku mai farin Jini GARKUWA RADIO mita goma da ɗigo tara, Da farko zamu fara leƙawa sashin siyasar Kano, zakuji cewa mai bawa gwamnatin jaha shawara ta musamman a ɓangaran matasa Alhaji Aliyu Audu Madaki, Wanda ya Ƙware a fanni bada tallafi taimakon yara mata marayu matasa wanda sunan shi yayi fice tun ma kafin gwamnatin ta bashi Muƙami, Ya ƙara rasa cikin da matarshi ke samu a karo na Huɗu nasan dai mai sauraro zai mamaki tare da aljabin yadda duk cikin da mai ɗakin mai bawa gwamnan shawara take samu yake ɓare wa, To ba abin mamaki bane in ka duba yadda yake shiga da fice da facaka da dukiya wadda wata majiya mai tushe ta tabbatar da Yadda yake salwantar da cikin matar tashi ne ta hanyar bawa matsafa Ƴaƴan cikin domin ai masa tsafi Kuɗinsa ya ƙara hauhawa wanda hakan shine maƙasudin arziƙinsa,wannan kenan sai kuma ɓangaran wutar lantarki wadda ta wadata acikin wannan jaha kada ku manta kuna sauraran wannan labarine daga wannan tasha tamu mai farin Jini dan kawo tallanku ko Gayyatar taron suna biki kuna iya ziyartarmu a shafikanmu na Facebook Ko adireshin mu dake Kan titin audu baƙo way_
Farha ta ƙarasa bayan ta yarfe zufar data wanke mata Jikinta kowa na ɗakin watsa labaran kallonta yake Jiki ba ƙarfi ta ɗauki jakarta kanta ciwo yake mata sai da ta gama labaran ma ta mance Ko sunanta bata faɗa ba Ga wata nadama na Cin zuciyarta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.