Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: RABO YA RANTSE.txt
Chapter 13 of 21
Ko Bitakan Office ÆŠin Md batai ba tayi hanyar titi sabida yadda idanunta ke Lumshewa.
Haka ta koma gida zuwa rana zazzaɓi mai zafi ya rufeta har haɗe haƙora takeyi.
Daga cikin garin kano duk wanda ya saurari labaran safiya na tashar Garkuwa yaji wannan ƙazafi da akaiwa Hasken matasa wasu sun yarda wasu sun ƙaryata kafin kace me labari ya cika gari Ƙofar Gidan Aliyu ya cika dam da matasa waɗanda suka zagaye Gidan domin bashi kariya koda wasu zasu yo zanga zanga dan barazana gare shi, Matasan Ƙofar na'isa kuwa Tuni sunyi zuga zuwa Gidan Radion garkuwa wasu da kalanzir wasu da ashana da taya Ba wata Sanya suka cinnawa Gidan Radion wuta wanda da ƙyar ma'aikatan suka sha Zuwa wani Lokaci gari ya ruɗe ƴan sanda sun cika titina sabida zanga zangar matasa waɗanda suka Fito suka nuna ƙin Goyon bayansu akan wannan ƙazafi da akaiwa Aliyu.
MD da gudawa ya ƙarasa gidanshi ya kasa zaune ya kasa tsaye tsoro nadama suke cin zuciyar shi yasan Ba Aliyu ba hatta ƙungiyar ƴan jaridu ta ƙasa sai ta tuhume shi akan wannan labari da tashar shi ta fitar sabida doka ce ga duk gidan Rediyon da bai tace labari ya tabbatar da ingancin shiba kafin ya fitar dashi, ga shinan son zuciya da bala'in Neman suna yaja masa bala'in da bai san Lokacin fitar shiba.
A guje Ammi ta nufi sashin Aliyu wanda duk ma'aikatan Sashin nasa sunyi cirko cirko wasu ma kuka suke sabida zuwa wannan Lokacin kowa yaji abin da ke faruwa.
Ta ƙarasa falon Musa na durƙushe agaban shi ga sautin maganar mai labaran nan raurau ya karaɗe Falon wanda Musa ya ɗauki Recording ya kunnawa Aliyu.............*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*11*
Zagaye Ƙaton Parloun shi yake hannun shi Goye a bayan shi Sam ba zaka fahimci inda Halin da yake ciki ya dosa ba Idanun shi ya rintse Har yanzu sautin Muryar yarinyar da take Labaran bai bar amsa kuwa acikin Dodon Kunnen shiba.
"Iya sanina bani da abokin faɗa a Wajan sana'ata Bani da Abokin Gaba bani da wanda na taɓa Musayar Harshe dashi a ko ina Why zaku Min haka mai nayi Muku zaku ɓata min suna a idanun al'ummah idan wasu sun yarda wasu ba zasu yarda Ba"
Da sauri ya Zube a gaban Ammi wadda ta tallafe haɓa da hannunta hawaye nabin Idanunta.
Ya kamo ƙafafunta ya ɗora kanshi akansu.
"Ammi ki yarda dani wallahi bani da Hannu a zubewar Cikin Mami, Arziƙi Allah ne yayi Minshi nima ina mamakin Yadda duk abin da na taɓa sai Allah ya saka mai nasibi Ke shaida ce ammi kinsan yadda Muka taso"
Yana fara maganar Muryarshi ta shaƙe ya soma tari da gudu Ammi Ta buɗe Frij ta ɗauko ruwa ta ɓalle Gorar ta fara bashi Musa na masa sannu.
"Nina haife ka Nina san waye kai Allah ya tsareka daga dukkan wanda ya nufoka da sharri Allah ya kare ka daga dukkan sharri"
Ammi ta faÉ—a cikin kuka.
Da gudu É—aya daga cikin masu gadin Gidan ya shigo falon Ammi ta zaro ido tana cewa.
"Sun shigo su kashe min shi ko? ku taimaka Ku Æoye min shi kada a far masa"
Mai gadin yayi Murmushi.
"Hajiya ku godewa Allah, Haƙiƙa baka Alkairi ka taɓe kamar yadda baka sharri ka gama lafiya, Dama zaki fito waje da sai Kin mayar da kukan ki Dariya sabida Ilahirin matasan Dake garinnan sunyi dafifi a ƙofar Gidannan domin bawa mai gida kariya, Yanzu haka mai girma gwamna ya turo da Motocin Ƴan sanda kusan Goma suna nan tsaye da Bindigu domin su bawa wannan Bawan Allah kariya Sannan matasan gari sun Je sun ƙona gidan Radion yanzu haka neman Mai gidan Radion suke ruwa a jallo dan dai basu sami Mutum Ko ɗaya bane daga cikin ma'aikatan sabida kowa ya gudu"
Ammi ta sauke ajiyar zuciya tana shafa kan Aliyu wanda ya kwantar dashi akan cinyarta.
Ya kasa magana Har Ammi ta sallami su Musa Falon yayi saura daga shi sai ita.
"Ka ɗauka hakan wata nasara ce daga Allah in sha Allah hakan ba ze zama sharri gareka ba sai Alkairi kuma bana son kai fushi ka daina taimako wannan ma ya zama ƙara ƙarfin ka wajan taimakon al'umma domin kaga ranar hakan da idanunka inda baka taimako da bamu san yadda abin zai zama ba, amman albarkacin al'ummar Annabi gashi kana ta samu kariya"
Aliyu yaƙi magana sabida zuciyarshi yadda take a karye ta yaya za'a ce shike salwantar da Cikin Mami dan ya ƙara arziƙi ta yaya za'a dangana dukiyar shi data tsafi shida ya sha wahala kafin ya tarata.
Duk yadda ake kiranshi a waya ya kasa ɗagawa Ta ya sadik kaɗai ya ɗaga data bashir waɗanda suka ɗaga hankalinsu akan Labarin da suka ji ya tabbatar Musu da cewa yana lafiya ya kashe wayar sai ta mai girma gwamna wanda ya bashi haƙuri yace kada ya saka abin aranshi hakan ma matakin nasara ce Kuma gwamnati zata ɗauki mataki akan shugaban Gidan radion dan zata binciko shi harma wadda tai labaran.
Bayan ya gama jin jawabin gwamna yayi godiya sai dai yace wa gwamna yabar Batun tuhumar mai gidan Radion shida kanshi zai Bibiyi Lamarin dan ya É—auki matakin daya dace sosai sukai magana da gwamna kafin yayi masa sallama bayan yace ga Jami'an tsaro nan ya Turo masa dan su kare lafiyar shi data iyalin shi yayi Godiya ya katse wayar.
Yawan ƴan jaridar dake ƙofar Gidan ya kai ya kawo dan ƴan jarida kamar su fasa gidan su shiga su ɗauko rahoto haka suka taru ga jama'a kota ina wannan tasa aka rufo gidan ma gaba ɗaya ya zama ba shiga ba fita daga gidan Madaki ma sosai ƴan uwan su Aliyu suka girgiza nan da nan Baba Usman Ƙanin Mahaifin Aliyu ya saka malamai aka hau sauke alkur'ani mai girma.
Mami kuka take tana kiran layin Aliyu dan hankalinta gaba ɗaya yana kanshi Ko kaɗan bata yarda da wannan labari ba sabida tasan waye Mijinta har ya fita damuwa akan asarar Cikin da suke yi Suma gidansu Mami sai rufe Ƙofa sukai sabida Yadda jama'a ke dafifin shigowa jaje.
Yana rangaji ya miƙe da sauri Ammi ta taimaka masa ya haye saman shi ya faɗa saman gado yana Lumshe idanunshi Ammi ta rufo masa ƙofar Ta nufi sashin sa da ƙyar ta rarrashi su sajeeda waɗanda suke Kukan abin da aka wa yayan nasu.
Wayar shi dake Ringing a karo na ba adadi ya laluba ya É—aga Muryar mami ke sauka cikin kunnen shi.
"Yaya dafatan kana lafiya? wallahi ni na yarda dakai Mijina sabida haka ka kwantar da hankalin ka wannan shiri ne na maƙiya"
Da.
"Umm"
Ya amsa mata ya kashe wayar yayi shuru yana sauraran Bugun zuciyar shi.
Ƴan jarida da sauran jama'a gajiya sukai suka bar ƙofar gidan har zuwa dare ba aji ɗuriyar shiba amman an tabbatar yana cikin Ƙoshin lafiya dama shi haka tsarin sa yake in yana cikin damuwa shuru yake In yana cikin ɓacin rai shuru yake ya killace kanshi wannan tasa Ammi bata sake komawa wajan shi ba tasan yana tunanin mafita ne na wannan matsala data afko masa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.