Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: RABO YA RANTSE.txt
Chapter 3 of 21
Ta farko ce ta ƙaraso gaban shi.
"Yallaɓai tunda ga ɗorayi unguwar Bello na tako da ƙafata ina fatan Allah ya haɗani da kai mijina ne ya rasu ya barni da marayu bakwai ina sana'ar wankau yau da gobe sanyi yaci ƙarfin jikina ina ta wahalar magani ga yarana ƙananu ne, takai ta kawo bamu da abin da zamu ci"
Ya dube ta kullum a cikin irin waÉ—annan al'amura yake kashe lokacinsa.
"Tom shikenan zan baki jarin da zaki sami abin da zaki dogara da kanki sabida ki taimaki yaran ki, ba zan baki kuɗin da bazaki sana'a dasu ba dan zan kashe miki zuciya kuma kinga in yau mune gobe bamu bane ba ina ganin na baki abin da zaki tsaya da ƙafafun ki yafi na baki kuɗin da zakici abinci"
Ya faÉ—a cikin muryarshi ta dakakkun Maza.
Nan da nan matar ta soma goge hawaye.
"Allah yayi maka albarka, Allah yasa ka gama lafiya, naje gidajen masu kuɗi yakai talatin da wannan buƙatar babu wanda ya dube ni, tabbas in da za'a sami jajurtattu irinka da yawa acikin al'ummah da tabbas bara da sace sace da maula da sun ƙare Allah yasa kafi haka"
Murmushi yayi kawai ya É—aga mata hannu batare daya ce komai ba.
Ta biyun itama ta matso gaban shi.
"Ni kuma mijina ne, yake aikin saka roɗi agarin ɗora dakin gaba ɗaya ginin ya faɗo masa sama da shekara biyar yana kwance yana jinya duk abin da muka tara ya ƙare"
Ta faÉ—a tana kuka.
"Share hawayen ki Allah ya bashi lafiya"
Ya faɗa da tausayawa A hankali sauran matan keta ƙaraso wa gaban shi ko wacce da kalar tata damuwar.
Sai da ya gama dasu sannan ya miƙe ya shiga cikin gida jim kaɗan ya fito Da leda a hannun shi ko wacce sai da ya sanya wani daga cikin masu hidimar gidan ya ɗauki sunanta da kwatancenta aka rubuta akan kuɗin da zai bata Kuɗi ne masu kauri ya babbasu yace ko wacce taje ta sami sana'ar da zata tsaya da kanta.
Aliyu yasha godiya wajan matan ya miƙe da kujerar da ya zauna ya shiga cikin gidan yana mai jin farin ciki a zuciyar shi burin sa kullum ya bayar shiyasa Allah bai taɓa hana shi ba.
Yana ƙoƙarin shiga sashin sa Musa dake zaman jiran shi yasha gaban Shi yana rage tsayin sa.
"Musa mai kake har yanzu baka tafi wajan iyalin kaba?"
Musa ya shafa kai yana zaro wayoyin Aliyu daga Aljihun sa.
"Yallaɓai dama wayoyin kane a waje na"
Ya miƙa masa, sallama sukai da Musa Ya kama hanyar part ɗin shi.
Yana shiga wanka yayi ya sauya kaya zuwa singlet da boxer ya sauka ƙasa sanin ba wani ma'aikacin dazai shigo masa Parlo a wannan lokacin tunda gejin su daga magariba ne zuwa Bayan magariba sun jere musu abinci sun bar part ɗin sun koma nasu sai kuma da safe.
Ya shiga kitchen ya haɗo coffee a cup sai turiri yake yana daga tsaye ya shanye shi tas ya aje cup ɗin ya koma saman shi alwala ya ɗauro yay sallah isha'i tare da shafa'i Wuturi sai ya tashi cikin dare ya idar ya jima yana addu'a sannan ya shafa ya cire kayan jikin shi yayi saura daga shi sai dogon farin wando wanda dama baya saka riga in zai kwanta bacci ko takan wayoyin shi baibi ba ya zube su a gefen gadon shi.......*Idan kina so na tallata miki kayan sana'arki a ƙasan shafukan littafina Duk shafi biyu 500 naira kimin magana kai tsaye domin a fara tallata miki hajarki*
09022260850
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*003*
Pillow guda ɗaya ya matse a saman ƙirjinshi bai rufa da komai ajikin shi ba, dama haka tsarin shi yake duk sanyi baya rufa idan yana bacci kuma baya sanya riga iya kacin shi dogon wando kaɗai, baccin shi yake cikin nutsuwa sabida yadda gajiya ta zirga zirga ta kashe masa jikin sa damma namijin duniya ne wajan gwagwar mayar rayuwa.
Ammi ta ƙarasa bedroom ɗinta bata zauna ba alwala ta ɗauro ta fito daga Toilet Sadiƙ Yayan Aliyu, Aliyu shike bin sa yana zaune a Garin lagos yana kula da kamfanin ALIYU na lagos,Tare yake zaune da matar shi acan Aunty sakinah da yaran shi guda uku mata, yayi sallama cikin ɗakin nata.
Fuskarta a sake ta amsa tana cewa.
"Kaikuma zuwan dare kayi kano kamar korarre"
SadiÆ™ ya shafa kai yana dariya.
"Hajiya Ammi tamu, to ki fara bani abinci naci sai muyi maganar data kawo ni"
Ammi tayi murmushi.
"Bari nai sallah tukunna sai na ji dakai"
Ta shinfiɗa darduma a nutse take sallar wadda taja lokaci mai tsayi dama Duk sun san yadda sallar Ammi take ɗaukar Lokaci Sadiƙ har sai da yakai ga yana gyangyaɗi a ƙasan carpet.
Muryar Ammi yaji.
"To sarkin bacci tashi mu fita daga falo sai kaci abincin"
Ta faɗa tana fita daga ɗakin Sadiƙ ya bita suka zube nan ƙasan carpet.
"Lah Yaya SadiÆ™ yaushe ka shigo bamu sani ba?"
Cewar sajeeda wadda ta buɗe ƙofar ɗakinsu ta fito tana murnar ganin sadiƙ sabida shi mai barkwanci ne da sakewa ba irin Ya Aliyu ba mai tsare gida sam in ya shigo sashin su basa sake wa har sai ya fita.
BuÉ—e hannunshi yayi yana dariya yana cewa.
"Zo mana autar Ammi ina safnah?"
Da sauri sajeeda ta ƙarasa jikin Sadiƙ ya rungumeta suna dariya Muryar Bashir Ce ta karaɗe Falon shima Dariyar yake shigowarshi kenan gidan.
"Babban yaya kaine da tsohon daran nan?"
Bashir ya faÉ—a yana dariya.
SadiÆ™ yace.
"Ina naga ta zama mai gida ya kirani É—azu naji muryar shi babu daÉ—i dama kullum abu a cunkushe babu fuskar far'a"
Bashir dariya ya saki sabida yasan da wa yake yana nufin Ya Aliyu.
Ammi ma dariyar tayi tana cewa.
"Ina ruwan ubana nina rasa wannan rashin far'a na wa ya É—ebo"
SadiÆ™ yayi dariya yace.
"Ammi ke ya gado danni Ammi wani bin in kika É—aure fuska wallahi har tsoron yi miki magana nake"
Gaba ɗaya Falon dariya aka saki Ammi ta ɗauki Pillow ta jefawa Sadiƙ Ya cafe yana dariya Safna ta fito itama Tafiya tai wajan Ya Sadiƙ tana Murnar ganin shi dan shi yake iya ɗaukar duk sangartar su saɓanin Aliyu da yake cin Ubansu babu sauƙi.
Ammi ce ta miƙe ta nufi kitchen ta haɗowa sadiƙ abinci yana ci ana hira har wajan Sha ɗayan dare Bashir ne ya fara miƙewa yayi musu sallama sabida Gobe zasu je Abuja shida Aliyu dan duba wasu motoci da aka kawo sabbi kamfanin Aliyun na can.
Su safna kuwa anga yaya sadiƙ ai sai ma miƙe ƙafa da sukai suna ta zuba masa zance kala kala suna bashi labarin makaranta shi kuma sai jansu yake yana ta sakin far'a Ammi wani irin daɗi take ji aranta gaba ɗaya ƴaƴan nata kansu a haɗe yake haka suke in sunga junan su kamar su haɗiye kansu Aliyu ne kaɗai bai da sakin fuska sai dai shi ɗin yafi dukkan Ƴaƴanta son ƴan uwanshi Kawai miskilancin sa ne da zafin zuciyarshi yasa ba'a fahimta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.