Complete Hausa Novels

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Buzu Book 3 Complete.txt

Chapter 84 of 99

Sai da Baba ya yi kuka mai isar sa sannan ya iya furta "Babu komai Nana, ni dai na gode wa Allah tun da kina nan cikin ƙoshin lafiya, Alhamdillah, Alhamdillah na gode wa Allah".

Haka ta rungume Nasiru ma tana kukan farinciki, ta ƙara tabattar da duk lalacewar naka naka ne, ta shiga farinciki mara misaltuwa da ganin ahalinta a tare da ita.

Har Alhaji Fatuhu ya tafi ranar, Shukura ba ta yi musu bayanin komai ba, sai dai ta kaÉ—u ta shiga tashin hankali da mutuwar É—an uwanta. Hajiya Amina ma babu rarrashin da ba ta yi mata ba, amma ba ta yi mata bayanin komai ba.
Washegari da rana, sai ga Yusra tare da Sagir da Hajiya Halima da Siyama. Hajiya Amina ta karɓe su hannu bibbiyu. Ta ce "Sagir na zata zan ganka tun a jiya, na kira gidanku na sanar da Shukura ta dawo. Ya ce "Mummy bana gari ne, ina can Abuja fa, Yusra babu lafiya"

"Wai Yusra haihuwa ki ka yi ne?" Mummy ta yi maganar tana kallon ta.

Shukura ce ta fito, Yusra ta ajiye wa Sagir yaron, ta nufi Shukura ta ce "'yar uwa babu abin da ya same ki ko?"

Shukura ta jinjina kai ta riƙe hannun Yusra ta ce "Yusra na gode sosai da sosai, na gode"
Yusra ta rungume ta tana rarrashinta.
Shukura ta ce "Mummy, ki kira Daddy a yi komai a kan idonsa, na kira Baban Rauda ma a wayarki"
Cikin rashin fahimta ta ce "To wai meyafaru?"
Shukura ta ce "Shi zan yi bayani"
Tana rufe bakinta, Alhaji Zailani ya fito, ya tsaya yana kallon Yusra da kuma Shukura.
Yayi murmushi ya ce "Har gangami ki ka yi na tona mini asiri Shukura? Shikenan, mu jira zuwan Fatuhun, ai tun da ki ka dawo na san za a yi hakan."

Gaba É—aya suka tsaya su na kallon Shukura.

Hajiya Amina ta ce "Shukura mene wai? Alhaji ka yi mini bayani mana"

Su na cikin maganar, Alhaji Fatuhu ya ƙaraso gidan, ya tarar da su a tsaye a falo. Ya ce "Hajiya Amina lafiya kuwa? Shukura ta kira ni a waya ta ce lallai na zo"

Hajiya Amina ta ce "Wallahi nima ban san abin da yake faruwa ba, shi ma na ji yana zancen za a tona masa asiri na kasa ganewa"

Ya kalli Shukura ya ce "Shukura, mene ne ki yi mana bayani"

Shukura ta yi shiru tana kallon Alhaji Zailani, amma ta kasa magana, kawai ta fashe da kuka.
Yusra ta ce "Ina gida wayar Baban Haidar ta lalace, ya saka layinsa a wayata, Shukura ta kira ta ce tana wani Asibiti a can wata ƙaramar hukuma a Kano. Wai garkuwa aka da ita ta kuɓuta, wata mata ta tsince ta, ta kaita Asibiti. Na ce ba zan tafi ba sai tare da ita, da magariba wasu suka zo Asibitin su na nemanta za su kashe ta. Shi ne na tafi da jaririn, ni ban ma san yadda aka yi ba na ganni a gidanmu na Abuja daga Asibitin. Amma babanta ne ya saka a sace ta"
Gaba É—aya suka kalli Yusra cike da mamaki.
Alhaji Fatuhu ya ce "Kin san me ki ke faÉ—a kuwa?"
Yusra ta ce "Na sani mana, ba fa ƙarya nake yi ba. Ai ita da kunya ta ce ga abin da ya yi, amma ni dai ku yi haƙuri na faɗa"

Alhaji Fatuhu ya ce "Amma kamar an ce ai ba ta da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, wataƙila...

Shukura cikin kuka ta ce "Yusra ba ƙarya take yi ba, Daddy ne ya sanya a sace ni, saboda ina bin diddigin yadda aka ce jaririna ya mutu, kuma saboda ya bayar da jaririna a matsayin sadaukarwarsa ta shekara a ƙungiyar asiri. Na so rufa masa asiri na yi shiru, amma ba zan iya ba, mussaman idan ina kallon mutanen da ya zalunta, da yadda yake ganin bayan rayuwarsu. Ni Yusuf ma ina kyautata zaton shi ne ya bayar da shi a kungiyar"

Cikin tsawa Alhaji Fatuhu ya ce "Shut up Shukura, mahaifinki ne fa, ki ke yi masa wannan tonon sililin a gaban mutane. Kuma tayaya za ki haɗa kai da abokiyar zaman ki, ku yi masa wannan ƙazafin?"

Shukura ta ce "Ko zan yi wa kowa ƙazafi yaya za a yi na yi masa? Bana jin komai ko a gaban waye zan tona masa asiri, iyaka dai a yi mini gori wataran hakan ba zai dame ni ba. Ɗana ya ɗauka ya bayar aka yi tsafi da shi aka yi maka asirin da ka rasa komai ka yi rashin lafiyar nan. Suka haɗa baki da Doctor Sharif aka yi mini tiyata aka ba su jaririna.
Tayaya zan iya rufa wa mutumin da ya yi mini wannan zaluncin asiri?. Nan Shukura ta din ga faÉ—ar miyagun ayyukan da Alhaji Zailani ya gaya mata ya yi da bakinsa.
Wani irin bugu zuciyar Hajiya Amina ta yi, take ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, tamkar an zare mata lakar jikinta. Wani irin gumi ya fara tsatsafo mata ko ta ina.
Alhaji Fatuhu bakinsa na rawa ya ce "Zailani, abin da yarinyar nan ta faÉ—a haka ne, ko kuma É—imuwa ta shiga ne?" Yayi shiru bai yi magana ba, sai tsare su da idanu da ya yi.
Sagir ya ɗan daddana wayarsa, mutumin nan da suka zo tare da Shukura ne ya shigo, tare da wasu ƙarti majiya ƙarfi su uku.
Bayan ya yi musu sallama, ya yi musu bayanin shi jami'in tsaro ne, kuma Likita, shi ne ya haɗu da Shukura a lokacin da nutanen da Alhaji Zailani ya tura, suka gano ta, suka yi yinƙurin kashe ta, ya yi amfani da ƙwarewar aiki, ya kama mutum biyu daga ciki. Kuma sun tabattar da Alhaji Zailani ne ya saka su wannan aiki.
Bakin Hajiya Amina na rawa, da kyar ta ce "Me na yi maka haka Zailani?" Daga nan ba ta sake cewa komai ba, ta silale ta faɗi ƙasa.

Alhaji Fatuhu shi ma kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi ya yi, ji yayi tamkar numfashinsa zai ɗauke. Sai yanzu wasu abubuwan da suka faru suke dawo masa, amma bai taɓa zaton Alhaji Zailani zai iya aikata masa wannan mugun abun ba.
Kafin a bar gidan da shi, ya tsaya ya kalli Alhaji Fatuhu ya ce "Kar ka yi mamakin abin da ya faru, domin ban taɓa sonka ba, duba da yadda ka fini ta ko ina, kuma ban yi nadamar abin da na aikata maka ba. Duk abubuwan nan da na yi babu wata cikakkiyar shaida da za a iya kama ni da laifi da ita, balle a hukunta ni. Sai shaidar sace 'yata da na yi, wannan ma na san yadda zan fitar da kaina.
Sai dai dole mu yi mutuwar kasko, domin ba ni kaɗai ba ne a ƙungiyar asirin, har da yayarka, da ta sadaukar naka da ɗanka da ya mutu, dan haka ko wani mataki zaka ɗauka a kaina, sai ka haɗa da ni da ita, gara ni abokinka ne kawai, ita kuma 'yar uwakka ce!".

*****

Nana ta so sanya kayanta na Nigeria, a gurin bikin nan, Hammad ya ce shigar buzaye za a yi mata. Ta sha gyara ta yi kyau. Agadez ta É—inke da tarin jama'a.
Tun daga kan gashin kanta, lungu da saƙo na jikinta, babu inda bai ga gyara ba.
Sai da ta tuna da lokacin bikinsu na farko, yadda aka kawo mata shadda ta alfarma. Yanzun ma haka ne, rigar ta sha aiki ita kanta shaddar ƙamshi take yi na musamman.
Babu babban abin da ya razana Nana, irin sarƙar da aka saka mata ta gold da ta sauka har cikinta. Ta kalli mai kwalliyar ta ce "Ni gaskiya a cire mini wannan sarƙar ba zan iya saka wa ba, fariyar ta yi yawa"
Matar ta ce "Ba fariya ba ce shugabata, ado ne na mutanen ƙasar nan, dan Allah kar ki ji wani abu, ai ana kammalawa dole za ki cire ne" Sai da aka yi ta fama da Nana sannan ta haƙura, gani take yi kamar ba ta hanyar da ya dace ta yi wa Allah godiya ba kenan, da wannan fariyar.
Ta din ga istigfari, da fatan Allah ya sanya kar hakan ya sanya ta ji wani abu na girman kai ko tinƙaho.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.