Complete Hausa Novels

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Buzu Book 3 Complete.txt

Chapter 39 of 99

Tafawa ya ce "Mai girma Matwalle, wannan kwana-kwanar ta yi yawa, ka yi mana bayani kai tsaye."

"Kamar yadda ka yi ta bin diddigi a baya, tabbas Hammad ya yi rashin lafiya, ya kuma je Nigeria jinya. Asal na san abin da ki ka gani ya É—aga miki hankali kina ta wasi-wasi. ÆŠan da Hammad yake da shi, ba É—an kowa ba ne face É—an matar da ki ka kawo a matsayin kukunsa. Wannan kukun tasa matarsa ce"

AREWABOOKS

Wani irin nannauyan numfashi Asal ta ja, tana jin kamar daga shi ba zata sake jan wani numfashin ba. Gaba É—aya sai ta kasa gane me ma ake son a yi mata bayani. Wace ce ma kukun? Take tambayar kanta.
Tafawa ma sak ya yi, yana murza yatsun hannunsa, ya tsare su da idanu ɗaya bayan ɗaya, sannan ya numfasa ya ce "Ku na nufin Imam Hammad ya auri wata wadda ba ƙabilarmu ba, daga Nigeria har ta haifa masa wannan yaron da na gani?"

Sardauna ya ce "Haka ne"

Ya sake rausayar da kai ya ce "To ina fatan a wannan karon, za ku yi adalci dokar masarauta ta yi aiki a kansa, a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata."

Sardauna ya ce "Tukuna dai, sai mun ga abin da hali ya yi, saboda yanzu hankalinmu na kan samun lafiyarsa"

"Lafiya, wace irin rashin lafiya kenan yake fama da ita? Kuma me ya kai shi Nigeria? Kuma a kan me ya karya dokar masarauta?"

Matawalle ya ce "Wannan duk abu ne da za ka ji daga baya, amma yanzu a kan wannan gaɓar muke, zuwa gaba kaɗan za mu duba abin da ya dace a yi"

Wani irin kuka Asal ta fashe da shi ta ce "Hammad, abin da za ka yi mini kenan, ka munafunce ni? Ka cutar da ni, ka ajiye ni hoto ban haihu ba ka je ka haihu da wata. Saboda ka tozarta ni ba ma ka auri Buzuwa daidai ni ba sai wannan ƙazama mummunar yarinyar?"

Tafawa ya ce "Rufe mini baki, mutuniyar banza uban waye ya ce ki je ki kawo ta gidan sarauta, a matsayin kukun mijinki, alhalin kin san ba haka dokar masarauta take ba?"

Hammad ya kalli Asal ya ce "Ki yi haƙuri, na san na yi miki laifi mai girman gaske, amma ina mai baki haƙuri yadda al'amuran suka kasance ba wai da gangan na yi ba. Kin san babu yadda za a yi ina zaune haka kurum na ɗau jiki na tafi Nigeria na...

"Ka yi mini shiru, babu wata magana da zaka faɗa na yarda da kai, maƙaryaci...

"Hattara!" Matawalle ya yi mata tsawa.

"Ko me ya yi miki, dole ki ambace shi da girmamawa kar ki kuskura ki faÉ—i wani abu mummuna a kansa, ko me ya yi kuwa. Dan haka ki kiyaye harshenki"

Cikin kuka take cewa "Wallahi sai ka sake ni, ba zan zauna da kai ba, kuma na bar ka da Allah sai ka sake ni"

Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Yarinyar kirki, na san za ki ji abin wani iri, amma babu abin da zai raba aurenki da Imam. Haryanzu mu na kan tattauna matakin da za mu É—auka amma sai kin bamu cikakken haÉ—in kai kin nutsu. Haryanzu ke ce halattacciyar matar Imam da kowa ya san da zamanta."

A fusace Tafawa ya tashi ya kalli Asal, da gaba ɗaya ta rikice take kuka ya ce "Ke tashi mu tafi" Ta yinƙura ta tashi ta yanke jiki ta faɗi.

Hammad ya taso da sauri ya nufo ta, amma Tafawa ya ce "Kar ka kuskura ka taɓa mini 'ya" Ya kalli Asadullah ya ce "Zo ka ɗauke ta mu tafi"

Hammad ya ce "Ba zai yiwu ba, ba zai ɗauke ta ba. Kar ya fara taɓa mini mata"

"Ni ka ke gayawa kar ya fara taɓa maka mata?"

"Ni nake da hurumin ɗaukarta, ko na taɓa ta ban yarda ya taɓa mini mata ba" Ya yi maganar yana tsare Tafawa da ido.

Sardauna ya ce "Tafawa ko da an samu rashin fahimta, bai kamata a ce ka hana shi taɓa matarsa ba, sai ka gama wannan ɓaɓatun ita kuma ta baka kunya, ai ba a shiga tsakanin mata da miji. Bari a kira barori mata su zo su ɗauke ta, a kai ta ɓangaren Gimbiya Bilkisu"

Ya ce "Babu wanda ya isa, ba wanda zai taɓa mini 'ya"

Sultan ya ce "Umarni ne, a kaita sashen Gimbiya Bilkisu, idan ta farfaɗo ta ɗan nutsu sai a kai ta gida" Tafawa ya tsaya cak yana kallon Sultan cikin ƙunar rai. Ƙaninsa yana ba shi umarni kuma dole ya bi.

*****
Wata kyakykywar matashiya ce ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune tana bawa jaririn Nono. A rikice ta ƙarasa da sauri tana faɗin "Sister kin farfaɗo Alhamdillah, Alhamdillah, Alhamdillah ala kulli halin. Barka da arziki sannu" Ta ƙarasa gaban gadon tana rungume Shukura.
Shukura ma ta rungume ta, tana faÉ—in "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi"

Ta kalli Shukura ta ce "Babu komai, ni dai na gode wa Allah da ya sanya ki ka farfaÉ—o ki ka tashi. Sannu 'yar uwa" Ta sake maganar cikin iyayi da kulawa.

Ta kalli likktar da ta take ta ɗawainiya da Shukura, ta ce "Sannu da ƙoƙari doctor, Allah ya biya ki kema"

Doctor ta ce "Ba komai, yi wa kai ne."

"Yanzu kawo lambar wani a kira miki"

Shukura ta É—an yi shiru sannan ta ce "To" Ta bayar da lambar Sagir, aka saka a wayar aka danna kiran wayar"

Shukura ta miƙa hannu, ta karɓi wayar.
Muryar Yusra ce ta yi mata sallama, ta tsuke fuska ta ce "Ina Baban Haidar"

Wata irin rikicewa Yusra ta yi, ta ce "Shukura ke ce? Ina ki ka tafi muke ta neman bamu ganki ba? Kina ina?"

Sai Shukura ta É—an yi saroro, jin yadda Yusra ta rikice da murna.

"Ina nan, idan yana kusa ba shi wayar"

A rikice Yusra ta sake cewa "Baya nan, ki gaya mini kina ina na zo na É—aukko ki?"

"A'a ina nan lafiya kalau, idan ya dawo ki haÉ—a ni da shi"

Yusra ta ce "Baya nan, layinsa ya saka a wayata, ni ban san lokacin da zai dawo ba, ki gaya mini kina ina?"

Kamar Shukura ta share ta katse wayar, sai kuma ta gaya mata. Tana can wani Asibitin kuÉ—i, a can wata local government a wajen Kano. Sannan ta É—ora da cewa "Amma kar ki gaya wa kowa mun yi waya da ke"

Yusra ta ce "Har mamanki? Tana can hankalinta a tashe fa ita ma"

"Eh har ita, kar ki gaya wa kowa, idan ya dawo ki haÉ—a ni da shi, ina Haidar? Yana lafiya?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido, cike da fargabar ko shi ma ya salwanta.

"Yana makaranta, to kina lafiya cikinki ma yana nan lafiya?"

Shukura ta ce "Eh, lafiya kalau"

"To dan Allah kar ki je ko ina daga nan gurin"

"Tom" Ta faɗa a taƙaice.

Matar ta kalli Shukura ta ce " 'Yar uwakki ce?"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.