Buzu Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Buzu Book 3 Complete.txt
Chapter 75 of 99
****
Labari ya cika ciki da wajen Agadez, kan cewar Hammad yana da ɗa, ya auri 'yar Nigeria, haka zalika an soke Al'adar hana auren baƙar fata.
Wasu daga cikin al'ummar garin hakan yayi musu daɗi, mussaman baƙaƙe, da suka din ga jin tamkar su zuba ruwa a ƙasa su sha.
Æangaren fararen buzayen kuwa, gani suke yi tamkar rage musu kima ne, da kuma rage karsashin Masarautar.
Cikin marasa gaskiya a fadar Sultan kuwa, cikinsu ya ɗuri ruwa cike da tashin hankali, saboda tsoron hukuncin da ka iya biyo bayan tonuwar asirinsu. Ga shi Sultan ya ƙi nuna musu ya san su ne, kuma tun daga ranar da aka kawo bokan nan fadar Sultan, ba a sake zaman majalissar ba.
WaÉ—anda ba su san Nana ba, suka din ga sintirin gidan Sultan, su na son ga Nana, amma Nana na kauwwame a sashin Sultan.
Tuni labari ya ishe Asal, wanda hakan ya sake gigitata, tamkar za ta yi hauka. Wani irin so da matsanancin kishin Hammad ya din ga taso mata, ji take yi tamkar za ta yi hauka. Gani take yi ta ƙasaƙanta ta tozarta, a ce Nana ce kishiyarta, matar da ta ɗauka tamkar baiwar da ta saka kuɗi ta saya, amma yanzu ita ke da komai, ita kuma tana gefe ta zama 'yar kallo.
Wasa-wasa Asal ta daina cin abinci sai kuka, ga Tafawa ba ta ita yake yi ba, ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke musu kawai yake yi.
Duk matsanancin kishin Hammad, haka ya ƙyale Nana da Imarana, suka kasance tare suna ta hira irin ta 'yan uwantaka, tare bawa junansu labarin gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa.
Ya ce "Bari na nuna miki wani abu" Imarana ya ɗan tashi ya fita, sannan ya dawo, ko da ya dawo ya miƙa wa Nana waya.
Nana ta karɓi wayar tana kallonsa, ya yi mata alama da ta saka a kunnenta.
Nana ta saka wayar a kunnenta, zuciyarta na É—an bugawa da sauri.
"Assalamu alaikum, Nana" Muryar Ummansu ce ta doki dodon kunnuwanta, a wani irin rikice Nana ta tashi tsaye, ta rasa ina zata dosa ta ce "Um..umma, muryarki ce ke ce?"
"Nice Nana, kina nan lafiya?"
Nana ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta ce "Umma, bani da bakin da zan yi miki magana, bani da idon da zan iya kallonki, ni mai tarin laifi ce"
"Shhh, Babu abin da ki ka yi mini na ba dai-dai ba Nana. Sai dai tashin hankali da fargaba na shige shi, na rashin sanin inda ki ke, da kuma wani hali ki ke ciki, ga tsohon ciki kin tafi kin bar gida. Amma Imrana ya zo inda nake, tare da Yayan mijinki, sun yi mini bayanin komai. Nana na yi sujuda na gode wa Allah, ba wai domin daular da ki ke ciki ba, ko kina auren wani ba, sai domin murnar kina cikin ƙoshin lafiya tare da ke da yaronki. Sun ce kar na gaya wa kowa, babu wanda ya sani, amma sun zo sun yi mini alkhairi Imrana ya zama babban mutum ya nutsu, kema hankalinki yana kwance. Ni dai fatana su yi su kawo mini ke, ko na wanko ƙafata na taho,amma sun ce na yi haƙuri kaɗan"
Cikin kuka Nana ta ce "Ni dai ki yafe mini dan Allah, tashin hankalin da na sanya ku a ciki, dan Allah ku yi haƙuri Umma" Imrana ya karɓe wayar ya ce "Umma sai anjima, da na sani ban haɗa ku ba, nema take ta rikice"
****
Hajiya Amina tana zaune tare da Alhaji Zailani, tana ta lallaɓa shi a kan ya ci abinci, amma ya ƙi ci, saboda shikaɗai ya san bala'in da yake ciki. Tun da ya yi mafarkin an huda saitin zuciyarsa, dodon ƙungiya yana sha masa jini, ya farka ya ji saitin zuciyarsa ya yi masa wani irin nauyi.
Ga jikinsa sai yi masa wani irin raɗaɗi yake yi, kamar ya yi wanka da yaji. Yana jin yadda wayarsa take ta ringing amma ya ƙi ɗagawa.
Daga ƙarshe, Hajiya Amina ta saka hannu ta ɗauki wayar, ta saka a kunnenta tana sallama.
Jin ta yi shiru ya sanya Alhaji Zailani É—agowa ya kalle ta, sai dai ta tsare shi da idanunta ba ta ce masa uffan ba.
Jiran Hajiya Amina yake yi ta yi magana, amma ta yi shiru ba ta yi magana ba. Jiki babu ƙwari ya ce "Ya dai? Meyafaru?"
Jiki a sanyaye ta ce "Daga makarantar su Yusuf ne, wai yana kwance a Asibiti babu lafiya, yau kwana uku kenan"
Ya waro ido ya ce "Yusuf É—in?" Ta jinjina masa kai.
"Ki kira su ki gaya musu, ni ba ni da lafiya, babu lallai na iya driving su dawo mini da É—ana gida"
Hajiya Amin ta jinjina kai tare da mayar da hankalinta kan wayar.
*****
Gidan Baba ya zama tamkar maƙabarta, babu walwala ko kaɗan, ko ƙaunar tunkarar gidan baya son ya yi.
Saboda matsananciyar damuwa, da takaicin abubuwan da suke faruwa a gidan.
Jamila kuwa kullum tana ɗaki, dan ta sha baƙar azaba, sai da ta kwana tara a Asibiti, da kyar aka samo kanta kamar ba zata rayu ba.
Ya daina shiga harkar Mama da yaranta gaba É—aya, ko abincin gidan ya daina ci. Ga damuwa da kewar yaransa Nana da Imrana da suka addabi zuciyarsa.
Ya fito daga cikin gida da buta a hannunsa, ya yi alwalar sallar Azahar sai ga wata danƙareriyar mota irin ta matafiya, sabuwa gal sai ƙyalli take yi ta shigo layin.
Bai damu ba, ya idar da alwalarsa ya ɗaukko wayarsa, yana son kiran can Buda, saboda yaga kiran wayarsu, bai samu ya ɗaga ba. Sai ya ga motar nan an tsaya da ita a ƙofar gidan. Sai ya yi tsuru yana kallon motar.
Sulei ne tare da Mahmoudu suka fito, suka nufo Baba. Ya tsaya saroro har suka ƙaraso inda yake.
Suka durƙusa har ƙasa suka gaishe shi, ya amsa musu yana bin su da kallo, kasancewar sun rufe fuskokinsu da takunkumi.
Bayan sun gaisa, Mahmoudu ya ce "Baba mu na tare da baƙi ne daga Agadez"
Baba ya ɗan yi shiru, shi dai ya san babu wanda ya sani a Agadez, amma ya miƙe ya ce "To bari na kawo muku abin zama" Ya tashi ya shiga cikin gidan, ya ɗaukko tabarma ya shimfiɗa musu, ya koma ya aiki Nasiru ya sayo ruwa. Ya zata iya su Mahmoudu ne baƙin, kawai ya ga Sulei ya je ya buɗe motar, wani dogon mutum mai jiki ya fito da wani matashi, shi ma sanye da rawani suka fito, suka nufo shimfiɗar. Shi dai Baba duk abin ya ɗaure masa kai, tsoro ya shige shi.
Ya yi musu barka da zuwa, suka zazzauna, Mahmoudu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Baba baka gane ni ba?" Baba ya yi shiru ya ce "Kamar dai na sanka, amma ban gane ka ba"
Imam Zahradeen ya sauke rawaninsa shi ma, shi ma dai Baban ya yi masa kallon sani.
Mahmoudu ya ce "Baba kamar baka gane mu ba ko?"
Baba ya ce "Gaskiya dai"
"Baƙi ka yi daga Agadez"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.