Buzu Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Buzu Book 3 Complete.txt
Chapter 50 of 99
Hammad ya ce "Babu komai, ni ba na jin daÉ—in zama nikaÉ—ai ne, na saba duk inda nake mu na tare, ni dai a kawo mini shi"
Matawalle ya ce "Ka yi haƙuri, Likitoci sun ce ba a buƙatar kowa ya zo inda ka ke ne"
Ya yi shiru yana tunanin, ina Asal da ko sau ɗaya ba ta zo ba ita ma. Sai dai a jikinsa ya din ga jin kewar wani abu mai muhimmanci a tare da shi, kamar yana jin matsananciyar ƙishirwa.
Sultan kuwa ya sanar da Asal batun ganin Hammad, amma ya ce mata rashin lafiya ce ta kama shi a Niemey, aka kai shi wani Asibiti a can, daga baya a ka kai shi faransa. Duk da ta yi mamakin yadda za a ce rashin lafiya ta kama mutum, a kai shi Asibiti amma ba a nemi ahalinsa an sanar da su ba tsawon shekaru.
Sai dai hakan ma sai da ta gaya wa Tafawa. Ya ruÉ—e ya rikice dan ya so a ce wani mummunan abin ne ya samu Hammad.
Tun da Asal ta ji labarin Hammad zai iya dawowa a kowane lokaci, take shirin karɓar sa, dan ba ƙaramin kewarsa ta yi ba. Dan ta shiga damuwa da tashin hankalin da sai da suka samun matsala da Tafawa bayan ɓacewar Hammad.
Tun da Sultan ya ce a kowane lokaci zai iya dawowa, ta sanya aka yi gyaran gidan sosai. Sannan ta fara lissafin canza kuyangin da za su din ga yi masa hidima. Ga Tafawa ya yi mata alwashin idan ba za ta ci gaba da ba shi haÉ—in kai ba, zai nemi wani ya yi masa, ko da kuwa ta kama a salwantar da ran Hammad É—in ne baki É—aya.
Sai dai duk da tunaninsa na Agadez ya dawo, bai fasa fama da wannan matsanancin zafin jikin ba, da yake jin tamkar ana ƙona shi ba. Sai dai ya rage tashi a kai a kai.
Haɗuwar Asal da Nana, ya zame wa Asal tamkar tsintar dami a kala, ta ga idan ta kawo Nana gidan sauratar Agdez, kanta a tukunya yake game da sha'anin sarauta, ga girki ta iya, saboda Hammad na son daddaɗan Abinci, ga kuma Nana baƙa ce 'yar Nigeria, babu yadda za a yi ta ɗauki hankalin Hammad, saboda baƙar mace ta haramta a gare su, bisa ga Al'adar Agadez. Sai dai abin da Asal ba ta sani ba shi ne; a rashin sani kaza ta kwana a kan dami.
AREWABOOKS
Tun da Hammad ya sauka a filin tashi da sauukar jirage, gabansaa yake faɗuwa, ya kuma rasa dalilin hakan. Jin sa yake yi tamkar yana daf da maganin ƙishirwar da ta addabe shi.
Bayan Nana ta yi amfani da ƙarfi, gurin tursasa wa Nana zuwa Agadez, ta sanya Nana cikin jerin waɗanda za su yi girkin karɓar Imam Hammad.
Gabba É—aya gida ya É—auka Hammad zai dawo, bayan shafe dogon lokaci yana jinya. Su kansu wasu daga cikin Imam Imam É—in, ba haka su ka so ba duk da abin jita-jita ake ta yi, Sultan bai tabattar da hakan ba, kuma a daren za a yi babban taro tare da 'yan majalisar Sarki, da kuma su Imam na shekara da ake gabatarwa.
Sai dai babu tsammani, su ka ga Hammad ya bayyana a gurin. Tun da ya shiga gurin, ya ji wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, da kowace irin AC aka kunna, sanyin baya wadatar da shi har cikin ƙashinsa ya ji ya gamsar da shi.
Ya ji wani irin jiri na neman ya ɗebe shi, amm ya daidaita nutsuwarsa, ya sunkuyar da kansa ƙasa ya rabe ya je ya zauna.
Bai É—ago kansa ba, ya ji Matawalle na tambayar me ya kawo wannan nan gurin. Aka sanar masa tana cikin masu girki ne.
Bai dai É—ago ba sai murmushi da yake yi, saboda barka da zuwa da ake ta yi masa.
Sai dai ƙirjinsa ya tsananta bugawa, da aka ce ta zo ta ɗanɗana Abincin, ta nufo inda suke. Ya kasa jurewa ya ɗaga kansa, sai ya ji kamar sanyin da yake ji yana ƙaruwa. Wani abu ya ji mara daɗi a ƙirjinsa ganin yadda ta ɗaura rigar girki a kan kayanta, ana ganin shape ɗin kyakykyawar surar da Allah ya yi mata ta bayyana. Kalar fatarta ya ɗauki hanklinsa, tsohon muradinsa na son baƙar mace ya motsa a zuciyarsa. A kallo ɗayan da ya yi mata duk ya nazarci wannan abubuwan ya sunkuyar da kansa. Amma ya nemi ya kasa jure bugun da zuciyarsa take yi babu ƙaƙƙautawa.
Bai ji daɗin yadda Matawalle ya saka a ka fita da Nana ba, saboda yadda duk ta rikice a gurin. Sai dai ya yi ta mamakin yadda aka ta shiga cikin masu girki, alhalin tana baƙar fata 'yar Nigeria.
Da suka tashi daga taron nan kuwa, da Asal ta gan shi, wani irin tsalle ta yi ta maƙalƙale shi, tana murna cikin matsanancin farin ciki har da hawayenta. Ya ɗago ta daga jikinsa yana murmushi yana kallon idanunta, da son gano ainihin abin da yake gani a idanun nata, dan abin da ya faru daren da ya bar Agadez fes yake dawo masa.
Ya tsura wa idanun Asal ido, ya ce "Kin yi kewata har haka?"
"Imam, kusan shekara biyu ba ma tare ka ce ko na yi kewar ka? tu me manques(Na yi kewar ka sosai) Ta yi maganar idanunta ɗauke da hawaye. Bai bari zuciyarsa ta ci gaba da raya masa abin da take raya masa ba. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "tu me manques. Na yi kewar ki sosai cherié. Ina fatan kina lafiya babu abin da ya same ki?"
"Ba abin da ya same ni, sai damuwar rashin sanin inda ka ke, ina ka tafi aka neme ka aka rasa haka, ka tayar mini da hankali na shiga damuwa sosai"
Ya yi shiru yana mamaki, Sultan ya ce masa faɗuwa ya yi, ya shiga coma na tsawon lokaci, yanzu kuma tana faɗin ya tafi ba a san inda yake ba, ga abin da ya faru na ƙarshe kan barinsa Agadez yana dawo masa. Sai ya kawar da tunanin komai daga cikin zuciyarsa.
Duk rawar kan da Asal take yi, da murnar dawowarsa gaba ɗaya hankalinsa ba a kan hakan yake ba. Jin sa yake yi ba daidai ba. Ya yi iya ƙoƙarinsa ya sarrafa tunaninsa da nutsuwarsa gurin ba ta dukkanin kulawa da kuma lokacinsa, amma hankalinsa na kan abin da shi kansa bai san mene ne ba.
Da dare ya yi kuwa, ya riga Asal kwanciya dan kar ma ta nemi wani abu a tare da shi, saboda fatansa ya gano takamaiman mene ne yake damunsa. Sannan ya yi mamaki rashin ganin Mahmoudu da bai yi ba.
Yana kwanciya bacci surar Nana ta bijiro masa, a ƙasan zuciyarsa ya ji bai ji daɗin fitowarta a haka ba. Da sauri ya yi istigfari dan gudun kar shaiɗan ne yake ƙara ƙawata masa ita. Amma duk da haka bai daina ganin ta a idonsa ba, ds yadda ta zuba masa ido duk ta rikice ba.
Ya yinƙura ya tashi zaune, ya ga Asal ta yi bacci, ya yi shiru yana tunanin wa zai tambaya wace ce ita.
Ya gaji da zancen zucin ya matsa kusa da Asal ya kwanta tare da rungume ta a jikinsa. Sai ƙamshin turare take yi da alama ta shiryawa dawowarsa sosai.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.