Buzu Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Buzu Book 3 Complete.txt
Chapter 24 of 99
Mahmoudu ya ce "Amma kar ya shaƙe ki fa, ko ya yi miki illa"
Ta ce "Ba zai yi mini ba, zai dawo daidai in sha Allah, idan ma ya shaƙenin zai dawo daidai in sha Allah, amma ku bani guri" Tamkar zai shige cikinta haka yake ƙoƙarin rungume ta.
Gaba É—aya Sultan ya ruÉ—e, Mahmoudu ya ce "Ranka ya daÉ—e, ta ce mu basu guri"
Sardauna ya ce "Tayaya za mu tafi mu bar su, idan ta cutar da shi fa?"
Mahmoudu ya ce "Ba za ta iya cutar da shi ba. Abin tsoron ma kar ya cutar da ita shi" Haka suka fita suka bar shi da Nana.
Su na fita Nana ta sassauta murya ta ce "Sayyid, ka nutsu ka yi addu'a, kar ka yi ihu, ka yi addu'a ka ji" Sai dai sam yanayinsa bai nuna yana cikin hayyacinsa ba.
Ta saka hannunta ta zuge rigarta ta cikin hijjabinta. Sai dai tana yi tana kokawa da shi. A hankali ta ba shi damar ƙanƙame ta kamar yadda yake ƙoƙarin yi. Wani irin nishi ya din ga saukewa mai sauti, jin sanyin jikin Nana. Sai dai sanyin bai kai wanda ya saba ji a jikinta ba.
A hankali ya yi lamo a jikinta, da fari Nana ta fara ƙoƙarin karanta masa Alqur'ani, sai dai ta kasa jurewa ta fashe da kuka. Saboda wani irin gigitaccen zafi ne yake ratsa ta daga jikinsa kamar an kunna musu wuta. Ga shi yadda ya danne ta ba za ta iya matsawa ba, balle ta samu afuwa.
"Ya hayyu ya ƙayyum Allah ka kawo mana ɗauki" Ta furta a lokacin da take jin yana ƙara matseta tamkar zai karya ƙasusuwanta.
Sun ɗauki lokaci a haka, kafin ta ji jikinsa ya saki, ya sassauta riƙon da ya yi mata. Ta ture shi da kyar ta ɗaukko pillow ta tayar masa da kansa da shi. Sai dai idanunsa a lumshe kamar mai bacci, saɓanin da da idanun a buɗe tar sai dai babu ƙwayar idon sai farar.
Ta koma gefe ta jingina da gadon da yake É—akin, ko rigarta ba ta iya gyarawa ba, ta gyara hijjabinta ta jingina ta lumshe idanunta.
Hawaye ne suka fara bin gefen idonta, wani irin azababben ciwo jikinta yake yi mata, kamar an yi mata dukan tsiya da kulki. Ga raÉ—aÉ—in da take ji a kan fatarta.
A tsorace take waige-waige, ganin bugiren da Ƙaisar yake kwnaciya babu kowa. Ta duba gurin zamansa nan ma baya nan. Ta fita da sauri zuwa ɗakin magungunansa, nan ma baya nan ga inda Giyaz ya yi ɓarna ba a gyara ba, tabbacin bai da lafiya bai gyara ba. Ta din ga shiga tana fita a cikin Libraryn tana kiran sunansa amma ta ji shiru.
Wata siririyar hanya ta bi, da haske ya ratso gurin. Ta bi hanyar sannu a hankali tana addu'a a cikin zuciyarta, da fatan Allah ya sanya ba wani abin ne ya samu Ƙaisar ɗin ba.
Bayan Library ɗin ta ɓulla, ta hango shi a cikin tafkin da yake gurin a kwance, ya lumshe idonsa. Da sauri Nana ta ƙarasa tana faɗin "Ƙaisar, wannan ai sai ka tsorata ni, meyasa ka dawo nan ka kwanta, jikin ne dai?"
Ya buÉ—e idanunsa ya kalle ta ya ce "A'a hutawa kawai nake yi" Nana ta samu guri ta zauna a gefe ta ce "A'a ai na san jikin ne, ba zaka faÉ—a mini ba ne"
Ya ce "Ya jikin mijinki?"
Ta ɗan yi shiru ta ce "Yana can Giyaz na ci gaba da azabtar da shi. Na rasa me ma zan yi gaba ɗaya, ni kaina a jikina nake jin na ƙone"
Ƙaisar ya tashi zaune sosai a cikin ruwan ya ce "Ba Giyaz ba ne kawai, akwai tasirin asirin nan da ake yi masa da wuta. Sannan kuma ga Giyaz, shi Giyaz yana wasa da ƙwaƙwalwarsa ne, ya sanya ya tuna wannan ya manta wancan. Sai kuma ya kan shafe shi sai ya yi wannan suman. Amma wannan ƙonewar yana da alaƙa da wutar da ake hurawa wadda aka yi masa asirin da ita"
Cikin damuwa Nana ta ce "To dan Allah waye ya yi masa asirin, kuma a ina aka yi masa?"
Ya girgiza kai ya ce "Ki yi haƙuri, ba na shiga duk abin da bai shafe ni ba, saboda ni har kullum zaman lafiya nake fata. Sai dai na ga uwargijiyarki a dalilinki ta tuna gadon nasu gidan, da ke ki ka guji naki. Babu lallai sihiri ya yi tasiri mai ƙarfi a jikinki. Zai iya yiwuwa kina daf da inda aka yi masa sihirin. A wannan karon ne za ki yi faɗan ƙarshe, kar ki yi da wasa ki yi da gasken gaske. Ki buɗe idanunki, kibiyoyin da ki ka gani ana harbinsa da su mahaifinsa na karewa, yanzu ke za ki tare su.
Ya fito daga cikin ruwan jikinsa yana ɗigar da ruwa, yana takawa da kyar, jikinsa duk wasu irin ramuka duk ya yi baƙi. Ya gyara zaman rigarsa ya rufe jikinsa sosai.
Ya sake duban Nana ya ce "Kar ki yadda ki komawa iyayenki gida, babu wani kyakykywan sakamako. Za ki sake komawa farko dan sunanki zai ɓaci. Kar kuma ki yarda a raba ki da ɗanki, kar ki aminta da duk wani murmushi da za ki gani a fuskokin mutane, kuma kar ki sakankance da ƙiyayyar da za ki gani. Kowanne na iya taimaka miki ki samu haske.
Kai da fata ki dage, duk rintsi kar ki kuskura a ci moriyar ganga a yada ke a gefe, saboda kin gama yi musu amfani. Ki kula sosai da sosai. Allah ya ba da sa'a"
Cikin damuwa Matawalle ya ce "Shirun nan fa ya yi yawa. Anya ba za mu je mu sake dubawa ba"
Sardauna ya ce "Abin da nake tunani kenan, kar abin da ba a so ya faru. Kai Mahmoudu tashi ka wuce gaba ka duba, idan lafiya mu shigo. Ni na kasa samun nutsuwa tun da na ji tana wai mu bata guri."
Mahmoudu ne ya fara yin gaba, ya tura ƙofar ɗakin a hankali ya hango Nana a jingine shi kuma yana kwance a kusa da ita a kan fulo.
Ya ƙarasa da sauri yana kiran sunan Nana, amma ba ta motsa ba, sai hawaye da yake ta fita daga idanunta da ta lumshe.
Ƙarasowa suka yi su ma, suka rufu a kan Hammad. Sai suka ga jikinsa ya saki, idanunsa a rufe wannan jijiyoyin duk sun koma yadda suke.
Sardauna ya ce "Ya aka yi ya koma daidai? Me ta yi masa?"
Mahmoudu ya ce "Ban san me ta yi masa ba, Nana" Ya yi maganar yana kallonta.
Sai dai shiru ba ta amsa ba.
Sultan ya taɓa Hammd yana kiran sunansa, amma shi ma bai motsa ba.
Kawai su ka ga Nana ta fara jijjiga, duk su ka ɗan ja da baya a tsorace su na kallonta. Mahmoudu ya rasa me zai yi. Sai bin su da kallo. A hankali kuma ta daina ta nemi guri ta kwanta a ƙasa.
Matawalle ya ce "Wai ni na kasa fahimtar wannan abin, me ya same su haka?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.