Complete Hausa Novels

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Buzu Book 3 Complete.txt

Chapter 14 of 99

Bayan fitarsa ya tsaya a harabar gidan, ya É—auki wayarsa ya kira Tafawa.
Tafawa ya É—aga tare da yin sallama.
Hammad ya amsa tare da cewa "Barka da dare ranka ya daÉ—e"

"Barka dai" Ya amsa a taƙaice.

"Yauwwa, dama na kira ka ne na sanar da kai, ka san abin da za ka din ga sanar da Asal, ka daina shiga cikin batun iyalina, idan ba haka ba za ka iya saka wa ta rasa ranta ko lafiyarta"

"Hammad, ni ka ke gaya wa haka?"

"Kai ka bani damar na gaya maka hakan ai. Abin da ba ka sani ba shi ne, Asal ta riga ta fara so na, tsawon lokacin da ya gabata, ci gaba da gaya mata magana kowace iri a kaina, ka iya haifar mata da matsala. Amma 'yarka ce duk abin da ka ke ganin shi ne daidai ka yi ba wani abu" Ya kashe wayarsa gaba É—aya, ya shiga mota da kansa ya ja motar ya bar gidan.

A zaune ya tarar da Nana a ɗakin da kayanta suke, ta sanya atamfa riga da skirt, kanta babu ɗan kwali. Ta yi parking ɗin black natural hair ɗin ta, da siririn band na yi wa yara kitso. Dan zabura ta yi, da ta ji motsinsa. Hannunsa riƙe da ledoji, ya ƙarasa ya zauna ya ajiye ledojin ya ce "Sannu da gida, na bar ki ke kaɗai ko?"

"Dama can ai nikaÉ—ai É—in nake rayuwata"

Ya yi murmushi ya ce "Haka ne, amma dai kin rayu da ni É—in ko?" Ta yi masa shiru tana kai hannunta ta É—auki É—an kwalin kayan, za ga É—aure kanta. Ya janye É—an kwalin ya ce "A haka nake son ganinki, kin yi mini kyau sosai da sosai"

"Sayyid, duk wannan abubuwan da ka ke yi, ba za su taɓa tasiri a kaina ba, ka bani ɗana kawai na kama gabana"

"Gaskiya ne maganganuna ba za su yi tasiri a kan ki ba, ciki har da kirana da Sayyid. Ga abinci na kawo miki, ki ci"

Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Ai na ci Abincin kamar yadda ka ce, yaushe za ka ba ni É—a na?"

"Kin ci, amma ba kamar yadda nake buƙata ba, sonake ki ƙara ƙiba, alamu sun nuna ba kya nutsuwa ki ci abinci ki ƙoshi" Ta kawar da kanta gefe, dan kar ma ya ci gaba da jan hirar. Dan ba ta son duk wani abu da zai sanya a ranta ta ji za ta iya ci gaba da rayuwa da shi."

Ya kwance rawaninsa, ya rage kayan jikinsa, ta kawar da kanta gefe, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri.
Ya zauna a kusa da ita ta É—ago ta kalle shi, gashin nan a kwance ya sha gyara. Ya É—ago mata yatsunsa ya ce "Ina zobena ne? Kin saka an addabe ni a kan zoben nan da yawa" Yana nuna mata yatsunsa.

Ta yamutsa fuska ta ce "Na yar da shi"

"Kin yar da zobena, kin ajiye turarrukana da mayukan gashina, ki na kallo ki na jin daɗi. Soyayyar gaskiya mara algus. Gobe in Allah ya kaimu za mu je gaban Sultan, mu ji hukuncin da za a yanke mana. Saboda na aikata laifi mai girman da babu wanda ya taɓa aikata shi sai ni."

Ayshercool.
08081012143
81
Nana ta taɓe baki ta ce "Wanda za a yanke maka dai, ni babu abin da ya haɗa ni da masarautarku, kawai a bani ɗa na na tafi"

Ya zura mata ido, ya jinjina kai ya ce "Kin daina so na dai kenan ko?"

"Eh" ta faÉ—a tana kawar da kanta gefe.

"Shikenan, zan ƙara miki lokaci, zuwa lokacin da ki ka ga ya dace ki saurare ni, amma ki sani, ni shugaba ne, kuma wasu lokutan idan aka tashi kawo gyara, toshe kunne muke yi, mu farantawa wani mu ɓatawa wani, domin samar da gayar. Dan haka duk abin da ya kama zan banƙara na aikata, domin ganin ba ki suɓuce mini ba, ko da kuwa abin da zan aikata ɗin na nufin ƙara miki ƙiyayyata. Yanzu dai ga abinci ki samu ki ci, sai ki kwanta ki huta da wuri zamu tafi" Ta murguɗa baki ta sake kawar da kanta gefe.
Duk wannan abubuwan da take yi masa, ko sau ɗaya bai ji haushinta ba, shi dai fatansa da roƙonsa ta saurare shi cikin nutsuwa, ya warware mata zare da abawa, saboda ya san ko shi ne haka ta faru a kansa, zai ce wulaƙanci ne aka yi masa.
Ganin ya ƙi tashi ya bata guri, ya sanya ta ɗago ta kalle shi, ta ga ya zuba mata ido, kamar zai lashe ta.
Ta sake kai hannu ta É—auki É—ankwalinta, amma ya jefa shi bayansa.
Wannan kallon da yake ƙanƙance ido ya fara yi mata, ta ƙara tsuke fuska tana tattara nutsuwarta, amma ya kai hannunsa kan gashinta, ya fara shafawa a hankali. Bai sani ba ko dan ya saba ganin irin gashinsu Asal na buzaye nai laushi da santsi ya sanya na Nana yake burge shi.
Baƙi ƙirin da shi natural, mai cika sosai da sosai. Ta hau ture hannunsa, amma yaƙi barin abin da yake yi, sai ma lumshe mata ido da ya hau yi.
Duk wani abu da Nana za ta yi ta baƙanta masa rai, tana aikatawa domin gujewa barin nusarar zuciyarta ta sake yarda da shi, ta ba shi wata damar ya cutar da ita.

Sai da ya bar ɗakin ta samu ta ci abinci, ta tura ƙofar ɗakin, sai dai babu mukulli yadda za ta datse ƙofar dan kar ya shigo mata.
Tana kwanciya bacci, nannauyan bacci ya sake yin awon gaba da ita.

*****
Doctor Sharif ne ya tashi a razane, bayan mummunan mafarkin da ya yi da Shukura, ta biyo shi tana kuka jikinta duk jinin haihuwa, da wata sharɓeɓiyar wuƙa tana, ya ba ta jaririnta.
Ya din ga gudu yana ihu, ya ɗan tsaya ya waiwaya kawai ya ganta a tsaye a kan matarsa, da wannan wuƙar a hannunta, tana kallon cikin tana kallonsa tana faɗin "Ka zo ka bani jaririna, ko na farka cikin matarka na ɗauke nata, ka ji abin da na ji" A daidai nan ya tashi cikin razani, ya haɗa uban gumi.
Ya kalli agogon ɗakinsa ya ga ƙarfe biyu da kwata na dare, kawai ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa, so yake ya je ya ga halin da matarsa take ciki, amma ya tuna wa zai fita ya bar wa yaransa mata su biyu da suke bacci. Doctor Sharif bai samu haihuwa da wuri ba bayan ya yi aure, sai da suka shekara goma sannan ta haifi yara mata biyu, yanzu za ta yi na uku ciki yana ta wahalar da ita. Tun da ya haɗa kai da Alhaji Zailani ya ba shi jaririn Shukura abin yake damunsa, amma tun da Alhaji Zailani ya shaƙa masa kuɗi, sai ya manta sai kuma yau da ya yi wannan mummunan mafarkin.

****
Yau ma Nana a kan gadon rannan ta hango Ƙaisar, lulluɓe da mayafi, hannunsa kawai ya ziro ta ƙasan mayafin yana rubutu a kan wani littafi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.