Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: WATA KISHIYAR.txt
Chapter 63 of 66
Page 62
YUSUF
Baze iya misalta irin murna da farincikin daya tsinci kansa a ciki ba jin abinda Ma'u ta fada. A sukawane ya fice daga gidan yana shiga motarsa Driver yaja suka tafi,
Tun kafin su fita daga Get din Estate dinsu Ma'u ya rangadawa Alhaji Qarami waya baya so ya bata lokaci ballantana ta dawo ta chanja magana dan yasan koda Ace abinda tayi niyyar gaya masa kenan to Juma'ar data yanke harda tagomashin bacin ran Bashir ya saka.
Sanda ya gayawa Ahaji Qarami maganar se ya zamana tsakaninsa da Yusuf din har an rasa ma wanene yafi wani murna nan take yace masa ba matsala ya gayawa mutanensa idan sun shirya gobe suje yanzu ze kira Baffan su ya sanar masa.
lafewa yayi a cikin kujerar motar yana sakin murmushi ransa fes jinsa kawai yake kamar wanda akayiwa Bushara da Aljanna tabbas ya yarda mahaqurci mawadaci kuma Allah shine meyi a sanda yaso ba'a saka shi ba kuma a hana shi.
Hajiyar ya dannawa kira dan da ita ya kamata ya fara raba wannan abin Farin cikin ringin biyu ta daga ckin kamilalliyar muryarta ta dattijai ta yi masa sallama.
"Hajiya barka da dare, Albishirinki Hajiya" Ya fada a jere
"Barka dai Babangida wane abin farin ciki ne haka ya faru da har muryarka ta gaza boyewa ko taqaddamar tikitin takarar taku ce ta qare kayi nasara?" Ta fada a sake daga jinta irin mutanen nan ne masu sakewa sosai da yaransu
Wani murmushi ya saki kamar yanagabanta kafin yace
"Wannan ai ba komai bane akan wannan albishir din Hajiya ki canka da kanki wane abu ne kike zaton ze sakani farin ciki haka?"
Shiru tayi se can tace "Asma'u, nasan dai a yanzu idan ba zancen takara ba toh sedai ita din nasan dai wadannan sune manyan burikan ka a rayuwa"
"Kin canka Hajiya yau Ma'u ta amsa da kanta ta bani damar na tura magabata na a daura mana aure wannan Juma'ar me zuwa dan haka Hajiya ki gayawa su Baba Sale idan ze yuwu gobe idan Allah ya kaimu suje, zan tura miki da Lambar Babban Yayansu se ki bashi suyi magana suji ina ne zasuje neman auran".
"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah, Babangida kaga abinda nake gayamaka ko? Ita rayuwa kabi ta a sannu. Duk yanda kaso da faruwar abu idan Allah be kawo shi ba haka zaka haqura. Yanzu kaga ribar haquri ko? Allah ya tabbatar da Alkahiri yasa yin na Allah ne, nayi murna nayi murna Babangida Allah yasa za'ayi damu bari na kira Kawun naka yanzu kuwa na sanar masa na tabbatar shima zeyi farin ciki da wannan Al'amari dan ko shekaran jiya dayazo seda yayi mun ciwon baki akan zancen auranka yace wasu da yawa ma basu yarda kana da aure ba ko wannan ze iya kawo maka tangarda a cikin tafiyar siyasarka" Hajiya ta fada cikin tsananin murna.
"Toh ai yanzu ciwon baki ya qare Hajiya in sha Allahu ki dai kirashi yanzun dan Allah kuyi magana a samu goben aje"
"Toh sarkin zumudi gobe ai yayi wuri ina lefinzuwa jibi haka?" Ta fada cikin tsokana, da sauri ya tare ta da cewa
"Haba Hajiya wane irin jibi kuma? Juma'a fa tace a daura aure kuma yau litinin nidai gara suje goben ayi komai. Mansur yana nan duk abinda ake da buqata a karba a hannunsa kafin na shigo"
"Toh Allah ya tabbatar mana da Alkahiri, bari na tura ayi mun magana da kawun naku nasan yanzu yana waje tunda ba'a dade da idar da sallah ba beci ace ya tafi gida ba" da haka sukayi sallama shi murna ita murna.
Ranar qaryar bacci duk iya satar sa hakayaga Yusuf ya qyale dan kwana yayi yana sallahda tasbihi na nuna godiyarsa ga Allah bisa cika masa wannan babban buri na rayuwarsa, gani yake ko Yanzu ya mutu ya samu farin cikin da ya dade yana kwadayi. Ma'u ta amsa soyayarsa ta yarda dashi a matsayin Mijin da zata aura.
Qarfe Sha biyu na washe garin ranar ta kafa tarihin da ko a hasase be taba hasko faruwarsa a rayuwarsa ba. Suna zaune gaban shugaban qasa a lokacin, tattaunawa ce me matuqar muhimmanci sukeyi saboda yana cikin kwamitin tsaro na qasa gaba daya hankalin sa rabi ne akan tattaunawar da sukeyi inda ya kasa rabin a jiran tsammanin sakamakoj neman auran da aka tafi masa.
Kunnensa maqale da Bluetooth yana sauraran duk abinda yake faruwa acan Kumo gidan Baffa Isiya saboda seda ya jaddadawa Qaninsa da aka tafi dashi akan suna zuwa ya kirashi a waya yana so yaji duk abinda akayi karma suje suce a qara lokaci akan abinda ya gaya musu.
Sanda yaji an fara karanto Siga tsakanin Baba Sale Wakilinsa da Baffa Isiya wakilin Ma'u miqewa tsaye yayi cikin tsananin mamaki haka mutanen da suke zaune tare dashi gaba daya suka saka ido suna kallonsa dan dama tuni sun lura da hankalin sa baya kan abinda sukeyi.
Besan lokacin daya sulale yayi sujjada a inda yake ba ta godiya ga Allah lokacin dayaji wani da be shaida muryarsa ba yana jaddada dauruwar aure tsakanin Yusuf Sulaiman Wunti da Asma'u Abdullahi Tukur se gani akayi hawaye suna tsere akan fuskar sa, abin dariya abin takaici fuskarsa shabe shabe yana haqaye kuma yana dariya yake gaya musu abinda ya faru, nan da nan suka hau taya shi murna dan duk wanda yasan Yusuf yasan Asma'u, kai ko mace me sunanta ya hadu da ita se taci wannanย darajar ya karramata.
Dole ya datse mitin ya fice suna ta tsokanarsa, ya ringa neman Layin Asma'u ya gagara samunta se ya mayar da Akalar kiran kan Alhaji Qarami suka hadu suna ta jimamai dan tuni Malam Kabiru ya kira ya zayyana masa dan shine ma Ummul aba'isin da suka sake fanfa Baffa Isiya akan a daura kawai to me za'a jira.
"Wato Yaya nasan halin Asma'u sarai shaqiyyar yarinya ce, wato ainihin dazu da safe ta kirani. Daga muryarta na fahimci ta kira tayi mun shaqiyancin nata ne se na yi kamar ban gane ba, tana ta wani hanya hanya ainihin danaga zata batamun lokaci kawai nace mata muna Kumo ai gashi ma har baqin sun iso ainihin idan sun tafi zan kirata alhalin a lukacin ma ina shan Shayi ne da Kubza ko shiryawa banyi ba" Bayanin da Yaya Kabiru yayi wa Alhaji Qarami kenan.
Duk yanda Yusuf yaso ya daure kasawa yayi dole ya yanki tikitin komawa Lagos na qarfe shidan yamma. baze iya ba yana buqatar ganin Ma'u a yau, ya rungumeta a jikinsa ya kirata da matarsa halalinsa aure ya bashi ita yanzu yana da dukkan wata cikakkiyar dama da iko a kanta wai dadi kashe shi shi Yusuf yau ya zama Angon Asmy.
Yana hanyar zuwa Airport Intee ta fado masa a rai, dafe kansa yayi, tun a daren jiya yaso ya shaida mata maganar auran da zeyi se gashi abubuwan sunzo a yanda babu wanda yayi zaton faruwarsu.
Lambarta ta America ya daddanna ya kira amma akace masa a kashe take, seda ya hadiye wani abu daya taso masa na bacin rai akan wannan dabi'ar ta Intee da sam bata dauke shi da qima ko mutunchi na Miji ba. Ya tabbatar da tafiya tayi wata qasar ba tareda ta nemi izininsa ba ko da yake abinda aka sabane ai, idan har ta gaya masa zataje wani guri to kudi ne bata dashi tana da buqatar ya bata.
Lambar mahaifiyarta ya nemo har ze danna ya tuna da a cikin watan nan da aka shiga akwai bikin qanwarta da suke uba daya da za'ayi a nan Nigeria zata iya yuwuwa sun taho bikin ma shine bashi da qimar da zata sanar masa seya canza akalar kiran zuwa lambarta ta Nigeria cikin Sa'a kuwa ta shiga.
Seda ta qaraci ringin ta katse ya sake kira dana dab da yankewa ta daga cikin muryar bacci tace
"Hello Sweet"
"Intee zaki taho Nigeria amma baki sanar dani ba me yasa kike..."
"Ai kaga halinka sweet qorafi qorafi baka da aikinyi kai se anyi maka laifi toh idan na gaya maka zanzo me zaka mun? Bana son takura ne nasan ina gaya maka zakazo ka fara damun mutum da jarabarka shiyasa ma ban neme kaba" Intee tayi saurin katse shi.
Shiru kawai yayi yana jinta, to meye ma baqo a cikin halinta ne wai shekara bakwai ai sun zama jiki sedai ya mata fatan shiriya idan tana da rabo, tunowa da abinda yasa ya kirata ya saka shi sakin wani murmushi a idonsa yana hango Asmynsa yana ayyana irin Albarkatun da ze diba a jikinta dan ko ba'a fada ba daga kallo kasan Asmy irin matan da Allah ya wadata su da komai ne ma'ana kyau na zahiri dana badini wanda ya same su sedai yai ta sujjada yana godewa Allah.
"Se mutum yayi magana ka fara fushi kuma, to jiya fa nazo ban taho da Asmy bane shi yasa ban kiraka ba kuma kaga hidimar biki zamu fara saura sati daya ina da buqatar na samu hutu saboda kwalliyata tayi kyau" Intee ta fada cikin shagwaba.
"Ba fushi nayi ba ai bakya laifi Yammata ya kamata kam ki huta kiyi kyau sosai kinji, dama ina so na gaya miki ne kin tuna maganar da mukayi kwanaki ko?"
"Wacce magana kasan nifa ban fita riqe abubuwa marasa muhimmanci da basu shafe ni ba"
"Hakane, toh maganar aure na da nayi miki" ya fada bayan daya ja numfashi yana jinjina halin matarsa a ransa
"Oh wai wannan maganar to ai tun lokacin ni na gaya maka bani da matsala da wannan kawai dai ka tabbata idan ka tashi auran ka samu classy mace wadda idan aka nunata aka ce mijin mu daya da ita bazan ji kunya ba kuma zata kulamuย dakai dakayu sosai shine kawai ni damuwata"
"Intee kina sona kuwa?" Ya fada cikin tsananin mamakinta saboda be yarda ba duk sanda take gaya masa gashi yanzu ta sake maimaita wa anya yarinyar nan tasan abinda take yi ma kuwa
"Ina sonka mana Sweet me yasa kake tambaya?" Ta fada ba tareda damuwar komai ba.
"Babu komai, kin tuna Asma'u? Takwarar Asmy wadda kika kaita gurinta a Lagos?"
"Uhm bazan iya tunata ba saboda bata da ajin da zan tsaya na kalleta har na gane kamanninta" ta fada a yatsine. Murmushi yayi me sauti kafin yace
"Koh? Toh ita zan aura ko nace miki ita na aura dan yau akaje tambayar mun auranta se kawai aka daura auran gaba daya"
"Haka iyayenta suka gaji da ita lalai me yasa Nigerians kwata kwata basu da lissafi ne se kace ana neman kai da ita da kyanta da komai daga zuwa tambayar auranta kamar wata tsohuwa za'a bada ita babu jan aji gaskiya an cuceta wallahi" Intee ta fada ranta a sake babu alamar wai Mijinta ne yace mata ya qara aure balle abin ya dadata da qasa.
Dariya Ya fashe da ita jin wai babu jan aji babu komai aka bada ita cikin sigar tsokana yace mata
"Toh ai abin daga ni ne, idan kin manta na tuna miki kema fa kina ganina kika rikice kika cewa Dady idan bani ba se kin fada rijiya haka babu jan ajin babu komai aka bani ke toh itama yanzu kin gani aka bani ita"
"Koma dai mene ne zan koma bacci na, da kasan wannan maganar cema da text kayi mun kawai, Allah ya sanya Alkahiri ka gayawa Amarya ta kulamun dakai sosai, Ina sonka se anjima" tana hama fadar haka ta kashe wayar.
Murmushi ya ringa saki wato ta kowanne bangaren Intee babu abinda ya shafeta ita kanta kawai ta sani, tayi wanka tayi kwalliya yau tana wannN qasa gobe tana waccen shikenan abinda ta saka a gaba babu zancen wasu haqqoqin aure ballantana har ta zauna tana kishinsa to Allah ya kyauta.
Harya shiga jirgi yana ci gaba da gwada Layin Ma'u yanzu ko yana shiga dagawa ne batayi, jikinsa yaji yayi sanyi duk karsashin da ya taho dashi yayi qasa besan wace tarba ze samu a gurinta ba. Da amincewarta aka daura auran nan ko kuwa itama shammatarta akayi irin yanda abun yazo masa?
To koma dai yaya ne aure ya dauru ba saki ba yaji duk abinda zatayi sedai tayi amma ko duniya zata taru bega ubanda ze iya kashe auran nan ba.
Yana sauka a Lagos kai tsaye gidanta ya wuce dan daman Driver sa na Aiport yana jiransa. Tundaga qofar gidan yana iya jiyo hayaniya daga ciki sedai baya gane abinda ake cewa, kwankwasawa ya shigayi amma shiru ba'a bude ba se ya koma mota da sauri ya dakko wayarsa daya bari ya shiga kiran layinta cikin sa'a Yanzu ta daga.
BASHIR
Farkawa yayi ya ganshi akan gadon Asibiti ga ledar qarin ruwa da aka saka masa harta qare Jini ya fara tafiya, da sauri ya zareta dan shi kadai ne a dakin babu kowa, ya jura qafafunsa qasa da niyyar tashi yana yunqurawa Kansa ya sara yayi saurin komawa kan gadon yana dafe kan da hannu biyu.
"Sannu ka tashi kenan?" Wata siririyar nurse data shiga dakin ta fada cikin harshen turanci tana qarasawa kusa dashi, hannun sa ta kama ta duba taga ya cire ruwan seta mayar da hannunta kansa inda ya dafe tana cewa
"Kan yana ciwo ne? Ka kwanta tukunna na dubaka be kamata ka tashi zaune ba daman se jikinka ya qara daidaita".
Seda taje ta yaye labulen window haske ya ratso dakin abinda ya tabbatar masa da cewar safiya tayi kenan kafin ta dawo ta hau auna Bp dinsa dasu pulse duk tana yi tana rubutawa bayan ta gama ta kalle shi tace
"Har yanzu jininka be sauka ba Mr, ka kwanta bari baje na kira likita ina zuwa" ta juya zata fita. Dakyar ya bude bakinsa da yake jin kamar muryarsa ma ta tafi gaba daya yace mata
"Ina so nayi sallah"
"Kayi haquri yanzu likita zezo" taja qofa tayi waje abinta.
Kwanciya yayi kansa yana bala'in sara masa zuciyarsa kanta wani bugu take fat fat kamar zata fasa qirjinsa ta fito kai shi gaba daya ma dubiyar juya masa take, me yasa tunda ya rasa Ma'u ya rasa kwanciyar hankali a rayuwar sa ne shi.
Yana nan kwance har Nurse suka dawo tare da likita, Dattijone ya manyanta nan da nan ya rufe Bashir da fada dan sanda suka shigo ma gaba daya yayi zurfi a tunani Likitan nata yi masa magana sam be ji ba seda ya taba shi kafin yayi firgigit ya farka.
"Da girmanka da komai kake abu kamar wani qaramin yaro, ta yaya kake tunanin zaka samu lafiya bayan ana qoqarin ganin jininka ya sauka kuma kana qara saka kanka a tunani? Koma me yake damunka yanzu ai ajiye shi zakayi ka ji da lafiyar ka amma kana neman ka kashe kanka a banza da tunane tunane haha mutane ku ringa yiwa kanku fada mana".
Shidai Bashir yayi shiru har ya gama dube duben sa yacewa Nurse din ta kama shi ta kaishi qofar bandakin da yace ze shiga. A cukule yace musu ze iya, haka ya daure da bin bango ya shiga dan duk takun da yayi ji yake kamar ana kwada masa guduma a kai.
Seda yayi sallar Asubar da ta kufce masa dan lokacin kusan tara na safe kenan, yana zaune yana lazumi rabi kuma tunanin Ma'u yake da yanda zebi ya gyara kwabarsa. Amirah ce ta fado masa a rai da jaririnta yayi saurin shafa Addu'a ya miqe dakyar dan se yanzu ya tuna da batun suturar jaririn ma.
Da karfin hali da komai ya gama cike duk takaddu aka bashi gawar Babyn a Ambulance suka tafi gida dan ya rigada ya kira Limamin masallacin da suke sallah na cikin Estate dinsu.
Yanzu da a gida yake cikin yan uwansa da komai anyi shi a tsanake amma yanzu bashi me yi masa dole ya daure duk wani ciwo ya tafi yayi.
Se bayan da aka gama Jana'izar Babyn daya sakawa Muhammad Bashir kafin ya shiga gida dukda Asibiti ya kamata ya koma dan shi kadai yasan abinda yakeji a jikinsa bayan ciwon kai yanzu harda zazzabi ne yake neman kama shi.
Addah na zaune zuru a palour ya tura qofar ya shiga, da bala'in sauri ta tare shi tana cewa
"Yanzu Bashir daga fita tun jiya se yanzu zaka dawo ina Amirar? Tun jiya nake kiran wayoyinku a kashe gaba daya hankali na ya tashi har su Nafi na kira na gaya musu da tace Naziru ma ze taho a jiyan amma Babanku ya hana wai ai da babu Lafiya za'a sani
Na ganka kai kadai ina ita Amiran? Qila ma gantalinku kuka tafi kuka barni a gida kwal kamar mayya bayan kasan baqin halin yayanka ba kulani suke ba".
Kujera ya samu ya zauna dan baze iya tsayuwa ba kafin yace mata
"Tana Asibiti"
"Na shiga uku meya sameta? Badai wata matsalar bace kuma?" addah ta fada tana dafe qirji, se yai jim kafin yace mata
"Ki shirya, bari na watsa ruwa muje" ya daddafa ya qarasa dakinsa.
Da sauri Addah ta shige dakin da take ta dauko wayarta da mayafi ta dawo falo ta rafka tagumi jikinta har tsuma yakeyi. Tana nan zaune ta jiyo horn daga waje, har zata leqa sega Bashir ya fito daga dakinsa ita se sannan ma ta fahimci layi yake idan yana tafiya haka tabi bayansa suka fita bayan da yace ta kulle gidan suka hau motar sa da ya saka Samuel ya dauko suka koma Asibitin.
Sun tarar da Amirah na zaune suna yar hira da matar da take dayaj gadon da yake dakin da take. Tana ganin su ta takwarkwashe fuska ta saka kuka Addah tayi kanta da saurin gaske taba tambayar lafiya musamman da bataga cikin Amiran ba se wara ido take gefe da gefe tana neman jinjiri.
Bashir kuwa yana ganin ta fara kukan ya juya ya fice, bashi da buqatar qarin damuwa a yanzu. Dakin da aka kwantar dashi dazu ya koma, yana shiga suka ci karo da Likitan nan ya kuwa rufeshi da fada kamar ze kai masa bugu akan ina ya tafi? Wama ya bashi izinin tashi daga gadon da har ze kama hanya ya tafi wani guri.
Shidai haka ya koma ya kwanta, seda ya karya da Abincin Asibitin da sam babu dandano ko kadan kafin aka masa Allurai harda me saka bacci nan da nan kuwa yayi awon gaba dashi.
Qarfe Biyar na yamma aka basu sallama daga shi har Amiran dan babu abinda yake damunta sedai ta koma gida kuma ta cigaba da jego Allah ya bada rayayye a gaba.
Musa abokinsa daya biya duba shi bayan sun tashi daga aiki ne ya roqa daya kaishi gida saboda gujewa surutuan Addah da suka hau motar sa Samuel ya kaisu gida
tun data samu labarin mutuwar Jaririn fa take kuka da hawaye yanda kasan itace ma Amiran, Gombe kuwa babu lokon da labari be isa ba acewarta dukda an saki Ma'u baqin Asirin da tayiwa Amirah na karta haihu a gidan be karye ba ai kuwa duk inda zata shiga se taje ta nemo makarinsa sedai baqin ciki ya kashe ta amma Amirah seta haifi Yaya a gidan Bashir.
Suna shiga gidan ya wuce dakinsa, wayarsa da ya saka a Silent ya ciro daga Aljihunsa jin tanaVibrating. Ya gane Lambar da ta kira dukda babu suna, Bala ne, da mamaki ya ringa kallon wayar rabon da suyi magana tun waccen ranar kusan wata nawa yanzu, lokaci daya wani bacin rai ya taso masa na tunawa da furucin Balan akan Ma'u se kawai ya ajiye wayar ya shiga cire rigar sa yana ayyana dalilin da ze sa Bala ya kirashi a yanzu bayan abinda ya faru har yana tunanin ze sake hada wata hulda dashi ne?
Alwala ya shiga ya dauro dan an kira sallar Magriba, seda ya saka jallabiyya a jikinsa kafin ya dauki wayar har ze zura a Aljihu yaga saqo akai daga lambar Balan, tsaki yaja ya fita daga dakin yana qoqarin goge saqon dan idan ma haquri yake bashi yayi ta banza dan shi dashi dai har Abada, har ya iya kallon fuskarsa yace idan da matar daya rabu da ita zata yarda daya aureta a matsayinsa na Amininsa ai wallahi in ba muqullin Aljanna bane a hannun Bala baya sake kula shi ba shima sedai idan shi kadai yake rabawa sannan.
Iqamar da yaji an tayar ta saka shi jefa wayar a Aljihu ba tareda ya goge saqon ba ya qara saurin tafiyarsa, a masallacin suka hadu dasu Aliyu, kallo daya yayi masa ya sunkuyar da kai shima be tsawwalla ba yana kallo suka fice daga masallacin dukda yana son magana da Aliyun, dole su chanza wani plan din tunda wannan ya rushe dan baze fa zuba ido yana ji yana gani ya rasa Ma'u ba.
Seda yayi sallar Isha kafin ya kamo hanyar gida, kiran sa akayi daga gidan abincinda yayo musu order ya daga ya qara yi musu kwantanceย yana kashewa saqon Bala daya bude dazu be kai ga gogewa ba ya dawo kan wayar.
"Ina tayaka baqin cikin yin wuf da tsohuwar matarka da akayi, gaskiya Bashir ka cika mara sa'a tunda har ka rasa mace Irin Asma'u"
Abinda aka rubuta a saqon kenan.
Wani tsaki yaja kamar ze tsinka harshensa ya goge saqon, ransa a bala'in ya shiga magana kamar wani sabon kamu yana cewa
"Wallahi Bala gamo na da kai baze yi kyau ba, saboda bala'i bazaka fita daga sabga ta ba ko shikenan Allah ya hadamu zaka maimaita abinda ka rubuta yanzu, nida Ma'u kuwa mutu ka raba sedai baqin ciki ya kashe duk me yinsa"
Ko gani dakyau baya yi ya haye kan step din qofar gidan sam be lura da Anty dake tsaye kamar wadda aka bawa aiki ba seda ta kira sunansa.
A dan firgice ya juya ya kalleta, fuskar ta a washe tana Murmushi me kama da dariya babu wannan hararar da take masa duk sanda suka hadu kamar zata rufe shi da duka tace
"Ai daga ciki nake ai aka ce baka nan ka tafi masallaci shiyasa nace bari na jira a nan karka dawo banga wucewarka ba".
Tsayuwarsa ya gyara ba tareda yayi magana ba yana jiran jin dame tazo kuma dan wannan murmushin nata toh Allah yasa dai ya zama Alkahiri
"Se mukaji Abin Arziqi a bazata, koda yake be zama lallai ya iso maka ba tunda muma duk yanzu saqon ya same mu kaga abin Allah daga zuwa tambayar auran Ma'u se kawai iyaye sukace a daura ayi duk wasu shiri daga baya, To me za'a jira abu ba auran budurwa ba Allah na tuba an daura aure dai akan sadaki me daraja bana tunanin ko auranta na fari ma tayi tsadar haka, kai gaskiya Ma'u tayi Goshi".
Yanda take maganar seka rantse da Allah wata qawarsu take bawa labari ko irin shaqiqin Ma'u da ze yi matuqar farin ciki da jin labarin, ta gama tsaf ta juya tana cewa
"Bari naje nima nayi sallar, kaini farin ciki yau ban ma san inda zan nufa ba wallahi Allah kenan wani ya qika da wuni wani da shekaru ze soka, gashi ta fito daga inda ba'a san darajarta ba ta shiga inda suke mararin samunta sema kaga yanda akace yan uwansa nata murna wallahi".
"Hasbunallahu wani'imal wakeel, La'ilaha'iah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" Bashir ya fada yana kaiwa qasa saboda yanda yaji qafafunsa sun gaza daukar sa gaba daya, kamar me ciwon Asthma haka numfashinsa ya shiga sarqe wa, qoqari yake ya bude baki ya dakatar da ita amma ya kasa harta bude gidan ta ta shige tana ci gaba da dariyarta.
"Ina tayaka baqin cikin Wuf da akayi da tsohuwar matar ka" saqon Bala ya dawo masa a qwaqwalwa. Dagaske Ma'u ta daura aure da wani ko kuwa da Bala da Anty wasa suke so suyi masa da hankali amma ai babu wanda yasan wani a cikin su ballantana su shirya yi masa yawo da tunani ai.
Hannunsa daya masa nauyi ya daga yana so ya zaro wayarsa amma ya kasa. To wama ze kira ya tabbatar da gaskiya ko qaryar maganar a yanzu?
Amma ai yafi kusa da Ma'un, a gurinta ya kamata ya samu tabbaci na koma menene.
Cikin azama ya yunqura ya miqe kamar bashi ne ya fadi qasa yanzu ya gaza tashi ba se gashi a kan qafafunsa cikin sassarfa ya isa qofar gidan Ma'u ya shiga bugawa kamar wanda yazo karbar Bashi.
Abdallah ne yazo ya bude masa, kafin yayi magana ya shige ciki ya fara kwada kiran Ma'u yana wulga ido cikin gidan yaga ta inda zata bullo.
ASMA'U
Suman wucin gadi nayi a zaune har Anty ta fice ta barni bana tsammanin ko numfashi ina shaqa a lokacin. Qarar wayata ce tasa na gane a raye nake amma sam bani da qarfin da zan dauketa dan kwayar idona kadai na iya juyawa na kalli wayar na sake maida ita na zurawa qofa ina jiran naga wani yazo ya tasheni daga baccin da nakeyi.
"Mami ga Abbi nan yazo, kizo ki ganshi kamar wani abun ne ya faru gaba daya a hargitse yake" Farida data shigo da gudu ta fada amma na gaza buda baki nayi mata magana se ido kawai dana zuba mata ido kamar wadda ta hadu da cutar mantau.
"Mami, Mami ki taso kinyi shiru ko kema baki da lafiya" ta fada bayan data maso kusa dani ta hau girgizani, ajiyar zuciya me qarfi na sauke nace
"Bacci nake kika tashe ni ko Farida?"
"Bacci a zaune kuma, idonki ma a bude yake fa Mami" ta fada da mamaki tana kallona. Zan sake magana kiran da Bashir yake kwalamun ya shiga kunnena kamar ma a qofar dakin yake seta miqe da sauri tana cewa
"Dan Allah ki taso ki gani Mami gaba daya ba'a hayyacin sa yake ba bamu san meyake damun sa ba daman jiya be kwana a gida ba se yanzu ya dawo" ta juya da sauri ta fice ina qoqarin tsayar da ita.
Yanda yake kwala kiran kamar wanda yake gayyar yaqin duniya na uku yasa na tattara dan qarfin daya rage mun a jikina na miqe, ina kaiwa qofar na jiyo shi cikin qaraji yana cewa
"Zaku gaya mun ko kuwa, dagaske ne Ma'u ta daura aure da wani daban bani ba? Da gaskene wani banza ze rabi gonar da take mallakina?"
Saurin bude qofar nayi na fita jin yanda ya qarasa maganar cikin tsawa dan ni kaina seda na razana, a dari naja da baya na riqe qofa ganin yanda ya juyo ya kalleni da idanunsa da suka rine kamar zeyi aman wuta gaba daya kamannin fuskarsa sun chanza zuwa wani daban da ban taba ganin sa a irin yanayin ba.
"Yawwa Ma'u ki gaya mun waccen matar qarya takeyi ba gaskiya ta fada ba, ki fada mub da bakinki babu wani Namiji daya isa ya mallake ki a duniya bayan ni" ya fada yana nufo ni, da saurin gaske na koma dakin na turo qofa dan Na tabbatar idan har ya riqe ni to qila ni kuma a haka nawa ajalin zezo, gaga labarin daya sakani gajeran suma se Bashir ya qarasa aikin ya murqushe ni na mutu.
Yanda yake buga qofar dakin yana kiran na bude idan ya balla ta ya shigo bazan ji dadin abinda zeyi mun ba. Na fito na gaya masa qaryane kawai shi abinda yake so yaji kenan to ni me zance masa bayan ni kaina ban gama tantance sahihancin labarin baki nima a cikin rudanin nake kamar sa ai an gara shi ba abinda ya shafe shi bane ni kuwa fa, taya ma za'a ce wai an daura mun aure daga zuwa tambaya sekace wata yar tsana.
Wayata da aka kira na janyo da sauri ban ko tsaya duba waye ba dan neman wanda ze kawo mana dauki daga buyagin Bashir kawai nake
"Hello Asmy inata buga qofa ba'a bude ba ko baku nan ne?" Aka fada da muryar da rudun da nake ciki be barni na gane waye ba.
"Ka shigo a bude take dan Allah kayi sauri Bashir ze illata mu dani da yara" na fada ina tsalle kamar wata yarinya tunda dau naji ance ana waje ai magana ta qare dauki yazo kawai.
YUSUF
Duka daya yayiwa qofar da qafa ta bude idan ma a kulle take oho shidai ya bude ya fada gidan cikin azama jin abinda ta fada. Ido hudu sukayi da Bashir dake aikin biga qofar dakinta yayi biji biji kamar wani sabon hauka ya waiwayo a fusace jin an shigo gidan karaf suka hada ido da Yusuf suka shiga muzurai kamar wasu sababin zakaru.
"Me ya kawo ka gidan nan? Bana gaya maka ka fita daga harkarta ba karna sake ganika a kudada mata ta shine ka dawo to kuwa yau senayi maganinka, idan ma dakai ake hada baki saboda a baqantamun rai duk senayi maganin ku zan nuna muku Ma'u tawace ni kadai" Bashir ya fada a zabure yana nufar inda Yusuf yake a tsaye ya harde hannaye a qirji seda yakai dab dashi ya tsaya yana huci kamar ze kai masa duka.
Murmushi Yusuf yayi yana kallonsa yace
"Yaka tsaya? Ka qaraso mana kayi maganin nawa ko ko ba haka kace ba?"
Muzurai kawai Bashir yake yana sake kallon Majiya qarfin da suke tsaye a bakin qofar daga bayan Yusuf jikinau kamar wadanda aka gina da Bulo ko karan hauka ya cije shi baze yarda fada ya hadashi da daya daga cikin su bama balle harsu biyu yanda suka zubo masa ido jira kawai suke a basu umarni su far masa yasan.
"Ya ka tsaya ne Malam Bashir kai nake jira fa" Yusuf ya sake fada, ganin Bashir na kallon bayansa yasa ya waiwaya shima seya saki murmushi me kama da dariya yayi musu alamar daua fita, suka rusuna masa a tare suka juya waje se ya maida kallonsa kan Bashir cikin qasa da murya yanda yaraj da suka zura musu ido bazasujiyo abinda yake fada ba yace
"Ashe ma duk kurarin banza kakeyi yan wadannan qananun kwarin sun tsorata ka duk fiffiqar da kakeyi ta tashi a banza. Bari kaji abu daya ze hana na wulaqanta ka saboda wadannan yaran, bana so mutunchi na ya zube a gaban su dan bazasu taba girmamani ba idan har na wulaqanta ka a gabansu amma hakan bashi yake nufin idan muka hadu a inda babu ido zan saka karnukana su yagalgala ka ba.
Karka dauki shirun da nake maka a baya a matsayin tsoro ko bazan iya mayar maka da martani bane Aa saboda a lokacin daga ni har kai laluben allura muke a duhu ba'a san hannun da ze dauka ba, amma yanzu da na tabbatar da Allura tazo hannuna ta zama halalina mallakina yanzu zan baka amsa daidai da duk abubuwan daka fada a baya.
Kace ina shiga gidan matan aure zaka bata mun suna ka gayawa duniya ni manemin matan aure ne ko? To bari kaji daga yanzu idanย na sake jin labarin anga koda sahun tayar motar ka ne a qofar gidan nan sena batar dakai"
Yanda ya fadi batarwar seda Bashir ya bude ido dakayu ya kalle shi, gani yayi ya juye masa kai bazakace wannan mutumin me yawan murmushi da fara'a bane.
"Kwarai ni ba suna zan bata maka ba dan baka da sunan da zan bata ba kuma kashe ka zanyi ba amma zan batar dakai, babu wanda ze sake ganinka gaba daya za'a shafe labarinka Bashir.
Babu kai babu MATATA, duk abinda ya shafi Yayanka nine wakili tsakanin ku idan bazaka iya tunkarata kai tsaye ba ka nemi wani cikin yan uwanta ka ringa magan dashi amma banyarda ba koda wasa magana ta sake hadaka da MATATA, ina da kishin abinda nake so na kuma san qima da darajar sa idan kana musu ka gwadani Bashir indai shirya mayar da yayanka marayun qarfi da yaji matarka tayi takabar dole Bashir ka sake Shigowa gidan nan ko ka tare MATATA a hanya"
A nutse yayi maganar amma tamkar saukar aradu haka Bashir ya ringa jinsu a tsakiyar kansa. Kalmar MATATA da yake fada tafi komai juya masa kwakwalwa dagaske kenan Ma'u tayi aure kuma wannan mutumin ta aura?
Qarar bude qofar dakin Ma'u da sukaji ta saka su waiwayawa gaba dayan su a tare kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.
ASMA'U
Sadaf sadaf na bude qofar dakina na fito yanda kasan barawo ya shigo sata tunda na dena jiyo hargagin Bashir na tabbatar da mun samu an kawo mana dauki kenan.
Gaba daya suka waiwayo suna kallona cikin wata irin Azama Yusuf ta iso gabana ba zato se jina nayi gaba daya a jikinsa ya rufe ni ruf seka rantse Farida ya rungume ko Amnah saboda yanda na zama wata yar firit a jikinsa.
Wani irin shokin naji ya taho mun tun daga tsakiyar kaina ya dire kan qafafuna, ban farfado ba naji sautin muryarsa tareda dumin numfashinsa da yake fitar da qamshin Na'ana'a daidai kunnena yana cewa
"Karki bari linzamin kishina ya kwace Asmy, meyasa zaki fito gaban wani namiji a haka ya kallo abinda yake mallakina".
Innalillahi, yanda kasan wadda wuta taja haka naji jikina ya dauki rawa nan da nan na shiga qoqarin janyewa daga jikinsa amma yaqi bani damar hakan sema qara qarfin ruqon da yayi mun yayi ta hanyar dora hannayensa biyu ya sake damqe quguna ya dora habarsa akan gashin kaina da se a sannan na lura ashe daga ni se wata doguwar rigar shifom me hannun Bes na fito kaina ko arziqin dankwali be samu ba.
"Yusuf ka bari meye haka dan Allah? Yara fa suna kallonka" na fada a rikice jikina yana rawa jin yanda yake qara danqe quguna yana qoqarin daidaita fuskarmu.
"Wadanne yaran? Tun kafin ki fito suka shige daki, ai kinyi qoqari sosai Asmy gurin basu tarbiyyar barin guri idan manya suna magana" ya qarasa tareda hade bakinmu guri daya ba tareda ya bani damar cewa komai ba, sumbatata yakeyi seka rantse da Allah babu wani abu daya iya a duniya sama da wannan ni kuwa ina tsaye kamar Bishiya yar shekara Dari bidirinsa kawai yake cikin wani irin sauqi yanda kasan dagani se shi muka rage a cikin duniya".
Qarar fashewar abu ta saka shi sakina dakyar yana mayar da numfashi muka daga kai a tare muka kalli inda Bashir yake tsaye, yawun dake barazanar sarqeni na hadiye ina raba ido kamar an jijjiga bera a jarka se na bude baki taread dora hannu akai ganin yanda hannun Bashir yake digar da jini gefe guda kuma mudubin Console dina ne a rugurguje da alama shi ya nausa da hannunsa.
"Kash ya zaka huce akan mudubi beji ba be gani ba, wai daman kana tsaye baka yarda da abinda na fada maka ba kenan? Ka tabbata wannan shine karo na qarshe da zaka sake ganin abinda yake haramiyarka ka kuma fita idan ba haka ba inada tsageru daidai da kai biyu kawai ka gani anan idan kuma kana musu ka jira minti biyar tayi yawa sena saka sun zagaye gidan ka.
Wani irin kallon da na gagara fassarawa Bashir ya bimu dashi dagani har Yusuf din kafin ya tsayar da idonsa akaina se kuma ya juya cikin rangaji ya fice daga gidan har sannan hannunsa yana zubar da Jini.
Ya bata mun farin cikina, gaba daya ya rusamun tsarin dana zo dashi na tarbar Amaryata" Yusuf ya fada yana kallona har sannan hannayensa na saqale da quguna wani irin abu nake yana shiga jikina duk yanda naso na bude baki nayi masa magana kona fizge jikina na kasa yanda kasan wadda ya saka waya ya daddaure haka nake jina.
BASHIR๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
WATA KISHIYAR ๐ฅฐ๐น
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.