Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: WATA KISHIYAR.txt
Chapter 39 of 66
Page 39
A qofar gidan motar mu ta tsaya, idona akan Bashir da suke tsaye tareda wasu mutum biyu da ban gabe su waye ba.
“Ku jirani karku fito” na fadawa yaran, seda na yi kokawa da duk wani rauni da karayar zuciyar daya taso mun kafin na bude motar na fito ina gyara mayafin kaina gaba daya mutanen gurin suka bini da kallo banda Bashir da tunda muka hada ido ya maida kansa qasa kaman wanda aka kama yayi qarya.
Kai tsaye cikin gidan na shiga, nayi sallama ina jiyo hayaniyar su daga cikin dakin Dada amma ba’a Amsa ba dan haka na nufi can din, har na kai bakin qofar naji an kira sunana, sena waiwaya.
Alhajin su Bashir ne yana tsaye daga qofar dakinsa ya yafito ni da hannu sena juya na koma gurinsa.
Ina durqushe a gabansa kusan minti biyu kafin yaja numfashi yace dani
“Asma’u kiyi haquri nasan an cutar dake amma zan roqeki Arziqi kar kice musu komai yanzu, ki barsu akwai ranar da su da kansu zasu maidawa junan su martanin abinda sukayi miki.
Na sani Qarin aure ba haramun bane amma ta yanda aka shirya naki sam be kamata ba. Ya zama zamba cikin aminci. Ki sani Ita Amana daya ce kuma wanda yacita baya taba zama lafiya, idan har Bashir da uwarsa sun qulla wannan aure dan su ci mutunchin ki Asma’u in Allah ya yarda muna raye ko mun mutu se sunga sakayyar cin Amanar da sukayi miki.
Ina qara roqonki da kiyi haquri, ki qara akan wanda kike yi in sha Allahu bazaki tabe ba, duk me neman gazawarki akan idonsa zakiyita ci gaba da yardar Allah”.
Kuka nakeyi dagaske a raina ina hasaso irin tarin qaunar da na nunawa Bashir da Ahalinsa, a tsahon zamana dashi kusan shekara goma sha uku yanzu bazan iya cewa taka maimai ga wani abun laifi daya taba hadani da wata daga cikin su ba, a kullum cikin kyautata musu nake iya qarfina kuma duk albarkacin so da qaunar da nakeyi wa Bashir din ce ta shafi su amma ace a gurinsu basu da abokin hamayya seni.
Sosai nasha kuka na ba tareda Baba ya hanani ba in banda “kiyi haquri Asma’u” babu abinda yake cewa.
“Naji zan haqura Baba bazan tanka musu ba amma kayi haquri bana jin zan iya ci gaba da zama da Bashir. Bazan iya ci gaba da zama cikin Ahalin da basa qaunata ba Baba. Sannan Baba Amirah fa, yarinyar dana raina da hannuna ita zan hada miji da ita wallahi bazan iya ba.
“Zan bi umarnin ka a yanzu zan koma ba tareda na cewa kowa cikin su komai ba amma Baba karka roqeni ci gaba da zama da Bashir saboda ina girmamaka bazan iya tsallake unarninka ba amma tabbas zan cutu. Zuciyata zata iya bugawa a dalilin haka muddin zan zauna inuwa daya da Amirah a matsayin kishiyata” na fada cikin sheshsheqa me qarfi.
Se Baba yayi murmushi wanda da ganinsa na takaici ne kafij yace
“Asma’u ke Yarinyar kirki ce sannan abar Alfaharin duk Miji me hankali da yayi katarin samun irin ki sannan ko wanne uba zeyi alfaharin zamtowarki Suruka a gare shi.
Bazan so na rasa nagartacciyar suruka irin ki a cikin zuria’ata ba domin ke din mayafi ce da kika lullube Bashir duk kuma ranar da wannan mayafin ya yaye ba baki nayiwa Bashir ba tabbas se rayuwar sa ta shiga cikin gararin rayuwa.
Idan har ki ka ce bazaki ci gaba da zama da Bashir ba ni me tsaya miki ne in tayaki kwatar yancin kanki amma yanzu kije ki samu nutsuwar zuciya, karki yanke hukunci cikin fushi idan kika nutsu duk abinda kika yankewa zuciyarki ki dawo ni ki gaya mun in Allah ya yarda zan baki goyon baya dari bisa dari ki share hawayenki yanzu”.
“Baba bana tunanin ina da buqatar yin wani dogon nazari ka taimakeni kawai kasa Bashir ya sawwaqe mun dan ina da yaqinin ko ba yanzu ba watarana se sunyi nasarar fiddani daga dakina” na fada cikin kuka, se ya tare ni da cewa
“Haba Asma’u ke da na sanki jaruma ya zaki karaya tun yanzu ki bada qofar da za’a ci galaba akanki? Maganar su fitar dake daga dakinki kuka babu wanda ya isa yayi Abinda Allah beyi ba, kije gida ki huta ki bawa zuciyarki haquri idan kuma kinga bazaki iya karbar Al’amarin ba ki dawo zan tsaya miki”.
“Shikenan Nagode Baba Allah ya qara girma”
“Nima na gode Asma’u Allah yayi miki albarka keda zuri’arki gaba daya”. Haka mukayi sallama da Baba seda yasakani na share hawayena tas yace naje na dauraye fuskata a bayin da yake cikin palour sa kafin na fito.
Ina fitowa naci karo da Dada da yayanta sun fito daga dakinta, Yanda kasan anyi ruwan sama an dauke haka sukayi shiru gaba daya suka zubo mun idanu kamar wanda sukaga wata sabuwar Halitta nayi musu kudin goro gaba dayabna watsar na nufi qofar fita.
Sanda Na fita ban tarar da Bashir a waje ba se Naziru suna tsaye a jikin motar da muka zo tareda yara. Kallo daya nayi masa na kama murfin motar na bude se ya riqe yana cewa
“Wallahi Anty babu sa hannuna basu gayamun ba se ana gobe za’a daura, da nace zan gaya miki Dada tace duk wanda ya kuskura ya sanar dake wallahi se tayi masa baki shiyasa ko Yaya Amiru da kika kira jiya ya kasa gaya miki komai” ban bi takansa ba na cewa me motar muje na nuna masa hanya ya qara sa damu gidan mu gidan Baffana. A waje na barsu ana sauke kayan mu bayan na sallame shi na wuce ciki.
A yanzu babu abinda nake buqata sama da na kebe ni kadai a inda zan sha kukana kar wani ya rarraahe ni. Dakin Hajia Babba nayi masauki na haye can qarshen gadonta na saka kaina a cinya na ringa rirgar kukan da wadda akayi wa irin abinda akayi mun ce kawai zata fahimce ni, tambayar kaina nakeyi me nayiwa Bashir a rayuwa daya qullaceni yaga ta haka kadai ya kamata ya rama.
Ina jin matan gidan mu suka ringa shigowa suna bani baki amma na toshe kunnena, nasha kukana seda naji Numfashi shina yana barazanar daukewa kafin na bawa kaina haquri na koma sauke ajiyar zuciya kawai ga wani masufaffen ciwon kai daya dirar mun maqogarona kuwa kamar ze tsage saboda bushewa dan in ban manta ba rabonda ko ruwa ya wuce ta cikinsa tun kafin na samu wannan baqin labarin.
Har dare ina cikin dakin sallah kadai na tashi nayi na koma na kwanta ba tareda na ko kalli kayan abincin da Hajiyar ta kawo mun ba. Haka ta zauna akaina tana ta faman yi mun nasiha dana gaji da jinta sena sa mata kuka dole ta tashi ta bani guri, qarin abinda yake damuna ganin har zuwa sannan banji komai daga Bashir ba, be zo ba be kuma kirani a waya ba haka na kwana kafin safiya jikina ya rijice dole se da aka danganani da Asibiti.
Gwajij farko likita ya tabbar mun da jini na ne ya hau sosai abinda ya saukar mun da mugun ciwon kai kenan ga kuma zazzabi me zafi, shawara ya bani da koma menen yake damuna nayi haquri na kuma fawwalawa Allah domin lafiyata tana gaba da komai, duk wani al’amari na rayuwa baze tafiyar mun daidai ba idan babu lafiya daga nan yayi mun Allurai da zasu taimaka mun zafin jikin ya ragu da ciwon kan ya bani magunguna muka tafi gida.
Seda akayi mun wuqa wuqa sannan naci abinci nasha maganin ban dade ba bacci ya dauke ni seda na shafe awanni ina yi kafin na tashi.
A yammacin ranar Alhaji Qarami yazo, bashi kadai ba kusan yayyena dukka seda suka zo gida aka taru masu tsinewa Bashir nayi masu bani baki sunayi. A bakin su nakeji wai ashe jiya da daddare ma yazo gidan ma, nidai ina kwance ina jinyar zuciyata.
Seda muka kwana biyu da dawowa a daren ranar da daddare ina kwance a daki da carbi a hannuna ina ja Jafar ya shigo yace wai naje inji Dadyn Abuja. Da dogon Hijabi na har qasa nayi sallama a Palour Hajia Babba kaina a qasa seda na kai tsakiya sannan ido na ya sauka akan Bashir da Bala se Abdulkarim Dan Qanin Baban su ne, ba tareda na qara ko taku daya ba na juya da niyyar fita Alhaji Qarami ya dakatar dani dole na koma na samu can gefe kusada qofa na zauna ina jin zuciyata kamar an watsa fetur an cinna mata wuta.
“Asma’u mijinki ne yazo bada haquri shine nace a kiraki tunda ke akayiwa laifi ke ya cancanci abawa haquri ko” Alhajin ya fada yana kallona, kafin ya miqe yana sake cewa”ki matsa ciki kin zauna a bakin qofa ga dare idan kun gama ki same ni gurin Hajia Umma ina son ganinki”.
naji shi sarai amma ban dago ba ban kuma matsa daga inda nake ba ya tsallakeni ya fice daga palour, be san jira kawai nakeyi ma na samu wata dama na fice na bar musu gurin dan bazan iya musa masa ba tun farko dalilin da ya sa na zauna ma kenan.
“Gamu munzo guiwoyin mu a qasa Asma’u munsan ba’a kyauta miki ba ni kaina wallahi bansan abinda ya faru ba kenan se daga baya amma ki dubi girman Allah kiyi haquri, kuskure dai an rigada anyi shi sedai muyi fatan Allah ya kiyaye na gama amma yanzu kiyi haquri ku karbi qaddara a yanda tazo muku” Abdulkari ya fada, se na daga kai na kallesu ina shirin buda baki nayi magana Bala ya rigani da cewa
“Allah ya huci ran uwar gida sarautar mata, kinsan fa kinsha kan mutumin bala’in tsoronki yakeyi shiyasa ya kasa gaya miki zancen auran nan. Kuma ma ni gani nayi ai ba wani abu a ciki tunda qanwarki ce daman da aje a dakko miki Bare wadda baki san halin ta ba Uwargida ai gara ta gida ko, easy kawai ki shanye a koma a ci gaba da gashi”
“Sedai a koma a ci gaba da gasa ubanka Bala” na fada a fusace ina miqewa tsaye kafin na nuna Bashir da yai tsamo tsamo kamar kazar data sha dukan ruwa ya zate ido yana aikawa Bala da mugun kallon katobarar dayayi nace
“Kai kuma tun da sauran burbudin mutunta juna a tsakanin mu ka rubuta takaddata ka aiko mun da ita dan wallahi Bashir kayi kadan ka wulaqanta ni kayi mun kishiya ta rashin mutunchi, idan kuma kaqi tabbas kotu ce zata raba auran mu da kai” ina fadar haka na juya amma kafin na kai waje Bashir da bansan tasowarsa ya riqe ni kamar dansanda da Barawo yana cewa
“Bazan iya ba Ma’u, na sani nayi kuskure amma wallahi rashin sanin ta inda zan fara gaya miki maganar yasa na aikata haka. Basan a ya zaki kalleni ba Ma’u idan nace miki zan qara aure. Ni kaina na rasa ta yanda Al’amura suka juya har na fara son Amirah na yarda kiyi mun duk irin hukuncin da kikaga ya dace komai tsananinsa zan dauka amma bazan taba iya rabuwa da ke ba Ma’u”
Wani tuquqi ne ya taso mun, yanzu har Bashir ya iya kallon tsabar idona yace dani wai yana son Amirah lallai na yarda In da ranka zaka sha kallo. Hannayensa daya riqeni na banbare daga jikina ina cewa
“Tunda kana sonta seka je ka zauna da ita amma ni dai wallahi na gama zaman aure dakai ko kaine autan maza Bashir kaje ka zauna da matar so tunda na gamayi maka rana”
“Kiyi haquri dan girman Allah Ma’u ki yafe mun ki bani dama na wanke kaina nayi miki Alqawarin babu abinda ze chanza a tsakanina dake saboda wannan auran, Ina sonki ina qaunar ki ki dauka wannan abun yana cikin qaddadarar mu daga ni har ke” ya fada yana qoqarin sake kama hannuna nayi baya ina cewa
“Qaddarar ka dai kai kadai kuma ka matsa karka sake rabar jikina idan ba haka ba Bashir sena kwada maka mari wallahi”. Sosai na birkice nayi masa tijara yanda ne taba tsammani ba a rayuwar sa, na hada da Balan da Abdulkarimun nayi musu zagi na tsamar nama kafin na jadda da masa akan ya kawo mun takaddata dan wallahi na gama zama da Bashir na yarda su Addahn suci galaba a kaina. Dana hada miji da Amirah gara na fita na bar mata gidan ta zauna dashi ita kadai.
Bangaren Hajia Umma na wuce gurin Alhaji Qarami, banko bashi dama yayi magana ba na fashe masa da kuka ina rantsuwar bazan komawa Bashir ba ya saka shi ya kawo mun takaddata na tsane shi na tsani zama dashi. Haka yayita bani haquri ya kuma tabbatar mun da cewa tilas Bashir ya sake ni tunda har na nemi hakan amma yanzu na kwantar da hankalina kodan jinina da akace ya hau a samu ya sauka kar kuma na sake janyo wa kaina wata matsalar.
Haka na kwashe sati biyu cif a gida muna kan wannan danbaruwar, kullum Bashir se ya zo kamar maye haka ze durqusa yana bani haquri nima kuma ban fasa ci masa mutunchi da jaddada masa cewa ya bani takaddata ba tunda ba’a aure dole nace na gama.
Gashi makarantar yara kullum se kiran waya sukeyi an koma tuni lafiya basu dawo ba nace musu mun bar gari ne za’a zo a fada officially a cire su haka gurin aikina ma da suka tuntubeni tunda hutun sati uku na dauka gashi na haura kawai se nanemi takaddar hutu ba tareda biyan Albashi ba, dan bazan bar aiki na ba saboda a yanzu ne nafi buqatar sa Idan Bashir ya sake ina da buqatar neman hanyoyin da zan ruqe kaina da Yayana dasu.
Bazan manta ranar da Dada da Addah suka wanko qafarsu wai sunzo biko na ba, na yaba da tsantsar rashin kunya irinta mutanen nan. A ranar nayi musu abunda Bahaushw yake cewa idan Malam beji kunyar hawa Jaki ba to shima Jakin baze ji kunyar kada shi ba.
Na fito musu a yar zamani na wanke su tas da soso da sabulu na kuma sake jaddada musu da idan sunji haushi su saka Dan su ya sake ni su gani tsakanij ni dashi waya rasa na raka su da Allah ya isar abinda sukayi mun kuma in sha Allahu nan kusa zasu ga sakayyar yaudarata da sukayi haka suka kwashi kafafu a sanyaye dan ba Dada ba Addah kanta da bata raina abin kunya tayi mamakin yanda na sakawa idona toka nayi musu tas.
Daukata sukeyi a duk yanda suka takani zan biyune shiyasa ma yanzun suka zo saboda horon da Bashir yaje yayi musu akan kodai suje su bani haquri na koma dakina ko kuma ya saki Amirah tunda ita ce duk musabbabin tashin hankalin da akeyi.
Wai mutane saboda qin Allah se kaga sun kirani da sunan wai ban kyauta ba abinda nayi wa iyayen Bashir tunda auren daya qara ai ba haramci bane da zance ni bazan zauna da kishiya ba.
Har da wadda take cemun ilimina be amfana mun komai ba ina Karatun islamiyyar da nayi ina Bokon nawa zan zauna ina ja ina jayayya da abinda Allah ya halasta, ban dagawa ko wace yar iska qafa ba na kuma roqi Allah duk wadda tace nayi Haquri Allah yasa ayi mata abinda yafi nawa muni idan yaso se taji in ma rashin tawakkalin me ya sakani yin haka ko yaya.
A cikin wannan yana yi wata rana muka samu baquncin Goggo da tunda aka fara wannan abun sau daya mukayi magana da ita shima ni na kirata kuma tace mun nayi haquri daga haka bata qara komai ba.
Ina kwance a daki aka kirani a lokacin idan ka ganni se na baka tausayi, na rame na fige fuskata babu komai daga ido se dogon hanci ina shiga palour idona ya sauka akan Bashir daje zaune a qasa, ban lura da sauran mutanen da suke ciki ba na hau kansa da masifa ina cewa
“Wallahi ko maye ne kai Bashir haka zaka ganni ka kyale tunda nace banayi banga wanda ya isa ya tilastani ci gaba da zama da kai ba, ka tashi ka tafi tun kafin nasa azo a fitar dakai mara zuciya kawai”
“Idan baki saka an fita dashi ba baki isa fitsararriya mara mutunchi ba Asma’u” muryar Goggo da ban san da zuwan ta ba ta katse ni kafin ta ci gaba da cewa
“Ashe duk rashin mutunchi da diban Albarkar da akace kinayi dagaske ne kuma a gaban ku Hajiya kuna kallo aka rasa wanda ze tsawatar mata. Saboda bakida mutunchi Mijin naki kike sakawa a gaba kina fada masa irin wadannan maganganun ku to bari kiji shi Allah babu ruwansa ze hukuntaki ne akan laifin ki na sabawa miji da ci masa mutunci babu ruwan Allah da cewar Bashir ya auro miki wadda bakya so anyi miki ba daidai ba dan haka tun wuri ki dawo cikin hankalinki kafin ki kanki wuta da qafafunki.
Sannan saboda kin zama yar kanki se abinda kika tsarawa ranki zakiyi shine kike iqirarin zaki kashe auranki saboda kanki farau kishiya ko kuma kece ta qarshe da za’ayiwa ko?
Ki idan kina da hankali ma ya kamata ki tashi jiniyoyij wuya akan za’a miki kishiya, gidan mu mata nawa Ubanki ya aura gamu nan mu Hudu ya mutu ya bari kin taba gabin wata tayi tashin hankali da yar uwarta a cikin gidan nan?”
“Amma Goggon su bazaki hada mu dasu ba, ko bayan haka hanyar da Bashir yabi tayin qarin auransa ce bata dace ba kuma ko wacce mace akayiwa irin haka dole ranta ya baci ai” Hajia Anjin ta tare Goggo jin yanda take ta surfa fada, se Goggon ta kalleta tace
“Saboda ya auri yar uwarsa ne take tashin hankali dan ba’a gaya mata ba, ai ba kansa aka fara ba tunda ubanta ma a sanda ya auro ni ai baku sani ba tafiya yayi bikin abokinsa ya dawo muku da ni a matsayin kishiya me yasa a sannan ku baku yi tashin hankali kunce bazaku yarda ba?”
“Aa Maryam Allah ya jiqan Alhaji bazaki taba hadashi da wannan yaron ba domin Alhaji Adali ne gamu nan dukka bari kiji kafin A daura auran ku da Alhaji seda ya kira mu a wayar landilayin da daddaya ko waccen mu seda ya gaya mana abinda ya faru ya kuma sanar mana da cewa ze aureki bisa wasiyyar Sama’ila dan haka da yardar mu da Amincewar mu Alhaji ya auro ki, sannan tunda tace bazata koma ba ai Asma’u ta wuce yarinta bare ace za’a zabar mata abinda zatayi”
Hajia Babba ta fada sauran suka amsa da “kwarai haka aka yi.
“To shikenan tunda kun daure mata gindin tayi duk rashin mutunchin da take so kun bata goyon baya ni baza’a hada kai dani ba, Ke Asma’u idan na isa dake ki tattara ya naki ya naki yanzu ki bi mijinki, kuma diban Albarkar da kikayiwa uwarsa da yayarta kije ki basu haquri, dan cikin matan yayyen ki kaf babu wadda ta taba duban idon mu ta gaya mana maganar banza balle mu yayanmu suje suyiwa na wasu”.
Tunda suka fara mahawarar na durqushe a gurin ina Kuka, wato qarata Bashir ya kai gurin Goggo ita kuma ta goya masa baya. Da sauri na daga kai na kalleta hankali tashe jin irin umarnin data bani, se nayi saurin matsawa kusada ita ina cewa
“Amma Goggo...”
“Karki ce mun komai sedai kuman idan kin shirya nuna mun ban isa dake din ba shikenan” ta yi saurin katse ni, se na mayar da kaina qasa na ci gaba da kuka me ciwo, ya zalunce ni kuma ha hadani da mahaifiyata Bashir wane irin mugun mutum ne a rayuwa.
Haka naja qaqafuna na koma daki na shiga tattara kayana ina kuka yarana da suka biyoni suna tayani. Ina cikin hada kayan Hajia Babba ta shigo dakin,
“Ki bar shirin yanzu Asma’u tace ku bari zuwa jibi se ki koma. Kiyi haquri ita rayuwar Ya mace daman haka da qalubale wata rana komai ze zama tarihi in sha Allahu” haka tayi ta bani baki har seda naji zuciyata tayi sanyi na kwanta a kan Gado ina saka da cin alwashin irin gashin qumar da zanyiwa Bashir idan har na koma gidan sa. Shi da sake jin dadin zama dani har abada.
Washe gari Goggo ta koma bayan ta sake yi mun kakkausan gargadi akan idan na sake ta sake jin wani abu se tayi mummunan saba mun, na koma gidana na zauna kuma duk abinda zan gani naje nayi haquri karna kuskura na dauki dabi’ar kai qara ko na ce zan sake yin yaji.
“Asma’u badan bana sonki yasa nayi miki haka ba, nasan ba’a kyauta miki ba amma hakan baze zama silar da zaki bar uban yayanki ba idan kin rabu da Bashir saboda kishiya qarshe dai wata zaki je ki tarar a duk inda zaki fada to menene amfanin haka” Goggo ta fada cikin lallama bayan da ta gama yimun fadan kuma, sena share hawayena tunda yanzu ta sakko se muyi magana ta fahimta nace
“Wallahi Goggo ni ba qarin auran sa ko rashin gayamun da beyi bane ya dame ni amma me yasa ze auri Amirah?”
“Saboda yana sonta kuma ita Allah ya zaba masa kin san dai duk yanda mutum yaso da son kasancewar abu idan Allah be hukunta hakan ba baze faru ba ko, haka duk yanda ka kai ga qin abu idan Allah ya qaddara faruwar sa babu abinda ya isa ya tsayar da hakan to kar kiyi jayayya da hukuncin Allah Asma’u, ki dauka daman tun kafin wanzuwar duniya yanda Ubangiji ya qaddara ke matar Bashir ce haka itama aka rubuto matar sa ce dan haka dole se ya aure ku.
Maganar munafunci ko yaudarar ki da sukayi wannan ki barwa Allah komai kina zaune se kiga ya saka miki a ruwan sanyi kinji ko kiyi haquri kar kuma wannan dalilin yasa kice zaki quntata zamanki da mijinki, a yanzu ne ya kamata kija shi a jiki dakyau ki bashi dukkan kulawa da soyayyar data kamata saboda ba ke kadai bace, duk abinda ya rasa a gurinki ze same shi a wani gurin daga nan kuma se hankalin sa ya fi karkata can saboda zuciya ai tana son me kyautata mata ke kuma daga qarshe se kiga kamar dan ya samu wata ne ya watsar dake bayan ke kika bada damar hakan.
Dan haka bani da damuwa akan ki Ma’uta nasan zaki riqe kanbun nan naki na Uwargida sarautar mata dakyau ina so ki nuna musu cewa ke din fa badai mutum ba se Allah, Allah yayi miki Albarka ya ci gaba da kareki a duk inda kike”.
Kalaman Goggo sunyi tasiri sosai a zuciyata dan gaskiya ta fada da ace wata daban aka auro mun davkuwa tabbas na nuna mata cewa kishi da MA’U ba wasa bane se ta shirya amma a duk sanda na tuna wa Bashir ya aura se naji bazan iya amfani da ko daya daga cikin abinda ta fada din ba.
Haka ta koma Yola washe garin ranar nima yan uwana suka raka ni gidan mu na Gombe bayan da suka hadu suka sake yi mun nasiha da rarrashi, banje na bawa su Dada haquri ba itama kuma Goggon bata tsananta ba tunda na yarda zan koma din ta rabu dani.
Gini yayi kyau sosai kuma an saka komai na amfani sabo daga yanayin kyau da tsaruwar kayan na tabbatar da aikin Yan gidan mu ne sunyi zumunchi sosai suka hada mun gida kamar na wata sabuwar Amarya ko tsohon lokaci nada ba’a saka a gidan ba.
Yanda kowa ya ringa yabawa ni kuwa baqin sa nake gani dan da gidan da mamallakinsa a yanzu basa gabana ko kadan biyayyar iyaye ce ta dawo dani cikinsa.
Bayan kowa ya watse Bashir ya shigo yanda kasan wasu Baqin da basu taba haduwa ba haka muka zama, shi yana kaffa kaffa dani karya yi abinda ze zama laifi ni kuma na baiwa Banza ajiyarsa ina ta sabgogina se shi da yaransa yake ta magana yana tambayarsu abubuwan da suke buqata wanda sarai nasan dani yake naji dadi da suka ce masa babu.
Su kansu yaran daga kan Amna zuwa Farida ba wani sakewa sukayi dashi ba Abdallah da yan biyu ne babu abinda ya sha musu kai suke ta murna sunyi kewar Abbi. Aliyu daman yafi kowa daukar zafi, kuka ya ringayi da gaske lokacin da yaji maganar auran ya kuma dauki fushi da uban ko yau din da muka dawo ina kallon yanda yake cika yana batsewa.
Da daddare gurin qarfe tara muna zaune a palourn qasa muna hira muka ga an bude qofa, da yake irin wadda bata buduwa ta wajen nan ce nasan Bashir ne shine yake da key dan haka ban ko kalli qofar ba na sake hada rai na zubawa TV ido.
Da sallama a bakinsa ya shigo, takun qarar takalmin da naji bayan muryarsa ya saka na waiwaya da mamakin naga shi da waye haka karaf idona ya sauka cikin na Amirah data sha Kwalliya da wani Material Cotton baqi me Pink din flowers dinkin riga da skirt sun kamata dam se wani dan yalolon gyale data yafo a kafada.
Cikin abinda be wuce second biyar ba na qare mata kallo na mayar da kaina zuwa ga TV ina nanata “La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minzzalimin” a zuciyata saboda jin wani abu yana tasomun kamar zanyi aman zuciyata har wata zufa naji tana tsatstsafo mun.
Ta gefen ido nake kallon sanda suka zauna akan kujera, ina jin qamshin turaren data saka ya baza gurin irin turaren da nake amfani dasu ne na Maryam collection ta zauna a kusa da Bashir sosai kamar zata shige jikinsa shi kuma se turata yake yi abin ma se ya bani dariya na dan yi murmushi a raina nace “yaro yaro ne” amma ban ko juya na kalle su ba.
Ina jin yaran suka hada baki suka gaishe shi ya amsa a zatona zasu gaida Amirah se naji dif sun ma mayar da hankali akan film din da muke kallo Bashir da qarfin hali naji yana cewa wai
“Baku ga Antyn ku ba baku gaisheta ba”
“Wacece tana ina ai mu kai kadai muka gani Abbi se Amirah” Aliyu ya fada yana kafe uban da kallo wanda mamaki ne nasan ya hana Bashir din magana. Yanda kasan bana gurin haka nayi musu dayake film din yazo qarshe ana gamawa yaran suka miqe dan daman abinda ya zaunar da mu kenan nima se na shiga qoqarin miqewa Bashir ya dakatar da ni da cewa
“Ma’u ina kuma zaki je gurinki fa muka zo” sena koma na zauna na waiwaya ina kallon sa da murmushi akan fuskata wanda a badini kuka nakeyi cikin zuciyata amma nayi Alqawarin wannan yarinyar bata isa taga gazawata ba, se a yanzu nima na dawo hayyacina tabbas idan na bar mata gidan ta ci galaba akaina dan haka zan zauna kuma ba zaman dadi ba kowa se yaji a jikinsa.
“Amirah baki gaida Antyn ki ba “ ya fada bayan dana zauna, Amirah da ta hada fuska bakin nan kamar ze tabo POP tace “Nima ai yayanta basu gaishe ni ba, kana ji fa wannan marakunyar Aliyun cewa yayi ma be ganni ba kuma baka ce komai ba”.
Dukda qasa qasa tayi maganar amma tsaf naji ta a raina nace “zanci uwarki ne yarinya mu dai ke zuwa”.
Kamar me jira kuwa l Bashir ya hau masifa yana fada mata maganganu, abin haushi abin dariya dramar tasu ganin abin bana qare bane na miqe nace masa
“Ka rufe mana qofar idan kun fita” ban ko saurara ba na haye sama na barsu a gurin. Har na kwanta Bashir ya shigo dakin, da saurin gaske ya nufoni kafin ya qaraso na dire daga gadon ban yi wata wata ba na izge Fitilar gefeb gadona daga soket na daga ta na nuna masa ina cewa
“Wallahi ka kuskura hannunka ya tabani sena yi maka rotse da wannan, badai ka hadani da Goggo ta tilastani dawowa gidan ka ba, ka tabbatar da ka kaiwa tashin hankali katin gayyata da hannunka”.
Yanda nayin ya tabbatar masa dagaske idan ya matsa zan iya kwada masan, daga nesa ya ringa yi mun magiya da nayi haquri na saurare shi amma nayi masa banza haka ya qaraci nacinsa ya fita ya bar mun dakin.
Haka muka ci gaba da rayuwa a gidan tsakanina da Bashir daga kallo se harara shi kuma kullum yana nan a lalace gurin roqona da bani haquri amma nayi kunnen uwar shegu dashi dukda qasan raina na fara hucewa bafa wai dan na manta da abinda yayi mun ba Aa sedai kawai na yarda cewa komai muqaddari ne a rayuwa daman tun a lauhul mahfuz an rubuta faruwar wannan al’amari a rayuwar mu.
Kusan sati biyu ranar ya same ni da batun komawa Lagos saboda hutun daya dauka ya qare, a lokacin bani da zabi kodan aikina da makarantar yara da suke zaune a gida ya kamata na koma sannan hakan ze dada nisan tani da Amirah dukda ko a yanzun ma tun ranar farkon suka shigo bamu sake haduwa ba. Haka muka fara shirye shiryen tafiya, ana i gobe zamu tafi ban san meya shigar da Ahmad bangaren ta ba se kukan sa muka jiyo a waje Amna ta tafi da gudu ta dakko shi ina duba fuskar yaro naga shatin yatsu da alamar marinsa akayi.
Cikin tsananin bacin rai na tambayeshi waya mare shi, yana kuka da maganar sa da bata gama fita ba yace “Anty Amirah ce, da safe Abbi ya nuna masa gurin yace tana ciki shine yaje suyi wasa (Sun saba tana wasa dasu) saboda na zubar da Tea ban sani ba ta mare ni”.
Zan dauki komai amma banda taba mun yara musamman ma ya zamana da cin zali amma tayi kadan dana taka gurinta nayi mata kashe di dan haka zan jira wanda ya ajiyeta yazo shine daidai yina. Da yamma Bashir ya dawo, yana shigowa Ahmad din ya tafi gurinsa da gudu ya fashe da sabon kuka yana gaya masa abinda ya faru.
“Ka ja mata kunne karta kuskura ta sake taba mun yara idan ba haka ba zan dauki mataki” na fada ba tareda na kalle shi ba. Se ya juya da Ahmad din a hannunsa suka fita ban san me yace mata ba dab da magriba dan har nayi alwala naji ana buga qofa.
Farida nacewa taje ta bude, tana budewa kuwa ta turo qofar da qarfi dan qiris ya tage ta buge Faridan, seda ta qaraso tsakiyar Palour ta wani tsaya ta kama qugu tace “Saboda munafunci shine za’a hadani da Mijina dan na daki yaro, ai barna yayi mun kuma ko yanzu wani ya sake zuwa yayi mun wani abu se na daka yaro sedai duk abinda za’ayi ayi, mtsw aikin banza kawai...” ban bari ta kai qarshen rashin kunyar tata ba na kai mata wani bahagon mari cikin sa’a na sameta dakyau na doke bakin fitsarar take kuwa leben ta ya fashe kafin ta gama gane abinda ya faru na sake kai mata wani ta dama ta fasa qara ta dafe kunci dama da hagu tana ihu daidai lokacin Bashir ya shigo.
Ban damu da shigowarsa ba ko ihun da takeyi na nunata nace “wannan gargadi nayi miki duk ranar da kika sake tako qafar ki gurin nan ki qaddara ma gaisuwa ce ta kawoki ba wai kinzo yimun fitsara da rashin kunya ba wallahi se nayi miki dukan da zaki kasa tashi, wawiya mata hankali kawai” na juya na haye sama Bashit yabi bayana muka barta a gurin tana zunduma ihu.
“Ma’u meya faru” ya fada bayan daya tarar dani”
“Kaja mata kunne tafi kowa sanin ni ha sa’arta bace idan tana ji da rashin kunya da fitsararta ni daidai nake da ita zan koya mata hankalin da bata dashi” na juya na tayar da sallah ta na barshi a tsaye.
Washe garin ranar muka koma Lagos, Sanda muka je na tarar Bashir ya sake gyara mana palour an chanza komai na ciki, sannan ga sabuwar mota me kyau model din shekarar a ajiye a inda nake saka mota ta, lambar jikin tsohuwar tawa dana gani a jiki ya tabbatar mun da tawa ce.
Haka ya ringa yi mun abubuwa har makaranta ya chanzawa yara ya mayar da su wata da tun farko naso a saka su yace tayi tsada abubuwa dai kala kala wanda duk na neman shiri ne, daga qarshe dai bayan dogon jan rai da ban haquri dana sha kala kala daga gurin Bashir na haqura na sakko muka dawo zaman mu lafiya badan na manta abinda yayi mun ba sedan ban isa na jada hukuncin Allah ba.
Iya horon da zan yi masa nayi ya kuma sauke kai ya bani haquri da tarin alqawarurruka kala kala Albarkacin son da nake masa da dattijantakar mahaifinsa ga kuma Alfarmar Mahaifiyata daya shiga na cire komai daga zuciyata ta na nemi muqulli na kulle wancan baqin littafin na rayuwar mu muka bude sabon babin rayuwa me cike da qauna da Aminci, haka rayuwa taci gaba da gara mana yau fari gobe baqi har kawo wannan lokacin da me afkuwa ta afku, Bashir ya yanke igiyoyin auran mu a lokacin dana gama ammana da bashi rayuwata.
CiGaBaN LaBaRi
Afuwan Uzuri ya riqeni kuyi manaji da wannan 🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.