Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: WATA KISHIYAR.txt
Chapter 2 of 66
Page 2
WATA KISHIYA(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
Ni kadai tsuru kamar mayya a gida har qarfe 10pm ga gyangyadi inayi amma na kasa shiga daki na kwanta saboda tsoro gashi har sannan basu dawo ba. Tsayuwar motarsa da naji ta sani miqewa daidai lokacin da Ahmad ya kwaso da gudu yana kwallamun kira "Mami Mami"
"Na'am Ahmad meya faru" na fada ina tare shi, labarin inda sukaje ya fara bani, gurin wasan da ya kaisu, Favorite restaurant dina sukaje suka ci abinci daga nan suka tsaya Cinema sukayi kallo abinda ya saka su yin dare kenan.
Saboda gajiya kowa dakinsu suka nufa, dakaina nayiwa Twins wanka na shirya su kafin 11pm gida yayi tsit duk sunyi bacci sannan na shiga dakina raina yana suya,
Tsabar bacin rai ko takan take away din da sukamun ban bi ba nima wankan na shiga ina sake danne zuciyata na shirya na nufi dakin Baban Ali.
A kan gado na sameshi yayi daidai yana amsa waya fuskarsa dauke da wani shegen murmushin da bazan iya tuna rabonda yayi mun shi ba ko ba'a fada ba nasan da Amira yake waya dan Baban Ali bashida kwashe kwashen yammata, Ada ni kadai ce a rayuwarsa kafin ya kwaso min Alaqaqai.
Wayar dana tarar yana yi ita ta qara bata mun rai saboda wannan ai wulaqanci ne ko? Nasan matar sa ce amma ya kamata nima ya mutuntani idan zeyi wayarsa se ya nemi kebantaccen wuri bawai cikin dakina akan Gado na ba, wannan sabuwar ta'asar da ya samu ta fara kaini bango dan haka ban san sanda na saki wani wawan tsaki ba ina janye ido na daga kansa bayan mun hada ido.
"Ke dawa kike tsaki?" Ya tambayeni still wayar na kunnensa.
"Ni da waye a dakin" na fada raina na qara quna.
"Anty ce ko" na jiyo muryar Amira na tambayar sa daidai sanda na duqa kusa dashi dan na dauke Safar daya ajiye akan gadon sena daga sauti yanda nasan zata jiyo nace "Nice din yar iya ko kina da magana ne"
"A ko yaushe ina gaya miki ki ringa jan girmanki ko? Amma shikenan" ya fada yana miqewa daga kan gadon ya nufi qofa. Wani baqin ciki ya tokare mun wuya, kawai na haye gadon na kwanta tareda fashe wa da kuka.
Duk yanda nake daurewa se Bashir ya qure ni tunda ya auri yarinyar nan ban sakeyin sati ba tare da nayi kukan baqin ciki ba shikenan ni a haka zan qare? Bansan sandaya dawo dakin ba na dai farka cikin dare naji mutum ya kwaqumeni aiko na ingizashi da qarfi har seda ya farka na tashi daga gadon na shige toilet. Fitsari nayi na dauro Alwala, hijabina na zura na fara jero Salloli tare da dogayen Addua.
Kamar kullum a duk sanda muka samu sabani na fara sallar dare nan haka ze zabga tagumi yana kallona in ya gaji shima ya to Alwalar ya tada Sallah (bawai dan banayi ba Aa nafi tsawaita Idan mun yi fada dan karna kwanta kusa dashi dan duk bala'i bama raba gado ππ) nasan me yake tunani qila qarar sa nake kaiwa gurin Allah ko ππ wallahi ko daya duk abinda Bashir yake mun ban taba yi masa Allah ya isa ba sedai ma in roqi Allah daya yafe masa ya kuma bashi ikon Yin Adalci a tsakanin mu ya ci gaba da bashi yanda zeyi ya kula damu. Ko ba komai nasan Bashir yana sona nima kuma ina sonsa to ban rabu dashi a lokacin Matsi ba se yanzu da dadi ya samu se in tafi in barwa yar taka haye?? ina ba wannan magana.
Ban sallame ba har seda aka kira sallar Asuba, ina kallonsa ya fita masallaci kafin nima na tashi nayi Raka'atanul fajir sannan na bada Farillah. Rashin samun bacci cikin dare yasa ina idarwa ko Azkar ban samu yi ba na koma bacci, sanda na farka goma harta gota dan haka anan dakin nayi wanka na shirya kafin na fito palour.
Ko ina qalqal sun gyara dan ko kadan banyi wasa wurin koyawa yarana aikin gida ba komai nidasu mukeyi bani da me aiki tunda har kuma yanzu dana ke fita aiki da safe kafin mu fita mukeyin komai tunda kuma ba wuni muke a gidanba baya yin datti. Babu kowa a palor se Baban Ali yana aiki a system dinsa ya dago yai mun kallo daya tareda mai da kai ya cigaba se na qarasa kusa dashi ciki ciki nace masa ina kwana dan har yanzu haushin sa nake ji, se ya amsa ba tareda ya kalleni ba.
A dakin Boys najiyo hayaniya da alama PS sukeyi tunda suna da Tv a dakin nan suke yin Game dukda lokaci da yawa yana dauketa saboda karsu shagala da wasa a qi karatu amma Weekend dama aikin kenan wani sa'in hardashi zasu hada anan palour suyi.
Kitchen na nufa dan naga sun kwashe kayan kan dining, a roba na tarar da dankali ciki ruwa an yanka su, nasan Amnace ta ajiyemun tunda tasan nafison dankali da an kwashe daga wuta nan da nan na maida man da sukayi suya na zuba kafin na debo kwai guda uku na fasa tareda zuba abubuwan da nake da buqata a ciki, ina kwashe dankalin na maida wani pan din na soya kwai, scramble nayi dan ban fiya son me fefe ba na juye akan plate din chips na zuba Ketchup a gefe na fito. Ta gabansa na wuya ina juya jiki tareda baza masa qanshin turarukan dana fesa aikuwa naji yanda yaja numfashi da ajiyar zuciya ina kuma jin idanunsa akaina har na zauna a dining amma kafin na juyo ya dauke idonsa, girgiza kai nayi ina sake cika da mamakin Bashir a raina haka naja kayan tea na hada ina ci ina dan kallon drama da akeyi a Tv.
Har na gama ci babu wanda ya leqo a yaran Gogan ma anata latsa laptop kamar besan Anyi digona a palour ba sena taso na dawo cikin palour na nemi 1 sitter dake facing nashi na karkace ina latsa wayata nima. Whatsapp na shiga group dinmu na Secondary na bude aikuwa na tarar da chats bila adadin, ban samu damar bi ba saboda wasu ne suke qara shigowa se kawai na fara bi daga nan. Ban karanta message din mutum hudu ba na fuskanci dalilin ubannin messages din dana gani ashe Labor zaayiwa kishiya (Labor prefect dinmu da muna school kuma abin dadin qanwar daya daga cikin yan ajin namu qawarta ta hannun dama zaa auro mata, tasan mijin zeyi aure amma bata san yarinyar ba se yau da taje karban lefen Qanwar Qawarta taga dangin Mijinta ne yan kawo lefen π€£π€£πππ€£π€£π)
Wata muguwar dariya na sheqe da ita har ina kwarewa da ta saka Baban Ali dagowa ya zubamun ido, yasan Ma'u sarai tabbas mugunta ta gano shine dalilin wannan Dariyar. Be gama tunanin kuwa ba na fara voice note still ina dariyata nace "Alhamdulillahi layi ya fara ja ashe? To Allah ya qarawa mazajenmu budi suyi ta auran mana qannemu" na tura ina sake sheqewa da wata dariyar ganin yanda Safiya Sani Labor keta kumfar baki da daukan Alwashi kala da kala ita ma yayar Amarya Zulaiha Balarabe tana aiko da nata.
Masifar da Safiya takeyi seta tunamun da lokacin da za'ayimun tawa kishiyar mun hadu gurin gate together dabanyi niyyar zuwa ba saboda a lokacin bana cikin nutsuwata. A kallo daya zaa gane damuwar da nake ciki duk na hargitse, na tuna yanda ta sakani a loko tana mun wa'azi.
"Wallahi Asma'u kin bani mamaki kin kuma bata wayonki kamar wadda bata san Allah ba, duk ina karatun islamiyyar da kikayi? Kin karanta Alqur'ani tsaf kin haddace da fassara amma kina nema ki kasa aiki dashi. Karin auran nan kinsan umarnine na Ubangiji in har Namiji nada hali da biyu akace ya fara sedai ko in baze iya adalci ba ko kina so kice Bashir ba Adali bane?? Sannan ma ke ai kiji dadi koba komai kinsan wadda za'a auro miki ciki da bai baki da fargabar azo a tarwatsa miki gida tunda Ai Amirah kusan tarbiyyarki ce ma. Haka matar nan ta dage tanamun wa'azi har na sauketa kan layin gidanta mukayi sallama na wuce a raina ina Addu'ar insha Allahu itama se an mata taji in da dadi (Ni fa alokacin duk wanda ya bani haquri se na masa Addu'a Allah yasa shima a masa kuma Alhamdulillah gashi tana karbuwa kuwa π€£π€£).
Wani mulmulen ashar ta dannomun bayan taji voice dina nan kuwa na samu nayi na ci gaba da kunnata kafin kace me fada yabar kan Yayar Amarya ya dawo kaina harta na jcewa qila dani aka hada baki nace oho dai aikin gama ya gama biki saura 2 weeks , wannan nishadi ya mantar dani wanzuwar Baban Ali a gurin har wurin 12 sannan yara suka fito muka ci gaba da sabgogin mu. Gaba daya dai haka muka cinye weekend din ba dadi tsakanin mu Monday muka koma aiki. Office dinsa yafi kusa da makarantar yara dan haka kullum shi yake fita dasu ni kuma tunda ina rigashi tashi sena biya na debo su amma yau bayan mun fito gaba daya har Ahmad ya kama handle ze bude gaban mota ya dakatar dashu da cewa "kuje Maminku ce zata kaiku"
Sororo nayi ina kallonsa araina nace meye haka toh sukuwa yara suka dauki Murna dan dama mitarsu kullum yawanci Friends dinsu Momys dinsu ke kawo su school dalilin ma daya sa na dawo ina dakkosu ke nan dan da duk shiyake hadawa. Tafiya ta qaru haka nayita sauri gudun makara na samu na ajiyesu amma dukda haka ni seda nayi latti dan school din tana gaba da office dina innaje sena dawo baya while shi kuma yana gaba da school din dole seya wuceta zeje nasa office din.
Wuni nayi ina mamaki wato duk sati da sabon salon da ze bullo dashi? Allah dai ya kyauta.
A daddafe muka cinye satin kullum kuwa sena makara dan kafin na kaisu na juyo traffic ya fara haduwa, abun takaicin wani sa'in zamu hadu a hanya har Horn ze mun in na tsaya ajiyesu ya wuce ni abin na qona mun rai ni kuma nayi alqawarin bazan masa magana ko na tambayi dalilin dayasa yake hakan ba nasan dai duk sare sarin neman fitina ne in tanka su samu nayi dani a dangi to an dena (Dangin fulani dangin magana π).
Muna haka Weekend ya zagayo wannan karon ma yaransa ya diba suka fita yawonsu, abunda ya ragemun haushi ranar Saturday wuni nayi rama baccin gajiyar sati daban samu nayi ba danayi sannan Sunday fita mukayi nima da Matan layin mu dama muna haka once in a month zamu hada picnic muje beach a dan warware takaicin Namiji ππ mu shaqi iskar duniya to wannan Lahadin ma can muka wuni dan a gida na fita na barsu ma muka dawo kusan lokaci daya.
Yanda Bashir ya tsume haka nima na tsume na fita a sabgarsa sam tunda haka yake da buqata ina jinsa ze raba dare yana waya da Amaryarsa har inji yana ce mata tayi haquri ta kusa dawowa kusada shi ai, wani lokacin naji haushi wani sa'in nayi mamaki kai Namiji dai a barshi kawai.
A da idan aka cemun Bashir ze sake kallon wata mace da sunan soyayya zance qarya ne amma daga sanda ya koyamun hankali ko ji nayi mace na shan Alwashi akan Namiji zan dakatar da ita dan tabbas Akan Bashir na sake yarda da akace Namiji Badan goyo bane (Inji Asma'u fa π).
Ranar Laraba na tashi da ciwon kai da ya saukar mun da zazzabi, ina nade akan gado har Bashir ya fita masallaci, a zaune na iyayin sallah ina idarwa na koma kan gado na nade har ya dawo ya fara shirye shiryen fita office. Dukda ya ganni akwance which is unusual hakan be saka ya tambaye ni dalili ba abinda yai matuqar qona mun rai ace har mun kai matsayin haka kamar wasu maqiya to wai duk me yayi zafi ne?
Seda ya gama shirinsa tsaf sannan ya kalleni
"Yau bazaki je aiki ba kenan? Se ki tashi ki miqasu karsu makara" yasa kai ya fice daga dakin. Wasu hawayen baqin ciki ne suka fara tsere a fuskata, idan Bashir ya gaji da zama dani gara ya fito ya fada mun yafi wannan Kisan mummuqen da yakeyimun ai, shigowar Jafar ta sakani share hawayena, ya matso kusa da ni yana cewa
"Mami mun shirya fa ko Abbi ne ze kaimu yau?" Cikin muryata da kuka ya fara dishewa nace mace
"Kuje maza ku bishi Jafar bani da lafiya"
Nan da nan fuskar yaron ta chanza zuwa tausayi yace "sorry Mami kinsha magani toh?
Bari na hado miki breakfast to Abbi baze kaiki Asibiti ba?"
Dole na qirqiro murmushin dole nace "it is not that serious Jafar Kaina ne yake ciwo nasan stress ne dana qara hutawa ze dena, maza kuje ku tafi and don't tell your brothers ku wuce Makaranta kawai Allah yai muku Albarka ya bada Ilimi me amfani" na qarasa ina dafa kansa se ya amsa da "Amin Mami Allah ya baki lafiya, Bye love you" ya mun peck a goshi ya fita da sauri dan su kansu kwana biyu ba wani gane kan Abbin suke ba.
Yana fita na miqe dakyar na tsaya bakin window ina hangensu,
Shiya gaya musu Abbi ne ze kaisu dan haka suka fita da sauri dan har ya gama Shan Tea ya fita yama kunna mota. Da ido ya bisu ganin sun jere masa a gaba, cike da baqin miskilancinsa yace " yadai kunzo kun mun layi a gaba?"
"Abbi Mami ce tace kai zaka kaimu bata da lafiya" cewar Jafar.
Seda gabansa ya fadi jin bata da lafiya dan ciwon Asma'u ba abune me sauqi ba, irin mutanen nan ce da suke dadewa basuyi ciwo ba amma in ya kwanatar dasu kamar bazasuyi ba. Harya niyyata daya koma yaji me yake damunta se wata zuciyar tace masa qila dan taja attention dinsa ne ya sakata kwanciya tace musu bata da lafiya dan Asma'u can pretend yasanta sarai dan haka ya qara gintse fuska tareda bude qofar sa ya shiga yana cewa "kuje ku ce mata tazo ta kaiku you are getting late"
"Abbi kana jifa yace bata da lafiya base ka kaimu ba tunda hanyar zaka bi" Farida ta fada dan ita yar gaba gaba ce daman, be amsata ba yai wa motarsa key ya qara gaba se suka rakashi da idanu gaba daya kamar yanda nima Mamakin sa ya nemi kashe ni a tsaye BASHIR dai shine haka? BASHIR dana sani me jarabar son yaya da tattalinsu kamar kwai, to kodai shiga tsakanin mu akayi da BASHIR ne?????https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS
ππππππππππππππππππππππ
WATA KISHIYAR π₯°πΉ
(Alkhairi CE KO SHARRI)
ππππππππππππππππππππππ
Na Maryamah_Mrs AM
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.