Wata Kishiyar Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: WATA KISHIYAR.txt
Chapter 57 of 66
Page 56
“Innalillahi Addah ta qona shi” Amirah dake zaune akan gado ta dora hannaye biyu akai tana fada.
“Kan bala’i kika qona shi To wallahi kin taro ruwan dafa kanki daman ni kika so ki la’anta kenanAllah ya kareni tsiyarki ta fada akan Dana ai kuwa bazamu yarda ba daganan har kotun qoli” Addah ta sake hayayyaqowa matar dake tsaye tana numfarfashi.
Irin shinqimemiyar nance ta gaske, itama cikin masifa da yarbanci ta hayayyaqowa Addahn, wato da gani fadan a duhu akeyinsa dan babu me gane yaran wani a cikin su gefe kuma ga Nurses biyu da suna ta faman bada baki amma ko wacce ta kafe taqi haqura.
Cikin radadin Azaba Bashir ya juya ya fita daga dakin dan har seda ya cire takalmin qafar da ruwan ya zuba. Kai tsaye dakin likitan da yake duba Amirah ya nufa yana dingisa qafa suka ci karo dashi a hanya
“Yawwa Engineer wannan wace irin mata ce ka kawo mana gaba daya tazo ta tayar wa da mutane hankali kamar ta manta Asibiti tazo? Muji ka fita da ita kuma karta sake dawo mana. Kai itama matar taka bari kawai a rubuta muku sallama idan yaso ta ringa zuwa daga gida ana dubata kawai” Likita ya tare Bashir tun kafin shi yayi masa magana.
“Ka taimaka ka fara dubamun qafata farko ruwan zafi suka watsa mun” Bashir ya fada yana zama a kan kujerar dake gaban Office din likita, se likitan yayi saurin durqusawa ya kama qafar yana haskawa, Dakin wanke ciwo suka tafi Allah ya so shi qunar iya sama ce dan haka magani kawai aka saka mishi ya rubuta masa wanda ze siya yasha sannan ya gaya masa ya dan dakata da saka takalmi saboda karya takura fatar ta kwaye.
Saboda baqin ciki ko dakin be sake komawa ba yayi tafiyarsa gida a ransa yana ayyana irin abinda zeyi musu daga Addan har Amiran idan suka dawo masa gida.
Hajia Addah kuwa abinda ya faru Bayan ta dawo daga gidan Ma’u ranta a jagule da irin tarbar da Ma’un tayi mata. Sam bata taba tsammatar haka daga gareta ba saboda yanda tasan Ma’u da haba haba da lamarinsu ada idan suka je gidanta kamar zata goyasu saboda kirki amma yau ita tayiwa wannan korar kai tsaye ba tareda wata shakka ko shayi ba koda yake ada Suruka take a wajenta a yanzu kuwa babu sauran alaqa sedai ta kara kawai ai.
Babu abinda ya qara tayar mata da hankali irin nutsuwa da kyan da taga Ma’un ta qara ga uwar daula data zuba a gidan ta dan yafi na Bashir din sau biyar wallahi jifa wasu kujeru tana zama akai taji ta ta lume qa qamshi ta ko ina duk se taji ta raina gidan Bashir yanzu data dawo ba kamar zuwanta dazu ba da ta ga gidan kamar wadda taje wata Villa yanzu kuwa se taga duk ya zamar mata wani qauye dama ga rashin gyara gaba daya dai abin ya zama se a hankali.
Tana zaune ta zabga tagumi Aliyu nata buga Game dinsa dan be nuna alamar ma yaji shigowar mutum ba sega sallamar Jafar da kwandon Abinci. Bata jira ya qaraso ba ta taro shi dan dagaske yunwa takeji, badan bazata gane ta inda suka shigo unguwar bama da fita zatayi tunda da yan kudinta a jaka ta nemi abinci to Lagos kuma abinci ai se kalar wanda ta zaba zataci.
Haka ta zauna tana ci tana zubawa Ma’u Albarka seda ta cinye kwan nan tas da sinqin biredi ga qaton kofin data zuba shayi tayi gyatsa kafin ta dakko wayarta tana kallon Jafar tace
“Kai Allah dai yawa uwarku Albarka yasa kuma kuji qanta, ungo nan ka duba zakaga wata lamba da aka kira qarshe ta wani qedari ce da ubanku yace ze zo ya kaini Asibiti na duba Antyn ku kirashi maza kace na shirya idan kuma zaka rakani to se mu tafi tare”.
Lambar Samuel Jafar ya nemo ya kira ya gaya masa saqon Addah, yana qunquni ya amsa gashi nan zuwa dan dazu daya dakkota har suka Zo tana zabga masa masifa dukda bajin abinda take fada yake ba amma yasan zaginsa takeyi.
“Kai nima dai Jafaru zaka fara koyamun turancin nan tunda naga garin gaba daya kowa shi yakeyi karna fita wata rana na manta hanyar gida na rasa waze dawo dani” Ta fada tana dariya bayan daya miqa mata wayar yace Samuel din yana zuwa.
“Allah yasa na ki fitan ki bata daman yan yankan kai na garin nan sunfi son irin ki masifaffun tsofaffi ai” Aliyu dake gaban Tv ya fada ba tareda ya juyo ya kalle ta ba, nan kuwa ta hau sababi tana fadar sedai a sace uban sa badai ita ba shege me baqin hali. Dake dangado ne kuwa ya manna mata hauka tayi tayi ba ita ta haqura ba seda Jafar ya gaya mata ga Samuel ya dawo sannan ta fita, tayi tayi su tafi tare yaqi dan yana Tsoron Maminsa haka ta kama hanya tana ci gaba da mitar ta.
Har bakin dakin da Amirah take Samuel ya rakata ta tura qofar tareda doka uwar sallama kamar me magana da yan sama dai dai nan abokiyar zaman Amiran da aka kawo jiya da daddare tana fama da matsanan cin ciwon kai dakyar aka samu tayi bacci a sannan Mahaifiyarta dake jinyarta na zaune suna hira jefi jefi da Amirah cikin harshen turanci sega sallamar Addah.
Cikin sauri tayiwa Addah data shigo tana sake jaddada sallama da qarin ko bacci sukeyi ne alamar tayi shiru da hannu tana nuna mata yarinyar da har ta fara mutsu mutsu alamar tana son farkawa.
“Ji wata masifa Allah ya tsaga mun baki a ringa mun alama wai nayi shiru in ke bakya amsa sallama ai ita Amiran yar musulmai ce balle kice duk kune aikin banza kai” Addah ta fada cikin daga murya tana kaiwa zaune kan kujrar dake gaban gadon Amirah kafin taci gaba da cewa
“Haka kika qanjale Amirah sannu ko da yake iya jarabar Bashir kadai ta isa ta ramar dake kai wannan Bashir dai ko azababbe daga zuwana fa harya...”
“Dan Allah Addah kiyi shiru dakyar aka samu tayi bacci wallahi kanta ne yake ciwo sosai” Amirah ta katse ta kamar zatayi kuka ganin yarinyar ta fara riqe kanta da alamar ta farka daga baccin kenan. Cikin masifa Addah ta waiwaya ta kalleta tace
“To ni ina ruwana? Ni na dora mata ciwon da za’a hanani magana ko yaya ina da akwai dakin masu kudi da mutum ze zauna shi kadai me yasa basu kama can ba se kuma ni a takurani ke dallah karki qaramun bacin rai akan wanda nake ciki”
Kuka yarinyar ta fara dan ba ita da take ciwon kai ba ko me lafiya dole kansa ya buga irin yanda Addah take taqarqarewa yana daga murya kamar me magana da yan sama. Masifa ta shigayi ita dai matar tana ta qoqarin kama yarta dake fizge fizge ganin abin ya fara yawa yasa ta fita da gudu se gata ta dawo da Nurses guda biyu suka rufu akan yarinyar qarshe se fita da ita dga dakin sukayi saboda yanda Addah ta qiyin shiru gashi anyi anyi ta fita daga dakin taqi se zabga salallami take wai wannan wane kalar sharri ne daga zuwanta se kace wata mayya yarinya zata fara fizge fizge to Allah ya isanta.
Tana cikin sababin matar data bi bayan yarta ta tabbatar da lafiyarta ta dawo dakin ba tareda Addah ta ankare ba tayi kanta tana zazzaga mata masifa cikin yarbanci bakinta ne mutu ba itama ta shiga zaginta da Hausa Amirah dai ka tsakiya tana basu haquri amma babu meji data ga suna neman bawa hammata iska seta koma kan gado ta zabga tagumi kawai tana kallonsu da abin yayi tsamari shine matar ta jefawa Addah flask dai dai sanda Bashir ya shigo tsautsayin ya fada akan sa.
Shiru sukayi gaba daya suna kallon Bashir din daya juya ya fice daga dakin, matar ta dora hannu tana yan tsalle tsalle irin nasu tana kiran Jesus Addah ko harara ta maka mata tace
“Ai wallahi se mun daure ki, badai kin qona mun Da ba wato da kasheni kikayi niyya ko? To ki shirya yanzu za’a turo miki sammaci wallahi” A fusace ta juya kan Amirah da duk ta rikice tace
“Ke kuma kukan uwar me kikeyi dallah taso muje mu ga halin da qafar take ciki idan ta sale Aradu sena qonata itama haka kawai zata nakasa mun dan Yar uwa bazan kyaleta ba.
Suna fitowa daga dakin Nurse ta taresu ta miqawa Amiran Farar takadda ta sallama dole suka koma suka hau tattare kaya.
Haka suka fito harabar Asibiti neman duniya babu motar da Aka kawo Addah balle kuma ta Bashir da daman basu saka ran ganinsa ba. A wayar Addah Amirah ta shiga kiransa dan ta gaya masa an sallame su ya turo Samuel ya kaisu gida, kiran Farko harta qaraci ringin be daga ba ana biyu kuwa aka ce mata wayar ma a kashe take.
Lambar Samuel din da Addah ta nuna mata ta kira ya daga suka gaisa kafin ma tace sake magana ya gaya mata Oga ya aikeshi Abeokuta ze kai wani saqo kamar zata rusa kuka haka ta kashe wayar suka samu qasan wata bishiya suka zauna gashiba wani gama jin qwarin jikinta tayi ba dan cikin nata bana me zafin laulayi ne ga Addah da taqi yin shiru se masifa take wai an musu wulaqanci yanzu ta ina zasu koma gida.
Dabarar sake kiran Samuel tayi akan ya gaya mata kwatancen unguwar tasu idan yaso ko Taxi ne se su hau ta kaisu, hakan akayi sukayi shahada suka hau Taxi dan Addah tana shiga ta tuna da fatan da Aliyu yayi mata dazu nan da nan ta jawo jarbi ta hau ja baki ya mutu basu suka saki ransu ba seda suka gansu a qofar Estate din kafin kowacce ta saki ajiyar zuciya.
Har qofar gida ya ajiye su, suka sauke kaya Addah ta zuge jaka ta ciro dari biyar ta bawo me Taxi ta qyafe tana jiran ya miqo mata chanji. Kallonta yayi ya kalli kudin kafin ya juya kan Amirah ya fara tambayarta kudinsa tunda ita ce mejin Turanci.
Tambayarsa tayi nawa yace mata dubu goma zasu bayar tunda Drop suka dauka ta waiwaya ta kalli Addah tace
“Addah dubu goma ne kudin motar, ki bashi dan Allah idan mun shiga ciki se mu warware na gaji ni jiri nake ji” ta juya zata shige cikin gida Addah ta fizgota tana cewa
“Dan fashi ne ya dakko mu ko yaya? Wannan tafiyar Asibitin da bata fi nayita a qafa ba inda nasan hanya ita ce zakice a bashi dubu goma saboda ubanki ne ya bani ajiyar kudin?
To banda su, dari uku nayi niyyar bayarwa shima saboda an shigo damu ciki ne amma da a bakin get ya ajiye mu dari dari zan bayar seki nemi dubu taran ki cika masa” ta mayar da dari biyar din cikin jaka ta harhado yan hamsin da dari na dari uku ta watsa masa tayi gaba abinta.
Kamar Amirah zatayi kuka ta shiga roqon ta data bayar zata biyata dan ita sisi bata magani a hannunta ko a cikin gidan gashi babu motar Bashir ballantana tace yana gida zata shiga karbo ita kuwa Addah fafur taqi qara ko sile sema masifa da take zazzagawa me Taxi daya juya P cap baya yana jira yaga zasu bashi kudinsa ne ko se ya dauki mataki.
Ganin suna neman bata masa lokaci gashi wadda yaga kamar kudin a hannunta suke na neman shigewa gida yasa ya fizge jakar Addah, babu bata lokaci ya zazzage komai a qasa sega kudi kuwa suka zubo ya irigi dubu gomansa cif ya shige mota ko kula ihun barawa da Addah take zundumaqa beyi ba ya qara wuta abinsa to masu wucewa ma babu wanda ya kulasu dakyar Amirah ta turata suka shige gida se dafe kanta take daya dauki ciwo saboda bala’in Addah.
A cikin gidan ma Sabon tashin hankali ta dasa mata akan kudinta ganin babu sarki se Allah yasa ta shige daki ta kullo kanta, wayarta ta shiga dubawa dan ta kira Bashir ko ze zo ya kashe wannan wutar ta ganta amma babu chaji seta jona ta shiga wanka saboda jikinta sam babu dadi.
Lokacin data fito wayar tadan caju, lambarsa ta shiga kira yanzu a kunne take amma kiran na shiga za’a katse shi ta kira yafi sau biyar qarshe dan kanta ta haqura ga yunwa tana ji amma tsoron karonsu da Addah idan ta fita palour yasa ta gwammace ta sha ruwa da wani Biscuit da yake a dakin ta kwanta ledar magungunanta kansu suna palour haka ta haqura bata sha ba.
BASHIR
Daga Asibiti kai tsaye gidan Musa ya wuce dan yanzu can kadai yake iya zuwa ya rage zafi tunda Musan shi kadai ne bashi da mata.
Cikin jimamin abinda ya sami qafarsa ya tare shi, ya ringa masa sannu kuwa qasan ransa kuwa dariya ce fal musamman dayaji wai da surukarsa ake fada tsautsayi ya fada kansa suka qonashi shi kuwa Bashir wace irin sirika yake da ita me fada da mutane a Asibiti?
A gidan ya wuni zir, duk dai hirar da sukayi akan yanda ze gyarota da Ma’u ne dan ya gayawa Musan yanda sukayi da Abubakar, shi ya qara bashi kwarin guiwa akan ya ci gaba da binsa yana bashi haquri wata rana ze dace sannan kar ya daga qafa a Gurin Ma’u duk irin wulaqanci da cin kashin da zata masa ya daure daman ance ai ramuwar gayya tafi ta gayya zafi amma idan yayi haqurin buqata ta biya shikenan shi yaci riba.
Shi ya sake bashi shawara ya ringa tura mata text na ban haquri akai akai. Gyara zama Musa yayi yaci gaba da ce masa
“Kaifa matsalar ka Bashir na fuskanci gaba dayanka se a hankali yar soyayyar nan naga alamar baka iyata ba se tsare gida da hade fuska kawai. Sufa mata da ka gani suna son tattali da kulawa ko baka da sisi indai mace na samun nutsuwa da Farin ciki a gurinka zata Yi haquri ta zauna dakai amma ko kafi qaruna kudi indai ta rasa wannan ba ko wacce bace dukiya take a gabanta zata iya rabuwa dakai ta tafi inda aka san darajarta ne ko kuma tana tare da kai ta ringa kula wasu cana waje da suke bata kulawa suna yabonta.
Da yawa maza mu muke bada qofar da matan mu suke aikata wasu abubuwa da basu kamata ba a bayan idon mu. Yanzu misali kaine kullum cikin hade rai a gidanka, kaida matarka idan taga haqoranka to magana kakeyi babu dariya babu lafazi me dadi balle ace tayi kwalliya ka yaba ko ka zauna kayi wasa da raha da ita tsakanin ku se bada umarni kamar wata yar aiki da ubangidanta dan Allah ta yaya kake tunanin idan ta hadu da wanda ze bata duk irin wadannan kulawar data rasa a gurinka ba bazata kulashi ba?
Ba kowacce mace ce take da qarfin zuciyar daure wasu abubuwan ba, wata koda ba ta sigar fasiqanci ba, wata da sunan aboki zakaga ta hadu da wani namiji da zasu zama kamar wasu Qawaye ko Aminai duk wani sirri nata daya kamata ta yi shi tare dakai shi ze maye mata gurbi ya zama abokin shawararta se kaga matar aure wai tana da wani Besty duk waya ja Mijinta kuma ka tabbatar duk dakon zunubin da zatayo tare za’a kasafta muku dan kai ka yanka mata tikitin da har zata kula wani banza can da auranka.
Ka duba yanzu ko a gurin aikin mu yanda mata suka lalace matan aure kaga suna qazamar rayuwa suna mu’amala da wasu mazan a waje da bana auransu ba a kaso goma idan ka tarasu bakwai wallahi mazansu nada sa hannu cikin fadawarsu wannan halakar saboda basu da ma lokacin su ballantana su san damuwarsu har su maganta musu ita da yawan maza muna dauka kudi shine maganin ko wacce matsala idan ka wadata mace shikenan ka gama mata komai wanda sam abin ba haka yake ba dole ka kula da matarka ta kowanne bangare ka tabbatar da cewa ka toshe mata duk wata buqata idan kayi haka kuma kaga wata matsala ta faru seka qaddara cewa jarabawa ce kuma daga ubangiji amma ba wai dan kai ka bayar da qofar faruwar hakan ba.
Dan haka nidai shawarata Bashir ka canja takunka, ba Asma’u ba ko wacce mace zaka zauna da ita dole ne kasan qima da martabarta. Ka sani cewar ba Alfarma kayi musu daka auresu ba ballantana ka dauka dole suyi haqurin zama dakai da halinka Aa zamane na ibadah da Allah ya hadaku kowa yana da haqqi akan dan uwansa”
“Haka ne kuma zanyi qoqari na gyara kuskurena Musa dan ina buqatar Ma’u a rayuwa ta wallahi” Bashir ya fada bayan daya sauke tagumin da yayi.
“Au saboda ka dawo da Asma’u zaka chanja hili kenan? Bashir bari fa na gaya maka gaskiya Halinka cikin goma bakwai basu da kyau ta fannin zaman takewa. Kai bafa matanka ba kadai mu kanmu haquri muke dakai wani lokacin saboda shi hali zanen dutseaka ce ba’a chanza wa mutum shi amma a wannan karon in har kana so lamuranka su daidaita dole fa seka daidaita sahu a to.
Kai in banda ma halinka Bashir a zamanin nan ka samu mace kamar Asma’u bafa ajinka bace wallahi in ma gaya maka gaskiya Allah ne kawai ya kashe ya baka ka samu tana sonka take hidimta maka da jikinta da Aljihunta, matar nan fa ko daure fuska kayi se hankalinta ya tashi. Ka tashi ka tafka mata kishiya ta wulaqanci koni Namiji naji zafin abinda kayi ballantana ita sannan ka qara mata da tukwuicin saki kai ni idan ta haqura da wuri ta dawo maka gaskiya bata mun daidai ba”.
Daure fuska Bashir yayi tamau yana kallonsa yace
“Karka kuskura kace mun kaima kana son matata dan shine mafi girman kuskuren da zaka aikata, mu kadai ne a gidan nan yanzu zan murqusheka ka mutu Ba wanda yasan meya faru”.
Dariya Musa yayi harda fadowa daga kan kujera kafin yace
“Maida wuqar Malam ashe daba ka fara ban sani ba. Ai ni idan zan so Ma’u bazaka sani ba, qila se kaji nayi aure kawai kazo gidana ka ganta a matsayin matata amma ni sam ba haka nake ba, babu kuma haka a tsakanin mu kawai dai ina nuna maka irin girman asarar daka tafka ne a rayuwarka kuma idan baka hanzarta ba kana ji kana kallo sedai ka mutu kana cizon yatsa da daka sani ka mayar da yayanka marayun dole ka rabasu da uwar su haka kawai”.
Ganin da yayi daga shawara kuma abin na Musa na neman ya koma wulaqanci yasa yayi masa sallama ya kamo hanyar gida, a hanya ya tsaya wani guri da suke siyan Shawarma da wani Gas meat da Ma’u take bala’in so ya siya da yawa ya hado da Madarar ruwa da kwali itama kalar wadda take sha kafin ya kamo hanyar gida.
A qofar gidanta ya ci burki, a waya ya kira Amnah yace tazo ba tareda ya fito ba ya ce ta bude bayan motar ta kwashe ledojin ciki.
Ya dade a mota kafin ya fito qafa daya da takalmi daya babu ya dauki tasa ledar Naman da Madarar ya shige gida, Hajia Addah na zaune a palour ta tasa Amirah data gama zaman dakin ta fito a gaba har sannan dai zancen dubu goma yaqi ci yaqi qarewa.
Kallo daya ya musu sanda Amirah ta masa sannu da zuwa ya wuce daki tabi bayansa, tun dazu take jira ya dawo ita dai ya taimaketa ya biya Addah kudinta kota samu ta shaqi iska a gidan yana shiga dakin kan ya rufo tayi wuf itama ta fada ya kuwa balla mata harara ta sunkuyar da kai se ya wuce ya ajiye ledar hannunsa ya shiga bandaki.
Tana zaune se hadiyar yawu take saboda qamshin naman da duk ya cika dakin ya fito, kamar munafuka tayi qasa dakai tana gaishe shi ya amsa a taqaice yana cire rigar jikinsa ganin taqi fita yace mata
“Lafiya?”
“Am daman Yaya an sallamo mune na kiraka da wayar Addah lokacin baka dauka ba na kira Samuel shima yace mun...”
“Na sani na aike shi ba gashi kun dawo ba se akayi yaya to?” Ya katseta murya a cunkushe, qasan ransa har yana tunanin wane hankali ne yazo mata da har tayi tunanin zuwa ta duba shi kodai Addah ce ta sakata dan yasan a kalar nata tunanin dai bazatayi ba, maganar tace ta katse shi da take cewa
“Daman Taxi muka hawo ta dawo damu, shine seda muka zo yace wai kudin motar dubu Ashirin tunda drop muka dauka to Addah ce ta biya tun safen take ta mun masifa akan na biyata kudinta kuma ni ko sisi bani dashi nayi ta kiranka ma dazun kana rejecting gata can wallahi ko abincin kirki ta hanani naci da masifarta”
Wani mugun kallo me nuna zallar bacin rai yake aika mata, wato kudi take da buqata tun dazun dalilin kiran da ta ringa masa kenan, qonewar da uwarta taja masa ma bata dameta balle taji ya qafarsa kawai kudi ze bata a mugun fusace ya nuna mata qofa ba tareda yayi magana ba.
Amirah dake ta Addu’a a ranta Allah yasa ya bata goman ta ajiye dan tunda tazo sile biyar bata hadasu ba kai ko katin waya bashi ne kusan dubu biyar taci na Mtn saboda ya dena saka mata, da tana Gombe kuwa duk satin Allah yar dubu dayar nan dai seya saka mata wani lokacin ma biyu ga yar cuwa cuwar da takeyi ta karbi kudi a hannun Naziru na cefane anan kuwa shi yake siyo komai kuma se abinda ta gani kawai dan waca wacar nan data san anayi a gidan bata san me yasa yanzu kusan komai a qididdige yake ba ba yanda ta saba ganin sanda Anty tana nan komai na danqare a Freezer ba sedai su bude su diba.
Ita da yake ya raina mata hankali se abinda yaga dama yake siya ya ajiye kuma idan ya qare abinda yake ci ze siyo da wuri, daman nama ne yafi damuwa dashi, tana son kifi amma tunda tayi masa wani farfesun kifi ita kanta dai ranar data ci haka qarnin yayi ta taso mata be sake siyowa ba tayi nacin harta gaji to tunda ta samu ciki ma ya dena cin abincinta, daman yaran ba ci suke ba sedai su dafa abinda suke so ko su shigo dashi daga can gidan sedai tayi ta qara qararta ita kadai ga cikin me dan banzan kwadayi haka zata yita hadiyar yawu idan ta jiyo qamshin abincin makwafta.
Tsawat daya daka mata ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi dan ashe yana ta mata magana ma bata ji ba, da sauri ta tattari qafarta tayi waje tana fita suka kusa karo da Addah dake labe a bakin qofa cikin matuqar takaici Amirah ta kalleta kafin ta wuce dakinta wata kwalla na sakko mata.
Bashir kuwa sallah kawai ya tayar dan idan ya tsaya takaicin Amirah yana iya shaqe shi kawai aga ya fadi, so kuma yake yayi isha ya zauna ya tsarawa Ma’u Saqo ya tura mata dan ya qudurce indai soyayya ce matsalar to kuwa ko Sharukan se dai yazo ya kwashi kos a gurinsa a wanna karon.
ASMA’U
Bayan dana dawo daga rabon abinci sallah kawai nayi na kwanta dan na gaji sosai bani na farka ba se dab da magriba. Kiran Yaya Abubakar na gani guda biyu na shiga bandaki na wanko fuskata da bakina kafin na dawo na zauna na danna kiran lambar sa.
Bayan mun gaisa yake cemun
“Dazu Bashir ya kirani a waya wai yana bani haquri, ban san rashin kunyarsa harta kai haka ba se yau tukunna nadai ja masa kunne akan karya kuskura ya sake kirana in ba haka ba yasan sauran”
“Lallai Baban Ali shi har yana da qarfin guiwar kiran ka kenan, haka fa jiya yazo qofar gidan nan wai yana bani haquri harda durqusawarsa” na cikin mamakin tsaurin idon Bashir.
“Asma’u” ya kira sunana da sautin da yake nuna muhimmancin abinda ze gaya mun sena gyara zama dakyau na amsa ina sauraronsa yaci gaba da cewa
“Kafin ki auri Bashir kin taba tambayata abinda yasa bana farin ciki da auran ku ko to yau zan baki amsa. Bashir Abokina ne kin sani tun na yarinta dan haka nasan halinsa ciki da bai, halayyata da tashi sunyi kamanceveniya ta wani bangaren saboda dani dashi murdaddun mutane ne da ake shan wahalar gane gaban mu.
A bangaren auratayya muna da buqatar samun tsayayyar mace me taurin zuciya da ra’ayin riqau ta yanda dole sedai ko mu zubda makaman mu mu bita ko kuma ya zamana anyi 50 50 ma’ana kowa ya riqe bangare daya bawai wadda zamu taka yanda muka ga dama ba kuma ta biyu.
Baki dace da Bashir ba saboda ke mace ce me sanyin hali da saurin yarda tareda sadaukarwa inda ace Aliyu marigayi ne ya nemi auranki dukda yaso hakan amma Bashir yayi masa shigar sauri, a lokacin da na zamo kan gaba a komai saboda nasan bazaki taba nadamar zabarsa ba saboda halayyat ku kusan daya ce, dake dashi zaku ringa rige rigen kyautatawa junan ku amma Allah be hukunta faruwar Al’amarin a haka ba ya qaddara cewar Bashir din dai shine Mijinki harda rabon zuri’a a tsakanin ku.
Banaqin Bashir saboda shima mutumin kirki ne kuskurensa kuma ajizanci ne irin na ko wanne dan Adam kuma na tabbatar da nima da ace irin ki nake aure da ko ba dukka ba se an samu kwatankwacin halayyar Bashir a cikin gidana saboda nasan duk abinda na dakko zata yarda kuma ya zauna.
Bance Bashir baya son ki ba amma ki sani son da kike masa ko nace kina bayyana soyayyarki sama da tasa shi kansa wannan babban dalili ne da Namiji ze riqe ya kuka juyaki duk ta yanda yaso saboda yasan kina sonsa zakuma ki zauna dashi a duk yanda yake.
Abinda nake so na gaya miki Ma’u, Bazan hanaki ba idan har zuciyarki ta aminta da ki koma gidan Bashir amma ki riqe abu guda daya shine ke din dai kece ba wata sabuwa ta daban ba haka Bashir yana nan a Bashir din da kika sani babu abinda ze chanza daga halayyarsa ta ainihi duk wani chanji da ze zo miki dashi na dan lokacine dole wata rana se an koma gidan jiya.
Karki duba kowa ko wani abu ki duba makomar rayuwar ki, Kin cancanci samun rayuwa me cike da Farin ciki Ma’u kiyiwa kanki gata, idan har farin cikin ki yana tareda Bashir ki koma gidansa ku zauna zamu ci gaba da binki da fatan Alkhairi kamar yanda muke miki a koda Yaushe idan kuma kina da zabin daya fishi Allah ya tabbatar miki da Alkahiri yasa kiyi farin ciki dashi na har abada”.
Shiru nayi kamar wadda aka zarewa laka har Yaya Abubakar ya gama mun magana dakyar na iya cewa
“Nagode Yaya, nima a yanzu banida wani zabi se abinda Allah ya zaba mun, in sha Allahu yau zan fara istikara ina kuma fatan Allah ya saka mun duk abinda yafi Alkahiri a zuciyata Nagode kwarai Yaya Allah ya saka da Alkahiri”
“Babu komai Allah ya jishshemu Alkhairi, Ina Yaran ina fatan dai babu wata matsala ko?”
“Babu komai Yaya, ai yanzu ma kusan anan suke dan bacci ne kawai yake mayar dasu can gidan shima wani lokacin anan suke kwana kuma baya magana dan Farida daman ta dawo nan gaba daya”
“Toh haka ake so, kin gani ko tashin hankalin daman bashi da amfani yanzu gashi a ruwan sanyi ai kusan sun dawo hannunki, Allah ya wuce mana gaba”
“Amin yah rabb Nagode yaya a gaida su Anty Nasiba” daga haka mukayi sallama ina ta juya maganganunsa a raina, matsaya daya dai na zauna akai itace ta neman zabin Allah tunda shine dahir
Bayan sallar Isha ina zaune ina lazumi sega Amnah da leda niqi niqi tun kafin ta ajiye qamshin abinda yake ciki ya doki hancina nan take kuma na gano na ina ne.
Kallonta nayi da alamun tambaya ta ajiye su kusada ni tana cewa
“Abbi ne ya kirani a waya yace na kawo miki”
“Zaki tattara ki wuce mun dasu daga nan ko yaya, me yasa daya kiraki baki zo kin gaya mun kafin ki fita ba” na fada ina rufeta da fada. Setayi rau rau kamar zatayi kuka tace
“Mami Abbi ne fa ba wani ba, kuma ai...”
“Amnah ni kike gayawa Abbi ne ba wani ba Abbin ubanki ne ko yaya? Ki shiga hankalinki Amnah kuma ki kwashe kayan nan ki fita dasu kafin na bata miki rai”.
Kayan ta diba seda ta kai bakin qofa kafin ta waiwayo ta kalleni tace
“To mu zamu ci Mami idan ke ba zaki ci ba”
“Amnah se naci ubanki idan na taso wallahi ki tattara ki mayar masa idan ba haka ba zamu gamu”
Da sauri ta fice ta barni ina mita ni kadai, qamshin naman kuma seya tado mun da tsohon kwadayi dan ina bala’in son Gashin gurin. Seda nayi Shafa’i da wutri na nayi Addu’oi kafin na fito palour ina jin badan dare yayi ba da tabbas sena fita na siyo naman nan dan dai bazanci na hannun Bashir ba.
Turus nayi daga bakin qofa ina kallonsu yanda sukayi face face da naman sunaci wasu nacin shawarma.
“Yanzu Amnah me na gaya miki?” Na fada ina kallonta, se tayi saurin ajiye Naman hannunta tana zare ido tace
“Wallahi Mami shiya ce mu cinye kuma ma seda Addah da Anty Amirah suka diba da gaba daya ma suka qwace seda Abbi yayi ta masifa kafin suka bamu kuma Addah ta sake biyo mu ta dibar musu”
“Shikenan ai kun kyauta, idan kin gama ki dafa mun Indomie ki kawo mun” na fada ina komawa ciki.
Wayata na dauka, Ina so na kira Yusuf wata zuciyar kuma tana hanani. Saqo ne ya shigo wayata, Bashir ne na bude na fara karantawa bansan sanda na bushe da dariya ba saboda ganin irin abubuwan da ya rubuto wato kalaman soyayyane kala da kala a ciki gaba daya se naga abin wani banbarakwai.
Ina gama karantawa na goge shi ina tuno da wani saqo da Yusuf ya turo mun dazu da yamma se kawai na danna kiran lambar sa.
“Allah yasa muga Annabi” ya fada yana daga wayar, senayi murmushi me sauti nace
“Amin”.
“Amma Asmy batan lamba kikayi ko?”
“Me ka gani?”
“Babu komai, kawai dai nasan kina sane bazaki kirani a waya ba sedai tuntuben lamba kikayi”
“To shikenan bari na kashe tunda haka kace” na fada kamar zan kashe din se yayi saurin tare ni da cewa
“Aa bafa haka nake nufi ba, Allah ya taimaki Amaryar Yusufa barka da dare toh ya kike?”
“Barka dai Excellency ya aiki ya Jama’a?”
“Aiki Alhamdulillah kinsan kuwa yau wunin Site nayi na dawo duk na gaji wallahi Asmy, ya gida ya yara ya kuma kewata?”
“Ni na rasa irin son kudinka dai Yusuf, idan ba haka ba dan Allah ina kai ina Wani supervision na aiki? Dan Allah ka barwa sauran Jama’a suma su samu mana”
Dariya yayi yace
“Asmy kenan, nifa ko Inyamuri baze nunamun neman kudi ba, dazu naje wani qauye zamu siyo gyada muna zuwa suka lullube motata nace kai ku matsamun ni ba wannan ya kawo ni ba neman Halal na fito yau”.
Dariya sosai nayi, daga nan muka shiga hira har Amnah ta kawo mun Indomin, Allah Alah nake mu gama magana ba tareda ya taso mun da zancen dazu ba, seda zamuyi sallama kuwa yace
“Saura kwana shida, ina Addu’a Allah yasa naji Alkhairi”
“Amin Allah ya sa muga Alkahiri” nima na fada daga nan mukayi sallama.
Ban kwanta bacci ba se gurin uku da rabi na dare, sosai nayi sallolina da Addu’oi na rufe da sallar Istikara tareda kyakykyawan yaqinin samun haske a cikin al’amarina na kuma bude zuciyata ko Bashir, ko Yusuf ko ma wani ne daban Allah ya zaba mun zan karbe shi nayi fatan ya zame min siradin zuwa Aljannah.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.