Best Hausa Novels

Bibiyata Yake Yi Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 14

PAGE 8

FREE PAGE SUN KUSA ƘAREWA KUSHIGO CIKI DAN AFAFATA DAKU."

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073

*********

Da sauri maryam tafito ta taras dani sauran Friends namu na biye da ita abaya, hakan yasa na maida wayar nafasa duba saƙon, cikeda jin Haushi Maryam tace.

*Inata yimiki magana ki jirani ko ina kika kai hankalinki? Ko saurarona bakiyiba. kuma Bakima yiwa Ummi sallama ba" hatta gama maganar bance komaiba yanayin da nake ciki bazai barni na maida mata da masifa kamar yanda nasaba ba, dan haka na sakar mata murmushi. Sai kawai tasake baki tana kallona, ƙarasowa tayi daff dani yayinda Friends namu suma suka ƙaraso wajan. Cikeda al'ajabi maryam tace.

"lafiya kike kuwa babe?" cikeda nishaÉ—i nace.

"Me kika gani?" jijjiga kai kawai tayi batareda tace komaiba tayi gaba zuwa parking-lot, ganin babu kowa a wajan yasanya ta dawo wajanmu ta ɗaga waya takira driver ɗin kusan tare suka fito da Hamma ina ɗaga idanuwa na na kalleshi zuciyata tahau bugawa da sauri, Coppee brown Shadda ce ajikinsa ɗinkin jamba kansa hula hannunsa ɗaure da agogon fata shima brown yayi matuƙar ƙyau acikin shaddannan daƙyar na iya saita kaina na ɗauke idanuwana daga kallonsa, yazo dai-dai yanda muke yayinda kamshin turarensa ya rigashi isowa, Maryam na ƙoƙarin ɗaga waya tayo kira mukaji muryarsa yana faɗin.

"kuzo mutafi" batareda ya kallemuba yayi maganar yaci gaba da tafiyarsa. Maryam tayi saurin sauƙe wayar tabi bayansa, nima na rufa mata baya."

Shirune yabiyo bayan zamanmi gabaki É—aya acikin motan saida mukahau titi batareda ya kallemi ba hankalinsa nakan TiTi yace.

"Ina zakuje?"

"Gisansu Mamee" Maryam tabashi takaicecciyar amsa,

A ƙofar gidan yakaimu ya zubamu yajuya abunsa, ajiyar zuciya na sauke a lokacin dana fita a motar danko kwararren numfashi nakasa jaa gani nake kamar daga numfashina zai iya fahimtar abunda yake cikin zuciyata."

ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin gidanmu na buɗe mana muka shiga, muka ratsa da harabar gidan har zuwa cikin gidan, fadeelah takasa haƙuri tafara faɗin.

"Zainab Ashe kuma gidanku masu kuÉ—ine" Hafsa wacce muka taho tareda ita tace.

"Ai daga gani yanda kawancensu yayi ƙarfi itada maryam kinsan dole sai dai idan matsayi yazo ɗaya"
Fadeelah tace.

"bantaɓa saniba sai yau" murmushi kawai nayi musu, dan Tabbas ga duk wanda yaga gidanmu zaiyi tsammanin cewa munada dukiya sosai, amma mu kaɗai damuke rayuwa acikin gidan mukasan irin halinda muke ciki, Sai dai kawai muce Alhamdulillhi."

Ɗakin mama muka wuce Kai tsaye a falo muka zauna mama na ciki natashi nayi ciki Maryam tabi bayana cikin drinks ɗinda aka siya san walimar sauƙarmu na ɗebo musu haɗeda ruwan pure water na ajiye."

Maryam tafito tawuce É—akin anty danyi mata godiya Muna zaune tadawo ta samesmu,

Anan muka zauna sai wajan biyu kafinnan suka tafi."

Wunin ranar gabaki ɗaya nayishi cikin farin ciki sakamakon abunda yafaru tsakanina da Hamma iya tsawon samina dashi bantaɓa ganin ya kalli yanda nakeba sai ayai da idanuwanmu suka sarƙe cikinna juna, ba shakka Hamma yanada kwakkwaran dalilinsa daya sanya baya kallon mutane ido cikin ido mai yiwuwa ya gane akwai ƙwayar halittar kyau a cikisu wanda zaija hankali haɗeda fuskar mai kallonsu.
Har Æ´an gidanmu saida suka gane farin cikin danake ciki amma sai suka É—auki hakan A É—aukin walimar dana keyi.

Ban sake bi takan wayarba barema na tuna da saƙon da aka turo dan wasu lokuta nakanji kamar nadaina buɗe saƙonma gabaki ɗaya, nayi blocking numbern yafi sau babu adadi amma haka zanji shigowar saƙo ina dubawa zanga blocking ɗin dannayi ya sauƙa, shiyasa hankalina yafi karkata ga cewa aljani ke turamin message.

Wajajen la'asar muna zaune nida Anty fadeelah da Aysha mama ta shigo É—akin. Tana kallonmu cikeda sha'awar yanda ta samemu muna hira tsakaninmu na Æ´an uwa, dukanmu mukayi mata sannu ta amsa, sannan ta dubeni tace.

"Mamee kifito kizo ki tafi aikar Habibu shinkafa kam na aika ansayo, nasan yanzu yakusa isowa ko jallof kiyi masa da Æ´an haÉ—e-haÉ—e.

"Toh Ganinan zuwa Mama yanzu zan fito" mama tajuya tana faÉ—in.

"Gara kifito dan nasan yakusa sauƙa" bayan fitar Mama Aysha tadubeni tace.

"Habibu É—an uwanki yayanki ne zai dawo?"
Bankaiga bata amsa ba Anty fadeelah ta jefa mata harara haÉ—eda faÉ—in.

"keba É—an uwanki bane?" Aysha tace.

"maida wuƙar nifa haka nake nufi ba ina nufin Yayanta"

"Kema ai yayanki ne" Cewar Anty fadeelah. Dariya nayi sannan nace.

"Anty fadeelah bazai girmeta ba kota girmeshi ko suzo sa'anni dan immediate nake binsa tsakaninmu babu wani rata sosai."

"Shekarunki nawa?" Suka haÉ—a baki wajan tambaya.

"19years zan cika this month nabasu amsa atakaice"

"eh tabbas bazai girmeta ba" cewar Anty fadeelah.

"Aysha ce tace. Amma ai akwai wani bayan shi ko? Ina nufin first born ɗin Mamanku" jin zancen nayi yayimin wani iri nayi Murmushi mai cikeda ciwo ban iya bata amsar tambayarta ba, ƙarancin shekaruna bai hanani jin zafi da raɗaɗin irin ahlin danake dashi ba, Mu kanmu bamu gama sanin junanmu ba. Cikin sanyayyar murya nace.

"Bansan wata irin rayuwa muke ciki a ahalinmu ba, ashe damu daku gabaki ɗayanmu rayuwa iri ɗaya mukeyi muna rayuwa batareda munsan junanmu ba, nikaina bansan ku nawa bane a cikin mahaifiyarku haka kuma baku saniba, wannan wace irin rayuwa ce? Koma wace irice bamai kyau bace. Gabaki ɗayanmu nasan bamajin daɗin yanda wannan al'amari yake kasancewa, idan munason gyara mu yakamata mu tashi mu gyara iyayenmu daban muma daban, Abunda yake tsakaninsu bai kamata ya shefemu ba, Habibu shine babban ɗan Mama ƴan uwan Mama ne suka biya masa karatu a ƙasar waje yagama yau zai dawo mu huɗune gabaki ɗaya a wajanta kukam nasan kunada yawa yaya Ahmad Kawai nasani saiku yanzu da kuka dawo cikin rayuwarmu, gabaki ɗaya sauran banace ban sansu ba bakuma zan iya tunasu ba saboda lokacin da tsawo" ƙarashe faɗin hakan ina miƙewa
Jikinsu gabaki É—aya yayi sany nima jiki a sanyaye nace.

"Bari naje Mama na jirana" nasaka kai nafice.

A É—aki nasamu Mama tabani kuÉ—in aikar harna juya zan fita sai kuma na juyo na kalleta nace.

"Mama mai yasa bakwa saka su anty fadeelah aiki?"
Ta É—auki lokaci tana kallona kamar bazatayi magana ba har ina shirin fita sai naji tace.

"Saboda tsoron abunda zaije yazo" n ajijjiga kai sannan nace.

"ku kawarda kanku kan abunda mutane zasuce komai zakuyi kuyi zuciyarku É—aya tsakani da Allah koma menene yaje yazo toh zaizo dasauki" gyaÉ—a kai tayi tace.

"Toh uwar Mata sarkin sanin yakamata jemin aika nikam ki dawo" najuya nifice ban daɗe a kasuwarba nadawo saboda aikar batada yawa. Ina dawowa nacire Hijabi nafito harabar kitchen ɗinmu nahau aiki Anty tazo tazauna tana tayani, Muna cikin aiki Mama tafito daga ɗakin Baba dan batama san da dawowata ba danaga batanan kawai sai nahau yin aikin tunda nasan ko tananan ma ni ce ƙarfin aikin.

Mama tana fitowa tace.

"Mamee jeki kira ƴan uwanki kuzo ku haɗu kuyi aikin" Abun yazomin a bazata tunda ban ɗauka mama taji maganata ba dan haka namiƙe na nufi kiransu Anty ta dubi Mama tace.

"Amma Mama dakin barsu kawai saboda abunda zaije yazo kinga iya zamansu basu taɓa tunanin tayamu aiki ba tunda aikin ba gagararmu zaiyiba kibarsu suyi zamansu ni wallh banason rikici" Mama ta nisa tace.

"Antynsu Lamarin gidannan yana buƙatar gyara zamanda mukeyi da zuba idanuwa bazai gyara lamarinba. Har indai kina tunanin makomar Ƴaƴanki ko bayan Babamu toh ki taimaka wajan sanya hannu a gyara wannan lamari, Abaya munyi kuskure matuƙa da bamu zuba ido munja gefe ba toda al'amarin bai taɓarɓare hakaba"

cikeda Biyyya Anty tace shikenaan in sha Allahu zan taimaka amma bana tunanin sanya hannuna zai gyara lamarin baƙya kallon har yanzu irin gaisuwarda take shiga tsakanina da yarannan? Ko kallon mutumci fa ban ishesu ba" Mama batakai ga tankawa ba muka fito daga ɗakinmu ganin fuskarsu ya nunawa Mama lallai sunji daɗin kiranda akayi musu. Muna ƙarasowa Mama tacewa anty.

"Tashi kibarsu suyi aikin su kaɗai tunda idan gidan miji sukaje babu mai tayasu, mu dukanmu muka saka dariya Anty tatashi mukaci gaba da aikinmu Har aka kira magrib Baba yafito Sallah ya taras damu muna aiki ba ƙaramin daɗi yajiba dan har fiskarsa tanuna farin cikinsa yakasa ɓoyuwa Har yace.

"Mamee" Bayan na amsa mai ya tuna saiya canja yace.

"fadeela a haɗamin baƙin shayi ki kawomin ɗaki idanna dawo sallar isha'i Mamee ta gwada miki irin haɗin da akemin" mu duka muka amsa haɗeda yimasa adawo lpy."

muka tashi Sallah Bayan mundawo mukaci gaba da aiki saida aka kira isha'i kafinnan muka tashi na nunawa anty fadeelah yanda zata haɗawa Baba shayin, yana shogowa tajuye takai masa tadawo mukaci gaba da aiki, adaren sai muka gama aikin tass, Rice and stew mukayi sai vegetable pepper chicken da kajin da Baba yasiyo ƙwara biyu da ƙananun snacks dama Mama tana kunun Ayah na sayarwa kuma yana tafiya sosai dan haka saida mukayi mata muka ɗureshi a gorina Asyha ta jera mata a fridge sauran aikin da mukayi ƙananun coolern da mama takawo mana muka ɗebawa Habibu da Baba nasu sauran muka na cikin gida, Mama tace tunda mu mukasha wahalar aikinmu toh muraba kayanmu, kintatawa mukayi muka raba.

Sai ƙarfe tara sannan Habibu ya iso Kowa yayi murnar ganinsa barinni dukda bawata jituwa bane a tsakaninmu.

Sai kusan sha É—aya muka shiga É—aki domin anzauna anata hira da Habibu hardasu Aysha da fadeelah duk da babu wani sabo tsakani,

Hasken da wayata takeyine ya tabbatarmin akwai saƙo akai na ɗauka shaff ni nama manta da saƙon ɗazu gashi har wani yasake shigowa. Sakon farko saƙone kamar haka.

(انت تملك قلبي)

Mtsww naja tsaki afili a zuciyata ina faɗin wannan mutumin yafiya iyaye da kinibibi, saƙo bazai taɓa yinsa da Hausa ba kullum larabci wasu lokutan ya sirka da turanci Ko yana ganin hakan zai burgenine oho masa. Saƙo na biyu kuma

العد التنازلي
hakan yana nufin (countdown )

العد التنازلي

Shine heading na rubutun
Sannan a ƙasansa kullum yana irge bansan irgen menene amma tabbas nasan akwai abunda yake nufi da wannan irgen Nidai na zuba idanuwan dan ganin yaushe wannan irgen zai ƙare.

Fita nayi daga wajan message ɗin na shiga phone na shigarda numbern Hamma danaji dazu Maryam tana faɗawa fadeelah ƙawarmu alokacin na riƙeta akaina. Harna danna calling nayi sauri nayi hanging, nasaka hannu naɗan bugu kaina bansan meyake damuna ba idanna kira ya ɗauka toh me zance masa? Ajiyar zuciya nayi nashiga nayi saving numbern da Hamma❤️ Harda ƴar heart agaba.
Zuciyata cikeda jin daÉ—in kasancewar numbern Hamma a wayata na kwanta bacci."

Washe gari ma haka muka tashi da aikin walimar sauƙata gabaki ɗaya gidan muka saka Hannu a aikin domin yayi mana sauri amma hakanma saida mukayi dare sosai muka gama muka saba a ledojin da drinks gabaki ɗaya komai yazama intact muna tashi washe gari sai dai muwuce wajan sauƙa da sassafe."

Aysha ce tayimi jan lalle a hannuna daƙafafuna dake dashi na kwana sai asuba nacire kafin gari yagama wayewa yayi maroon yayi matuƙar kyau sosai."

Ƙarfe tara muka wuce wajan sauƙa batareda ɓata lokaciba aka fara gudabarda abunda ya taramu, dake muryata nada sauti ninayi katatu a wajan sauƙan, maryam kuma tana cikin masu gudanarda baiti.

Anan aka fara kiran na ɗaya dana biyu har zuwa na biyar babu sunana kona maryam aciki, ƙunƙuni maryam takeyi inata dariya nace.

"ke babe kiji tsoron Allah wallh kidaina borin kunya kefa kanki kinsan bakida ƙoƙoarin da zaki fito cikin jerim mutane biyar kinga ni bansakawa kaina ba Alhamdulillhi tunda dai nasan na haddace kuma yana kaina in Sha Allahu kuma zanyi aiki dashi toh menene abun damuwa? Ke bakiga suma kansu malamn suna alfahari da karatunmu ba? Tunda dai aka sakamu acikin wabda zasu fitarda makaranta kunya ai Alhamdulillhi" Tsaki maryam taja nace.

"Nace sai kije kiyi tayi banza mai borin kunya" faɗa muka farayi a wajan mukayi baram-baram. Wayata tafara ruri na ɗagota na duba a yanda true caller da tunanin numbern babban wata company ne wanda suke deleveryn kaya ina ɗauka aka sanar dani inada saƙo ƙofar makaranta nafito na karɓa, ina miƙewa Maryama tace.

ina zuwa babe?" harna fara mata bayani saina tuno munyi faÉ—a dan haka na haÉ—e rai nace.

" ina ruwanki nayi hanyar fita."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab  m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance  zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️Ote
Comment
Follow
share

To be cintinued

Zaynab Alabura

*BIBIYATA YAKEYI*
_(WAYE SHI?)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

BY
ZAYNAB BAWA

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.