Bibiyata Yake Yi Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel.txt
Chapter 3 of 14
PAGE 4
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid 200
*ƘADDARAR RAYUWA*
Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?
Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073
   Sallama nayi a bakin dakin mahaifinmu ya amsamin Sallamata yana daga zaune a kan kujera jikina yafara rawa dakyar na sanya kafata nashiga palourn, idona yakai kan takardar dake gefensa tana ajiye, na dago kaina na kalli fuskarsa dan ganin yanayin da yake ciki murmushi ya sakarmin Hadeda fadin matso nan zo kusa ki zauna da sauri na karasa nazauna a kasa gefen kujerarda yake a zaune, nima nasaki murmushin dan yanayin fuskarsa ya tabbatarmin babu wata matsala amma ina tunani toh baisan da cewa result yafito ba,
"Mamee andawo daga makarantar?" Muryarsa ta katsemin tunanina "Eh Baba mundawo shine mama tace kana nemana sannu da hutawa"
Murmshi yayi mai sautin Dariya yaÉ—auko takardar yace.
"Mamee kinyi abun kai yanzu na aika yayanki yaje ya karbo result dinku gashinan acikin mutane dari biyar kece ta goma sha uku"
bansan lokacinda nadaka tsalle ina ihu ba Baba dariya kawai yakeyi na suri takardar nayi waje girgiza kai kawai yayi a gaskiya yayi murna sosai dacin wannan jarabawa da nayi dan tabbas yanaso tayi karatu dan tayi karama idan aure yace zaiyi mata,
Mama tana zaune a yanda nabarta na shiga ciki da gudu ina fadin na "haye mama na haye"
"Me kika haye?" Ban kulataba naci gaba da tsalle ina murna Mama tace.
"Ke banason Hauka ki tsaya ki fadamin me kika haya?"
"Jarabawar Weeding mana Mama ta nursing Baba yasa aka karbomin na haye, murna sosai Mama tayi tana fadin "kai Alhamdulillah amma naji dadi Allah yacigaba da baki nasara Arayuwarki" na amsa da,
"Amin" sannan nawuce izuwa dakin anty na nuna mata na juyo zuwa dakin Baba dan kai masa takardun dan duk wasu takardunmu shike ajiyewa,
 A yanda nabarshi anan na sameshi ya kunna Babban TV dake babban palourn nasa wanda yake ajiye akan TV stand na makalawa a bango ne amma dake yayi girma sai kawai aka ajiyeshi,
 Mika masa takardun nayi na zauna dake kwallo yake kallo nima nafara kallo, dama tun asali wajan mahaifina na koyi kallon kwallo domin bayida wata tasha dayake kallo irin sunna Tv daganan kuma sai tashar kwallo duk kwallonda za'ayi baya missing shiyasa gabaki daya gidanmu akayi mana searching tashar da take kama wasan ball kai tsaye, muna kallo muna yar Hirarmu dake kaff cikin yan wasan kwallo babu wanda bansansu ba, muna cikin kallo akaci team din da muke supporting cikeda bacin rai da takaici na bugi kujerarda take gefena, Baba yajiyo ya dubeni shima yaji babu dadi yace.
"Sorry kiyi hakuri zamu rama yanzu tunda Akwai Hammud Acikin yan wasan kwallon nan, Shekara nawa yanzu yakafa tarihin da ba'a taba kafawa ba a kwallon kafa izuwa yanzu duniya ta yarda cewa kaff yan wasan kwallon duniya Babu kamarsa" Baba yanamin hirar kamar wanda yakeyi da abokinsa shi kansa yaji dadin zama tayashi kallon wasan ball din danayi dan yanason yin kallo da wani gefensa koda kuwa ace bamai kallon kwallon bane bare ni da dama nice wacce na gado kallonsa ko mazan gidanmu Babu mai son wasan kwallon kafa kamar yanda nakeso. Baba baiyi shaidar Hammod a banza ba dan kuwa ya Rama cin kwallon da akayi musu, Baba yace.
"Kingani koh kingai koh" Mama ce tashigo dakin da Sallama mu duka muka amsata amma ni ban juyo na kalleta ba gabaki daya hankalina nakan ball din, mama tace "mamee tashi kije ana shirin kiran Sallah shima baban naku yanzu zai tafi masallaci"
Mikewa nayi zan fice sai da nakai bakin kofa Baba ya kirani "Mamee" na juyo nace "Na'am" ki dafamin Baƙin shayi idanna dawo a masallaci saiki kawomin toh na amsa sannan na fice . Ina fita mama tadubi Baba tace"
"Yarinyar nan yanzu tanaso tafika kallon ball abun har damuna yakeyi idan tafara kallo" murmushi Baba yayi yace .
"Ke baki fahimceta ba amma ni na fahimceta. tafara kallon ball ne kawai danta farantamin tun shekarun baya idan tazo taganni cikin damuwa saita canja tasha zuwa ta kwallo tunda tasan inaso dan kawai ta cireni a damuwa. Yarinyace karama amma tanada matukar wayo, duk wani abunda zai kawo farin ciki a cikin gidannan shi takeyi yanzu ki kalla taci jarabawarta dan kawai ta faranta mana inaji ajikina ta dalilinta kan gidannan zai dawo ya hade kamar yanda yake a shekarun baya. Kinga ta dalilinta yan uwanta guda biyu sun dawo gareni inaji wata rana zatayi abunda zaisa gabaki dayansu su dawo" mama ta kalleshi da rashin fahimta, Baba ya nisa sannan yace.
"Aysha da Fadeela sun dawo nanne saboda mahaifiyarsu tasamu labarin na sanya Mamee a makaranta shiyasa taturomin yaran acewarta suma na biya musu ita gani takeyi kamar ta kuntatamin saboda ta turamin yaran bazan iya daukar dawainiyarsu duka ba, amma abunda bata saniba shine naji dadin hakan matuka domin kuwa sun dawo gidan mahaifinsu kenan dawowa tahar Abada, kuma a yanda na lura sunajin dadin zama da mamee sosai Alkhairai dayawa idan zasu faru dani ta dalilin mamee ne inaji ajikina itace silar yayewar duk wata damuwarmu."Â Cikeda damuwa Mama tace.
"Toh amma yaya zaka iya daukaan dawainiyar karatunsu duka? Ko Mameen zata hakura fadeelah tunda itace Babba tafara a hankali sai musan yanda za'ayi"Â Girgiza kai yayi yace.
"Baza'ayi hakaba Mamee tayi kokari taci jarabawar ne danta faranta min nima ya zamenin kamar dole na faranta mata dole mamee zataci gaba da karatunnan ta farantamin nima zanyi mata haka kyautatawar da zanyi mata kenan"
"Amma tayaya? Tayaya zaka iya daukan nauyin karatun yara uku?" Karki damu Allah zai kawo mana hanya, shiru kawai tayi amma tausayinsa ya cikata tasan baida halin daukar nauyin karatun yaran gabaki dayansu, yanzu haka zaije ya takura kansa ne gashi ba cikekken lafiyane dashi ba, sai takeji inama ace Mamee tafadi wannan jarabawar dan tananne kadai zai samu sauki, kiran Sallar magrib da aka fara yine ya sanyashi mikewa yashige ciki yayi alwala yafito yawuce zuwa masallaci."
Ban tashi daurawa Baba ruwan shayinba saida aka kira isha'i saboda nasan idan yafita sallar magrib baya shigowa gida sai yayi Sallar isha'i bayan nagama najuye a flask ina jiran shigowarsa na mika masa ruwan shayin. Dauka nayi nakai masa bayan naji shigowarsa wannan ka'idane kullum sai Baba yasha ruwan shayi idan banice na dafa masa ba toh matansa ne zasu dafa sukai masa.
  Da wayar Mama nakira maryam na shaida mata cewa nima na haye jarabawar domin jiya tun tana tsokanata har itama kanta tadawo ta damu. Ganin yanda nashiga damuwa yasa itama tashiga damuwa amma dake nayi zuciya yasa harna taho ban kulata ba.
Maryam tayi murna sosai kamar yanda nayi ihu haka itama najiota cikin wayar tana ihu tana fadawa mahaifiyarta kashe wayar nayi dan kada mucinyewa mama kudin wayarsa. Mintuna kalilanta biyo da kira cikin sigar zolaye tace.
"Kai ashe dai babu rabon za'ayi miki aure da karancin shekaru" tsaki naja sannan nace.
"Kefa maryam baki iya samun abuba wallh shiyasa wata rana har banaso nabaki labari banza"
"Malama kina sake zagina zan kashe wayata" cikin halin ko inkula nace.
"Toh kashe mana dama ni nasaka ki kirani" mtsewww taja tsaki takashe wayar bin wayar nayi da kallo Afili na furta.
"Lallai maryam bakida mutumci" na ajiye wayar gefe ko mintuna biyu bata bada a tsakani ba tasake danna kiran ina kallon wayar yashigo kamar bazan amsaba sai kuma na amsa ina ciccin magani.
Mukaci gaba dayin wayar daga karshe dai muka sake yin fada kowa tayi fushi ta ajiye wayar.
Sabbin Uniform Baba yakara dinkamin saboda sati daya kawai suka bada zamu koma aji duk wani abunda za'a bukata kafin sati Baba ya tanadarmun dashi.
Sati yana cikawa muka fara daukan darasi a makaranta.
Baba ya aika Yaya Ahmad ya sayawa fadeela da Aysha form na polytechnic amma Aysha tace. Ita nursing takeso ko degree Baba yace. Sai dai tajira wata shekara. Hakan akayi danta gwammaci ta bata shekara guda ta yarda zata jira, dake lokacin ina cuku cukun biyan JAMB kawai sai Baba ya biya mata. idan lokaci yayi zata zana.
Ina zaune adaki ina duba littafaina Baba yaturo akirani babu bata lokaci natashi natafi shida Mama nasamesu a falonsa nashiga da Sallama su dukansu suka amsa, bayan nayi musu Sannu da hutawa na zauna gefen Baba,
Ganin ana buga kwallo ya sanya nasan dalilin kiranda Baba yayimin na zauna muka fara kalla Mama har gyangyadi tafara dan bata iya kallan kwallon. saida aka gama sannan Baba ya dauko wani abu a leda ya mika min dake ledar mai ruwan garau ce ina kallo na fahimci menene aciki amma na bude dan tabbatarwa,
Wayace sabuwa dall a fankonta android Baba ya siyamin, ihu nasaka saida mama tatashi daga gyangyadin da takeyi cikeda bacin rai take fadin.
"Yau nikam wannan shashanci ya isheni ke yaushe zakiyi hankali? Da zarar anci kwallo kin cikawa mutane gida da ihu kenan?"
"Mama kingani ba kwallo akaci ba Baba ne ya saimin waya" da mamaki mama ke kallon wayar Hannuna sannan tajuya tadubi Baba tace.
"A'ina kasamu kudi kasai mata waya Alhaji? Dan Allah saboda karatun yarinyarnan kada ka sanya kanka cikin damuwa da waya da babu waya zatayi karatunta" Murmusawa yayi sannan yace.
"Shekarun Baya kenan ai yanzu lokaci ya canja idan babu wayar bazata samu damar yin karatun ba"
"Amma!" Baba ya daga mata hannu sannan yace.
"Nasan zaki tambayi yanda nasamu kudi daya dga cikin gonakina nadauka na bada hayarta ta shekara biyar daganan harsu gama karatunsu zan sami kudinda zanna biya musu hankali kwance"
Jikina yayi sanyi matuka jin cewa saida ya jinginarda gonarsa kafin yasamu kudinda zai biya mana karatu. Toh wannan Bawan Allahn dame zamu saka masa?
Komawa nayi na zauna jiki a sanyaye nace.
"Baba Allah ya saka maka da dumbin alkhairai masu yawa Allah yabiya maka bukatunka yasaka maka da aljanna"
"Amin" ya amsa cikeda jin dadi. Mama dake tanason korata a wajan tace.
"Kinfasa zuwa karatun da kikace zakije ne?" Kai na girgiza mata dasauri nace.
"Banfasa ba"
"Toh naji baki tambayi Babannaku ba" Baba yace.
"Karatu Zataje ta?"
"Eh itada kawarta amma naji batayi maganarba"
"Shikenan tajeta Allah yabasu sa'a" na amsa da "Amin" sannan nafice. Ina shiga daki na É—auki wayar Mama na kira Maryam tace Zatzo ta daukeni. Minti talatin ta iso nayi musu sallma muka fice karatun 2hours kawai mukayi Maryam ta matsa sai mun wuce gidansu dake ban tambaya naki amma danaga tayi fushi tana faÉ—in.
"Tunda muke dake baki taɓa zuwa gidanmu ba amma ni naje gidanku sau babu iyaka Allah har indai yau bakije gidanmu ba toh bankara zuwa naku gidan"
"Duk mai yayi zafi haka? muje amma bazan daÉ—e ba tunda kinga ban fadawa Baba ba"
Murna sosai Maryam tayi dake dama driver yana jira kai tsaye muka wuce gidansu dake unguwar fadaman mada anan garin bauchi,
Gidansu ya haÉ—u sosai gidane Babba tsararre mai hawa biyu tun daga wajan gidanma abun kallo ne bare awuce zuwa ciki, a yanda maryam take mu'amala faram-faram da mutane baza'a taba dauka dukiyarsu har takai hakaba sai dai dama daga yanayinta zaka gane sunada hali.
Mai gadi ya bude mana gate muka shigr bayan minfito a motar kai tsaye É—akin mamansu muka fara shiga muka gaidata, tanada fara'a sosai cikeda Murna take faÉ—in.
"Yau wace rana Mamee tazo gidanmu kullum saijin labarin Mamee amma ban taɓa ganinta ba" dariya kawai nayi muka wuce ciki ta falonda muka ratsa zamu wuce muka riski wani Saurayi zaune yana danne-danne a laptop ta company apple dake gabansa,
batareda ya juyo ba Yace.
"Harkinyi karatun kenan?"
"Eh mungama shine muka taho gida"
Murmushi yayi mai sauti wanda yasanyani satan kallonsa iya gefen fuskarsa nake kallo amma hakan bai hanani gane kamanninsa ba, kyakkyawane sosai na karshe duk yanda nake kallon kyawun Maryam nasa ya zarce nan fatarsa har wani tarr tayi sai sheki takeyi kamar madara gashi yanda yake tafiyarda laptop na gabansa cikin tsari da nutsuwa gwanin ban sha'awa saukarda idona kasa nayi na tattaro nutsuwata da sanyayyar murya nace.
"Ina wuni" batareda ya dago ya kalleni ba ya amsa maryam taja hannuna mukabar wajan, É—akinta muka shiga shima da É—an karamin palour da saitin kujeru sai kuma uwar dakin da saitin gado kamar dakin amarya kayanda aka zuba mata adakin amaryarma idanba yar masu hali ba bazata samu kamarsa ba.
kwanciya nayi kan bed É—in ina maida numfashi maryam ta kalleni tana faÉ—in.
"Sannu" ita a tunaninta gajiya nayi yansa nake maida numfashin abunda bata saniba shine tunda nayi arba da Yayanta bugun zuciyata ta sauwa."
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
✔ï¸Ote
Comment
Follow
share
To be cintinued
Zaynab Alabura
*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023
*بسم الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…*
BY
  ZAYNAB BAWA
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.