Bibiyata Yake Yi Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel.txt
Chapter 13 of 14
PAGE 14
Ganin baida wata mafita yasa yaje ya samu mahaufiyarsa da maganar yasha faɗa sosai, ita cewama tayi yayi ƙarami a auren gabaki ɗayansa nawa yake da zaice zaiyi aure ko mahaifinsa baiyi aure dawuri hakaba sannan gashi abokin mahaifinsu ya rigada ya bashi ɗiyarsa itakam bada ita za'a watsa masa ƙasa a ido ba, shidai dayake baida kunya ya taro auren toh yaje da kansa ya samu abokin mahaifin nasa yayi masa bayani."
Rashin mafita da rashin samun goyon bayan mahaifiyarsa ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba yarasa ta ina zai kamo bakin zaren komai ya cukurkuɗe masa shi bai taɓa tunanin iyayenta zasu amince mata da aurensu ba shiyasa yabata dama kai tsaye akan taje ta samesu. Gannin baida wata mafita yasa yarufe idanuwansa ya tunkari abokin mahaifin nasa ga mamakinsa bai nuna wata damuwa ba ya gwada zai tsaya masa har ayi auren kuma bai janye ƙudirinsa na bashi auren ɗiyarsa ba yace masa bazaiyi alƙawari ya karya ba dan haka zancen bashi aurenta yananan daram. Sannan yace zai kira mahaifiyarsa ya shawo kanta. cikeda kunyarsa yayi masa godiya yatafi.
Yatafi yabarshi da al'ajabi iyayen mace zasuzo ganin iyayen namiji baisan yanda lamarin nasu yake acan ba amma sukama nan bahaka sukeyi ba."
Gabaki ɗaya mahaifanta suka taho tareda ita suka sauƙa a gidan daya saya mata.
Bayan sun iso ta kirashi ta sanar dashi shi washe gari abokin mahaifinsa yatada wasu daga cikin ƴan uwan babansu Muhammad sukaje can gidan dan nema masa aure. Sun tafi da goron tambayarsu da sadakinsu. Sunsha mamaki matuƙa ganin gidanda yaje yataro aure. amma ga mamakinsu an karɓesu Hannu bibbiyu akayi magana ta manya. Mahaifinta ya sanar dasu cewa zai yanke lokacin aure idanya yanke zai sanar dasu."
Muhammad yana gida sai taraddadin irin karɓanda za'ayiwa mahaifansa yakeyi amma bayan dawowarsu dayaji komai yatafi dai-dai sai hankalinsa ya kwanta.
Yana zaune wayar tafara ruri saida yasamu kansa da murmushi ya É—aga wayar tace.
"kaga nacika zancena koh? Yanzu maganar aure ba fashi dole sai anyi" ya taɓe baki jin yanda take maganar aure ba shauƙi babu alamunsa yace.
"Eh boss lady nagani kincika maganarki"
"Toh yanzu yaushe zan ganka Dady ma nason ganinka kafin yatafi kuma zuwa gobe zai koma" Saida yaja numfashi sannan yace.
"In sha Allah zanzo bayan magrib dan kema inaso muyi magana dake"
"Okay I'll be waiting for you sai kazo". Sukayi sallama. Bayan magrib ya shirya domin samu mahaifinta. dake dama mahaifin yasanda zuwansa yasa akayi masa tarɓa ta musamman, da mahaifinta yafara ganawa ya sameshi sukayi magana sosai ta fahimta sannan mahaifinta ya gamsu zai bashi aurenta ɗari bisa ɗari. Tun farko daya ganshi ya tabbata dole ƴarsa da kamu da soyayyarsa saboda kyawun da Allah yayi masa sai bayan ya zauna sunyi magana yagane nutsuwarsa da kyawawan kalamansa. Kowane laffuza zai furta yana tacesu ya tauna ya aunasu a mizani sannan yake furtasu mahaifiya ya yaba sosai da irin mjinda ƴarsa tasamo"
Bayan sungama da mahaifin yafita yabasu waje sannan ita tashigo. Kamar yanda suka saba mu'amalarsu haka sukayi babu wani canji dukda maganar aure tashiga tsakani haka take yimasa magana cikeda umarni da gadara shi atunaninsa zata canja idan bata canjaba yanzu yasan dole zata canja da zarar anyi auren daya tuna hakan saiya samu sanyi acikin zuciyarsa. ta kalleshi tace.
"yanzu me dame kake gani zaamu shirya a bikin?" maganarta ta dawo dashi daga duniyar tunaninsa ya nisa sannan yace.
"Bikinda ba yanzu za'ayishi ba mubari sai lokacin yayi sai mushirya abunda za'ayi"
"Nasan Dady bazai saka lokaci kai tsawo ba danmu familyn mu ba'a saka lokaci mai tsawo abiki"
"Eh toh mu namu famlyn ya bambamta gaskiya danmu ana sakawa da tsayi dan agama haɗa komai na al'ada, kuma kinga ƙarfinmu da naku ba ɗaya ba so mu dole mubi komai a hankali, yatsine baki tayi tace.
"Au nina É—auka anwuce wannan ai kana dani menene wata damuwarka da abunda za'a kashe hidimar biki? Zanji da komai" girgiza kai yayi yace.
"Nidai nafiso abi komai a hankali banaso kiyi hidimar abunda ya shefeni zanyi da kaina kuma tunda kinga abokin mahaifina zan auri Æ´arsa nan gaba shima bazan É—aura masa nauyi ba zanfiso nayi komai da kaina" canja fuska tayi ta É—aureta tamau tace.
"Banganeba? Har yanzu batun aurenka da yarinyarnan yana nan? NaÉ—auka anwuce wajan tunda yanzu zakayi aure" girgiza kai yayi yace.
"Bamu wuceba nafaɗa miki nayi alƙawarin aurenta kamar yanda mahaifinta yayi alƙawarin auramin ita banaji akwai wani abunda zai kunce wannan alƙawari kisakawa ranki ko ba daɗe ko bajima zan aureta wannan arubuce yake" Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba tace.
"nikuwa har yanzu ba'a haifi macenda zan haɗa miji da itaba dole ka zaɓa koni ko ita" yayi murmushi sannan yace.
"Dole ai Sallah ce kedai kije kiyi tunani kiji ko akwai macenda zaki iya haɗa miji da ita idan kin yanke shawara saiki sanar dani" fuuuu tabar wajan bata sake juyowa ba haka yajuya yatafi yanajin ransa babu daɗi shidai bazai ce yafasa aurenta ba kuma bazai fas alƙawarinsa ba idan taji zata iya ahaka ashirye yake daya aureta. Tana shiga cikeda takaici take sanarwa mahaifiyarta abunda yafaru. Mahaifyar tace.
"Toh ki haƙura da aurensa mana tunda bashine kaɗai namiji ba zaki samu wanda yafishi"
"Bazan iyaba tabata amsa kai tsaye" tace.
"toh ki yarda ki aureshi ahaka daga baya zamusan yanda zamuyi bazai tada zancen aurenba zamu sake masa kuÉ—i arufe bakinsa yanda zamu juyashi son ranmu" wannan shawara tayi haka suka yanke sannan tace kada su sanarda mahaifinta dan bazai yardaba."
Saida yayi ƙwana biyu bai nemetaba itama bata nemeshiba saida tagaji dan kanta taga baida niyyar kira ita takira. Yana picking tace.
"Kwana biyu meyasa baka nemeni ba?" baka janye akan maganarka bane?" Murmushi yayi sannan yace.
"NaÉ—auka zaki nemeni kamar yanda muka tsaya idan kin yanke shawara"
"Yanzu baka yanke ba kenan?" ta jefo masa tambaya.
"Uhum" kawai yace mata tace.
"toh shikenan naji na yarda ka aureta É—in" tayi magana kamar wanda idan baya yardaba ba auren zaiyi ba."
Bayan sati biyu mahaifinta ya saka lokacin biki wata mai zuwa aka fara shirye shiryen biki yanda suke kashe kuÉ—i kamar wanda basusan darajarsa ba ansaka lokacin bikin yayi kusa yanda shi da danginsa babu wani abunda suka tanada Kuma basusan yanda zasuyi ba shidai abokin mahaifinsa yayi nasa tunda ya biya masa sadaki yanzu sai dai ya taimakesu da abubuwanda baza'a rasaba. Sanin cewa baidashi ya sanya zainab ta sake masa kuÉ—i kamar bata sonsu sanin bashida yanda zaiyi ya sanya ya amshi kuÉ—in yana amfani dasu amma zuciyarsa a kullum tana jiye masa tsoron abunda zaije yazo dan yanaji wata rana dole akwai abunda zai biyo bayan wannan kashe masa kuÉ—inda takeyi. Dama duk namijinda zai sake jiki yaci kuÉ—in mace toh ya jirayi sakamako."
Lokacin biki yayi anyi hidima bana wasa ba mahaifinta ya nuna bajintarsa a auren É—iyarsa tilo wani gida daban yasiya yabasu wanda zasu zauna aciki. Duk wata hidima a wajan bikin shi ya É—auki nauyinta anyi biki komai angama lpy."
******
Mahaifinta ya biyawa Amarya da ango suka tafi honeymoon daganan sukace saudi suka dawo.
suna zaune agidansu lpy amma daga baya halayanta suka fara damunsa tunda sukayi aure koda sau ɗaya bata taɓa gaisheshi a matsayinsa na mijinta ba, gadara da iko kuwa yanzu ƙaruwa sukayi komai umarni take bashi gani takeyi kamar itace mai juya gidan dole kuma abita tunda gidan ma mahaifintane kuma dukiyar mahaifinta sukeci.
Suna zamane babu wata soyayya ko kyautatawa babu mu'amala kai kyau atsakani, batasan yanda ake kulada miji shi kansaba bare aje kulada gida sau ɗaya yayi mata complain dake shi dama bamai ƙorafi bane sai kawai gani anƙaro ƴan aiki. Mamakine ya kamashi sosai shin ƴan aiki zasu kula dashi kenan?"
Gashi ko fita zatayi ita bazata taɓa tambayarsa ba sai dai yadawo yaga batanan, sannan yanzu yagama school amma har yanzu bai samu aikiba itakuma ta wajanta babu alamin za'a sama masa aikin.
Da saninta ta hana mahaifi ta sama masa aiki saboda tana gani da zarar ya kafu da ƙafafunsa toh tabbas wata rana zaiyi maganar aure gara ta su zamana dimun da'iman duk wani abinda sukeso ana tanada musu shima kansa ta hutar dashi basai yasha wahalar aikiba sannan bazaisa wahalar nema wajan sana'a ba yana kwance ake tanada masa komai.
Daya gaji da irin wannan zamanda yakeyi sai kawai ya yanke shawarar nemawa kansa aiki haka yayitabi bai sami aikiba sai wata rana kawai school ɗinda yagama suka bashi appointment na lacturing a wajan yadawo gida da murnarsa ya shaida mata sam batayi murna da aikin daya samu ba. Kwanaki kaɗan da faruwar hakan akayi terminating appointment ɗinsa. Baisan daliliba haka ya haƙura daga baya yazo yagane cewa matarsa ce sila sai yabar zancen aiki yashiga neman sana'a ranarda tasan yana sana'a kuka ta sanyashi gaba tanayi tana faɗin dame ta rageshi bayan babu wani abunda ya nema yarasa yau abun kunyane ace anga mijinta wajan sana'a sirikin senate president, har mahaifinta saida yashiga maganar akan shima bai yardaba zai zubar masa da kima duk abunda yakeso ya sanar dashi zai bashi.
Wannan dalilin yasa ya zauna gabaki ɗaya ya daina taɓuka komai sai dai kawai akawo yakashe."
ana cikin haka kwatsam saiga ciki nan rikici yatashi tace itakam bata shirya haihuwa yanzu ba sai dai azubar da cikin. Rikici har gaban iyayenta wannan karon kam basu bata gaskiya ba dan haka dole tabar cikin amma anyi differing karatunta saboda tana laulayi sosai."
ZAYAB ALABURA
*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.