Best Hausa Novels

Bibiyata Yake Yi Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel.txt

Chapter 6 of 14

PAGE 7

   FREE PAGE SUN KUSA ƘAREWA KUSHIGO CIKI DAN AFAFATA DAKU."

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝

   ******

   Munata shirye shiryen walima dan haka yau ban fita school saura 2days walimar Sauƙanmu gidanmu da gidansu maryam gabaki ɗaya anata shirye-shirye, Baba ya bugamin Memo masu girma guda ɗari sunana da Maryam ne ajiki domin maryam yanzu tadawo ƴar gida agidanmu kamar yanda nima nadawo agidansu, Mama kuma key holder ta buga mana mai suna ajiki anty tayi mana sticker kowanne guda ɗari ne dan haka na rabasu a tsakiya na 50-50 kowanne natafi dan kaiwa maryam nata, Itama nasamu gidansu anata shirye-shiryen walimar, ganin motar Hamma a harabar gidan ya sanyani sakin murmushi dan nasan yana gida ta iya yiwuwa nayi arba dashi hakan kuma zai samamin sanyi acikin zuciyata.

  Part ɗin Umminsu Maryam nafara wucewa na sameta da wasu daga cikin ƴan uwanta suna shirin walima domin ita maryam za'ayi mata walima agida.

  Shiga nayi muka gaisa tacemin  maryam na ɗaki da ƙawayenta suna aiki, miƙewa nayi nashige ciki. A falonda Hamma yake zama natsaya naketa raba idanuwa na ko zan ganshi amma wayam ina tunanin jama'arda suke gidanne yasa bai zaunaba gabaki ɗaya sai naji babu daɗi nan da nan murmushin dake kan kumatuna ya sauƙa jiki a sanyaye nayi sallama na shiga falon maryam, tana jina ta saki ihu tana faɗin ƴar halak kinƙi ambato wallhy babe yanzu nake zancenki,

Raɓawa  ta cikin  ƙawayenta nayi bance komaiba na isa kujera ma zauna sannan na taɓe baki nace.

"Toh sai me? Ninace kiyi hira tane da zaki cikamin kunne daga shigowata?" harara ta wurgamin tace.

"keh wallh ba'a abun arziki dake"

"saina tsiya" na ƙarasa  maganarta.

Cousin sisters ɗintane a falon da wasu daga cikin ƙawayenmu wanda mukeyin nursing tare su biyu ga dukkan alamu sunzo tayata aikine dan dama tun daga lokacin da suka fuskamci babanta  hamshaƙin mai kuɗine suke shige mata.

  Souvenir ne agabansu dayawa ga dukkan alamu shiryasu sukeyi, Sannu da aiki kawai nayi musu na dubi maryam nace ga aikanki inji mama da Baba da Anty,

  Na miƙa mata ƙatuwar jakar danazo dashi karɓa tayi ta buɗesu taciro tafara  karanta ihu tasaka tana faɗin.

"Mufa ƴan gatane tako ina taɓe baki kawai nayi danni bana cikin yanayin  raha  duka abubuwan taciro tana dubawa tana sake faɗin kyawun da sukayi,

Miƙewa tayi tafice ta nunawa Ummi sannan tadawo tana faɗin idan zaki tafi tare zamuje naje nayiwa Su mama Godiya, bance mata komaiba na zame na ƙwanta na lumshe idanuwa na, zuciyata aai azalzalata takeyi ina muradin ganin Hamma ko zatayimin sauƙin abunda nakeji, Ganin haka ya sanya Maryam ta ɗauko ko wata matslarce dan haka tatashi saiji nayi ta riƙo hannuna na buɗe idanuwana tace.

"zo muje" miƙewa nayi nabita muka shige ɗaki baya saki hannuna na ba saida muka ƙarasa Har bakin gado muka zauna, Sannan tace.

"menene yake damunki babe? Kinyi wani iri badai akan Ɓoyeyyen masoyi kika shiga wannna damuwar ba?" kallonta nayi na wani lokaci yayinda a zuciyata nabata amsa da cewar Hammanta ne yake azalzalar zuciyata. Afili kuma banda wani zaɓi face ɓoye abunda yake cikin zuciyata nace.

  "waye kuwa zai sani cikin damuwa idanba shiba? Babe anya mutuminnan kuwa ba aljani bane?"

"Wani abunne kuma ya sake faruwa" ta tambaya na gyaÉ—a kaina sannan nace.

"kinsan mutuminnan har whatsapp ɗina yake bibiya" 

"kamar Yaya?" ta tambaya. Dalla-dalla Nayi mata bayanin abu da yafaru jiya tsakanina da Sageer na É—aura da faÉ—in.

"Allah ina ganin wannan mutumin aljanine idanba hakaba tayaya yasan cewa munyi chat dashi,

"Toh Babe menene abun damuwa anan?" naÉ—auka faruwar wannan abin zaisa ki fahimci cewa wannan mutumin masoyinkine na gaske bawai dawata manufa yake bibiyarki ba"

"toh amma WAYE SHI? idan abunda kika faɗa hakane yanzu yaci ace ya bayyana kansa" cikin sigar ƙwantarda hankali maryam take faɗin shikenan dai in sha Allahu zuwa agama hidimar wannan walimat zamusam wanene shi,

"Allah yayarda" kawai nace. Muka tashi mukayi palour, gabaki É—ayansu saida na lura da canji a fuskarsu sunso duk maganar da zamuyi muyita a gabansu.

    Ɗaya daga cikin friends namu fadeela wanda muke school tare takasa ɓoye cikinta saida tafito tayi magana, Amma cikin sigar wasa dama kuma wasu lokutan jealousy comes in jokes so ba kowacce dariya bace taketa soyayya, Cikin wasa tace.

"Wato gulmarce dake mu karen ware ne yasa baza'ayi a gabanmu ba. Toh Allah yabaku haƙuri" Ina ƙoƙarin zama nabata amsa da faɗin.

"Dama kin kwantarda hankalinki danmu babu gulmar da mukayi" Dariya tayi alamun itama taÉ—auki hakan a wasa.

Marairaice fuska tayi  dake dama ƴar azabar iyeyice ni haka kawai jinina bai haɗu da itaba gabaki ɗaya kalar tarbiyarmu ba ɗaya ba. Taddubi Maryam tace.

"Har yanzu Hamma bai fitoba, Wallh Maryam Hammanki ya haɗu sosai ajin ƙarshe, nifa danshi nake zuwa gidanku, Ko raina ke ɓace idan nayi arba da kyakkaywar fuskarsa sainaji ɓacin raina ya gushe,
Jin kalamanta ya sanya gabana yafara faɗuwa ji nakeyi kamar ta zubamin garwashi a ƙoƙon zuciyata, ɗaya daga cikin cousin ɗin maryam ta miƙe haɗeda jan tsaki tabi  Fadeelah sa harara  fuuu tafice aɗakin,

Fadeela ta dubi maryam wacce take kunshe dariyarta tace.

"Maryam kodai budurwarsa ce?" Dariyar da take ɓoyewa ce ta ƙwace tace.

"ni in nasanine? Aida kin tambayeta tun kafin tafita"

"uhmm ai alamu ma yanuna koba budurwarsa bace itama tana sonsa cewar fadeela" jijjiga kai Maryam tayi tace.

"Au kema sonsa É—in kikeyi kenan?"

"toh idanba sonsa ba me nakeyi Maryam?" ashe kallon sakara kikemin kenan tunda baki fahimci ina sonsa ba"

Kama haɓa maryam tayi tace.

"ni nikuma A'a gaki ga Hamma Allah yabaki sa'a har yanzu ba'a samu macenda ta isheshi kallo ba amma zaki iya gwada sa'arki"

Cikin muryar damuwa fadeelah tace.

"Dan Allah bani numbernsa" inaji maryam ta karanto mata haÉ—eda faÉ—in.

"karki cemasa nice nabaki" Jikina yayi matuƙar sanyi Jin maganar Maryam da fadeela sai nakeji kamar wanda zazzaɓi yakeso ya rufeni. Jiki a sanyaye na miƙe nayi musu sallama maryam tace na jirata tagama Mutafi tare ko takanta banbi ba banma fahimci abunda take nufi ba nafara tafiya, jiki a sanyaye. Harna shiga falon batareda na ankaraba, kamshin turarensa ne yadawo dani daga cikin Hayyacina dasauri nayi ƙoƙarin juyawa ko zan kalloshi Bumm naji na buge mutum nayi baya zan faɗi ya sanya hannuwansa ya tallafoni da sauri tsoron kada na faɗi yasa ya haɗa jikina da nasa A tsorace na ɗago da kaina shima niɗin yake kallo yayinda idanuwanmu ya sarƙe acikin na juna, wani irin abune naga yana yawo a cikin ƙwayar idanuwansa wanda nakasa fahimtar abunda yake yawo aciki, Tsawon  sanina dashi 2years bai taɓa kallona irin haka ba, Bazan iya juran kallon dayake yimin bah hakan yasa na yi ƙoƙarin Ƙwace jikina batareda wata gardama ba ya sakeni naja baya na sunkuyarda kaina ƙasa harya buɗe baki zaiyi magama amma yaanyin da zuciyarsa take bugawa da  sauri ya sanya ya fasa ya raɓa yawuce, Ajiyar zuciya na sauƙe nabi bayansa da kallo bansan lokacin da murmushi ya kuɓucemin yayinda zuciyata take wani irin bugu kamar zata faso ƙirjina ta fito waje.

  Jiki a saɓule na isa harabar gidan ina fita wayata ta buga alamun shigowar message, dake na sauya sautin shigowar saƙon wannan lambar ya sanya batareda na dubaba nasan wanda yaturo saƙon, danna canja sautin shigowar saƙonsa saboda kowanne saƙo yashigo saina samu kaina da faɗuwar gaba, jiki a saɓule na ciro wayata dan duba saƙon."

PAID BOOK

Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️Ote
Comment
Follow
share

To be cintinued

Zaynab Alabura

*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023

*بسم الله الرحمن الرحيم*

BY
ZAYNAB BAWA

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.