Best Hausa Novels

Bibiyata Yake Yi Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bibiyata Yake Yi Part Complete Hausa Novel.txt

Chapter 12 of 14

PAGE 13

      Zainab wanda ake yiwa laƙani da Hajiya zainab Ta kasance ƴar garin Abuja mahaifanta suna zaune acan. babanta ɗan siyasa ne. yana riƙe da babban muƙamin gomnati (Senate president) Yaran mahaifanta ukune kacal a duniya sauran biyun duka mazane itace ƙarama acikinsu daga can mahaifinta ya turota karatu Bauchi bayan  nuna sha'awarta nason karatu agarin Bauchi, duk wani jindaɗi na rayuwa ya tanada mata gida na musamman ya saya mata ya ajiye mata motocin da zata ringa zirga-zirga dasu, sannan ya zuba masu sanya masa idanuwa akan tarbiyarta dukda kasancewa tanada masifar jijji dakai ga girman kai yasan abune mawuyaci ta ɓata lokacin wajan kula samari dan ko samarin Abuja basa gabanta.

  Matsayinta da matsayin mahaifinta yasa takecin karanta babu babbaka ta taka wanda taso tayi abota da wanda taso kuma ta samu duk abunda taso hatta da ƙawayenta  yasa take wainasu yanda ranta yakeso
da takasu son ranta bbu wanda  zai iya fitowa yanuna mata ba dai-dai take yiba sudai tunda tana sake musu abunda suke buƙata (kuɗi) to koma menene tayi a wajansu dai-dai ne.

  Ana hakane ta ɗaura idanuwata Akan muhammad ta rikice da ganinsa amma ko ƙawayenta sai take nuna musu kamar abun bai dameta ba. Kullum zancensu ɗaya taje ta Sameshi har shawara suke bata akan ta sakar masa kuɗi nan da nan zai narke akanta amma ita tana gani kasawane a matsayinta tace tana sonsa kai tsaye sai dai tabiyo ta wata hanya daban."

Shine tayi amfani da hanyar karatu dan cimma muradinta akansa gashi nan dai toh muradinta zai cinmu? Kokuwa bazata kaiga cimma muradintaba?.

*****
      Miƙewa yayi yace.

"Toh mungama darasinnmu nayau zan iya tafiya idan anbani izini" dasauri itama ta miƙe tace.

"da naiman izini kakeyi a wajena daba miƙewa zaka fara yiba zaka fara tambayane idanna baka umarni saika tafi" murmushi yayi yace.

  "Toh agafarceni gaba  zan kiyaye amma yanzu inason na ɗauko yara a school" Tafiya tafarayi tace.

"muje"

"muje ina?" ya faÉ—a yana zaro ido.

"yanda zakaje taafaɗa sannan ta ƙarasa wajan motarta, tsayawa yayi baibitaba ganin baya tahowa ya sanya ya juyo tace.

"what are you waiting for muje mana" girgiza kai yayi yace.
   
   "ƙannena zanje ɗaukowa a school duk lokacinda banida abunyi ni nake ɗauko so bazai yiwu muje tare ba kiyi zamanki kawai na hutasar dake"

"Nima ƙannena ne dan haka kabarni muje tare" baisan dalilin dayasa bayson yimata musu ba kodan dama gabaki ɗaya shiba maison jayayya bane. Dan haka yabita ya ayanda takeso ɗin yana isa dai-dai yanda take ta miƙa masa key ɗin motar haɗeda faɗin.

"Drive" yana amsa  ta wuce seat ɗin mai zaman banza ta zauna tana jiransa ya shigo ya tayarda motar suka nufi makarantar yaran. Koda suka isa sun samu anrigada an tashesu dan haka yana ganinsu ya ƙarasa wajanda suke yayi parking suna kallonsa suka ƙaraso su huɗu Babbarce ta gaishesu ta juya dake dama ita tana ajin ƙarshe a secondary itaba lokaci ɗaya suke tashi ba amma duk aka tashesu saita fito dasu sukan ɗanyi jira na lokaci saboda idan bayida abunyi shi yake ɗaukansu ya wuce dasu gida idan taga ya jima baizoba saita tsara musu abun hawa saitaga tashinsu sannan takoma ciki, wacce tabita tana junior sai kuma ƙaramarsu tana ajin ƙarshe a primary, dake  matan suna gidan abokin mahaifinsu yasanya suka kasance su huɗu saboda ya haɗasu ya sakasu  makaranta da ɗiyarsa wacce itama ƙaramarce bazata wuce sa'ar wanda take primary ɗinba.

  Suka shiga yakaisu har zuwa ƙofar gida ya ajiyesu sannan yace bari ya kaita saiya hau abun hawa yadawo  ahanya  ta dubeshi tace.

"su dukansu ƙannenka ne?" ya girgiza mata kai taace.

  "bani labarinka toh bansan komai gameda kai ba" ya juya ya dubeta sannan ya maida hankalinsa ga tuƙinda yakeyi yafara magana.

  "Wannan ukun da kika gani sune ƙannena ɗayar yarinyar ƴar abokin mahaifinane kuma itace yarinyarda zan aura" saida gabanta ya faɗi ta dubeshi tace.

"Amma dai wasa kake koh? Wannan ƙaramar yarinyar?" tayi maganar tana duban fuskarsa taga babu alamun wasa sai tashiga taytayinta amma abun ya dameta cikin ranta kamar zatayi haƙuri sai kuma taji bazata iyaba tace.

  "Yanzu kai soyyaya kakeyi da wannan yarinya ƙarama ko wasa kakemin?" girgiza kansa yayi yace.

"eh toh.  farko da wasandai yafara amma yanzu yawuce wasa yarinyar abokin mahaifinane kamar yanda na faɗa miki. bayan rasa mahaifinmu shine ya ɗauki ƙannena nikuma ina tare da mahaifiyata toh dafarko ina yiwa yarinyar wasa har mahaifinta yashiga maganar da cewar ko bayan ransa batada mijin  saini mutumne mai karamci matuƙa"  Jin wannan maganar  yasa gabaki ɗaya tarasa abunda yake mata daɗi cikeda ɓacin randa yakasa ɓoyuwa tace.

  "Yanzu kana nufin kana sonta kenan?"

"Eh inasonta yanzu nake ƙara fahimtar hakan Amma ai kamar yanda kika gani tayi ƙarama so yanzu babu batun soyyaya harsai ta girma"   daganan bata ƙara cewa komaiba dan ranta gabaki ɗaya yayi mata babu daɗi shirune yabiyo bayan tattaunawarsu. Yabi ƙwatancen datayi masa yakaita har ƙofar gida. Itakam batamasan sun isoba saboda yanayinda take cike.

"Mun iso" yaceda ita bata jishi ba yace.

"Madam mun iso ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta dubeshi kamar zatayi magana saita fasa yace.

"Akwai wani abunne?"  harda buɗe baki zatayi magana saita tuno wacece ita bazai yiwu da buɗewa namiji abinda yake cikinta ba saita sauya zancen da faɗin amma akwai tazarar shekaru a tsakaninku, bambancin yayi yawa. Cikeda rashin damuwa yace.

"Atamu al'adar aiba komai bane hakan am just 23 itakuma yanzu take 11yrs bambamcin 12years ne which is normal ana yawan samun hakan" jiki a sanyaye takama handle ɗin ƙofar zata fita yayi saurin dakatarda ita da faɗin.

  "Dakata madam nine zanfita ko kin mantane?"

"Idan kafita ame zakaje gida toh kaje da ita inada wacce zanhau gobe"  Ya buɗe motar sannan yace.

Da ame nake zuwa gida karki damu  ina taran achaɓa yanzu zai kaini gida yana faɗin haka ya fice.

  Aranar  zaynab Batayi bacci ba maganarda sukayi ta tsaya mata arai, ashe ita tanata holoƙon banzane atunaninta tana gini ashe ginin nata ƙwata-ƙwata baiyiba bare aje matsayin  rushe shi. Amma dukda hakan yanda takeji da kanta dakuma gadarar ita wacece bazai taɓa yiwuwa tafito ta bayyana masa abunda yake ranta ba, har yanzu tana bakarta nacewa dole sai dakansa yafara bayyana mata abunda yake ransa a yanzu dai ta janye maganarta tabaya datace saita garashi kafin ta amsa izuwa yanzu yana zuwa mata da batun soyayya zata amshe.

******

Shaƙuwa mai mugun ƙarfi tashiga tsakaninsu A yanzu koda yaushe ga ganshi tofa tare zaka gansu da ita mutane har suna faɗin soyayya sukeyi amma banda anasu wajan dan sunsan ko kalmar so bata taɓa shiga tsakaninsu ba. Ana haka lokacin gama makarantarsu Muhammad yayi anata shirye shiryen gamawa amma babu wani alamun zai gwada mata yana sonta.

     yana zaune cikin abokanansa wayarsa tafara ruri dake ita tabashi wayar kuma lambarta kaɗai aciki yasanya yanaji yasan itake kiransa.  Saida yafita acikinsu sannan ya amsa Cikeda bada Umarni tace.

"Kazo gida ka Sameni"  shiru yayi bai bata amsaba saida ta ɗaga wayar taga ko ta katse ne ganin bata katsena ya sanya ta maida wayar kunnenta tace.

"kan jina?"

"ina jinki amma bazan iya zuwa gidanda kike ke kaÉ—ai ba ki fito saimu haÉ—u ko a school dan yanzu haka ina school É—inne, kabani 30minute tafaÉ—a sannan ta katse wayar.

"Saida ta É—auki 1hour kafin ta iso" tazo har yanda yake ta sameshi, sukaje can wani waje suka zauna sannan ya kalleta yace.

"wani abunne yafaru? Naga kin buƙaci nazo gida na sameki"

  "magana nakeso muyi dakai" 
"uhum ina jinki"

"Ka kalleni dakyau inaso zanyi maka wata tambaya ce" Ya kalleta yace

" na kalla"

"Banida kyau ne" ta tambaya.

Ganin alamunta babu wasa yasa shima bai É—auki lamarinda wasa ba yace.

" kina dashi wani abunne?"  Ta ɓata rai sosai sannan tafara faɗin.

"inada kyau. Inada kuÉ—i. Inada ilimi. Kuma inada wayewa dan meyasa har yanzu bakace kana sona ba?" tafaÉ—a cikeda tuhuma. shima ya haÉ—e rai yace.

"ke me yahanaki cewa kina sona?"

"Saboda zai taɓamin jin kimata" tabashi amsa taɓe baki yayi yace.

  " shikenan so bai kai soba har indai akwai maganar jinkai aciki" Shiru tayi tarasa yanda zatayi tace.

  "zan iya sauƙarda jiji dakaina da komai nace maka ina sonka amma inaso kasani dole akwai sakamakon da zai biyo bayan kalmar soyayyata. Ko kaƙi ko kaso har indai kabari na furta maka kalmar so to saika aureni wannan shine sakamakon kalmar Dan soyayyata bazata taɓa tafiya a banza ba kota ƙarfin iko saina saka ka aureni dan haka ka zauna kayi tunani kafin kabari kalnar so tafito abakina dan idanta rigada tafito babu jaa dabaya" Murmushi yayi yana mamakin kalamanta komai saita nuna ita mai iko ce komai saita sako gadara da isa da jijji dakai aciki.

  "Banajin akwai zancen aure tsakanina dake tunda ko ba'a faɗa mikiba kinsan kinwuce sa'ar aurena ko mahaifanki baanji zasu bari na aureki"

"Mahaifana kakeji?" shikenan kabani kwana biyi kaga abinda zan iya. Cikeda rashin damuwa yace.

"Nabaki.

  "Gobe zantafi Abuja idan na isa zan nemeka"

"Allah yakaimu ya kaiki lafiya kawai ya faÉ—a" dan yasan idanta tafi ba lallai bane iyayenta su barta tadawo idan sukaji zancenda taje musu dashi."

  Washe gari sassafe tashirya tawuce Abuja."

  Muhammad baisan abunda yake faruwa ba acikin ƙwana biyunnan saita  tasan yanda tayi ta shawo kan mahaifanta dukda bawani wahala tasha wajan jawo ra'ayinsu ba dan mahaifinta yana ganin har indai mutum yacika qualities ɗinda yakeso so beside dukiya ko komai mai sauƙine yanada arziki wanda yana tunanin har zuriarsa ta ƙare bazasuyi talauci so toh menene amfanin dukiyarsa idan bai bawa yarsa da mijinta ba?"

  Yayi na'am da zancenda takawo masa dan haka ya yanke idan zata koma zai bita sutafi tare dan yaje ya gana da iyayen yaron.

Takirashi ta shaida masa abun yazo masa a bazata dan haka yashiga matuƙar tashin hankali tayaya zai iya tunkarar mutumin daya zama musu uba alokacinda suke tsakanin buƙatar uba kuma yayi musu alƙawarin aurar masa da ƴarsa da zancen auren wata daban? Yasan ko mahaifiyarsa bazatayi na'am da zancen ba."

ZAYNAB ALABURA

*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*

Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.