Bakar Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: BAKAR INUWA BILLY.txt
Chapter 65 of 74
*_Episode 69-70_*
............Washe gari Raudha ta tashi batajin daÉ—i sosai. Dan har saida Dr Hauwa ta shigo ta dubata har dasu karin ruwa. Sai hankalin Ramadhan ya rabu biyu ga meeting da za'a zauna duk da dai babu Raudha a ciki. Ga jikinta kuma.
   Itako Gimbiya Su'adah tana can sun fice a sace ita da Safina zuwa gidan Addah Asmah, dan tana son tasan mike faruwa kafin a zauna zaman meeting duk da tasan har dasu Adda Asmah ɗin za'ayi. Lokacin da motar su gimbiya Su'adah ke shiga layin su Adda Asmah a lokacine driver daya ɗakko fulani zai kai Taura House shi kuma ke fita. Dan Addah Asmah tace fulanin tayi gaba suma zasu ƙaraso ita da mijinta da Aynah da kuma mijin Ayana ɗin da suke so ya saketa take a yau.
   Saboda yanayin hayaniyar mutane yasa Safina bata tsaya da motar ko'ina ba sai ƙofar falon baya data san su Adda Asmah nada ita. Dan kafin tai aure idan tana son haɗuwa da Faisal mijinta tasha satar fita ta wajen taje ta dawo wani bai sani ba. Ta wajen babu kowa, sai daga ɗan bayansu ta backyard suke jiyo ƙananun hayaniyar masu wanke-wanke. Ginbiya Su'adah takai hannu zata buɗe ƙofar wani furici mai kama da saukar aradu yay azamar taka mata birki, tai kuma saurin damƙe hanun Safina dake shirin yin magana tana girgiza mata kai....
   Su gimbiya Su'adah sun iso gidanne a dai-dai lokacin da Adda Asmah da Aynah ke tare a wannan falo, waya Adda Asmah keyi da bokanta akan abinda zasuyi idan anje wajen taro. Shine furucin ƙarshe data maimaita kamar yanda bokan ya faɗa ya shiga kunnen gimbiya Su'adah. Kasancewar sun gama wayar Adda Asmah ta ajiye a sanyaye tana duban Aynah data kafa mata ido.
   “Mom wai yanaga jikinki kamar yayi sanyi?â€.
       “Tabbas dole jikina yay sanyi Aina'u. Sai dai zan iya aikata komai saboda ke. Kamar yanda malam yace na kirashi kafin muwuce wajen taron shine na kirashi, dan wannan dalilinne ma yasa nace Ammy (fulani) tai gaba zamu biyota. Yanzu har ita ta bar sanin sirrinmu tunda bazatace batason Su'adah kamar yanda take sona ba.....â€
    “Hakane Mom, amma nidai sanar dani mike faruwa kawai?â€.
  “DaÉ—ina dake wutar ciki. Abinda kikaga ya girgizani da maganar malam ya tabbatarmin bincikensa na jiya ya nuna masa zasuyi taurin kai akan yarda da buÆ™atar mu, amma idan muka jajirce za'a iya samun nasa Æ™ila. Sai dai Ramadhan É—in shine babbar matsala yanzu, saboda akwai yarinyar dake tsaye a kansa game da addu'a hatta azkar baya wasa yanzu safe da yamma, yace inhar tana tare da shi mawuyacine duk wani aiki namu yanzu yay tasiri a kansa dan tanada jajircewa. Hasashena ya bani tabbas shegiyar yarinyarnan ce Æ´ar karuwai. Maganarsa ta Æ™arshe data firgitani itace zaÉ“in daya bamu akan Ramadhan É—in, kodai akawar da shi kowa ya rasa shi da yarinyar, kokuma mu haÆ™ur......â€
    “Ina bazai yuwuba Mom, wlhy bazan iya haÆ™ura da Ramadhan ba. Idan nai haka ko to tabbaci ban cika mace ba. Har yaushe zuciyarki ta fara tausayine Mom?.â€
   “Nima ba tausayi nake jiba Aynah, domin zan iya komai a kanki, ciki kuwa harda kauda duk wanda ya tare min gaba. Tunda muka taso a gidanmu kowa yafi son Su'adah duk da kasantuwarta yarinya mai girman kai da É—aukar kowa ba komai ba. Ba Æ™yau tafini ba, amma ko kaya mukasa kafin a yabamin an yaba nata saboda ta iya tsara ado. Kullum a makaranta takan É—auki maki na jarabawa fiye da nawa. A gida mahaifinmu yafi sonta fiye da kowane É—a, dan hatta da shawararsa mai muhimmanci yakanyi da Su'adah baiyi da su Ammy ba. Mu duka Æ´aÆ´an sarki ne amma ita kaÉ—ai ake kira da gimbiya duk da nice babba. A koda yaushe wannan abu nacimun rai, taya zan fita komai amma yazam kullum itace da nasara sama da tawa? Hatta a shekarufa na fita. Abinda ya Æ™ara baÆ™anta raina da rayuwa lokacin da muke UK a school, tunda na fara ganin Basheer Hameed Taura na kamu da sonsa. Amma abin mamaki saina tsincesa tare da Æ´ar uwata Su'adah har sun fara soyayya ni ina nan ina Æ™ulla yanda zan tunkaresa da tawa soyayyar. Na shiga tashin hankali mara misali Aynah, har takai naji bazan iya jurewaba na tunkaresa da batun. Hummm karkiga irin korar kare da Basheer yamin tare da dogon gargaÉ—i, tun daga nan karatuna ya shiga hanyar taÉ“arÉ“arewa har muka dawo gida babu komai a result É—ina. Itako ta dawo da sakamako mai Æ™yau cike da nasarori. Muna dawowa babu É“ata lokaci aka fara shirin aurar damu, ita aka aura mata wanda take so ni aka auramin mahaifinki batare da ina sonsa ba, dan iyayenmu ne suka Æ™ulla hakan. Watan Su'adah goma cif a Taura House ta haife É—anta namiji santalele. Niko a lokacin ko É“atan wata. Naji zafin hakan matuÆ™a amma naita Æ™oÆ™arin dannewa. Bayan shekara biyu da yayensa ta sake Mardiyya, har lokacin ni babu labari. Nadai taÆ™aice miki sai a harhuwar Lubnah muka haihu tare, lokacin tanada yara har uku kenan niko 1 kuma mace ke. Na Æ™ara na biyu ma mace. Wannan ya Æ™aramin tsanarta dan koba komai ta É—arani da namiji kuma Æ´aÆ´anta sunfi nawa. DaÉ—in daÉ—awa É—anta shine É—a tilo namiji agaba É—aya Taura family. Nasha auna cutar da Ramadhan amma bai yuwuba saboda kakankinsa kullum nane suke da shi kamar sun san burina. Iyayi nayi Su'adah ta amshi Ramadhan a hanunsu amma sun hanata. Dan haka nasa akai aiki akansa aka tura masa wasu hatsabiban ajanu dakan maidashi tamkar wani mahaukaci. Sai dai mahaukacin ma naso ya koma baki É—aya hakan bai kasance ba. Tun lokacin aurensa na farko naso ki auresa amma ya nuna baya ra'ayi, dan a yanzu babban burina shine ki auri Ramadhan ki Æ™wato mana duk wani abinda Su'adah kejin tanada shi a hannu daya fini, amma kuma sai komai ya lalace bayan mun É—akko hanyar nasara......â€
    “To amma Mom duk da waÉ—an nan abubuwan shine kike tunanin bazamuyi abinda malam yace ba. Ramadhan nada taurin kai, na tabbatar da wahala ya yarda da aurena, sai dai in uwarsa ce tace zata tsine masa. Idan ma tace hakan shi wannan jakin da aka auramin zai sakeni ne ta cikin sauÆ™i.....â€
    “Inko har duk abinda kika lissafo haka al'amarin zai zama to tabbas dolene Ramadhan ya mutu. Dan kawar da shine kawai zai sakama zuciyata salama akan Su'adah. Tunda bazamu samesaba to kowa ya rasa shikenan Æ™urun-Æ™us!!....…â€
   Wani irin banko ƙofar da akai ne ya dakatar da Aynah data fara dariya, atake sukai diri-diri, gimbiya Su'adah da kanta ke wani irin juyawa tanajin hajijiya ta shiga nuna adda Asmah da hannu sai dai abinda take son faɗa ya gagara fita. Safina datai wani tsalle ta shaƙo wuyan Adda Asmah ta buga da bango, hakanne yasa itama Ayna yin kukan kura a kanta ta shaƙeta. Ƴan biki ne suka fara shigowa a guje saboda ihun da Addah Asmah ta buga na azaba, har goshinta ya fashe jini na zuba......
*_TAURA HOUSE_*
    Kowa ya hallara su kaɗai ake jira, mai-martaba da ransa ya gama ɓaci yana ƙoƙarin cewa a kirasu sai ga kiran daddyn Aynah ya shigo masa. Cikin tashin hankali ya shiga ambaton kalmar innalillahi.... Har ƙarshe, kafin ya ajiye wayar ya sanarma ƴan falon da duk hankalinsu ke kansa iya abinda Daddyn Aynah ya sanar masa. Zaram Ramadhan ya miƙe amma sai Bappi ya dakatar da shi.
   “Ina zaka kuma?â€.
 “Bappi can gidan mana, kanajifa faÉ—a mizai haÉ—a Maah da Mom faÉ—a a duniyar nan?â€.
   “Koma miye ai zamu sani yanzu, ko kana mantawa da matsayinka a yanzune wai. Koma ka zauna Basheer yaje ya taho da suâ€.
  Babu yanda ya iya ya koma ya zauna kamar zaiyi kuka. Zuciyarsa sai kaikawo take da tunanin mike faruwa? Miya faruwa? Mi akayi?. Hakama sauran kowa tunaninsa kenan sai dai babu mai bada gamsashiyyar amsa akai zaman jiran isowarsu.
     ★Kusan awa guda suna zaman jira dan sai da Pa yay jan ido suka yadda suka taho dalilin ita gimbiya Su'adah na tsoron nata mijin, itako Adda Asmah ta raina nata. Wujiga-wijiga suka shigo musamman gimbiya Su'adah da sai da Safina ta bata taimakon gaggawa acan amma da yanzu labarin ba wannan ake ba kuma. Kowa hankalinsa ya tashi da yanayin nasu, musamman ma Ramadhan da cikin rawar jiki yaje ya taya Safina riƙo Maah dake tafiya kamar zata zube ƙasa sai hakki take sama-sama. Shidai Bappi uffan baiceba, binsu kawai yake da kallo hakama mai-martaba. Pa kuwa yanayinsa na nuna ko'a jikinsa dan dama irin wannan ranar yake addu'ar tazo duk da bai san mike faruwa ba shima har yanzun.
   “Inaga muyi abinda ya taramu kamar zaifiâ€.
  Cewar Pa da alamun ɗaci a muryarsa. Bappi zaiyi magana Mai-martaba ya katsesa.
   “Gaskiya Basheer ya faÉ—a dan nima sonake na wuce akan lokaciâ€.
   Bappi ya haɗiye abinda yay niyyar faɗa kawai yana girgiza kansa. Daga haka aka buɗe taro da addu'a sannan aka fara abinda ya tara ɗin game da sauya maganar auren Ramadhan da Aynah.
    Bayan dawowar Ramadhan hayyacinsa, adare ranar Bappi ya sanar masa duk abinda ake ciki, amma sai ya dage akan shi bai taɓa jin son wata Ayna'u ba. Bakuma zai fara a yanzu ba bayan so na ƴan uwantaka dake tsakaninsu. Ya kuma tabbatar masa komi za'ai shi bazai aureta ba matarsa ta ishesa. Babu irin lallashin da Bappi bai masaba a wannan dare amma yace shifa yana akan bakansa.
  Washe gari ma daya dawo gidan kafin yaje ga Raudha maganar da suka fara tattaunawa da Pa da Bappi da Anne harma da su Yafendo da Mai-martaba a waya kenan amma Ramadhan yace yana kan bakansa. Baice zai auri Ayna'u ba kuma ayanzu bazai amsa ba. Dagiyarsa ya sake tabbatar musu akwai sihiri tattare da shi sanda ya dinga musu hauka akan auren Ayna'u garda ɓatawa da su Anne. Wannan dalilin ya sakasu sallamarsa suka tattauna abinda ya dace a tsakaninsu. Mahaifin Aynah shine ya kawo shawarar a rufe komai iya su ranar ɗaurin aure yanada wanda zai aurama Aynah dan a raba gardama komai ya zama ƙarshe basai anta jan zancen ba. Wannan shawara tama kowa, dan haka suka rufe komai hatta Ramadhan baisan da haka ba sai da aka ɗaura aure da wani daban ba shi ɗin ba.
    “ALLAH na gode maka da hakanma ta kasance, Ramadhan ka yafemin, duk halin daka shiga akan Ayna'u hardani a ciki, daban basu goyon bayaba da ba'a nema sabautamin rayuwarka har gashi yau ana iÆ™irarin kashemin kai ba...â€
   Gimbiya Su'adah ta faÉ—a cikin kuka hanunta riÆ™e dana Ramadhan. Tsitt falon yay cikin rashin fahimtar kalaman nata..........âœ
  Â
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app É—in dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹ðŸ»â€â™€ï¸â›¹ðŸ»â€â™€ï¸ðŸ˜˜_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*â¤â€ðŸ”¥
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇ðŸ¼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuÉ—in littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇ðŸ¼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇ðŸ¼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇ðŸ»_*
Da É—umi-É—uminsa💃ðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following É—ina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰ðŸ¤ðŸ»ðŸ‘‡ðŸ»_
*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email É—inki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taÉ“a *Sign Up* shikenan an buÉ—e account a ArewaBooks💃ðŸ»ðŸ˜‚.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions É—in nanðŸ˜ðŸ˜˜ðŸ˜ðŸ¥°ðŸ˜ðŸ˜Š_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™ðŸ»_*_________________
*_Typing📲_*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.