Bakar Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: BAKAR INUWA BILLY.txt
Chapter 21 of 74
*_Episode 20_*
.............★A ɓangaren gimbiya su'adah da fulani da Asmah suna akan bakansu na ganin sun hana auren Ramadhan da Raudha suma. Sai dai kuma hayaniyar campaign ta sakasu ajiye wannan batun gefe. Kowa fatansa a yanzu Ramadhan ya haye mulki kawai, daga nan koma miye zai biyo baya sai ayi. Dan sun ɗau alwashin yaronsu bazai auri ɗiyar talakawa ba. Zuwa yanzu sunyi bincike mai tsanani akan Raudha har Hutawa, shiyyasa suke tunanin karya lagon su Bappi da wannan sirrin a haukarsu.
★★★
    Raudha kam tun kwanaki biyu da kai kuɗin aurenta aunty Hannah da First lady suka yanke shawarar ɗauketa anan gidan, tare da kafama hajiyar birni hujja da kar Asabe ta zugeta, aiko tai azamar amincewa dan ita kanta lamarin Asaben tsoro yake bata duk da tasanta da kafiyar tsiya tunba yanzu ba. Tunda itama haka tayi ga masu kuɗi na sonta a wancan lokacin amma ta dage sai M. Dauda, itako a yanzu bazata yarda Asaben tai mata baƙin cikin samun abubuwa da damaba a dalilin auren Raudhan. Sun maidata wani gida keɓantacce wai ana koya mata dabarun mulki irin na first lady. Bawai suna mata hakan danta ƙaru ba, sunayine kawai danta saki jiki dasu har idan buƙatar sakata musu aiki ya taso anan gaba tayi babu musu.
    Kasancewar an haÉ—ota dasu Yasmin kuma harda aunty Hannah duk da bata cika zama ba saboda yawon campaign sai hankalinta bai tashiba sosai, ga wata dattijuwa da sukace tana aikine a fadar shugaban Æ™asar shekaru goma kenan cir na mulkinsa mama tambaya, sai Æ™arin mutane biyu Æ´an gayu sukuma masu koya mata abubun daya shafi gyaran jiki da dai sauransu. Sai shahararriyar mai kayan gyaran jikin nan dake gyare Raudha É—in lungu da saÆ™o da ingatattun kayanta kayan Æ™amshi dana sanyi *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* _(guys ku garzaya dan zaku samu duk abinda kuke buÆ™ata ga amaryar kb, daga kayan Æ™amshin jiki, gida, kayan mata, maganin sanyi ingantacce😋😘ðŸ˜ðŸ¤—)_
     Kuma akwai wata islamiyya dake anan kusa da gidan saboda matsawarta yasa suka sakata ita dasu Yasmin. Sai dai bata fita sai da dogon hijjabin Uniform ɗin makarantar harda niƙaf. Ba'a dabarun mulki kawai aka tsayaba har gyaran jiki dasu saka kaya, girki duk koya mata akeyi, dan ma Alhmdllhi dama ta iya abubuwa da yawa na aikin cikin gida sai dai bana ƴan gayu irin haka ba, ba kuma sosai take girki ba a gida saboda icce suke amfani da shi ita kuma Asthma.
    A gefe kuma damuwar auren nata na nan daram a ranta. Musamman yawan ganin Ramadhan da takeyi a tv saboda campaign yanzun. Hakama idan ta fita islamiyya duk da anguwace ta manya tana ganin posters nashi. Ita kanta tasan ƙyaƙyƙyawane, yanayinsa da kwarjininsa dole ya shiga ran mai kallonsa da hanzari, sai dai ko kaɗan batajin sonsa a ranta, kamar yanda tasan itama bazai taɓa ya sota ba. ita da kanta kuma tana tilastama kanta saka ƙinsa a ranta saboda wasu dalilai
    ★Al'amarin campaign ya miƙa, kowa yana hangen nasara tattare da Ramadhan duk da masu iya magana kance siyasa kamar mace mai ciki ce, ba'a san mi zata haifa ba. Abubuwa da yawa masu daɗi da marasa daɗi sun faru a wajen campaign ɗin nan, wasu sun wuce an manta, wasu ko bazasu gogu a zuciyaba sai bayan mutuwa.
   Da gaske Ramadhan ya manta da batun wata Raudha saboda hargitsin campaign, sai idan wani ya ambaci sunanta ko zancen auren nasa ya fita a bakin wani yake tuna wata sa rana dake kansa ta aure. Sai dai ga Bappi da Pa da Anne ba haka bane, dan sunata shirye-shiryensu na biki duk da hatsaniyar campaign ɗin da kowa ke a ciki. Ga gimbiya Su'adah kuwa tunda ta gama binciki tushen Raudha hankalinta ya sake tashi ta birkicema Pa. Ko kulata baiyiba balle ta samu amsa. Hakan ya kuma ɓata ranta ita da su Fulani, batare da sanin kowaba suka shiga ƙulle-ƙullen yanda zasu ɓadda Raudha, sai dai sunbi duk wata hanya data dace amma basu sameta ba saboda ɓoyeta da akayi. Wannan dalilinne yasa gimbiya Su'adah tun karar Pa ana gab da rufe campaign.
    “Wai nikan nakega ya kamata ko sau É—ayane ai matar da Ramadhan zai aura a ganta wajen campaign, kar mutane su fassara rashin ganin nata da wani abu kuma aiâ€.
   Shiru kamar Pa bazai amsaba duk da tasan ya jita sarai, sai da ya gama kallon rahoton da akeyi a tv game da taron campaign daya faru na Alhaji Andi ƙaura a jihar Sato sannan, cikin fushi dajin ɗacin kalaman da Alhaji Andi ƙaura yay amfani dasu a wajen da yarfen da yayma Ramadhan yasa muryarsa kausasa.
    “K dake matsayin uwarsa tunda aka fara campaign É—in kinje ne?â€.
   Fuska ta kumbura, cikin zafinta tace, “Miye alaÆ™ar ganina da ganinta a wajen? Kuma ni ai inada masu zuwaminâ€.
   “To itama ai danginta sunje sun wakilceta, dan mahaifinta campaign É—in da yayi a yankinsu bana tunanin wani a gidan nan yayi kwatankwacinsa ma.â€
   “Tunda ko yana neman gindin zama da shegen kwaÉ—ayi ai dole yayi. Imagine yarona kamar Ramadhan dake da kowane irin gata na duniya ya Æ™are da auren Æ´ar karuwa da É—an duniya. Jikar mai tuwo-tuwo tikari a saudia. Miyasa idan dan alkairin da tayinne baza'a bata kuÉ—i itada iyayen nata ba tunda su sukafi buÆ™ata. Sai an wani Æ™aÆ™abama yarona? Idan kuma auren nata dole ne basai a samu wani a bashiba a ma'aikatan gidan nanâ€.
    Pa yasan ya cigaba da saurarenta zai iya mata abinda duk yazo masa a rai, dan haka ya miƙe tsam ya bar mata falon. Hakan ba ƙaramin sake ƙona mata rai yayiba, dan harda ƙwalla suka taru mata a ido, zuciyarta na ƙarajin tsanar Raudha da duk wanda ya shafeta. Tayi alƙawarin koda sunfi ƙarfinta anyi auren nan wlhy sai Raudha ta gwammace mutuwa da rayuwa.
    Da wannan ɓacin ran ta yini ranar, da daddare ta buƙaci ganin Ramadhan, duk da yanda yake a matuƙar gajiye dan yau jihar Nobama sukaje campaign haka ya daure ya amsa kiran nata. Tunda ya shigo take kallonsa, duk ya rame yayi duhu saboda wahalar kai kawo, sai dai hakan bai dametaba, dan tasan yana samun mulki zai koma normal harma yafi da.
    “Barka da dare Maa!â€
Ya faÉ—a cike da girmamawa yana kaiwa zaune kujerar dake gefenta. Tab.. É—in hannunta ta ajiye cike da Æ™asaitarta tana dubansa. “Baka dai, lafiya ne na ganka sukuku?â€.
    Numfashi yaÉ—an furzar, cikin muryarsa mai É—an faÉ—i yace, “Kaina ke ciwo, nasan hayaniyarnan ce kawaiâ€.
     “Basai kasha magani ba, ya za'ai mutum ya zauna da ciwoâ€.
   “Bana son na cika yawan shan maganinne, nasan da nayi barci zan wareâ€.
     Baki kawai ta É—an taÉ“e, ta sake harÉ—e Æ™afa É—aya kan É—aya da tsuke fuska. Dan tana so ya fahimci ba zancen wasa bane. “Ina muka tsaye game da auren wannan yarinyar da aka Æ™aÆ™aba maka?â€.
    Baya ya É—anyi da jikinsa ya kwantar a kujerar, ya lumshe idanunsa tamkar baiji mitace ba. Kusan sakan biyar sannan ya furzar da iska batare daya buÉ—e idanun ba. “Babu wani abu da zan iya yi akan auren nan tunda Pa da Bappi da Anne sun dage, kawai na yanke zan auretan daga baya zan san abunyiâ€.
     “Jikar tikari mai tuwo-tuwon zaka yarda ka aura? To bara na faÉ—a maka idan ma baka saniba. Uwarta kanta sai da tai karuwanci, a barikinne ma ta haÉ—u da uban yarinyar dan shima É—an duniyarne na bugawa a magazine, daga kakarta har Æ´an uwan uwarta duk karuwai ne har yanzun. Idan ma barci kake ka farka, duk yanda zaka zame ka zame kafin cikar waÉ—an nan kwanakin da suka tsaidaâ€.
   Harga ALLAH maganganunta sun sokesa. Kuma dama tayi amfani dasu ne dansu soke-san tunda tasan yanda ya tsani karuwai tun yanada Æ™arancin shekarunsa balle yanzun. Idanunsa dake kumbure da É—an ja a cikinsu saboda rashin samun isashen barci ya zuba mata. Sai kuma yaÉ—an janye cikin taune lips. “Maa waya faÉ—a miki?â€.
    Harara ta danƙara masa tana miƙewa, “Kaje ka bincika tunda na saba maka ƙarya...†Tana faɗa tabar wajen.
    “Maa Please.....â€
Ya faÉ—a da sauri yana Æ™oÆ™arin ganin ta tsaya amma tai masa banza ta shige. Jagwab ya koma ya zauna a kujerar yana dafe kansa daya Æ™ara Æ™arfin gudun ciwo. _(Ƴar karuwa, jikar tikari mai tuwo-tuwo. Ubanta ma a yawon duniya suka haÉ—u da mamarta sukai aure, sannan duk Æ´an uwan uwarta karuwaine har yanzun)._ “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'unâ€. Ya faÉ—a a fili yana dafe kansa da ya sake wata irin sarawa kamar zai faÉ—o Æ™asa. Duk yanda yaso miÆ™ewa a wajen kasawa yay. ALLAH ya taimakesa sai ga Rafi'a Æ™anwarsa ta uku ta shigo falon da shayi a hannu da waya a kunne alamar magana takeyi.
   Cikin sauri tace, “Subahanallahi Yaya!â€. Wayar da kofin shayin ta dire bisa centre table tayo kansa, duk yanda taso taimaka masa ya tashi ta kasa, dole ta fita ta kira Pa da sauran Æ´an uwanta dake can babban falo kowa na harkar gabansa. WaÉ—anda ke a cikin É—akunan barcinsu kuma suka firfito suma saboda yanda take kwakwazon kiran Pa.
    Komai Pa baice masaba, sai taimaka masa da yayi ya miƙe, da kansa ya kaisa har sashen su Anne su Rafi'a biye da shi hankali tashe, wasunsu ma hawaye sukeyi duk da bawai ya suma bane ko yanayi yayi tsamari. Kawai dai idan ka kallesa kasan babu lafiya tare da shi.
   Suma su Anne hankalinsu ya tashi, a take aka nemo doctor duk da yace su barshi shi lafiyarsa ƙalau, amma basu sauraresa ba. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga doctor Shamsu. Koda ya dubasa sai yace musu gajiyace da ƴar damuwar data saka jininsa ɗan haurawa. Sai kuma sugar ɗinsa yayi low sosai da alama kwana biyu baya kula da shan maganinsa.
    Da ƙyar Ramadhan ya yarda aka saka masa drip, sai da Bappi yay masa jan ido ma, ALLAH ya taimaka bai jima da fara shiga jikinsaba barci mai nauyi yay awon gaba da shi. Su duka tausayinsane ya kamasu. Dan sun san yana matuƙar ƙoƙari akan abinda bai saba ba. Duk da yana zirga-zirgar kasuwanci ba irin wannan bace. Dan ko hayaniyar campaign ɗin nan tashin hankaline. Balle kuma akwai ƴan kunji-kunji kala-kala a gefe ga abokan hamayya dama abokan tafiyar.
    Duk fita sukai suna masa fatan samun lafiya ganin yayi barci. Sai dai ran Pa a ɓace yake sanin Gimbiya Su'adah ce ta sake saka Ramadhan ɗin cikin wannan yanayin, kuma duk abin nan da akeyi babu idonta a wajen.
    A É“angaren gimbiya Su'adah kam duk taji komai, taÆ™i fitowane danta sake jaddadama Ramadhan fushinta ya tabbatar da zancen bana wasa bane. Dan taji daÉ—in yanda taga zancen yayi tasiri a ransa. Hakan yasa babu É“ata lokaci ta kira Asma data bata shawarar ta sanar mata. Cikin jin daÉ—i adda Asmah tace, “Su'adah ai dama na faÉ—a miki hakanne kawai zaisa Ramadhan yay mana biyayya. Ni yanzu ina ganin mu haÉ—a wani shiri da zai sake sakashi tsanarta. Suma kakannin nasa susan mike faruwa idan ma basu sani baâ€.
   “Okay ina saurarenki wace idea ceâ€.
    Idanu sosai Gimbiya Su'adah ta zaro bayan ta gama jin yayar tata adda Asma. Cikin rawar harshe tace, “Anya Adda Asmah wannan shawaran yayi kuwa? Karki mantafa mulki Ramadhan ke nema. Koyaya abu yake yanzu zai ita taÉ“a kujerar da yake neman. Abokan hamayya na masa yarfe da Æ™azafi inaga wannan ta fito......â€
    “Su'adah ki kwantar da hankalinki, babu ta inda wannan zai shafi Ramadhan. Sai ma É—aga darajarsa da zai Æ™araâ€.
   “Uhm-uhm Adda kedai bari sai mun sanar ma Fulaniâ€.
    Wani irin takaici ya baibaye Adda Asmah daga can, ji take kamar ta jawo Æ™anwar tata ta hau duka. Amma a fili sai tace “To hakan yayiâ€.
   Koda Gimbiya Su'adah ta kira Fulani ta sanar mata zaginta ta hau yi. Duk da ta yabama Æ™oÆ™arin ta na farko akan sanarma Ramadhan su waye dangin Raudha É—in. Amma maganar fita da tsiraicin suce Raudha ce da wani wannan gangancine. “Ku miyasa baku da hankali. a tunaninku dan kunyi video na bogi kunce itama yarinyar karuwace zai hana mutuncin Ramadhan taÉ“uwa ne. To idan baku san siyasa ba ko mulki ku farka. Wannan abun zai iya ruguza duk wata nasarar da muka samu a campaign duk da kuwa bai aureta ba, idan ma baku sani ba zancen auren nan nata shi kansa wani mutunci ya Æ™ara masa ga al'umma har a wajen campaign. Idan zamu kaudashi kuwa zamuyine a sirrance bawai mu nuna wa duniya ba marasa tunani kawai. Ku fitar da video É—in abokan adawa sujuyar da shi akan tare take da Ramadhan É—in a ciki shashashu kawaiâ€.
   Shiru gimbiya Su'adah tai da waya a hannu dan Fulani na gama faɗa ta yanke wayarta. Itama irin wannan tunanin tayi tun farko shiyyasa ta bijirema Addar tata. Inko hakane gara ta tattara zancen Raudha gefe tukunna, dan duk abinda zai hana ɗanta hawa mulkin nan zata kwana ta yini yaƙi da shi ne.
______________________________
   Badan Ramadhan ya warke ba ya miƙe ya koma filin daga, amma Alhmdllh ɗan ƙarin ruwan da akai masa yasa jikinsa yin daɗi. Ranar wata juma'a bayan sakkowa massallaci yay campaign nasa na ƙarshe a ƙauyensu Taura. Inda ɗunbin jama'a suka taru har abin ya bama mutane tsoro musamman abokan hamayya irinsu Alhaji Andi ƙaura. Su president kam ji suke kamar su goya Ramadhan a baya dan daɗi. Dan kuwa sun san burinsu na dawowar mulki garesu ya gama cika. Sai kuma fatan kauda Ramadhan a shekaru biyun da suka ɗiba masa (wa'iyazubillah. Sun manta ran kowa a hannun ALLAH yake. Sannan shike bada mulki ga wanda yaso a kuma lokacin da yaso).
     Muslata irin farin cikin da Ramadhan ya shiga a yau ɓata lokaci ne. Dan kuwa ya tsorata da yawan mutanen da suka taru dominsa. Har yanaji a ransa kodai akwai aljanu kamar yanda wasu ke faɗa ne. Sai dai farin cikin nasa bai hana jin ɗacin da tsanar Raudha da ahalinta ba. Duk yanda yake turesu a ransa sun kasa gushewa.
______________________________
*_RANA BATA ƘARYA SAI DAI UWAR ƊIY TAJI KUNYA_*
   A faɗin ƙasar NAYA da kewaye yau itace daren zaɓen shugaban ƙasa. Dan haka ta kowanne sashe akwai abinda ke gudana ga kowa. Wasu fatan nasara, wasu shirye-shiryen kota kwana, wasu addu'oi. A cikin masu salla da addu'a a wannan dare harda Ramadhan, Anne, Bappi, Pa, Yafendo, Inna da wasu a cikin ƴan uwan ahalin Taura. A masarautar Bino ma dai Mai-martaba ya kwana raya wannan dare. Yayinda irinsu Gimbiya Su'adah sukejin mulki kamar sun samesa ne.
  Duk da Raudha bata jin son Ramadhan ta masa fatan alkairi, harta kwanta kuma zuciyarta taita zingurinta akan ta tashi tayi salla ko raka'a biyu ne. Tabi shawarar zuciyarta tayi kuma ta roƙi ALLAH samun shugaba na gari bawai Ramadhan ba.
*_WASHE GARI:_* kusan tara na safe Feena ta shigo ta sakata shiga wanka. Batare da tasan dalili cewa tai wankan ba tace ai yanzu tai wanka ita. Fita Feena tayi, babu jimawa ta dawo da kaya a hannu da makeup kit. Sam Raudha batason wannan ƙaƙale-ƙaƙalen, amma saboda Aunty Hannah ta shigo ta mata magana dole ta amine akai mata light make-up ɗin. Sannan ta saka kayan da aka kawo matan. Tabbas tayi ƙyau, sai dai bazata iya fita da gyalen da aka haɗo kayan da shi ba. Dan haka ta ɗakko gogaggen hijjab ɗinta daya shiga da kayan ta saka. Duk jarabar aunty Hannah dole ta barta dan kuka ta sanya musu.
      Tana zaune fuska a kumbure tana shan tea É—in da aunty Hannah ta tilasta mata sha Yasmin ta iso da saÆ™on “Mom wai ga baÆ™on yazo inji mama tambayaâ€.
   Cikin sauri aunty Hannah ta amshe kofin shayin hannun Raudha É—in. “Sai ki tashi tunda dama haka kike so ki fita bakici komai ba. Sai ki tashi ya iso kuje ku jefa Æ™uri'a muma zamuje tare da tawagar shugaban Æ™asaâ€
    Sosai gaban Raudha ya faɗi, ta ɗago da sauri ta dubi Aunty Hannah. Sai dai kafin tai magana Feena ma ta shigo.
   “Hajiya suna jiranta faâ€.
Da sauri Aunty Hannah ta miÆ™ar da Raudha, bag É—in da zata riÆ™e mai Æ™yau ta saÆ™ala mata a hannu, hakan sai yay matuÆ™ar sake fito da tsarin kwalliyar tata musamman da hijjab É—in ke iya cinyarta kawai, gashi mai hannu, ya kuma É—au guga ya kwanta luf da haska Æ™yaÆ™yÆ™yawar farar fuskarta kasancewar blue color ne, sai hakan ya Æ™ara bama skirt É—in nata fitowa sosai ya buÉ—e. Kamar zata fasa kuka ta zura takalman da aka ajiye mata masu É—an tudu da suka sake fidda Æ™yawun Æ™afarta.........âœ
  Â
*_BAƘAR INUWA...👇ðŸ»_*
Da É—umi-É—uminsa💃ðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_A AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following É—ina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰ðŸ¤ðŸ»ðŸ‘‡ðŸ»_
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇ðŸ¾ðŸ‘‡ðŸ¾ðŸ‘‡ðŸ¾ðŸ‘‡ðŸ¾ðŸ‘‡ðŸ¾
*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
--------
Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
_Account No_ - *1220077999*
_Account Name_ - *Arewa Books Publishers*
_Bank_ - *Zenith Bank*
Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:
Amount Paid: - Nawa aka tura?
Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa
Transferred time: - lokacin da aka turo
Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi
Deposit date: - ranar da aka turo
Sai ayi SUBMIT.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email É—inki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taÉ“a *Sign Up* shikenan an buÉ—e account a ArewaBooks💃ðŸ»ðŸ˜‚.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions É—in nanðŸ˜ðŸ˜˜ðŸ˜ðŸ¥°ðŸ˜ðŸ˜Š_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™ðŸ»_*
[6/10, 7:45 PM] NANA: *_Typing📲_*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.