Bakar Inuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: BAKAR INUWA BILLY.txt
Chapter 49 of 74
*_Episode 48_*
MAGANIN SANYI SADIDAN.08046881166
Kashi 90% cikin 100% na matan wannan zamani basuda matsalar da take damunsu kwarai irin sanyi,
Toga maganin sanyi kankat,
Bazanmaki rantsuwaba domin batadakyau ga Sanaa,ama zanbaki tabbaci Koda infection aka haifeki d izinin Allah ze warke,
Watakil kice kunyi magani harkungaji yaqi tfy to insha Allah ki jarraba wannan bi'iznillahi zaki dace.07046881166
Qulli ne guda daya tak zakisha d koko 2500 ne kudinshi,wlh zakibani lbr duk wani balain sanyi seyayi gudun fanfalaki y barki,
Dan Allah Dan grman Allah serious buyers Dan Allah chat me up 08046881166
*_Episode 48_*
.........Gaba ɗaya ya gama sabauta mata tunani da lafiyar jiki. Dan kuwa cak ya ɗauketa a karon farko na tarihi, bai direta ko inaba sai saman gado. Bai damu da rawar da jikinta keyiba da roƙon da take masa ya zame towel ɗin da taketa faman riƙo kai kace igiyar neman tsira ce. Batama san ta daka tsalle ta ruƙunƙumesa ba. Atare suka faɗa saman gadon.
    “Haba hajjaju ki bini a hankali mana ai zanyiâ€.
  Yay maganar yana danne dariya da ƙyar. Itako kuka ta fashe masa da shi da sake ƙanƙamesa. Burinta bai wuce karya kallar mata jiki ba. Tausayi ta bashi dan yasan wannan wani sabon al'amarine daga gareta. Yajawo bargo da hanu ya lulluɓesu yalwataccen murmushi shimfiɗe a fuskarsa. Jin bil haƙƙi kukan take kuma taƙi barinsa yay ko motsi ya sashi lalubar bakinta ya manne nashi. Cikin salon tsantsar zalama da yanayin da yake ciki ya fara binta da salon da batasan zai iya aikatawa ba.
    A wannan lokacin tsabar firgici zamu iya cewa Asthma ɗin Raudha ma motsawa ta nemayi. Dan da gaske numfashin ta a take ya fara fita a rarrabe har tana sarƙewa. Bai barta ba sai da ya fahimci yana neman kama wani layin saɓanin wanda yay niyyar bi kawai.
   Shiru yay bayan barinta yana sauraren yanda hawayenta ke sauka a Æ™irjinsa har yana huda riga yana ratsasa. Yay tattausan murmushi hanunsa saman kanta da akai ma kitson da baisan anyi ba. Sai da numfashinsu ya gama dai-daita ya kai bakinsa kan kunenta yana magana cikin muryar da batasan ya mallaka ba. “Cutie! Yaufa babu fashi sai anje duniyar samo Æ´an huÉ—un nan bazan iya É—aga Æ™afa baâ€.
   Sake ƙanƙamesa tai jikinta na rawa dan harga ALLAH tsoro ma yake bata. Kalamansa sake firgita rayuwarta takeyi. Shine na farko daya taɓa mata abinda wani namiji a duniya bai taɓa mata ba. Shine na farko daya taɓa ɗora hanunsa akan abinda wani mahaluki bai taɓa taɓawa ba. Shine na farko daya ganta a yanda wani bai taɓa gani ba sai yau, yau ɗin ma yanzun nan duk da bata da tabbacin ya kalleta ɗin...
   Ring ɗin da wayarsa tai a jikinsa ya sashi furzar da numfashi mai ƙarfi. Sosai idanunsa suka canja launi hakama fuskarsa tayi ja abinka da fari. Yasan Maah! ce, ya kuma san abinda take buƙata. Dan ta tabbatar masa tana son ganinsa daya dawo akan zancen aurensa da Aina'u. Da ƙyar ya iya saita kansa yakai wayar kunensa bayan ya ɗaga. Da sauri Raudha dake duƙunƙune a jikinsa tai saurin barin jikjnsa ta dire saman gadon. Bai hanata ba harta sake duƙunƙunewa cikin bargon daya rufa musu. Murmushi yay ganin yanda ta yayesa ita kuma ta nannaɗe a ciki kamar an nannaɗe gawa a likafani. Sosai ya tashi zaune ko zai sake samu muryarsa ta saisaitu.
    “Kiyi haÆ™uri Maah zanzo ALLAH amma sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Inaga ma anan zamu yi hutun nan na kwana huÉ—u yanzu kaina na ciwoâ€.
   Abinda ta faÉ—a ya sashi sake marairaicewa kamar yana gabanta. “Please maah i promise you bazan saÉ“a alÆ™awari baâ€.
   “Okay thanks you dear Mammah I love youâ€.
Wannan kalma ta Ramadhan ta bala'in faranta ran Gimbiya Su'adah. Sai taji gaba É—aya fushin da takeyi da shi ya kwaranye a zuciyarta. Sai dai hakan baisa taji zata janye maganar auren Aina'u ba, tana akan bakanta duk da suna kan rikici da Pa ne akan hakan ma. Dan kuwa su Bappi sunce su babu ruwansu indai Ramadhan ya amince su masu son hakane ai.
    Mikewa yay yana kallon Raudha dake Æ™udundune fuskarsa da murmushi. “Irin wannan nannaÉ—a haka Ustazah kamar wata shawarma?. Indai nine nayi nan ina jiran abinci da yunwa na dawo cikina kamar anmun sataâ€.
  Ya ƙare maganar da shafa cikin nasa daya ɗan taso. Shi kansa ya fahimci ya ƙara nauyi, kwana biyun nan baya iya fita training, dole ya dawo kar azo yakai matsayin da ƴar rigimarsa zata kasa ɗaukarsa wata ran. Da wannan tunanin ya fice ya barta bayan ya gwada yayeta ta sake saka masa kuka.
     Kallon-kallo Aina'u da Muneera kema juna ganin yanda Yayan nasu ya fito a ɗakin Raudha fuska ɗauke da ƙayataccen murmushi da sai dai su hanga yanama wani shi ko su Bappi. Wani irin zafine ya shiga ratsa zuciyar Aina da jin ƙara tsanar Raudha da duk wandama ke tare da ita. jitake zata iya kashe Raudha saboda Ramadhan a yanzu. Dan tun tana shakkar maganar auren nasu a yanzu abin ji take yana ƙara mata tasiri a rai da ɗokin kasancewarta matarsa kodan suma susha romon mulki, dan tasan dai ta auresa yanzu tabbas itace zata zama first lady bawai waccan kazamar yarinyar da ko tsarkin kashi batajin ta gama ƙwarewar yi. Momynta (Adda Asmah) ta gama tabbatar mata indai Ramadhan ne sai ya sota fiye da uwarsa ma a duniya da su Anne, dan zata mallake mata zuciyarsa yanda bazai sake tunawa da kallon wata mace da daraja a duniya ba sai ita. Tabbas tahau ta zauna. Ta kuma yarda. Dan ita shaidace Abbansu a tafin hanun Mom nasu yake. Sai abinda tace yake yi.
(Hummm🚶ðŸ»ðŸ¤•. ALLAH yasa sanda za'aima wasu hisabi muna aljannah a fadan MANZON ALLAH (S.A.W).
 ★★★
   Da ƙyar Raudha ta iya daurewa ranta ta tashi. Sai dai gaba ɗaya a tsorace take da komai ma. Yau gaba ɗaya Ramadhan ya rikita mata lissafi. Tama rasa wane kalar tunani zatai. Shiryawa tai cikin doguwar rigar abaya baƙa. Komai bata shafa ba sai khurah da turare. Sai dai ta wanko fuskarta saboda kukan datai. Cikin ɗar-ɗar da zuciyarta keyi ta fito domin sama masa abincin daya buƙata. Cikin sa'a ALLAH ya taimaketa tai kiciɓus da Bilkisu a kitchen ɗin sama. Dan ƙamshin da taji da motsine ma yaja hankalinta tunda tasan bamai shiga inba itaba sai mama ladi dake gyarawa.
   Ido taÉ—an waro kaÉ—an na mamaki. “La aunty Bilkisu..â€
   Bilkisu dake murmushi tai saurin cewa “Kamar kice komai. Kawai naga Yaya a bazatane shiyyasa na rugo kitchen É—in tunda ba salla zanyi ba. Mun shagala kwata-kwata bamu buÉ—e television ba balle muga batun dawowarsa.â€
    Ajiyar zuciya Raudha ta sauke. Cikin danne abinda ke taso mata tace, “Wlhy nima nasha mamaki.â€
   Ƴar dariya Bilkisu tai. “Uhm ya miki surprise na masoyane kawaiâ€.
   Kunya zancen Bilkisu ya bama Raudah, ta kauda kai kawai tana murmushi. Hannu ta saka suka karasa aikin da aready dama Bilkisun tana gab da kammalawa. Sai da suna haÉ—a abincin a basket Bilkisu ke faÉ—in. “Niko idonki kamar wadda tai kukaâ€.
   Da sauri Raudha tace, “Abune ya faÉ—amin a ido daÆ™yar na samu ya fita bayan nata zuba masa ruwaâ€.
  Sannu Bilkisun ta mata dan har zuciya ta yarda. Raudha ta ɗauka basket ɗin tana mata godiya da addu'ar ALLAH ya kaisu ran aurenta da yanzu haka ana shirin saka rana kusan su biyar.
     Da Æ™yar ta iya kawo kanta Æ™ofar É—akin nasa. Ji take kamar bazata iyaba amma ta daure matuÆ™a. knocking tayi kamar bataso. Tana shirin sake na biyu aka buÉ—e Æ™ofar. Bata yarda ta kallesa ba, dan tasan dai shine É—in. Shiko idonsa a kanta Æ™yam yana Æ™aremata kallo yanda abayar tai matuÆ™ar mata Æ™yau. Matsawa yay ya bata hanya ta shige batare da yace komaiba. Sai da ta gittashi ta shiga ya maida Æ™ofar ya rufe. Saman kujerar daya tashi ya koma ya zauna tare da É—aukar Tab.. Da ke a hanunsa kafin shigowarta. Ganin ya basar da ita ya sata daurewa tace, “Ga abincinâ€.
   “Zubaâ€
Ya faÉ—a a taÆ™aice batare da yabar abinda yakeyi ba. So yake yay dauriyar fasa abinda yay niyyar yi a gareta amma zuciyarsa taÆ™i amsar lallashin sam. Bai kalleta ba harta zuba masa gasashen naman ragon daketa Æ™amshi, yaji haÉ—i na musamman. Sai kunun madara da Bilkisu tayisa a nutse saboda sanin yanda yake Æ™aunarsa. Zata zuba abincin yay saurin dakatar da ita. “No bar nan kawaiâ€.
  Dakatawa tai ta maida kwanon ta rufe da tura table ɗin gabansa yanda zai samu nutsuwar ci. Sai da ya ɓata wasu sakanni ya ajiye tab.. Ɗin, dai-dai da miƙewar Raudha dake fatan samun hanyar guduwa dan yau bazata juri zama da shi a inuwa ɗaya ba. Caraf ya riƙo hanunta ya zaunar a gefensa.
   “Na sallameki ne?â€.
Jitai kamar ta fashe masa da kuka kawai, amma ta daure dan kar yaga kamar ta cika rashin wayo. Hankalinsa ya maida ga abincin zuciyarsa na tunanin ta yanda zai É“ullo mata ta saki jikinta. Sai dai ya kai laumar nama baki yake faÉ—in, “Uhhmm Bestie kinji wani gashi na musamman kamar a birnin sin. K karfa ki zata santi nake naji abunne har cikin kaiâ€.
    Murmushi ne ya suÉ“ucema Raudha. A hankali tace. “Uhhmm!â€.
      “Ai bakiji Humm bama sai kinciâ€. Ya É—ago gareta da tsoka daya ciro jikin dogon tsinken da Bilkisu ta tsiro guda uku. “BuÉ—e bakin kiji kar ayi babu keâ€.
   A kunyace tace, “ALLAH ni na Æ™oshiâ€.
   Fuska ya É“ata yana É—an hararta. “Keni bansan gulma buÉ—e baki. Ni nasan tun kan ki kawo namannan kike addu'ar ALLAH yasa na sammikiâ€.
     “Ya ALLAHUâ€. Ta faÉ—a da dasashshiyar muryarta dariya na suÉ“uce mata. Shima murmushin yake tare da sake kai mata naman bakinta. Dole ta buÉ—e saboda cewarsa. “ALLAH sai na miki É—ura. Kuma saina tauna yayi laushi na juye miki a baki dole ki haÉ—iyeâ€.
   Fuska ta yamutse alamar Æ™yankyami. Ya dungure mata kai da faÉ—in, “K yarinyarnanfa Æ´ar wulaÆ™ancice wani lokacin. Wai Æ™yanÆ™yaminama kikeji? Koda yake hakafa kikaimin kwanaki ina mura. Har shaÆ™a miki murar nai amma kikaÆ™i É—auka saboda É—an banzan Æ™arfin jininkiâ€.
   Yanzu kam kasa daurewa tai ta sanya dariya. “Kai Ya Ramadhan ko tausayi babu?â€.
   “K nifa kibar wani cemin Yaya niba Yayanki bane bamsan kalar dangi. Nasan dai akwai abota tsakaninmu sai kumaaaaa......â€
    Ya É—anja Æ™arshe yana kashe mata ido batare daya Æ™arasa ba. Ba shiri ta miÆ™e zaram amma yay saurin riÆ™eta ya maida. “Ustaza bansan fassara irin taku ta Ustazai fa. Kijira na karasa mana kafin ki kaini inda banje baâ€.
  Dole ta dawo ta zauna kamar ta É“uya a kujerar dan kunya. Ya dungure mata kai yana kai nama bakinsa da taÉ“e baki. “Gulmammiyar yarinya nafasan kema kin kamu. A yanzu nan duniya bayan Mommy da Abba babu wanda kike so Kamar Ramadhan...â€
   “Ni yaushe nace!â€.
Ta faɗa cikin suɓutar baki tana taɓe fuska.
       “Yo sai kin faÉ—a? Yanda kika kadandaneni ram É—azu ke daÉ—i mijima ai ya isa shaida.â€
   “Innalillahi....â€
Ta faÉ—a kamar zata fasa kuka dan kunya. Dariya ke cinsa yanda tai wuri-wuri da idanu na kunya. Ya danne da Æ™yar. “Oh kice baki son nawa mana kiga in gobe banje an É—auramin aure da Æ´ammata uku ba galla-gallaâ€.
     Ji Raudha tai kamar ya kwaɗa mata guduma a tsakkiyar zuciya. A take fara'ar fuskarta ta ɓace ɓat. Tai ƙasa da kai zuciyarta na mata zafi da kalamansa.....
   Wani daÉ—i ya baibaye Ramadhan kamar ya tashi ta taka rawa. Cikin shafa sumar dake zagaye da kumatunsa yace, “Oh su Ustazah ba kunya anga sumulmulin yaro É—an jikan Anne an maÆ™ale. Irin wannan kishi haka Ƙawata? To indai baki so nayo kishiyoyi yau kam dole naje farautar triple koda yake kefa huÉ—u ma naji kina faÉ—a saboda tsabar haÉ—ama keda ma ko É—an kiss É—in nan na zamani sau É—aya aka taÉ“a mik.......â€
    Ai bata bari ya Æ™arasa ba ta daka tsalle ta guntse masa baki da hannayenta. Wayyo dariya kamar ta kashe Ramadhan. Yasan ya riga ya gama da Æ´ar darunsa yau. Sai dai wani farin ciki ke dawainiya da shi ganin kishinsa Æ™uru-Æ™uru tattare da ita. Koba komai yaji daÉ—i bashi kaÉ—ai ke wahalar banzaba akanta ashe. Jikinsa ya jawota ya rungume. Cikin raÉ—a yace, “Na nayi shiru tashi kici abinciâ€.
    “Kaci kayanka, ko kaje kuci da Æ´ammatan nakaâ€.
   “Wayyo Ramadhana anyi kasuwa. Uhm-uhm fa Bestie ALLAH karki tsaya kallon ruwa Æ™waÉ—o ya miki Æ™afa. BABU SO MIYA KAWO KISHI?â€.
   Turesa ta shigayi da faÉ—in, “Wama zaice yana sonka É—in. Abotarma an fasaâ€.
      Nanma dariya kawai yakeyi yana sake riƙota dan ya fahimci so take tai amfani da damar ta tsere. Ya jima da gane tanada wayo duk da ƙarancin shekarunta. Matseta yay da ƙyau duk yanda taso ya hanata damar dole ta nutsu saboda abinda ya raɗa mata a kunne kamar ta nutse. tanaji tana gani ya tilasta mata cin nama da kunun wanda yay mata matuƙar daɗi. Dama da ƴar sauran yunwarta ta rana. Bayan sun kammala ta tattara kwanika zata fita da su ya hanata. Acewarsa ta tayashi salla ya bata labarin faransa tunda ita bata tambaya ba. Ganin ya zama serious doleta haƙura. Sai dai ta masa complain na rashin hijjab yace abu mai sauƙi yana da shi ai....
     Raudha dai dauriya kawai take amma tabbas a tsorace take. Bayan sun idar da salla ya dafa kanta yay addu'a kamar yanda musulinci ya tanada ya kuma dace ace tun randa aka kawota gidan hakan ta faru. sai dai lokacin gogan nata na bisa gajimaren hayaƙi hakan bata faru ba. Sosai Raudha tai mamakin yanda taji yana kwararo addu'oi. Sam batai zaton yanada ilimin addini kamar haka ba. Sai taji ya sake birgeta zuciyarta ta ƙara nauyi game da shi.
   Bayan sun idar ma ta buƙaci son zillewa ta gudu ya sake hanata. Ƙarshe ma kayan barci da batasan daga ina ya samosu ba ya bata wai ta saka. A matuƙar kunyace ta dubesa cikin marairaicewa amma ya nuna mata babu wani ɗaga ƙafa yau anan zata kwana. Shi ya gaji da raba musu makwanci da takeyi. Daga karshe ya haɗata da kunyar data sakata bin umarninsa dole.
    “Ustazah a haka za'a samo Æ´an huÉ—un kina gabas ina yamma. Gara dai kiba marasa É—a kunya ki haifama Maah jikan da taketa fatan gani. Gashi ma kin Æ™udiri surprising É—inta har Æ´an huÉ—u kika shirya.â€
    “Kai Ya Ramadhan magana wai bata wucewa a gunkaâ€.
  “Oh ikon ALLAH na kulafa kin fara bin hanyar rainani yarinyarnan. Ni miye nawa tunda faÉ—a kikai naji. Ai har Anne zanma albishir gobeâ€.
    “Na shiga tara dan ALLAH ka taimakeniâ€.
   “Hhhh taimako É—ayane zaki samu sai kin saka kayan nanâ€.
   Wannan kandagarki nasa ya sata shiga toilet ta canja. Sai dai ta jima tana duban kanta a mirror ɗin toilet ɗin ta kasa fitowa. Sai kallon kanta take cike da kunya da ganin ƙyawun da tayi kamar ba itaba. Sai dai gaskiya bazata iya fita da rigarba gabans....
   Maƙalewa tunaninta yay jin an buɗe ƙofar toilet ɗin. Tai mugun diriricewa ta ruɗe. Tama rasa mizata jawo ta rufama jikinta. Ramadhan da kamar suman wucin gadi ya riska a bakin ƙofar yana jan numfashi da ƙyar zuciyarsa na wani irin bugu da sauri-sauri. Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafa ya ƙaraso gareta. Sai dai a zahiri yanda yake a nutse bazaka taɓa fahimtar halin da yake a ciki ba. A bayanta ya tsaya idanunsa kafe akanta ta cikin mirror da suke fuskanta, sai dai ita ta duƙar da kai ta kuma kuɗindine jikinta da towel ɗin data sami nasarar jawowa.
    Ta bayan nata ya zuro hannayensa duka biyu ya zare towel É—in data rumtse a cikinsu. A wani irin tashin hankali taja numfashi a fisge da rumtse idanunta da Æ™arfi tana ayyanawa a ranta. “Shike nan tawa ta Æ™are ni Aminatuâ€.
    Lallausan murmushi ya saki yana yaye towel ɗin a hankali saboda furicin zuci datai ya fito fili. idunsa kuma a kan cute face nata da hawaye ke silalowa a hankali. Tabbas matarsa ƙyaƙyƙyawa ce, mai kuma ƙyawun surar jiki abin buƙatar kowane irin namiji mai lafiya. Ya ja nannauyar ajiyar zuciya da kamo kafaɗunta duka ya juyo da ita tana fuskantarsa. Rawa jikinta ya farayi dan ƙafafunta bazasu iya riƙe nauyin gangar jikintaba a yau.
     Tausayinta ya sake kamashi, sai kawai ya rungumota cikin jikinsa dan shi kansa ji yake jini na haura masa har saman ƙwaƙwalwar kansa. A tare suka saki kakkaurar ajiyar zuciya, sai kawai ya ɗauketa cak suka fice.
    Cikin gadonsa da kullum Raudha ke Æ™waÉ—ayin ganin an saki runmfar net dake jikinta ya nufa da ita. A hankali ya fara kai Æ™afarsa É—aya ya dire gwiwar sa akan lallausan gadon yana rankwafawa ya direta a gadon itama. Cikin wata irin murya mai tsananin sanyi da rauni yace, “To sakeniâ€.
    Sam bazata iyaba. Dan hanun nata ma rawa yakeyi, ta ƙara ƙanƙame wuyan nasa da hannayenta data tallafo ƙeyarsa hawaye na rige-rige sakkowa.
   “Ameenatuâ€.
Ya kira sunanta da murya mai tsananin tsada da tsantsane.
      “Uhhmyim!".
Ta faɗa a shaƙe.
  “Kiyi haÆ™uri na tashi zan canja kaya neâ€.
    Da sauri ta girgiza masa kai idanunta rumtse. “Ya Ramadhan tsoro nakejiâ€.
  Murmushi ya saki mai sanyi, a hankali ya kai bakinsa kan laɓɓanta da goshinta ya sumbata. Cikin sake raunana harshensa yace, “Nima tsoron nakeji shiyyasa na gayyatoki ki tayani kwana kar ojuju ya kamaniâ€.
   Yanda yake mata magana a kunne ya sata sake ƙanƙamesa. Ganinfa ba sakinshi zatai ba sai ya kawai ya kwanto jikinta gaba ɗaya ya sakar mata nauyinsa.
   “Mummy zan mutuâ€. Ta faÉ—a da Æ™yar jin nauyinsa na fitar hankali. Murmushi kawai yayi ya É—agata, baice komaiba ya fito a cikin gadon. Ita kuma ta samu damar nannaÉ—e kanta a bargon zuciyarta na gudu kamar zata faso Æ™irjinta ta fito kawai kowa ya huta. Harya koma toilet ya kammala kimtso kansa bata buÉ—e kanta ba. A haka ya kashe fitilar É—akin yabar lamps kawai ya shiga net É—in shima. Bargon data Æ™udundune a ciki ya É—aga shima ya shige..
Murmushi yayi jin yanda ta Æ™anÆ™ame waje guda lokacin daya kwanto jikinta. A hankali ya kai lips nashi ya sumbaceta ta gefen kunne, ta Æ™ara curewa waje guda jikinta na rawa. “Haba Ustazah, tsoro fa na ragwayen mata ne, ko kina so masu zuwa Bingon suzo kuma babu cikin Æ´an huÉ—un uhhm?â€.
Kasa cewa komai tai, sai hawayen tsoro dake mata gudu, babu abinda ke cin ran Ramadhan sai dariya. Musamman daya shafa fuskarta yaji hawaye.
“Oh ni Ramadhana, ni kuma haka ALLAH yay dani auren raguwa. Yo raguwa mana, tunkan ace kule ke kin tafi cas...â€
Tsabar yanda zuciyarta taje maƙura kuka ta fashe masa da shi mai ƙarfi. Ya danne dariyarsa da ƙyar tare da mirginota ta juyo suna fuskantar juna. Sai kawai ya rungumeta yana shafa kanta murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Sai da ya tabbatar ta nutsu ya dai-daita fuskarsu waje guda, cikin ɗan hasken dake a ɗakin yake kallonta, itako idonta a rumtse gam.
“Kodai mu haÆ™ura da farautar Æ´an huÉ—un kawai Ustazah?â€.
Da sauri ta É—aga mata kanta.
Ya saki murmushi mai faÉ—i da É—ora goshinsa kan nata ya riÆ™o hanunta cikin nashi. “Tom naji, amma idan an haÆ™ura minene tukuycina ni?â€.
“Wlhy zan maka nama da yawa da safeâ€.
Raudha ta faÉ—a da sauri cikin rawar murya. Mi Ramadhan zai inba dariya ba. Wato yarinyar nan ta maidashi mayen nama. A fili kuwa sai ya cewa yay “Okay ALLAH ya kaimu Ƙawata ta amanaâ€.
Daga haka É—akin yay shiru, jin kamar ya fara barci Raudha hankalinta ya fara kwanciya, itama sai ta lumshe na idanun. Idanu ya buÉ—e a hankali yana kallonta da murmushi. “Yaro yaroneâ€. Ya faÉ—a a hankali da jan bargo ya lulluÉ“esu baki É—aya.
Can cikin barci ta tsinkayi abinda yafi ƙarfin saninta, sai dai mai girma shugaban kasa da shirinsa yake, dan cikin ƙanƙanin lokaci yay mata dabaibayin daya sakata shagala da miƙa wuya, sai da labari yay nisa ta raina kanta.......
*_Bily kama bakinki iya nanðŸ¤ðŸš¶ðŸ»_*
      ★Kallo guda zakai mata kasan taci uban kuka harta godema ALLAH. Duk da kasancewarta ba fara tas ba yanayin saida ya nuna a fuskarta. Gaba É—aya ta jangwabe kamar ba Ustazah Raudha ta hutawa É—iyar baba Dauda da Asabe ba. Lallai ba Æ™arya daren jiya anci Æ™aniyar sabada. Dan kuwa dai mai girma shugaban Æ™asar Naya Ramadhan B Hameed Taura bai nuna yasan wata Raudha Æ´ar 18years ba balle ya bita a sannu. Babu da kalar yaren da bata roÆ™esa ba amma ya toshe jinsa da ganinsa ya nuna mata baya fahimtar kowanne yare saina cikar burinsa. Cizo da yakushi kuwa ya samu rabonsa gwargwadon iko har ba'a cewa komai. A Æ´an gidansu babu wanda bata lissafo yazo ya taimaketa ba har maÆ™wafta da su Anne sun sha kira........âœ
  _Mace Æ´ar gatan ALLAH. mace Æ´ar gatan duniya. Mace sarauniya. Mace farin cikin duniya. Mace duniyar duniya. Mata ina miÆ™o gaisuwar ban girma amma banda ballagazaye wanda suka gama rabarwa a waje🙄🙄ðŸ˜ðŸ‘©ðŸ»â€ðŸ¦¯_
   Â
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link É—in dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹ðŸ»â€â™€ï¸â›¹ðŸ»â€â™€ï¸ðŸ˜˜_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*â¤â€ðŸ”¥
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇ðŸ¼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuÉ—in littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇ðŸ¼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇ðŸ¼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇ðŸ»_*
Da É—umi-É—uminsa💃ðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»ðŸ’ƒðŸ»
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following É—ina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰ðŸ¤ðŸ»ðŸ‘‡ðŸ»_
*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email É—inki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taÉ“a *Sign Up* shikenan an buÉ—e account a ArewaBooks💃ðŸ»ðŸ˜‚.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions É—in nanðŸ˜ðŸ˜˜ðŸ˜ðŸ¥°ðŸ˜ðŸ˜Š_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™ðŸ»_*
[7/5, 11:13 AM] NANA: *_Typing📲_*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.