Trending Hausa Novels

Zinare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zinare Book 1.txt

Chapter 7 of 13

Page 24

SARTAJ
★washe gari yana farfaɗowa daga dogon sumar azabar da ya yi da ihun kiran Malik yafara yana roƙo da magiya.

A surutan Sartaj da aka sanarwa su ÆŠayyib da su kayi dawowar cikin dare suka fuskanci Malik yana bibiyarsu, irin bibiyar da basu san ta hanyar da zasu toshesa ba. Kuma sun kasa gano wane yake kai masa rahoto.

Mutanen Yankin da suka ji ai aikin Malik ne ya yankewa Sartaj ƙafa, tsoron gulmar kowa da cin amanar junansu ne ya ƙara shigarsu. Tunda ga shi an yankewa Sartaj ƙafar da yake zaryar kaiwa su Ɗayyib gulma dashi.

"Amma mai yasa Malik bai taimaki Naila ba, ko bai san halin da take ciki ba ne??????" Tambayoyin da suke ta yiwa junansu kenan.

Duk nacin da akayi Sartaj ya buɗe baki ya faɗi ina yaga Malik har ya yanke mai ƙafa, ƙin yin magana ya yi.

Washe gari da su ÆŠayyib suka zo dubasa ihu ya kurma yana rufe fuskarsa, alamun bayason ganinsu. Har suka bar É—akin bai buÉ—e fuskarsa ba.

Har Sartaj ya warke ba ya iya yin gulmar kowa, balle ya ambaci sunan Malik, gani yake yi kamar idan ya ambaci sunansa zai bayyana a gabansa.

Ranar da su ÆŠayyib suka yanke shawarar neman mafita akan Sartaj a Fadar Sarki Hammam gudun tonuwar asirinsu washe gari aka nemesa aka rasa shi da tsohuwar Mahaifiyarsa.

Ɓatan Sartaj da mahaifiyarsa ya yi matuƙar tayar da hankali Mutanen Daular Sarki Hammam, sama da yadda labarin tafiyar Naila da Kakarta Birnin Abyad ya tashi hankalin su, domin sun san ko su Naila sunje dole su dawo, saboda maganin matsalarta ya na wajensu. Saɓanin talakawan Yankin da suke ganin Sartaj ya gudune saboda abun kunyar da ya aikata.

A karon farko aka fara saka jami'ai a duk wani hanyar da zai kai mutum cikin Yankin Tudu domin kawo ƙarshen Malik, shima Sufyan cikin gaggawa ya shirya komawa, saboda ɓacewar maganin da yasan dole idan ya cigaba da zama za'a tambayesa ya na ina? da kuma gudun kar ɓarna Malik ta ratsa da shi, domin zuwa lokacin ya fuskanci a kwai wasu manyan sirrikan da bai san da su ba...

NAILA
Allah Ya amshi addu'ar Kaka. A tafiyar kwanakin da suka yi, ciwon Naila ya na yawan tashi, amma da zarar ya tashi Kaka za ta rungumeta ta yi ta tofamata addu'o'i har sai jikinta ya yi yaushi barci mai nauyi ya É—auketa

BIRNIN ABYAD

Da taimakon Allah suka isa Birnin Abyad. Kaka ta zuba ƙauyanci wasu lokutan garin Kallon Mutane har tuntuɓe takeyi.

Da ɗan ƙarfin da Naila take ji, take yi mata raɗar motar da zasu hau a kunne. Da hannu kaka take kwatanta mu su komai tunda batajin turanci, kuma batajin asalin yaren ƙasar. Kamar ko da yaushe idanun Naila maƙale a hanyar Babban Birnin Abyad, ƙewar Bushra da Yasar na bijiromin, suka wuce hanyar.

Gidansu Naila ba ƙaramin burge Kaka ya yi ba.
Ba ta hutu ba bayan sunyi salla ta fara gyara ko ina na sashen.
Da taimakon Kaka bayan ta gama gyare-gyarenta Naila tayi wanka. A ranar Kaka ta farayimata amfani da maganin su Sufyan kamar yadda Mallam ya koya mata. Bayan wannan ta haÉ—a har addu'o'in da ya bata.

Da guzurin kayan abincin da suka taho da shi daga Yankin Tudu suka fara amfani, kafin Naila ji sauƙi su canza ƙudi su siyo wasu.

A cikin kwana uku sauƙi ya fara samuwa, Naila tana iyayin komai da kanta, har tayi Sallah a tsaye a kan ƙafafuwanta.

Kwana biyu bayan nan Naila ta shirya ita da Kaka suka tafi Gidan Iyayen Yasar domin jin halin da yake ciki.

Yasar ya na kwance babu lafiya tsohon watanni biyar kamar yadda Mahaifiyarsa ta faÉ—a musu bayan sun gama gaisawa, ta ce Accident ya yi a kan hanyarsa ta dawowa daga Babban Birnin Abyad. Ya na barci lokacin da su Naila suka isa, bai farka ba har sai da suka fara haramar tafiya.

Da mamaki yake kallonsu kamar bai ganesu ba, har sai da Naila ta gaisheshi ta faɗamai sunana sannan ya fahimci ita ce. Da zafin naman ɗan ƙarfin da yake ji ya gyara zamansa ya na faɗin

"Naila! Maiyasameki kika koma haka? Ciwo kakayi? Maiyasa baki dawo Makaranta ba? Na so zuwa har Yankin Tudu cigiyarki Saboda na kira wayarki bana samu wannan tsautayin ya afkamin ki gafarceni."

Kai Naila ta sunkuyar ƙasa tana Kuka.
Kaka ce ta basu labarin jinyar da Naila ta yi. Dukkansu sun tausayawa Naila har Iyayen Yasar da a baya suke gudunta. Sun É—an jima a Gidan kafin su dawo Gida.

★washe gari sai ga siyayyar kayan abinci da kayan motsa baki kala-kala har da kayan sawar Kaka, da wayar amsa kira duk daga Gidansu Yasar. Su Naila sunyi farin ciki matuƙa tare da godiya mai tarin yawa.

A hankali a hankali jikin Naila ya fara murjewa saboda canjin cima, muhallahi da kuma lafiyar da take ƙara samu. Itama Kaka tsaf ta yi kyau, su na waya da mutanen Yankin Tudu lokaci zuwa lokaci da number da suka rubuto mata a jikin takarda.

Bayan Naila ta samu sauƙi, Yasar da kansa ya jagoranceta har Makarantasu duk da baya iya tafiya sosai saboda karayar ƙafarsa da bai gama warkewa ba.

Naila bata samu matsalaba albarcin Yasar da kuma shaidun da suka gani da ido, saboda har lokacin akwai banbanci da yadda nake a baya kafin ta bar Birnin Abyad.

Da farin ciki Naila ta dawo Gida, itama Kaka daÉ—i ne ya kamata, tayi ta yiwa Yasar godiya tana samai albarka.

A cikin watanni biyun da Makarantarsu Naila suka ƙaramata a matsayin hutu, jikinta ya yi kyau kamar bata taɓa jinya ba. Da kanta ta kai Kaka sukayi siyayya kafin su wuce Gidansu Yasar.

Irin motocin da muka gani a harabar gidanne yasa Naila ta cewa Kaka su juya, domin jikinta ya na bata wakilai ne daga wajen aikinsa na Babban Birnin Abyad. Sam Kaka ta nuna bata san zanceba ba, a cewar ta; "mu ina ruwanmu da su? mu da ba wajensu muka zo ba."

A living room ɗin farko idanuwan Naila suka sauka a kan mutumin da ta ke gani tamkar Malik, duk da ya sanya tabaran rage hasken ranar da ya sakaye idanuwansa, ga kuma tarin ƙasumbar da ya bari a fuskarsa. Sai mace ɗaya da take zaune a kujera daban itama Naila ta kasa gane ina ta santa ina ta taɓa ganinta kuma da wa take yi mata kama.

Kamar yadda Naila take Kallonsu bayan ta gaishesu haka Macen da ba wani shekaru bane da ita ta ƙuramata ido.
Kaka tunda ta gaishesu ta nufi cikin Gidan wajen ƙannen Yasar da suke wasa da dariya.

Namijin ne ya fara miƙewa gaba ɗayansa yana miƙawa Yasar hannu. Miƙewarsa ya sa ya fito sak a Malik ɗin da Naila take zargi, kallon da ta yi masa shekarun baya a gidan Abduh Dhahab yana shara da safiya ya ƙara dawowa idanunta. Zumbur ta miƙe tana kallonsa kamar zata cinyesa, kafin ta ambaci sunansa mahaifiyar Yasar da take ganin girmansu a matsayin su na Manyan Iyayen Gidan ɗanta ta ja hannun Naila ta zaunar da ni a gefenta, a tunaninta ciwon jinnun da Kaka tace ta yi ne ya ƙara dawowa. Da harshen ƙasar Abyad take ba su haƙurin Naila ba ta da lafiya ne.

Macen ce ta amsa mata amma Namijin fita ya yi. Itama Macen miƙewa tayi Zinaren da ta yi ado da shi na walwali a kunnenta da wuyarta.

Har mota Mahaifiyar Yasar da Yasar suka yi musu rakiya, har lokacin Naila tama zaune kamar an dasata.

Bayan sun dawo Yasar yake tambayar Naila n
Ta san su ne? Naila yasan ko tayi masa bayani ba lallai ya yarda da ita ba don haka ta ce mai "a'a." Har suka bar gidan bata saki jikinta ba, duk Yasar yana ankare da ni.

Rashin walwala da yadda Makka take haÉ—e rai bayan sun koma Gida yasa Kaka ta ce ta zo ta rakata su siyo abu, Yasar ya bata kuÉ—i.

Waccen wajen Siyayyar da ta taɓa haɗuwa da Sufyan ta ce suje. Ƙananun kayan CK da Yasar yake yawan siyomata ta sanya sai malulluɓi mai girman da ta nannaɗe har rabin fuskata da shi gudun haɗuwa da Sufyan, ko Sumaya.

Bayan isarsu
Su na cikin siyayya idanuwanta suka faÉ—a kansa da jami'ai biyu a bayansa, wannan dai mutumin da na gani a Gidan su Yasar da rana ne.

Ya na fita ta rufamai baya da hanzari ba tare da ta saurari Kaka da ke tambayar "Naila ina zaki je?"

Yana ƙoƙarin zura gangar jikinsa a Mota Naila ta ƙaraso ɗan nesa da Motar da Gudu, cikin ɗan ɗaga murya ta ce "Malik, dan Allah idan kaine ka tsaya na roƙeƙa"...✍🏻

Duk mai son Ɗaukar Malik haya a Yankinsu tayimin DM saboda irin su Sartaj😂😂 I came in peace ☹️
[7/31, 10:04 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥

NAFISA ALIYU SASAAL

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.