Zinare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zinare Book 1.txt
Chapter 10 of 13
Page 27
Bayan sun yi sallama Naila ta katse wayar, rungume kaka ta yi, ta sumbaci ƙuncinta tana dariya. Kai Kaka ta girgiza jikinta a sanyaye.
Kamar Naila bata lura da sanyi da jikin Kaka ya yi ba ta É—auko waya ina kiran layin Yasar.
Da tsananin farin ciki Naila ta basa labari.
"Alhamdulillah!" ya furta da daukakkiyar sauti kafin yafara tsokanarta da "Finally yokel sister ta zata leƙa Babban Birnin Abyad, har na hango idanuwanki wallahi" Kaka da ke sauraronsu dariya tasa haɗe da sakin ajjiyar zuciya.
Da tsokana Naila suka ƙare waya da Yasar.
Da yammaci Kaka Mallam ta kira, ta yi tsammanin zai soki zuwansu Babban Birnin Abyad amma sai taji ya furta "Alhamdulillah" ƙwarin gwiwa da addu'o'in tsari kala-kala ya ƙara bata domin acewarsa; abinda zaiyi sanadin zuwan Naila Babban Birnin Abyad ya daɗe ya na jira kuma gashi Allah ya kawo.
Kafatanin kuÉ—in da Naila take tarawa A banki ta turawa account É—in mutanen Yankin Tudu.
Kafin dare ya yi kiraye-kirayen su sai shigowa yake yi, abun dariyar duk da wayan mutum biyu ake wayan, talauci ya hana da yawansu mallakar wayoyin hannu.
Kaka bakinta kamar zai yage, banda "Ameen Ya Allah! Ameen thumma Ameen!" Babu abinda take maimatawa. Ba su daina kira suna Godiya da addu'o'i ba har sai da chajin wayar ya ƙare.
A jiyar zuciya Kaka ta sauke, lokaci zuwa lokaci sai ta saki murmushin farin ciki. Kusa da ita Naila ta matso taa zauna ta ce ;
"ya ya zakiji idan akace mutanen Yankin mu, sun samu farin cikin da ya fi wannan?"
"Zan ji daÉ—i Naila sama da wanda na ji a yanzu" Kaka ta faÉ—a da murmushi kwance a saman fuskarta.
"To ki saki ranki mu shiga Babban Birnin Abyad, In Shaa Allah ba zamu dawo ba sai da nasarar da zai kawowa Yankinmu gagarumin sauyi." Murmushi suka sakarwa juna.
Da yake Yasar ya zo hutun ƙarshen Mako Gida, ziyarar bazata shi da ƴan gidansu suka kai Gidansu Naila don tayata murna.
Kaka baki ta saki da ta ji abinda ya kawosu kafin da kwashe da dariya ta na cewa "wai ni kuyimin bayani wani irin arziƙi Naila zata samo a wannan Babban Birnin Abyad ɗin da kowa yake farin ciki, kar fa muje a siyar da mu" Dariya Yasar da Iyayensa suka kwashe da shi, ƙannensa da suka saba wasa da dariya su na tsokanarta.
Cikin raha Yasar yake bawa Kaka labarin da zarar ta shiga Babban Birnin Abyad zatasan ko wanda ya yi wanke-wanken rana É—aya dole ya fito da kuÉ—i mai tsoka.
Ana raha da wasa mukayi Dinner da su Yasar.
Sai dare sosai suka tafi Gida.
★washe gari su Naila suka fara kimtsa kayan da zasuyi tafiya da shi, amma har lokacin abinda yake bawa Naila mamaki shine tayaya za'ace zuwansu na kwana biyu ne zai warware ƙullin shekaru aru-arun da ko Kakanta ba haifa ba lokacin, ko dai ta Kaka kashesu za'ayi.
★washe gari daya kamar ranar tafiyarsu, tsaf Naila ta shirya cikin baƙin Abaya haka Kaka irin Abaya ɗaya suka sanya na Company ɗaya.
Har Gida ƙanin Yasar ya zo ya ɗaukesu saboda tare zasu wuce da Yasar don haka sai sun fara biyawa Gidansu tukunna
A dai-dai lokacin da Motarsu Naila ta gifta ta hangi Sufyan A cikin Motar da take kyautata zaton Taxi ne. Mamakin abinda ya kawoshi ta yi cikin daƙiƙu kafin na tattara lamarinsa na watsar tana danna wayarta.
SUFYAN.
Ƙwallane ya tararwa manyan idanuwansa da suka ƙara zama farare ƙal lokacin da mai gadi ya tabbatar masa da su Naila sun fita yanzunan ita da Kakarta. Yasan kuma ba Makaranta ta je ba, domin can ya fara biyawa akace sunyi hutu, a hankali ya nemi waje ya zauna ya zaro wayarsa. Bugu ɗaya Hindu ta ɗauka.
Ko sallamarsa Hindu bata amsa ba ta ce;
"Ka riski Naila?"
Jiki a sanyaye ya ce; " a'a"
Kuka ta saki na tsayin mintuna shida kafin ta É—ora da;
"Son zuciya shine mafarin halakata, bayan tafiyarka muka gano ka yardar da maganin makarin asirin jikin Naila a gidansu kamar yadda Malamin Yankinmu ya sanar mana, maimakon Jalal da Mahaifinka su ga laifinka, sai suka juye laifin akaina, acewarsu duk nina tsiro musu da wannan musibar, sun tisani a gaba da asiri kala-kala kullum cikin ciwo nake, na je wajen Mahaifiyata ÆŠayyib ya zugeta ta koroni.
Sufyan mafita ɗaya ya ragemaka, ka koma bakin aikinta ka riƙi aikinka da gaskiya da amana, amma a kowani yanayi ka ji tsoron Allah kuma kaji tsoron Malik, domin baya ganinka ba kuma ya tare dakai amma ka sani yana saurararka a duk inda kake a Babban Birnin Abyad kamar yadda malamin duba ya sanarmin, a yanzu amfaninka a wajen Ɗayyib shine ka bincikomai su wanene DHAHAB? banda wannan baka da wani amfani a gareshi, su kuma su Malik suna tare da kai ne domin ganin iya gudun ruwan Jalal, kamar taku ɗaya haka kake da mutuwarka Sufyan a tsakanin Ɗayyib da su Malik, amma abinda na faɗawa Ɗayyib ya hukuntani shine wanɗanda suka ƙirƙiri sabon Dhahab ba abokanan yaƙar su ba ne, saboda suna da damar shafe Yankin Tudu da mutanen cikinta, domin ko kai kanka da kake cikin Daularsu har yanzu mai asalin Dhahab ɗin bai san dakai ba, wataƙila da ya sani da tuni ka jima da ruɓe a cikin ƙarƙashin ƙasa. Ina gayamaka dukka wannan ne domin kayi takatsantsan kamar yadda malamin duba ya sanar da ni, ina nadama Sufyan, ka yafemin. Ba lallai mu sake magana makamanciyar wannan da kai ba, ba kuma lallai ka dawo ka riskeni a raye ba, amma Allah Ne shaida bani da masaniyar komai a kan kisan su Abduh da ahalinsa." Ɗif wayar Hindu ya katse kamar dai waccen ranar.
Wayar Sufyan ya bi da kallo yana zare idanuwansa da suka koma jajaye cikin ƙarajin da ya tashi dukka jijiyoyin wuyarsa da goshinsa ya na furta "Ummee! Ummee!! Ummee!!!" A lokaci ɗaya yana ƙara kiran layinta da baya shiga kwata-kwata. Hankali a tashe Mai gadin gidansu Naila ya kiran layin agajin ƙasar. Kafin su iso Sufyan ya zube ƙasa idanuwansa a juye.
NAILA.
Wannan hanyar da take bi da kallo tsayin shekaru yau gashi zata tunkareshi da ƙarfin ikon Allah.
In Shaa Allah anan Free pages É—in ZINARE ya tsaya. Ga waÉ—anda suka bibiya ba su da halin biya na gode da comments da addu'o'in ku, ga waÉ—anda suke da wadatar biya suma ina godiya mai tarin yawa Allah Ya bar zumunci.
KuÉ—in motar zuwa Babban Birnin Abyad Naira 500 ne kacal, ta wannan account É—in
Nafisat Aliyu Muhammad First Bank 3207955182 tare da tura shaidar biya ta 09132403788,08138665117. Ga masu bibiya kuma ta Arewabooks sai su ɗora. In Shaa Allah zamu cigaba da Posting ranar Monday, 4, August, 2025 da misalin ƙarfe 8:00pm
Na godeðŸ™ðŸ»
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
ZINARE.
2
BY
NAFISAT ALIYU SASAAL
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.