Zinare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zinare Book 1.txt
Chapter 2 of 13
*CHAPTER 2*
*TAFIYAR NAILA DA SUFYAN BABBAN BIRNIN ABYAD*
Pg 10
NAILA;
A dai-dai lokacin da mutanen Yankin su ke ji inama da su ne zasu tafi Babban Birnin Abyad Naila na maƙale da Kakarta ranta ba daɗi.
Gabannin sallar magrib Malamin da ya ke yiwa Kaka rubutu ya aiko da shi.
Kaka da ke cikin matsanancin damuwa saboda abubuwa ma su muhimmancin da takeson sanarwa Naila amma babu hali laƙwas tayi idonta ƙyam a kan dogayen yatsun Naila da ke juyemata rubutu a kofi.
Kanta Naila ta kamo bata saketa ba har sai da ta gama sha. Yunƙurawa tayi ta miƙe, sai dai ko taku ɗaya ba ta yi ba ta ji Muryar Kaka na ambaton sunanta
"Naila"
Da sauri ta juyo cikin mamaki kafin ta rungumeta da ƙarfi haɗe da kai mata sumba a gefe da gefe ƙuncinta. Da tsananin farin ciki ta ce;
" na ji daɗi sosai Kaka fargaba da komai ya gushe da ga gareni tunda ga shi kin faɗi sunana sosai Allah Ya cigaba da karemin ke Kaka" Kaka da tsananin farin ciki ta amsa da "Amin" sai dai bayan amsawarta ƙwallane ya cika idanuwanta da su ƙyam a kan Naila.
Ta yunƙura zatayi magana Naila ta dakatar da ita, ta hanyar girgiza mata kai. Amma duk da haka bayan wasu daƙiƙu sai da ta numfasa cikin karyewar zuciya ta fara magana;
"Kafiyata da nuna ikona ba za su yi tasiri a garemu ba, tunda tun kafin muje ko ina Hindu ta fito mana da manufarta ƙarara. Amma Allah Ba ya barci Naila, da ƙarfin mulkinSa zuwanki ƙasar Abyad babban nasara ne a gareki, makircinsu shine matakin nasararki In Shaa Allahu."
maganganun Kaka sun ƙarawa Naila ƙwarin gwiwa a kan wanda take da shi, har tanajin zata jurewa duk wasu ƙalubale da zasu biyo bayan zaman auren su da Sufyan.
A haka suka raba wannan dare su na hira saboda washe gari Naila za ta bar Gidan, mafi rinjayen hirar ta su a kan Tufar da Hindu ta ciyar da Kaka ne da kuma shawarwari da dabarun zaman Gidan Miji.
★washe gari da sassafe Dangin Mahaifin Naila su ka zo ɗaukarta, saboda sunfi son a zo ɗaukarta a inda su ka tsara. Kaka bata tanka ba sai rungume Naila da ta yi bayan ta sumbaci goshinta. Cikin ƙarfin halin danne kukan da ta ke yi ta ce; "Ki kula Naila, inanan ina jiran dawowarki wata rana da dumbin nasarar da zaki zamemin abin alfahari da Mutanen Yankinki gaba ɗaya, ki mayar da hankali kan sana'arki saboda sana'ar kitso baiwane mai girma a ƙasar Abyad. Daga ƙarshe ki tuna da shawarwarina, haƙuri, juriya da biyayya sune matakan nasararki" daga haka Kaka ta saki hannun Naila da ke kuka kamar zata shiɗe.
Barin Gidan Kaka zuwa Gidan ƙannen Mahaifinta ya tabbatarmata da ta bar Gidan Kaka kenan sai kuma wata rana idan da rai da lafiya. Bayan sun kai can zagaye ta su ka yi kowannen su na faɗar albarkacin bakinsa da sunan nasiha.
Ba bu nisihar Kawunnanta ɗaya da ya shigeta saboda kallon maƙiya ta ke yi mu su, kamar yadda su ka nunamata ƙiyayya a zahiri.
Ba ya tabbatar da ita cikakkiyar Marainiya ba ce, sai da dangin Mahaifinta su ka miƙata Masarautar Yankin Tudu. Sufyan ya na zaune a tsakankanin Iyayensa, wannan ya tunamata da nata Iyayen dalilin haka sai kukanta ya ƙaru, takaicin yadda ƴan uwan Mahaifinta su ka dinga ƙasƙantar da kansu duk don samun wajen zama a wajen Ɗayyib kamar ya kasheta.
A ranar ta zagaya Masarautar Yankin Tudu ta kuma tabbatar da kyansa da mutane su ke zuzutawa, har gaban Sarki Hammam sai da ta kai gaisuwa. Bayannan aka miƙata ɓangaren da zata kwana.
Bata shafe hour biyu da kwanciya ba Matasan mata ma su kusan shekaruna su ka shigo, da alama turosu akayi don tayata kwana. Ba su san ba barci ta ke yi ba su ka fara hira.
Cikin jimami É—aya ta ce;
"Ai ni na jiyo abinda yafi ƙarfina, ni dama na yi zargin Uwar gida Hindu bazata taɓa yarda wannan makirin ɗan nata ya auri ƴar ƙaramin Gidan da su ke talakawan fitik ba sai da wata manufa"
Cikin rashin yarda ɗayar ta ce "Ni kam sam na kasa yarda da zancenki Ƙawata, ta ya ya zata sadaukar da dukiyarsu da ake zuzutawa a kan abinda ba ta da tabbaci a kai, anya kuwa kin jiyota da dakyau?"
"Wallahi tsaf na jiyota, ke harda sharaɗi ta ce ta kafamai, karya kuskura ya kusanci Matar kar a haifo mu su ƙasƙantaccen jika, ya bari su ga kalar ɗaukakar da zai samu."
Naila tana jin su suka kwashe da dariya haɗe da tafawa, kafin ɗayar ta ƙara cewa;
"To wallahi ki adana wannan dogon bakin naki idan ba haka ba shi zai kai ki ya baro kin ji na gayamiki."
Da sauri ta damƙi bakin na ta kafin ta saki su ƙara kwashewa da dariya.
Daga kwancen da Naila take jikinta ya fara rawa, gumi da zazzaɓi su ka lulluɓeta lokaci ɗaya. Kuka mara sauti mai fitowa tun daga ƙasar zuciya na zuwar mata, ƙwarin gwiwarta na bin iska. Ta ɗauki lokaci tana kuka mara sauti kafin wahalallen barci ya fara ɗaukarta, har barci ya ƙarasa ɗauketa ba su daina tattaunawa ɓoyayyun sirrinkan da su ka shafi Masarautar ba.
★washe gari da ta farka da su tayi tozali su na barcinsu hankali kwance, daga yanayin suturun jikinsu ta gane ba Bayi bane Ƴaƴan Gida ne.
Shagali na musamman aka ƙara shiryawa kafin tafiyarsu Ƙasat Abyad.
Faɗa sosai Jalal kakan Sufyan da Mahaifinsa Ɗayyib su ka yimata. A ɓangaren Mahaifiyar Sufyan Hindu faɗar hannunka mai sanda tayimata mai surke da baƙaƙen maganganun da ke nuna ba Mata ta aurawa Sufyan ba Baiwa ta auramai. A gabanta ta ƙara jaddadawa Sufyan Umarninta, wanda bata raba ɗayan biyu akan hirar da taji ƴammatan jiya su na yi ne. Ba bu wani mai faɗa aji a Masarautar Yankin Tudu da baiyimata nasiha ba, wa su na su nasihar ta lallami suka yi mata wa su kuma gori da nuna iyaka ne kai tsaye.
Daga haka Drivern da zai kaisu iyakar Yankin Tudun da zasu hau Motar ƙasar Abyad ya ƙaraso. Sufyan da ke sanye cikin tsadadden farin yadi mai taushi, malalacin murmushin da ke nuna jin kanshi ya saki haɗe da ɗagawa Mutanen Yankin da su ka yi kirco-kirco su na washe baki hannu.
Idanuwansa a kan Mahaifiyarsa suka tsaya daga ƙarshe, alamar jinjina ya yi mata kafin ya shigo Mota ya na gyara zamansa a gefen da Naila ta ke.
Da sannu da sannu motarsu ta fara motsawa har lokacin mutanen Yankin na ɗaga musu hannu, kukan da Naila take ɓoyewa ya bayyana saboda tuna Mahaifana da Kakata da na san tana can tana kuka.
Naila ta bar Yankin Tudu da tarin rauni da tabo a cikin zuciyarta, ko yaya zamanta a ƙasar Abyad zai kasance??
Kuyi manage
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: .🔥ZINARE🔥
SASAAL
11
Duk kukan da Naila ta ke yi, Sufyan ya na jinta amma bai ce kanzil ba. Sai da ya fuskanci ba kukan ganin ido ba ne na gaske ne, sannan cikin isa da izzar fitarshi zakka a kaf faɗin ahalinsa saboda samun nasarar tafiya ƙasar Abyad yin karatu ya ce;
"Kukan na menene? Kinsan ina zakije kuwa? Dan Allah karki ɓatamin farin cikina, ke da ma baki da Iyaye, ko ni da na ke da Iyaye a raye bandamu sai ke. Kar ki bari tun kafin tafiyarmu ta yi nisa ki fara saɓawa umarni na kinji na gayamiki" da ga haka ya ɗora farin yatsun hannunsa da bai san wahalar komai ba a saman dogayen yatsun Naila.
Maganganunq sun soketa irin sukar da Marainiya ƴar uwa ta ce kawai za ta san zafin su, saboda ƙara jaddada matan da ya yi da gaske bata da Iyaye don haka bata da abin yiwa kuka.
Bata ƙara ko da tari ba sai idanuwanta da ta lumshe tana jin yadda Drivern Motar su ya ke kwarara gudu.
A tashar da zasu hau Motar da zai yi tafiyar kwanaki kafin isarsu ƙasar Abyad Drivern da ya ɗaukosu ya sauke su. Hannun Sufyan maƙale da nata, ya je ya siyamusu tikiti, suka shiga ƙaton Mota mai ɗaukar fasinja da yawa zuwa ƙasar Abyad.
Ba su jima a ciki ba bayan sunci abinci, aka fara sanarwa tashin motar da komai na cikinsa ya ke kamar na jirgin Sama.
A gefen Sufyan ta ke zauna, kamar zai sumbaceta haka ya sunkuyo da sunan ɗauramata belt. Bayan ya ɗauramata ya ƙara kamo hannunta ya sarƙewa da na shi.
Murmushi mai ciwo ta saki a cikin zuciyarta, tana ganin ba lallai Sufyan ya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa Mahaifiyarsa ba.
Tafiyar su bana yini da kwana ba ne tafiyar kwanaki ne, saboda da su Sufyan hamshaƙan ma su arziƙine da jirgin sama za su biya masu ba mota ba. Duk inda zasu tsaya ba bu magana a tsakaninta da Sufyan sai kayan guzurin da Mahaifiyarsa ta zubamai a ƙaramin Akwati mu ke ci akai-akai.
```BIRNIN ABYAD```
Lokacin da Motarsu ta iso Birnin Abyad, yanayin sanyin ƙasar, hasken Mutanen ciki, gina-ginensu, da wasu irin motoci ma su kyan gani a ido da kwaɗayin son shigarsu ne su ka haske mudu idanuwa.
Idanuwan Naila da ta ke jinsu kamar madara saboda haske a Yankinsu sai ta ke jin su a Birnin Abyad kamar sun koma jajaye saboda kyawun mutanen Birnin da take gani da gine-ginen su. Sai ta ke hasaso Yankinsu kamar wani kusurgumin daji mai duhu da ya ke da ƙaracin kayan more rayuwa. Fatarsu da na ke ganinsa mai haske da kyau a Yankinsu a take ya dusashe a idanuwanta ya koma sak na ƴan karkara, ƴan karkarar ma su ƙarancin komai na cigaban rayuwa.
A maganganunsu ta fuskanci ba sa kai ƙarshen zance sai sun haɗa da harshen nasarar da Malaminsu yake ta kwaɗaitar da su, su koya.
Wa sun su kuma nasarar kawai su ke yi babu sirki.
Tunano yadda Mutanen Yankin Tudu su ka dinga ɗago musi hannu lokacin tahowarsu sai tausayin su ya ƙara tsargamata musamman Kakarta da Mahaifanta.
Mahaifinta ya ƙare rayuwarsa a dinki ƙarshe rashin gatan Asibiti ya yi sanadiyar ajalinsa, haka Mahaifiyarta. Kakarta ce dai ba ta cire rai tare da Yaƙini haɗe da fatan wata rana ta zo taga duniyar Birnin Abyad ba.
A ɓangaren Sufyan shima ji ya yi duk ya muzanta, wannan jiji da kan da sumarsa da ya tara duk domin ya zo ya Yaƙi Ƴammatan Birnin Abyad sai ya bi ruwa, ya na jin inama da yana da hula a kusa ya lulluɓe gashin saboda Kunya. Farin fatar da ya ke yiwa Mutanen Yankin Tudu yanga da shi sai ya ga ashe da sauransa, Kananun kayan da idan ya sa a Yankinsu maza da mata su ke bi su na kallo har da tuntuɓe sai ya tashi kamar na ƴan Karkara.
Lambar wayar wanda zai kai su gidan da Iyayen Sufyan su ka kama musu ya zaro a ƴar ƙaramar jakar da ya ɗauko ya na yanga da shi a Yankin Tudu saɓanin isowar su Birnin Abyad da ya ɓoyeshi a hammata.
Cikin ƙarfin hali ya tambaya aka nunamai wajen kira. Shi kanshi sakayayyen wajen kiran da aka sakaye da gilashi abin a yaba ne.
Naila Nutsuwar ya ne ya ta taimaka wajen sakaya gidadancinta, saɓanin Sufyan da dama can ba wani cikakken nutsuwa ce da shi ba, dan dole ya ƙaƙabawa kanshi nutsuwar dole kamar ba Sufyan Ɗan gidan Ɗayyib shugaban kasuwar Tukwanen Zinare ba😂.
Ba su wani jima ba, Uban gidan ÆŠayyib mazaunin Birnin Abyad ya zo É—aukarsu.
Sai da suka tashi hawa Motar inda zamu je Makka ta fahimci ABYAD sunan ƙasar ne Birnin Abyad kuma shine inda aka sauke su kuma anan Mahaifan Sufyan su ka kama Gida, BABBAN BIRNIN ABYAD kuma shine asalin Babban Birnin da kaf faɗin ƙasar ba bu kamar shi.
To idan har Babban Birnin Abyad da take ji a bakin Mutanen Yankin Tudu ya fi inda suke ciki kyau da tsari to ya ya kyansa da mutanen cikina za su kasance??? Naila ta tamabayi kanta, lokacin da suka isa inda zasu shiga Mota.
Bayan sun shiga motar da za ta kai su Gidan da aka kama musu, idanuwanta su ka faɗa kan Motocin da akace su ne masu shiga Babban Birnin Abyad, ko da batayi karatu mai zurfi ba, bata kuma saba riƙe kuɗi ma su nauyi ba tasan ba motocin shigar mutane ne irinsu ba.
Tafiyar Motocin take kallo tana jin kamar ta fito ta bi su. Sai ta ke jin kamar tana ƙewar abinda ita kanta batasan menene a inda za su je ba, tana kallon tafiyar motocin wani yanayi na tsarga zuciyarta, haka ta yi taji har Motocin suka ɓacewa ganinta.
Kasa jurewa ta yi ta tambayi wanda ya zo É—aukarsu; " hour nawa ne tsakanin Birnin Abyad da Babban Birnin Abyad"
Amsar "hour biyar" ya ba ta tare da shaidamata mutum zai iya zuwa a ranar ya dawo a ranar. Sufyan da ya ke tunanin ta yi tambayar ne domin ta nuna Iyayensa ƙarya suke yi, da su ka ce sun kama mai Gida a Babban Birnin Abyad harara ya watsomata ya na cije baki.
Unguwar su da Gidan da aka kama musu abun a yaba ne, duk da ba ta jin komai akan Sufyan na soyayya ko makamancin haka sai da ta ji ya ɗan birgeta, saboda gida ne da bata taɓa mafarkin zata kwana a cikin irinsa ba har ƙarshen rayuwata.
SUFYAN;
Da Sufyan ya yi tozali da living room da two Bedrooms ɗin da su ka sha kayan ado dai-dai misali a matsayin hidimar da Mahaifansa su ka yi mai sai ya ji kwaɗayin son karya alƙawarin Mahaifiyarsa akan Naila na bin iska daga gangar jikinsa.
Da farko kafin tahowar su ya yi zargin ashe dukiyar da ake zuzutawa Kakansa na wajen Uwa ya mutu ya bari duk ƙaryane, banda ƙarya ne tayaya za'ace da dukka wannan dukiyar da wanda Mahaifinsa ya samo akayi hidimar kamamai Gida ba ma Siyamai ba da biya masa Makaranta a Birnin Abyad? Sai da ya gani da idonsa sannan ya tabbatar da dagaske ba ƙananun dukiya ba ne za su zaunar da mutum a unguwar da aka kama mu su Gida ba.( a nasa ganin kenan, domin a wajen masu zuzurutun dukiya, gadon da ake taƙamar Hindu tana da shi, bai wuce kuɗin kashewar mai arziƙi a yini biyu ba).
Idan har Mahaifiyarsa za ta yi irin wannan sadaukarwa saboda É—aukakarsa ba tare da damuwar komai ba, to ba bu abinda zai hana shima ya sadaukar mata da na sa farin cikin.
Amma duk da haka dole ya rage zafi, domin ba zai iya kwana É—aki É—aya da Naila ya tashi da ita ba tare da ya rage zafi ba.
Gidan ba su su ƙadai ba ne, mutum huɗu ne a Gidan amma kowa rayuwarsa yake yi, ba tare da damuwa da rayuwar Ɗan uwansa ba.
NAILA;
wanka ta yi ta ƙimtsa jikina. Sai a lokacin taga kamar ta ɗanyi kyan gani, saboda dattin Motar da ta wanke daga jikina. Ɗakin da Sufyan ya bata a matsayin nata take ƙarewa kallo, nutsuwa na saukarmata.
Cikin baƙaƙen Abayoyin da ta taho da su masu adon saƙi ta shirya ta tayar da Sallah ta inda ta ga an shimfiɗa abun Sallah alamun nan ne gabas.
Bayan awannin;
Uban gidan Ɗayyib ya hidimta musi ƙwarai da jikinsa da lokacinsa har ma da kuɗin aljihunsa. Abinci mai daɗin da basu taɓa ci ba ya siyomusu Da Suturar sawa kala biyu da ya siyo Sufyan don fara zuwa Makaranta sai wayar hannu da layi a ciki shima mai kyau dai-dai misali.
A kunyace Sufyan ya sa hannu ya karɓa ya na ƙara tabbatar da ashe ba shi kaɗai bane ya raina kayan jikinsa ba dagaske kyan ne ba su da shi.
Da yake saukar Safiya suka yi bayan sunci abinci, Uban gidan ÆŠayyib ya yi mu su Sallama da sunan washe gari zai dawo.
Barci ya kwashe kowannensu a É—akin da ya ke.
Ba su farka ba sai azahar shima babu wanda ya fito a cikin su tunda kowanne da abinci da zai ci a na dakin. Sai wajen ƙarfe 9 da ƴan mintina na dare Sufyan ya shigo ɗakin Nsila.
Gaisheshi ta yi ta ƙara gyara lulluɓin kanta.
Wayo da kuma shekarun da Sufyan ya fita yasa ya fara goge maganganun ƴan matan da ta ji a Masarsutar Yankin Tudu. Da farko kusa da ta ya matso ya zauna saboda ya lura kamar ta na da sani ko hasashe a kan abinda ya ke ranshi. Cikin taushin lafazin da lumshe idanuwansa da su ke tsaye ƙyam a kan fuskarta ya ce;
"Na san surutai da yawa za su yi ta zuwa kunnenki Naila, amma iyakacin wannan Gidan da kuɗin motar da Iyayena suka kashe mana ya kamata ace kin watsar da surutun auren manufa akayimana da ke, Mahaifiyata Mace ce mafaɗaciya kuma tana tsananin so na wannan dalilin yasa ta kuɗiri niyyar auramin matar da zata bauta min kamar Sarki da Baiwarsa, amma kisani Naila har cikin raina ban zaɓe ki domin kisha wahala a Gidana ba, sai domin muyi zaman aure ki bani goyon baya ɗari bisa ɗari akan karatu na. Mun zo nan ga shi kuma kuɗin Mahaifana ya ƙare a wannan hidimar da suka yimana, kuma a halin yanzu ina buƙatar suturun sawa kuɗin hidindimun makaranta da kuma abinda zamu ci Naila."
Naila da batasan sanda ta É—ago kanta ba, idanu ta zubamai domin sam bata fahimci ina ya dosa ba.
Fahimtar hakan ya sa ya cigaba da magana cikin ƙaramin sauti.
"Naila da Baiwarki zaki taimakamin Ni kuma na yi alƙawarin mayar da ke mace ƴar gata a cikin ƴan uwanki Mata."
Still Naila bata fahimci ina ya dosa ba don haka ta ƙara gyara zama.
Da kame-kame ya ce "ina so ki bi dukka Gidajen Unguwarnan ki sanar da su kina kitso, a kwai ma su ra'ayin kitso a cikin su, da wannan kaɗai zaki taimakamin Naila na roƙeki"
Dan jim Naila ta yi maganganun Kaka na dawo mata "ki mayar da hankali kan sana'arki saboda sana'ar kitso baiwane mai girma a ƙasar Abyad."
Cikin yarda da rauni irina Æ´a mace Naila ta É—aga kai alamar ta gamsu ko dan Kaka tayi alfahari da ita.
Da sauri Sufyan ya rungumeta kafin ya yi dabarar ragewa kanshi zafi, Bayan wani É—an lokaci ya tattara ya bar É—akin.
NAILA;
Da murmushin raɗaɗin da marata yakemin na mirgina na kwanta, abinda Sufyan bai sani ba zuciyata Macacciyace ba bu rai balle a yaudareta, da sha'awa yana da yare da ko ya taɓani baza ta ji komai ba sai dai bani da ikon hakan.
"Idan Æ™arya yakemin domin ya zalunci ne Allah Shi ne gatana," daga wannan hirar zucin Barci mai nauyi ya É—auketa...âœðŸ»
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c
🔥ZINARE🔥
SASAAL
12
★washe gari bayan nta yi sallar Asubahi bata koma barci ba, har sai da gari ya yi haske.
Barcinta bai yi nisa ba, Sufyan ya tasheta. Da kayan da aka siyomai jiya ya yi ado, ya yi kyau dai-dai misali domin baza ta ce sosai ba, a matsayinsa na Mazaunin Birnin Abyad. Bayan ta gaishesa ya ji bataƙara da komai ba sai ya haɗe rai ya na ƙara shafa wuyar Rigarshi.
Sam bata fahimci ina ya dosa ba, sai da ya yi tsaki haÉ—e da faÉ—in;
" Anya kuwa Naila ki na da lafiyar ido, na san babu Macen da za ta ce banyimata ba, amma ke kullum sai ki dinga nuna kamar Ni ɗin ba wani mai kyau ba ne, ko Hassada ki ke yimin?" ya tambaya da iya gaskiyarsa haɗe da murza zoben silver da ya ke matuƙar ji da shi.
Dariya ƙeta musamman a kan mugunta ba halinta ba ne, amma da ta ƙaremai kallo na tuna irin siffar Mutanen da suka gani a lokacin da suka iso Birnin Abyad sai da ta dara har jerarrun haƙwarana su ka bayyana. Tunda ta ke bata taɓa ganin Namiji mai son ace mai ya na da kyau ba irin Sufyan domin ko Mace albarka, "shi kuma kalar jarabawarsa kenan." Ta faɗa a cikin ranta amma a zahiri miƙewa ta yi kafaɗunsu na gogar na juna ta ce;
"Kai kyakkyawane ko ba ka yi kwalliya ba, balle yanzu da kayi ado da kayan da aka siya a Birnin Abyad, Godiya ta tabbata ga Ubangijin halittun da ya halicci Namiji kyakkyawa irinka Mijina."
Dariya da bata taɓa gani ya yi irinsa ba ya saki, ya na kamo fuskarta, sumba ya saukemata a goshi tsabar daɗin da yake ji har wani lumshe ido yake yi yana binata da kallo kamar zai lasheta.
Sallama ya yi mata, Har ya fita ya ƙara dawowa ya na jaddadamata alƙawarin da ta yi mai.
Bayanshi ta bi da kallo maganar Kaka na faɗomata; " ko wani Namiji da kalar halinsa, halin Mijin wata ba zai taɓa zama irin naki halin Mijin ba, dole a samu banbanci duk ƙanƙantarsa, don haka ki karanci halayyar Mijinki saboda samun sauƙin zama da shi." Ta gazgata zancen Kaka a kan Sufyan saboda duk daɗin soyayya ko kwalliyar da Mace za tayi domin ta ja ra'ayinsa ba ya ɗaɗashi da ƙasa a kan ta zauna ta na zuzuta kyansa da yaba kwalliyarsa sama da kyan da ya yi.
Kamar yadda nta alƙawartawa Sufyan da maƙotansu da su ke cikin gida ɗaya ta fara, ba ta jin turancin arziƙi amma kuma hakan bazai daƙusar da ƙudirinta ba. Ko da kwatacce ne da haɗe-haɗen iya wanda ta iya zata yi mu su bayani har su fahimta.
Biyun dukka Mata ne kuma tayi sa'a dukkansu gashinsu na kitsawa ne amma ɗaya kai tsaye ta shaidamata bata da ra'ayin yin kitso saboda zafi ya ke mata. Cikin ƙanƙan da kai kamar ta saba da ita ta kwantantamata ta zo ta gwada yimata hannuna ba shi da zafi. Ga mamakinta cikin raha ta ce to ta je around 2:00pm na dawo.
Abinda Ruwaida Maƙociyarta ta ce mata na ta je ta dawo ya ƙaramata ƙarfin gwiwar tunkarar ko ina domin tallata sana'arta. Mutum na ƙarshe a gidansu Namijine ɗan asalin ƙasar Abyad fatarsa fara fat.
Ta na shiga Sashensa Da sauri ta fito duk kiran da ya ke ƙwalamata bata juyo ba, tama jiyoshi ya na dariya da alamun mamakin Gidadancita ya ke yi.
Duk Gidan da zata shiga Daƙyar ake barinta, wasu su yimata tarba mai kyau wasu kuma su wulaƙantata. Gida na ƙarshe kuma mafi kyau a layin shi ta tunkara sai dai kai tsaye dakarun da su ke gadin Gidan su ka hanata Shiga.
A gajiye na dawo Gida, saboda ba laifi ta yawatu, ba kuma komai yasa ta dage ba, sai don sauya tunanin Sufyan daga wanda Mahaifiyarsa ta É—orashi a kai.
Kamar yadda Ruwaida ta ce ta dawo ƙarfe biyu haka ta koma akan lokaci.
Yanayin ɗiban kitson da yadda ya kwanta a saman farin tafin kan Ruwaida ya yi matuƙar ƙayatar da ita ga shi sam ba zafi, godiya tayimata da tsananin farin ciki a saman fuskarta.
Da Ruwaida ta tashi sallamarta, da iya adadin kuɗin a ke biyan makitsa a Birnin Abyad ta biyata, nutsuwarta ce kawai ta riƙe Naila.
A lissafin kuɗin da tayi zuwa na ƙasarsu, ko Iyalan Sarki Hammam da ake matuƙar ji da su, suke biyanta da kuɗi ma su ƙauri ba su taɓa bata kwatankwacinsa ba.
Ƙwalla ƙwance a ƙasan idanuwanta ta ke yiwa Ruwaida godiya.
Dariya Ruwaida ta saki cikin mamakin yadda Naila ta damu ta tambayeta daga ina take?
Saboda ta ƙara tausayamata ta naimomata customers, Naila ta fara ba ta labarin ita da Mijin tane su ka zo, ya zo Karatu ne kuma kuɗin iyayensu sun ƙare shine suke neman kuɗin cin abinci da sauran buƙatun rayuwa. Dafata Ruwaida tayi cikin tausayawa ta yimata alƙawarin zata naimo mata mutanen da zata dinga yi musu kitso ta na samun kuɗi amma na tambayi Mijina shin zai barta zuwa Gida-gida yin kitso?
Naila ba ta zaɓi yanke hukunci ba tare da ta tambayi Sufyan ba, don haka ta ce ta bari na yi shawara da shi idan ya dawo.
Daga haka dukayi sallama kuɗinta ma ƙanƙame a hannunta.
SUFYAN;
Lokacin da su ka isa Jami'ar Birnin Abyad da Ubangidan Ɗayyib ya yi cuku-cukun samo masa ya yi mamaki tare da ƙaƙabawa zuciyarsa cika alƙawarin Mahaifiyarsa babu gudu babu ja da baya.
Bayan sun gama yin komai. A ranar ƙarfe 12:00pm Sufyan ya fara ɗaukar lectures saboda tuni su ka fara ba bu shi.
Bayan sun gama lecture Harabar Makarantar ya fito ya naimi wajen zama, tunanin kuɗi da yadda zai yi kalar rayuwar da zai samu Mace wayayyiya ƴar Birnin Abyad ɗin da zai yaƙi mutanen Yankin Tudu da ita na ya zauna yi. Ya na cikin wannan yanayin wata matashiya mai kyan gaske ta raɓa gefenshi ta zauna. Sanye take cikin ƙaƙanun kayan Saint Laurent riga da wandon da suka amshi farin fatarta sai lulluɓin da ya lulluɓe iyakacin wuyarta bai sauko kafaɗunta ba.
"Barka dai kyakkyawan Matashi, sunana Sumaya, kai fa?" Ta faɗa da harshen nasara mai ɗauke da cikin wani irin sanyi murya tana miƙamai hannu.
"Kyakkyawan Matashin" da ta faɗa ya fi bugar da kan Sufyan a kan kyan fuskarta. A ƙiyastin da ya yi a cikin daƙiƙu zata yi sa'ar shekaru da shi, babu wani abu mai kyau a saman fuskarta da gangar jikinta da Naila da take cikin talauci bata da shi currently. sai wayewar da ta fi Naila da kuma hasken fatarta mai tsananin haske sosai.
Cikin salo da yadda ta birgesa har cikin ransa da jin nan take ya samu Abokiyar rayuwa ta zahiri matsawar ba ta fi ƙarfinsa ba ya ce;
" Barka dai ya ke kyakkyawa Sunana Sufyan na ji daɗin haɗuwa da ke" ya ƙarasa faɗa yana damƙar hannunta.
Daga haka kamar wasa hira mai cike da aji da zuzutawa kyansa irin yadda ya ke buri da ga Naila batayi ya ɓarke a tsakaninsu, har da musayar lambar waya.
Kan Sufyan bai ƙara ɗaukar zafi da kwaɗayin mallakar dukiya ba sai da yaga Sumaya har ɗan ƙaramin mashin mai kyau take da shi, ba irin na shi na Yankin Tudu ba.
Da aka tashesu Da sakin fuska ta yi masa tayin hawa, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗane.
A hirarrakin su kafin su isa Gida Sufyan ya fuskanci Sumaya ba wata Æ´ar ma su kuÉ—i ba ce a Birnin Abyad, naiman kuÉ—i ne ya kawo Mahaifanta har su ka haifeta a nan ta kuma yi dacen samun scholarship a Makarantarsu.
Ran Sufyan fari fes Sumaya ta saukeshi a layin Gidan su, kamar kar su rabu haka su ka yi sallama, Sufyan ya nufi hanyar Gate ɗinsu da ƙayataccen murmushi a saman fuskarsa.
NAILA;
Wanka ta yi taƙara shirya kanta cikin abayar ta dai mai adon saƙi, sai dai ba baƙi ba ne kamar ragowar. Ta na ƙoƙarin shiga kitchen don duba abinda zata iya dafawa daga Abinci da Ubangidan Ɗayyib ya kawo mu su, ta ji ana knocking. ƙofar ta nufa da saurinta, tana buɗewa taga ashe Ruwaida ce, kanta ba bu kallabi da alama bata da mu dashi ba duk da kasantuwarta cikakkiyar Musulma. Mazubin abinci mai kyau ta gani a hannunta. Cikin gwari-gwarin Turanci da zata fahimta Ruwaida ta shaidamata Abinci ta kawomata sannan gobe idan Mijinta ya amince ta shirya zata kaita wani Gida a ƙarshen layinsu da zan ta yi kitso. Godiya mai tarin yawa Naila ta yi mata sannan su ka yi sallama.
Bayan Naila ta koma ciki
Kasa taɓa abincin ta yi, ta zauna zamam jiran dawowar Sufyan su ci tare.
Sufyan;
Da murmushi a saman fuskarsa ya ƙwankwasa Naila ta buɗe mai ya shigo, yana ganinta ya kalli Abayar jikinta sai ya sauya fuska. Har cikin ranta bata kawo komai ba, sai ɗaukar da ta yi masa a matsayin bauɗaɗɗen mutum mai saurin fushi.
Fuska ba walwala ya amsa gaisuwata haɗe da sumbatar ƙuncinta kamar yadda al'adar Yankinsu ya ke.
Ruwan wanka ta nufi hanyar ɗakinsa domin haɗa mai ya dakatar da ita, ya miƙe ya shige har da mirzo mukulli, ita dai Na'ilah ba ta damu, ta dawo ta zauna
Bayan ya fito ta gabatar masa da Abincin da Ruwaida ta kawo musu, ba bu tambayar ina ta samo? Ta ci ko ba ta ci ba? Ya zauna ya take cikinsa sai kaÉ—an da ya ragemata. Jiki a sanyaye ta É—auka ta ci ranta babu daÉ—i.
Sufyan fahimtar sauyi a fuskar Naila yasa ya fara ƙorafin ai bai san bata ci ba, kuma maiyasa ma ba tasa hannu sunci tare ba? Batace mai komai ba, amma na ɗan ji sanyi a raina yadda ya nuna kulawarsa.
Bayan ta gama ci ta kai kwanukan madafi, ta fito da kuɗin da Ruwaida ta bata, da kuma naiman izininsa akan Gidan da ta ce zata kaita, ga mamakinta Sufyan ƙanƙameta ya yi yana dariyar nishaɗi, ba tare da wani jinkiri ba ya fara kasafta kuɗin.
"Naila kuɗinnan kawai abinda ya kamata shine na ƙara riga ko kala ɗayane ragowar kuma na samu na cin abinci a Makaranta Kinga yau ma da yunwa na wuni. Allah Ya yi miki albarka Naila" ya ƙarasa faɗa yana shafa duk inda hannunsa ya kai.
Tambayar izinin fitarta gobe da ta tambayesa murya na rawa ya ce ya amince ya na ƙara samata albarka.
Cikin dabara da girman zaluncin rashin tunanin halin da zan faɗa idan tasa buƙatar ta biya ya fara ragewa kanshi zafi, har sai da yaji ya gamsu dai-dai misali sannan ya tattara ya yi daƙinsa ya bar Naila a wajen.
SUFYAN;
Bayan ya shiga ɗakinsa wanka ya ƙarayi fuskar Sumaya da ya ke maƙalemai a cikin zuciyarsa na wasa da nutsuwarsa, sai ya ke ganin anya batafi Naila kyau ba? Dariya ya saki ya na lalubo wayarsa. Ba shi da kati kamar yadda ya sanar da Sumaya don haka ya zauna zaman jiran kiranta.
Kiranta ya na shigowa ya yi maza ya É—aga.
Sun jima su na hira kafin su yi sallama ran kowannen su fari fes.
Sumaya da Sufyan soyayyar da zai kai su ga aure sukewa junansu, duk da yinin su É—aya da haÉ—uwa.
Sumaya tana ganin ta samu Talaka irinta tunda Sufyan ya gayamata Karatu ya zo yi da Yarinyar da Mahaifansa su ka dage sai sun aura mai kar ya zo Birnin Abyad ya na neman Mata, idan ya so duk ranar da ya gama Karatu ya saketa idan kuma ya ji yana sonta to su cigaba da zamansu, shi kuma baya sonta ba kuma zai iya rayuwa da ita bayan ya gama Karatu ba. ÆŠari bisa ÆŠari Sumaya ta yarda da zancen Sufyan.
Shima Sufyan gani ya ke yi Sumaya itace Macen nunawa. Mace Æ´ar Birnin Abyad mai kyan sifa da tarin ilimi kuma ba Æ´ar talakawar fitik irin Naila ba.
Tabbas! Mahaifinsa ÆŠayyib zai yi alfahari da shi Kuma Tarihi zai maimaita kansa domin kamar yadda Marigayi Ubaidullahi Dhahab ya dawo Yankin Tudu da tarin dukiya da kuma zankaÉ—eÉ—iyar Matar Aure haka shima zai koma Yankin Tudu da tarin Dukiya da kuma Sumaya a matsayin Matarsa..âœðŸ»
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c
🔥ZINARE🔥
SASAAL
13
Har Dare ya yi Sufyan bai ƙara fitowa ba, dama ba wani damuwa ya yi da nemi Masallaci ba, kuma ya riga ya cika cikinsa..
NAILA;
Ba ta damu da rashin fitowar Sufyan ba tayi kwanciyarta bayan ta shiga Madafi da samawa cikinta wani abun..
★washe gari bayan Sallar Asubahi ba ta koma barci ba kamar jiya.
Bayan ta gama azkar ta tashi na ƙimtsa ko ina. Abinci mara nauyi ta dafa musu, ta jere a kan teburin cin abinci. Da ta tabbatar komai ya kammala sai ta koma ɗakinta domin yin wanka.
Sufyan ranshi fari fes ya tashi, saboda mafarkin ya zama hamshaƙin mai Dukiya sanadiyyar Sumaya. Bai koma barci ba, sai dai ba zama Karatun Alkur'ani ko azkar ya yi ba, wanka ya shiga.
Har Naila ta kammala girki gaban madubin washroom ya na kallon kansa, fatarsa kuwa tsabar dirza da soso a tunaninsa hakan zai sa ya ƙara haske, har zafi ya ke mai. Duk motsin Naila ya na jinta har ta kammala ta wuce daƙi.
Da sauri ya fito ya cinye kusan dukka abincin, yanajin alamun fitowarta ya tattara ya fita da sauri.
NAILA;
Lokacin da ta fito ta ga son zuciyar da Sufyan ya aikata bata yi mamaki ba, saboda tana san ran zai iyayin sama da haka matsawar hudubar Mahaifiyarsa bai bar zuciyarsa ba.
Ragowar ta ƙarasa cinyewa, bayan abincin ya ɗan sauka ta nemi waje ta kwanta tana jiran zuwan Ruwaida.
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana Ruwaida ta ƙwanƙwasa ƙofar sashensu. Da hanzari Naila ta lulluɓe sumar kanta har zuwa ƙasan kafaɗuna da yalwataccen malulluɓi. Da fara'a sosai na tarbe Ruwaida. Kamar dai jiya ba bu lulluɓi a ƙanta sai ƙaramin scarf ɗin data nannaɗe gashinta da shi. Ba ta karɓi tayin shigowarta Sashen su ba ta ce ta taho su tafi.
Su na tafe su ɗan hira har su ka kusa kai wa ƙofar Gidan da ya yi matuƙar birge Naila, amma jiya da ta je zata shiga tallata kitsonta aka hanata shiga. Nunawa Ruwaida gidan tayi haɗe da yimata bayanin abinda ya faru. Da farko dariyar da ya sa ta ɗan ranƙwafawa Ruwaida ta yi kafin ta ƙara kallon Naila ta kuma sakin murmushi, da sauƙin turancin da ta san zan fahimta ta ce "Karki ƙara zuwa saboda ba wajen zuwanki ba ne"
"Saboda me?" Naila ta tambaye Ruwaida da mamaki kwance a saman fuskarta.
Babu wasa a saman fuskar Ruwaida ta ce;
"Gidan Simbi ne, Matar Uzair. Ahalin Shahararren É—an kasuwa a Babban Birnin Abyad, ta zo gudanar da wani bincike ne a Asibitin jami'ar mu. Rayuwata ba bu sakewa sam, yawan zuwanki da sunan makitsiya zai iya janyomiki matsala don haka ki kula."
Naila jigum ta yi mutum ɗaya ta taɓa ji da irin sunan a Yankinsu, kuma itace ƴar autarsu Malik uwa ɗaya uba ɗaya. Don haka faɗar sunanta sai ya dawomata da tunanin abinda su ka faru shekarun baya. Simbi sun bar Yankin Tudu ta na yarinya ƙarama ta girmemata da Shekara ɗaya.
Naila a ranta ta ce;
"Nasan ma ba ita ba ce domin babu yadda za'ayi ko Malik da ya ke Babban yayansu ya mallaki irin wannan Gidan a Birnin Abyad balle ita."
Bata ƙara cewa Ruwaida komai ba har suka zo giftawa ta dai-dai saitin Gidan.
Naila ba ta da ciwon ido balle ta ce shi ya haddasamata ƙarancin gani, fitowar Mota mai ɓakin gilashin da akayi ƙasa da shi kaɗan saboda ɗagawa dakarun da su ke gadin gidan hannu ne yasa Naila tayi baya kafin ta saki ƙarar da ya ja hankalin har na cikin motar ya ɗago kai saitin da suke kafin ya zuge gilashinsa gaba ɗaya ya fice daga layin.
"SALMAN!" Naila ta faɗa a sarari, sai kuma ta tuna Salman to ai ya mutu, tun shekarun baya, to idan ba Salman ba ne wanda ta gani yanzu a Mota to wanene wannan? ko ƙaninshi ne? Ta tamabayi kanta.
Da hanzari Ruwaida ta tarota ta na faÉ—in "Naila! Menene ya sameki, kinsan shi ne? Ko bakyajin daÉ—i ne mu koma gida?"
Razanarta Naila ta shanye ta miƙe tsaye ba tare da bin bayan Motar da kallo ba ta ce;
"Na shiga razani ne sai na ke ganin kamar na sanshi"
Ajiyar zuciya Ruwaida ta sauke kafin ta ce "ohh Allah! Naila kin bani tsoro to ai mutane ma su kamaceceniya su na da yawa a duniyar nan ki kwantar da hankalinki kinji?" Kaina Naila ya É—aga mata alamun na gamsu.
Gidan da suka je dukka su Æ´ammatane su biyar kuma abokanan karatun Ruwaida. da alama Makarantarsu a kusa da nan yake.
Jarumtar Naila da son ta tara kuɗi domin cikawa Kaka burinta yasa ta yi juriya kitsa mu su gashin kansu dukka irin na Ruwaida ta yi mu su. Waje ɗaya suka haɗamata kuɗin da ya sanyaya rainta ta ji zazzaɓin da ya ke shirin rufeta ya sauka. Ba su wani jimaba bayan ta gama yi mu su suka bar Gidan. Yanayin shiru-shirun da ta koma lokaci ɗaya ya sanya Ruwaida itama cikin damuwa.
Dalilin haka ya sa bayan sun kai ta ja Naila ɓangaren kafin Sufyan ya dawo.
A kan kurajerun living room É—inta ma su taushi Naila ta lafe tana kallon shige da ficen Ruwaida daga parlo zuwa Madafi.
Cikin yanayinta na barkwanci Ruwaida ta ce Naila ta taso taa tayata girki.
Naila ta na shiga idanuwanta suka sauka a kan Tukunyar girkin Ruwaida, sunan jiki ne yasa ta ƙarasa kusa da Tukunyar da sauri, "DHAHAB" ne rubuce a jikin Tukunyar kuma tare da sunan a ka ƙera Tukunyar ba sticker aka manna ba. A take zuciyarta ta yi bugawar da ya sa na jingina da bango ƙwaƙwalwarta na tariyo mata shekarun baya.
Ruwaida da raha ta ce " kema Tukunyar ya birgeki ko?, ai Kamfanin ahalin su Simbi ne, Yayana a can ya ke aiki shi ya yi min kyautarsa ranar murnar zagayowar haihuwa ta, kinsan kuwa nawa ake siyar da Tukunyar nan, Tukunya ne mai matuƙar tsada, Ni kaɗai ce mai shi a cikin ƙawaye na, Tukunya ne da Sarakuna da ma su dukiya su ke girki da shi, shi kanshi Yayana da yake aiki a can da albashi shi muke rayuwa da ahalina a wadace, kinga kuwa ai ba ƙananun kuɗi ba n.." zubewar Naila ƙasa kamar gini ne ya dawo da hankalin Ruwaida da ke surutun Tukunyar Dhahab kanta. Hankali a tashe ta ja Naila da ƙyar zuwa living room.
Sashen Dr. Yasar moƙocinsu da Naila ta gudarwa Ruwaida ta nufa.
Da taimakon Yasar Naila ta dawo hayyacinta ko da su ka tambayeta abinda ya sameta ta faɗi bata ɓoye mu su abinda ya rikita ta ba.
Bayan ta gama ba su taƙaitaccen labarin Yakinsu Ajiyar zuciya dukkan su, su ka sauke.
Har cikin ranta Ruwaida ta yarda da gaske kamanceceniyar Mutumin da Naila ta gani sak Salman da Tukunya mai irin sunan Abduh Dhahab ne kawai su ka rikitata a matsayinsu na mutanen Yankinta ba tare da wani alaƙa ba a tsakaninsu ba, saɓanin Yasar da ya kasa yarda Naila ba ta da haɗin komai da abinda ya rikitarta sai alaƙar Yanki kawai.
Sai gabannin la'asar Ruwaida ta taimakamin na koma sashena.
SUFYAN; Bayan sun fito daga lecture, Sumaya ya sa rakasa ya zaɓo kalar rigar da take so. Sauƙin kayan sawar Ƙasar Abyad da abincin cin su ne yasa itama ya siya mata irin rigarsa su ka yi anko, ragowar kuɗin kuma abinci ya siya mu su mai lafiya suka ci suka ƙoshi, ɗan canjin da ya rage ya loda kati saboda kiran Mahaifinsa Ɗayyib.
A ɓangaren su Ɗayyib da Hindu lokacin da Sufyan ya kirasu ya basu labari sun sa masa albarka tare da nu na tsananin jin daɗin yadda Naila ta fara samun kuɗin da zai yi karatunsa hankali kwance, saboda Ɗayyib ya shaidamai bayan tafiyarsu da kwana ɗaya akaci Kasuwa bai san dalili ba sam babu cikini.
Bayanin Mahaifinsa sam bai É—aga mai hankalin ba, tunda ya samu Naila ta fara sana'ar da su ke samun kuÉ—in shiga. Bai ba su labarin haÉ—uwar sa da Sumaya ba saboda ya san bazasu ba shi goyan baya ba, za su ce yayi wuri ya É—akata shi kuma abinda ba ya son ji kenan.
A wannan yini da Sufyan da Sumaya su ka ƙarayi a Makaranta, shaƙuwa mai ƙarfin gaske ya ƙara shiga tsakaninsu. Kowannen su ya na jin ya yi dace da Abokin rayuwa dai-dai burinsa.
Kamar jiya ita ta koshi har bakin Layi.
NAILA; Bayan ta dawo kasa aikata komai ta yi, barcin ma da ya ɗauketa a zabure na miƙe saboda mummunar mafarkin da ta yi, wai ga Salman ya biyota zai ciremata harshe. A take wani irin tsoro da kaɗaici ya soma tsargata.
A haka Sufyan ya shigo ya same ta. Bai tantace muryata da kuka ya dusasar ba, balle kayan jikinta da batayi wanka balle ta sauya su, kuÉ—in da'aka biyata a wajen kitso ya tambaya bayan ya zauna.
Dama su na gefeta, don haka ta ɗauko ta miƙamai.
Da ƙarfi ya ce "Allah! Naila sannu da aiki, Naila idan na gama Karatu na samu aiki sai kinfi kowa jindaɗi, kuɗin da kika ba ni yau ma riga ɗaya kawai na siya da shi, haka na wuni da yunwa. Yanzu kinsan mai za'ayi zan ɗauki kuɗinnan na ƙarasa siyan kayan sawa kinga mun gama da wannan, ɗan abin ya rage kuma na riƙe kuɗin makaranta ko ya ya kika gani, ko da yake bari na tashi na je yanzu saboda gobe lecture 7:00am zan shiga." Ya ƙarasa faɗa ya na miƙewa.
Kafin Naila ta ahaÉ—iye hawayenta tuni Sufyan ya fice, ko tambayar dalilin da ya sa ban tayi girki ba baiyi ba.
Sufyan ya zaɓi zuwa ya siyo ba tare da jiran gari ya waye ba ne saboda Sumaya karta sa ran zai kuma siyamata wa su kayan.
Ko tsinke baiyi hikimar siyawa Naila ba tunda itama kayanta duk Abaya ne ma su arahar gaske ga adon da aka yi mai na saƙi sak na ƴan karkara. Chocolate kawai ya iya siya da Naila shima kuma sai da ya haɗa da na Sumaya.
Daɗin samun komai da sauƙi yasa yake ta murmushi shi kaɗai har ya dawo Gida.
Lokacin da Sufyan ya dawo Naila ta ga bai siyomata ko tsinke ba kasa shiru ta yi ta ce;
"Ba ka kyauta ba, tayaya zaka siyo kaya iya kai kaɗai bandani? " Da farko da zafinsa ya ɗago amma kome ya tuna sai ya fasa ya fara lallashita haɗe da tambayar abinda ya ke damunta. Da salon dabaru Sufyan ya kalamacata har ya yi nasarar tserewa daƙinsa bayan ya bata abinda ya siyomata.
Naila ta so ta ba shi labarin abinda ta gani amma gudun kar ya kira ya fesawa Mahaifiyarshi ya sa taja bakinta ta yi shiru.
Daga wannan ranar Sufyan ya ƙara zage damtse wajen yin ado da kaya kala-kala, da zarar ta samu kuɗi zai siyeta da daɗin baki ya karɓe, har Mahaifinsa ya sa ya tura Yaro a kaiwa Kaka waya suka gaisa Naila.
Ranar da Naila ta gaisa da Kaka bata runtsaba, saboda tanaso ta bata labarin abinda ta gani da wanda Sufyan yakemata amma babu hali domin zama Sufyan ya yi gadinta da sunan kallon talabijin.
A haka rayuwar ta miƙawa Naila da Sufyan, da kuɗin sana'ar kitsonta ya ke komai na Makaranta har ya yi wa Budurwarsa Sumaya hidima, duk Naila bata sani ba, da kuɗinta dai ya ƙara ƙawata living room ɗin su har da ɗakin kwanansa.
A ɓangarena Suturar sawa kuwa Naila bata da na arziƙi, idan tayi ƙorafi sai ya ce mezatayi da sutura ita da ba fita na ke yi ba, kitso kawai yake zuwa, shi dama kuma ba ya son idan zataje yiwa Mutane kitso ta yi kwalliya kar wani ya ƙwacemasa ita, shi ya fi son ya ganta ta yi ado da kayan da ta taho da shi saboda hakan na tunamai da Yankinsu.
A kwana a tashi Ruwaida ta fuskanci Sufyan cutar Naila yake yi domin kuwa duk ta rame tayi duhu saboda ƙewa da damuwa. Shawarar Naila ta fara ɓoye kuɗinta Ruwaida taba ta, idan sun taru za ta rakata ta siyi suturun sawa, idan Sufyan ya tambayeta ina ta samo ta ce ita ta siyamata da kuɗinta.
Bayan kwana biyu
Sufyan ya jera kwanaki uku ya na tambayar Naila kuɗi sai ta ce babu, da ya ga dai dagaske ta ke babu kuma aljihunsa ya yi ƙasa sai titsiyeta da tambayoyi, ƙarshe tana Madafi tana girki ya shiga ɗakinta ya bincike har sai da ya samu kuɗin da take ɓoyewa. Ta na tsaye ya shigo Madafi da kuɗin a hannunshi kafin ta yi magana ya kwasheta da mari cikin zafin rai yake masifar yasan Ruwaida ce take zugata, wallahi ta ci darajar itace take naimomata customers da sai ya ci mutuncinta ya wulaƙantata.
Sufyan ya yi tunanin ganin sauyi ko wani gagarumin ɓaci rai a saman fuskar Naila, amma sai ya ga akasin haka kamar baiyimata komai ba, cikin neman magana ya ce
"gaba zakiyi da ni saboda nayi miki faɗa ko,? to wai Naila saboda wa nakeyin wannan karatunnan? Saboda ke nake da ƴaƴan da zamu haifa, Naila saboda tsoron kar mu zo mu tara ƴaƴa babu kuɗin kula da su yasa kikaga na daure har yau ban kusanceki ba, duk wannan bai sa ki tausayamin ba haba Naila sai a fara zugaki ki na ɓoyemin samunki."
Murmushin mai ciwo Naila ta yi ta kalli fuskarshi ta ce;
"matacce ai ba shi da ran yin rigima da rayayye, idan kuma kasan yau ai ba kasan gobe ba, dalilin baiwar kitson da Allah Ya bani yasa ku ka kawoni Birnin Abyad, ga shi kana mora har ka na da Æ™arfin halin yin iko da shi. Ba ni da Æ™arfin yi ma iyaka amma lokaci zai yi maka a yanayin da baka taÉ“a tsammani ba"....âœðŸ»
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c
🔥ZINARE🔥
( ```The Gripping family saga with high Caliber)
```
SASAAL
14
Sufyan sak ya yi a tsaye har Naila ta gama magana ya kasa ce mata komai, har na ɓacewa ganinsa.
Bayan tafiyarta kafaÉ—arsa ya É—aga
A ganinsa mai zai jiyewa takaici? kuɗi ne dai dole ya karɓesu saboda da su ya dogara.
NAILA
★washe gari kamar ko yaushe bata koma barci ba, sai da ta gama Breakfast.
Ko da koma barci ta farka misalin tara na safe, ta fito Parlo a yadda ta jera abincin haka na samesa Sufyan bai ci ba. Tasan ya yi hakane saboda kuɗaɗents da ya karɓe, a karon farko hawayen takaicinsa su ka zubomata, bata tsawaita zubda hawayenta ba, bata kuma hana cikina abinci ba. Bayan ta ci na ƙoshi na fito harabar Gidan shan iska.
Yasar ta hango ya na yunƙurin fitowa, da farko ta yi niyyar guduwa saboda ba ta son haɗuwarsu, amma da na tuna taimakon da ya yi msta ranar da accident ɗin sashen Ruwaida ya faru sai ta jirkirta.
Yasar manazarcin halayyar ÆŠan adam ne, kuma likita a babban Asibitin Birnin Abyad. Gaishesa kawai ta yi ta matsar da kanta gefe.
Matsowarsa kusa da ita ya sa ta juyo tana zare ido.
Yadda ta zare ido na ne ya sa shu saki dariya ya na shafa tarin sumar kanshi da ya tattara wajen É—aya ya É—aure kamar Mace.
Ba bu zato ta ji ya ce;
"Maimakon zama haka mai zai hana Mijinki ya naima miki gurbin karatu a jami'ar su, idan ma ba shi da hali ki naimi izininsa ni zan biya miki Fisabilillah."
kalamansa sun wanke dattin da ya jima danƙare a cikin ƙwaƙwalwar Naila na tsahon lokaci, maganarsa abun dubawa ne a gareta, kuma shawara ne mai kyau amma tuna Sufyan ya sa ta ce;
"mijina ba zai yarjemin ba" ta faÉ—a da murya da ya bayyana rauninta.
Yasar ya kai wa su daƙiƙu ya na kallonta kafin ya murmusa da cewa;
"idan Mijinki ya na da sauƙin kishin da zai barki zuwa Gidajen da maza da mata su ke rayuwa, kamar Campus ɗin su Ruwaida kiyiwa Ɗalibai kitso, to babu dalilin da zai sa ya hanaki naiman ilimi. Menene amfanin neman da ba zamu gina gobenmu da shi ba?"
Kamar talabijin haka Naila ta zubawa fuskar Yasar mai tsananin haske da kyau ido, ba haskensa da kyansa ta ke kallo ba, gaskiyar da ya faÉ—a take gani a saman fuskarsa.
YASAR Duk da ya san Naila ta gamsu ɗari bisa ɗari kuma ta yarda da maganarsa amma tana kwakwanton naiman mafita sai ya ƙara ce mata;
"ga hanya mafi sauƙin warwarewa kanki komai, ki fara naiman izininsa a kan na ce zan biyaki kuɗi mai yawa ki kitsamin kaina, ki ji mai zai ce, idan ya ce a'a sai ki san dabarabar da za kiyi ki tambayesa izinin naimar miki jami'a, idan kuma ya ce eh, kin samu hanyar da zaki tafi Jami'a cikin sauƙi, ki nutsu ki warware komai dalla-dalla za ki fahimce ni da kyau".
Cikin nauyin baki Naila ta yi mai godia. Har ya ɓacewa ganinta bata daina kallon hanyar da yabi ba.
Yinin ranar a tunani ta ƙaresa domin ta kasa yarda Sufyan ba ya kishinta, shi da ya ce kishin ta ne ya ke hanashi siyamata kaya kar wa su, su ga kyanta, duk da tasan ba ya sonta sosai kamar kuɗin da na ke samu, amma ta yarda da zancensa.
Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa ta miƙe ta ƙarayin wanka, kayan dai da ta taho da su daga Yankinmu ta saka, duk sun ƙode sun jeme.
SUFYAN; Sufyan kayan ciye-ciye da ice cream kala-kala ya siya mu su shi da Sumaya, har sun dawo sunyi lecture ya tuna rashin siyawa Naila kaya zai ƙara tunzura ta, har ta ɓullo da wata dabarar tara kuɗin a inda ba zai gani ba balle ya ƙwata, musamman wajen Ruwaida, kuma siya mata kayan zai kawar da tunanin ba ya sonta ba ya son farin cikinta a ranta. Bai naimi rakiyar Sumaya ba ya tafi, kusan rabin kuɗin da ya ɗaukemata ya siyamata kaya da su ba dan ransa ya so ba.
Da ya dawo Makaranta da Kayan Ƙiri-ƙiri Sumaya ta nuna ƙishinta, ranar ko ƴar hirar da su ke yi a kan hanya ba su yi ba, bakinta a gaba take tuƙi, takaici da kishi na nuƙurƙusarta. Ko da ta sauke Sufyan kafin ya yi mata sallama ta figi mashin ɗin ta.
Jiki a sanyaye Sufyan ya shigo gida.
Da Sufyan ya shigo bai bawa Naila kayan da ya siyo ba, É—akinsa ya wuce da kayan ransa fal kokwanton ko dai gobe ya kaiwa Sumaya, saboda bai ji daÉ—in yadda su ka rabu ba.
Jikinsa ba kuzari ya tsakuri abincin da ta girka, itama Naila tata fuskar sam ba fara'a. Bayan ta tabbatar ya huta ta sako masa hirar neman izininsa zata yiwa Yasar moƙocinsu kitso tare da bayyana masa irin kuɗin da ya ce zai ba ta. Ga mamakinta Sufyan ko alamar banbanci tsakanin jinsi Namiji da na Mace bai nuna ba yace ai neman kuɗi ne babu Matsala. Zuciyarta da jinina na gudana da sauri-da sauri ta tambayesa izinin komawa Makaranta, kai tsaye ya ce mata;
"ba ni da kuɗi, ko kuɗin da kike ba ni kike yiwa baƙin ciki Naila?" Muryarta ta na rawar kukan da ya tahomata tana ƙoƙarin dannewa ta ce;
"ance ba sai ka biya ba za'a samomin Scholarship" kamar an tsikaresa haka ya miƙe ya na masifa kamar zai taune harshensa. Sai da ta bari ya gama kumfar bakinsa, sannan ta miƙe haɗe da cewa;
"zuwa Makaranta da sunan naiman ilimi sai zama aji ɗaya da Maza, amma kowa da Mazauninsa, ba bu kuma tilas ɗin mu'amalantar juna, iskanci ne. Amma zuwa Gidan da Maza su ke rayuwa da sunan sana'a haɗe da kama kansu na kitsa saboda za su bani kuɗi mai yawa shi ba Iskanci ba ne Sana'a ce ko? Idan ka rayu a matsayin miji a gareni sannan ka zaɓi zaluntata da duƙushemin rayuwa wacce riba za ka samu Sufyan?"
Ƙasa ya yi da kansa, ganin ba shi da mafita sai ya fara lallashinta haɗe da garzayawa ɗakinsa a hanzarce ya kwaso kayan da ya siyo mata yake kokwanton ba ta. Kamar zai yi kuka haka yake magiyar gwadata ya ke yi kamar yadda akasarin Maza suke yaudarar Mata da sunan gwaji.
A cewarsa idan banda gwadata ya ke yi ta ya ya zai yarda ta yiwa Yasar kitso sai ka ce ba Musulmi ba, shi kansa Yasar ɗin ai ba mutumin ƙwarai ba ne, idan ban da haka ta yaya zai ce Matar aure ta yi mai kitso. Da ire-iren waɗannan kalaman ya so yaudarata.
Ba bu daɗin bakinsa ɗaya da ya samu gurbi a cikin zuciyar Naila, amma ta ji daɗin kayan da ya siyomata. Kamar komai ya wuce haka ta nunamai, domin ya ƙara shashantar da ita sai ya fara ragewa kanshi zafi kamar yadda ya saba.
Bayan ta koma daƙina kuka da ya sanyamsta ciwon kai ta yi, ba ta da wanda zats buɗewa zuciyarta ta zazzage masa dukka damuwarta sai dai tasha kukanta ita ɗaya a ɗaki.
★washe gari da Sufyan zai fita Makaranta Cikin dabara ya ke ja mata kunnen rage mu'amalantar Ruwaida idan ba haka ba zata kaita ta baro.
Abinda bai sani ba
Kalaman Ruwaida ga Naila ma su taushi ne haka zuciyarta da niyyarta dukkan ma su kyau ne a kan Naila, idan ma cuta ce Ruwaida ta rasa wacce zata cuta sai irin Naila.
Naila Ba ta ce mai kanzil ba har ya bar Gidan.
Da ga ranar ta ƙauracewa zaman harabar Gidan saboda Yasar, idan ka ganta a waje to Ruwaida ce ta haɗata da customer, ko kitso idan aka biyota Gida a living room ta ke zama su yi.
A hankali a hankali Naila ta fara rama mai busar da Mutum tambayar duniya idan Ruwaida ta yi mata sai na ce mata"ba komai".
Sufyan ya haramtamata gaisawa da Kaka kullum sai ya ce ya kira ÆŠayyib Mahaifinsa ba ya samu.
A kwana a tashi cikin hikimar Ubangiji suka shekara É—aya da rabi a Birnin Abyad.
A ɓangaren Sufyan ya canza ya ƙara haske ya yi kyau sak mazaunin Birnin Abyad, saɓanin Naila ta da ta bushe ta rame idan ta yi dariya sai haƙora su cikamata fuska.
Ta ƙara samun customers wa su ta je Gida tayi musu wa su kuma su biyota Gida, duk tarin kuɗin da take samu Sufyan ne yake kwashewa domin akwai ranar da ta ɓoye kuɗi a wajen Ruwaida, har ya titsiyeta da tambaya.
Bata ɓoye masa su na wajen Ruwaida ba, a ranar sai da ya yi mata dukkan da ya hanata motsi. Bayan ya fita Makaranta ya kira Mahaifinsa ya yi mai bayani. A take shima ya sanar da Uban Gidansa, washe gari jami'an tsaro mata suka zo har Gidan su ka jawa Ruwaida kunne haɗe da karɓe kuɗin da na ke tarawa, bayannan su ka yi mata tsakani da ni.
Ruwaida ta na tsoron abinda zai taɓa karatunta. Ba tare da ta nemi ƙara ganin Naila ko tambaya ta sane abinda aka yi mata ko ba na sane ba, ta tattara Kayanta ta tashi bar Gidan, sai ma su kwashe kayanta kawai Naila ta gani.
Tun da ga lokacin sai Naila ta ƙara zama kamar sha-sha-sha. Ga shi Yasar tun da ya ya bata shawara na yi watsi da shi har take gudun haɗuwa da shi ya tattara lamarinta ya watsar ko haɗuwa sukayi ta gaishesa daƙyar ya ke amsawa. Yasar bai ƙara tsanar Naila ba sai da ya ji labarin abin da ya faru tsakanin Sufyan da Ruwaida. Daga wannan ranar ko gaishesa Naila ta yi baya amsawa.
Abubuwan da su ka faru da Naila sun sa ta yi losing hope, sai ta ke ganin sakarwa Sufyan komai ya yi iyakacin zaluncin da Allah Ya ƙaddara a cikin rayuwata shi kawai ya fiyemata sauƙi.
Da ga wannan dukan farkon da Sufyan ya yimata ya mayar da ita kamar jaka, akan abu ƙalilan sai ya zaneta, ɗai-ɗaikun ranaku ne baya kai hannunsa jikinta, ga dabaru da ya ɓullo da shi, haka zai sakamata videon tsaraicin wa su ya ce ta nutsu na kalla irinsa zata yimai. Da farko gardamar bazan yi ba ta yi mai, ai kuwa ya kamata ya yi mata dukan tsiya, abisa tilas ɗin rashin zaɓi ta fara bin umarnin Sufyan.
A haka su ka ƙara shafe shekara ɗaya cikin uƙuba da tsanani, ba ta gaisawa da Kaka, ba ta da abokin hira, domin wacce ta tare a ɓangaren Ruwaida sai da Yasar ya ja mata kunnen kar ta kuskura ta kula Naila idan ba haka ba zan ƙulla mata sharrin da Allah ne Kaɗai zai wanke ta.
Da kuɗin guminta Sufyan ya ke rayuwa, da kuɗin guminta ya ke tari a Bankin da Ubangidan mahaifinsa ya yi mai jagora ya buɗe, da kuma kuɗin guminta ya ke yiwa budurwasa Sumaya siyayya. Ita kuma ko cikakken Suturar sawa ba ta da shi, idan ta yi dariya tsananin munin ta sai ya bayyana saboda rashin namar fuska har wani yamushewa fatatar ta yi. Sufyan ma ya kance ba ta da abinda zai mora a jikinta duk ta rame sai ƙasusuwan da zasu jimai ciwo, da wannan yake fakewa sai dai ya tuɓe ya yi ta umartata tana yimai abinda zai gamsar da shi.
A ɓangaren Sumaya da Sufyan soyayyar su kullum ƙara armashi ya ke yi saboda basa ɓoyewa junansu komai sai na ɓangaren da ya shafi sirrin su, Sumaya ko sunan Naila bata son ji a bakin Sufyan wannan dalilin ya sa baya yi mata hirar ta.
A yammacin wata asabar Naila ta shirya zuwa Gidan ƙawayen Ruwaida da ta taɓa kaita, domin ba ta muzantata a wajen kowa ba, dukka ƙawayenta waɗanda su ke kiranta ta yi musu kitso ba su daina ba, Ruwaida ce dai kawai ta ƙauracewa haɗuwa da ita.
Ta na fitowa na haɗu da Yasar, da ta gaishesa daƙyar ya amsa yana gyara zamansa a han ɗan tudun da ya ke zaune.
Naila bata yi nisa da Gidan su ba, ta hango lafiyayyen mota mai farin gilashin da mutum zai iya ganin na ciki, fuskar Salman ta gani kamar dai yadda ta gani a farkon zuwanta Birnin Abyad. Da gudu ta tunkari mota da ya ke tafiya a hankali ta na kuka haɗe da magana da iyakacin ƙarfin muryarta;
"Salman na san kai ne ka tsaya ka cikamin alƙawarina na roƙeka, ina shan wahala ka taimakeni ba ni da kowa a Birnin Abyad ka ji ƙaina ka faɗamin ina SULAIM yake? da gaske ya ƙone ya mutu?"
kamar yadda Naila ta yi tsammani bai tsaya ba tana ji tana gani su ka haɗa ido cikin ido da mutumin da ta ke ganin sak Salman sannan yaƙarawa Motarsa gudu ya barta a wajen. Ƙasa ta zube ina kuka.
Yasar da ya ga komai kuma ya kasa jurewa nufo inda Naila ta ke ya yi, ya kamo hannunta ya kawota har harabar gidansu. Cikin taushin murya ya ce;
"Naila menene ya ke damunki, ka faÉ—amin gaskiya daga ina ki ke(ma'ana Yankinta) "
kasa magana ta yi saboda shesheƙa.
Naila ta ɗauki mintina a haka, kafin ta daki ƙirjinta saitin zuciyarta inda ke ji kamar zai fashe, sannan na fara magana sheshekar kuka na tare ta;
" ina shan wahala🥹, ina so na koma Yankina, ina ji kamar zan mutu..."âœðŸ»
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c
🔥ZINARE🔥
SASAAL
15
Tana na gama furta ciwo da raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyata, sai ta ƙasa magana saboda kukan da ya ci ƙarfina.
Kamar talabijin haka Yasar ya zubamata fararen idanuwansa.
Ta kai wa su daƙiƙu tana kuka, kafin ta cigaba da magana;
"Sufyan ya na ganamin azaba, ya na dukana, ba ya barina na mori kuɗin da na ke samu. Ruwaida ita ce take taimakamin kuma ya yi mata sharri saboda ina tara kuɗi a wajenta ta bar gidan nan. Ni marainiya ce, ba ni gata kuma ba ni da ƙarfin yin komai ka taimakamin na koma Yankina"
Kai ya sunkuyar ƙasa saboda tausayi ya jima a haka kafin ya ɗago ya ce;
"Ina ne Yankin ku Naila? Kuma maiyasa Æ´an uwanki tunda sun san ba su da halin da za su iya taimaka miki a ko wani lokaci su ka ba wa Sufyan ya taho da ke har Birnin Abyad? Wannan gangancine mai girman gaske"
Ba bu ƙarya a maganarsa amma ƙaddara ta riga fata. Cikin sanyin yanayin da ya ɗan fara shigar Naila ta ba shi labarin Yankin da ta fito. Amma ba ta ba shi labarin dalilin da yasa ta ke bibiyar mutumin da ta ke zargin Salman ba ne.
Yasar ya gamsu da bayaninta, amma sai ya ƙara jefomata tambayar "maiyasa ki ke kiran Mutumin da ya wuce ɗazun har ki ke cewa ya taimaka miki? Wanene kuma Sulaim ɗin da kike tambayarsa ɗan uwanki ne? Ki faɗamin gaskiya idan da hali zan iya taimakawa."
Ƙur Naila ta yiwa Yasar da ido, tarihin abinda ya faru na kusantowa ganina kamar a lokacin su ke faruwa.
Waje ta samu ta zauna Yasar ya biyo bayanta.
A baya labarin Yankinta da mahaifanta sun mutu kawai ta faɗamai da rashin adalcin danginta na ɓangaren Uwa da na ɓangaren Uba, amma tunda ya nuna zai taimaketa ta koma Yankinta to dole ya san asalin inane Yankin Tudu da kuma surƙullen da ya ke cikinsa.
Kamar Yasar ya na ganin komai haka ta ke ba shi labari tun da ga lokacin da ta yi wayo har zuwa mutuwar Salman da abubuwan da suka faru bayan nan har aurenta da Sufyan da kuma manufar Mahaifansa a kanta.
Mamaki ne zalla a saman fuskar Yasar, banda yana da ilimin nazatar Ɗan adam da kai tsaye zai ƙaryata Naila, wani irin Yanki ne wannan? Wa su irin mutanene ma su ƙaracin basira ne a Yankin?
Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa Yasar gajarta tunaninsa. Cikin alhini ya ce;
"Tabbas! Naila akwai DHAHAB CITY a Babban Birnin Abyad, Unguwar da wani mashahurin mai arziƙi ya gina, Shekaru goma sha biyar baya. Ahalina ne ma su tsauri da tsantseni domin dai-dai ma su gadin alƙaryar Dhahab ababen tsoro ne, sai dai shi ba sunanshi Abduh ba sunansa Muhammad Dhahab kuma a zahirin da mu mutanen gari mu ka sani Ɗan asalin ƙasar Abyad ne, amma wa su na cewa ba shi da asali babu wanda yasan gaskiya. Duk wani mai hidima da ma'aikatan Company's ɗin su, su na da record ɗin komai na sa, rayuwar su ba bu sakewa sam duniyar su tamkar daban ya ke da namu, ba bu wanda yasan sirrinsu sai makusantan su, Tun shekarun baya na naimi aikin tsaron sashen Mahaifiyar Muhammad Dhahab a yanar Gizo kamar yadda na ga an wallafa saboda ma su irin ilimina ake nema, amma saboda sun kasa samun cikakken bayani asalin ni ɗan inane da kuma inda Mahaifana su ke zaune, sai su ka fasa ɗaukata duk da cancanta ta, na yi kuka a waccen lokacin saboda albashin aikin ninkin wanda na ke samu a yanzu ne sau huɗu. Gane rashin samun cikakken asalina ya sa suka hanani aikin sai na tattaro Mahaifana na tara kuɗi na siya mu su Gida a Birnin Abyad, saɓanin daa da su ke zaune a bayan gari. Sai dai duk da na yi haka samun aikin sai ya gagareni haka na gaji na haƙura.
Bayyanar Simbi ahalin Gidan Muhammad Dhahab a Asibitin mu sai ya dawomin da burina na baya, wannan dalilin yasa na fara bibiyarta ta taimakamin saboda zan ƙara samun sakewa wajen taimakawa mahaifana har na samu na yi aure, amma sai Simbi ta wulaƙantani dalilin da ya sa nayi zuciya kenan na haƙura da aikin.
Amma Naila dole yanzu zan ƙara zage damtse har Simbi ta saurareni, saboda shigata Dhahab zai bayyanarmin alaƙar tarihin Yankin Tudu da rayuwar su, fatana ki tayani da addu'a."
Baki, hanci, da ido dukka Naila ta saki tana kallon Yasar, cikin kokwanto ta ce "menene sunan wanda aka ce shine Mijin Simbi mutumin da ya ke yimin kama da Salman?"
ÆŠan dariya Yasar ya yi kafin ya ce;
"A binciken da na yi Simbi sam ba ta da Miji, kuma wanda ki ke gani sunansa Uzair, ba shi cikakken lafiya sosai saboda ya taɓa ciwon da ya yi shekara shida a kwance kafin ya warke, bansan wani ciwo ba ne, amma na samu bayanin ne da ga Yayan Ruwaida amintaccen ma'aikaci a kamfanin su, shima a sirrince ya faɗamin don haka ki kiyaye" kafin ya ƙarasa tuni Naila ta ɗora hannuwanta dukka biyu a kan bakinta alamun ba bu wanda zai ji.
Dariya Yasar ya yi kafin ya ɗora da nasihar ta kwantar da hankalinta da ƙarfin mulkin Allah sai sunyi nasarar shiga Dhahab ko a masu goge-goge ne.
Naila sai ta ji dukka ƙuncinta ya yaye sai ta ke ganin kamar komai ya zo ƙarshe, da wannan farin cikin sukayi sallama ta koma ciki ta yi wanka ta ci abinci. Gidan kitson da bata je ba kenan ta kwanta barci.
Daga wannan ranar Naila bata ƙara ji daga Yasar ba gaba ɗaya ma sai ta daina ganinsa. Da farko ta ɗan damu sai da ya ba da gajeran saƙonsa na suturar sawa ma su kyau da kayan ciye-ciye ya risketa ta kwantar da hankalinta.
Babban akwatinta ta sauko da shi, na ɗura kayan a cikin gudun kar Sufyan ya gani saboda ya kusa dawowa. Ta na kici-kicin mayar da akwatin hotonta da na Sulaim da ta sa aka wanke mata ƙaraminsa ya faɗo, da sauri ta ɗauke saboda har ga Allah batasan ya na cikin aljihun bayan Akwatinta da ta taho da shi ba, kuma tasha zuba kuɗi a ciki na kwashe amma hoton bai taɓa bayyana kansa ba. Da wani irin farin ciki ta ke kallon hoton. Batasan ta ɗauki lokaci a haka ba sai da taji Muryar Sufyan a bayanta, dama kuma da ɗayan key ɗin Parlon ya dawo tafiya Makaranta.
Firgitarwar da bayyanar Sufyan a lokacin da bata yi tsammani ba ne, yasa ta saki ƙara haɗe sakin ƙaramin hoton ƙasa, kallon hoton Sufyan ya fara yi sannan ya yunƙuro dasauri zai ɗauka ransa na suya, kafin ya cimma hoton tuni ta yi hanzarin ɗaukewa tana zare ido.
Fes Sufyan ya ga waɗanda suke jikin hoton, ciwon da ya jima da shafesa a tarihin rayuwarsa ya yunƙuromai. Cikin ɗacin zuciya ya fara dukanta ya na ƙwallo da ita, ya na cewa;
"ba ni hoton nan wato amanata ki ke ci ko? Shi yasa kullum bakya ganin kyawuna, kina maƙale da wannan hoton shaiɗanin da ya addabi mutane duk da ba ya raye, wallahi idan baki bani ba sai na kusa kashe ki" maganganun sa ba su ƙarawa Naila komai ba sai ƙaimin ƙara dunƙulewa da ta yi da hoton waje ɗaya, idan ya kasheta ma ai ta huta da uƙubarsa.
Har ya gama dukanta bata warware daga ɗunƙulewar da ta yi ba, cikin azabar kishi ya sa mukulli ya kullota yana huci...
Kuma ya yi rantsuwar ba zai buɗeta ba har sai ta bubbuga da kanta ta yarda bashi hoton ya ƙona sannan ta ba shi haƙuri.
Haka Naila ta kwana ta wuni kulle, inda Allah Ya taimaketa akwai kayan ciye-ciyen da Yasar ya aikomata da su, idan ta É—anci sai ta kora da ruwan banÉ—aki ta É—oro alwala ta kaiwa Ubangiji kukanta.
A haka ta shafe kwana uku tana manejin abinda Yasar ya bata tana korawa da ruwa kuma cikin hukuncin Ubangiji sai ta ji na ƙoshi.
A ranta take faÉ—in;
Banda shirmen Sufyan idan har shi da ya ke a iya haka yana ganin yafi ƙarfina to ina ga SULAIM da ya fishi komai ace ya na raye mai zai yi da ita? Sulaim tamkar Aboki ya ke a gareta har ya bar duniya, ba bu soyayya balle alƙawarin aure a tsakaninsu. Dalilin da yasa soyayyarsa ta samun matsuguni a cikin zuciyarta shine barinsa duniya, ta hanyar da dole a tausayamai, a kuma kasa mantawa da shi. Amma ko a raye ko a Mace bazata taɓa sawa ranta lallai Sulaim sai ya so ta ko ya aureta ba, matsawar ba ƙasƙancin da Sufyan yake nunamata dama take so ta fuskanta ba.
SUFYAN; A kwana na biyu da kulle Naila a ɗaki kafatanin kuɗin da ya ɗan rage a Bankinsa saboda ya turawa Gida kuɗi a rabawa Danginsa har da Dangin Naila da Kakarta da sukai ta samai albarka tare da farin cikin Naila tana cikin daula, su ka ƙare, ga shi ya saba siyawa Sumaya kaza, da su ice cream da sauransu har Gida ya ke siyamata ta kaiwa Iyayenta.
Tun washe garin da ya kulle Naila yake sa ran yunwa zai ci ƙaniyarta ta buga ƙofar ta ba shi haƙuri haɗe da ba shi hoton, amma ya ji shiru.
Kwana uku da kulleta daƙyar ya kalato canjin aljihunsa ya tafi Makaranta. Ranar ba su ci abincin arziƙi ba don haka ya keɓe ya kira wayar da ya tura kuɗi aka siyawa Mahaifiyarsa .
Hindu masifa takeyi bayan gama saurarar Sufyan kamar zata cijeshi ta waya..
"yanzu kai saboda ba ka san ciwon kanka ba shine zaka kulleta ka janyowa kanka asarar kuɗi ma su yawa, a kwana ukun nan banda kulletan da kayi da nawa zata samo maka? Amma wallahi Sufyan sam ba bu basira a cikin ƙwaƙwalwarka, har yanzu ba zaka daina kishi da Sulaim da yake matacce ka gina rayuwarka ba, Yankin Tudu kowa ya na samaka albarka, kai kana can kana shirme? To idan bata so Sulaim ba a matsayinsa na mutumin da su ke tafiya Makaranta tare su dawo tare su yi raha tare kuma ya ƙone lokaci ɗaya ba wa kake so ta so eh? dabba mara tunani!"
Saukar kalamanta sai da ya sauya kalar fararen idanuwansa, ya na jin kamar ana barbaɗa masa yaji, zagin da Ɗayyib Mahaifinsa ya ɗoramai da shi bayan ya karɓi watan ne yaƙarasa birkitasa, cikin rawar murya ya ke ba su haƙuri amma still Ɗayyib faɗi ya ke
" to yanzu haka Kasuwar Tukwanen Zinare ya mutu miɗis, sabuwar yunwa ta kunnowa Yankin mu kai, saboda an samu hamshaƙin mai arziƙin da ya saci fasaharmu ya mayar da su Tukwane na alfarma a kaf faɗin duniya ba bu inda ba'a siya, mu kuma an watsar da namu saboda ya zama tsohon yayi. Shine kai mun samu ka tsira zaka dawo damu baya, Allah Ya wadaran wannan son kyau na ka Sufyan! kai kullum ba ka da zance sai zancen Mutumin da tuni ya ruɓe a ƙarƙashin ƙasa, idan ka dama ka gyara to, idan kuma baka dama ba kai sani. Kasan da abinda zaka biya kuɗin hayar ku idan ya ƙare"
Sufyan kanshi ne ya ɗauki zafi a take ya fasa kuka yana ba su haƙuri. Shi gaba ɗaya ya manta da kusantowar biyan kuɗin hayar su.
Tahowar Sumaya inda ya ke ne yasa ya yi mu su sallama haɗe da yi mu su alƙawarin komai ya wuce, In Shaa Allahu zai gyara.
NAILA
Kayan ciye-ciyen da Yasar ya aikomata da shi ba laifin ya na da yawa, amma ba irin sosai ɗinnan ba, rashin sanin ranar da Sufyan zai buɗeta yasa take cancanensa kar ya ƙare ta rasa abin ci, saboda ko zai mutu bazata ba shi Hotonta da Sulaim ya ƙona ba.
Da yammaci ta na zaune a inda ta yi sallar la'asar ta ji ya buɗe kofar, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bai ce mata komai ba, ya bar ƙofar a buɗe ya juya ya fice.
★washe gari saboda rashin kuɗi ko Makaranta bai je ba. Ya na ɗaki ma su zuwa tambayar kitso su ka zo har mutum uku, ɗam jim Naila ta yi kamar ta ce mu su ba ta da lafiya, amma yadda su ka nuna su na son kitson ya sa ta amince. Sufyan dake laɓe yana kallonsu ajiyar zuciya ya sauke bayan ta amince ya koma ya kwanta yana murmushi.
Bayan ta gama su na fita ya yi zumbur ya fito ya ƙwace kuɗin fuskarsa ƙunshe da dariya.
YASAR; duk wata hanya da zai bi ya samu ganin Simbi abin ya ci tura, abinda ma ya lura da shi kamar ba iya son haÉ—uwa da shi ne ba ta yi ba, gaba É—aya gudun mutane ta ke yi. Ranar da ya ji labarin saura kwana É—aya ta gama abinda ya kawota ta koma Dhahab a bakin ofishinta ya wuni.
Ta na fitowa ma su gadin lafiyarta su ka rufa mata baya, kai tsaye tasa a hana Yasar bin bayanta. Sai dai kafin su kaiga riƙeshi ya taka da gudu zuwa inda motarta ya ke dai-dai inda ta ke tsaye yadda za ta jiyosa cikin yanayin maganar da matsawar tasan Naila zata fahimcesa a hankali da kuma sauri ya ce;
"Yankin Tudu, Daular Sarki Hammam Naila Æ´ar Gidan Mahmoud madinki, Aminin Abduh Dhahab....âœðŸ»
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c
🔥ZINARE🔥
SASAAL
16
"Yankin Tudu Daular Sarki Hammam, Naila ƴar gidan Mahmoud madinki, Aminin Abduh Dhahab." Yasar ya ƙarasa faɗa zuciyarsa na bugawa da sauri.
Dukan mai laifi kai tsaye ba tare da gudanar da ƙwaƙwaran bincike ba laifi ne mai girman gaske a ƙasar Abyad. Wannan dalilin yasa ko da jami'ai masu tsaron lafiyar Simbi suka cimma Yasar ba su taɓasa ba sun dai yi mai katanga tsakaninsa da ita.
SIMBI; Designer jakar hannunta mai tsananin nauyin kuɗin da ya dace da arziƙinsu ta ƙanƙame da fararen hannunta ma su sanyi kyau ga mai Kallonsu, kafin ta juyo da kyakkyawar fuskarta. Idanuwanta da suke farare ƙal ta zubawa fuskar Yasar, batason dogon magana da shi, saboda doguwar magana a tsakanin su tamkar karya alƙwarin Alhalinta ne, don haka ta ce;
"A ina kasan dukka wannan?."
Jira take yi ya saki layi ta sa akamashi saboda gudun shigarta matsala amma da yake Yasar wayayyene akan aikinsa da kuma fahimtar inda ta dosa kai tsaye ya ce;
"Layinmu gidan na uku hannun hangu makitsiya mai ƙaracin shekaru."
Jami'an tsaronta shirme suka É—auki kalaman Yasar saboda ba su fuskanci ina kalamansa su ka dosa ba tunda ba su ji abinda ya faÉ—a lokacin da ya risketa ba. Umarnin barin wajen suka ba shi, bayan Simba ta shiga Mota.
Yasar bai musa ba ya juya ya bar wajen, maimakon ya koma Gidansa sai ya wuce na Iyayensa saboda yasan dole abi bayansa, domin ko shakka ba ya yi labarin tare Simbi da ya yi da tsayawarta ya isa Babban Birnin Abyad.
SIMBI; bata manta fuskar Yasar ba, saboda tun ranar da ta gansa ta ji ya birgeta a ƙofar Gidan da ya faɗa, kuma a wannan ƙofar Gidan ya naimi taimakon aiki da gareta gaba da gaba na ƙarshe lokacin ta fito workout, gudun matsala da sanin abun da take saƙawa zuciyarta akansa ba zai taɓa tabbataba yasa tasa a wulaƙantashi saboda ya yi zuciya kar ya ƙara bibiyarta.
Bata manta Naila ba, ba kuma zata mantata ba har abada, saboda ƙawarta ce kuma maƙiyiyar Ƴar uwarta Barirah.
WAIWAYEN SHEKARUN BAYA
Lokacin wasannin ƙarshe mako a Daular Sarki Hammam akwai wata matashiya mai kusan Shekarun Sulaim da ta kwashewa Naila ƙafafu saboda ta matso kusa da inda su ke wasa, har Naila ta kawo ƙararta wajen Sulaim. Ƙanwar Malik ce Uba ɗaya Sunanta Barirah.
Mahaifinsu Malik, ya auri Mata biyu matarsa ta farko ita ce Mahaifiyarsu Malik, tun da suka haifi Malik ba su ƙara samun wani ba har Malik ya kai shekaru biyar, son ƴaƴa ya sa shi ƙara aure, ya auri Mahaifiyar Barirah. Bayan wani lokaci ta haifin Barirah sa'ar Sulaim daganan itama ba ta ƙara ba, sai Mahifiyar Malik da ta ƙara haihuwar Simbi, baƙin kishi da rashin son zaman lafiyar Mahaifiyar Barirah ya sa Mahaifin Malik sauwwaƙemata ya kuma karɓi ƴarsa Barirah.
Barirah muguwar gaske ce musamman idan taga ta fika ƙarfi, ba ta baro komai na halin Mahaifiyarta ba. Da farko bata tsani Naila ba tana dai cin zalinta matsawar suka haɗu, amma daga lokacin da Sulaim da take son ya kulata ya riƙe Naila a matsayin ƙawa ta tsaneta ko aikota akayi Gidansu sai ta ranƙwasheta.
Wannan tsanar bai sauya zani ba duk tsayin shekarun da su Barirah suka kwashe a cikin daula.
DAWOWAR LABARI
A cikin Mota Simbi take hira da zuciyarta
Tabbas! bata manta fuskar Naila ba, amma mai ya kawo Naila Birnin Abyad? Allah Ya sa ba wani Yaƙinne yake shirin tunkaro su ba.
Bayan kwana ɗaya kafin Komawar Simbi Babban Birnin Abyad, ta yi yunƙurin bincike don tabbatar da ainihin abinda yasa Yasar ya iya yin kasadar tararta kai tsaye saboda matsalar Naila kawai da kuma abinda ya kawo Nailan Birnin Abyad, kafin komai ya lalace. Ta hanyar kiran Bushra da take sa'arta, wacce suka zama tamkar zuri'a ɗaya a Dhahab, kuma take kyautata zaton zata iya yimata bincike akan Naila, saboda ba ta so take wajen Naila da kanta ta ganeta. babu ja Bushra ta amince dama kuma tana Birnin Abyad itama bata koma ba.
NAILA ; kamar kullum da sassafe ta yi ayyukanta bata wahalar da kanta wajen girkawa Sufyan Breakfast ba saboda ba ci zaiyi ba, idan ta yi a wajen yake barmata kayanta.
Wanka ta yi ta ɗauko Abayar da ta zamemata tamkar ta gado ta saka, saboda tana jin tsoron saka wanda Yasar ya aikomata da su gudun duka da ga Sufyan, domin wanda Sufyan ɗin ya siyomata masu sauƙin kuɗine marasa quality duk sun zaizaye wa su guraren ma duk sun yage.
Bayan ta gama saka kaya turare ta fesa saboda customers kamar yadda Rufaida ta É—orata a kai tuntuni saboda a wasu lokutan jikin mutum ya kan É—anyi tsami wanda hakan ya ke takurawa ma su zuwa kitso musamman idan suka É—ora kansu a tsakanin ciyoyi.
Sana'ar da ya zamemata jiki ko da yaushe ta zauna yi( tunani) wa ni lokacin ta saki kuka wa ni lokacin kuma ta yi dariya. Ta na cikin tunani ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Da hanzari ta miƙe ta nufi ƙofar, ta buɗe.
Bata taɓa ganin fuskarta ba, don haka tayi mata tarba na musamman tana washe haƙoran da suke ƙara bayyana ramata. Ƴar gayu ce kuma da alama daga Gidan arziƙi ta fito.
A lokutan baya Naila ba ta da yawan surutu ba ta da yawan dariya irinna rashin kamun kai, amma tunani da ƙunci rayuwa suka sa ta zama mai tsananin surutun da ita kanta batasan tanayi ba, ga dariya da take yawan yi na rashin dalili wanda ya zarta a kirashi fara'a.
Ba mai yawa wacce yazo kitson ta ce ta na so ba, don haka ta yi mata irin yadda take buƙata.
Da ta tashi tafiya kuɗi mai yawan da daa abayane ta bawa Naila su ihun murna zatasa saboda tana da yaƙinin zata tara ta gina Gobena da su, amma yanzu Sufyan ya na dawowa zai ƙwace.
Rashin fara'ar Naila da yadda ta yi ƙasa da kaine yasa wacce ta zo kitson ta magantu;
"Baiwar Allah ko kuɗin ne ba su yi miki ba, na ga kamar ranki a ɓace" ta ƙasara faɗa tana karantar yanayin Naila.
A hankali Naila ta ɗago idanuwanta da ƙwalla yasa ta ke ganinta dishi-dishi ta ce;
"Na gode! na gode!! Allah Ya biyaki, amma dan Allah daga ina kike na baki kuɗin ki taramin?" Naila ta ƙarasa faɗa kamar wacce batasan me take yi ba.
Idanu ta zaro ta ce; "ta yaya ba ki Sanni ba zaki bani ijjiyar kuɗi bakya tsoron na gudu da su? saboda me ke bazaki ɓoye a ɗakinki ba ko ɓarayi su na damunku na sanar da jami'ai?"
Kai Naila ta girgiza hawayen da bata iya yiwa idanuwanta shamaki da su ya tahomata.
Idanuwa wacce ta zo kitso ta ƙara zarowa wannan karan da mamakin bayyane a saman fuskarta, cikin tashin hankali ta ce;
"Menene matsalar Baiwar Allah?"
Cikin kuka Naila ta ce;
"Inaso na koma Yankina amma bana iya tara kuɗi Mijina kwashewa ya ke yi domin gina gobensa, ya na dukana kullum, ki taimakamin kinji Don Allah nasan kinfi ƙarfin su bazaki Gudu da shi ba"
kamo Naila ta yi zuwa jikinta tana shafa bayana ta ce;
" Ya ya sunanki kuma ina ne Yankin ku? Ko zan iya taimakawa"
Da sauri Naila ta ce ; " sunana Naila, yankin mu shine Yankin Tudu"
Naila tana jin lokacin da zuciyar wacce ta zo kitso wajenta ya ya buga da sauri, saboda kanta dake jingine har lokacin a saman KafaÉ—arta.
Da sanyi murya wacce ta zo kitso wajenta ta ce;
" Maiyasa ba zaki bawa Mijinki kuÉ—inki ya gina gobensa ba, gina gobensa ai tamkar gina na ki ne"
Kuka Naila tasa tana roƙonta ganin kamar ba ta fuskanceta ba.
Gwauron numfashi ta sauke, tana kallon Naila ta ce;
"Zan karɓa amma sai kin sanar da ni dalilin dayasa baƙyason mijinki ya mori kuɗinki alhali kuna tare bai sake ki ba"
Kamar wacce take jira haka Naila ta soma sako mata zance da wanda ta tambaya da wanda bata tambaya ba.
Da Naila ta gama labari
Ba ta ce mata komai sai bayanta da ta ɗan bubbuga tayi mata sallama ba tare da karɓi kuɗinba.
Ba kowa Ba ce tazo wajen Naila kitso ba fa ce Bushra wacce Simbi ta Turo, kuma ta naÉ—i dukka hirarsu da Naila.
SIMBI; Recording É—in da Bushra tasa mata, da yake Bushra gwanar tausayi ce ta kuma sauraro tana kuka.
Daga wannan ranar kullum sai Simbi ta tura Bushra Gidan Naila da sunan tayata hira a haka suka samu dukka bayanan da suke so, amma har lokacin Simbi ba ta tuna fuskar Sufyan ba tunda sun bar Yankin Tudu ya na yaro.
Har lokacin komawar Simbi Dhahab ya yi, ba su samu damar bincikar Sufyan ba, don haka ta bar ragowar aikin a hannun Bushra ta tattauna da Yasar a sirrince domin ya taimaka musu wajen bibiyar Sufyan.
NAILA
Dalili yawan tambayoyin Bushra da yadda ta saki jiki da ita duk da kasancewarta ƴar masu hali yasa Naila ta fara zargin ko Sufyan ne ya turota, da ta fara zargin haka sai ta daina bata kuɗinta ya ɓoyemata ta nuna mata ta sauko ta fison Mijinta ya gina gobensa domin su tashi tare su tsira tare.
Babu kalar tambayar da Bushra batayiwa Naila ba akan wasu sirrika na Sufyan da ta gano amma Naila taƙi faɗa saboda tsoro.
YASAR; kamar yadda ya yi zargi bayan barin wajen Simbi za'a bibiyi bayansa haka kuwa a kayi, A sirrince É—aya daga cikin masu tsaron tafiyar Simbi ya bi bayansa ya bincika babu makitsiya a gidan, daga haka ya É—ora mizanin maganganunsa akan shirme kamar yadda sukayi zargi tun farko.
Da sunan Ganin likita Bushra ta samu keɓewa da Yasar daya koma gaban Mahaifansa da zama saboda tsaro.
Alƙawarin naimarmasa aiki ta yi matsawar ya gayamata Ɗan gidan wanene Sufyan a Yankin Tudu.
Ko batayi alƙawarin cikamai burinsa na samun aiki a Dhahab ba ya yi alƙawarin taimakon Naila ta koma Yankin su ta kowacce fuska.
Bai ɓoyewa Bushra komai ba, ya kuma roƙeta ta riƙe amana, kuma a shirye yake domin ba da gudunmawa idan hakan ta taso.
BUSHRA
A wannan rana kwanan tunani Bushra ta yi. Matsawar Simbi tasan Sufyan jinin masarautar Yankin Tudu ne, to ba shakka ba za ta taimaki Naila ba, dama kuma can ba wai tana son taimakon Naila ta wata fuskar bane daban sai na mayar da ita Yankinsu. Amma ga Bushra ba irin wannan taimakon takeson yi wa Naila ba, wanda zatayi farin ciki na har abada takeson yi mata.
Ko da sukayi waya da Simbi kai tsaye ta sanar mata bata gama bincike ba.
A cikin kwana biyu Bushra ta binciko Sufyan ciki da wajensa har da soyayyarsa da Sumaya da abinda yakeyi da kuÉ—in Naila saboda ta samu tabbacin baya sana'ar komai.
Ta na son Naila taje Dhahab amma ta yaya?
Ta na kuma son Sufyan ya ɗanɗani azaba ƙiri-ƙiri irin ɗanɗanar da zai gusar da nutsuwar zuciyarsa yana ji yana gani, amma dole sai ya riski Dhahab to amma ta yaya riskarsa Dhahab zai yiwu?
Tsakiyar Dare ta naimi layin Mahaifanta, sunyi magana ya fi na hour huɗu, kafin ta suyi sallama, ba tare da jinkiri ba, ta dannawa Yasar kira. Suka tattauna yadda zasu ɓullowa Sufyan.
★washe gari Bushra da ke lulluɓe cikin shigar larabawa ita da Yasar suka kaiwa Sufyan ziyara Makaranta. Sufyan tsaf ya gane Yasar, wannan dalilin yasa ya tsamke fuskarsa ya na bawa Sumaya umarnin ta jirasa yana zuwa.
Da suka keɓe bayan sun Gaisa sama-sama
Suka ce masa takardunsa daga kan na primary har na secondary suke so da kuma shaidar takardun jami'ar da ya ke zuwa zasu samar masa aiki a Dhabah amma sai takardun Makarantarsa sun kasance na Birnin Abyad, za kuma a samar mishi sabon jami'a a can idan ya kama aiki.
Kwaɗayin da burin duniya su suka taru suka lulluɓewa Sufyan ido ya kasa tantace cuta da so da kuma tantance ina ne Dhabah maiyasa suka zaɓi naima mai aiki. Jikinsa na rawa ya tashi gefe ya kira Mahaifinsa.
ÆŠayyib ihun murna yasa ba tare da tsayawa saurarar sunan Ma'aikatarba ya kira amininsa.
Ɗayyib ya na kiran Amininsa ya sanar da shi buƙatarsu
Kai tsaye amininsa ya sanar da shi bashi da hanyar da zai samarwa Sufyan takardun bogin primary da sakandaren ƙasar Abyad.
Ko da Ɗayyib ya kira ya sanar da Sufyan a take jikinsa da ke rawar murna ya yi sanyi laƙwas.
Jiki a sanyaye ya dawo wajensu Yasar ya yi musu bayani. Bushra da ke tantance son banza irin na Sufyan kai tsaye ta ce zata samar mai amma sai ya yi mata alƙawarin barin matarsa ta naimi jami'a ya kuma daina karɓe mata kuɗin sana'arta.
Son banza bai sa Sufyan ya tambayar kanshi ina Bushra ta samu labari ba, ya ce ya amince amma a iya bakinsa ya tsaya, domin har cikin ransa ya yi alƙawarin jami'a sai dai Naila ta ga anayi....
A cikin kwana biyu Bushra da ƙarfin ikon Mahaifinta a ƙasar Abyad suka samarwa Sufyan takardun bogi.
Tare da Takardun Yasar Bushra ta shigar ta hanyar yanar Gizo tare da addu'ar dacewa,.domin batason Malik yasan aikinta kai tsaye duk da akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu.
Duk wannan wainar da ake toyawa Naila batasan ana yiba, sai shige da ficen Sufyan da take gani a ruÉ—e.
BUSHRA
★washe gari abinda ya shigar da Bushara Toilet ya fi sau uku shine ÆŠaukar Sufyan aiki tare da wani irin albashin da ya tsoratata. Ba ita kaÉ—aiba dai-dai da Mahaifinta ya shiga zullumi da ta sanar mai, ya kuma gano akwai babban YaÆ™i domin ko rantsuwa ya yi bazai yi kaffara Malik da ya É—aukesa aiki ya gano wanene SUFYAN.....âœðŸ»
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥
SASAAL
17
Har yamma ta yi liƙis nutsuwar Bushra bai dawo jikinta gaba ɗaya ba. Idan wayarta ta yi vibrating har firgita takeyi.
Dole zancen Mahaifinta ya zama gaskiya banda haka Sufyan bai cancanci ya samu aiki lokaci É—aya haka ba, dama dai Yasar ne da takaddunsa suke nunawa gogewarsa.
Har dare Mahaifinta bai kirata ya samu kira daga saman Dhahab ba wanna dalilin yasa ta É—an samu nutsuwa a ranta, amma duk da haka sai da ta kira Simbi.
Yanayin muryar Simbi da shawarar da take bata na ta dawo ta ƙyale Naila domin ita ta fasa taimakonta ne yasa Bushra ta ɗan jo sanyi a ranta, saboda da an samu matsala zata ji a bakin Simbi, sai a lokacin ta samu sukunin kiran Yasar tayimai bayani.
Shawarar su haÉ—u washe gari a Gidansu Naila suka yanke.
NAILA; tunda ta ɗauke yardata a kan Bushra ta miƙawa Allah komai tare da alƙawarin ba zata ƙara naiman taimako a wajen kowa ba.
A tsakanin kwana da wuni Sufyan sam bai tambayeta kuÉ—i ba, kuma a kan idonsa ta kitsa kan mutum biyu.
Bata yi mamaki ba, domin ga dukkan alamu akwai gagarumin al'amarin da ya tisosa a gaba.
A daren cikon kwana na huÉ—un da ya yi da daina tambayarta kuÉ—i, kuma itama bata ba shi ba, ya kirata É—akinsa.
Cikin muzurai yake sanar da ita samun aikinsa dalilin tonon Asirin da ta yi masa a wajen Bushra É—aya gano daga baya, to ga kuÉ—inta ya barmata amma ta jira hukuncin da zai biyo baya.
Har ya gama kumfar bakinsa da maganganun izgilancinsa Naila batace masa komai ba.
Daga ƙarshe ya jamata kunnen karta kuskura Bushra da Yasar su naima mata jami'a ta yarda ta je. Idan kuma ta saɓawa umarninsa wallahi sai ya hukuntata da hukuncin da har ta mutu bazan manta da shi ba.
Babu abinda ya motsa daga jikinta balle ya gane na fahimcesa ko bata fahimcesa ba, takaicin hakan yasa ya haureta da ƙafa ya na faɗin;
"Fice min daga ɗaki, sha-sha-sha kawai ai gashi garin ki tonamin asiri kin janyomin daukaka, kuma wallah na rantse bazaki ci ko sisi daga arziƙina ba"
Sam surutansa ba su dameta ba, tunda zai barta ta dinga tara kuÉ—inta. Kuma ko su Bushra sun tambayeta tanason zuwa jami'a da babban murya zata amsa "eh". Kanzil ba tace ba har ya gama masifarsa ta bar ÆŠakin.
SUFYAN; ranshi fari fes yake ji, sunan ma'aikatar da za'a samarmai aiki na kai kawo a cikin zuciyarsa, anya babu wani sirri a cikin wanda ya kara DHAHAB(ZINARE) a cikin sunansa, Abdulyasar Dhahab Ubaidullahi Dhahab, Abduh Dhahab, duk ba su bar duniya ba sai da suka zama ababen koyi, ga shi ya kuma samun wani mai arziƙin a Babban Birnin Abyad shima Dhahab. Tabbas! A kwai wani ɓoyayyen abu a cikin wannan sunan tunda shi kanshi asalin DHAHAB(zinare) ba abun yadawa bane abune da ake kokawa a kansa. Kakanninsa da suka ƙi kwantar da kai subi Abdulyasar Dhahab tun farko ai gashi za su mutu babu wanda ya sansu sai ƙananun muƙamin Sarautar da suke taƙama da ita. Anya bazai koma Sufyan Dhahab ba kuwa? Dariya ya bawa kanshi yana shafa sumar kanshi, tare da ayyanawa ransa irin girman kuɗin da zai dinga kashewa sumarsa, duk da dai bai san iyakacin albashin da za'a biyasa ba. Yanzu matsalarsa ita ce Naila, hanyar da zai rabu da ita ya korata Yankin Tudu kawai yake nema ba tare da su Bushra da Yasar sun ga baƙinsa ko butulcewarsa ba, tunda ko yana so ko baya so Naila ce sanadi. Da Sumaya yake son su tare a Babban Birnin Abyad idan komai ya yi masa yadda yake so.
Tuna irin abubuwan da zai yi idan ya fara aiki yasa ya tashi yana taka rawa.
NAILA; bayan ta koma ɗaki kuɗinta ta ƙara adanawa tana lissafa irin kayan da zata siyawa Kaaka duk ranar da Allah ya ƙaddara tafiyarta, godiya tayiwa Allah sannan na godewa Bushra tare da alƙawarin naiman yafiyarta duk ranar da Allah Ya haɗata da ita abisa munana mata zato da tayi.
Ranta babu damuwar komai sai godiyar sauyin da ta fara samu nayi alwalar kwanciya barci, cikin abinda bai gaza minti biyu ba, bayan tayi addu'o'i barci mai nauyi ya É—auketa.
★washe gari iyakacin abincin cikinta ta girka.
Sufyan fita ya yi ya jubgowa kanshi siyayyar lafiyayyen Breakfast daga kuÉ—inta da yake tarawa a Banki.
Daga dawo
Ko kallonsa batayi ba ta tattara na bar living room ɗin. Hakan da tayi ba ƙaramin haushi ya bashi ba, don haka ya hau zage-zage da gorin ai ta kusa daina ganinsa sai ta dafa gidan ta cinye ni kaɗai idan ta samu kuɗin biyan haya, domin wallahi shi bazai biya ko sisi ba, ko ta tattara ta koma Yankin Tudu tunda bata da kunya ta fara rainashi bazatw roƙeshi ya sammata abinda ya siyoba ta sawa kanta girman kai alhali ita ba ƴar kowa ba ce face ƴar Madinkin da ya ke talakan fitik ta sanadiyyar rashin kuɗin zuwa Babban Asibiti ciwon ciki ya kasheshi.
Kamar babu mutum a gidan haka Naila tayimai shiru, amma a É—aki kuka takeyi zuciyarta na suya.
Bai daÉ—e da gama Breakfast ba su Yasar suka iso Gidan.
Jiki na rawa ya shigo da su Living room yana baza kunnuwar jin dalilin zuwansu har Gida. Ba su fara bayani ba sai dai suka bashi umarnin kiran Naila.
Da ya shigo kiran Na'ilah sai da ya
Na mata kunnen karta kuskura ta saɓawa abinda zai ce ya yi mata, sannan ya kamo hannunta muka fito tare.
Naila tana hangosu ta ƙwace hannunta ta nufi Bushra.
ƙam ta rungume Bushra tana nanata kalmar ta yafemata ta zargeta da cin amanarta ashe tanadin da ban taɓa tunani ba tayimata.
Sufyan harara yake watsowa Naila ta ƙasan ido saboda ya matsu ya ji dalilin da ya kawo su. Sai da Naila ta nutsu tukunna sannan Bushra ta fara yi mai bayanin samun aikinsa da kuma irin albashin da za'a dinga biyansa duk wata.
Duk yadda Sufyan ya so yaja aji ko ya kame kansa kasawa ya yi ya miƙe zurbur yana zaro idanunsa, kafin ya fashe da kuka yana yi musu godiya. Kai suka girgiza a tare suna haɗa bakin faɗin;
"Naila zaka yiwa godiya dalilin gwagwarmayarta kakai matsayin da kake kai a yau, don haka karka manta alkhairinta domin shine tsanin nasararka" da gigin farin ciki ya fara nanata "Naila na gode! na gode!! na gode!!!" A tunanin Naila Sufyan ya sauya kenan don haka ta taso ta ƙanƙamesa tana yiwa su Bushra godiya, suma murmushine kwance a saman fuskokinsu.
Bushra bata nanata naimarwa Naila jami'a ba tunda sun riga sun yi maganar da Sufyan tun farko kuma ya nuna ya amincewarsa. Bayan wani lokaci Yasar yayimusu sallama Bushra kuma ta zauna Naila ta kitsa mata kanta. Shima Sufyan barin Gidan ya yi da sunan zuwa Makaranta, zuciyar Bushra na suya tabi bayansa da kallo saboda ko shakka batayi wajen Sumaya zaije. Kenan Sufyan ba zai taɓa sauyawa ba.
Naila da bata fahimci komai ba bakinta a washe take yiwa Bushra kitso tana janta da hira.
A hankali a hankali hirarsuu ta faÉ—o kan Sulaim da yadda suka haÉ—u da sanadiyyar mutuwar Mahaifiyarta da ko Yasar Naila ba ta faÉ—awa ba, ta dai ce masa Mahaifiyarta ta mutu.
Bushra tari ne ya sarƙeta ta hau yi babu kakkautawa, sannu Naila ta fara yimata kafin ta wuce kitchen ta ɗauko mata ruwa.
Bayan tarin ya tsagaita sai ta yiwa Naila murmushi ta ce;
"idan har kin aminta dani inaso ki É—aukomin hoton Sulaim na gani."
Da hanzari Naila ta miƙe tana dariya na nufi Ɗakina.
Bayan ta ɗauko ta miƙawa Bushra,
Bushra ta ɗebi mintina tana kallon hoton, sannan ta miƙamin tana janyo gilashinta mai ɗan duhun da Naila take iya ganin idanuwanta amma ba sosai ba ta manna.
Naila ba ta kawo komai ba a ranta ta hau yaba gilashin da ƙoda irin kyan da ya yi mata. Bushra ba ta ta cewa Naila komai ba sai ɗan danne-dannen da ta yi a waya.
kamar daga sama Naila ta ji Bushra ta ce;
"Idan yau ace Mairam Matar Mahaifin Sulaim kuma Æ´ar Uwar mahaifiyarki da Mahaifiyarki ta rasa ranta wajen hidimtamata amma tabi umarnin iyayenta ta gudu ta barki duk da tasan zakisha wahala, kika ganta cikin daular da take da damar nemanki ta taimaka miki amma batayi ba yaya zaki ji?"
Kanta Naila ta ɗago dakyau hawayen tuna irin mutuwar azabar da Mahaifiyarta tayi na zubowa ƙuncinta, cikin dakiya da kyakkyawar fata ga kowa ta ce; "wataƙila tana da dalili, ina kyautatamata zato a duk inda take, idan da rai da rabo wata rana Allah zai ƙaddara saduwarmu, amma gareni na yafe mata duniya da Lahira." Ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka.
Rungumeta Bushra ta yi cikin ƙosawa ta ce;
"Yaushe zaki daina barin hawayenki suna zuba Naila? dole duk wani matakin nasara na tare da ƙalubale, Karki bari yawan kukanki yazama lagonki a wajen maƙiyanki"
Kai Naila take girgizawa. A haka Bushra tayi ta lallashinta har ta yi shiru. Kafin ta bar Gidan sai da ta bata kuɗi masu yawa tace ta ɓoye zata ƙara dawowa kafin ta wuce Babban Birnin Abyad.
SUFYAN; Kuɗin Naima da yake tarawa kaf ya kwashe sukayi ƙwarya-ƙwaryar walima shida iyayen Sumaya da ƙawayenta, tare da alƙawarin da zarar yaje Babban Birnin Abyad ya samu yadda yake so shirye-shiryen auren su da Sumaya zai kankama.
Sai dare sosai ya dawo Gida.
★washe gari ma da sassafe ya bar gida. Duk Naila ba ta damu ba, ta bar shige da ficen nasa a matsayin shirye-shiryen tafiya Babban Birnin Abyad.
Ranar da jirginsu zai tashi a bakin Bushra da zo gidan Naila ta ji labari, sai dai bata nunamata batasaniba.
Bushra ta yiwa Naila kyautar kuɗi masu yawan gaske ta kuma yimata alƙawarin zata zana jarabawar share fagen shiga jami'a da taimakon Yasar. Da ta tashi tafiya waya mai kyau da tsada ta bata ta ce ta ɓoye kar ta bari Sufyan ya gani.
Naila bata fahimci tsanarta ya yi nisa a zuciyar Sufyan kuma har abadan bazai taɓa ƙaunarta ba, sai da taga dare ya yi babu Sufyan ko da ta kira Yasar da wayar da Bushra ta bata da lambobin su a ciki, a nan takejin labarin ashe Sufyan tun da yamma jirginsu ya tashi. Ta yi kuka mai raɗaɗi da ciwon da bansan iyakarsa ba bayan sunyi sallama da Yasar, kafin ta haƙura ta kulle kanta a ɗaki.
Tafiyar Bushra da Sufyan ne yasa Yasar dawowa ɓangarensa tare da ƙaramar ƙanwarsu da zamu zasu jarabawa tare sai dai Naila ta girmeta amma ta fi Naila girman jiki.
Naila ta ji daɗin dawowar Yasar da ƙanwarsa, da kai tsaye ɓangarenta ya turota don tayata kwana.
A take Naila ta saki ranta domin fuskantar sabuwar rayuwata.
SUFYAN; kafin tafiyar Babban Birnin Abyad tunda sassafe Naila tana barci ya ɗauki iya ƴan kayan da zai ɗauka ya bar gidan, a Makarantar suka wuni da Sumaya tana kukan zatayi ƙewarsa. Gudun lalacewar komai yasa bai barta ta rakasa airport ba kamar yadda ta buƙata.
Tare da Bushra suka hau jirgi..
Bayan sun isa filin jirgin Babban Birnin Abyad mota daban-daban suka hau da Bushra baima ƙara ganinta ba, kamar ba tare suka taho ba. Ma'aikacin Company ya kira kamar yadda Yasar da ya kira ya yi mai bayani haɗe da turomai Number.
Kamfanin Dhahab bai ƙarasa c
Tsakiyar Babban Birnin Abyad ba kuma anan inda Company ya ke anan staff quarters É—insu yake.
Apartment ɗin da yasa Sufyan zubewa ƙasa yana yiwa Allah godiya aka kaishi. Ranar kwana ya yi bawa Sumaya labari haka su Ɗayyib da ya kira. Sam ya manta da Naila.
Kan Sufyan bai ƙara kwancewa ba sai da aka kaishi Office ɗin da ake ce nashi ne.
Duk da Sufyan yana da son banza da kwaɗayin son tara abin duniya sai da ya tsorata ba kaɗan ba. Tayaya ya samu matsayin da ko da dukka karatunsa ya kammala ba zai samu ba? anya Bushra da Yasar da Naila ba haɗa baki sukayi domin a siyar dashi ba tunda yana cinyemata kuɗin kitso? Hannunsa na karkarwa ya lalubo wayarsa😂.
🔥
SASAAL
18
Duk number wanda ya kira ba ya samu hatta number Bushra da bai ƙara gani ba a kashe yake. A take nadamar rashin siyawa Naila waya ya lulluɓesa, da yanzu ita zai kira yayiwa barazana tunda yasan matsoraciyace.
Fatar hannunsa, takalmin ƙafarsa da kayan jikinsa ya kalla, ya ƙara kallon ofishin bai san sanda ya fashe da kuka ba. Sam Chemistry bai haɗu ba dole akwai manufa. Cikin kuka yake ƙara zagaye ofishin har da Bedroom da washroom.
Lokacin da ya gama ƙarewa komai na ofishin kallo sai ya ƙara sakin kuka, hannunsa na tsuma ya ƙara lalubo wayarsa a karo na biyu ya dannawa mahaifinsa kira, saboda daa baiyi niyyar kiransu ba kar ya ɗaga musu hankali.
Duk son duniyar Sufyan a bayan Hindu Mahaifiyarsa yake haka itama duk son duniyarta a bayan Ɗayyib suke, domin shi bashi da tsoro akan duk wani abu daya kafawa ƙahon zuƙa.
Sufyan cikin kuka yake bawa Ɗayyib labari. Maimakon ya ji tashin hankali a muryarsa sai ya ji ya saki ƙaramin dariya.
Da ƙwarin gwiwa ya ce;
"Naila bata da muguwar zuciyar sayar da kurwarka Sufyan"
Kai Sufyan ya girgiza idanuwansa ƙyam akan kujerar alfarmar da yake a matsayin mazauninsa.
"Baaba bazaka fahimta ba, ba su kirani interview ba balle na tantance ƙwarewa ta ce yasa suka bani wannan ofishin, babu wani abu daga neman aiki sai shiga ofishi, tun daga ranar da na sauka ko Bushra banƙara gani ba, Baaba ni dai kawai haƙura zanyi da aikin nan"
Da zafin muryar da zai nutsar da Sufyan kar yaja musu asara ÆŠayyib ya ce;
"Ka kwantar da hankali ka, duk na sa Ubangidana ya bincikamin komai, kana tunanin rayuwar kara zube kakeyi a Birnin Abyad? Har soyayyarku da Sumaya na sani, da bushashar da kakeyi da KuÉ—in sana'ar Naila, dama abinda muka turaka kayi kenan?
To ka buɗe kunnuwanka dakyau ka saurareni. Ka mayar da hankali kan aikinka domin fansar dukiyar da Mahaifiyarka da ni kaina muka sadaukar akanka ba ka zauna yin shirme ba. Inaso ka tara kuɗi Ubangidana yaƙara bincikamin komai a kan ma'aikatarku domin sanin muhimman abubuwa akan mai kuɗi sai da kuɗi.
Yaya ma sunan ma'aikatar taku ka ce?"
Kafin Sufyan ya ɓude bakinsa da ya yimai nauyi saboda kalaman Mahaifinsa da suka sanyaya mai jiki, an buɗe ƙofar ba tare da naiman izini ba. A gigice ya katse kiran.
Rashin nutsuwar da yake ciki da kuma rashin sanin matsayin da aka bashi yasa bai tuhumi wanda ya shigo maiyasa bai naimi izini ba.
Ɗayyib bai haƙura ba ya cigaba da kira Sufyan a ɗan gajarce ya ɗaga ya ce ya bari idan yaje Gida zasuyi waya.
Cikin ƙwarewa bayan sun Gaisa da wanda ya shigo yake koyawa Sufyan yadda zai gudanar da aikinsa.
Fara'ar fuskar Baturen da yadda yake nunamai yadda zai gudanar da aikinsa ne yasa Sufyan ya É—an saki jiki.
Ko da Baturen ya fita sai da ya ƙara ƙarewa komai kallo yanajin alfahari da girman kansa na ƙaruwa a hankali. Murmushi ne ya kufcemai bayan ya sauke ajiyar zuciya wawtar dayaso tafkawa na dawomai.
Bayan Sufyan ya isa Gida ko cikakken hutun minti biyu bai yi ba, aka aiko mai da lafiyayyun kayan fita Office. Cikin isa yake gwada kowanne kanshi na ƙara girma.
Da yake Sufyan sha-sha-sha ne ko da ya nutsu maimakon ya kira Mahaifinsa sai ya kira Sumayya suka yi ta waya har barci ya É—aukesa.
★sai washe gari da safe ya tuna da kiran Mahaifinsa, a gurguje ya kirasa suka gaisa sama-sama.
Irin motar da aka zo É—aukarsa zuwa office ne yasa ya ji daÉ—i kamar ya kashe shi, cikin isa ya gyara kwalar rigarsa haÉ—e da motsa kafaÉ—unsa kafin ya shige.
Daga wannan rana aikin Sufyan da ya mayar da kai ya miƙa, cikin kwanaki ya ƙara gogewa ya fara ɗaukar hanyar zama Sufyan Dhahab ɗin da yake fata.
A computer yake ganin irin Tukwanen da Company Dhahab suke ƙerawa amma bai taɓa ganinsu ido da ido ba, domin ma'aikar da ake ƙera Tukwanen daban yake da na sarrafa shinkafa da yake aiki. Sai dai labarin Tukunyar da ya ke datsa jefi-jefi a wajen Abokanan aikinsa.
Hankalin Sufyan ya ƙara tsayuwa waje ɗaya bayan samun tabbacin Turawane manyan Company, ƴan asalin ƙasar Abyad tsirrai ne a ciki.
Cikin ɗumbin narasa, kwanciyar hankali, ƙaruwar soyayyarsa da Sumaya, manta Naila gaba ɗayanta, rayuwar Sufyan ya miƙa.
BUSHRA; tun ranar da ta sauka a Babban Birnin Abyad bata samu nutsuwa ba sai da ta tattara ta bar ƙasar gaba ɗaya. Saboda har lokacin bata cire ran samun kira daga Malik ba. Lokacin da taje Dhahab ma a tsaitsaye suka gaisa da Simbi Uzair ya dawo da ita Gida. Daga wannan rana ta ƙauracewa ƙasar Abyad gaba ɗaya, sai saƙon kuɗi da take aikawa Yasar ya bawa Naila.
NAILA; Duk da ta saki jikinta a wasu lokutan tanajin ranta babu daÉ—i, tanaason magana da Kaaka amma bata da hanyar samunta.
Tana cikin wannan yanayin ta zana jarabawar share fagen shiga jami'a ita da ƙanwar Yasar. Har lokacin babu kira daga Sufyan, kuma bai zoba, ko Yasar ya daina kira a waya.
Kwanaki biyu da gama zana jarabawar su aka kira Yasar Interview a Dhahab Babban Birnin Abyad.
Rai babu daɗi Yasar ya fara shirin tafiya Babban Birnin Abyad. Bazata taɓa manta alkhairin da ya yimata ba, da abubuwa dayawa da bazan taɓa iya mantawa da su ba, ya yi mata alƙawarin zaman ƙanwarsa a tare da ita.
Sai dai da yaje yiwa Iyayensa sallama ƙememe suka nuna ba su amince ƴar su ta zauna a inda babu mafaɗi ba, da yake Naila ta rakasa domin dawowa tare da ƙanwarsa a gabanta suka dinga sakin maganganu marasa daɗi da nuna ita ɗin ba wata abar aji tausayi ba ce. Bata yi kuka ba, ba kuma taga laifinsu ba amma ta ɗan ji haushinsu tunda ko ba komai ai sai su yi tunanin suma tasu ɗiyar zata iya tsintar rayuwarta a cikin kwatankwacin irin wanda ta riski na ta a ciki.
Har suka dawo Gida haƙuri Yasar yake bata, ta na ta nunamai babu komai.
A washe garin ranar da ya rage saura kwana ɗaya Yasar ya tafi Babban Birnin Abyad ya kai Naila ya buɗemata asusun ajiyar kuɗi a Babban bankin Birnin Abyad, tare da siyayyan kayan abinci da kayan maƙulashe kala-kala.
★washe gari da sassafe Yasar ya fito zai tafi. Ta yi kuka irin kukan da ban san iyakarsa ba, sai take ji kamar ita kaɗaice a duniyarta, sai ta ke jin kamar ta bishi taga inane wannan Dhabah ɗin, su waye a ciki, tanaji a jikinta kamar ta san su, kamar tana da alaƙa da su. Cikin kuka ta ce idan ya je ya gaishemata da mutanen cikin Dhahab. Duk yadda Yasar yaso ya jure kasawa ya yi yasa kuka da haka suka rabu da Naila ba tare da sanin ranar da zasu ƙara ganin juna ba.
Naila bata taɓajin kaɗaicin da ta ji ba a kaf rayuwata irin ranar da Yasar ya bar Birnin Abyad. Ko ina yayimata shiru wa su lokutan sai ta ji kamar motsi a bayanta wa su lokutan kuma sai ta ji kamar ana kiran sunana. A wannan dare ta gane girman rahamar zama da mutum a waje ɗaya.
A haka wahalallen barci ya É—auketa cike da mafarkai ma su ban tsoro.
A haka ta shafe kwana uku cikin kaÉ—aici duk da tana waya da Yasar jefi-jefi a rana.
Tun tana jin tsoro har ta haƙura ta sanyawa zuciyata dakiya.
Da sannu zuciyarta ta ƙeƙashe ta daina jin tsoron komai. Zata tashi da safe ta yi Breakfast ta ci na ƙoshi idan rana tayi ta tafi Gidan Customers ɗinta wa su kuma su biyota Gida. Idan Dare ya yi ta ɗauki kuɗi a cikin kuɗin sana'arta ta je nasha Ice cream a wajen da Yasar ya nunamata.
A haka rayuwata ta miƙa, jarabawarau ta fito tayi kyau. Da taimakon Abokin Yasar ta samu gurbi a jami'a mai zaman kanta na Birnin Abyad duk Bushra ce ta biya ta hanyar Yasar, shi kuma ya turawa amininsa.
KuÉ—in siyayyar kayan abinci da abubuwan amfani Yasar ya turomata. Da ta rasa kalar godiyar da zanyi musu shi da Bushra kuka na sanya.
Duk da Bushra ta ƙauracewa waya da ita, ta ƙauracewa zuwa inda take domin ta jima da dawowa Babban Birnin Abyad amma saboda tana tsoron kar ta cigaba da zuwa wajen Naila asamu matsala, sai ta daina kiranta, ta daina zuwa wajenta ko ta shigo Birnin Abyad gudun kar ta ƙara saka Naila a cikin matsala.
Da taimakon Abokin Yasar Naila ta kammala komai na fara attending lectures
A ranar da ta fara zuwa Makaranta da yamma bayan sallar la'asar ta fita siyayyar abinda zatayi amfani dashi tunda a Hostel zata zauna saboda tazarar Makarantar da Gidansu.
Doguwar Riga mai taushi da faÉ—i taa sa ta naÉ—a mayafin da ya yiwa fuskarta da ya rage rama kyan gaske. Waya da card É—in da zatayi siyayya dashi kawai ta É—auka.
Wajen siyayya mafi girma a Birnin Abyad ta nufa saboda a can zata samu duk abinda take so.
Tun shigowarta ta hango Sufyan hannunsa sarƙafe da na Macen da bata sani ba (Sumaya).
Ya yi kyau irin kyan da yake buri, ya ƙara haske da ƙiba kamar ba Sufyan ba. Macen ce ta fara hangota kamar ta Santa, sai ta ƙara ƙanƙame hannun Sufyan cikin kishin da ya bayyana a saman fuskarta. Naila ba ta nuna ta gansu ba, ta fara ɗaukar abinda ya kawota.
Duk yadda Matashiyar da ke tare da Sufyan ta so janye hankalin daga ɓangaren da Naila take sai da ya waiwayo.
Da farko bai gane Naila ba sai daga baya. Hannun Sumaya ya saki da sauri ransa na suya, hassadar yadda ta canza har ta samun ƴanci da kuɗin yin siyayya a wajen da ya kawo Budurwarsa na cin zuciyarsa. Naila tana sane da tahowarsa kafin ya ƙaraso ta yi wuf ta nufi wajen biya. A kwai mutane a wajen don haka ya juya ya na ɗaukar komai a hanzarce don suyi su gama, bai damu da yadda Budurwartasa take ƙunci ba.
Lokacin da ya iso da jibgin kayan siyayyarsu lokacin Naila ta nufi ƙofar fita.
Yaso jirkintawa su gama biya amma ganin kamar hakan zai ɗauki lokaci har Naila ta ɓacemasa kawai sai ya miƙawa Sumaya card ya bi bayanta da sauri ba tare da tsayawa kallon ƙuntatacciyar fuskar Sumaya ba.
Ya na fitowa Naila tana shiga Taxi kafin ya shiga Mota tuni mai Taxi ya bar wajen.
Lafiyayyen motar da Company Dhahab suka siyamasa ya shige a hanzarce. Da speed ya bi bayansu kar su tsere mai, ganin sun É—auki wani hanyar daban ba na gidan daya sani ba sai ya ji hassada na naiman kassarashi zuciyarsa na tiriri.
Naila suna isa gare É—in Makarantarsu da É—an hanzari ta sauko daga Taxi dama tun a ciki taa sallamesa.
Gate É—in Makarantar nufa hankalinta a kwance duk da ta hango motar da na ke kyautata zaton na Sufyan ne.
ID ta nuna ta Securities su ka barta ta wuce.
Tana shiga ta ƙara shiga Motar da zai kai ta har bakin Hostel ɗinsu. Sai a lokacin ta saki ɗan dariyar da ya ƙaramata kyau tana hasaso irin ƙuncin da Sufyan zaiji domin tasan ko shi yafi kowa kuɗi baza'a barshi ya shigo ba, tunda bashi da Numbern wayar kowa kuma bai san kowa ba a Makarantar.
Sufyan sai ta nutsuwarsa ya yi bayan ya yi parking domin kai tsaye suka hanashi shiga kamar yadda ya so.
Ba irin bayanin da bai yi ba, babu kuma irin rantsuwar da baiyi ba shi Mijin Naila ne amma suka nuna su sam basu santa ba duk kwatancen da ya yi musu.
"shin yamasan a gaban wani University yake tsaye kuwa? Securities suka tambayeshi.
Sai a lokacin ya ɗaga kai yana kallon sunan da yake jiki saman Dogon Ginin ɓaro-ɓaro a take ya ji hassada na naiman kasheshi jirin baƙin ciki na naiman kai shi ƙasa. Sum-sum ya dawo wajen Motarsa yana jin muzanta a karon farko tun bayan tafiyarsa Babban Birnin Abyad.
Da ya shiga Mota kasa jurewa ya yi, ya fara dukan kujerun motar ya na surutai "Ni Naila zata yiwa taurin kai, har ta yarda su kawota jami'a irin wannan, wallahi! Wallahi!!! Wallahi!!! Sai nayi sanadiyyar barinta Birnin Abyad wayyo zuciyata zata fashe" ya Æ™asara faÉ—a ya na dukan saitin zuciyarsa....âœðŸ»
[7/24, 9:20 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥
SASAAL
19
Sufyan ba wannan ne zuwansa Birnin Abyad na farko ba. Tun lokacin da aikinsa ya miƙa komai ya yi mai yadda yake so ya fara kawowa Sumaya ziyara.
Sumaya macece tasan kuma abinda Sufyan yake yiwa Iyalinsa ba daidai ba ne, a addini har ma da al'ada amma son kai da tsanin son zuciyar kutsa kai cikin abinda batasan mafarinsa ba yasa take ganin kamar Sufyan ma son Iyalinsa ya ke yi banda haka ya saketa mana kawai ita ya gabatar da ita a wajen Iyayensa suyi aurensu. Har layin tasha zuwa taga yaya Naila take..
Son zuciyar Sumaya kaÉ—an ne akan na Mahaifanta, domin su cewa su kayi bazasu ba shi Sumaya ba har sai ya saki Naila.
SUMAYA
Da Sufyan ya dammaƙa mata Card zuciyarta ce kawai bata haɗiya ba, kishi ya toshe komai nata gani take yi duk kuɗin da Sufyan yake ikirarin ba shi da shi Naila yake kashewa ba Iyayensa yake turawa ba kamar yadda ya faɗa. Saboda tun fara aikin Sufyan ranar ne kawai tasan ya yi mata siyayya ma su nauyin kuɗi, duk zuwa idan ya yi ƴan kuɗine yake rabawa Mahaifanta. Amma ga Matarsa nan tayi kyau tasa sutura na alfarma, saboda kishin ma kar wani ya ganta har rufa mata baya ya yi yana muzurai sai ka ce wani sakarai. To kenan yaudararta ya ke yi da ya ce ba ya zuwa wajen Naila?
Da kuka shaɓe-shaɓe ta tari Taxi ta nufi Gida.
SUFYAN; bayan ya gama bige-bige da ayyana irin ramuwar gayyar da zai yi akan abinda Naila ta yi mai sai ya É—auki hanyar Gidan su Sumaya.
Kukan da take yi da irin maganganun da take saki Iyayenta na ƙara tunzura ta ne su ka ƙara harzuƙa Sufyan, cikin tsananin fushi ya buge kofin tangaran ɗin da su ka zuba masa lemo a ciki, a take ya fashe. Sumaya tana yunƙurin zaginsa ya zuba mata marin da ya taɓa zuciyar Iyayenta, Babanta ma na yunƙurin kwasamai mari ya riƙemai hannu, kafin ya jefar da hannun da iya ƙarfinsa. Cikin isa da takaici ya ce;
"ki je mun rabu! kuma karki ƙara nemana tunda har yau baki fuskanci Naila itace mukullin ƙofar nasarata ba" yana gama faɗa ya bar madaidacin living room ɗin da aka ƙawata da kuɗin Naila kafin ya samu aiki.
Da sakakken baki ya bar su, saukar kalmarsa na "sun rabu" na cakar zuƙatansu sama da raɗaɗi marin da ya saukewa Sumaya da hannun Mahaifinta da ya jefar, saboda Sufyan da shi suke taƙama domin sanadiyyar haɗuwarsa da Sumaya rayuwarsu ta sauya ba kaɗan ba. Sumaya kuka take yi har da birgima, danasanin abinda ta aikata na mamaye zuciyarta. Sufyan baya ɓoyemata tasan da kuɗin kitson Naila suke ci suke sha a makarantar kuma sanadiyyar Naila ya samu aikin da ya ke yi, amma ita ta rasa dalilin da ya sa ta tsani Naila.
Daga wannan rana Sufyan ya ƙauracewa kiran Sumaya. Ga hotuna da ya ke saki masu kyan gaske a shafukansa, duk domin Sumaya tasan ko a jikinsa. Ya yi narasa kuwa domin Sumaya ƙara gigicewa tayi. Ba dare ba rana kullum sai ta turamai saƙo.
Rasa yadda zata shawo kanshi yasa ta turamai saƙon tayasa fakon Naila, har ya samu damar mayar da ita Yankin Tudu kamar yadda yake yawan faɗe tun kafin ya tafi Babban Birnin Abyad.
cikin jimami ta zauna zaman jiran amsar da zai bata.
NAILA; cikin nasara da wadatacciyar nutsuwa ta fara gudanar da karatunta.
A ɓangaren sana'arta kuɗi ta ke samu ba kaɗan ba, saboda ƴaƴan manyan mutane da suke Campus ɗin su waɗanda kansu ya ke kitsuwa a wajenta suke yin kitso.
Cikin watanni ta ƙara zama wayayyiyar mace sai sanyin kyau da ɗabi'a. Ba ta shiga sabgar da bai shafeta ba tana kuma tsayawa a iya matsayina.
Tana zuwa Gida jefi-jefi musamman ranar sati. Batun Sufyan kuwa tuni ta share shi a ranta, ta mayar da hankali kan abinda ya kaita Makaranta. Yasar kullum shi yake ba ta ƙarfin gwiwar yin karatu idan sunyi waya, domin shine matakin zamanta a Birnin Abyad na din-din har ta kawo Kaaka su ƙarasa rayuwarsu. Wannan ƙwarin gwiwar da Yasar yake bata ba ƙaramin dadinsa ta ke ji ba.
A hankali komai ya yi ta sauyawa watanni na shuɗewa, shauƙin son zuwa Yankin Tudu domin ganin Kaaka na ƙara mamaye ran Naila, a haka suka fara shirye-shiryen zana jarabawar da zamu yi hutu mai ɗan tsahon da zata iya zuwa Yankin Tudu ta taho da Kaaka. Kamar yadda Yasar ya shawarceta tunda tana samun kuɗi.
SUFYAN; bai daina son Sumaya ba amma yanason ta gane shi ɗin Namijin da za'a lallaɓa ba wanda za'ayiwa hargagi ko rashin kunya ba. Ko da yaga saƙonta fuska ya yi, domin yasan ba ta da wani abun tsinanawa, kawai don ya kulata ne.
Magiya da nacinta ba dare ba rana ne ya dawo da soyayyarsu har ya fara yunƙurin tarar Mahaifansa da batun ta, tare da shawarar da ya yanke na sawwaƙewa Naila kafin ya aiwatar da ƙudirinsa a kanta.
Cikar Sufyan shekara ɗaya a ma'aikatar Dhahab yasa sukayi mai kyautar da ya hanasa runtsawa. Waya kuwa kwana sukayi suna yi da Ɗayyib, cikin isa Sufyan yake bada umarnin abinda za'ayi da kuɗin. Ba bu lissafin yinƙurin yin wani abu na cigaban Yankinsu a kason kuɗin da duk wani kuɗi da yake turawa sai Gidan Sarautar su da aka ƙara ƙawatawa, musamman ɓangaren Mahaifansa Ɗayyib da ɓangaren Kakansa Jalal.
Ba bu wani tsarin tallafi da suka tsiro da shi a matsayinsa na Ɗan Yankin da ya samu cigaba a Babban Birnin Abyad sai dai mutanen gari su gani a jikin Iyayensa, ƴan Masarautar su da Gidajensu, duk da mummunar talaucin da suke fama da shi. Har lafiyayyen titi aka shimfiɗa daga farkon shigowa Yankin Tudu har ƙofar Masarautar su.
A ɓangaren Ɗayyib da Sufyan ya fara samun kuɗi Gidan Game ya buɗe ƙato matasa su samu kuɗi suyi ta bugawa Yara kuma su sato kuɗin Mahaifansu. Abun takaicin sai Matasa da Iyayensu sun sha wahala sun ƙera Tukwane sun samu an siya daƙyar sai Ƴaƴan su kwashe kuɗin su gudu gidan Game ɗin Ɗayyib.
Cikin ƙanƙani lokaci shima ya fara zama hamshaƙi.
Dukka wannan facakar sai dai Æ´an uwan Naila da Kaakarta su ji labari, kamar dai gama garin mutane ba surukan Sufyan ba.
Æullowar batun auren Sumaya da Sufyan, ya tayar da Æ™ura a tsakanin Hindu da ÆŠayyib don sai da sukayi faÉ—an da ya kaita ga tafiya Gidansu. Ta kafe bata yarda da auren ba matsawar ita ta haifi Sufyan domin malaman tsibbunta sun sanar da ita sakin Naila zai rusa komai, haÆ™urin mutanen da suka zubawa Sufyan É—in ido ya na zaluntarta har suka É—aukesa aiki zai Æ™are daganan suyi masa É—aurin talalar da zai mutu a É—aure.
Sam ÆŠayyib bai yarda da batun Hindu ba, acewarsa É—aukakar Sufyan daga Allah ne, babu wata Naila don haka dole su bar Sufyan ya rayu da abinda yake so.
Ankai ruwa a tsakanin su har sai da Jalal Mahaifin ÆŠayyib ya shiga faÉ—an da suke yi a sirrince don bakowa ba ne yasan Hindu bata gidan ba.
Sai da Mahaifiyar Hindu ta saka baki, sannan ta yarda da auren amma da sharaÉ—in ko zai saki Naila sai lokacin da ta yarjemai. A kan haka suka bar zancen.
Da tsananin rawar kai Sufyan yake rabon katin aurensa ga Manyan ma'aikatarsu. A cewarsa ma bai taɓa Aure ba.
Labarin auren Sumaya da Sufyan sai da yaje har kunnen Bushra, ba tare da ɓata lokacin ba ta naimi Yasar ya toshe duk wata hanya da Naila za ta iya jin labari, saboda kar hakan ya kawomata tsaiko a jarabawar da take zanawa. Kuma da zarar ta gama ya shirya mata tafiya Yankin Tudu.
A rabon Invitation card da Sufyan yake yi ne, Baturen da yake sama da shi ya bashi shawarar ya shirya katin gayyata na musamman ga GM wataƙila ya samu alheri mai yawan gaske.
Da yake Sufyan ɗan son banza ne a daren ya biya kuɗi mai yawa aka shiryamai katin gayyata na musamman. Washe gari kafin ya shiga office ya miƙawa ogansa ya bawa GM ba tare da nutsuwa ya yi tunanin maiyasa tunda ya ke aiki a Dhahab bai taɓa ganin GM ba, ko da gilmawarsa ne.
Gaba ɗaya sai Sufyan ya matsu ranar Aurensa ya zo, irin shagalin da ya tanadi maƙudan kuɗi za'ayi a Yankin Tudu na sanyashi jin alfaharin da bai taɓa jiba.
Ɗayyib da su Sarki Hammam da ya yi kwantan ɓauna kamar yana tare su ne su suka zo Birnin Abyad Gidansu Sumaya naimawa Sufyan aure. A take Iyayen Sumaya da suka matsu da komai suka ce sun bashi sati mai zuwa a ɗaura aure su tafi da Ita Yankin Tudu su je can suyi Biki, a maimakon wata ɗaya da suka tsara da Sufyan tun kafin zuwan Iyayensa ya yi rawar kan buga katin gayyata.
Iyayen Sumaya sun ce su basu da wani shagali da zasu yi bayan É—aurin Aure.
Abin takaici daga Ɗayyib har da muƙarabansa da suka zo Birnin Abyad tare ba bu wanda ya tambayi ina ƴarsu Naila Ƴar Yankin su take? a wani yanayi take ciki?. Kowannen su fuska ya yi yana dirzar duniyar da ya samu.
Da rawar jiki Sufyan yake ƙara bawa manyansa haƙurin matso da lokaci kusa an samu akasi. Wa su sun nuna zasu je wasu kuma tambayarsa suka yi babu wani shagali da za'ayi ranakun da zasu biyo bayan ɗaurin auren da zasu iya zuwa? Da sanyin jiki ya sanar da su na Yankin Tudu tunda yasan ba lallai su je ba.
Ga ɗumbin mamakinsa washe gari ya samu saƙo GM ya ce ya amsa gayyata amma ba zai samu zuwa ɗaurin aure ba, sai dai na Yankin Tudu da za'ayi In Shaa Allahu. Sufyan ihu yasa ya na tsalle, har ya fara hango irin ƙafafa da zafin kan da zai yi, inama da Naila tana wajen ya nunamata ko babu ita shi ya zama kafin Allah a Dhahab sai dai ta mutu da baƙin ciki.
Cikin walwala da son Daular da ya ke iya canza tunanin ɗan Adam lokaci ƙanƙani su Ɗayyin suka cika sati guda a Birnin Abyad.
Ranar ÆŠaurin aure
Irin fareren Turawan da suka zo ɗaurin auren Sufyan da Sumaya a Birnin Abyad ne yasa bakin Ɗayyib yaƙi rufuwa. Bayan komai ya lafa sun keɓe Ɗayyib ya murmusa cikin alfahari ya ce;
"Sufyan ina alfahari da kai akanka na fara samun cikar burina na tsayin shekaru, kaga Ubangidana ko, sam bai halarci ɗaurin aure nan ba kuma nasan yana gari, dama ina sane da shi, tun daga kan takardun da na ce ya samar maka ya ƙauracewa waya dani, to dama haka rayuwa take, yau ina jina na daban ya ya ma kace sunan wannan Ma'aikata taku mai albarka." Ya ƙarasa faɗa yana kafa lemo mai tsada a baki.
Sufyan da ke murmushin isa É—an dariya ya yi kafin ya ce "DHAHAB"
Azababben tari ne ya sarƙe Ɗayyib lemon da ya kurɓa ya soma biyomai ta hanci da baki...
NAILA; A dai-dai lokacin da Tari ya sarÆ™e ÆŠayyib Naila ta kammala haÉ—a kayan tafiya Yankin Tudu....âœðŸ»
Wanene General manager company sarrafa shinkafar Dhahab da Sufyan yake aiki a ƙarƙashin shi?😄
Maiyasa ya zaɓi zuwa wata ƙasar shagalin ta ya murnar ma'aikacin da ya ke ƙasan-ƙasansa duk da girman matsayinsa.
Yaya zaman Naila a Yankin Tudu zai kasance shin zata dawo ko bazata dawo ba? Kaaka tana raye ko bata raye?
Wani 🔥🔥 ne zai kama a Yankin Tudu?
Next page In Shaa Allah
[7/25, 8:47 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥
NAFISA ALIYU SASAAL
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.