Triplets Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: TRIPLETS BOOK 2.txt
Chapter 8 of 8
Cigaba da kukanta ta yi tana goge hawaye da majina da tissue dake saman bedside drawer kusa da ita.
"Kin dai san bana son kukan nan naki ko?" Shine abin da ya faÉ—a, kuma ya yi maganar kasa kasa kamar wadda baya son furta maganar.
Cikin sauri ta goge hawayen nata tare da dakatar da kukan nata tana faÉ—in "Kayi hakuri". "Me yasa kika yi mani alkawarin da kika san ba zaki cika ba?".
Zaro idanunta waje ta yi a É—an tsorace ta ce "Me na yi maka kuma?" Shiru ya É—an yi kafin ya ce "Daga yau na yi niyar fita daga harkarki amma kuma sai na kasa yin hakan, shiyasa kika ga tun da muka yi waya da safe ban sake kira ki ba, kuma ban turo maki sako ba saboda na saka a raina zan rabu da ke ne dan baki É—auke ni da mahimmanci ba".
Kuka ta sa mashi tana faÉ—in "Me nayi maka da zaka ce mani hakan?"
A wannan karon da ɗan ɗaga murya ya fara magana kuma da alama ransa a matukar ɓace "Me yasa kika ce ba zaki yi wa Irfan dariya ba kuma kika yi mashi har ma da kwanciya a jikinsa? Me yasa zaki yi mani hakan? Kin dai san ina da kishi kuma na gaya maki tun da wuri, ni ban shiga hakkin ki ba na barki kina hira da shi dan naga kina son hira da shi ɗin, amma me yasa ke kuma zaki baƙanta mani rai har haka? Me yasa da kuka je wajen cin abinci kika bashi abinci a baki? Me yasa zaki bari ya taɓa jikin ki lokacin da ya goge maki ice cream a bakin ki? Kin san ya naji kuwa? Kinsan adadin tafasar da zuciyata ta yi kuwa? Kin san irin cikin azabar da na wuni yau kuwa? Do you know how much i love you kuwa? Meyasa kike kokarin tarwatsa mani zuciyata? Me nayi maki? Laifi nayi ne dan nace ina son ki? Amma dai ba komai dole na koyawa zuciyata kin ki ko zan huta!!".
Sosai Akila take kuka kamar ranta zai fita, ta kasa magana saboda bata da abin da zata gaya mashi.
Sun É—auki tsawon minti goma a haka kafin ya ce "Heartbeat ki daina kukan nan haka ya isa bana son ji, kina kara mani ciwo akan ciwo kin ji ko?" A wannan karon ya yi maganar tasa cikin sanyin murya da kuma sigar rarrashi.
"Heartbeat ba zan iya yin shiru ba, ba zan iya ba". Kara yin kasa da muryarsa ya yi cike da shagwaɓa da sigar rarrashi ya fara magana "Bana son kukan ki ko kuma in ganki a cikin damuwa, hakan kuma yasa ma na kiraki yanzu saboda naga kin kasa barci kina cikin damuwa har da kuka wadda nima zuciyata ta kasa juran hakan, ki daina ki yi shiru ko kuma nima na fara yi maki nawa kukan, kuma ni gaskiya ina da wuyar rarrashi gara ma ki sani".
Kwanciya ta yi tare da rungume pillow a kirjinta ta ja bargo ta shige ciki tana faɗin "Heartbeat kasan wahalar da ni da ka yi yau kuwa? Tun karfe ɗaya na rana da na dawo cikin gidan nan nake cikin bakin ciki da ɓacin rai na ganin baka kirani ba, me yasa zaka yi mani hakan? Meyasa ka zaɓi ka wahalar da Heartbeat taka? Ko dan kasan na damu da kai ne? Muna hira da yaya Irfan amma kai nake tunani, komai nake yi fa kai nake tunani, why zaka yi mani hakan?".
Nisawa ya yi kafin ya fara magana a nutse tare da yin kasa da murya cikin salo da zai nuna maka ya san me yake yi "Heartbeat duk wahalar da kika sha baki kai ni ba, yau zuciyata kamar zata fashe nake ji, na wuni cikin tashin hankali da rashin natsuwa, na sha wahala, idan na rufe idanuna kawai ke nake gani kina kwance a karjin Irfan kina yi mashi dariya, heartbeat ya kike so na yi da rayuwata ne? Baki san yadda nake da zafin kishi da kuma zafin zuciya bane shiyasa, wlh tun da naje school yau na kasa iya komai, duk lecture da aka yi mana a banza ya tafi, ban iya jin me suke faɗe ba, ke kawai nake tunani, ba zan ɓoye maki ba yau kin cutar da zuciyata sosai da sosai".
"Na tuba ba zan kara ba ka ji? Kada ka sake yi mani hakan kai ma, idan ka sake yi mani hakan ya zo da karar kwana zan iya mutuwa wlh".
Shiru ya É—an yi kafin ya ce "Nima kada ki sake rungumar wani a gaban idanuna ko da kuwa su Yaya Akil ne, bana so, ni kaÉ—ai kawai zaki runguma, kuma ina nan zuwa har gida nan ba da jimawa sosai ba, amma dai ba yanzu ba kuma ba a kwanakin nan ba, za'a É—an jima".
Jinjina mashi kai ta yi tana kara tabbatar mashi ba zata kara ba ta tuba. To ya amsa mata da shi tare da tambayarta ina Ammie da Abba, Akil da kuma Imran.
Su na É—aki ta bashi amsa, kara tambayarta ya yi suna lafiya ko? Nan ma e ta amsa mashi da shi.
Shiru ya É—an yi kafin ya sake cewa "To ayi mani dariya mana ko zan ji sanyi a raina". Tana daga cikin bargon ta turo baki tana faÉ—in "Ni ba zan yi ba, kuma daga yau ma na daina yin dariya".
"Kai innalillahi menene a bayan ki yake tafiyar nan heartbeat?!" Ya faɗa da ɗan karfi. Ihu ta kurma tare da miƙewa ta fito daga cikin bargon, a sukwane ta diro kasa daga saman gadon tana zare idanu kuma har lokacin wayar tana a kunnenta.
Karo na farko data fara jin sautin dariyarsa mai É—aukar hankali, tun da ta ji yana dariya tasan da gangan ya yi mata hakan dan haka sai ta sa mashi kuka ita kuma.
"Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat, na tuba ba zan kara ba, amma dai idan kika sake cewa ba zaki yi mani dariya ba to fin hakan ma sai na yi maki". Zama ta yi a gefen gadon tana dafe kirjinta dan har ga Allah ba ƙaramin tsoratata ya yi ba, a tunanin ta ma snake ne ko wani abin tsoron.
Sosai ya shiga rarrashinta tare da bata hakuri yana kara gaya mata ba zai kara ba, da kyar ta yarda ta koma saman gadon ta kwanta tana zuba mashi shagwaɓa.
Dariya ya yi yana gaya mata idan wani abin ne ma zai taɓa ta ai shine na farko da zai fara tare mata shi dan kada ya taɓa ta, to ta amsa mashi da shi
Daga karshe dai shima shagwaɓar ya fara zuba mata abin gwanin burgewa dan ya iya shagwaɓa tare da rarrashin mace, duk abin da zai sanya mutun farinciki ya iya shi sosai, ga iya saka mutun dariya, hakan ma yasa Akila ta yi saurin kamuwa da kaunarsa ba kaɗan ba, hakan yasa ba zata iya jure rashin jin wannan zazzakar murya tasa ko kuma daddaɗar massages ɗin nan nasa masu kwantar wa da mutun hankali duk ɓacin rai ɗin da yake a ciki ba.
Sun sha hira sun biya missed na juna da suka yi wunin yau, ba sune suka kwanta ba sai karfe huɗu na asuba sannan ne ya ce ta kwanta ta samu barci awa ɗaya da ya rage shi kuma bari ya yi nafilar da ta hana shi yi tun ɗazun, da haka suka yi sallama cike da kaunar juna, a wani ɓangare na zuƙatansu kuma suna bakin cikin zasu yi missing na juna.
Suna katse kiran ta É—aura wayar saman bedside drawer tare da runtse idanunta ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.
Asuba ta gari, nima kuma na dasa aya sai gobe idan mai dukka ya kai mu zamu haÉ—u a Washington DC dan mu ji wani hali Musharraf da Aseef tare da su daddy suke a ciki....... Ma'assalam âœï¸ðŸ¥±
💖💖TRIPLETS💖💖
E83-84💖
💖WASHINGTON DC💖
Yau yana da class karfe 8 tun karfe 6 ya tashi ya nufi gym, good 1 hour ya É—auka yana motsa jikinsa kafin ya sha ruwan lemon cup É—aya sannan ya wuce ya koma cikin gida yana ta faman haÉ—a zufa.
Kai tsaye toilet ya kufa ya yi wanka tare da fitowa ya shirya cikin shigarsa ta mutunci ta cikakken musulmi.
Bayan ya kammala sai tashin kamshi yake yi, ya yi wani irin kyau na musamman, ba zaka taɓa cewa Michael na baya bane, ya zama cikakken gwarzon namiji, yanzu haka jikinsa ta fara murɗewa irin na ƴan uwansa saboda baya wasa da gym, safe da yamma dukka sai ya yi, da yake shi yafi siffantuwa da Lion yanzu sai ya dawo kusan kammanin Lion ɗin sak, kuma kamannin Josephine ya kara bayyana karara akan face nasa, da kallo ɗaya zaka yi mashi ba sai ka tambayi me a tsakaninsa da Josephine da kuma William ba saboda kammani, ta kowani ɓangare akwai Kamannin iyayen nasu a tattare da shi, kusan ma zaace shi kaɗai ne ya ɗauko kamanin su dukkansu, domin kuwa Lion dai da iya daddy kawai ya siffantu sai dai kama ta jini da idan ka gan shi ka ga Josephine zaka san e lallai akwai jini, shi kuma James ainahi da Michael ɗin suke ɗan kama, amma ba sosai can can ba, shi kuma Michael idan ka kalle shi kallon farat ɗaya sak fuskar Josephine zaka gani, idan kuma ka kalleshi da kyau zaka kalli fuskar daddy, kuma kunga Lion ya suffantu da daddy kaɗan shiyasa Michael yake kama da shi Lion ɗin, idanu kuma kowa da tasa, Lion dai idanun daddy ne blue eyes, brown eyes kuma na Josephine ne, dan ita ke da brown eyes irin na Michael, shi kuma James idanunsa irin na Tyson ne wato TGA kenan.
Ƴan kwana biyun nan Aseef yana busy sosai saboda shirye shiryen Exams, baya zama sosai hakan yasa ya bar gashin kansa ta taru sosai har ta ɗan sauƙo mashi a bayan wuyarsa, kuma ba karamin kyau ta yi mashi ba, shine dai kawai baya so yake askewa.
Yanzu ma tsayawa ya yi a gaban mirror yana ƙoƙarin fara rage tsawon gashin nasa, daga ta bayansa ya ji Musharraf yana faɗin "A'a my Aseef ka bar gashin nan dan Allah, wlh ba karamin kyau ya yi maka ba".
Fuska É—auke da kayatatcen murmushi ya juyo da kallonsa zuwa kan Musharraf É—in yana faÉ—in "To shikenan Uncle ai duk abin da kake so nima ina son shi, yanzu dai ina kwana?".
Murmushi Musharraf ya yi yana faÉ—in "Lafiya lou my pleasure what about you? How was your night?".
"Am fine uncle, kasan me nake so da kai?" Girgiza mashi kai Musharraf ya yi alamar A'a.
"Good, uncle tun da Allah yasa tafiyarka Nigeria yau bata yi wu ba sai jibi ina son daga yau zuwa jibin nan mu fita tare, akwai abubuwa da zamu je mu yi ciki kuma harda shopping zan je na yi maka". Jinjina kai Musharraf ya yi alamar to.
"Okey uncle ka shirya da wuri mu fita tare ka je ka kalli school namu, daga nan kuma sai mu wuce yawo, yanzu dai je ka shirya bari na duba daddy mu gaisa" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi waje, shi kuma Musharraf ya wuce zuwa nasa bedroom É—in.
Aseef yana fita kai tsaye bedroom na daddy ya nufa, babu ko excuse ya faÉ—a cikin É—akin, tsaye a gaban mirror ya isko daddy yana shafa mayukansa masu balain tsada da kuma kyau, kyakkywar farar towel ne É—aure a kugunsa da alama wanka ya fito.
Mutuwar tsaye Aseef ya yi yana kallon zanen tattoo dake a bayan daddy, zanen Lion ne wato zaki ita ce daddy ya zana a bayansa ta buÉ—e baki da waÆ´an nan zabga zabgan hakwaran nata, daga gefen kafaÉ—arsa kuma zanen kunama ne.
Shi kuwa daddy jin an shigo mashi É—aki ne yasa ya É—ago blue eyes É—in nan nasa ta cikin mirror dan ya ga wanene, dama kuma ya san cewa Aseef ne, dan ba bu mai shigo mashi É—aki da safen nan sai Aseef.
"My son what happened? Why are you looking at me like this?" Ya faɗa yana ƙoƙarin juyowa.
"Daddy I saw something like tattoo on your back". Ya faÉ—a da mamaki a face nasa. Jinjina mashi kai daddy ya yi alamar yah tabbas tattoo ne.
"Daddy tattoo? Do you know what tattoo means?". Juyawa daddy ya yi tare da cigaba da abin da yake yi yana faÉ—in "Do you know my name before?".
Girgiza mashi kai Aseef ya yi mamaki ya hana shi yin magana. "My name is dangerous Boss, i want you to know my story before, alokacin da nake da 20 to 35 year, mummyn ku ita ce first parson da ta fara sanya William ya risinar da kansa kasa, time da muke school yadda ka kalli Romeo haka nake, kowa tsorona yake ji a school, wannan tattoo da ka gani ba irin tattoo da kake tunani na shahrarrun ƴan iskan duniya bane, no wannan tattoo ne da yake nuna cewa mune manya a cikin school na mu a time ɗin, ni before ko wine bana sha, sanadiyar bakin cikin da mum ɗinku ta saka mani me yasa na fara shan wine dan na rage damuwa, a lokacin da muka yi tashe, muna kula da lafiyar mu sosai da sosai domin karantun lafiya kuke yi a time ɗin, duk soyayyar mum ɗin ku ya sanya na zama haka, lokacin dana fara ganinta a school ranar da ta fara zuwa a sabuwar student, faɗa ya fara haɗani da ita, bata san cewa mune manya a school ɗin ba, ta zo zata wuce ta jefar mani da ledar sweet a gabana, da nace ta ɗauke shine ta ki saboda tana ji da kai a lokacin ita ma, ni kuma zuciya ta ɗebeni na mareta, ai kuwa ita ma bata yi kasa a gwiwa ba ta ɗaukeni da marin da na kasa mantawa da shi har yau, dayawa daga cikin matan school namu suna haukar so na saboda kyan da nake da shi, kuma kowa yana tsorona amma sai ga mum ɗin ku ta mareni a ganan kowa da kowa, raina ya yi mugun ɓaci ba kaɗan ba, ban san time da na fara dukanta ba dan haushi, da kyar su HERRY suka ruƙe ni, daga nan ne fa muka saka kafar wando ɗaya da ita a school ɗin, kullun idan ta zo sai na takurawa rayuwarta, ga shi kuma kasa da mu take, lokacin muna kusa da shekarar kammala wa, ma'ana saura shekara ɗaya mu gama, na saka mata ido na dameta, duk abin da take yi sai na takura mata, daga takura ya zama soyayya har ya kai mu ga aure, abin da ya sa kaga ban cire tattoo ɗin nan ba saboda ina tuna lokacin samartakan mu, mu biyar ne a lokacin, amma yanzu uku sun mutu remain me and herry, sannan wannan kunamar da kaga na zana a kafaɗata ba ni na yi ba, mummynku ta zana mani da hannunta, ina matukar kaumarta fiye da tunaninka, shiyasa na kasa goge wannan tattoo ɗin dan ita ta yi mani kuma tana kaunar shi, shiyasa na barshi dan in rinƙa tunata da shi, mutuniyar kirki ce, daga baya ne ta canza kamar ba ita ba".
Ya kai karshen maganar yana hawaye, da sauri Aseef ya kariso wajensa tare da fara rartashinsa yana bashi hakuri, rungume juna suka yi.
Sun ɗan jima a haka kafin nan Aseef ya sake shi yana gaya mashi zai ta fi school, to ya amsa da shi suka yi sallama Aseef ya manna mashi kiss a goshi kafin shima ya mannawa Aseef ɗin a kumatu, Aseef yana matuƙar kaunar daddynsa while shima yana kaunar ƴaƴan nasa, Allah ne kawai yasan dalilin da yasa su basu wani son shi sai Aseef ɗin, shima Aseef dan yana sabon mutun ne Shiyasa, babu komai a ransa sai kaunar mutane.
Aseef na fita daddy ya zauna saman table chair yana hawaye, yau ya tuna da soyayyarsa ta baya, ya tuna irin diramar da suka kwasa da Mummynsu a school, tsumin soyayyarta ta taso mashi, ji yake yi kamar ya ganshi ga shi ga ita sun koma kamar lokacin da suke zuba soyayya a school nasu, mum ta haɗu over, daga baya kuma kome ya tuna sai ya goge hawayen nasa ya miƙe ya cigaba da abin da yake yi kamar ba shi ba.
Shi kuwa Aseef yana fita part nasa ya koma. A palo ya isko Musharraf yana tsaye ya shirya cikin kananan kaya, ya yi kyau over, sosai Aseef ya ya bawa kyan da ya yi sannan suka jera suka fita zuwa palon kasa.
"Uncle mu wuce ko mu tsaya mu yi breakfast?" Cewar Aseef. Musharraf na ƙoƙarin amsa mashi magana sai suka ji uncle Herry ta bayansu yana faɗin "Michael wai ya har yanzu TGA shiru ne?".
Juyowa Aseef É—in ya yi yana kallonsa fuska É—auke da murmushi ya ce "Uncle Herry uncle T yana nan dawo soon, wani aiki suka tafi" to uncle Herry ya amsa da shi.
Dawo da kallonsa kan Musharraf ya yi yana kara tambayar shi, shin su yi breakfast ne ko dai su wuce kawai, da yake Musharraf ya san halinsu sarai basu cin abinci a waje dan tsabar shegen kyankyani da suke da shi kamar me, basu yarda su ci abincin da wata hannu ta girka bayan sojojin gidan, suma sojojin dan saboda suna kallon duk yadda suke yi masu girkin ne Shiyasa, suna kallon komai a tsabtace suke yin sa, ba dan haka ba da ba zasu iya ci ba, Triplets gabaɗayansu ne masu wannan shegen kyankyani kamar me, harta James mai ɗan saukin kan, idan kana son ka ga ɓacin ransa to ka kawo datti a filin da yake, yanzun nan zai haɗa maka jini da majina a fuska, sun yi mugun tsanar abin kyama ko datti. Musharraf ya san ko sun fita Aseef ba zai taɓa yarda ya ci abinci a wani waje ba, sai dai ya kai Musharraf ɗin wajen cin abinci shi kuma ya zauna har sai sun dawo gida ya ci, yasan halinsa sarai, sanin hakan yasa ya ce a'a su hakura su yi breakfast a gida tukun nan su fita, to Aseef ya amsa da shi sannan suka nufi dining room shi kuma uncle Herry ya koma bedroom nasa.
Suna zuwa wajen waÆ´an nan jibga jibgan bodyguards É—in suka fara sara masu kamar yadda sojojin gidan suke yi masu.
Shafa kumatun ɗaya daga cikin bodyguards ɗin Aseef ya yi yana faɗin "Wai ku bakwa gajiya da tsayuwa ne? Haba mana ku rinƙa samun huto, kowace rai tana son hutu fa my people's". Mamaki ne ya kama bodyguards ɗin nan, har wani kallon kallo suke yi wa junansu.
Zama Aseef ya yi yana faɗin "Bodyguards shidda kuje ku kwanta ku huta idan karfe 2 na rana ta yi sai ku zo ku karɓi ƴan uwanku shiddan nan suma su je su huta sai can dare ku haɗu gaba ɗaya ku kwanta ku huta. Abin nufi a nan Aseef ya raba masu aikin kenan, bawan Allah mai adalci yanzu kwata kwata baya son yaga wani ko wata suna wahala, Allah sarki musulci duniya ne wlh, babu abin da ya kai shi daɗi, kuduba kafin ya musulta shine fa yake cewa zai yankewa masu girki hannu da wuƙa, yanzu kuma ya musulta yau an wayi gari har hira da wasa da dariya yake yi da su, Allahu Akbar, Allah Alhamdulila da ya kasance muna a cikin adddinin musulci, zama musulmi babbar ni'ima ce wadda ba kowa yake samun wannan damar ta ni'imar ba.
Tsabar mamaki da farinciki bodyguard É—in nan sun kasa magana, sai kallon juna kawai suke yi. Ganin haka yasa Aseef É—in ya sake ce masu "Mamakin me kuke yi? Ni É—in dai Michael nine, kuma nine na baku wannan hutun, duk kuma wanda ya zo saman table ya ce ina sauran, ku ce nine na basu hutu, wai ni kam shin mu nawane ma a gidan nan da bodyguards uku ba zasu isa su yi serving namu abinci ba? Kawai dai sai an wahalar da bayin Allah a rayuwar nan ta duniya, kai kaÉ—ai sai ka ce sai ka tattare komai ya zama naka, to idan da kowa sai ya tattara komai ai da mu kam ma kwata kwata duniyar ma ba zamu zo ba, Allah mai iko, to daga yau ma na raba ku, bodyguards huÉ—u ne zasu yi serving na abincin safe, idan mun gama breakfast su tafi suje su kwanta su huta, sai kuma idan lokacin cin abincin rana ta yi, kafin mu zo saman table sai bodyguards huÉ—u waÆ´an da zasu yi serving abincin rana su kuma sai suzo su kara gyara table É—in kafin mu zo, da daddare ma haka, kun ga ku sha biyun nan kowa da hurhuÉ—u zaku yi aiki".
Zube gwiwowinsu a kasa suka yi tsabar murna da farinciki har da hawaye suka yi, bayin Allah ashe suna gajiya da tsayuwar da suke yi na 24 hours É—in nan, ashe suna shan wahala sosai.
Ganin sun zube a hasa suna hawayene yasa Aseef ya miƙe shima ya tsugunna a gabansu yana tambayarsu ko lafiya? Ko dai hutun ne basu so?".
Har wani ja baya suka yi ganin shima ya zube gwiwowinsa a ganansu, sun tsorata sosai, addu'a suke yi kada Lion ya ga Michael ya zube a gabansu ko wani daga cikin gidan ya ce sun yi wa Michael É—in wani abin ne a kashe su a banza.
Da kyar Aseef ya shawo kansu suka yarda suka kuma gane cewa e lallai Aseef É—in ne, kuma shi ne ya zama mai adalci haka, sun yi murna sosai, Aseef bawan Allah da kansa ya yi ta goge masu hawaye yana mai gaya masu addinin musulunci addinine wadda ya Æ´anta ko wani É—an adam, dan haka suma Æ´antattune, suna da Æ´anci, nan take biyu daga cikinsu suka ce ai sun san addinin musulunci sosai, suna Æ´awan ganin musulmai a Media sun san musulmai suna da kirki sosai, addinin akwai adalci sosai dan haka su zasu musulta.
Ba karamin daÉ—i Aseef ya ji ba, a wajen ya basu kalmar shada tare da basu kyautar makudan kuÉ—aÉ—e, sosai su ka yi farinciki fiye da tunanin mai tunani, su kuma sauran sai nazari da tunani suke yi akan addin.
Da haka Aseef ya ce suma waÆ´an da basu musultar ba su bashi account number bari ya yi masu kyauta domin yau ranar sadaka ce, yau duk sadakar da zai yi yana fatan Allah ya bawa Musharraf ladan, uncle Musharraf zai yi wa sadaka.
Haka kuwa akayi, dukkansu saura goma da basu musultar nan ba sai da Aseef ya sanya masu kuÉ—i a cikin account nasu, sannan ya ce huÉ—u su tsaya a wajen table saura takwas É—in kuma suje su huta wa ransu sai da rana.
Da haka suka yi sallama Aseef ya ciro wayarsa ya kira number Lion.
Yau karo na farko a duk rayuwar da Aseef ya yi da Lion yau ita ce rana ta farko da ya kira Lion kira ta farko ya ɗauka, wannan shine zai nuna maka Lion yana cikin damuwa, domin dama ya faɗa maku Aseef ne kawai mai ɗebe mashi kewa da kuma rage mashi damuwar da yake a cikinta, mutane sun kasa ganewa duk tarin makudan dukiya da kake da shi ba zata iya yi maka komai ba idan kana cikin wata matsala ko jarabawa ta Ubangiji, amma sai mutane su dage sai sun yi kuɗi ta ko wace hanya, su dai kuɗi kuɗi kawai, suna ganin kamar shi ne kwanciyar hankali da farinciki, tabbas kuɗi yana sanya farinciki kuma yana maganin wata damuwar, amma fa ba kowanne ba, kuma idan ta hanyar da bata dace ba aka sami kuɗin sai ma karawa mutun azaba da zai yi a maimakon maganin matsala, kuɗi bata isa ta warware maka kaddarar da Ubangiji ya ɗaura maka ba, yanzu tambaya a nan shine wani irin kuɗi ne su Lion basu da shi? Ga kuɗi ga mulki isa da duk wani abin da bawa yake ganin shine jin daɗin duniya, sune ke mulkar kasar baki ɗaya tun da kakansu ke a kan kujerar president, ga Lion da babbar muƙamin da babu biyunsa, sannan ga jarumta na iya tunkarar komai da zai kawo masu matsala, uwa uba ga makudan kuɗaɗe da su kansu basu san iya kan shi ba, amma kuma sai me, ga shi dai kullun suna cikin damuwa, daga Lion har James ɗin kullun suna cikin damuwa, Aseef ne kawai bawan Allah wadda bai san komai ba sai kaunar mutane, shine kawai yake cikin farincikin da har yake sanya ƴan uwan nasa farinciki, yanzu wani idan ya ga mutun irin Lion ko ya ji labarinsa sai ya ce shikenan su kam ba zasu taɓa shiga damuwa ba, dan suna da kuɗi, to ga dai shi nan kullun cikin binciko wani matsalar suke yi suna shiga damuwa.
"Hello Lion" kamar dai kullun wannan halin tasa tana nan idan aka yi mashi magana sai ya jima kafin ya amsa.
"Aseef what is going on?" Shine abin da Lion ya tambaya bayan Æ´an mintoci kenan.
"Lion please ina son kasa Tyrone ya tura wa duk wani maaikacin da muke biya albashi a gidan nan sadaka, tun da shine dama mai biyansu albashi, a hannunsa komai yake, to ya sanya masu kuÉ—i a account nasu da nufin Allah ya bawa uncle Musharraf lada ka ji ko?" Shiru Lion ya É—an yi na Æ´an mintoci da ba za su wuci 5 ba.
Can kuma sai ya ce "Okey what about your Exams?" Nan Aseef ya gaya mashi e next week zai fara exam É—in yanzu ma school zai ta fi, to Lion ya amsa da shi tare da ce mashi ya kula da kansa, daga nan suka yi sallama.
Yana ajiye wayar suka fara cin abinci shi da Musharraf a cikin plate É—aya saboda tsananin kaunar juna da suke yi, sauri sauri suka ci abincin dan karfe takwas ta kusa.
Suna kammalawa suka wuce izuwa parking space na gidan.
Yau ma dai tare da su Lucky Aseef ya tafi, sai dai kuma yau su Lucky dukkansu a gidan baya suka zauna, uncle Musharraf ya zauna a gidan gaba.
Da gudu Aseef ya figi motar suka hau titin zuwa bakin gate ɗin gidan, basu wani ɓata lokaci ba suka fice daga gidan.
Sai da suka fita Aseef ya tuna bai bawa Brady abinci ba, hakan yasa ya juyo da kan motar ya dawo ya ba shi abincin, dan ya san Brady baya yarda da kowa a gidan idan ba Lion ba sai kuma shi, to ko wani ya kai mashi abinci ma ba zai ci ba.
Bayan ya bashi abincin ne kuma suka wuce Harvard University.
Suna zuwa Aseef ya kai Musharraf office É—in É—aya daga cikin malamansu wanda suke shiri da shi sosai, da ya kai shi ma sai da ya gayawa uncle É—in nasa ya kula mashi da uncle Musharraf sosai da sosai bari ya yi attending lecture yana zuwa.
Da haka suka yi sallama ya bar su Lucky kuma a wajen motarsa suna gadi.
After 2 hours ya dawo ya É—auki Musharraf suka bar school É—in zuwa shopping kamar yadda ya faÉ—a.
Sosai Musharraf ya É—auki duk kayan da yake so, ciki kuma har da jallabiyas da dama, bayan shi kuma ya kwashi tsaraba yadda yake so, yana É—auka Aseef yana kara mashi wani, duk abin da ya É—auki guda É—aya sai Aseef ya kara mashi uku akansa.
Sun zo daidai wajen sayar da kayan sanyi Aseef ya yi karo da wani black guy, É—an baya kaÉ—an Aseef ya yi kafin ya ce sorry, shi kuma guy É—in sai ya ce kayi hakuri sannan ya wuce, shiru Aseef ya yi yana kallon guy É—in har ya wuce yana kuma maimai ta kalmar kayi hakuri da guy É—in ya ce.
Taɓa shi Musharraf ya yi yanan faɗin "Kana mamakine dan ka ji ya yi Hausa?" Juyowa ya yi yana faɗin "Uncle Musharraf what is Hausa?" Nan Musharraf ya gaya mashi Hausa tana ɗaya daga cikin yarukan Nigeria.
Murmushi ya yi yana faɗin lallai sai an koya mashi yaren nan, ko Musharraf ya koma za su rinƙa yin lecture Hausa ta waya, to Musharraf ya ce, kuma ya ji daɗi zai koyawa ɗaya daga cikin TRIPLETS Hausa.
Haka suka kammala sayayyarsu suka wuce zuwa masallaci domin azahar ta yi, ko da suka je Masallaci a mota suka bar su Lucky su kuma suka shiga ciki.
Bayan sun idar da sallah ne suka fito, suna fita suka haɗu da Aryan yana ƙoƙarin shiga Masallaci hannunsa na riƙe da kwalin dabino mai ɗan girma.
Ganinsu yasa ya kariso wajen da sauri dan yanzu ko Aseef yana sanye da face mask Aryan ya riga da ya san shi, yana gane shi, su kuma Triplets dama duk in da zasu je da face mask a fuskarsu.
Yana zuwa Aseef ya miƙa mashi hannu suka gaisa yana tambayar shi akan me bai zo ya yi sallah a cikin jam'i ba? Ya yi maganar kuma yana karɓar dabinon sadaka dake a hannun Aryan ɗin, ko wace rana Aryan yana zuwa da dabino ya raba sadaka yana addu'ar Allah ya kai wa Aseef ladar, dan Aseef ya yi masu komai a rayuwa, yanzu ga shi shagon da Aseef ya buɗe masu ta kara kirman sosai saboda sada da suke yi tare da kyautatawa al'ummar Annabi.
Aryan bai taɓa tunanin cewa Aseef zai ci wannan dabino ta sadaka ba, sai kuma ya ga ya deɓi guda shidda ya bawa Musharraf uku ya riƙe uku, duk da yake dabinon a wanke take sai da Aseef ya sake wanketa tas sannan ya sa ɗaya a bakinsa yana yi wa Aryan faɗa akan ko me yake yi kada ya kuskura ya sake bari Sallah ta sake wuce shi, idan ba haka ba zai bashi hukunci mai tsanani domin yanzu a kani na jini Aseef yake ɗaukar Aryan, shiyasa idan ya yi ba daidai ba Aseef ɗin yake cewa zai hukunta shi.
Hakuri Aryan ya bashi tare da yi mashi alkawarin In Sha Allah sallah ba zata taɓa sake wuce shi ba, zai rinƙa ƙoƙari ya zo akan lokaci, yanzu ma toilet ya shigane Shiyasa, amma ya zama dole ya rinƙa bin jam'i matukar yana son cigaba a rayuwarsa.
Jinjina kai Aseef ya yi kafin su sake gaisawa da Aryan É—in daga nan kuma suka rungumi juna, bayan sun raba jikinsu ne kuma Aryan ya rungumi Musharraf dan shi Aryan a yayan Aseef yake kallon Musharraf, bai damu da cewa Musharraf baki ne akan hasken Aseef ba, shi dai kawai tun da ya gansu a tare kuma kullun suna a tare shikenan, amma fa batun kyau, Musharraf fa kyakkywar gaske ne, shiyasa da farko JAMES ya kira shi da balarabe, kuma yana É—aya daga cikin dalilin da ya sanya Aryan ya yi tunanin ko dai yayan Aseef É—in ne dan kyau dake a gare shi shima.
Sallama suka yi Aseef ya ce Aryan ya je ya yi sallah kada lokaci ta kure, to ya amsa tare sa wucewa cikin masallaci, su kuma suka sauƙo kasan stap ɗin zuwa wajen motar su.
Kamar yadda aka saba jama'a ne sosai suka taru a wajen motar suna jiran isowarsu dan Aseef ya saba yi masu sadaka, yana zuwa kuwa ya zaro kuÉ—i ya fara raba masu kamar ko da yaushe, yau duk sadakar da ya yi yana addu'ar Allah ya bawa Musharraf ladan ne.
Sosai yau ma ya yi sadaka, sai da ya sanya gaba É—aya mutanen dake a wajen farinciki sannan suka shiga mota zuwa gida.
Suna a kan hanya ne yake gayamawa Musharraf gobe kuma a account ɗin Areef zai ɗebi kuɗi ya zuba a account nasa dan kuɗin sa ya yi kasa, kuma ya ga ji da karɓar kuɗi a wajen Lion, zai bar Lion ya sha iska na kwana biyu, yanzu zai koma account ɗin Areef daga nan kuma sai account na uncle T, duk sai ya kwashi kuɗinsu ya yi ta sadaka ko Allah zai sanya suma su musulta, bare ma uncle T.
Sai dariya Musharraf yake yi mashi tare da yi mashi addu'ar Allah dafa mashi ya gama karatun shi shima ya kama aiki dan ya tara kuɗin kansa, dan ma Allah yasa ƴan uwan nasa suna matukar kaunar junansu, kuma basu damuwa dan wani ya taɓa dukiyarsu ma bare kuma shi da yake cikonsu, wata zubin daddy da kansa yake cewa Aseef ɗin ya zo ya ɗebi kuɗi a account nasa iya yadda zai buƙata, da yake daddy ba abin da yake yi da kuɗin suna zaune, tsawon shekaru yana aiki, ya tara makudan kuɗaɗe, kuma yanzu ma kullun sai kuɗi ta shigo Account nasa saboda babbar hospital ɗin dake Washington DC tasa ce, shi ya gina kayansa da kansa, kullun cikin kuɗi yake ko bai je aiki ba, ga uncle T shima akwai kuɗi sosai, kuma dukkansu Aseef ya san sirrin bankin su, dan shine bashi da aiki sai dai a bashi kuɗin, shiyasa dan ya rage masu wahala suka nuna mashi komai na daga siririn account nasu, ya ciri kuɗi time da yake so dukka ga card nasu a cikin ɗaki.
Suna zuwa gida ya fara mayar da su Lucky É—akin su kafin nan ya wuce izuwa part nasa, soja É—aya ne ya kwasan musu sayyayar da suka sawo izuwa part nasu.
Aseef yana shiga toilet ya wuce ya yi wanka sannan ya zo suka ci abincin rana bayan shima Musharraf É—in ya yi wanka kenan.
Bayan sun gama cin abinci ne suka zauna Aseef ya ce Musharraf ya fara koya mashi yaren Hausa, to Musharraf ya amsa da shi sannan suka fara da gaisuwa.
Idan Musharraf ya ce ina kwana sai Aseef ya ce innkowa saboda harshen a lanƙwashe take ba ta taɓa furta kalma makamanciyar Hausa ba, abin ma dariya ya rinƙa bawa Musharraf har da hawaye saboda dariya, kunsan idan aka ce yare ba naka ba to fa sai a hankali zaka sha wahala wajen iya furta shi, ai kuwa Aseef dai ya sha bakar wahala har haɗa zufa ya yi wajen dole dole sai ya yi hausa shi.
Wunin ranar dai a haka suka wuni a koyan Hausa, kuma a iya gaisuwa kawai suka tsaya, shima bai zauna daidai ba kawai dai ayi sha'ani. Har lokacin sallar la'asar ya yi sannan suka wuce masallaci, daga masallaci kuma suka wuce yawata gari dan Musharraf ya ga koina kafin ya koma, har white house sai da Aseef ya kai shi, amma fa da suka je white house Musharraf ya ga ikon Allah, domin kuwa ya ga yadda ake nuna kiyayya karara, karara suka nuna mashi kiyayya dan shi bakar fata ce a cikinsu, da Aseef ya lura da haka sai ya ce su tafi kawai dan baya son hayaniya kuma baya son abin da zai ɓatawa Musharraf ɗin rai, shima Musharraf ɗin tafiyar ta fi mashi alkhari.
Suna barin white house suka sake lulawa duniyar yawo har cikin New York basu bari ba.........nu kuma na haÉ—a kayana zuwa
NIGERIA dan na ga me yake gudana, wata kila kafin mu dawo su Musharraf ma sun dawo.
# GIDAN LIONðŸ¦
Yau dai Rimsha ta riga Imran tashin daga barcin safe, ba laifi kafar tata ta É—an sake ta, ita kuwa jelly ko tashi sallar asuba ta kasa yi, Imran ba dan ya so ba ya kyaleta ta cigaba da barcinta.
Misalin karfe 7 na safe Rimsha ta fito, ta ci wankanta cikin wandon jeans palazo, ta kasa a buÉ—e ta sama ya matseta, sai Æ´ar T-shirt da ta sanya a jikinta, ta yi kyau matuka kamar ba ita ba, yanzu da yake tana girma wani sihirtaccen kyau take karawa, ga shape nan kamar me ba'a magana, akwai hips irin mum É—inta, sannan akwai tula tulan breast irin na gwaggo, ga breast É—in tata a sama sannan ga su da faÉ—i sosai alamar ba zasu kwanta ba, komai zamzam tamkar ita ta yi kanta, sai tashin wani fitinannen kamshi take yi, da kyar ta sha bakar wahala ta É—aure wannan curly hair nata, yana da tsantsi sosai baya É—auruwa ta daÉ—i, bayan ta É—aure shi sai ta sanya turban cap a kanta mai shegen kyau launin blue kalar jeans É—in jikinta, shi kuma rigar jikinta karine tas kamar yanzu ta ciro shi daga ladarsa.
Tana fito palon sama ta nufi hanyar sauka izuwa palon kasa, har zata wuce sai ta hango bedroom na Lion a buɗe, lallaɓawa ta yi ta nufi wajen da nufin ta leƙa ta ga ko zata samu ganinsa, ai kuwa bata kai ga leƙawa ba ta ji takun manya ta bayanta yana haurowa saman benen, ya je ne dama ya bawa Areef magungunansa da Dr Tyrion ya bada ya rinƙa sha, an samu an yi mashi aiki cikin nasara yanzu sauƙi kawai suke jira.
Ai kuwa ko ba'a faÉ—a mata ba tasan cewa tabbas Lion ne mai wannan taku, da wani irin mahaukacin gudu ya watsa ta shiga bedroom nata, tana shiga shi kuma yana shigowa cikin palon, lumshe dara daran blue eyes É—in nan nasa ya yi, tabbas ya ga geftawar abu kamar mutun ya shiga bedroom nata, sai dai bai san daga ina ta fito bane.
Shiru ya ɗan tsaya, jikinsa na sanye da wasu irin kaya masu haukata kwakwalwar wadda ya kallesu, riga da wando ne dukka iri ɗaya, launin ash color mai ashe ne, sai walwali kayan suke yi, rigar ya yi kamar T-shirt amma ba t-shirt bane, suna da bala'in laushi sosai, da alama kuma kayan barci ne, sai tashin wannan sihirtaccen kamshin nan nasa mai kwantar da hankalin mai shaƙa yake yi, ya ɗaure dark black curly hair nan nasa a bayan wuyarsa, sannan ya bar wannan guntu na gaban goshin, kallo ɗaya zaka yi mashi ka gane jikinsa a mace yake domin kuwa ga shi nan dai sai wani faman lumshe idanu yake yi kamar mai jin barci.
Bedroom nasa ya shige domin kuwa kwakwalwarsa ta gaya mashi wace ce ta gifta É—in, dan yasan ba Imran bane, bai damu ba saboda yasan ai tana zuwa wajen Imran, so ya yi tunanin daga É—akin Imran É—in ta fito.
Ita kuwa tana shiga bedroom nata ta laɓe a bakin kofa tana kallonsa ta mahangar kofar, shi kuma baya ganinta, a yaune ta samu damar kallon fuskarsa sosai a zahiri, ba a camera ba, ba kuma a hoto ba, wani irin sake haukacewa da kaunarsa zuciyarta ta yi, ji take yi kamar ta je ta rungume shi, har wani zogi zuciyarta take yi mata, baiwar Allah.
Ta jima tsaye a wajen tana tunani kafin ta sake fitowa ta nufi palon kasa. Babu kowa a palon dan haka sai ta shiga cikin kitchen ta É—ebi fruits a wani kyakkywar plate mai shegen kyau da tsada ta fito ta nufi waje harabar gidan baki É—aya.
Tun da ta fito sojan dake tsaron gate É—in nan ya zuba mata idanu, yana zaune shi da Mark kamar dai jiya, sai hira suke yi. Ganin ya yi shiru yana kallon wani waje ne yasa Mark ya juyo dan ya ga me yake kallo ya É—auke mashi hankali haka, ganin ita ce kamar wata tauraruwa a tsakiyar duhun dare ne ya sa ya daka mata tsawa akan ina zata je? Jikinta har ya soma karma ta ce garden zata je, daga nan bai sake yi mata magana ba ta wuce ta nufi garden É—in, shi kuma gate man ya bita da ido kamar wani tsohon maye yana wani lashe baki.
Sai da ta kure wa ganin sa ne ya ce "Mark i really like this girl, she is so cute". Shiru Mark bai yi magana ba kuma bai ɗago ya kalle shi ba, sauƙe ajiyar zuciya ya yi yana mai sake maimai tawa Mark abin da ya faɗa.
Sai lokacin mark ya ɗago kai cikin sanyin murya ya ce "You are not serious, Sister babbar aminin oga ce fa, ban taɓa ganin oga ya tsaya yana magana da wani kamar yadda suke magana da brother ɗin yarinyar can ba, ko tsawar da na daka mata yanzu ma dan na san ba wanda zai ji ne shiyasa, amma ba dan haka ba da ba zan yi mata ba, zan baka shawara kada ka bari idanunka ya sake kallon yarinyar nan, if not lahira zata yi baƙo, kasan dai yadda oga yake kaunar brother ɗinta dole idan abu ya sameta bro ɗin nata ya shiga damuwa, idan kuma ya shiga damuwa dole oga zai tanka maganar dan na lura baya son yaga friend ɗin nasa a cikin damuwa, to ni dai na baka shawara idan ka ɗauka ka tsira akasin haka kuma ka san sauran". Shiru gate man ya yi yana nazarin maganganun Mark.
Ita kuwa saman ɗaya daga cikin kyawawan kujerun dake a wajen ta je ta zauna, wani irin daɗi ta ji lokacin da hancinta ya shaƙo mata kamshin perfume ɗin Lion, alama ya nuna yana yawan zama a wajen kenan, dan kuwa gaba ɗaya wajen kamshin perfume nasa ne yake tashi.
Cikin natsuwa ta fara yankawa kanta fruits É—in tana sha, already a wanke suke daga fridge ta É—ebo su. Har wani lumshe idanunta take yi daÉ—in apple na ratsata ga kamshin perfume É—in abin begenta dake karawa abin armashi.
A ɓangaren su Imran kuwa sai karfe 9 jelly ta farka daga nauyayyar barcin da take yi, Imran bai san ma tana period ba shiyasa ma ya yi kokarin tashinta da asuba ta yi sallah.
Tana buÉ—e waÆ´an nan dara daran idanun nata kai tsaye sai cikin idanunsa, yana zaune a tsakiyar gadon ya tsareta da ido tana kallonta. Sai tashin kamshi yake yi, ya yi wanka ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda milk color.
Wani kayatatcen murmushi ta sakar mashi tana faɗin "Yaya Imran baka tashe ni ba sai da na tashi da kai na". Shima murmushin ya sakar mata kafin ya ce "A'a na tashe ki mana, ke ce dai kin gaji sosai kika ki tashi". Turo ɗan bakin nan ta yi, a shagwaɓe ta ce "Yaya Imran wajen daddyn fa?" "Tashi ki je kiyi wanka ki yi sallah ki shirya mu tafi".
Miƙewa ta yi tana faɗin To. Sai kuma me tana tashi suka kalli jini a wajen da ta kwanta, ihu ta kurma mashi tare da rungume shi dan tana mugun tsoron jini, kuma a tunaninta ciwo ta ji, idan ta ga jini har jiri take gani, shima dai rungumeta ya yi yana mamakin daga ina wannan jinin kuma.
Bai kai ga yin magana ba ya ga jinin gaba ɗaya ya ɓata mata kayan jikinta, a nan ne ya gane jinin menene sai dai kuma matsalar ta yaya zai yi mata bayani ta gane dan yasan halinta sarai. Can dai wata dabara ta faɗo mashi akan ya kira Akila ko kuma Rimsha ɗaya daga cikinsu ta yi mata bayani, dan yasan idan su ne suka yi mata magana zata ɗauki maganar da mahimmanci saɓanin shi da suke tare a baya ko da yaushe.
Haka kuwa aka yi, ya kira layin Akila bata ɗauka ba lokacin tana waya da ɓoyayyen masoyinta, kiran Rimsha ma ya yi a waya, a lokacin ita kuma ta gama shan fruits nata har ta dawo cikin gida tana kwance a bedroom nata, bugu ɗaya ta ɗauka ya ce ta zo ɗaki ta same shi, to ta amsa mashi da shi sannan ta fito ta zo.
Jelly na kwance a jikinsa tana kukan bata son ganin jinin nan, mamaki ne ya kama Rimsha akan wace ce jelly kuma.
Alama ya yi mata da hannu akan ta kariso saman gadon, da sauri ta kariso. Cke da jin kunya ya gaya mata abin da yake faruwa da kuma wace ce jelly sannan ya É—aura da cewa ta yi wa jelly'n karin bayani akan jinin.
Abin da bai sani ba shi ne ita ma Rimshan bata taɓa yin period ba, shekarunta 14 ita kuma jelly 16, jelly ita ce sa'ar JEHAN 16 suke da shi, amma dai da yake ta yi karatun addini sosai, kuma ta samu karin haske wajen mummynta sai ta amsa mashi da to.
Da kyar Jelly ta yarda ya saketa ya fice daga É—akin dan ya basu waje su ji daÉ—in yin magana, ya san halin Rimsha sarai da shegen kunya, idan yana nan ba zata yi wani magana ba.
Yana fita ta riƙo hannun Jelly ta fara yi mata bayayi ta yadda zata fahimta, a nan ne Rimsha ta fahimci e tabbas ita ma jelly ta karanta, sai dai rashin uwa ne yasa bata samu wanda zai iya fayyace mata komai ba, ita dai ta karanta mace tana jini kamar yadda suma su Rimshan suka karanta, Allah dai ya taimaka su mummy ta yi masu dalla dalla yadda za su fahimta ne shiyasa suka iya gane komai.
Sosai Jelly ta fahimta sannan Rimsha ta riƙe hannunta ta sauƙo kasan gadon ta nufi toilet dan yin wanka, ita kuma Rimsha sarkin son tsab ta gyaran bedroom ɗin ta fara yi tare da cire bed sheet ɗin ta sauya wata.
Kafin jelly ta fito ta gyare ko'ina tsab tare da feshe ko'ina da air freshener masu daÉ—in kamshi, ita kanta jelly da ta fito sai da É—akin ya burgeta ina ga kuma Imran.
Zama ta yi a saman mirror chair tana kallon mayukan Imran dan bata ma iya shafawa ba, idan baku mance ba komai daddy ne yake yi mata, ba abin da ta iya sai karatun makaranta kawai, ko abinci a baki daddy yake bata.
A takaice dai daga karshe Imran shi ya zo ya shafa mata mai sannan ya ce Rimsha ta kawo mata kayanta kala É—aya doguwar riga mai É—an girma wadda zai yi wa Jellyn, domin kunga jelly ta girmi Rimsha.
To Rimsha ta amsa da shi sannan ta nufi hanyar fita daga É—akin, har zata fita sai kuma ya ce mata ta shirya yanzu za su je gidan Abbi, da murna ta amsa mashi da to sannan ta fice.
Bayan ya gama shafa mata mai ɗin ya ɗago yana karewa surar jikinta kallo, daga ita sai towel a kirji wadda bai gama rufe mata cinyoyinta ba, wani irin yanayi ya shiga lokaci guda, ita kuma bata ma san yana kallonta ba, hankalinta na can wajen mirror tana kallon face nata, ita da kanta ta yi wa kanta kyau bare kuma shi, shi kuwa ji yake yi tamkar ya........Kayarsa, ya ƙosa su je wajen daddy a shafa fatiha ko kiss ne ya samu ya yi mata ko zai rage zafin da yake ji. TOH FAH TEAM ƊIN IMRAN, ANYI WALKIYA MUN GANKU, ASHE DAMA HAKA KUKE? DAMA WATO DAN RASHINTA A KUSA NE YASA KUKA KOMA SO SILENT KO? E LALLAI AKWAI AIKI
A haka Rimsha ta dawo ta same su, hannunta ɗauke da abaya pink color, ita ma ta sauya kayan jikinta zuwa abaya black color tare da yafa gyalen abayar a kanta, ba ƙaramin kyau ta yi ba.
Jin sallamar ta ne yasa Imran ya dawo hayyacinsa tare da miƙewa ya fice daga cikin ɗakin da sauri yana faɗin su shirya su same shi a wajen motarsa, to suka amsa mashi da shi.
Kayan ma jelly bata iya sawa da kyau ba sai da Rimsha ta taya ta, godiya ta yi mata tana tambayarta sunan ta, "Sunana Rimsha". Ta bata amsa, sake maimai ta sunan jelly ta yi sunan ya yi mata mugun daÉ—i.
Bayan sun kammala suka fita zuwa parking space na gidan, zaune cikin mota suka isko shi yana jiransu, ya je ya yi sallama da Lion ya kuma duba jikin Areef sannan ya dawo cikin motar ya zauna.
Gidan baya Rimsha ta je zata shiga, cikin sauri ya ce mata A'a ta dawo gidan gaba su haÉ—u su biyun dukka, to ta amsa da shi tare da dawowa gidan gaban suka zauna a tare, jelly tana matukar kaunar Rimsha tun da ta fara ganinta shiyasa ta yarda suka zauna a tare.
Da gudu ya ja motar suka bar gidan, sai tambayarsa Jelly take yi nan gidan waye ne, ko dai shine gidansu, bakin abin magana ya ki yin shiru kwata kwata, haka ya rinƙa biye mata har suka isa gidan Abbi, ita kam Rimsha hanya kawai take gani abinta.
Yana kashe motarsa a parking space na gidan suka fito suka jera zuwa cikin gida, gaba ɗaya kayan da jelly ta sa sun sake ɓaci da jini saboda bata sanya always ba, amma ba su lura da jinin ba, da yake ta baya ne kuma jerawa suka yi zuwa cikin palo.
Bazata Imran yake son yi wa daddy shiyasa bai kira shi a waya ba. Da sallama É—auke a bakinsu suka shiga palon, Aunty, Abbi, sune kawai a palon suna breakfast a saman table, da yake shima Abbi bai san jelly ba sai bai gane ta ba.
Da fara'a suka tarbe su tare da yi masu iso, saman sofa suka zauna, sai tambayar ina daddy yake Jelly take yi, har da wani cewa ko dai yana Kano ne?.
Abbi na ƙoƙarin yin magana aunty ta ce "Wannan yarinyar ta taɓa zuwa gidan nan ita da wata ƴar uwar Ommu, sun zo lokacin har ta ce mani mai idon mayu" kallon tsab jelly ta yi mata kafin ta ce "Ba dai Jalila ba sai dai wata" jelly bakin dai yana nan bai mutu ba, ba'a yi mata ya kyale.
Aunty zata sake yin magana Abbi ya katse ta da cewa "Imran wace ce wannan mai tsananin kama da Maik? Ko dai Jelly ce?". Gyaɗa mashi kai Imran ya yi alamar e, zubur Abbi ya miƙe yana mai kabbara ga ubangiji tare da ciro wayarsa da sauri dan ya kira daddy.
Lokacin da kiran ta shigo wayar daddy yana tsaye a gaban mirror yana gyara hular kansan ya yi waka ya shirya cikin manyan kaya zasu fita shida babynsa, ita ma ta yi wanka tana sanye da doguwar riga black color, dukkansu sun yi kyau sosai da sosai.
Ganin kiran Abbi ne yasa ya ɗauka da wuri. "Maik ka zo palo yanzun nan ka same ni". Shine abin da Abbi ya ce, wani irin faɗuwar gaba ya ji, da sauri ya nufi hanyar fita yana faɗin "Baby ta so muje Abbi na kiran mu, kuma yadda ya ce na yi saurin nan da alama akwai abin da yake faruwa". Miƙewa ta yi ta fara dingisa kafa dan har yanzu bata gama warwarewa sosai ba.
Ganin zata ɓata mashi lokaci ne yasa ya ɗauketa cak kamar yadda yake ɗaukar Jelly suka fita. Tun da ya doso palo gabansa ke faɗuwa, sunan Allah kawai yake ta kira a cikin zuciyarsa.
Suna shiga palo bai lura da su Imran ba ya nufi saman sofa ya ajiye Ayla, É—agowa da zai yi idanunsa sai a kan fuskar Jelly dake zaune kusa da Imran tana ta kallon shi tun da ya shigo dan ta tabbatar da shi É—in ne dan gaskiya ya sauya sosai.
Wani irin ɗagowa ya yi da sauri dan ya tabbatarwa da idanunsa abin da yake gani ne, ita ma miƙewa ta yi tsaye tare da nufo shi da gudu ta faɗa jikinsa tana ambatar sunan sa wato daddy.
Mutuwar tsaye ya yi kamar wadda aka zarewa laka a jiki, Abbi kam abu ya yi mashi daɗi har da ciro waya ya fara yi masu Video, a wannan hali Hajiya Hadizatu ta sauƙo kasa ta samesu, yau tana sanye ne da shadda yellow color, ta ci kwalliya da alama fita zata yi.
Kallon walaƙanci ta yi masu kafin ta ce "Matsiyata an taru kenan ba? Dan anga mijina yanzu ya wuce tsara shine duk aka tare mashi a gida".
ÆŠago kai Jelly ta yi daga jikin daddynta ta kalleta sama da kasa kafin ta ce "Yaya Imran wace ce wannan kuma kamar wata busasshen kifi, fuska kamar na big da muke kallo a discovery". Jelly kenan bata barin ko ta kwana, ka yi mutunci da ita ma ya ka kare bare kuma rashin mutunci ta haÉ—a ku, ai gidan shi ka zo in dai jelly ce, tsab zata wankeka soso da sabulu, bata barin magana ta faÉ—i kasa ba tare da ta bada amsa ba
Guntse dariya Aunty ta yi shi kuma daddy sai lokacin ya ɗan samu karfi da ya sanya hannu ya ɗan bude mata baki, kuka ta sa mashi tana kara rungume shi, ita kuwa Hajiya Hadiza ran ta ya yi muguwar ɓaci, wato ita ce mai kamar an busar da kifi ga kuma fuska kamar alade ba, lallai idan ta kyale yarinyar nan ta cuceta, a zafafe ta yi kan daddy da nufin ya fisgo Jelly ta yi mata ɗan iskan duka duk da bata san wace ce bace kuma bata kalli face nata da kyau ba sakamakon tana manne da jikin daddynta.
Sai wani huci Ommu take yi jelly ta ɓata mata rai, gadan gadan ta mufe ta...........
Sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu.
💖💖TRIPLETS💖💖
E85-86💖
Sai wani huci Ommu take yi jelly ta ɓata mata rai, gadan gadan ta mufe ta, da sauri Abbi ya tare ta yana faɗin "Amma dai Hadiza baki da hankali ko?, Me zaki daka a jikin yarinyar nan". Jelly kuwa tana daga kwance a jikin daddynta ta ce "Kai ni zaki daka ma kenan? Amma dai baki da hankali ko? To id...." Bata karisa ba daddy ya rufe mata baki tare da kara rungumeta sosai yana mamaki wai har yanzu dama jelly bata canza ba kenan?.
Shi kuwa Imran zuciyarsa har ta fara dukan uku uku dan Ommu zata bugi jelly, kuma dama ba bari shima zai yi a dake ta ɗin ba, shima daddynta fa bai yi kasa a gwiwa ba wajen sakinta ya juyo dan ya ga karshen rashin kunyar Ommu, idan ta yi gigin yunkurin taɓa ta wlh yau sai ya tsintsin ka mata mari sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Ommu kuwa a kule ta ce "Matsiyata dama ba dole ayi haka É—in ba, idan ba ku yi ba ai ba ku cika Æ´aÆ´an talakawa ba". Shi kam daddyn Jelly mamaki ya hana shi yin magana, wai me Ommu ta gani a tattare da sune da take ce masu Æ´aÆ´an talawa, ko dai wani sabon iskanci ne,? Domin kuwa Ommu ta yi masu farin sani tun iyayensu wato kakannin su Jelly suma raye kenan, tasan irin ruwan kuÉ—in da suke da shi kamar me, to kodai dan daddyn Jelly É—in ya dawo gidan da zama ne?.
Shi kuwa Imran da abin ya ɓata mashi rai sai ya ce ya mata "Idan kina da account bani bari na baki koda 10 million ne ki rage zafi domin na ga kina da buƙa ta" ya kai karshen maganar tare da juyowa da kallon sa izuwa kan bappan nasa wato Abbi.
"Bappa ka yi hakuri amma ba zan iya juran wannan cin mutuncin ba, Irfan abokina ne kuma ɗan uwana, amma kuma ko da iyayen mu ne suka kauce hanya addini ya bamu dama mu yi masu gyara ta yadda za su fahimta, ina matukar kaunar Irfan kuma muna girmama juna, duk abin da ya faru shekaran jiya ina sane, to yana da kyau mu taka mata birki domin ba yara bane mu, ta zo ta same mu cikin kanne mu, ku kuma cikin ƴaƴanku ta haɗa mu ta ci mana mutunci saboda ita bata san mutunci ba, to wlh ya isa haka, dama saboda Irfan ne muke yi mata hakuri, wlh ba dan haka ba wannan da tana prison yanzu, duk abin da ya faru a gidan bayan tafiyar mu ranar Akila ta gaya mani a waya, wlh Allah zan iya cewa Ommu kin zama mace mai saa ta farko da Akil ya ɗagawa kafa, ina mai tabbatar maki badan Irfan ba da babu abin da zai hana Akil ya sharara maki maruka wadda za su sanya ki manta hanyar da ki ka nufa, su sanya ki gani taurari, su sanya kunnuwarki doɗewa, ni ki bani account number bari na cireki daga kangin tsiya da kuma talaucin nan ko zamu samu sake a gidan bappanmu idan muka zo!!". Ya kai karshen maganar rai a matukar ɓace, dama an ce mai hakuri bai iya fushi ba.
Sakin Jelly daddy ya yi yana faÉ—in "Rimsha ku je sama wajen Hanan ko, babyn daddy ta shi ku je ko?".
To suka amsa da shi, da kyar Ayla ta miƙe, da sauri Aunty ta zo ta dafa mata suka wuce sama, domin ita ma Aunty bata son tsayawa a wajen dan bata ma son jin hayaniyar tasu.
Dawo da kallonsa a kanta daddy ya yi tare da ɗaure fuska nan yau shima ransa ya yi mugun ɓaci, yau karo na biyu kenan da take cin mutuncin su a gaban ƴaƴansu to gaskiyar Imran ne yana da kyau su taka mata birki domin iskancin nata ya fara wuce misali.
"Hadiza ina ganin mutunci ki ne nima dan saboda Irfan, yaron kirki, Allah ya rufa mishi asiri ba ke kika raine shi ba, wlh nasan da ke kika ba su tarbiya Æ´aran nan da sai sun zama kannen sheÉ—anu, yanzu ke ba abin kunya bane ma ki É—auko kafar ki da sunan wai kin dawo gidan nan? Wlh ta bakin Imran kin yi babbar sa'ar Akil aure ta sauya shi, ba dan haka ba ko yaya suke da Irfan sai ya dalla maki mari, idan ma baki yi sa'a ba sai kin wuce gadon asibiti, yanzu tsabar rashin kunya Æ´aÆ´an yaya babban ne talakawa? Ke kin sani a gaba É—aya cikin mu a tsabar kuÉ—i dai daga Hosain sai Yaya babba wato Abban su Imran, ko dai dama baki san su Imran Æ´aÆ´an yaya babba bane? To idan baki sani ba yanzu ki sani Akil kawai zai iya sayan Familynku baki É—aya, sannan bugu da kari Æ´aÆ´an Umaiya ce wadda ta ma fi yaya babba kuÉ—i, kuma ke kin sani ko ada baya da yaya ki ka kwaci kanki a hannun Umaiya? To ki sani barewa ba zata yi gudu É—an ta ya yi rarrafe ba, tun wuri ki fita har karmu idan ba haka ba zaki yi dana sani, yadda ki ka san Umaiya a da to yanzu Akil ne photo copyn ta, shiyasa ki ka ji munce maki kin ciri tuta tun da har Akil ya iya danne zuciya ya kyaleki!!!".
Cikin sauri Ommu ta ce "Yanzu kenan Umaisha É—an gidan Yaya babban ta aura?".
Ba wanda ya tanka mata a cikinsu, cikin zumuÉ—i ta ce "Kai amma Alhadulillah da ya kasance ba Æ´aÆ´an Matsiyata Æ´ar cikina ta aura ba, kai abin ya min daÉ—i". Tana gama magana ta juyawa ta nufi sama, sai daÉ—i take ji.
Girgiza kai daddy ya yi tare da komawa ya zauna a saman sofa, shima Abbi zama ya yi a saman sofa yana mamakin hali irin na Aunty, Baiwar Allah mace mai sanin Yakamata, bata son hayaniya, mafi yawancin mata suna son su ga ana ci wa kishiyarsu mutunci amma ban da Aunty, da zarar sun fara faÉ—a zata wuce É—akinta dan ma kada ta ga abin da yake faruwa, bata son hayaniya kuma bata son abin haushi, tana da zuciya mai kyau sosai, har cikin ransa yau Abbi ya ji wani irin mugun daÉ—i abin da Aunty ta aikata, ta san abin da take yi.
Shi kuma Imran sama ya haura domin ya je ya kira su jelly.
Jim kaɗan sai ga Ommu ta fito riƙe da wayarta ta canza shiga zuwa doguwar riga, da alama ya fasa fitan kenan.
Kusa da Abbi ta zo ta tsaya tare da miƙa mashi wayarta tana faɗin "Saka Mani number Umaisha ko kuma na mijinta a nan bari na kira shi ya kawo mani ita yanzun nan zan yi magana da ita".
Kallon daddyn Jelly Abbi ya yi, mamaki ya hana su magana, tun da ta dawo bata nemi yaran ba sai da ta ji Umaisha na auren Akil sannan ne zata ne me su dan ta ji ruwan kuÉ—i.
Sosai daddy yake addu'ar kada ta lalatawa yaran nan aurensu, dan yasan halinta sarai, zata iya kai Umaisha ta barota, kuma kun san tsakanin uwa da Æ´a, sannan Ommu ba ruwanta da wai Æ´ar cikinta ce, idan bukatar ta ya biya shikenan ai.
Ƙin saka mata number Abbi ya yi, ya ce bashi da shi, ba dan ta so ba ta hakura ta koma sama tana tunanin yadda zata yi.
Tana komawa ba jimawa sai ga su Imran sun sauƙo kasa, jelly ta canza kaya zuwa doguwar riga ash color, shi kuma Imran yana manne da waya a kunne yana magana da Akil akan su zo gidan Abbi yanzu an gane Jelly.
Aunty na rungume da Ayla suka sauƙo kasa. Jikin daddy jelly ta je ta haye tana zuba mashi shagwaɓa akan tana kewarsa, da hannu ya yi wa Ayla alama akan ta zo ita ma, ba musu ta je dan dama bata taɓa yin musu da shi ba.
Ta gefen jikinsa ya jawota yana faÉ—in "Babyn daddy wannan ita ce Jelly" jin abin da daddy ya ce yasa Jelly ta yi saurin É—ago kai tana maimaita sunnan da daddy ya kira Ayla da shi.
Kamar wadda aka yi wa allura haka Jelly ta diro kasa ta yi zaman Æ´an bori a tsakiyar carpet É—in tare da fara wuwwurga kafafu a kasa tana ihu kamar ba lafiya ba, daddy ya san me take yi wa ihu, wato dan ya kira Ayla da babyn daddy shi ne take kuka, sunan babyn daddy sunan Jelly É—in ne da yake kiranta da shi lokacin suna Kano.
Imran ne ya yi saurin marisowa wajenta tare da riƙota yana faɗin "Jelly menene?".
Cikin kuka ta ce "Yaya Imran daddy fa yanzu ya daina so na, kana ganin wata babyn ya samu". Babbar magana wai ɗan sanda ya ga gawar soja, dama shi daddy already yasan za'ayi hakan, yasan ba zata taɓa yarda da Ayla ba, shiyasa ya ce tana dawowa za'a ɗaura mata aure da Imran kowa ma ya huta.
Cikin sigar rarrashi Imran ya ce "Jelly wannan fa mummynki ce ba wai wata ba, mummy zaki ce mata".
Cak ta tsaya da kukan nata tare da ɗago idanu da sauri ta sauƙe akan Ayla ɗin. Kallon minti ɗaya ta yi mata kafin kuma ta kwashe da dariya kamar wata zautatciya, daddy kam ko ajikinsa dan ya san halin kayarsa, in dai jelly ce to fin hakan ma zata yi, sai ta sa ka ka yi tunanin ko kaine mahaukaci, wlh tsab jelly zata sanya ka fara tunanin anya kana lafiya kuwa? Anya kai ba mahaukaci bane kuwa?.
Shi kuwa Imran da yake har yanzu yana da sauran karatu akanta sai ya ce "Jelly lafiya kike dariya kuma?" Kara sautin dariyar tata ta yi har da rike ciki, kamar ba ita ba ce mai yin kuka yanzun nan.
Sai da ta yi dariyarta mai isarta sannan ta ce "Amma yaya Imran a sanina dai kafin mu zo nan lafiya lou kake, ya akayi kuma yanzu ka canza kamar mara lafiya?" ÆŠan kallon kansa ya yi dan ko zai ga abin da ta gani a tattare da shi da ta ce mashi ba shi da lafiya.
Shikam daddy a zuciyarsa cewa ya yi kaɗan ka gani Imran ba dai jelly ba, wata rana sai ta sanya ka tuɓe wando a cikin jama'a, Abbi kuwa ban da murmushi ba abin da yake yi, ita kuwa Aunty yau ta ga duniya a wajen jelly, ta ga abin mamaki, Rimsha kam ko a jikinta, Hanan ce ma ta ɗan tsorata da ganin abin da jellyn take yi.
"Jelly wai me yake faruwa ne?" Cewar Imran, cikin dariya ta ce "Yaya Imran wannan Æ´ar karamar yarinyar da bata wuce na kamata na haÉ—iyeta na kora ruwa bace mummyna? Wai ka manta mummyna ta rasu ne? To idan ka manta na tuna maka, mummyna bata nan wannan kuma ai ko mai....." Bata karasa ba ta ja birki sakamakon karewa fuskar Ayla kallo da take yi.
Zubur ta miƙe tana faɗin "Ya na kalli tana kama da mumnyn kuma?" Da yake ta san fuskar mumnynta a hoto, da sauri ta koma jikin daddy tana tambayarsa ya akayi take kama da mummynta kuma.
Daddy bai san time ɗin da ya ce mata "kanwar mummyn ki ce ai". Imran yana ƙoƙarin gaya mata ita ce matar daddy, daddy ya yi saurin dakatar da shi domin kuwa yasan a yanzu dai jelly ba zata taɓa yarda da Ayla matarsa ba, for now dai a barta a kanwar mummyn kawai zai fi, sai ta kara hankali idan ta je gidan mijinta, idan ba haka ba yanzu zata yi masu karamin hauka.
Suna a haka wayar Imran ta fara kara, hannu yasa a aljihun nasa ya ciro wayar, Nawid ne yake kiransa, picking ya yi tare da manna wayar a kunnensa.
Maganar minti 5 suka yi, sannan Imran ya ce sai kun zo, daga nan suka yi sallama, hakan kuma ya yi daidai da danno hancin motar Akil cikin gidan.
Zama Imran ya koma ya yi a saman sofa, ita kuma Jelly tuni ta rungumi Ayla sun fara hira a matsayin kanwar mummynta, dama ta jima tana cewa daddy ya kai ta wajen ƴan uwan mumnynta ko kuma ya kawo mata su gida ta gansu, amma kullun sai ya rinƙa ce mata zai yi zai yi amma bai taɓa yi ɗin ba, sai ga shi yau ta ga kanwar mummyn nata ai farinciki ba'a magana, har da rungumar Ayla ta yi suna ta hira.
A haka Akil ya shigo ya same su, tare da Akila, Umaisha da kuma A'afia suke tafe, duk ya haÉ—o kansu dan su zo su sake kulla zumunci.
Sai murna suke yi kamar me, daddy ne ya ce da Akila ta tashi ta je ta ɗauko mashi kuɗi a cikin drawer mirror a ɗakinsa ta kawo mashi, to ta amsa mashi da shi tare da miƙe wa da sauri ta nufi waje.
Tana shiga palon suka ci karo da Irfan zai fito, cikin sauri ta yi baya zata faɗi, yana ƙoƙarin riƙota ta kauce mashi ta faɗi kasa, bata son ya taɓa ta dan kada ɓoyayyen masoyi ya ɓata rai.
Yadda ta kauce mashin ba ƙaramin mamaki ta ba shi ba, amma kuma bai kawo komai a ransa ba ya duka yana son ɗagota tare da yi mata sannu, kin yarda ya ɗagota ta yi, nan ta ce mashi a'a ya bari zata tashi, bai damu ba dan shima dama ba wani son cika taɓa jikinta ya yi ba, dan tsaro.
Bayan ta miƙe suka gaisa ya tambayeta yaushe suka zo, nan ta gaya mashi yanzun nan kuma daddy ne ya aiketa su Imran suna palo, da Muryarsa ya ce to ta ɗauko saƙon daddyn sai su wuce zuwa cikin gidan tare, to ta amsa da shi sannan ta wuce zuwa bedroom ɗin na daddy tare da taimakonsa wajen nuna mata bedroom ɗin.
KuÉ—i ta É—auko mashi wadda a kalla zasu iya kai 500k, Irfan na tsaye har ta fito suka jera zuwa cikkn gida.
Kamar yadda ta barsu haka ta shigo ta same su, sai hira ake zubawa kamar ba gobe, miƙawa daddy kuɗin ta zo ta yi tana faɗin "ga shi nan bappa".
Karɓa daddy ya yi tare da miƙawa Abbi ya ce ga sadakin Jelly, a matsayinsa na waliyin Imran, yana neman alfarmar da a ɗaura auren nan yanzu, Allah sarki kuruci dangin hauka, jin hakan yasa jelly ta rungume shi tana dariya tana faɗin zata zama matar yaya Imran, zata zama matar yaya Imran, shi kuwa Imran kasa da kansa ya yi duk kunya ta rufe shi, nan take Akil da Irfan suka fara tsokanarsa, aunty ce ta ce da Jelly ta ta so ta zo su ɗan yi magana.
To jelly ta amsa da shi tare da tashi ta je, har ga Allah duk wanda ya zauna da Aunty dole zata shiga ransa domin tana da halayya masu kyau, kowa ya zo gidan ita yake so ba Ommu ba, tana da tarin masoya ciki kuma har da Æ´aÆ´an Ommu É—in, domin Irfan yana kaunarta sosai saboda kirkinta, haka su Aafia ma, suna sonta, kowa nata ne bata da mugunta ko kaÉ—an.
Miƙewa Abbi ya yi ya ce su je waje bari ya kira makwabtansa sai a ɗaura auren. A tare gaba ɗaya mazan suka fita, su kuma matan suka cigaba da hira Aunty tana yiwa Jelly nasiha akan ta natsu, tare da kara mata haske a kan abubuwa.
Mu koma baya kaÉ—an, lokacin da daddyn Jelly ya ce su haura sama, time da Ommu take yi masu rashin mutunci, da suka shiga aunty ta kalli jini a jikin jelly hakan yasa ta saka jelly ta shiga toilet ta wanke jikinta ta bata sabon pant da kuma always ta saka, wannan dalilin yasa jelly ta fara kaunar Aunty, saboda kirkinta, bata share mutane. Bayan ta saka always É—in Aunty ta kara bata doguwar rigarta ta sanya a jikin ta, wannan shine abin da ya faru bayan shigarsu É—aki. MU KOMA IN DA MUKE A STORY.
Suna tsaka da hira aka sako waƙar bodyguard na Salman Khan a Tv, a ɗari Jelly ta miƙe tare da kure Volume na Tv ta fara tikar rawa.
Sai murmushi kowa yake yi yana kallonta, jawo hannun Rismha ta yi akan ta taso su yi, ai kuwa Rimsha bata ki ba suka shiga yin rawa a tare, sake jawo hannun Ayla ta yi, nan fa ita kuma Ayla ta saka kuka dan ba zata iya ba, jelly a tunaninta dan bata so ne yasa take kuka saboda idan baku mance ba halin jelly ɗin ce, idan bata son abu sai ta kama kuka, to tana tunanin kamar kowa ma haka ne, shiyasa sai ta kyale Ayla ɗin kawai suka cigaba da rawa da Rimsha, miƙewa ita ma Akila ta yi suka fara takawa a tare, da kaɗan da kaɗan Umaisha ma ta bi bayansu suka bar Aafia, Hanan da kuma Ayla sai Aunty, sun zuba masu idanu suna kallon yadda suke taka rawa kamar ba gobe, abin ba ƙaramin ƙayatarwa ya yi ba. HAPPINESS IS FREE.
A can waje kuma ana famar É—aura aure.
After some minutes.
Bayan an ɗaura aure an dawo a palo suka sake ba je wa, Imran, Akil ba wanda ya tuna da Ammie zata karɓi wannan aure ne ko ba zata karɓa ba, sannan idan baku mance ba, jelly tun kafin ta san waye Hajiya Umaiya ta nuna bata son ta, idan baku mance ba bakar muguwa munafuka take kiran Hajiya Umaiya, ya kuke tunanin wannan zama zata kasan ce? Anya Ammie zata karɓi Jelly kuwa?. Ko dai zata gasa jelly kamar yadda ta gasa Umaisha? Mu dai je zuwa.
Sai murna suke yi, duk fuskar wadda ka kalla a cikin palon nan zaka kalli tsantsan farinciki a tattare da shi.
A wanann halin su Nawid suka iso suka same su, shi da Umminsa da kuma Hajiya Batula.
Abin da ya faru a gida bayan komar Nawid da ya kawo wa Imran Jelly shine, da ya koma bai sami Abbo a gidan ba, abin ya É—aure mashi kai, kwata kwata babu Abbo babu alamar sa, kuma ga kofar É—akin a rufe kamar yadda ya rufe Abbo É—in, shi ne da ya dawo ya buÉ—e kofar, to ta ina Abbo ya fita?.
Ransa cike da tunani tare da mamaki ya kwanta kawai, amma ya kasa yin barci har wayewan gari.
Da gari ya waye ne Ummi ta tambayi ina baby, sai ya ce tana gidansu Abokinsa, bai gaya mata me ya faru, me Abbo ya aikata ba, ya rufe abin shi kaÉ—ai domin bai kawo a ransa cewa tsafi Abbo zai yi da jelly ba, ya yi tunanin raping É—in ta kawai zai yi, shiyasa ya rufe maganar dan a cewarsa abin kunya ne ya faÉ—i hakan, ya rufawa mahaifinsa asiri.
Nan fa Ummi ta fara faɗa akan me zai ɗauki baby ya kaita wani waje, ita ba ta yarda ba sai dai su je gidansu abokin a tare, hakuri ya rinƙa bata akan bari ya je ya ɗauko babyn, ina ta ki yarda ta ce sai dai su tafi tare, haka kuwa akayi shine suka taho tare, shi kuma Abbo shiru ba labarinsa, Allah kaɗai ya san ina ya tafi, ita ma Ummi bata neme shi ba, saboda ana hidimar biki tasan ba zama yake yi a gidan ba.
STORY💖
Hannu Nawid ya miƙawa dukka mazan cikin palon, ɗaya bayan ɗaya suka gaisa, su kuma matan suka gaisa da baki, ya sha mamakin ganin jelly a jikin daddy, kamar zai magana sai kuma dai ya danne ya yi shiru, ita ma Ummi gaisawa suka yi da mutanen cikin Palon, ita kuma Hajiya Batula mamakin ganin su daddyn Jelly ya hana ta magana, shima daddyn ido kawai ya bita da shi dan bai san me zai ce mata ba, Abbi ne kawai ya ce "Batula dama kin san hanyar gidana? Kin san in da nake shine baki taɓa zuwa ba?".
Shiru ta yi ta kasa magana, abubuwan da suka faru a baya ne kawai suka fara dawo mata a cikin ƙwaƙwalwarta. Hannu Abbi ya sa ya nuna mata sofa akan ta zauna, ba musu ta zauna gaba ɗaya palon suka yi shiru.
Ummi ne ta katse masu shirun da cewa "Baby kin san shine da kika zauna a jikinsa?" Ta yi maganar tana kallon daddy da jelly ke a jikinsa, Jelly kam ko kallon in da take ma bata yi ba, domin bata sansu ba.
Imran ne ya ce "Ummi babanta ne ai". A razane suka miƙe a tare ita da Nawid, kallon juna suka yi kafin su sake kallon Imran ɗin. Abbi ne ya ce masu su zauna sai ayi magana a nutse, ba musu suka zauna, Imran Abbi ya fara tambaya akan me ya faru a ina kanwar Hadiza wato Ummi ta san Jelly?.
Nan Imran ya basu labarin duk abin da ya faru daga lokacin da Nawid ya kira shi a waya akan zai kawo mashi jelly har zuwa yanzu. Kallon Ummi Abbi ya yi kafin ya tambayeta me ya faru, a ina kuma ta sami jelly da har ta riƙeta na tsawon wannan watanni. Ita ma dai Ummi ba ɓoye ɓoye ta fara basu labari tun daga farko har izuwa yau da take zaune a gabansu.
Lokacin da ta kai karshen maganar ba wanda bai nisa ba a cikin Palon, haka zalika ba wanda bai yi hamdala ga Allah ba, ita ma jelly sai da ta É—ago ta kalli Ummin É—in, nan take ta ji Kaunar matar ta kamata, Ummi mai zuciyar imani, duk da jelly ta manta su amma tana kaunar Ummi, bare ma da Ummi ta bada labarin irin zaman da suka yi, sai ta kara jin tana son Ummin sosai.
Shiru palon ya É—an yi na tsowon mintuna kafin daddyn Jelly ya fara magana a nutse, "A gaskiya bani da bakin da zan iya gode maki na wannan abin da kika yi Mani, sai dai na yi maki addu'ar Allah ya baki gidan aljanna, kai kuma Nawid ina mai baka hakuri domin ba'afi minti 20 ba dana cika alkawarin dana É—auka na aurawa Imran auren jelly, yanzu jelly matar Imran ce, amma kuma a matsayina na mahaifi a garesu na baka auren Aafia kuma a yanzu za'a É—aura ba sai anjuma ba". Gaba É—aya palon zubawa Daddyn Jelly idanu suka yi.
Ita dai Aafia bata damu ba, idan baku manta ba tana bala'in kaunar Dr Nawid tun suna school da su Rufee, hakan yasa bata wani damu ba dan ance za'a aura mata shi.
Shi kuwa Nawid kallon Æ´an matan dake wajen ya yi yana son tantance wace ce Aafia a cikinsu, ganin hakan yasa daddy ya ce "Ga Aafia É—in nan mai black dressing".
Kwata kwata Nawid bata yi mashi ba, amma ba yadda zai yi, yama fi son Hanan akanta, domin A'afia irin siraran matan nan ne, shi kuma ya fi so ya ga ko'ina a cike. Ba dan ya so ba ya karɓi aurenta, Daddyn Jelly dai shi ya sake biyan sadaki, a ranar aka ɗaura auren, jin abin suke yi kamar mafarki Nawid dai zuciya bata so ba, sai dai kuma ya cire son jelly a zuciyarsa, domin yasan irin son da Imran yake yi mata, sai dai bai san ita ɗin ba ce, amma kullun idan sun haɗu Imran ba shi da magana da ta wuci na jelly'nsa matarsa hakan yasa ma ya cire ta zuciyarsa, kuma koda an ɗaura mashi aure da ita kafin su gane iyayenta, idan ya san cewa ita Imran yake so to zai saketa, dan shi zai bawa wani labarin irin son da Imran yake yi wa Jelly ba dai wani ya ba shi ba.
Karin wata Haske Abbo shine wannan alhajin da yake neman Aafia ruwa a jallo a baya, wadda ya yi sanadiyar mutuwar Yusuf yayan Rufee, kuma shine wannan man ɗin na school ɗin su A'afia wadda ya kashe Amal kanwar Rufee ɗin, akwai abin da yake so a tattare da Aafia wadda shi kaɗai ya barwa kansa sani, ya rasa Aafia ce sanadiyar koma warta gidan su Akil wadda babu wani ɗan iskan matsafi ko aljanin da ya isa ya nufi gidansu Akil ɗin, hakan yasa Aafia ta kubcewa Abbo, amma ba dan haka ba, kowani motsi zata yi akan idanunsa take yi, akwai wani mata ki da yake son ta kai ne dan ya yi amfani da ita, shiyasa ya rinƙa bibiyarta yana kula da ita.
Ya kuke ganin wannan abin zai kasance, daga karshe dai ga Aafia zata koma gidan Abbon baki É—aya, to mu dai je zuwa, ni dai na yi gaba sai kun zo.
Yau murna a wajen Æ´an gidan ba'a magana, sun yi wunin cikin farin ciki, while ita kuma Ommu tana cikin É—aki tana zuba barcinta dan ita bata wani damu da fita waje ba, bata fitowa palo sosai sai dai idan wani abin zata É—auka.
After some hours, bayan sallar la'asar rana ta yi sanyi, sun yi sallah sun ci abinci sun zauna suna hira, Ummi ta ce da Nawid su koma gida.
Miƙewa ya yi suka sallami su Abbi tare da yi masu godiya sosai da sosai zasu tafi, Abbi ya ce su wuce da Aafia, mamaki ne ya kama Ummi, a nata tunanin sai sun kawo lefe da sauran abubuwan biki, Abbi ya ce kada su damu abawa Nawid matarsa daga baya za'a kawo mata kayanta da abubuwan da ake buƙata, har kasa Ummi ta duƙa tana yi wa Abbi godiya tare da fatan alkhari, shima godiya ya yi masu na riƙe jelly da amana da suka yi, rungume Jelly Ummi ta yi tana mai kara jin kaunarta har cikin ranta, ita ma jelly sosai take kaunar Ummin duk da bata iya tuna rayuwar da ta yi a gidan nasu ba, amma dai ta na jin a jikinta tabbas ta taɓa rayuwa da su kamar yadda suka faɗa.
Har wajen mota gaba ɗaya family suka rakosu, sai kuka Aafia take yi, lokaci guda an rabata da ƴan uwanta, bata taɓa tunanin wannan zuwan da su yi zata rabu da ƴan uwanta ba, abin ya yi mugun taɓa mata zuciya, sai rarrashinta Ummi take yi tare da rungumarta suka zauna a gidan baya na mota, shi kuma Nawid gaisawa suka kara yi da su Imran sannan suka yi sallama bayan ya zubawa su Abbi godiya, ya shiga gidan gaba na motar, ayya Ummi ta ɗauka da Aafia da jellyn ɗaya ne, bata banbanta su ba ta rungumo Aafia kamar Jelly, a haka suka bar gidan, Nawid ya ja mota.
Duk wannan abin da ake yi Ommu tana sane amma bata leƙo ba, jirama take yi mutane su ragu ta jawo Umaisha ɗaki ta ɗaurata akan hanya dan su sami kuɗi, ita idan ba magana ta kuɗi ake yi ba, to ba zaka same ta a wajen ba.
Jama'a wai shin ina Ommu take kai kudi ne? Me take yi da sune?
Tana ji aka aurar da Aafia, amma bata wani damu ba, da ma taga É—an Æ´ar uwarta ta aura sai ta É—an ji haushi domin a nata ganin Nawid ba shi makudan arziki sosai.
Bayan tafiyar su Nawid ne su Abbi kuma suka juya za su koma cikin gida, cikin dabara Akil ya jawo Umaisha suka shige cikin motarsa dan shi fa baya iya zama 2 hours bai murjesu ba wato tula tula, idan bai taɓa su ba har zazzaɓi yake yi, Abbi yana ganinsu suka shiga cikin mota, amma sai ya yi kamar bai gansu ba, kuma tunani ma ya yi akan su zo su wuce gidansu kada su yi masu abin kunya a nan, yara kamar wasu chewing gum kullun suna manne.
Shi kuwa Imran ango na Jelly, yana son keɓewa da matarsa amma ba hali domin kuwa shi ba irin su Akil bane, yana da kunya sosai, daddyn Jelly da ya fahimci hakan sai ya ce da jelly'n ta je ɗakinsa ta ɗauko mashi agogonsa.
kamar ta san ɗakin nasa ganin Akila ta fita waje ɗazun da ya ce ta ɗauko mashi kuɗi, haka ta wani miƙe da sauri ta nufi wajen ita ma, kuma dama yasan bata san ɗakin nasa bane yasa ya aikata dan kawai ta fita Imran ya bi bayanta su je su ɗan tattauna, dan gaskiya Imran ya wahala akanta sosai, yana da kyau yanzu su sami lokaci sosai a tare.
Tana fita kuwa Imran ya zame cikin sanÉ—a ya bi bayanta, da yake part biyu ne a gidan, daga nasu Irfan É—in sai na su Abbin, hakan yasa tana fita ta nufi É—ayan part É—in, shima yana fita ya bi bayanta.
A palon ta tsaya da yake É—akuna uku ne a cikin palon, ta tsaya tana tunanin wanene na daddy'nta, daga ta baya ya runhumeta tare da kwanto da kansa a saman kafaÉ—unta.
"Yaya Imran" ta ambata tana ƙoƙarin juyowa, "Waye ya gaya maki nine?" Ya yi maganar tare da juyo da ita suna fuskantar juna.
"Ba wanda ya gaya mani kawai a cikin zuciyata na ji cewa kai ɗin ne". Ranƙwafo da kansa ya yi a saman tata suka haɗa goshi, har cikin ido take kallon shi, yayin da shima yake kallon cikin idanunta.
"Jelly kin san yadda yaya Imran yake son ki kuwa?" Turo ɗan bakin nan nata ta yi har yana taɓa nashi, cikin shagwaɓa ta ce "E ai nima ina son ka ko?". Wani dogon numfashi ya ka lokacin da bakinta ya taɓa nasa.
A hankali ya ɗan fito da harshensa yana lasan saman lips nata, ƙoƙarin kwace kanta ta yi domin ta raba jikinta da nashi, riƙeta sosai ya yi tare da capko lips nata na kasa ya fara tsotsa, zaro idanunta ta yi tana kallonsa, cikin sauri ya sa hannunsa ya rufe mata idanun nata dan kunyar kallon cikin idonta yake yi a yayin da yake kissing nata.
Da karfi ta ture shi tana faÉ—in "Wlh sai na gaya wa daddy kai É—an iska ne, wato abin da ake yi a film shine zaka yi mani ko? Wlh bana sonka tunda dai haka ka ke, kuma dole na gayawa daddy abin da ya ce kada na yarda wani namiji ya yi mani ka yi mani yau". Ta kai karshen maganar cikin kuka tare da juyawa da sauri dan ta koma cikin gida.
Da sauri ya riƙota yana mai bata hakuri akan dan Allah kada ta faɗa ya tuba ba zai sake ba, kin yarda ta yi har da rantsuwa sai ta faɗa.
Yana cikin bata hakuri ta kwace kanta da karfi, da gudu ta juya zuwa part É—in su Abbi, dafe kansa ya yi yana tunanin jama'ar dake a cikin palon, dama dai iya daddy ne to da da É—an sauki, amma har da su Akila a wajen fa, tuna hakan yasa ya juya da sauri ya je ya shiga motarsa tare da kiran Rimsha a waya akan ta fito da sauri su tafi domin a gaskiya ba zai iya haÉ—a idanu da jama'ar palon ba, kuma yasan ba makawa jelly sai ta faÉ—i wannan magana, me ma ya kai ni yi mata kiss a gidan nan? Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
A haka Rimsha ta fito ta same shi, cikin sauri ya ce ta shiga su je, ai kuwa ba ɓata lokaci ta shiga, da gudu ya figi motar suka bar gidan suka nufi gidan Lion, kunya ta kore shi a gidan.
Yana shiga gidan Lion sai ya ga ba motar Lion É—in, hakan ya tabbatar mashi da Lion baya gidan kenan, kallon gateman ya yi tare da tambayarsa Lion ya fita ne? E ya amsa mashi tare da ce mashi sun fita tare da Mark, jinjina kai ya yi kafin ya ce da Rimsha su je su duba jikin Areef sannan su wuce bedroom nasu.
Jerawa suka yi zuwa cikin gidan. Kwance su isko Areef, da kallo É—aya Imran ya yi mashi ya san ba lafiya ba domin kuwa gaba É—aya ya sauya kamar ba shi ba, abin da kuma yake faruwa shi ne, G.M.A sun gane Lion yana son cire Areef daga cikin su, ya sanya ta ko'ina ana yi wa Areef É—in saukar Al Qur'ani mai girma, ga addua'o'i, shima Lion É—in kwata kwata yanzu baya barcin dare, kwana kai wa Allah kukansa yake yi, yana gayawa Allah damuwarsa, azumi kuwa ba'a magana, yana yi wa Areef azumi sosai ga sadaka da karatun Al Qur'ani mai girma, duk fitar da yake yi kwanakin nan gidajen gajiyayyu da gidan marayu yake zuwa ya raba masu makudan kudaÉ—e, hakan yasa ya sakarwa Aseef ma kuÉ—i dan su yi ta sadaka ta ko'ina, saboda ya san duk girma bala'i da masifa da bawa yake a ciki, sadaka tana ruguje sharrin ta kawo Alkhari, wannan faÉ—ar Allah ne, Æ´an uwana mu lizimci yin sadaka ko yaya take, bata kaÉ—an ba ta yawa, abin da kake renawa wlh wani kuma ita ce abu mafi girma a rayuwarsa.
Lion ya fahimci kafin su fitar da Aseef daga cikin wannan bala'i sai sun tashi tsaye sosai, idan ba haka ba suna ji suna gani za su rasa É—an uwansu lokaci guda, hakan yasa Lion yake cikin matsananciyar damuwa a kwanan nan, kwata kwata baya cikin kwanciyar hankali, kawai dai ba'a iya gane mashi ne shiyasa ba wanda ya san yana cikin damuwa.
G.M.A. sun gane ana ƙoƙarin cire Areef daga tarkon da suka sanya shi, shiyasa suke takura mashi kwanan nan, suna azabtar da bawan Allah nan fiye da tunanin mai tunani, kuma kada ku manta duk abin da Areef zai ji a jikinsa su ma TRIPLETS za su ji a jikinsu, yana ɗaya daga cikin abin da yasa Lion ya kara shiga tashin hankali, domin yasan Areef ya fi su shiga cikin wannan azaba da suke ji a jikin nasu.
A yau shugaban G.M.A gaba É—aya ne da kansa ya zo jikin Areef yana azabtar da shi, shiyasa yau ya fi shiga bala'i fiye da kullun, kuma ogan nasu kun san ya fi sauran haÉ—ari, abin da ya sa kuma ya shiga jikin Areef É—in yau da kansa, dan saboda ya ga sauran idan suka shiga jikin na Areef da Lion ya zo kusa da Areef É—in za su gudu saboda perfume nasa, to shine yau shi ogan ya zo da kansa dan ya samu ya azabtar da Areef yadda ya kamata.
Imran ya tsorata ji ya yi kamar kada su karisa cikin É—akin, amma kuma sai ya daure suka karisa kusa da gadon.
Jin sallamarsu ya sanya Areef É—ago kansa tare da waro idanunsa da suka kara girma yanzu, dama ga su da halittar manya manyan idanu abin sai ya zama abin tsoro.
Yana ɗago idanu kai tsaye sai kan Rimsha, wani irin zirrrrr ya ji a jikinsa, cikin sauri ya miƙe zaune yana kare mata kallo, wani irin karfin bala'i ya ji ta zo mashi lokaci guda kamar wani doki.
A zafafe ya damki wuyarta da karfi ya shaƙeta, nan take kuma idanuwansa dukka suka sauya launi daga ask color izuwa jawur kamar jini, fuskar nan tasa har wani ja ta yi, kumatunsa har kerma yake yi, ba shi da wata burin da ta wuce ya ga ya zuƙe mata jini tas.
Da sauri Imran ya yi kansa yana ambato sunansa tare da fara yunkurin kwaceta daga hannunsa.
Yana daga zaunen da hannu É—aya ya yi wurgi da Imran É—in gefe guda, ita kuma tuni ta fara fita a hayyacinta, idanuwanta duk sun yi jawur sun firfito waje, ga shi gidan babu kowa, soja É—aya ne kawai ya rage wadda yake a bakin gate, Lion ya fita tare da É—ayan sojan.
A yadda Areef yake yanzu ko sojoji goma basu isa su danne shi ba bare kuma soja É—aya, mai kwatar Rimsha a hannunsa sai Allah sai kuma Lion.
Ba ƙaramin buguwa Imran ya yi ba, da karfi ya matse idanunsa saboda azabar da ya ji, amma da ya ga Rimsha tana ƙoƙarin mutuwa sai ya sake miƙewa ya nufi Areef ɗin, da iya karfinsa ya sanya hannunsa a kan na Areef dake a wuyarta yana ƙoƙarin ɓanɓaro hannun nasa.
Da karfi Areef ya shaƙo shi da hannunsa ɗaya ya sake wurgi da shi ta baki kofa, hakan kuma ya yi daidai da shigowar Lion cikin ɗakin, domin karfe 5 ta cika ya dawo bawa Areef ɗin magani.
Sake miƙewa Imran ya yi bai lura da Lion ɗin ba ya sake nufar Areef ɗin, har kasa ya duƙa yana mashi magiya akan ya sake dan Allah kada ya kashe ta wlh bata da kowa, sake riƙo shi Areef ya yi ya haɗa kansu da Rimsha ya buga da karfi, wani irin azababben ihu Imran ya saki ita kuma Rimsha diff kake ji kamar babu rai a jikinta, kai daga ganin wanann karfi kasan ba iya Areef shi kaɗai bane.
Da karfi ya sake hankaɗe Imran ɗin, yana ƙoƙarin zubewa kasa da sauri Lion ya tare shi ya faɗa saman faffaɗar kirjinsa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ɗauki Imran ɗin cak ya kwantar da shi a saman carpet dake a gaban bed ɗin na Areef.
Yau da yake ogan G.M.A da kansa ne sai bai gudu ba dan Lion ya zo, yana jin azaba saboda kamshin perfume É—in na Lion É—in, amma saboda taurin kai ya dage sai ya sha jinin Rimsha ya ki guduwa, Imran kuwa sai numfashin sama sama yake yi, amma dai ya ji mugun daÉ—i da Lion ya dawo, kuma ya sami kwarin gwiwa akan koma yaya Lion ba zai bari Areef ya kashe Rimsha ba, ko dan addinin Musulunci zai taimaketa.
Gently Lion ya tako zuwa gaban gadon, hannu ɗaya ya sanya da nufin ya ciri hannun Areef daga shakar da ya yi wa wuyarta, amma Areef ya ki sakinta, sai ma kara matse ta da ya yi, ɗan ciza laɓɓansa ya yi kafin ya murɗe hannun Areef ɗin da ɗan karfi, nan take ya saki wuyar tata, yana numfashin kamar nishi.
Tana ƙoƙarin zubewa kasa Lion ya riƙota da hannu ɗaya dan idan ta faɗi kasa akwai matsala, tana faɗuwa za su zuƙe mata jini kaf. Ɗaga ta ya yi da hannu ɗaya ya ɗaurata a saman kafaɗarsa, ya juya da niyar ya nufi waje da ita.
A zafafe Areef ya diro kasa daga saman gadon tamkar ba shi ne mara lafiyar da aka yi wa aiki ba, Allah sarki ba shi bane, kun san dama G.M.A a cike suke da bakin cikin dan Lion yana shiga masu hanci da kudundune, to yau suna ganin sun sami damar da za su É—auki fansa akan Lion É—in tun da ga shi ya zo, shiyasa gabaÉ—ayansu suka zo suka taru a jikin Areef É—in suka kara mashi karfi kamar kosasshen doki.
Ganin haka yasa Lion ba tare da ya yi magana ba ya yi wa Imran alama da hannu akan ya miƙe ya karɓe ta su fita, da sauri Imran ya miƙe ya zo ya karɓeta suka fita.
A zafafe Lion ya juyo suna fuskantar juna da Areef, daga kasa ya fara kallon Areef É—in zuwa sama, G.M.A sun kara mashi girma kamar ba shi ba.
Lumshe dara daran blue eyes nasa ya yi kafin ya juya da nufin ya bar É—akin domin tausayin É—an uwan nasa yake yi, yana jin kamar ba zai iya dukan Areef É—in ba saboda yau jikinsa a mace yake.
Yana juyawa Areef ya nufo yi gadan gadan, yana ƙoƙarin shaƙo shi ta baya, a sukwane Lion ya duƙa kasa tare da juyowa ya kai mashi wani irin duka a gefen kirjinsa wadda ta sanya shi yin baya.
Wani irin kukan damusa Areef ya yi alamar dukan ta yi mashi zafi. Da iya karfinsa ya nufi Lion, sai wani irin abu yake yi kamar horo.
Zuba mashi ido Lion ya yi sai da ya iso ya ɗaga hannu yana ƙoƙarin kaiwa Lion ɗin shaƙa a wuya, wani irin damƙa Lion ya yi mashi tare da ɗaga shi sama ya yi wurgi da shi a saman gadon, bai barshi ya miƙe ba ya sanya hannunsa ya shaƙesa da karfi tare da zaro mashi wayan nan dara daran blue ɗin nasa sannan ya daka mashi wata irin mahaukaciyar tsawa mai rikita ƙwaƙwalwa, nan take Areef ya natsu sit kamar babu shi a ɗakin.
A hankali Lion ya zame hannunsa daga riƙon da ya yi mashi a wuyar tasa, yana mai jin zafi a zuciyarsa, a zahirin gaskiya Lion ya fi Areef jin ciwo da kuma ɗacin halin da yake a ciki.
Juyawa Areef É—in baya ya yi yana mai watsa dark black curly hair sa, shi kuma Areef wani irin numfashi yake fitarwa tamkar gurnanin zaki, daga ji kunsan ba lafiya ba, bawan Allah.......... Nima haka na ajiye alkalamina sai mun haÉ—u Monday idan mai dukka ya kai mu.
💖💖TRIPLETS💖💖
E87-88💖
Juyawa Areef É—in baya ya yi yana mai watsa dark black curly hair sa, shi kuma Areef wani irin numfashi yake fitarwa tamkar gurnanin zaki, daga ji kunsan ba lafiya ba, bawan Allah.
Lion ya ɗan jima a haka kafin ya juyo tare da zama a gefen ɗan uwan nasa ya fara tofa mashi addua'o'i yana shafa mashi,. Wannan abin da ya faru ba karamin ɓatawa Lion rai suka yi ba, yau da ido huɗu ya yi da su to wlh sai dai wasu ba dai su ba, yanzu idan ya ce zai dake su a jikin Areef ba za su taɓa tsayawa ba, sai dai ma ya daki Areef a banza, domin kuwa da zarar sun ga zai dake su to wlh gudu za su yi su barshe ya yi ta jibgan Areef ɗin a banza, shiyasa bai wani saki jiki wajen dukan Areef ɗin ba.
Ya jima yana yi mashi addu'a har barci ta ɗauke shi, sannan ne ya miƙe tare da gyara mashi kwanciya ya jawo bargo ya rufe shi zuwa kirjinsa tare da kara gudun Ac dake a ɗakin sannan ya nufi waje yana mai jin sauƙi a jikinsa, alamar sun rabu da Areef ɗin kenan.
Yana fita bedroom nasa ya wuce kai tsaya, toilet ya shiga, wanka ya yi tare da shiryawa cikin pajama launin white color, ya yi kyau sosai, sai dai kuma kallo ɗaya zaka yi mashi ka gane tabbas bashi da lafiya saboda rama da ya yi, amma ba zaka taɓa gane cewa yana cikin damuwa ko yau ransa a ɓace ba, domin kullun a haka fuska take a ɗaure.
Saman bed nasa ya hau ya kwanta yayin da manyan malamai suke ta fama yi masu saukar Al Qur'ani mai girma, a daidai lokacin ne kuma Aseef ya kira shi a waya, kuma video call.
Bawan Allah har wani nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin nan ya É—auki kiran. Yau karo na farko daya É—an zaro ido lokacin da ya É—auki kira Aseef. Kayatatcen murmushi ne É—auka akan fuskar Aseef É—in yayin da kuma ya zaro brown eyes nasa tamkar yana kallon wani abin, Lion ya san me yake yi mawa, shiyasa shima ya zare mashi ido sai su zama iri É—aya kawai.
Shiru Lion bai yi magana ba yayin da shi kuma Aseef yake zaune a saman bed nasa daga shi sai shot jikinsa babu riga, wata iriyar gashi ne mai bala'i kyau ga tsantsi kwance a saman faffaÉ—ar kirjin nasa, shima dai breast É—in nasa tamkar na Æ´an uwan nasa ne, bul bul da su.
Kallo ɗaya Lion ya yi mashi sannan ya kawar da kansa gefe yana tunanin shi kuma Aseef me ya je ya jajuɓo masu, domin daga ganinsa akwai wata a ƙasa, dama kuma shi ɗan nema ne, ya iya rigima idan aka taɓa shi.
"Lion please and please smile now, smile for me even for one time in my life". Ya faÉ—a yana kara faÉ—aÉ—a murmushin nasa.
Lion yana ƙoƙarin kunna laptop nasa, ba tare da kalli Aseef ɗin ba ya ce "What is smile?". Aseef bai yi mamaki ba dan Lion ya ce bai san menene murmushi ba, domin kuwa tun da suka girma suka yi wayo, bai taɓa ganin koda makamancin murmushi komai kankantarta akan fuskar Lion ba, kullun fuskarsa a yanayi ɗaya take, wato a fusace, a ɗaure kamar hadari.
"My lion look at my face, look at the way am smiling, to haka zaka yi, I'm very sure idan ka yi murmushi or dariya idan a kusa da mutane kake to ba za'a rasa waƴan da za su suma ba saboda kyan ka, please maybe ma nima zan iya suma saboda kyanka, ni nama rasa ya zanyi, kwata kwata even your teeth ban taɓa gani a waje ba, idan zaka yi magana baka buɗe baki sosai bare mutun ya ga hakwaranka, sai dai ka yi maganar da wani ma zai ce baka motsa Lips naka ba, anya kuwa ma kana da hakwara kuwa? Sannan anya kana da harshe ma kuwa?". Ya kai karshen maganar tare da ɗaga kai sama kamar mai tunani.
A zahirin gaskiya wannan magana da Aseef ya yi ta karshe na cewa ko Lion yana da hakwara da harshe, ya yi tane da sa ran ko Lion zai yi murmushi, da gangan ya yi, amma ina sai ya ga akasin haka, kuma gaskiyar Aseef ne ko hakwaran Lion ba su gani a waje, domin idan zai yi magana ba zaka taɓa cewa ma yana motsa lips nasa ba, saboda kasa kasa yake fitar da words, hakwara ma ba su gani bare kuma murmushi, da girmansu da wayonsu dai bai taɓa makamancin murmushi ba, wata kila da suna yara sun yi, kun dai ji yanzu shi bai ma san me murmushi ba. Lion duniya ne gaskiya wai
"Aseef what is going on on your side?" Shi ne abin da Lion ya faÉ—a, "Lion wai yanzu da gaske ba zaka yi murmushi ba? Wlh ina matukar so na ga murmushi kane fa".
Sai lokacin ya dawo da kallonsa kan wayar tasa. "Aseef i said what is smile?".
Ɗan turo baki ya yi yau ya tuna da shagwaɓa ta baya, "Kai Lion ai na ce maka ga shi nan akan face na ina yi ko?, to kamar haka zaka yi mani".
"Aseef i don't know how to do this nonsense, cox idan ba ka kyaleni da shirmen nan naka ba i will going to block your number, because I don't have time for nonsense, ko wani 1 second in my life yana cikin lissafi, so ka kyaleni".
Shiru Aseef ya yi dama ya san Lion ba zai taɓa yin murmushin ba bare kuma dariya, shi haka yake kullun, su kuma suna son ganin ace yau ga shi koda ɗan murmushi ne ya yi wadda zai sanya kyawawan hakwaransa bayyana, amma ina abin ya faskara.
Haka Aseef ba dan ya so ba ya kyale zancen murmushin ya É—auko wata hirar dan ya sanya É—an uwan nasa farinciki.
A ɓangaren Imran kuwa, bedroom nasa ya wuce da Rimsha, yau ba dan jinin Hajiya Umaiya ne yake gudu a jikinsa ba, to da tabbas da wuya ya yi rai, dan saboda ba iya wurgi da shi kawai Areef ya yi niyar ya yi ba, sun yi niyar shan nasa jinin shima, Allah dai ya tsare shi ne kawai ta dalilin mamarsa.
Saman bed ya kwantar da Rimshan tare da kwanciya a gefenta yana mai da numfashi.
Kwanciyar 5 mins ya yi kafin ya samu da kyar ya yunkura ya miƙe ya nufi toilet.
A gurguje ya yi wanka dan ya É—an sami karfi, shiryawa ya yi cikin kananan kaya sannan ya É—auki Rimsha suka wuce hospital dan a duba lafiyarta.
Sun yi sa'a Baiwar Allah da suka je asibiti ba wata babbar matsala ta samu ba, kawai shakar ne da aka yi mata ta ji wuya, bayan haka ba su taɓa wani abin na daga halittarta ko wani cutar wa ba, sosai Imran ya ji daɗi da jin hakan.
A ɓangaren JELLY kuwa, tana baro part ɗin su Irfan garden ta nufa, da yake garden ɗin yana ta gefen part ɗin su Abbin ne. Saman ɗaya daga cikin kujerun dake a wajen ta yi zaman minti 20 kafin ta miƙe ta nufi cikin gida.
Kamar yadda ta bar su daddy haka ta koma ta samesu, jikin daddy ta je ta haye tare da fara kuka.
Abbi duk ya rikice da ganin kukar tata, nan take ya fara tambayarta me ya faru, waye ya taɓa ta, amma saboda iskanci irin nata ko sannu ba wanda ta ce wa, shi dai daddy yanzu yana nadamar abubuwa da dama da ya rinƙa barinta tana yi time da take karama, bai taɓa zaton zata girma tana yin abin ba, ciki kuma har da shagwaɓa da kuma kuka babu dalili, dan jelly idan tsiyarta ta motsa haka kawai zata zauna ta yi ta kuka kamar wadda ta rasa iyayenta, sai ta yi mai isarta sannan ta yi shiru, ga shi bata jin rarrashi ko kaɗan, idan ta fara to sai ta kai in da take bukatar tsayawa, sannan ta tsaya.
A yanzu ma haka ne, sai tambayarta gaba É—aya jama'ar palon suke yi, duk sun taru a kanta, amma taki cewa kowa ko sannu, abin ya É—aga masu hankali sosai, sun rikice kada wani abin ne ya faru, amma saboda iskanci irin na Jelly taki ciresu a duhu, ta kyale su sai bugawa zuciyarsu take yi, Akil kam har da zuwa ya duba waje ko zai ga wani abin da ya sanya ta kuka tun da daga wajen ta fito, kuma dai shima daga wajen ya dawo yanzu ba daÉ—e wa, shi bai ga komai ba, amma dai ita ta shigo tana kuka.
Sosai daddy ya rinƙa dannarsu akan su je su zauna su kwantar da hankalinsu yana da tabbacin ba wani abin da ya sameta, iya shegene kawai, amma ina sun ki, kowa ya dage sai lallaɓata yake yi tare da yi mata kalamar rarrashi ko zata faɗi abin da akayi mata, Irfan har da zagewa yana rarrashinta, Abbi ma baa magana, Hjy Batula Aunty duk sai kara shagwaɓa ta suke yi.
Daddy dai da ya ga ba su gama sanin halin Jelly ba sai ya barsu ya zuba masu ido domin yanzu su san halinta dan saboda gaba.
Kuma babban abin mamakin shine kukan nata babu hawaye, ta yadda ma zaka san tsagen iskanci ne yake yi mata yawo akai, ko É—ingon hawaye babu, kai bama alamar hawayen a waÆ´an nan busassanun idanun nata masu gashin ido a tsaitsaye.
Sun kwashi good 30mins a haka sai fama suke yi da ita, Akil dai ya koma gefe ya zauna dan idan ya ce zai biye mata to tsab zai karyata a gaban baban nata, gudun kada ayi hakan ne yasa ya koma gefe kawai ya kyale su.
Sai da ta kara wani minti goma sannan cikin kukan nata ta ce "Daddy bani wayarka".
Daga nan ne fa kowa ya koma mazauninsa ya zauna Aunty kam ta rasa a wani mataki zata ajiye Jelly, shi kuma daddy godiya ya yi ga Allah da ya sa suka ga halin nata a fili, Ayla Baiwar Allah yau ta ga iskanci mai lasisi, mamaki ya sa bakinta ma ya gaza rufuwa, shi kuwa daddy miƙa mata wayar tasa ya yi kamar yadda ta buƙata.
Karɓa ta yi har lokacin bata dai na kukan ba, da yake wayar ma akwai password sai ta rubuta sunan ta, tana rubutawa wayar ta buɗe, dama ta san shine pin na daddyn nata tun a tsohuwar wayarsa.
Contract nasa ta shiga, dealing number Imran ta yi, tana rubutawa sunan sa ya bayyana a yadda daddy ya yi saving, my son, kiran number ta fara yi.
Lokacin da kiran ya shigo kuma suna asibiti shi da Rismha, bata daina kuka ba har ya É—auki kiran, kuma ya É—auki kiran ne da tunanin ko dai daddy ne tun da number sane.
A nitse ya ce "Hello Bappa" cikin kuka ta ce "Yaya Imran ina kake?". Jin kukanta ya sa ya ruÉ—e shima sosai, hankali a tashe ya ce "Jelly menene yake faruwa? Me akayi miki kuma?".
Hannu daddy ta kama ta zura a bakinta tare da gyara kwanciyarta tana mai juya kukan nata izuwa tsantsar na shagwaɓa har da turo baki kamar ba ita ba, gaba ɗaya palo sun mayar da ita Tv harta Akil yau yana ganin ikon Allah, su Aunty kam ba'a magana sun sami Tv ai, Abbi ma dai ta ɗaure mashi kai tare da jefa shi cikin tunanin anya tana da lafiya kuwa.
"Yaya Imran ya naga har yanzu baka shigo palo ba? Ina son ka shigo ne fa na yi maganar akan idon ka" ta faÉ—a tana tsotsar yatsan daddy da ta sanya a cikin bakinta.
ÆŠan dafe kansa Imran ya yi kafin ya ce "My wife please ki rufa mani asiri kada ki faÉ—a kin ji ko? Na yi maki alkawarin ba zan kara ba, idan kika faÉ—a wlh zaki ja mani abubuwa da dama, ciki kuma har da raini tsakanina da kanne na, wato su AKILA".
"To ni ba kanwar ka bace? Ai nima raina ka kenan zai yi ko? Tun da ni ka yi wa abin, ni a kaina baka ji kada na raina ka ba? Sai su Akila?, To ni dai gaskiya sai na faÉ—a ka shigo ko karka shigo yanzu kuwa zan gaya sai anjuma" . Diff ta katse kiran tare da kwashewa da dariya kamar ba ita ba.
Miƙewa Akil ya yi tare da karasowa wajen yana faɗin Irfan ya zo ya riƙe mashi ita bari su yi mata ruƙiya wata kira aljanun kan nata za su tafi.
Cikin sauri daddy ya ce bari ma ya riƙeta da kanshi domin idan aljanun suka tafi sai ya fi kowa murna. Zuba masu ido ta yi tana kallon ikon Allah.
Ai kuwa har Akil ya gama ruƙiyarsa ba bu wani motsin da zai nuna maka da aljanu a kan Jelly, lafiya lou take kawai dai iskanci ne kwando kwando ta tara a kan nata, shiru palon ya yi suna kallon ikon Allah.
Miƙewa ta yi daga jikin daddy ta haye sama abinta kamar wadda aka kira hannunta na riƙe da wayar daddynta wadda Imran yake ta kira tun ɗazun, bawan Allah duk ta rikita shi, sai addu'a yake yi Allah yasa kada ta faɗa
Tana shiga É—akin Hanan ta yi picking na call É—in tare da hayewa saman gado tana faÉ—in "Yaya Imran É—ina ina kewar wlh, dan Allah ka dawo cikin palo ka ji?".
Nauyayyar ajiyar zuciya bawan Allah ya sauƙe kafin ya ce "My wife kin faɗa ne ko baki faɗa ba?" Juya waƴan nan dara daran idanun nata ta yi kafin ta ce "E na faɗa kuma daddy ya ce zaka zo ka same shi".
Shiru ya É—an yi kafin ya ce "To shikenan da daddare zan zo sai na bawa daddyn hakuri kema kuma ki yi hakuri ba zan sake ba".
Shiru itama ta É—an yi kafin ta ce "Yaya Imran dama idan mutun ya yi wa matarsa kiss sai ya bawa babanta hakuri ne? Ina cewa da zarar an É—aura aure kun zama mallakin juna".
Imran ya kasa magana, ya rasa ma ta ina zai fara, ya rasa wani amsa zai bawa yarinyar nan, ya rasa me zai ce mata, anya jelly ba zata haukata shi ba wata rana kuwa? Anya kuwa tana lafiya?.
Turo baki ta yi cikin shagwaɓa tare da yin kasa da murya ta ce "Yaya Imran kai fa mijina ne ba zan tona maka asiri ba, amma dai kada ka sake cinye mani bakina haka, ya yi yawa fa, kuma dama ina son yi maka wasan kafin a kai ni gidan kane shiyasa na yi maka haka, na yi karatun islamiyya ai, kuma ina kallon film sosai, sannan daddy da kansa lokacin da zai aura min Muneer ya gaya mani me ake nufi da aure, so ka ga ai na sani, amma dai yaya Imran kana da tsoro dayawa fa, i am the winner a wannan game ɗin". Ta kai karshen maganar tana dariya.
Bawan Allah bai san time da murmushi ta suɓuce mashi ba, cike da so da kuma kaunarta ya ce "Amma dai gaskiya kin gama da ni, kin saka ni na gudu na bar gidan, amma ba komai zan rama ne, bari na damke ki zaki yi bayani da yaren da ke kanki baki san shi ba".
Dariya ta yi ta mirgina ta mirgino kafin ta ce "Yaya Imran ba wani bayanin da zanyi mijina yaya Imran zai kwace ni daga hannunka ai". "Da gaske?" Ya faÉ—a yana É—aga gera É—aya kamar tana a gaban shi.
Jinjina mashi kai ta yi tana faɗin "E da gaske". Jinjina kai shima ya yi kafin ya ce "To Shikenan ina nan zuwa gidan ai, a nan zamu ci abincin dare, wani irin kwalliya zaki yi wa mijinki?" Ƴar dariya ta yi har sai da hakwaranta suka bayyana.
"Wani irin kwalliya kake so Yayana?" Shiru ya yi yana tunani, can kuma sai ya ce "Wando da riga masu kyau sai ki sanya hijabi a sama dan kada kowa ya kalla mani ke" murmushi ta yi kamar ba ita ba, ta nitsu sosai ta ce "Tom an gama amma dai...." Sai kuma ta yi shiru.
"Amma dai me My jelly?" "Ba komai yaya Imran" "Gaskiya ban yarda ba, akwai dai wani abu, gaya mani menene?". Shiru ta É—an yi kafin ta ce "Amma dai zaka kawo mani chewing gum da kuma ice candy ko?".
Cool murmushi ya saki yana faÉ—in "Iya shi kaÉ—ai kike so ko dai akwai wani abin?" "Shi kaÉ—ai nake so, sai kuma ganin fuskarka, Allah ina kewarka sosai".
"Allah sarki muna asibiti ne da Rimsha, amma dai yanzu za mu baro asibitin, idan mun fito sai mu wuto nan kawai".
Ɗan kiƙewa ta yi a zabure tana faɗin "Me ya kai ku asibiti kuma?" Tana magana tana kara zare idanun nan nata sosai, "Ɗan ciwon kai ne yake damun Rimsha, amma dai an bata magani yanzu zamu taho".
Koma wa ta yi ta kwanta tana kara dafe kirjinta domin ta ɗan ji sauƙi jin ba wata matsala ba ce ta faru.
"My jelly zaki bi yaya Imran naki idan na zo ko?" Shiru ta yi mashi bata amsa ba, a can cikin zuciyarta kuma tunanin kalar tsiyar da zata yi mashi shi da daddy take yi, dan ta yi niyar sai ta yi masu tsiya sosai da sosai.
"My jelly baki jina ne?" Ya faɗa daidai lokacin da yake miƙawa Dr hannu suna gaisawa akan za su wuce shi da Rimsha, tun da Allah yasa ta farfaɗo kuma ta dawo cikin hayyacinta, Allah ya takaita abin saboda addu'a da karatun Al Qur'ani mai girma da take yawan yi.
"Yaya Imran ka bari sai ka zo É—in ka ji ko?". To ya amsa mata da shi sannan suka yi sallama, ta É—aura wayar a saman bedside drawer tare da gyara kwanciyarta ta kwanta tana tunanin kiss da ya yi mata É—azun, wani irin yanayi ta ji a jikinta.
A can palo kuma, cigaba da hiransu suka yi, da farko sun yi niyyar bin bayar Jelly É—in, amma daddy ya dakatar da su a in da yake gaya masu su fita harkarta, domin lafiya lou take, iskanci ne kawai.
Hakan yasa suka kyaleta aka cigaba da hira, miƙewa Akil ya yi ya fice waje dan ya amsa kiran da ake yi Mashi, Umaisha, Akila, Hanan, a tare suka miƙe dan su haura sama su bawa iyayen nasu fili su tattauna.
"Aunty Ayla muje ko?" Cewar Umaisha, É—an satar kallon daddy ta yi domin ba iya tafiya zata yi ba.
"Umaisha ku je Batula zata zo tare da ita". Shi ne abin da daddy ya faÉ—a, to suka amsa da shi kafin su wuce sama.
Dawo da kallonsa kan Hjy Batula daddy ya yi yana faÉ—in "Batula Æ´aÆ´anki nawa ne a yanzu?" Duk kunya ya isheta, ta zubar da Æ´an uwanta, shiyasa tun da ta shigo palon ta kasa sakewa saboda kunyarsu da take ji.
"Ƴaƴana uku, biyu maza ɗaya mace, akwai HAROON da HARISH sai ABLA ita ce auta".
Addua sosai Abbi da daddy suka yi wa Æ´aÆ´an nata tare da ita kanta, sannan suka ce ta saki jikinta komai ya wuce ai, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta yi masu godiya sosai da sosai.
"Batula taimakawa Ayla ta bi bayan Æ´an uwanta zuwa sama". Cewar daddy.
To ta amsa da shi tare da tambayar wace ce Ayla ɗin. A takaice sama sama Abbi ya bata labari, sosai ta yi murna sannan ta yi wa daddy gaisuwar rasuwar mummy jelly kafin ta riƙo hannun Ayla ɗin dan su nufi sama.
Ƴar kara ta saki lokacin da ta miƙe, girgiza kai daddy ya yi Ayla raguwa ce ta karshe, hakan yasa yake cewa tayi yarinya, ba wai shekarun yake dubawa ba, shi yasan me yake dubawa yasa yake kiranta da yarinya.
Ganin abin da ya faru yasa Hjy Batula ta gane me ya wanzu a tsakanin yayan nata da kuma matar tasa, hakan yasa ta kara Kaunar Ayla sosai da sosai, cikin dabara ta taimaka mata suka wuce sama, miƙewa ita ma Aunty ta yi dan ta bi bayansu, shima dai Irfan miƙewa ya yi ya fice daga Palon dan ya ba su waje su sha hirarsu.
Bayan Hajiya Batula ta kai Ayla ta dawo, nan fa suka ba ke hira su uku, Abbi, daddy, da kuma ita Hjy Batular, sai hiran baya suke yi.
Misalin karfe 6:30 Imran ya shigo tare da Rimsha, yadda su Akila suka bar su Hjy Batula haka su Imran suka zo suka same su.
Tambaya Imran ya yi akan ina su AKILA, suna sama Abbi ya bashi amsa, cewa Rimsha ya yi akan ta bi su sama su zauna tare shi kuma bari ya duba Irfan yana zuwa. Da haka suka rabu, sai kallon Rimsha Hjy Batula take yi, É—azun ribibi sun yi yawa, bata samu damar ganin Rimshan ba sai yanzu da su Nawid suka tafi, komai ya saitu.
"Batula lafiya kike kallon Rimsha haka?" Cewar Abbi, ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ce "Wlh ta yi mani kama da Baban su HAROON ne, sosai fa shiyasa nake kallonta".
"Babansu Haroon kuma?" Cewar Daddyn Jelly, E ta amsa da shi. "To ko dai suna da dangantaka ne?" Cikin sauri ta girgiza kai tana faÉ—in "Kai ina baban su Haroon ba shi da wasu bakin Æ´an uwa da ban sansu ba, kama dai ce kawai, shima kamar ai hancin ne da ido sai yanayin fuska".
To masu karatu kada ku mance Mummy'n Rimsha ƴan uwan mahaifinta ƴan Maiduguri ne, kuma a halin yanzu can ta tafi neman ƴan uwan nata, zata iya yi wu suna da alaƙa da mijin Hjy Batula, mu dai je zuwa dan jin yadda wannan cakwakiya zata warware mana.
Haka suka ci-gaba da yin hirarsu while su kuma ƴan matan suna sama suna zuba iya shege san ransu, AKILA ta tasa su a gaba tana koya masu shagwaɓa kirsa da kisisina na jan hankalin miji, Aunty dai ta saki baki tana kallon yadda Akila ke zuba masu lecture.
Riƙo kunnan jelly da kyau Akila ta yi tana faɗin "Wlh ki natsu ki sanya mani yayana cikin farinciki, kin san dai yanzu ba zan bi bayanki ba sai an buga football, idan yaya Imran ya cinye kwallon sai na dawo bayanki, amma dai yanzu gaskiya ina bayan ɗan uwana, ki saurareni da kyau, fagen shagwaɓa ba sai na koya maki ba wannan kece shugaba, kin kware ta wannan hanya, sai dai mu koma salon iya magana, iya magana yana sanya miji ya yi abu ko bai yi niya ba, idan kina magana da shi kuma ki rinƙa ɗan yin wasu abubuwa kamar karamar yarinya, hakan zai ja hankalinsa ba kaɗa ba, amma fa ki tabbar kin iya yin hakan sosai ta yadda zaki sanya shi jin daɗi ne ba wai ki ɓata mashi rai ba, dan wata idan ance ta yi abu kamar yarinya sai ta je tana yi mashi shirme da hauka tasa ya ji kamar ya ɗauketa da marin da sai ta suma a wajen dan haushi, to na dai gaya maki ba haka ake yi ba, yanzu idan kina son ce mashi ku fita zuwa anguwa, ba kawai zuwa zaki yi ki ce mashi yaya Imran zamu fita zuwa anguwa ko? Ba haka zaki yi ba, zuwa zaki yi ki kwanta a jikisa, dama gaki da shegen san jiki kamar mage, to idan kika kwanta, ki yi ta yi mashi kukan shagwaɓa ki na ɗan jan hancinsa, idan ya ce maki lafiya, ba haka kawai zaki ba shi amsa ba a'a, cikin salo mai ɗaukar hankali ki juya idanun nan na ki, ki yi mashi fari kafin kice kyau ka yi mani mijina aljannata, shiyasa na ji ina son in zo in yi ta kallon fuskar ka ina ɗan jan wannan kyakkywa kuma dogon hancin naka, wlh ko bai nuna maki ba sai ya ji daɗi a cikin ransa, ki cigaba da zuba mashi shagwaɓa da wasanni na taɓa wasu ɓangarori daga jikinsa, sai kun yi nisa kun lula duniyar da ba zai iya yi maki musu ba a can, sannan ki gaya mashi abin da kike so ta sigar da dole ya amince ko da baya so ɗin, sannan kuma kada ya kasance lullun ta hanya ɗaya zaki rinƙa bi wajen isar mashi da saƙon abin da kike so, idan ya zamana ta hanya ɗaya ne to zai gane ki ya zama watara ma da kin zo kin fara yi mashi ma zai ce kawai ki faɗi abin da ya kawo ki dan yasan ba haka nan ba, so akwai hanyoyi da dama da zaki rinƙa isar mashi da saƙo ba tare da ya gane hakan ba, ciki kuma har da girki tare da kula da shi a lokacin da yake cin abincin, idan da dama ki rinƙa bashi a baki, kuma kada ki yarda ya zamana sai kina son abu a wajensa ne zaki nuna mashi soyayya, a'a kullun ya zama cikin zuba mashi sabon salon soyayya mai rikitarwa kike yi, mace bata tsufa kuma bata girma a gaban mijinta, dan haka ki saki jiki ki kula da shi, wlh miji ko tsohone yana son kulawa, sai kuma batun sanya kaya, kada ki yarda ki ce zaki sanyawa yaya Imran ɗina manyan kaya, idan na ji kin yi hakan zamu haɗu dake ne, idan kuna ɗaki ku biyu, ki samo wasu shegun kayan barci masu birkita tunani da kuma lissafin ƙwaƙwalwar ɗan Adam, su zaki ɗauko ki sanya ki taho gare shi, wani lokaci kuma kada ki zo kai tsaye, ki rinƙa ɗan yawo ta gabansa kamar mai yin wani abin, zaki ga da kansa zai jawoki jikinsa dan ya ƙosa ki zo ke kuma kin ki, kinga gidan yaya Imran ke kaɗai ce, to dan haka duk wasu manyan kaya ki ajiye su a gefe guda, ki kwaso shegun kaya dan a buga harka, sannan kada ki rinƙa sanya breziya da daddare, ina ki barsu su kai mashi saƙon suna da buƙatar shi, idan ya gansu a tsaitsayen nan ba karamin haukace miki ya birkice maki zai yi ba, kada ki kuskura ki bar mani kwakwalwar yaya Imran ta zauna shiru har ta yi tunanin wani abin, idan yaya Imran zai yi wani tunani to ya zamana tunaninki ne ke kaɗai da kuma kayan abubuwanki, ga ki dirarriya, dan haka ki diranwa tunaninsa a ko da yaushe ki......" Bata karisa ba Aunty ta rufe mata baki da hannunta tana salati domin yau ta ji abin da ya fi karfinta.
Gaba É—aya cikin É—akin babu wanda bai nisa ba, wasu kam irin su Rimsha har da jan dogon numfashi.
"Akila shekarunki nawa?" Cewar Aunty, ta yi maganar tamkar ba lafiya ba, muryarta cike da mamaki tab, bata taɓa jin karatu irin na Akila ba, ba wanda ta taɓa jin yana bada irin wannan shawari sai a bakin Akilar.
Cire hannun Auntyn Akila ta yi daga bakin nata tana faÉ—in "Aunty me ya faru? Shekaruna ai É—aya ne da Umaisha 18 to 19 muke". Mamaki ya hana Aunty sake yin magana.
Akila na ƙoƙarin sake tambayar auntyn ko dai lafiya. Sai ta ji wayarta ya yi kara alamar shigowar sako. Wani irin sihirtaccen kayatatcen murmushi ne ya bayyana akana face nata domin tasan sakon abin son ta abin begenta ne wato ɓoyayyen masoyi.
Zuba mata ido gaba ɗaya ɗakin suka yi har da jelly mai ɗaukar lecture ma binta da ido ta yi, yau Jelly ta natsu tsit tamkar ba ita ba, duk cikinsu harta aunty ba wanda bai karu da karatun nan da Akila ta yi masu yanzu ba, sai saka zancen a ransu suke yi, kowa yana saƙa yadda zai yi wa masoyinsa, ita kuwa Rimsha har ta hangota tana yi wa Lion hakan, ita kam Hanan ta dai ɗauki karantun ta ajiye a cikin zuciyarta dan bata da masoyin ma bare kuma ta ce zata yi tunanin yi mashi, ta dai ajiye ne sai Allah ya kawo mata sai ta yi mashi, Umaisha kam jirama take yi suyi sallar mangariba ta je ta zubawa mijinta kala kala sala sala abin data koya na yau, ita ma dai Aunty ta ɗauki wasu daga ciki, ta kuma yi niyar kwatanta yi wa Abbi ta gani.
Ɗaukar wayarta Akila ta yi ta buɗe saƙon nasa, sai murmushi take yi, a cikin zuciyarta ta fara karanta saƙon nasa.
"My heartbeat gaskiya ke karshece wajen iya soyayya, wannan irin lecture haka? Anya idan muka yi aure zaki barni na fita kuwa? Gaskiya na ji daÉ—i kuma na mori mata sosai da sosai, Allah ya mallaka mani ke my heartbeat É—ita É—aya tamkar da billon, nasan kina kewar voice na, amma ki yi mani afuwa zuwa karfe 10 dare zan kira ki ko? Yanzu abubuwa sun É—an sha kai na ne, amma ayi mani afuwa gimbiyata".
Duk sun zuba mata ido suna kallon yadda take murmushi tana kallon screen ɗin wayarta, a tunanin Umaisha da Irfan take yi, shi take yi wa wannan murmushi, saƙonsa take karantawa, dan a iya saninsu shi kaɗai ne saurayinta.
Suna a haka har aka kira sallar mangariba, a tare suka miƙe dan su je su yi alwala, jelly dai kwanciya ta yi dan bata Sallah, ita kuwa Akila bayan ta yi alwala kafin ta yi sallah sai da masoyin ɓoye ya tura mata massage akan ta yi masu addu'a sosai idan ta yi sallah, dama already ya saba faɗa mata hakan, duk idan zata yi sallah sai ya yi mata massage akan idan ta yi, ta yi masu addu'ar zama mata da miji su mallaki juna, kuma haka take yi, duk in ta yi sallah sai ta yi masu addu'a akan zama mata da miji, daren jiya ma har istihara ta yi akan su shi da Irfan, tana addu'ar Allah ya zaɓa mata wadda ya fi zama mata alkhari a cikinsu, amma abin mamaki shine duk da bata san waye masoyin ɓoye ɗin ba tana ji a jikinta shine zaɓin da Allah ya yi mata, saboda ta fi samun kwanciyar hankali idan ta kasance suna hira da shi, sannan tana yawan mafarkin wata kyakkyawar face ɗin a matsayin tasa, ba barcin da zata yi ba tare da ta kalli wannan fuska ba, sai dai kuma wannan fuska data Abbanta take yi mata kamanni, shine babban abin da yake damunta, wadda take mafarki a matsayin fuskar masoyin ɓoye kamar Abbanta dan dai shi yaro ne kawai, kuma mafarki ai zata iya mai da mutun yaro ta kuma mai da shi babba.
Bayan sun yi sallar isha ne Jelly ta tsara wankarta sosai, ta shirya cikin irin kayan da Imran ya ce yake buƙata, Aunty ta bata wani pant ɗin tare da Always dan ta sanya, karɓa ta yi ta sanya a jikinta sannan ta nufi palo tana gayawa Akila ta tafi wajen yaya Imran dan tun ɗazun yake kiran layin daddy da wayar ke a hannunta.
To AKILA ta ce tare da kara ja mata kunne akan ta natsu ta yi abin da ya dace, kada ta yi mashi shirme, dawowa ta yi ta ringume Akilar kafin su yi sallama, ta rungumi Ayla sannan ta rungumi Rimsha tare da Umaisha suka yi sallama.
Jelly na fita massage ɗin Masoyin ɓoye ya shigo wayar Akila, cikin zumuɗi Akila ta duba, saƙo ne kamar haka. "Heartbeat ɗina wannan yarinya da ta fita yanzu ta yi mani kama da brother na fa, sai dai ba sosai ba ido ne ya yi kama". Shiru ta yi tana haɗa maganganun a cikin ƙwaƙwalwarta, tunani take yi koma waye masoyin ɓoye nan tana ji a jikinta na kusa da ita ne, kuma da wuya idan ma ba ɗan uwanta bane domin a mafarki tana kallon shi mai kama da Abbanta, yanzu kuma ya ce idanun Jelly kamar na ɗan uwansa, to kenan akwai alaƙa a tsakaninsu ne ko yaya. Tana tsaka da tunani massage nasa ya sake shigowa.
"Heartbeat ki É—auki duk abin da zuciyarki zata gaya maki a kaina, amma dai am sorry to say kamar ni ba mutun bane, but kada ki ji tsoro kin ji ko? Ni bana cutar da kowa sai dai ya so kowa da alkhari, sisterki da ta fita yanzu abin da yasa na yi magana akanta saboda tana da manyan idanu sosai kamar wannan É—ayar sister ta ki wato Rimsha, girman idanun nasu yasa nake ganin kamar brother na, amma ba wani abu bane, ni dai fatana kada ki gujeni".
Wurgar da wayar tata ta yi jin ya ce shi ba mutun bane, nan take jikinta ya fara kerma, da sauri ta diro kasa daga saman gadon ta yi waje wanjensu Abbi dan ma kada ya kamata. (TO FA YAU DAI GA AKILA NA GUDUN MASOYIN ÆOYE🤣🙃)
Su Umaisha kuwa ganin ta fita yasa suma suka miƙe suka fice suka bar wayar tata a tsakiyar gado, ita ma Ayla tana jan kafa a hankali haka ta bi bayansu.
Suna fita wayar ta kawo wutar screen da kanta daga nan kuma ta shiga massage da kanta ta goge massages ɗin ɓoyayyen masoyi na karshe daya turo na cewa shi ba mutun bane, wayar da kanta ta goge saƙon sannan wani saƙo ya shigo na ɓoyayyen masoyi akan wasa yake yi mata shi mutun ne, daga nan wayar ta yi switch off na kanta da kanta. To fa Babbar al'amari kenan
A ɓangaren Jelly kuwa, bata sanya hijabin kamar yadda Imran ya ce mata ba, ta dai sanya wasu shegun riga da wando da Aunty ta bata daga cikin kayan lefenta, su ta sanya a jikinta sai tashin kamshi take yi, duk ilahirin shape da wasu halittu na jikinta sun bayyana, kayan sun matseta sosai ne saboda ta fi Aunty cikar halittu.
A palo ta isko su daddy, Abbi, daddy, Auntyn, Irfan, Hjy Batula, da kuma Akil, sai hira suke yi, shi kuma Imran yana zaune a garden na gidan yana jiranta, tun da suka dawo sallar isha ya wuce can. Kada ku manta duk abin da ake yi Ommu tana sane tana jinsu kawai dai fitowa ne bazata yi ba dan bata jituwa da dangin na Abbi.
Zuwa ta yi ta rungumi daddy tare da yi mashi kiss a goshi, shima kiss É—in ya yi mata, wucewa ta yi ta nufi waje ba tare da ta yi wa kowa magana ba domin bata sansu ba.
"Jelly baki gaishe da su yaya Deen ba". Cewar daddynta, juyowa ta yi fuska É—auke da murmushi tana faÉ—in "Daddy i don't know them ai, among of them who is Yaya Deen É—in?".
Da hannu ya nuna mata waye yaya Deen a cikin su, juyawa ta yi zuwa jiki Abbin ta haye tana faÉ—in "Yaya Deen good evening?" Akil ne ya ce mata "Bappa zaki ce not yaya Deen, he is your uncle not your brother". ÆŠan kallon Akil É—in ta yi kafin ta ce "Okey tom uncle good evening". Jelly ba dai son jiki ba, ta ce bata san su ba, amma ta hayewa Abbi jiki ta kwanta.
Da fara'a Abbi ya amsa sannan ya tambayeta wannan kwalliya da ta ci kuma sai ina, ba ko kunya ta gaya mashi yaya Imran ne yake kiranta kuma shine ya ce ta yi mashi kwalliya haka, yau duk rashin kunya irin na Akil sai da jelly ta sanya shi jin kunya, domin a irin yadda yake kallon Imran ustadz bai kai shi har zuwa wannan layin na sanya mace yin wasu dressing É—in ba.
Shi kuwa Abbi danasanin tambayar tata ya yi domin ta fara bashi labarin har irin kayan da Imran ya ce ta sanya mashi, da dai daddy ya ga zata tonawa yaron shi asiri sai ya ce ta tashi ta tafi surutun ya isa haka. Ba musu ta miƙe tare da miƙawa daddyn wayarsa ta fice abinta, da ido daddy ya bita yana mamakin tare da tausayawa Imran, dan yana da aiki babba a gabansa.
Tana fita ta nufi garden É—in sai wani kwas kwas take da takalmarta mai tsawo. Gaba É—aya wutar garden É—in a kashe, wajen a akwai duhu, É—an tsorata ta yi da ganin wajen haka, amma sanin cewa Imran yana wajen yasa ta karisa wajen da confidence nata.
A tsakiyar wajen ta tsaya tana ƴan waige waige ko zata ga alamunsa, amma ina shiru. Tana ƙoƙarin juyawa sai ta ji an rungumeta ta baya, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "Yaya Imran ka bani tsoro fa".
Murya can kasa kasa ya ce "Sorry my wife, ai so nake na tsorataki dama, amma kuma sai na ji na kasa".
Ɗan murmushi ta yi kafin ta ce "Da ka tsorata ni kuwa da mun ɓata". Juyo da ita ya yi suna fuskantar juna a duhu, a hankali ya jawota jikinsa tare da riƙota ta bayanta yana haɗe goshinsu waje guda.
"Meyasa baki sanya hijabin da nace ba?" Ya yi maganar cikin wata irinyar murya mai kwantar da hankalin mai sauraro. Sarkin son jini, kwantar da kanta a kirjinsa ta yi a shagwaɓe ta ce "Yaya Imran ai ni bana son hijabin ne". Wani irin yanayi ta jefashi yadda ta yi maganar nan tata.
Riƙota da kyau ya yi suka zauna a saman ɗaya daga cikin kujerun wajen tana a saman cinyarsa. A daidai saitin kunnenta ya kawo bakinsa, cikin raɗa kamar wani zai ji su ya ce "Zaki bi mijinki mu tafi tare?" Tana daga lafe a kirjinsa ta ce "E zan bika mana".
Wani irin daɗi ya ji wadda ya sanya shi natseta a jikinsa sosai da sosai. "Yaya Imran zaka ɓallani fa". Ta faɗa a shagwaɓe.
"My wife zaki bawa mijinki damar yin kissing naki? Na yi ko sau ɗaya ne?" Girgiza mashi kai tayi alamar bata so, shiru ya ɗan yi kafin ya ce "To shikenan tun da baki so, ni ma bana so dan bana son abin da bakya so". Ya kai karshen maganar tare da fara shafa bayanta yana mai jan wani irin numfashi yana sauƙewa a hankali hankali.
Jin abin da ya ce yasa ta ɗago kanta daga kirjin nasa tare da gyara zamanta ta haɗe fuskokinsu waje guda. "Yaya Imran ni fa matarka ce, me yasa zaka tambaye ni dan zaka yi mani abin da ya kasance halak ɗin ka?" Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe ba tare da ya yi magana ba ya haɗe bakinsu waje guda ya fara bata hot kiss, shiru ta natsu tana karɓar saƙon da yake aika mata da shi, while a can cikin gida kuma, sun koma saman table dan cin abincin dare.
💖💖TRIPLETS💖💖
dedicated to AISHA BAITA JIDDAH 💘 (MUMMO RIMSHA)
E89-90💖
Jin abin da ya ce yasa ta ɗago kanta daga kirjin nasa tare da gyara zamanta ta haɗe fuskokinsu waje guda. "Yaya Imran ni fa matarka ce, me yasa zaka tambaye ni dan zaka yi mani abin da ya kasance halak ɗin ka?" Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe ba tare da ya yi magana ba ya haɗe bakinsu waje guda ya fara bata hot kiss, shiru ta natsu tana karɓar saƙon da yake aika mata da shi, while a can cikin gida kuma, sun koma saman table dan cin abincin dare.
Akil ba kunya ya rinƙa bawa Umaisha abinci a baki kamar yadda suka saba, yau sai wani yauki Umaishar take yi mashi kamar mace mai karamin ciki, Hjy Batula ta lura da hakan, shiyasa ma ta zage take ta faman turawa Umaishar duk abin da take buƙata, har da tambayarta ko akwai wani abin kwaɗayi da take buƙata, kamar an ce mata cike Umaisha ke da shi, Abbi ma dai ba'a barshi a baya ba, tsab ya gano ƴar tasa kamar akwai ajiya a jikinta, shiyasa shima yau yake bata kulawa ta musamman, oga Akil kuwa ya san komai domin ko wani motsi na matarsa tsab ya san komai, sai dai wani sain nuna mata yake yi kamar bai san komai ɗin ba, dan su cigaba da zaman lafiya, dama kuma haka ya dace namiji ya kasance, ba komai ne zaka rinƙa nunawa mace ka sani ba, domin mata ba su son ka rinƙa nuna masu kamar kai ka san komai ɗin kana fariya, idan hakan tana kasancewa to da wuya a rinƙa samun jituwa a tsakaninku.
Akila kuwa duk ta susuce ta zama wata sukuku da ita, tunanin abin da masoyin ɓoye ya ce mata ne gabaɗaya ya birkita mata kwakwalwa, ta zama kamar ba ita ba, Irfan ya yi rarrashin duniyar nan akan ta gaya mashi mene ne yake damun ta, amma ina taki gaya mashi, ba dan ya so ba ya kyaleta.
A ɓangaren gidan Lion kuwa. Lokacin da Areef ya farka daga barcinsa, ya farka ne yafiya lou kamar babu wani abin da ya faru, sai dai fa ya farka da ciwon jiki, gabaɗaya zafi jikinsa yake yi mashi, wayarsa ya ɗauka dake a saman bedside drawer ya duba time, 6:40 pm dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali kafin ya fara duba cikin wayar tasa, miss calls ɗin daddynsu ne da Aseef a cike a ciki, gobe Musharraf zai ta so shiyasa Aseef yake ta kiran shi a waya dan ya ji jirgin ina zai bi domin da jirgin kasuwa zai zo, ya bi jirgin Spain ne ko yaya.
Layin Imran ya fara kira akan ya aiko mashi Rimsha ta É—ebo mashi drinks a freezer dake a kitchen, na cikin bedroom nasa sun kare, tun É—azun ya so cewa a kawo mashi, amma bai sami dama ba, Saboda lokaci jikinsa na ya mashi ciwo sosai.
Number Imran bata shiga hakan yasa ya ce bari ya kira Lion, bai kai ga kiran Lion É—in ba kiran Aseef ta shigo, É—aukar kiran ya yi video call ne, dan Aseef bai cika kiransu normal call ba, sai dai video call dan ya gansu su gan shi.
Har lokacin bawan Allah murmushi ne akan face nasa, ya fito ne daga gym yana nufar cikin gida, iya singlet da shot ne kawai a jikinsa, sai haÉ—a zufa yake yi, kewar É—an uwan nasa ne ta takura mashi ya sanya shi ya kira shi dan suga juna ko ya É—an ji daÉ—i.
Areef bai san time da murmushi ta subce mashi ba ganin É—an uwan nasa yana murmushi. "Aseef daga ganin face naka akwai wata a kasa, so what is this?".
Kara faɗaɗa murmushin sa ya yi kafin ya ce "Ina murna ne na ɗan iya kalmomi almost 10 a cikin yaren Hosa (Hausa)" kunsan harshen nasa ne a lanƙwashe take akan yaren Hausa, shiyasa bai iya kiran Hausar ba.
Girgiza kai Areef ya yi yana mamakin yau Aseef ne da karya, to fa babbar magana, abin da bai taɓa kwatantawa ba, za su iya rantsewa da Allah koda a bayan Aseef ɗin ne, zasu iya bugan kirji suce bai taɓa yin karya ba, haka yake duk abin zai fito daga bakinsa to gaskiya ce, hakan yasa duk gidan bayan Lion idan ya yi magana babu mai musa maganar tasa, domin kuwa idan sun musa ma kansu suka yi wa, shi dai gaskiya ya faɗa.
Sosai Areef ya zuba mashi idanu dan ya karanci me a fuskar tasa da ya yi mashi karya akanta yau, abin ya É—an É—aure mashi kai.
Ganin Areef yana ta kallon shi ne yasa ya É—an kawar da wayar daga saitin face nasa yana faÉ—in "Why are you looking at me like this? What are you looking for?".
Murmushi Areef ya saki domin ya kuma ganowa karara akwai abin da Aseef ya ɓoye mashi, da alama kuma damuwa ce domin wannan murmushi da take kan face ɗin nasa ta dole ce, ba kamar murmushin da ya saba yi masu bane, idan baku manta ba shima Lion lokacin da Aseef ɗin ya kirashi da kallo ɗaya ya yi mashi ya ce to me Aseef kuma ya jajuɓo masu, kunga kenan akwai dai wani abin a kasa kamar dai yadda suke tunani, amma ya kafe akan lallai shi bashi da damuwar komai, amma kuma da alama Lion ya san da damuwar shiyasa ma bai tambayi dalilin shigarta ba.
"Aseef where is uncle Musharraf?" Cikin sauri ya dawo da wayar saitin face nasa yana faÉ—in "Uncle yana cikin gida yana karisa shirye shiryensa dan kaga jirgin safe zai bi ai". Ya yi maganar tamkar zai yi kuka, jinjina kai Areef ya yi domin ya gano me matsalar dama kuma ya yi mashi tambayar ne dan ya bugi cikinsa ya gano me ainahin damuwar, sai dai kuma koma yaya ba zai iya barin Musharraf a Usa ba tun da basu nan, yasan halin Æ´an uwansa sarai, ko daddy idan ya san Musharraf musulmi ne yana iya kashe shi da kansa, gara idan da suna nan ma, ko Lion ba zai bari ayi mashi wanin abin ba tun da ya kasance musulmi.
Sun jima suna hira Areef yana kara karfafa mashi gwiwa akan ya gama exams ya zo ya same su, tare kuma da kwantar mashi da hankali akan kada ya damu da tafiyar Musharraf, shi dai kawai ya tsaya ya yi karatu, da haka suka sha hira na ƴan uwa masu masifar kaunar junansu kafin su yi sallama Areef ya kira Lion bai ɗauka ba, hakan yasa ya yi kokarin ya miƙe da kansa yana jan kafa ya fito Palo, shi kuma Aseef toilet ya wuce dan yin wanka bayan ya ɗaura wayar a saman bed nasa kenan.
Babu kowa a palon da Areef ya fito, a hankali yake jan kafarsa da yake a kirji akayi mashi aikin, shiyasa ma yake iya takawa a hankali, da kyar ya haura sama ya nufi É—akin da yake zaton ita ce ta Lion É—in, Sakamakon kamshin perfume nasa da ya yi yawa a É—akin.
Babu kowa a cikin É—akin sai saukar ruwa dake tashi daga toilet alamar yana wanka kenan.
Saman gado Areef ya haye ya kwanta yana sauke numfashi ya kawo da kyar.
Idan muka koma gidan Abbi kuwa, IMRAN & JELLY sosai ya yi kissing nata son ranshi, bata hana shi ba, kuma bata yi mashi kuka ba domin bata a hayyacinta, ya gama kashe mata jiki dukka, tuni ya sanya ta ta lula duniyar sama jannati, ba ta ma san time daya zura hannunsa a cikin rigarta ba, sai dai ta ji wani irin yanayi mai wuyar misiltawa ya kara ninkuwa mata a jikinta, kankame shi ta yi tana sakar mashi wani irin numfashi wadda ke kara rikitar da shi.
Hakan yasa ya kara birkice mata yana aika mata saƙonni babu wasa, daga karshe ma kwantar da ita ya yi a saman kujerar ya yi mata rumfa da kirjinsa tare da ɗage rigarta sama ya capco nipple nata ya fara tsotsa kamar sweet.
A wannan lokacin ne kuma ta samu damar sakar mashi kuka domin nipples É—in sun fara yi mata zafi, ya murjesu sosai sannan kuma ya zo yana tsotsa mata.
Can kasa kasa ya fara jiyo kukan nata, da kaÉ—an da kaÉ—an har ya jiyo sautin tata da kyau, idanunsa a rufe, da kyar ya koma gefenta ya zauna tare da jingina kansa da jikin headboard na kujerar yana sauke wani zazzafar numfashi.
Ita kuwa cigaba da kuka ta yi duk da ya kyaleta É—in ma, ba ita ta yi shiru ba har sai da ya rarrasheta sannan ta yi shiru, amma fa ya sha fama wajen rarrashin nan nata kafin ya samu ta yi shiru.
Rumgumeta ya yi suka yi shiru, ban da saukar numfashin su dake tashi a hankali babu wani abin da zaka ji a wajen.
A cikin gida kuwa, sun kammala cin abinci lafiya lou, Akil ya ce su za su koma gida sai jibi za su zo, kiransa gefe guda Hjy Batula ta yi dan su yi magana, da yake yanzu da ya yi aure ya yi sauki sosai sai ya bi goggon tasa, da a baya kafin ya yi aure ne kuwa da ba zai je ba sai dai ta yi maganar tata a nan.
Sun É—auki minti talatin suna magana kafin ya dawo cikin palon, sallama suka yi wa su Abbi, sannan ya rungumo matarsa a gaban kowa, ba kunya haka suka nufi waje.
Ba su kai ga fita ba muryar Ommu ta katse su da cewa "Umaisha zo mu je É—aki ina da magana dake". Gaba É—aya palon zuba mata idanu suka yi, mamaki ne ya kama su dama tana cikin gidan nan, Hjy Batula kuwa mamaki ne ya kamata dama Hadiza yar kawarta matar yayanta ne ko yaya abin yake ne bata gane ba.
Abbi kuwa ɓata rai ya yi ya ce maza su wuce su tafi dare ya yi, meyasa tun da safe da suka zo bata fito sun yi maganar ba sai yanzu? Haka ba dan ta so ba tana ji tana gani Umaisha suka wuce da mijinta, sai dai kuma ta ci alwashin dole ta nemi number Umaisha ko ta halin yaya ne ma, ta waya ma abin zai fi tafiya mata daidai a cewarta.
Salati Hjy batula ta sanya, dan sai yanzu ta gane wace ce Hajiya Hadiza, tun tana amrya amrya tun da ta haifi Irfan yana jariri rabon da su sake haÉ—uwa sai yanzu, shiyasa ma bata gane ta ba, shekaru wajen 27 ai ba wasa ba, dole zata canza.
Har wajen mota yau ma suka raka su AKil, ya bar Akila a nan ta kwana dan ta nace lallai da Jelly zata kwana yau, ga shi kuma basu isa suce Akila su tafi da Jelly É—in su je gida su kwana ba, saboda Ammie ba zata yarda ba, shiyasa kawai suka barta su kwana da Jelly'n a nan shi ya san me zai gayawa Ammie idan ta tambayi ina Akilar.
Akil dai bai samu damar sallama da Imran ba, domin Imran baya nan duniyar, yana can sama jannati, haka ya ja mota suka wuce shi da matarsa su Abbi kuma suka koma cikin palo.
Imran dai bai dawo da jelly ba sai wuraren karfe 10 na dare, sannan ya dawo da ita cikin gida, lokacin babu kowa a palo, daddyn Jelly ya wuce part nasa shi da Aylarsa, shi ma Irfan ya wuce part nasa bayan ya yi ya yi akan Akila ta gaya mashi menene yake damunta taki ya, haka ya hakura damuwa cike fal ransa ya wuce part nasa ya kwanta kawai, amma dai barci ta gagara zuwa mashi, sai tunanin heartbeat yake yi, yayin da ita kuma take tunanin wani na da ban.
---
Saman table Imran ya haye tare da zuba masu abinci shi da amaryarsa, shima dai kamar Akil, a baki ya rin ƙa bata tana ci tana zuba mashi shagwaɓa, idan da sabo ya saba bata abinci a baki tun bata kai haka ba, kullun idan ya je Kano daddy ya huta, shi ne mai bata abincin, hakan yasa suka saba sosai.
Su kuwa su Rimsha suna É—akin Hanan, da ita Rimsnan da Akila sai Hanan da kuma Hjy Batula dake ta yi masu karin lectures, Aunty kuwa ta shige ciki ita da mijinta abinta, dan yau Hjy Hadiza ta kyale mata abin, da alama akwai abin da take shiryawa ne Shiyasa bata bi ta kan Abbin ba.
A takaice dai Imran sai karfe 11 suka baro gidan Abbi shi da Rimsna bayan ya yi wa Jelly alkawarin gobe zai zo da Rimsha ya haÉ—a su suje wajen lalle da gyaran gashi, dan dama tun kwana biyu da suka wuce Rimsha take damunsa akan tana son ayi mata kunshi.
Abin da ya sanya Imran bai tafi da Jelly ba shi ne ba'a gidansa yake ba, ba zai iya bari a kaita gidansu kuma baya nan ba, saboda yasan irin kiyayyar da Ammie take yi wa familyn Abbansu, wannan dalili ya sa ya ce da daddy a barta a nan zuwa next week, daddy bai musa mashi ba domin shima dai har cikin zuciyarsa baya son yar tasa É—aya tilo a duniya ta yi nisa da shi bayan rabuwarsu na Æ´an watanni, abin akwai wahala amma ya zai yi, ya zama dole wata rana hakan ta faru.
Da haka dai suka yi sallama ya É—auki Rimsha suka koma gida, amma sai da Æ´an sandan kan hanya masu kamen dare suka tare su suna tambayarsu daga ina suka fito, ina Imran zai kai karamar yarinya kamar Rimsha a cikin daren nan, domin babu alamar kamanni a fuskokinsu bare ace Æ´an uwa sa ce.
Ba musu ya gaya masu, barinsu suka yi suka wuce bayan sun gama ƴan dube dubansu a cikin motar dan tabbatar da babu wani abu na cutarwa da Imran ɗin ya ɗauko, sai da suka tabbatar babun ne sannan suka basu iznin wucewa, lokacin da suka dawo gida, Lion na tsaye a balcony bedroom nasa, bai yi barci ba, yana riƙe da cup mai shegen kyau a hannunsa, da alama coffee yake sha, kun san kuma coffee tana ɗaya daga cikin abin da yake sha idan yana cikin farinciki, to wannan ma haka ne da alama daren yau dai yana cikin farinciki, sai dai kamar kullun ba'a ganewa, kuma da alama farinciki tasa tana da alaƙa da samun nasara akan aikin Areef da yake yi.
Kallo É—aya ya yi wa su Imran ya mai da kallonsa kan wayar dake a hannunsa, bathrobe milk color ce a jikinsa, ya É—aure dark black curly hair nan nasa a baya, ya bar wannan guntu na gaban goshin, kamar dai kullun sai tashin fitinannen kamshi perfume É—in nan nasa yake yi, da yake dare ta yi sosai ga kuma blue light a wajen, sai fuskarsa ta kara wani irin haske saboda ba hasken rana mai disashe hasken duk wata haske.
Cikin gida su Imran suka wuto sai kallon saman Rimshan take yi tana kallonsa, duk da ba wani kallon face nasa da kyau take yi ba.
A palon sama suka rabu da Imran, kowa ya wuce bedroom nasa dan yin wanka ayi shirin barci. Haka kuwa akayi kusan a tare suka yi wanka suka shirya cikin kayan barci.
Rimsha ta kwanta bayan ta sanya kayan barci riga da wando launin navy blue, shi kuma Imran launin purple ya sanya, ita Rimsha ta kwanta tare da É—aukar wayarta tana dubawa, uban miss call na A'A ne turun wadda za su kai miss call 66 mamaki ne ya kamata, ita yau kwata kwata ma ta mance da wata waya, shere miss call É—in ta yi ta shiga hotuna, kamar kullun sai da ta kalli gabaÉ—aya hotunan Lion sannan ta ajiye wayar tare da yin addu'ar barci ta kwanta.
Shi kuma Imran sai da ya kira layin daddy suka zuba soyayya da jelly har 1 sannan ya ce su yi barci bayan ya sha shagwaɓa iya son ranta sannan ta kyale shi, bawan Allah rungume da pillow yana murmushi ya yi barci.
Washegari bayan sun karya kamar yadda ya faÉ—a haka ya ce Rimsha ta shirya su je sayayya daga nan ayi mata kunshe sai gyaran gashi ita da kanta baya kitsuwa saboda tsantsi, to ta amsa da shi sannan ta shirya.
Kafin su fita sai da suka fara shiga wajen Areef duk da a tsorace suke da shi, amma Imran ya yi imanin ba wata matsala domin Lion ko zai mutu ba zai taɓa barin ɗan uwansa a cikin matsala ba, yana bala'in kaunarsu fiye da kansa, sune komai nasa, idan ya ga fuskokinsu ma musamman Aseef har wani daɗi yake ji da yake dai ba'a gane mashi ne kawai, kuma a zahirin gaskiya Lion ya fi kaunar Areef akan Aseef, abin da yasa jama'a suke ganin kamar ya fi son Aseef saboda Aseef a mai rauni sosai ya taso, ya tashi da wannan ciwo wadda yasa gaba ɗaya familyn William jacop suka ja shi a jiki sosai, hakan yasa shima Lion ɗin ya fi kusanci sosai da Aseef ɗin akan Areef, amma ko da yanayin yadda suke mu'amala ya ci ace mai hankali yasan cewa ya fi son Areef, saboda Areef na farko ma ya fi su saurin shiga ran mutane, duk da dukkansu akwai bala'in farinjini, amma shi Areef sauƙin kansa da rashin ja da manya ga son mutane yasa ya fi shiga rai, shi kuma Aseef kunsa yadda dai yake a baya idan ba Lion ba, ba wanda ya isa ya bashi umarnin akan abu, ko Areef sai dai ya lallaɓa shi su rabu lafiya, sannan kaifin ƙwaƙwalwa da basira yasa Lion ya fi kaunar Areef dan yana son mutane masu brain sosai, to Areef fa akwai ƙwaƙwalwa kamar dai Lion ɗin, ku da kun gani, mara ƙwaƙwalwa ba zai iya kwatanta abu ɗaya a cikin waƴan da Areef ya yi ba.
Da sallama É—auke a bakinsu suka shiga cikin É—akin, yana zaune a saman bed nasa, yau ya zuro kyawawan fararen kafafunsa kasan bed É—in.
Ya ilahi ya lillahi Rimsha ta ruÉ—e da kanin kafafunsa, musamman yatsunsa ga kunba (farce) kafar tasa sai wani kyalli suke yi farere tas kamar madara, Allah ya yi masu halitta wadda ina da tabbacin ko su aka ce su yi halittar kansu ba za su yi ya wuce hakan ba, saboda sun hallitu kyau iya kyau, kuma Allah da ikonsa dukkansu TRIPLETS É—in halittar kafarsu iri É—aya haka zali hannunsu har yatsun hannayen nasu iri É—aya.
Sai kallon kafafun nasa take yi, ganin haka yasa cikin zolaya ya ce "Kafar Lion ya fi nawa kyau fa". Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi. Zuba mata idanu ya yi sai kallonta yake yi kafin ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya sannan ya ce "Rimsha you are so very very beautiful, gaskiya ina matukar son ki da ɗan uwana, I don't know the reason why nake jin kin kwanta mani a raina, you are very lucky gaskiya, ban taba expecting cewa akwai wata rana da zan bawa mace goyon baya akan abu ba, and also my brother he is very lucky idan har ya same ki, cos na san ba zaki bani kunya ba, and then ba zaki taɓa ɓatawa ɗan uwana zuciyarsa ba, daga ni har su muna da bukatar mu sami soyayya wadda zata goge mana memory mu ta baya, mu iya soyayyar daddynmu kawai muka sani, yana da kyau yanzu mu san wani, am very sure ɗan uwana zai samu irin wannan soyayya a tattare dake, na san zaki yi mamakin faɗa da nake yi akan ɗan uwana ba akan kai na ba ko?" duk da na zayyano kyawawan zaton da nake yi maki, nasan zaku yi mamakin me yasa ni ban ce ina sonki ba sai dai in ce ina sonki da Lion, to kada ki yi mamaki, ki sani ɗan uwana ya yi mana abun da ba zamu iya biyan shi ba, sai dai mu yi mashi addu'a, yana kaunar mu fiye da kansa, kullun cikin yi mana abin da muke bala'in so yake yi, bamu taɓa ce mashi muna son abu ya ce mana a'a ba, idan kuma kika ga ya ce mana a'a to tabbas wannan abun ya bincika ba Alkhari bane a gare mu, idan muna cikin damuwa baya iya barci har sai ya fitar da mu, ɗazun na ce maki soyayyar daddy kawai muka sani ne domin ban yi niyar jan magana dake ba, amma a zahirin gaskiya soyayar da Lion yake yi mana tafi ta daddy, so kin ga kuwa yana da kyau muma duk abin da muka san zai zama na Alkhari a gare shi, to ya kama mu tsaya sosai wajen ganin mun sama mashi shi, sannan bugu da kari shi mutun ne mai wuyar sha'anin, shawo kansa akwai bakar wahala, idan muka samu ya yarda dake shikenan, amma yardar ne wahalar domin zuciyarsa ta fi cutuwa akan abin da mace ta yi mana sama da tamu zuciyar, bai iya gaba ba kamar yadda bai iya so ba, abubuwa biyun nan duk wanda yake yi to fa yana yi ne da gaske babu wasa, idan ya so ka to da gaske ne kuma zaka ji matukar daɗi, haka idan ya kika ba zai taba yi wuya ya sake son ka ba, mawuyacin abune ya waiga ya kalli mace, kai ina da wuya ma hakan ta kasan ce, amma muna sa ran hakan a tattare dake, shi wani irin bahagon mutun ne wadda duk yadda kuke ba zaki taɓa gane ina ya dosa ba, so na san abubu da dama akan shi, shi ne ma dalilin da yasa na tsaya akan ki, domin kina ɗaya daga cikin irin mutanen da yake so, na farko kina da tarayya mai kyau da kuma kyakkyawar zuciya, na biyu hankali, kina da hankali sosai, na uku ilimi, na huɗu son addini da kuma aiki da abin da addini ya koyar da mu, na biyar iya soyayya." Ya yi magana ta karshe na iya soyayya yana ɗaga mata gera ɗaya.
Æoye fuska ta yi a jikin Imran tana murmushi. "Kina mamakin yadda aka yi na san abubuwa akan ki ko?". Cikin sauri ta É—ago da kan nata tare da gyaÉ—a mashi kai alamar e tana mamaki.
"Zan gaya maki amma ba yanzu ba, sai dai kuma ki sani babu abin da ban sani ba a kan ki wadda Prof ya sani, sai dai prof ya ɓoye mani cewa ke ba kanwarsa bace, ni kuma na gano hakan ne ta wata hanya da shima sai nan gaba zan gaya maki, yanzu dai ina zaku je?".
A wannan karon Imran ne ya bashi amsar in da za su je É—in, shiru ya É—an yi kafin ya ce "Okey amma dai ya kamata mrs Saif ta dai'na fita gaskiya, cos tun da gyara za ku je tom ayi gyara sosai zan sanya Lion ya biya kuÉ—in gyaran ta hanyar da bai yi zato ba, kai dai prof idan ka ga kuÉ—i a account naka kada ka kira shi ma bare ka tambaya har ya gane plan na ne, Rimsha kada ki kuskura na ji ko na gani kin kula wani ko kin kalli wani, dan nima ina da bala'i kishi kamar É—an uwana, to amma yau Monday me ya hana ki zuwa school?".
Imran ne ya amsa mashi da shi ya hanata zuwa dan za su je shopping da sauran su, sosai Areef ya ɓata rai in da ya yi wa Imran ɗin faɗa sosai akan kada ya kuskura ya sake wannan gangancin dan za su fita ya hanata zuwa school, ba za su hakura da fitar sai ta dawo ba, ita ma faɗa ya yi mata sosai akan kada ya sake jin ta yi hakan.
To ta amsa da shi sannan suka yi sallama, da kyar Areef ɗin ya miƙe dan ya rakasu, Imran yana ce mashi ya bari ya bari shi kuma ya ce a'a gara ya rinƙa takawa a hankali hankali zai fi mashi.
Haka dai ya rakasu har harabar gidan sannan ya dawo ya zauna a palon kasa dan ya É—an huta, har cikin zuciyarsa ya rasa dalilin da ya sanya yake kaunar Rimsha, har mamaki abin yake ba shi, ta shiga zuciyarsa farat É—aya, amma dai ba wa kansa yake yi wa kaunar tata ba, É—an uwansa yake yi wa, dan shima Lion É—in ya samu farinciki a rayuwarsa, su kuma kullun Lion É—in yana cikin sanya su farinciki, shi ne dai bashi da mai sanya shi sai dai su É—in, to yana da kyau ya samu gaskiya, duk da abune mai matukar wuya, amma Areef yana sa ran tabbas da izinin Allah za su yi nasara, tun da har Aseef ma ya sa baki za su yi nasara, yanzu dai fatan ya samu lafiya kawai yake yi.
Imran kuwa gidan Abbi ya wuce ya É—auki Jelly, Hanan da kuma Akila suka wuce.
Wajen gyaran jiki suka fara zuwa aka yi masu su dulka da sauransu. Yaran nan sun dawo kamar wasu taurari, daga nan sai kunshi da aka zana masu mai shegen kyau, Rimsha kamar wata tauraruwa haka ta zama, ga wannan curly hair nata ya sha gyara sai santin shi su Akila suke yi, da haka suka wuce shopping in da ya saya masu atamfofi da laces dan baya son irin shigar da Rimsha take yi a gidan nan nasu, saboda ya lura sojojin nan sun fara saka mata ido, ga shi kuma wani lokaci suna fita su barta a gidan ita kaɗai, kada wata rana su fita sojojin su cutar da ita, kuma idan suka cutar da ita ko da Lion ya hukunta su ko kashe su ma ya yi sun riga da dai sun cuceta dai, abin da ya wuce ba zai dawo ba, to maganin bari kada a fara, kuma ya duba gaba ɗaya kayanta dukka kanana ne, abayas ɗin ma basu da yawa sosai, wannan dalili yasa ya saya masu atamfofi da laces dan ayi mata ɗinkin hausawa ta rinƙa dressing mai kyau tana rufe jikinta dan gudun matsala.
Daga wajen shopping ɗin suka wuce wajen ɗinki dan su bada kayan ɗinki. Da suka je Imran yaki yarda taila ya gwada su, shi da kansa ya karɓa ya gwadasu sannan ya gayawa tailan size nasu ya rubuta, sosai Rimsha ta ji daɗi da Imran ya yi hakan, domin dama a cikin zuciyarta ba yarda zata yi tailor ya taɓa ta ba.
Tailor ya faÉ—i kuÉ—insa Imran ya yi mashi transfer sannan suka wuce suka nufi gida.
Sai misalin karfe 4 na yamma Imran suka dawo gidan Lion bayan ya mayar da su jelly da niki nikin kayan da suka saya gidan Abbi, ansha yawo ansha shopping da gyara, sun yi kyau fiye da tunanin mai tunani bare ma Rimsha kam ba'a magana, duk wanda ya kalleta sai ya sake waigawa ya kalleta.
Suna shiga cikin palo kamar yadda suka saba É—akin Areef suka fara shiga, baya nan, da mamaki suka fita suka haura sama.
A Palon sama suka isko shi yana zaune saman sofa yana shan coffee. Kusa da shi Imran ya je ya zauna ita kuma Rimsha ta nufi bedroom nata dan ta ajiye niki nikin kayan hannunta bayan ta gaishe shi kenan.
"Wannan murna da faricnikin fa na menene?" Cewar Imran, yana tambayar Areef É—in. Fuska É—auke da murmushi Areef ya ce "Daga yanzu zuwa ko yaushe zaka iya ganin uncle Musharraf da nake gaya maka, baka ga babu motar Lion a waje bane? Ai É—auko mani shi Mark ya je yi a airport".
Murmushi shima Imran É—in ya yi zai yi magana kenan suka ji sallama a bakin kofar palon, a tare suka kai kallonsu wajen, Musharraf ne da Mark dake a bayansa ya yi mashi jagora ne zuwa cikin gida, sun je É—akin Areef É—in baya nan shi ne suka bi yo shi nan sama.
Sai murmushi Areef yake yi tare da yi masu iso, shi kuma Imran a razane ya miƙe tsaye yana faɗin "Yallaɓoi dama kai ne uncle Musharraf ɗin?". Sai lokacin Musharraf ya lura da Imran dake wajen, jinjina mashi kai ya yi alamar e shi ne.
Cike da murna ne ko tashin hankali ne Imran ya kasa gane wa, da karfi ya kwalawa Rimsha kira yana faÉ—in "Rimsha ki zo ga daddynki" ya yi maganar da turanci da yake yanzu ba su cika yin magana da hausa ba saboda su Areef É—in da basaji, yaren, so sai turancin kawai ya bi bakinsu suma.
Wani irin miƙewa Areef ya yi yana mamaki daddyn Rimsha kuma? Allah sarki shine dalilin da ya sanya Areef yake kaunarta kenan.
Ita kuma jin abin da Imran ya ce ne yasa ta fito da gudu yayin da shima Musharraf ɗin ba shi da burin da ya wuce ya ganta ɗin, domin a nasa tunanin dukka family'n sa sun mutu basu raye, shiyasa time da ya dawo Nigeria ya ga gidansa a rufe da kwaɗo sai kawai ya zaɓi da ya bar kasar baki ɗaya tun da ba wanda ya rage mashi a cikin su mummy, kuma dama a tunaninsa yasan da wuya ƴan adawa su kyale mashi family'n sa tun da shima sun yi yunkurin kashe shi Allah ya tseratar da shi, wannan dalili yasa ya bar kasar gabaɗaya da nufin kuma ya barta kenan ba zai kara dawowa ba.
Ganin tabbas da gaske daddyn tane yasa ta kwansa a guje ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, shi dai Areef ya kasa magana, sai ma murmushi da yake yi domin yanzu ya kara samun karfin gwiwa wajen taimakawa Rimsha akan abin sonta, tun da ta kasance ƴar cikin Musharraf to halin kirkinta ma ya wuci hakan domin duk abin da Musharraf ya rinƙa yi wa Aseef suna sane da shi, shi kuma Areef Allah ne kawai ya jarrabe shi da kaunar Musharraf ɗin ba ma wai dai abubuwan da ya yi masu ba.
Rimsha an sha kuka kamar ba gobe, shima Musharraf sai da ya yi kwalla, Areef da Imran ne suka rinƙa rarrashinsu, da kyar suka yi shiru, duk fa wannan abin da suke yi Lion yana bedroom nasa yana jinsu, sai aikin latsa waya yake yi kamar babu shi a gidan.
Bayan sun yi shiru komai ya lafa ne daddy yake tambayarta ina su mummy, nan take gaya mashi ita ma bata sani ba, ita kaɗai ta rage, daga nan ne sama sama ta shiga bashi labarin abubuwan da suka faru har izuwa yau, ya sha kuka kamar ƙaramin yaro. Akan siyasa aka tarwatsa mashi farincikinsa, wannan bala'i dame ta yi kama, kowa duniya kawai ya sa a gaba.
Shi dai Mark yana tsaye ne kawai yana binsu da ido dan ba jin me suke faÉ—e yake yi ba, shi dai kawai ya ga ana magana ana kuka, shima dai Areef kukan kawai yake ganin ake yi, bayan haka baya gane komai tun da ba yaren yake ji ba, amma dai ya fahimci labari Rimsha take bayarwa, sai daga baya bayan komai ya lafane an sha kuka an koshi sannan Imran yake mayarwa da Areef abubuwan da suka faru, sosai Areef ya jinjina kai tare kuma da yi wa kansa alkawarin idan ya samu lafiya dole ya bankaÉ—o gaskiya, dole ya yi bincike akan suwa ye suka yi wa Uncle nasa hakan, a cikin rayuwar Areef idan ka cire TRIPLETS nasa to Musharraf shine mutun na biyu da yake kauna, haka Allah ya jarabce shi, hakan kuma yasa ya yi alkawarin biwa uncle É—in nasa hakkinsa, ba zai bar Nigeria ba sai ya yi wannan aiki koda kuwa ita zata zama aikinsa ta karshe a duniya ko a hukumance.
Shiru suka É—an yi na É—an lokacin, sai shesshekar kuka Rimsha take yi ta lafe a jikin daddynta, zama daddy ya yi ta zauna a saman cinyarsa tare da kwantar da kanta a kirjinsa idanunta sun yi jawur saboda kuka, suma su Imran komawa kowa ya yi ya zauna, Areef dai abin ya yi mashi daÉ—i sosai da Rimsha ya kasance Æ´ar Musharraf.
Katse masu shirun daddy wato Musharraf ya yi da tambayar a ina Rimsha take zama yanzu, wannan karon da turanci suke maganar. Nan Imran ya ba shi labari yadda ake ciki, ai kuwa daddy ya ji babu daÉ—i, cike da jin haushi kuma cikin yaren turanci dan ma Areef ya ji ba sai an fassara mashi ba, ya fara magana "Ba zai yi wu Rimsha ta zauna cikin zaratan maza haka ba, ba zan yarda da hakan ba, dan haka ta kwashe kayanta mu je na mai data gidana na nan Kd, ban yarda ta zauna a nan ba, maza tashi ki kwaso kayan ki mu tafi". Ya kai karshen maganar tasa cikin izza da nuna isa akan ya isa da ita.
Ita kuwa cikin zumuɗin ganin daddynta yasa ta miƙe ta shige ciki dan ta haɗo kayanta, sai faɗa daddy yake yi akan me Imran bai kai ta gidansu ba ko kuma gidan Abbi da zai kawo ta nan cikin maza, ga Areef bashi da lafiya kuma yasan halin turawan nan sarai wasu basu da hankali idan sojojin nan suka yi mata wani abin fa, idan baku manta ba Musharraf suna da kwantaciya a kasa tsakaninsa da Lion na marinsa da Lion ya taɓa yi, hakan yasa Musharraf ɗin baya son Rimshan ta zauna a nan dan sanin bakin halin irin na Lion.
Shi dai Areef sai ƙoƙarin dannan daddyn yake yi domin Lion na gida, shi kuma Lion idan yana waje ba wanda ya isa ya nuna yana da izza ko kuma ya nuna yana da iko da wani matukar yana waje, idan yana wajen to shine sarki, shi ne zai yi iko da kowa, idan ka yi gigin kin hakan to fa ka shirya kukan da mutuwa ta fi maka sauki, hmmm kuma ga shi a cikin gidan Lion ɗin daddy ke nuna izza yana magana son ransa har da nuna isa, ai da wuya daddy ya wanye lafiya da Lion ɗin.
Ai kuwa Rimsha tana fito da trolley ta akan su tafi Lion ya fito daga cikin ɗakin daidai lokacin kuma da daddy ya miƙe akan su tafi.
Tsare Musharraf É—in da waÆ´an nan idanun nasa masu rikitar da É—an adam ya yi, sannan gently in a cool voice ya fara magana "Ke wuce ki koma ciki, kai kuma wuce a mayarda kai in da ka fito, magana kake yi akan tana zaune a cikin maza ko? To kasani daga yau ta zama Æ´ar aikina, even gyaran bedroom ita zata yi, abinci komai dare idan ban ci ba to bazata yi barci ba dole sai ta kawo mani, kuma ta jira na ci sannan ta yi barci idan na bata izini, kamar dai yadda ka ga bodyguards na gida haka zata zama mana Æ´ar aiki, turawa basu da hankali ka ce ba? zan gwada maka kuwa, zaka ga karshen zama a cikin maza".
Cikin sauri Areef ya ce "No Lion please ka kyale shi ya zauna to, idan ya so sai su zauna da yarinyar tasa, you know fa ina kaunarsa....".
Wani kallo ya wurgawa Areef É—in wanda ya sanya shi haÉ—iye maganar tasa ba tare da ya karisa ba. Tsawa ya daka masu akan ya gama magana Musharraf ya wuce a mai da shi Airport ya koma Washington DC, daga yau ya mashi hannu riga da Rimsha tun da har da nuna masu izza a cikin gidansa, to ya rabasu ya ga karshen tsiya, kuma dole ta zauna a cikin maza ta yi masu aiki domin ba shi kaÉ—ai zata yi wa aiki ba, harda su Areef da su Mark sai ya ga karshe rashin kunyar Musharraf, zama cikin maza yanzu ta fara karo wasu sojoji ma zai yi su kara yawa a gidan su kai ko su 12 ta yadda zai tabbata yes a cikin zaratan mazan take zaune ita kaÉ—ai mace bakinciki ya kashe Musharraf É—in su gani.
Ba yadda Areef bai yi ƙoƙarin fahimtar da shi ba akan ya yi hakuri ya kyaye Musharraf, amma ina baya magana biyu, sai ma tsawa da ya kara daga masu wadda ta sanya Rimsha kwasowa a guje tare da sakin trolley ɗin nata ta rungume daddyn tana kuka kamar ranta zai fita, duk yadda take son zama kusa da Lion to bai kai rabin son kasancewa da iyayenta, tana son kasancewa da daddy ta da yanzu kewarsa ya yi mata katutu.
Shi dai Areef ya ji daɗi da Lion ya ce Rimsha ta zama ƴar aikinsa daga yau, amma bai ji daɗin raba uba da ƴa da ya yi ba, bai kyauta ba suna tsaka da kewar juna na tsawon watanni, yau da suka haɗu kuma ya zo ya raba su, abin ya ɓatawa Areef rai.
Shi kuma Imran cikin sanyin murya ya ce "Saif it's my uncle, pls stop telling him that, please and please, evan for the sake of me" ya yi maganar tamkar zai yi kuka, domin abin ya taɓa mashi zuciya sosai, ganin daddyn Rimsha yake yi tamkar Abbansa, kuma ya ji zafin rabasu da Lion ɗin ya yi shi da Rimshan.
Shiru Lion ya yi har kamar ba zai sake magana ba. Sun kwashe tsawon good five minutes a tsaye a wajen, sai kuka Rimsha ta ke yi, shi kuma daddy yana kankame da ita a kirjinsa.
Har sun fidda ran zai sake yin magana, sai kuma suka ji sexy voice nasa can kasa-kasa ya ce "I dnt care even if it's your father not your uncle, am done talking". Tashin hankali, zaro ido waje Imran ya yi ya rasa bakin magana, shi kan shi daddy raba jikinsa da tata ya yi yana kallon fuskar ta, taci kuka har ta godewa Allah, duk idanun nata sun kunbura luhu-lugu, har wani ja kasar idanuwan nata suka yi, saboda kukan da ta sha, shi kuma Lion juyawa ya yi ya koma bedroom nasa.
Areef kuwa girgiza kai kawai yake yi domin dama yasan in dai Lion na waje ka gwada izza a wajen to ba makawa sai ya saka ka kuka, a tsarinsa koma a ina koma waye shi ne sarki, ba'a isa a nuna isa a kusa da shi ba Musharraf ya yi kuskure.
Mark kuwa cewa daddy ya yi ya wuce su koma airport kada Lion ya sake fitowa.
Juyawa daddy ya yi a yaune yake dana sanin sanin su Lion da ya yi a rayuwarsa, cikin kunan rai tare da raunin zuciya ya ce "Imran ga amanar Rimsha, sannan a yau saboda Rimsha zan gaya maka cewa ni ne Hosain, na san kasan labarin kanin Abbanka Hosain, to ni ne, na gaya maka hakan ne kuma domin ka kula da Rimsha kanwar ka ce, kada ka bari komai ya same ta, sannan kuma kada ka gayawa su Yaya babba cewa Rimsha Æ´ata ce, kada ma ka gaya masu ka ganni, akwai dalili yin haka, sai Allah ya kaddara saduwarmu ko idan kun zo in da nake zan gaya maka komai, yanzu dai gata nan ka kula mani da ita". Ya kai karshen maganar tare da juyawa wajen Areef, shima ya bashi amarnar Rimsha sannan ya wuce zuciyarsa cike da tunanin ya Rimsha zata rayu a cikin shegun kafuran sojojin nan, ga shi Lion ya ce Za'a karo wasu sojojin, ya san halinsu sarai basu da imani, da tsawa kawai za su sanya Rimsha mutuwa ba tare da ta shirya ba, ga shi basu É—auki zina kamar wata laifi ba ce, amma kuma kasan cewar tana hannun Areef da Imran yasa ya É—an sami kwanciyar hankali tare da kwarin gwiwa akan da izinin Allah babu abin da zai same ta, sai dai kuma yana jin bugun zuciya idan ya tuna cewa Æ´ar aiki Rimsha zata zama, yasan babu wanda ya isa ya canzata a wannan Æ´ar aiki da Lion ya kira ta da shi, sai shi Lion É—in da kansa, kuma yasan aiki a karkashin waÆ´an nan masu taurin zuciya ba karamin abu bane, Allah nema kaÉ—ai yasan irin aikin da zata yi wa su Mark kuma, Allah dai ya sa ba barinta da wankin kayan aikinsu masu hangen bala'in tauri da takalmarsu za'ayi ba. Sai tunani kala kala Musharraf yake yi har suka fita.
Ita ma Rimsha kuka take yi kamar ranta zai fita, rungumeta Areef ya yi yana rarrashinta, tana ji tana gani daddy ya wuce ya fita, da sauri Imran ya bi bayansa dan ya raka shi waje, sai dai fa duk jikin Imran ya mutu jin cewa Daddyn Rimsha shine Hosain kanin mahaifinsu, lokaci guda Imran ya ji cewa lallai yana son sanin ainahin tarinhin abin da ya raba kan wannan family har haka, me ya rabasu kenan, wannan gaba na tun ba'a san za su zo duniya ba, sun rarrabu kashi kashi ta yadda yanzu Æ´aÆ´ansu sun ta so amma basu san cewa iyayensu bane, kenan bayan daddy ma akwai wani ne ko kuma yaya, shin su nawa ne ma a wajen iyayen nasu, ina Hassan É—in Hosain É—in yake?. Wannan shine tambayoyi da Imran yake yi wa kansa da kansa, wadda kuma ba wanda zai iya ba shi wannan amsa sai Abbansa, domin shi ne yaya babba a cikin su Abbin gaba É—aya, yasan komai kenan.
Allah sarki Areef sai fama da rartashin ta yake yi, yau Rimsha ta ci kuka kamar ba zata rayu ba, har wani sarkewa numfashinta yake yi, gata ga daddynta amma an sake rabasu, ita ba ƴar aikin Lion da zata zama bane ma ya dameta, duk da ta san cewa yi wa Lion aiki babbar bala'i ce domin sai mai dakiyar zuciya irin sojojin nasa za su iya, amma dai duk da haka abin bai taɓa ta sosai ba kamar yadda rabata da daddy ya taɓata. Allah sarki sai kokarin Areef yake yi da ita akan kada ta suma.
Daga karshe ma zazzaɓi ne mai zafi ya rufeta kwance a jikin Areef ɗin, kafin Imran ya dawo jikinta ya yi zafi jau kamar wuta, da yake tana kwance a jikin Areef ɗin sai bai ji zafin da jikin nata ya yi ba, har sai da Imran ya dawo yana ƙoƙarin ɗagata daga jikin Areef ɗin dan ciwon dake jikinsa kada ta fama mashi, a nan ne ya ji jikin nata ya yi zafi kamar wuta.
"Subhanallah Rimsha lafiya, zazzaɓi ne fa a jikinki". Shine abin da Imran ya faɗa bayan ya ɗago ta. Yunkurawa Areef ya yi wadda gaba ɗaya jikinsa ta yi la'asar saboda raba uba da ƴa da Lion ya yi, tsawon watanni ba su tare wannan wace iriyar bakar zuciya ce a kirjin Lion? Shine tambayar da Areef ya yi wa kansa, mutun yana ji yana gani ya raba uba da ƴa suna kuka dukkansu amma ko kaɗan Lion bai ji wani alamar tausayi ba bare ya tausaya masu, tamkar ma ba shi ya yi hakan ba.
Hannu Areef ya kai ya taɓa wutarta, zafi jau kamar wuta, ko motsin kirki ta kasa yi, ta zama wata sukuku sai yadda suka yi da ita, duk yadda Imran ya juyata haka take juyawa tana daga kwance a jikinsa. Baiwar Allah.........
💖💖TRIPLETS💖💖
E91-92💖
Hannu Areef ya kai ya taɓa wutarta, zafi jau kamar wuta, ko motsin kirki ta kasa yi, ta zama wata sukuku sai yadda suka yi da ita, duk yadda Imran ya juyata haka take juyawa tana daga kwance a jikinsa. Baiwar Allah.
Ɗagowa Areef ya yi ya kalli Imran ɗin kafin ya ce "Take her to hospital, ni ba zan iya dubata yanzu ba, because gaba ɗaya am very weak". Jinjina mashi kai Imran ya yi sannan ya saɓe ta a kafaɗarsa ya nufi waje da ita, shi kuma Areef ya koma ya zauna a saman sofa yana sauke numfashi a hankali.
Abin mamaki kuma abin al'ajabi shi ne da Imran ya zo fita gidan gateman ya hana shi fita, mamaki ne sosai ya kama shi tare da tambayar gateman ɗin akan me zai hana shi fita, cikin girmamawa ya ce "Am sorry sir oga ya ce kada na kara barin wani ya shiga ko kuma ya fita gidan nan ba tare da izinin sa ba, ko da kuwa kune". Imran ya gane matsalar wato yau ran Lion ya ɓaci, ba rashin lafiya ba ko mutuwa Rimsha zata yi sai dai ta mutu, dan mugunta da ganganma ya hana a fita da ita saboda yau babanta ya yi maga da izza kuma yana wajen, shine zai sauƙe akan ƴarsa kenan, Babbar magana.
Shiru Imran ya É—an tsaya kafin ya juya kan motar ya dawo cikin gidan, haka ya sake É—aukarta suka koma ciki domin yasan tun da Lion ya ce haka to fa ko Areef a wannan karon sai dai ya ce da Rimsha ta yi hakuri, amma babu wanda ya isa ya canza wannan magana daga ba za su fita daga gidan ba, lallai Lion ya shirya mugunta kenan.
A palon sama ya isko Areef a nan kuma ya gaya mashi abin da Lion ya ce, Areef bai yi mamaki ba domin kuwa ya san tun da suka yi haka da Musharraf tofa sai dai addu'a dan tabbas Musharraf ya ɗan ɓata mashi rai gaskiya ita kuma Rimsha sai dai suce Allah ya kwaceta daga hannunsa kawai, amma dai zata ci bakar wahala ba ɗan kaɗan ba.
Haka Areef ya daure ya ce da Imran ya ɗauko mashi A box a ɗaki bari ya duba ta, dama kunsan jami'ai irin haka ba su rasa iya wani sashe na aiki a ɓangaren lafiya domin kula da kansu idan bullet ya taɓa su ko makamancin hakan, to shima Areef hakan ne ya iya aikin likita duk da ba sosai bane.
Ɗakin Rimshan suka wuce, a nan Areef ya dubata tare da yi mata alluran zazzaɓi, amma fa sun sha dirama kafin ayi wannan aluran, sai da Imran yasa karfi ya danneta kafin nan Areef ya samu ya danna alluran ya yi mata, cikin alluran da ya yi matan kuma har da na barci domin ta ɗan samu ta huta wata kila idan ta tashi ƙwaƙwalwarta ta ɗan yi fresh.
A haka suka barota a cikin É—akin tana barci suka koma palo suka zauna, sosai suka nutsa a duniyar hira a tsakaninsu, duk wannan abin da suke yi Lion yana jinsu domin ai a palon saman suke.
A ɓangaren gidan Abbi kuwa, bayan sun koma gida da suka yi sallar mangariba suka ci abinci ne suka wuce ɗakinsu while ita kuma Akila Akil ya zo ya ɗauketa ya mai da ita gida, yanzu ya rage daga Jelly sai Hanan, su biyu ne kawai a cikin ɗakin.
Yau wani irin wanka na musamman aunty ta ci, sai tariyo kalaman Akila a cikin ƙwaƙwalwarta take yi, wata magana da Akila ta sake gayawa Jelly safiyar yau ne ya tsaya mata a ranta, maganar kuma ba wata bace fa ce cewa da ta yi, ba sai kin tambayi mijinki wani irin dressing yake so ki rinƙa yi mashi ba, a cikin kayan da yake saya maki a nan zaki gane, idan ke amarya ce ki duba cikin kayan lefenki ki gani, abin da ya fi so shi zai saya maki dayawa, idan kuma kun jima da shi to zaki ga idan kun je sayan kaya zai yi ta cewa ki ɗauki kaza ki ɗauki kaza, to wani abin ba sai kin tambaye shi ba, da kansa zaki ga ya fi damuwa da saya maki irin shi dan yana so. Wannan magana ta tsayawa aunty a rai domin kuwa Abbi ya zu ba mata riga da wando masu shegen kyau sosai a cikin lefenta, a cikima ta ɗauki ɗaya daren jiya ta bawa Jelly, kenan Abbi yana son a rinƙa yi mashi dressing na riga da wando? Sannan ga uban wasu shegun kayan barci daya zuba mata wadda a kalla za su iya kai kala 20 saboda yawa, kenan shima Abbi yana so a rinƙa sanya mashi? Tabbas Akila ta faɗi gaskiya ko kala ne miji yake so zaki ga idan zaku sayi abu zai rinƙa ce maki ki ɗauki kalar can tafi kyau kuma zata yi maki kyau, bawai dan zata yi maki kyau ɗin bane, aa shi dai ya fi son ganinki da wannan kalar ne, amma sai kaga wasu mata dan ya ce ga kalar da zata yi maki kyau sai ta ce a'a ba zai yi mata kyau ba, aa ya yi haske sosai ko kuma ya yi duhu ko dai ya yi kalar fatar ta, complain dai kala kala idan bata son kalar abin da ya zaɓa mata ɗin, dama ba dan ya yi maki ke kyau ba yasa ya ce ki ɗauka, shi ne dai kalar da ya fi so, to dan haka sai mu lura.
Wasu shegun kayan barci Aunty ta ɗauko wadda kusan da su da babu duk ɗaya ne, haka ta sanya a jikinta kuma ta bi shawarar Akila bata sanya bra ba, ta sake su abinta, sai tashi wani fitinannen kamshi take yi, lokacin da ta shirya Abbi yana ɗakinsa baya nan, hakan yasa ta ɗauki wayarta tare da sanya hijabi ta fito zuwa ɗakin nasa, a lokacin ita kuma Ommu tana can tana saƙa ta yadda zata karɓi 10 million a hannun Akil ta hanyar Umaisha.
Bakinta É—auke da sallama ta shiga cikin É—akin Abbin, baya É—akin yana toilet yana wanka, cire hijabin jikinta ta yi ta ajiye tare da nufar gaban mirror tana kara feshe jikinta da wasu kalar perfume É—in nasa.
A haka ya fito ya sameta, bayan ta ya fara kallo, da farko ma ya zaci Ommu ce domin sirantar ko ace yanayin jikinsu kusan É—aya, sai da ya ga tsawon da kuma tudun bayan ne ya fahimci ba Ommu bace, gabaÉ—aya kunya ta kama Aunty, bata saba ba, ta kasa juyowa su yi ido biyu da Abbin, har wani yarrrr jikinta yake yi saboda kunya.
Shi kuma Abbi ya tsare ta da ido sosai yana kare mata kallo daga sama har kasa, ta yi kyau iya kyau kuma ta tafi da imaninsa fiye da Ommu, domin dama babu haÉ—i ta fi Ommu komai, kawai rashin É—aukar wankar shegun dressing da bata yi ne yasa ake mata kallon kamar ba komai É—in.
Ta kasa juyowa shi kuma Abbi ya kasa cire idanunsa daga kanta, da dai taga ba zai daina kallonta ba kuma yaki karisowa cikin É—akin yana tsaye a bakin kofar toilet, sai ta hakura ta juyo a hankali tare da fara kallon kasa ta ki haÉ—a ido da shi.
Ya ilahi ya lalliahi ai kuwa ashe bai ga komai ta baya ba sai da ta juyo ta gaba, cikin sauri ya kariso wajen da take tare da rungumarta a jikinsa, wani nauyayyar ajiyar zuciya suka sauƙe a tare, tunani ta fara yi kenan gaskiyar Akila? Lallai kam to ita ina zata iya irin waƴan nan dressing da Ommu ke yi, ai sai yara ita kunya ba zai barta ba.
Tana can tana tunani shi kuwa Abbi yana sabgar gabansa dama daga shi sai towel.... na haÉ—a kayana zuwa wajen daddyn Jelly dan na basu waje.
Sai lallaɓa Aylarsa yake yi suna kwance saman bed nasa tana kwance a saman kirjinsa, amma fa sai da aka yi wa Jelly dabara na cewa Ayla zata kwana da Ommu ne sannan ta yarda da rashin Ayla a ɗakinsu, ba dan haka ba, ba zata taɓa yarda Ayla ta kwana da daddynta ba, duk da an ce mata kanwar mummynta ne, amma ta yi mugun raina Ayla ɗin sosai, kuma da farko ma taki yarda ta kwana da Hanan, ta kafe sai da daddy zata kwana, sai da Abbi ya yi mata dabara tare da lallaɓata sannan ta yarda su kwana da Hanan ɗin.
"Babyn daddy daddynki yana cikin wani hali, zaki iya taimaka Mashi?" Ya tambaya yana shafa bayanta. Tana daga lafe a kirjinsa ta ce "Daddy sosaima, zan taimaka maka".
Ajiyar zuciya ya sauke har ga Allah ba zai iya jure sati guda da Dr ta ce ba, yau kwana uku ma ji yake yi kamar zai mutu saboda azababben sha'awarta dake damunsa, to ina ga an cika sati, ai sai dai a kwashe shi sai asibiti kawai.
"Baby kanki nake so ki bani kin ji ko?" Ya yi maganar can kasan maƙoshinsa. Da yake bata san me hakan yake nufi ba sai ta ce "To daddy na baka ai".
Kara matseta sosai ya yi a jikinsa, Baiwar Allah bata gama samun sauƙi ba amma yana ƙoƙarin sake tsunduma ta cikin wani yanayin kuma.
Juyawa da ita ya yi izuwa saman bed ɗin ya yi mata rumfa da kirjinsa, nan take ya fara murzanta son ranshi, a wannan karonma ta ci bakar wahala a hannunsa, ta yi kuka kamar mene ne, amma dai Allah ya takaita ba suma, bata suma ba, sai dai fa ta wahala zallar madarar wahala, sai nishi take yi tana kuka kasa kasa da kyar da kyar, kuka kuma mai taɓa zuciya, Daddynta yana neman kasheta shi da kansa.
Shi kuwa sai aikin rarrashi yake yi, duk ya birkice mata kamar ba shi ba, amma kuma ya kwashi daÉ—i iya son ransa, yau nema ya san ya kwanta da ita, ranar farko bakar wahala shima yasa saboda......
Da kansa ya yi mata wanka kamar dai yadda ya saba yi mata, magungunarta ya ɗebo ya bata ta sha sannan suka kwanta bayan shima ya yi wankar kenan, rungumota sosai ya yi a jikinsa kamar na ce zan kwace mashi ita, da haka barci ya yi awon gana da su sai sauke ajiyar zuciya irin na wadda yaci kuka ta ƙoshi take yi.
A ɓangaren Akila kuwa, yau ma dai masoyin ɓoye ya hanata yin waya da Irfan, idan Irfan ya kira sai ya ji wayar a kashe yayin da shi kuma masoyin ɓoyen sai misalin karfe 10 ya kirata a waya.
Gaba É—aya ta mance da abin da ya faru jiya a gidan Abbi, ta mance ya ce mata shi ba mutun bane, hakan yasa ta É—auki kiran tasa cikin zumuÉ—i.
Sallama ta yi mashi kamar ko da yaushe, cikin fara'a ya amsa mata sallamar tata tare da yi mata barka da dare, bakinta ya ki rufuwa saboda murmushi ta amsa mashi da lafiya Lou fatan shima haka ne?.
Ya É—an yi shiru kafin ya amsa mata da lafiya Lou Alhamdulila ina su Akil da kuma ango Imran, ta sha mamakin jin wannan tambayar tasa, amma sai bata yi gigin tambayarsa a ina ya san cewa Imran ya yi aure ba, kawai sai ta ce mashi suna nan lafiya lou.
"Heartbeat ɗin heartbeat ɗinta me ya same ki? Yau na ji gabaɗaya kin sauya". Cikin shagwaɓa ta ce "Kai ne mana". Da sauri ya ce "Subhanallah ni kuma my heartbeat?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e shi ɗin dai.
"Heartbeat me na yi maki kuma?" Nisawa ta yi kafin ta ce "Me yasa kaki ka bayyana mani kanka? Me yasa kake bawa zuciyarta wahala? Haba mana bugun zuciyata why kake azabtar da ni kuma kake ikirarin cewa sona kake yi?".
ÆŠan dafe kansa ya yi yana faÉ—in "Nayi kuskure matata amma ki yi mani afuwa kin ji ko? Ba zan sake ba, kuma zan tura maki hotona yanzu, amma me yasa kike da tsoro haka ne? Ni mutun ne ba aljani ba kawai jiya na yi maki zolaya ne na tsakanin masoya, amma tuba nake yi Gimbiyata".
Wani irin daddaÉ—ar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "To shikenan Heartbeat É—i na, komai ya wuce amma dai ina matukar son na ganka, ka turo mani pic naka please".
"Zan turo maki amma ki yi mani murmushi tukun nan ko my pleasure?". Wani kayatatcen murmushi ne ya subce mata tare da sanya hannunta ta rufe face nata tana faÉ—in "Uhm Uhm yanzu dai sai da ka saka ni Murmushi ko?".
Wani irin shagwaɓe murya ya yi cikin salo mai jan hankali tare da kwarewa a iya shagwaɓa ya ce "Uhm uhm ba dole na sanya bugun zuciyata murmushi ba, kin san yadda nake ji a cikin zuciyarta idan kika yi murmushi kuwa?" Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a tamkar tana gaban shi.
"My heartbeat idan ki ka yi murmushi ji nake yi duniya ta tsaya mani cak, ji nake yi tamkar bana a duniyar nan, wani irin baƙon yanayi ne ke ratsa zuciyarta har izuwa gabaɗaya sassan da jini ke gudana a jikin nawa, ina tsintar kaina a cikin wani irin farinci wadda ba zai misaltu a gare ni ba, ina jin kamar an yi mani albishir ne da gidan aljanna, please my bugun zuciya keep smile kin ji ko matar Heartbeat ɗin ta".
Wani irin daÉ—i ta ji a cikin zuciyarta, har wani irin sanyi kamar an zuba mata kankara take ji yana ratsata, jinta take yi a sabuwar duniya, kara narke mashi ta yi suka cigaba da zubawa juna kalaman soyayya da Kauna, gabaÉ—aya ya sanya ta ta mance da zancen hoto, dama kuma da gangan ya yi hakan domin baya son tura mata hoton nasa a yanzu, yana tura mata zata gane shi, shi kuma ba haka yake so ba, yana so ne sai ta kamu da son shi wadda ba zata iya rabuwa da shi ba, sannan sai ya kawo mata kansa har gida su ga juna, kuma yana so ne ta so shi tsakani da Allah ba tare da ta san waye shi ba.
Ya kware wajen iya shagwaɓa da soyayya, hakan yasa yau har kukan daɗi Akila ta yi mashi, domin ya fita iya soyayya da komai nesa ba kusa ba, hawaye babbiyu yau ta yi mashi kuka, cikin sigar shagwaɓa kuma ya rarrashi kayarsa, yana bala'i kaunarta fiye da tunanin mai tunani, sai dai kuma akwai shi da zuciya da kishi tare da neman magana, da gangan wani lokaci yake tsorata domin yana jin daɗin yin hakan, yana jin daɗin yaga yana tsoratata tana zuba mashi kukan shagwaɓa, hakan ba karamin daɗi yake yi mashi ba.
Sai misalin karfe 1 na dare sannan ya ce ta kwanta shiru kada ta yi magana, duk abin da zai faÉ—a bai ce ta bashi amsa ba, ta dai yi shiru har barci ya É—auketa, amma ta bar mashi wayarta a kunnnenta yana makale domin ta saurari abin da zai na gaya mata É—in har ta yi barci, okey ta amsa mashi da shi sannan ta yi abin da ya faÉ—a É—in dukka tare da kara jawo bargo ta shige.
Wasu shegun zafafan kalamai ya fara faɗa mata a kunnenta, yana yi yana haɗa mata da shagwaɓa, sai murmushi take yi har barci ya ɗauketa fuska ɗauke da murmushi, shiru ya yi yana sauraran yadda numfashinta ke sauƙa a hankali hankali har karfe biyu na dare, sannan ne ya kace kiran cike da begenta, bai gaji da jin muryarta ba, haka zalika wannan shagwaɓar tata baya isarsa, baya gajiya kwata kwata, ita ma ta iya soyayya sai dai ko rabin shi bata kai ba, tana bashi kulawa iya iyawarta.
Cike da kewarta shima ya kwanta tare da jawo lallausan bargo ya shige ciki, ya rufe har kansa.
A ɓangaren su Jelly da yaya Imran ma dai an sha waya har karfe 1 sannan shima ya ce ta kwanta ta yi barci dan saboda tashin asuba, yasan halinta sarai bata tashin asuba ta daɗi idan ana tashinta, amma fa shi a nashi ɓangaren da rungumar pillow ta barshi ya kwana, ta zuba mashi shagwaɓa da soyayya son ranta, ta bar bawan Allah da matse pillow domin ta jefa shi cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa.
A ɓangaren Rimsha kuwa, ba ita ta farka ba sai karfe 8 na dare, baiwar Allah ta tashi lafiya Lou sai dai ciwo da jininta yake ɗan yi mata. A hankali ta sauƙo kasa ta nufi toilet.
Wanka ta fara yi kafin ta É—auro alwala ta zo ta gabatar da sallar mangariba da kuma isha, sannan ta shirya cikin wando da kuma riga kamar yadda ta sa ba, yau garin akwai iska da hadari da alama ruwan sama za'ayi, hakan yasa ta É—auki jacket data É—auko a É—akin Imran ta sanya a jikinta ta fito palo dan ta yi magana da yaya Imran.
Da sallama a bakinta ta shiga É—akin nasa, baya nan hakan yasa ta wuce kasa dan tasan yanan tare da Areef a É—akinsa kenan.
Sallama ta yi masu a bakin kofar, har suna haÉ—a baki wajen amsa mata sallamar tata tare da bata izinin shigowa, cikin natsuwa ta shigo cikin É—akin.
Areef na zaune saman gado da gabaÉ—aya jikinsa, shi kuma Imsan yana zaune ne a bakin gadon, Areef ya jingina kansa da jikin headboard na gadon yana fuskartar Imran É—in, shigowarta tasa gabaÉ—aya suka zuba mata idanu cike da tausayinta fal ransu.
Gaishesu ta zo ta yi kafin Areef ya yi mata alama akan ta zo kusa da shi ta zauna, shima dai Areef kallon Æ´ar baby yake yi wa Rimsha kamar Imran É—in, kuma gaskiya ce yarinya ce 14 years da Æ´an hayaniya ne fa ke gare ta.
Ba musu ta koma gefensa ta zauna domin tun da ta ga daddynta ya yarda da su, sai ita ma ta kara yarda da su dama can already ta yarda da su, karawa kawai ta yi a yanzu.
ÆŠan kwantar mata da kanta ya yi a jikinsa Imran yana hana shi kada ya fama ciwonsa amma ina bai damu ba, shi dai burinsa kada ta shiga damuwa tunda Imran É—in ya gaya mashi halin da take ciki na rashin lafiya na abinda Dr ya ce, shiyasa shima baya son barinta ta shiga damuwa.
Wayarsa ya ɗauko ya fara kiran layin da Aseef ya sai wa Musharraf jiya kafin ya baro Usa, bugu ɗaya daddyn ya ɗauka domin shima ya ƙagu ya yi magana da Rimshan kuma ya kira layin Areef ɗin bata shiga.
Juya kiran Areef ya yi ta koma video call, bawan Allah yana cikin jirgi ba su sauƙa ba, murmushi Areef ya sakar mashi kafin ya ce "Uncle please promise me akan ba zaka shiga damuwa ba? Na maka alkawari sai in da karfi na ya kare, amma tabbas zan bawa sister kulawa sosai".
Jinjina kai daddy ya yi yana faɗin "James in dai Rimsha a hannunku take kai da Imran, to ba zan taɓa shiga damuwa ba". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Uncle just call me Areef not James, ni musulmi ne, amma kada ka bari kowa ya sani a gida, a baya ma abin da ya sa ban gaya maka ba, ina tunanin zaka iya gaya wa wani ne, ciki kuma har da Aseef a lokacin, zan gaya maka dalilin da yasa bana so a san ni musulmi ne, amma ba yanzu ba, yanzu ka yi magana da gimbiyar TRIPLETS tukunnan".
Daddy bai kawo komai a ransa na sunan da Areef ya kira Rimsha da shi na gimbiya TRIPLETS ba, ya É—auka kawai dan hankalinsa ya kwanta ne yasa ya ce hakan, dan haka sai bai wani damu ba, shi kuma Areef ya juya wayar zuwa kan fuskar Rimsha da ta kwantar da kanta a saman kafaÉ—arsa ta gefen kirjinsa ya yi.
Ganin daddynta yasa ta miƙe cikin sauri tana faɗin "Daddy daddy please ka dawo ka ji? Daddy idan baka dawo ba zan iya mutu wa, babu JEHAN babu MUMMY babu GWAGGO, ni kaɗai na saura daddy, dan Allah ka dawo mu nemo ina suke" tana magana tana hawaye.
Katse kiran Areef ya yi ba tare da ya bar daddy ya yi magana ba, rai a ɗan ɓace ya fara magana "Rimsha me yake damun ki ne? Me yasa kike son tayarwa da uncle hankali ne? Ki sani uncle yana bukatar kwanciyar hankali fiye da ke, ko so kike ki saka mana shi a cikin damuwa ne? Ki ja wani ciwon ya kama mana shi ko? To zamu ɓata dake in dai zaki rinƙa yi wa Uncle kuka, kuma ba zan sake haɗa ku a waya ba".
Hakuri ta fara bashi akan ba zata kara ba, ta tuba. "Okey ki yi mani alkawarin ba zaki sake cewa uncle wani abin da zai tayar mashi da hankali ba? Ki yi mani alkawarin farinciki zaki rinƙa sanya shi kullum?". Da sauri ta fara gyaɗa mashi kai akan ta yi alkawarin farinciki zata rinƙa sanya daddyn.
"Good to jeki ki kawo mani wayarki, sai ki dawo ku yi magana da uncle ɗin kin ji?". Okey ta amsa mashi da shi sannan ta miƙe da sauri ta fice daga ɗakin, shi dai Imran ya kasa magana domin kuwa ba ƙaramin daɗin yadda Areef yake kaunar Rimsha ya ji ba, shima a yanzu kauna na daban yake yi mata bayan jin cewa ƴar uwarsa ce, kun san Imran dama yana bala'in kaunar ƴan uwansa sosai da sosai.
Da sallama ta dawo cikin ɗakin lokacin kuma Areef ya sake kiran daddy dan su cigaba da magana da ita. A in da ta tashi a nan ta koma ta zauna, cikin girmamawa ta miƙa mashi wayar tata shi ma ya miƙo mata nasa dan su cigaba da magana da daddy, karɓa ta yi tare da kawo wa saitin fuskarta, ai kuwa zancen Areef gaskiya ce, ta ɗagawa daddy hankali har kwallah sai da ya yi, ga idanunsa nan akwai alamar kwallah a ciki.
Hakuri ta fara bawa daddyn tare da ƙoƙarin nuna mashi ta hakura zata zauna da ƴan uwanta, kamar dai yadda suka yi da Areef haka ta yi ƙoƙarin nunawa daddy cewa tana farinciki.
Shi kuma Areef ba tare da ta gaya mashi password na wayar ba, da kansa ya buÉ—e wayar ya shiga cikin domin ya sanya mata number daddynta, ganin uban miss call na number da aka rubuta Yaya Ahmad ne yasa ya É—ago ya kalli Imran tare da tambayarsa waye kuma Yaya Ahmad a cikin familynsu.
Sai da gaban Imran ya faÉ—i domin yasan halin Areef sosai da sosai, zai iya sanyawa a É—aure A'A akan Rimsha, komai kuÉ—in dangin su A'A kuwa, duk da cewa kusan suke da mulkin NIGERIA a yanzu, tsab Areef zai iya É—aure gabaÉ—aya familynsu, abin da su Areef É—in sune ke juya kasar Nigeria koma ace Africa baki É—aya, yah gwamnatin kasar su ke mulkar Nigeria da sunan an bamu Æ´anci, to waye gwamnatin kuma? Ai kunga sune gwamnatin tun da kakansu ne akan mulki, to kunga a gwamnatan ce za su É—aure A'A É—aurin da ba zai iya fitowa ba ma kuwa.
Cikin sigar da Areef zai fahimtar Imran ya gaya mashi waye A'A me kuma ya haÉ—a shi da Rimsha sannan da abin da yake so a wajen ta, da yake Areef akwai kwakwalwa sosai sai bai tuhumi Rimsha akan me yasa take kula shi ba, ya yi amfani da abin da ya gani na ganin yawan miss call nasa a wayarta, which means kenan Rimsha bata É—aukar kiransa, idan bata É—aukar kiransa kuma ai bata damu da shi ba, idan kuma bata damu da shi ba babu so kenan.
Number A'A É—in ya kira tare da sanya wayar a hand-free, bugu É—aya Ahmad ya É—auka murya can kasa kasa ya ce "Rimsha sai yau kika tuna da ni ko? Wai me na yi maki ne kike neman kashe Ni? Kin manta alkawari da ki ka yi mani ko?" Cikin yaren Hausa ya yi maganar so Areef bai fahimci me yake faÉ—a ba, dan haka sai ya fara magana cikin yaren English. "Hyyy man that's is not Rimsha, kanin mijijta yake magana ko kuma in ce maka yayanta zaka fi fahimta, bana son ka sake kiran wannan number a rayuwarka, ka mance da wace ce Rimsha a rayuwarka, zai fi zama maka alkhari if not zaka yi regretting zuwanka duniya".
Ita kuwa Rimsha ko a jikinta, a lokacin kuma ta gama magana da daddynta sai wani murmushi take yi, dama kunsan ba son A'A take yi ba, shiyasa bata wani damu ba dan Areef ya karta mashi warning,
Shiru A'A ya É—an yi kafin ya ce "To ai Rimsha bata da wani yaya idan ba Imran ba, cos ba zan daina kiranta ba domin ita nake burin na aura". Yana kai karshen maganar diff ya katse kiran. Tab an ce rashin sani ya fi dare duhu, A'A ya yi abu a duhu kuwa, bai san da waye yake magana ba.
A'A yana katse kiran kuma sai ga shi ya kira number Imran, ba musu Imran ya ɗauki kiran, cikin yaren Hausa suka fara magana a in da Imran ɗin yake gaya mashi waye ne ya kira shi da number Rismha yanzun nan, wani irin mahaukacin razana A'A ya yi, jikinsa har kerma yake yi, lokaci guda ya dibirbirce ya fita hayyacinsa, sai faman haɗa words yake yi wajen magana, da kyar ya iya tambayar ya akayi wayar Rismha ta shiga hannun ɗaya daga cikin familyn William jacop, a nan ne Imran ya gaya mashi me yake gudana sai dai ya ɓoye mashi cewa Areef kawai ke son Romshan ban da Lion, ce mashi ma ya yi Lion ne yake sonta da kansa, kuma shi ya ajiyeta a gidan, tuni A'A ya yi wurgi da soyayyar Rimsha domin ya sani ba shi da yadda zai yi ya iya tunkarar Lion ba, ba zai iya ba, ubansa ya yi kaɗan, hakan yasa shi ma ya hakura da ita ya fawalawa Allah kawai, da haka suka yi sallama sannan A'A ya rubuta sakon ban hakuri na Long page ya tura ta layin Rimsha dan Areef ya gani.
Har lokacin wayar na hannun Areef yana tunanin kalar bakin hukuncin da zai yi wa A'A sai ya ga sakon ban hakuri tare da yin alkawarin ya fita harkar Rimsha har abada, guntun tsaki ya ja kafin ya goge saƙon bayan ya karanta kenan.
(OH LION YANA ZAUNE ANA TA YI MASHI KARYAR WAI SHI YA AJIYE RIMSHA A GIDAN, IMRAN ƊAN DUNIYA NE YASEEN🤣 BARI WATARANA YA JI LABARI YA DAMKESU ZA SU YI BAYANI)
Imran yana gama magana da A'A kiran Lion ya shigo wayar tasa akan ya sanya Rimsha ta kawo mashi abinci É—aki sannan idan ya gama ta je ta gyarawa su Mark É—akinsu aikinta ya fara daga yanzu. Cikin tashin hankali Imran ya kalli Areef in da yake gaya mashi abin da Lion ya ce kenan.
Jinjina kai Areef ya yi kafin ya ce "Ta je ta yi, a yadda Lion yake a yanzu ba wanda zai iya shawo kansa, kasan yau ne ranar da abin ya faru, ba zan iya tinkararsa ba nima, amma bari a kwana biyu, zan gwada shawo kansa akan ya hakura ya kyalata ta yi iya aikinsa kawai ban da na su Mark, ba zan yarda tana shiga É—akin wasu ba, a matsayina na wadda aka bawa amanarta dole na kula da ita fiye da kaina, uncle ya yarda da ni ne yasa ya bani amanarta, to nima ba zan zuba mashi kasa a ido ba, yanzu dai ta je ta yi duk abin da ya ce mata, Rimsha ki je kitchen ki É—auki abincinsa ki kai mashi, idan ya ci sai ki kwashe kayan abincin ki mayar kitchen É—in, sannan ki je ki gyarawa su Mark É—akinsu ko?".
A lokacin ta gama magana da daddy kenan saƙon ya iso mata, Allah ya tsare daddy bai ji ba, da zuciyarsa zata fashe idan ya ji da gaske aiki zata yi kuma harda kartin nan su Mark zata yi wa aiki.
Jiki ba kwari ta miƙe ta fito ta nufi kitchen, already abincin a shirye yake, Mark ya shirya mashi komai, sai sheki kayan da aka zuba abincin yake yi, tamkar yanzu aka fito da su daga ledarsu.
Da kyar ta iya É—aukar abincin saboda tray É—in ya yi girma sosai, a lokacin kuma karfe 10 ta yi.
Kirjinta sai dukan uku uku yake yi, ba ƙaramin razana ta yi ba, sai ambato sunan Allah take yi a cikin zuciyarta, aiki a karkashin irin su Lion sai da ambato sunan Allah domin a samu kwarin gwiwa.
FaÉ—uwar gabanta tare da bugawar zuciyarta kara ninkuwa ya yi lokacin data nufi kofar É—akinsa, sosai ta tsananta ambatar sunan Allah da take yi.
Muryarta sai kerma yake yi yana wani sarkewa ta yi sallama a bakin kofar, shiru bai amsa ba kuma yana zaune a bakin bed nasa, jikinsa na sanye da kayan barci masu shegen kyau launin sky blue mai haske, sai latsa laptop yake yi ya É—aure gashin kannan nasa, wannan fitinannen kamshi perfume É—in nasa ne ya kauraye gaba É—aya cikin É—akin, ya yi kyau sosai tamkar shi ya yi kansa.
Ta É—auki almost 30 mins tana tsaye tana yi mashi sallama amma kamar babu shi a cikin É—akin, sai da ta ji zata iya faÉ—uwa saboda gajiya, sannan ta daure ta kutsa cikin É—akin cike da tsoron me zai biyo baya da ta shiga babu izininsa.
Saura kaɗan ta saki tray ɗin abincin ganin shi da ta yi, a hakan ma ba fuskarsa kai tsaye ta gani ba, a'a yana duke yana kallon laptop nasa, kawai dai jikinsa ta gani ya razana ta duk da yana cikin kayan barci, ba ainahin surar jikinsa ta gani ba, kamshin perfume nasa kuma ba ƙaramin kwantar mata da hankali ya yi ba, ya sanyata ta shiga wata duniya.
Da kyar ta iya karisawa gaban lallausa kuma tsadadden Chinese carpet É—in dake a ta gaban katafaren gadonsa ta ajiye tray É—in, abin da ya sa ta kai wajen kuma ta ga su Imran a wajen suke cin abinci har shi ma Areef É—in, a saman irin wannan carpet É—in na É—akinsu suke cin abincin.
Bayan ta ajiye ta tsaya a gefe tare da É—aga mashi gaisuwa, tamkar babu shi a cikin É—akin, latsa laptop nasa yake yi cikin matsuwa da kwanciyar hankali tare da aji.
Rimsha ta kwashi tsawon 40 mins tana tsaye a wajen nan ba tare da ta motsa ba, shi kuma aikin gabansa kawai yake yi, idan da saboda duk mai yi mashi aiki ya saba da hakan, idan baku manta ba haka bodyguards na gidansu suke fama da shi, wani lokacin ma ya gama zamansa suna tsaye ya É—auki tsawon awa ko sama da haka, daga karshe kuma ya tashi ya bar wajen ba tare da ya ci abincin ba, shi dai halinsa sai shi.
Har hamman barci ta fara yi tsaye a wajen, shi kuwa saboda bakar mugunta sai da ya kara minti goma sannan ya miƙe a nutse ya shiga toilet, ta kasar ido ta bi shi da kallo zuciyarta yana mugun kara tsananta bugu da yake yi, tamkar zai fasa kirjinta ya fito, tana mutuwar tsoronsa fiye da tunanin mai tunani.
Brush ya yi sannan ya fito ya zauna a kusa da tray ɗin, ba tare da ya yi magana ba ya yi shiru, cikin sauri ta duƙa tana ƙoƙarin zuba mashi abincin. Wani irin razana ta yi jin sexy voice nasa ya ce ta miƙo mashi wayarsa dake a saman bedside drawer, da sauri ta miƙe ta ɗauko mashi wayar ta dawo ta miƙa mashi, ba tare da kalle ta ba ya karɓi wayar ya fara latsawa.
Ita kuma ta ɗauko wani cup mai shegen bala'in kyau wadda shi kaɗai ma kawai ya ishi mutun ya kwashi mintoci yana kallonsa, da alama kuma cup ne mai bala'i tsada, kuma da alama dai cup ne na musamman, sai kyalli yake yi fari tas da shi, zuba mashi hot green tea na kasarsu mai shegen kamshi ta yi, sai tiriri yake yi, a nutse ta tura mashi a gabansa, sannan ta fara zuba mashi abinci a plate mai shegen kyau, kuma plate ɗin irin cup ɗin ne, da alama set ne, ta san cewa shine abin da yake buƙata tun da shi aka shirya a saman tray ɗin.
Ɗaukar tea ɗin ya yi ya fara sha domin ya fi buƙatarsa da zafi sosai, a hankali yake kai cup ɗin saitin ɗan bakinsa yana kurɓa.
Ita kuwa sai faman zuba mashi duk wani abin dake a saman tray É—in take yi a cikin plates, bai wuce sha biyar ya yi wa tea É—in ba ya dawo da kallonsa saman abincin da take zuba mashi domin ya gani kar ta cika mashi abinci sosai saboda ba wani ci sosai ke gare shi ba.
Lokacin da dara daran blue eyes nasa ya sauƙa a saman hannunta da take zuba mashi abincin, wani irin wurgi da cup ɗin hannunsa ya yi ya miƙe da sauri ya nufi toilet. A razane ita ma ta miƙe tare da dafe saitin zuciyarta dake yi mata barazanar tarwatsewa, Baiwar Allah faɗuwar gaba da bugun zuciyar ma kawai zai iya sanya ta ta mutu ba tare da ta shirya ba.
Shi kuwa amai ya rinƙa kwarawa kamar zai amayar da hanjin cikinsa, har wani ja idanunsa suka yi, tunani ta fara yi akan me ya sanya shi yin amai ne haka?.
Tana tsaye tana tunani har ya fito ya sameta. Kasa kasa ya motsa laɓɓansa ya ce ta zube gwiwowinta a kasa. Cikin sauri ta yi kasa jikinta na ta ɓari sosai, dama ga zazzaɓi. Rai a ɓace ya kara kallon hannun nata, a rayuwarsa ya tsani zanen lalle kamar me, kyamar abin yake yi fiye da tunanin mai tunani, wannan dalili ta sanya shi yin amai dan ya ci abin da ta taɓa da hannunta mai lalle.
Gaban mirrorsa ya nufa ya ɗauko wani chemical dake a cikin drawers na wajen, ya dawo wajen da take duƙe.
Gently ya ce mata ta bashi hannunta, jininta na karma ta haɗe hannunta dukka biyu ta miƙa mashi.
Babu tausayi ko kaɗan a face nasa haka ya zuba mata wannan chemical ɗin a hannayenta. Wani baƙin azaba ne ya dira mata lokaci guda wadda ya sanyata sakin wani irin kuka mai sauti tare da ratsa duk wata zuciya mai imani da tsautsayi, amma fa shi kokaɗan babu alamar tausayi a face nasa, ta yi mugun ɓata mashi rai ba kaɗan ba.
Nan take hannayen nata suka fara zubar da jini sakamakon chemical É—in ya farfasa mata fatar jikinta.
A takaice ya ce ta yi mashi shiru ko kuma ya take wuyarta a nan, ba shiri ta ja bakinta ta yi shiru, tana jin azaba ta haÉ—iye kukan nata kamar an É—auke wutar nepa.
Bayan ya gama zuba mata chemical ɗin ya rufe robar tare da maida shi mazauninsa yana faɗin ta goga hannun nata da kyau dan tsabar rashin imani da baƙin mugunta.
Hawaye wani na bin wani haka ta fara goga hannayen nata cikin na juna chemical É—in yana kara ratsata.
Sai da ya tabbatar gaba ɗaya zanen lallen ya fita sannan ya ce ta miƙe ta je ta cinye abincin nan duka, kada ta rage ko kwara ɗaya, sannan ta kwashi kayan abincin ta je ta zubar da su a bola baya son ya sake ganinsu dan ta taɓa da hannunta kai lalle.
BABBAR MAGANA taya za'ayi ta cinye abinci kula guda, kula ma kuma ba ƙarami ba, sannan ga sauran kuloli na su ferfesu da sauransu, ga kuma su fruits, kun dai san halinsa idan ya yi magana whikenan babu wanda ya isa ya sanya shi ya sauya ko da kuwa me zai faru. (DA RABON CIKIN RIMSHA ZAI FASHE YAU)
Da kyar ta iya miƙewa ta nufi wajen abincin, tana mai danasanin zuwanta duniya ma baki ɗaya, ƴar tsawa ya daka mata akan ta fara wanke jinin hannayenta ta daina ɓata mashi ɗaki, kuma ta yi maza ta fara gyara mashi ɗaki wajen da chemical da kuma jininta ya ɓata kafin ta zo ta cinye abincin.
Ta rasa ya zata yi, ta rasa a ina zata wanke hannun nata da ya ce ta wanke, shin in je toilet nawa ne ko dai yaya? Ta tambayi kanta da kanta.
Ganin babu mai bata amsa yasa ta nufi waje tare da runtse ido tana mai jiran jin wani tsawar tasa, ai kuwa hakan ne ta faru domin kuwa sai lokacin idanunsa suka sauƙa akan kunshin kafarta, wannan dalili yasa ta sake jin voice nasa ya ce ta dawo ta ɗauki chemical ɗin da kanta ta zubawa kafarta ta goge kunshin nan, Allah sarki kunshin da aka yi mata jiya jiya.
Tana hawaye ta dawo da kanta ta É—auki chemical É—in daga wajen da taga ya ajiye, shi kuma komawa saman bed nasa ya yi ya zauna tare da cigaba da latsa laptop nasa kamar É—azun.
Ita kuma da kanta ta zubawa kanta chemical tana kuka ta goge wannan kunshi na kafarta tas, sannan ta miƙe kafar tata sai jini yake yi ta nufi waje.
Tana fita bedroom nata ta nufa, tana shiga ta zube gwiwowinta a kasa tare da sakin wani marayar kuka, tana cikin yi sai ta tuna da abin da ya ce ne ta zo ta gyara mashi ɗaki, hakan yasa ta miƙe da sauri ta nufi toilet nata.
Wani irin bakin azaba ta ji lokacin da ta zuba ruwa a kafar tata da hannun nata, wani irin zogi da raÉ—aÉ—i suke yi mata, jikinta har lokacin kerma yake yi, ita tunanin yadda za'ayi ta cinye abincin da ya ce É—in nan ne ma yake damunta.
Haka dai ta wanke kafar tata da hannun nata duk sun yi jawur da su, chemical É—in duk ya tsastsage mata soft skin nata, duk wanda ya ganta a halin da take a ciki sai ya tausaya mata tare da matsa mata kwallah.
Da kyar ta iya jan kafarta ta koma É—akin nasa, gyara wajen da ya baci da chemical da kuma jininta ta fara yi, sai da ta gyare shi tsab, sannan ta zauna ta fara cin abicnin kamar yadda ya saka ta.
Shi kuwa tamkar babu shi a É—akin, ya fasa cin abicin ya hakura, dan already ta riga da ta tayar mashi da zuciya, komai ya ce zai ci yanzu amai zai sanya shi, idan baku mance ba dukka TRIPLETS shegen bala'in kyakkyanin ke gare su na fitar hankali, amma É—an gara Areef da yake ya rayuwa a wurare daban daban wadda hakan ta sanya kyakkyanin tasa ta ragu, Lion da Aseef kam ba'a magana kyankyaninsu ya wuci tunanin mai tunani, ya wuci misali.
Wani irin wahalallen amai ne ya zo mata lokacin da ta fara cin abincin nasu, amma saboda bala'in tsoronsa yasa ta haÉ—iye amai É—in, ta daure ta fara cin abincin, wani irin É—anÉ—ano ne abinci nasu yake da shi wadda ita dai bai yi mata ba kwata kwata, haka abincin nasu ya yi mata.
Tun tana ci da É—an daÉ—in rai har ta fara kuka mai sauti, wlh tamkar babu Lion a cikin É—akin nan, da kukan nata ma ya isshe shi tsawa ya daka mata akan ta dai'na damunsa ko kuma ya taketa a nan, ta gama cin abincin nan ta je ta gyarawa su Mark É—aki.
Yau taga bala'i da tashin hankali, bata taɓa tunanin rashin imaninsa ya kai har haka ba. Tana tsaka da cin abincin tana kuka hannunta kuma yana jini har lokacin,
💖💖TRIPLETS💖💖
E93-94💖
Yau taga bala'i da tashin hankali, bata taɓa tunanin rashin imaninsa ya kai har haka ba. Tana tsaka da cin abincin tana kuka hannunta kuma yana jini kaɗan kaɗan har lokacin.
A haka Imran da Areef suka shigo suka same ta.
Wani irin bakin ciki Areef ya ji lokacin da ya ga me yake faruwa, Rimsha cikinta ya cika kamar zai fashe, ga shi kuma yanzu ne ma ta ci rabin abincin dake a cikin kular, ga kuma su ferfesu a gefe sannan ga fruits da su drinks, a ina zata zuba su kuma? Ga shi ya ce ko É—iko na abin dake a kan tray É—in kada ta tage mashi.
Imran kam kasa jurewa ya yi ya saki Areef ya juya da sauri ya fice daga cikin É—akin dan gudun kada zuciyarsa ta buga, shi kuma Areef ya ma rasa me zai ce, ya rasa ta ina zai fara yi wa Lion bayani akan ya yi wa Allah ya rabu da yarinyar nan haka.
Sosai ya tsare Lion da ido yana kallonsa yayin da ita kuma take lodan abinci, tamkar Lion bai san ana ganinsa ba, kamar bai san da shigowarsu É—akin ba, aikin gabansa kawai yake yi.
Wucewa Areef ya yi izuwa in da take zaune, a gefenta ya zauna tare da É—aukar spoon suka fara cin abincin tare, ko sannu Lion bai ce masu ba, shi kuma Areef bai lura da hannun nata ba.
Da kyar da zufa suka kammala cin abincin nan, dukkansu sun kasa shan ruwa saboda bala'in ƙoshi, ita kam magana ma ta kasa yi sai nishi sama sama take yi.
Da hannu Areef ya yi mata alama akan ta kwashe kayan abincin ta fita da su waje, tana nishi da kyar da makyarkyata ta miƙe tare da ɗaukar kayan ta fice tana jan kafa.
Zuba mata ido Areef ya yi yana kallon yadda kafarta ya yi wani irin tsage tsage yana fitar da jini kaɗan kaɗan, tunawa ya yi da ɗazun kamar ya ganta da kunshi a kafarta, kenan chemical Lion ya zuba mata a jiki dan baya son ganin kunshin, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun wannan wace iriyar bala'i ce, ya faɗa a ransa tare da miƙewa da kyar shima saboda ciwonsa ya haye saman bed ɗin na Lion yana tunanin ta yadda zai ɓullo wa Lion dan su warware wannan matsala a tsakaninsu.
Ita kuwa tana fita bedroom nata ta wuce da kayan abinci, saman carpet ta ɗaura tray ɗin tare da nufar toilet da gudu ta rinƙa sheƙa amai kamar wadda aka yi wa wahayin aman.
Amai take zubawa babu kama hannun yaro, baiwar Allah tun tana iya gani sosai har idanunta suka rufe, wani irin jirine ya kwasheta tana ƙoƙarin zubewa kasa a cikin toilet ɗin Imran da ya shigo tun ɗazun ya tsaya yana kare mata kallo, cikin zafin nama ya tarota ta faɗa jikinsa tana jan numfashi da kyar da kyar.
Zuba ruwa a cikin baff É—in wanka ya yi tare da surka na zafi dana sanyi sannan ya É—auketa kacokam ya sumdumata cikin ruwan.
Sai sauke wahalallen numfashi take yi, wani irin yanayi ta tsinci kanta mai wuyar fassarawa. Shi kuma juyawa ya yi ya fita daga cikin toilet É—in dan ya bata dama ta yi wanka ko zata samu karfin jikinta.
Yana fita ya wuce bedroom na Lion, nan ya isko Areef kwance saman bed, daga baya ya tsaya yau iya ɓacin rai ya shiga ɓacin rai fiye da tunanin mai tunani, akan kanwarsa kam ba zai iya juran wannan walaƙanci ba, dole su bar gidan nan yau.
Cikin natsuwa ya ce "Saif zan É—auki kanwata mu koma gida tun da Areef yana nan!" Shiru Lion bai tanka mashi ba, dama kuma yasan ba zai tanka a yanzu ba, sai time da ya ga dama.
Haka kuwa akayi sai da Imran ya É—auki tsawon 20 mins a tsaye kafin nan gently ba tare da ya É—ago ba ya fara magana "Ba bu in da zaka je har sai na bar Nigeria, sannan kuma wannan yariya Æ´ar aikin muce, idan kuka matsa mani to wlh daga nan har Washington DC zata tabbata a Æ´ar aiki, so zaka iya komawa bedroom naka!!". Ya yi maganar with he's full confidence tare da nuna isa tamkar shine wanda ya haifi Imran É—in, wannan isa da ya nuna ma ko Abban Imran baya nuna shi ba
Shiru Imran ya yi domin ba yadda zai yi, ba ta yadda zai fita gidan ba tare da izinin Lion ba, kuma ma ko da ya fita Lion yana zaune a cikin ɗaki zai sa a dawo da shi, wannan wace iriyar bakar kaddara ce? Ya tambayi kansa, shi kuwa Areef kashewa Imran ɗin ido ɗaya ya yi tare da yi mashi alama akan kada ya sake magana, domin idan ya sake magana za'a iya samun matsala, zai jawa Rimsha wata bala'in ce, gara kawai su kyale shi zuwa nan da kwana biyu idan ya sauƙa ya huce to sai su tunkare shi da zancen ta daina yi wa su Mark aiki, amma yanzu kam su kyale shi tukunnan tun da a yaune abin ya faru.
Jiki ba kwari Imran ya juya ya fice daga bedroom É—in ya koma na Rimsha dan yaga wani hali take a ciki baiwar Allah.
Ta gama wanka sai faman dafa bango take yi dan ta fito daga toilet É—in, wani azababben ciwo kanta yake yi mata, wani irin duhu duhu take gani a cikin idonta, lokaci guda gabaÉ—aya ta sauya tamkar ba ita ba.
Riƙota Imran ya yi suka kariso cikin ɗakin, saman bed nata ya zaunar da ita tare da ɗauko mata wani abaya daga cikin kayanta sannan ya zo ya sanya mata a jikinta kafin ya ce ta kwance towel ɗin bari ya je ya maida cikin toilet , ba musu ta ɗan miƙe ta kwance mashi, nan take ta fara rawan sanyi na zazzaɓi.
Bayan ya mai da towel É—in cikin toilet ya dawo ya bata maganin da Areef ya bata É—azun, sannan ya ce ta haura saman gado ta kwanta, haka ta haura ta kwanta ya ja bargo ya rufa mata tare da yi mata addu'ar barci ya fito ya barta kwance, zuciyarsa cike fal da tunaninta.
Bedroom nasa ya wuce a in da ya je ya yi wanka shima ya haye gadonsa tare da kashe wayarsa dan yau baya jin zai iya hira da jelly É—in ma, yana cikin yanayi mara daÉ—i.
Shi kuma Areef yau a É—akin Lion ya kwana, a tare suka kwana.
A ɓangaren Akil da Umaisha kuwa, kwance Umaisha take saman gado daga ita sai wata ƴar shegiyar riga mai ƙaramin hannu wadda ta tsaya mata a iya cinya, ba pant kuma babu bra a jikinta, haka zalika kwanciyar da ta yi yasa rigar ta yi sama, santala santalan cinyoyinta a waje, sai wani yauki take yi tana wani kara bin lafiyar gado, da alama cikin nata ɗan son jikine.
Ɗaure da towel a kugunsa ya fito daga toilet, yayin da yake riƙe da wani karami kuma yana goge kansa da jikinsa da shi.
Wani irin yawu ya haÉ—iye ganinta da ya yi a haka, wurgi da towel É—in hannunsa ya yi ya haye saman gadon yana faÉ—in "Wife kina haukata yaya Akil sosai".
Juyowa ta yi suna fuskantar juna, turo bakin nan ta yi cikin yauki da shagwaɓa ta ce "Yaya Akil dan Allah ka matsa mani jikina ciwo yake yi mani".
Bakinsa ya kawo saitin kunnenta yana faÉ—in "Yanzu zan baki abin da ya fi matsa jiki, gwaggo batula ta wani ce mani wai na barki sai babynmu ya yi kwari idan ba haka ba zan iya zubar da cikin, ina ba zan iya ba, Allah zai tsare mana babynmu dan haka ajiye zancen gwaggo Batula a gefe, bari na kara mani wani babyn dan mu sami twins tun da wanan É—in bai yi girma ba, 2 weeks ne kawai, bari yau na karo guda biyu, idan kin kasa haihuwa sai na taya ki".
Ita ma da yake yar nema ce sai ta mirgino ta shige jikinsa, riƙeta sosai ya yi tare da kawo bakinsa daf da kunnenta kasa kasa kamar wani na yi masu laɓe ya ce "Wife kin san fa aka ce mace tafi daɗi idan tana da ƙaramin ciki, dan haka bari na shanye daɗin dukka na more kafin ki haife cikin na kara maki wasu, dan Allah ƴaƴa dozen nake so".
Ita dai bata yi magana ba sai wani nanukar jikinsa take yi É—an cikin nasu ma da gulma wai É—umin jikin babansa yake son ji kullun, shiyasa take ta wani kara shige mashi jikinsa, shi kuwa ganin haka yasa ya fara bata a jikinta ba kama hannu yaro.
A ɓangaren gidan Abba kuwa yau ma kamar kullun Akila dai an zuba love da masoyin ɓoye fiye da tunanin mai tunani, sai dai kuma fa yau ma sai da ya saka ta kuka da salon soyayyarsa, haka kuma ya zauna ya zama mata kamar karamin yaro, yana zuba shagwaɓa yana rarrashinta har sai da ta yi shiru, sannan ya yi mata kamar jiya, ya ce ta bar wayar manne a kunnenta bari ya zuba mata zafafan kalamai har zuwa ta yi barci.
Haka kuwa akayi, ya kasheta da kalaman da sai da ta yi mafarkinsa, wani irin barci ta yi mai cike da nishaÉ—i tare da begen masoyin nata.
Idan muka koma gidan LION kuwa, a wannan dare dai Imran ne ya sake miƙe wa da kansa ya je ya yi sauran aikin Rismha da bata kammala ba, sannan ya dawo ya kwanta.
DREAM (Mafarki)
Misalin karfe biyu na dare, zaune take a cikin palonsu na sama, daga ita sai wandon jeans guntu zuwa santala santalan cinyoyinta, ta sama kuma wata yar riga ce mara nauyi wadda ta tsaya mata a iya cibiyarta, hannunta riƙe yake da wani tsadadden haɗadɗen cup mai shegen kyau wadda ke ɗauke da custard da spoon a ciki, a hankali take ɗeba da spoon tana kaiwa ɗan bakin nan nata, sai wani murmushi take yi tana cikin nishaɗi sosai.
Daga ta bayanta ta ji ya zuro mata hannu izuwa saman wuyarta, ko bata juya ba ta san wanene domin kuwa kamshin perfume nasa ya isar mata da saƙon wanene ɗin, ɗebar custard ɗin ta ta yi zata kai bakinta, cikin sauri ya sanya hannun nasa a bakinta ya rufe mata, a lokacin kuma tana gab da kai spoon ɗin cikin ɗan bakin nata, hakan yasa custard ɗin ta zuba mashi a hannunsa.
Ƴar kara ya yi mata a shagwaɓe, da sauri ta ajiye cup ɗin tare da riƙo hannun nasa in da custard ɗin ya taɓa ta lashe tas sannan ta cigaba da lasar hannun nasa.
Ɗaukar ɗayar hannunsa ya yi ya ɗaura a saman shafaffen cikinta yana shafawa a hankali,. Cikin nata a shafe tamkar bata taɓa zuba abinci a ciki ba.
Wani irin dogon numfashi ta ja tare da sauƙe wa a hankali, matso da ɗan bakinsa ya yi saitin kunnenta, kasa kasa ya ce "Meesha mu je ciki in baki wani abu mai daɗi kin ji ko?" Ɗan juyo da face nata ta yi da nufin ta yi magana, bata kai ga yin maganar ba ya manna mata kiss a kumatunta yana faɗin "Please mu je mana, abun daɗi fa zan baki".
Okey ta ce mashi tare da miƙe wa ta juyo suna fuskantar juna, wani irin ihu ta kurma da ganin cikin kwayar idanunsa, a razane ta farka daga barcin da take yi, sai haɗa wani uban zufa take yi tamkar ba gobe, da alama zazzaɓin nata ya sauƙa, jikinta har kerma yake yi.
Da kyar da addu'a da ambato sunan Allah ta samu ta mai da barci, domin ba zata iya tashi ta yi nafila ba saboda rashin lafiya da take a ciki, ta kasa tashi hakan yasa ta gwammaci komawa kawai ta kwanta zai fiye mata alkhari.
Da kyar ta samu ta iya mayar da barcin nata, cike da danasanin mafarkin Lion da ta yi a yau.
Washegari sai karfe 7 ta samu dama ta iya tashi daga barcin wahala da ya É—auketa tun bayan sallar asuba.
Wayarta da Imran ya ajiye mata a saman bedside drawer ta fara dubawa, nan fa ta sami miss call na new number har kala uku, ko wani number kuma ya mata miss call zai kai guda biyar.
Shiru ta É—an yi tana tunanin waye zata fara kira a cikinsu, daga karshe dai ta yanke shawarar bari ta kira ta farkon da ta fara kiran nata ta ji ko wanene.
Bugu ɗaya aka ɗauki kiran, cike da zumuɗi ta ce "Hello Rimsha". Duk da halin da take a ciki hakan bai hanata sakin cool murmushi ba, cike da so da kauna ta ce "Anaya ke ce dama?" Daga ɗayan ɓangaren ta ce "E Rimsha nice na ga jiya baki zo school bane shi ne yanzu na gama shiri daddy zai kai mu sai nace bari na kira number da kika bani na ji ko lafiya". Daga jin yadda take magana tana cikin matuƙar faricniki tare da jin daɗin samun Rimshan a waya.
Kara faÉ—aÉ—a murmushin Rimsha ta yi kafin ta ce "Anaya wlh kaina ne kawai yake ciwo Shiyasa ban zo ba, amma gobe zan zo In Sha Allah". "Subhanallah Allah sarki Rimsha Allah ya baki lafiya, to idan na dawo school zan ce daddy ya sanya driver ya kawo ni gidanku sai na duba ki ko? Wannan shine numberta ki yi saving kin ji?".
"To Anaya amma sai na fara gayawa yaya Imran zaki zo tukun nan, idan ya yarda to Shikenan sai na kiraki na gaya maki" to Anaya ta ce sannan suka yi sallama sai murmushi Rimsha take yi, baki ya ki rufuwa, haka ita ma Anaya É—in, tana matukar Kaunar Rimsha sosai, ita ma Rimshan tana matukar kaunar tane sakamakon ta ce Anayar tana yi mata mugun kama da Jehan, tamkar Æ´an biyun Jehan ce ita, harta shekarunsu kusan É—aya ne, sai dai Jehan ta É—an fi Anaya kaÉ—an amma bacin haka komai har tafiyarsu yanayin magana komai iri É—aya, sai dai kuma Anaya tana dariya, ita kuma Jehan ba sai na sake faÉ—a ba, kunsan kwata kwata bata ma san me murmushi ba bare kuma dariya, wannan shine kawai banbancin Anaya da Jehan,. Kada ku mance JEHAN da Nawazudden take kama sosai.
ANAYA AZHARUDDEEN SALMAN SULTAN nasan daga jin sunan kun san wace ce Anaya a wajen su Rimsha, sai dai kuma ita Rimshan bata sani ba, domin bata san wanene Azharuddeen É—in bama, daddynta kawai ta sani, sai kuma yanzu da ta san cewa su Imran ma Æ´an uwanta ne.
To musan waye Azharuddeen kaɗan a tare, nasan daga jin karshen sunansa na SALMAN SULTAN kun fahimci cewa ɗan uwane ga NAWAZUDDEN SALMAN SULTAN, to Azharuddeen dai shine Hasan ɗin Nawazudden, Professor ne lecturer a jami'ar Ahmadu Bello University Zaria, sai dai mazaunin cikin garin Kaduna ne, a nan yake shi da family'nsa baki ɗaya, yana da gida a zaria a in da yake sauƙa ya kwana sai ranar Friday ya dawo cikin Kd wajen family'nsa, shararren mai kuɗi ne na bugawa a jarida, bayan Professor ne kuma yana da kampanoni da dama a faɗin kasar nan wadda take amsa sunan SALMAN SULTAN, ƴaƴan sa uku, babba namiji ɗaya mai suna Feroz shine babba mai shekara 18 yanzu a duniya, sai kuma Anaya mai shekara 15 a duniya, sai autarsu Zaira mai shekara 14 sana'ar Rimsha kenan, da yake matarsa babbar likita ce sai ta ɗauki hutun haihuwa tun daga kan Zaira ta ce ta yi auta ba ƙari.
Azharuddeen wato Hassan yana bala'in Kaunar Æ´aÆ´an nan nasa fiye da tunanin mai tunani, hala zalika yana kaunar Æ´an uwansa su Abbi, da su yake kwana da su yake tashi, yana yawan bibiyar lamuransu, shi ya rayu da su na tsawon lokaci, daga bayane ya zame kansa daga garesu, amma Daddyn su Rimsha tun yana yaro ya barsu, hakan yasa da wuya su iya gane shi a yanzu, idan dai ba shi ne ya ce masu shine wane ba, amma fa lokacin da ya fito takarar shugaban kasa sunansa ya fara yawo a duniyar Africa baki É—aya, har gida PROF AZHARUDDEEN ya zo dan ya ganshi ido da ido domin ya tabbatarwa da kansa wannan kamanni dake a kan fuskokinsu, amma ko da ya zo Daddyn Rimsha ya ce sam ba shi bane Hosain, sunane kawai ta yi iri É—aya wadda kuma ana iya samun hakan a cikin jama'a tunda dai duniya da faÉ—i take, Azharuddeen ya ji ne kawai amma bai yarda ba, abin da kuma yasa ya kyale daddyn ya tafi dan saboda kada ace sai yanzu da daddyn ya yi kuÉ—i ya zama wani shi ne za su neme shi, hakan yasa kawai suka kyale shi, amma ba su cire tuhumar akan cewa shine Hosain ba, haka zalika suma su Abbi sun tuhumeshi ne saboda sunansa, suma ya musa masu saboda wani dalili nashi da bamu sani ba, wata kila sai gaba za su buÉ—e mana komai mu sani. WANNAN SHINE TAKAITATCEN WAYE AZHARUDDEEN SALMAN SULTAN IN KIYA HASSAN A YANZU, SAI MUN SHIGA CIKIN LABARIN KUMA ZAMU SAN AINAHIN TOSHEN KAN ZANCE AKAN FAMILY'N.
Ajiye wayar ta yi bayan sun gama magana da Anaya, cikin sanyin jiki ta sauƙo kasa daga saman gadon ta nufi toilet, ruwa mai zafi sosai ta zuba ta yi wanka da shi, sannan ta fito bayan ta ɗauro alwala dan ita kullun cikin zama da alwala take.
Shiryawa ta yi cikin riga da wando kamar yadda ta saba, sannan ta sanya takalmin flat shoe mai shegen kyau, ta yi kyau sosai kamar ka sace ta ku gudu ka je ka ajiyeta kayi ta kallo dan kyau, sai wani kara cika take yi kwana biyun nan, tamkar ba ita ba, idan ta yi murmushi Yanzu wani irin lotsa dimple nata yake har wani irin rami yake yi saboda ta kara kumatu, har lokacin hannunta basu dai na yi mata zafi ba, hannun ya fi yi mata zafi domin dayawa ya zuba mata chemical É—in a hannu, a kafa kuma ita ce ta zuba da kanta, so kaÉ—an kaÉ—an ta zuba, ba sosai ba, da hannu da kafar duk sun kumbura, kun san idan fatar mutun ta tsage dole wajen ya kumbura, a hakan ma dan daren jiya da tana barci Areef ya shigo É—akin ya shafa mata magani, da yake jiya taci wuya sosai, da ta kwanta ko motsawa bata yi ba, wani irin barci mai nauyi ne ya É—auketa, hakan yasa bata ma san time da Areef ya shafa mata maganin ba.
A hankali ta fito palon sama, kamar kullum babu kowa a palo, wuce wa ta yi ta nufi kasan benen dan ta je ta gaishe da Areef, sai tashin kamshi take yi abinta.
Da sallama É—auke a bakinta ta shigo cikin É—akin, yau yana zaune ne a saman sofa set dake a cikin É—akin, daga shi sai singlet fara tas da three quarter zuwa gwiwa, ya yi wanka, kai Allah ya yi wa TRIPLETS halitta, wani irin sihirtaccen kyau na musamman ne ke gare su, sai kallon shi take yi, yau ma kamar jiya cikin zolaya ya ce mata "Da gaske Lion ya fini kyau, amma dai jiya da nace maki kafarsa ya fi nawa kyau wasa nake yi maki, halittar kafarmu duk iri É—aya, amma dai ya fini kyau sosai gaskiya".
A yau dai bata ɓoye fuska ba, sai ma ɗan ɗaure fuska da ta yi jin ya amfaci sunan Lion, ta tuna azaban da ta sha daren jiya ne.
Kamar dai ko yaushe, gefensa ya nuna mata ta je ta zauna yana faɗin "Dan Allah Rimsha ki yafe wa ɗan uwana, kada ki ce zaki dai'na son shi saboda abin da ya faru jiya, duk abin da ya ɓata mu zamu gyara, shi kuma zai biya ki amma sai gaba, ina sa ran haka, kiyi hakuri saboda mu kin ji ko?".
Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e ta ji. Wayarsa ya ɗauko ya fara kiran layin Aseef video call, dama tun ɗazun Aseef ya takura mashi akan ya haɗa da RIMSHA ya ce mata sorry da abin da ya faru,. Allah mai iko wai yau family'n William jacop ne za su cewa wata sorry, sorry ma kuma ga mace, tab lallai musulci duniya ne, musulci daban take, idan Allah ya yo ka a musulmi to ko tabbata ka yi kana gode mashi baka biya shi ba, addini mai sanyi, mai sauƙi, tausayin na kasa, girmama iyaye, kamanta adalci, rashin wariya, kaunar juna, Allah mun gode maka da ka yo mu a musulmai.
Yanzu haka a yadda Lion yake nan Addinin Musulunci ta sanyaya mashi zuciya sosai da sosai, da lokacin da yake kristar ne Rimsha ta sanya shi amai, da sai dai muce Allah ya jiƙanta, dan ko bai kasheta ba, to wlh ba zata sake moruwa ba, amma da yake akwai sanyin musulci a ransa sai ya tsaya a iya chemical, yanzu ga shi saboda musulci Aseef ya ce a kira mashi ita ya bata hakurin abin da ɗan uwansa ya yi mata, yanzu sun san da cewa ba komai ne idan suka yi ya zama daidai ba, dole akwai abin da ba daidai ɗin ba, kuma idan sun san sun yi ba daidai ɗin ba, suna kokarin su gyara, idan wannan murɗaɗen ɗan uwan nasu ne ya yi wadda shi ya fi karfin ba da hakuri, kuma idan ka ce mashi hakan zaka karɓi hukun dan baya son wannan kalma ta sorry, to idan shine ya yi abin da ba daidai ba, su biyun suna kokari su gyara su kuma bada hakuri a madadinsa, BAYIN ALLAN.
Bugu É—aya Aseef ya É—auki kiran, yana zaune a saman table yana cin abincin, yau wani irin azababben kyau ya yi, idanunsa na sanye da wata shegiyar glasa mai bala'in kyau da tsada baka mai É—an girma, jikinsa na sanye da high neck t-shirt maroon color da wandon jeans fara tas, bayan sarkar da Lion ya ba shi akwai wasu karkar zinari guda biyu a wuyar tasa, daga hannunsa ma akwai sarkar hannu masu bala'i kyau da tsada, yau ya yi wa gashin kansa penti, amma daga É—an gefene ya sanya purple color ya tura iya gefen kunnensa, kunsan gashin nasa yanzu ta yi tsawo, kuma Musharraf ya ce kada ya aske, shine ya barta har kalata yake yi yanzu, ba karamin kyau ta yi mashi ba, sai tashin wani irin fitinannen kamshi yake yi, ga kwarjini bala'i a tattare da su, sannan ga farin jini na fitar hankali.
Cikin sanyin murya ta ce "Good morning yaya ASEEF". Maimaita kalmar yayan ya yi kafin ya amsa mata, sosai Rimsha take kallonsa saboda na gaya maku shi ya fi kama da Lion akan James.
Zubawa sarkokin wuyarsa idanu ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce "Wannan sarkar ta so ta yi kama da nawa, sai dai kuma akwai banbanci sosai da sosai, nawa complete ne kuma nawa round ne ba mai Heart ba, amma nima nawa yana kyalli kamar haka".
Fuska É—auke da murmushi ya ce "ina naki É—in yake, kawo bari na gani". Okey ta amsa mashi da shi sannan ta É—an yi kasa da wuyar rigarta ta fito da sarkar, É—an murmushi ya yi kafin ya ce "Akwai bambanci da namu sosai, na farko naki ba real zinari bane, akwai miss, namu kuma zinari ne zalla, baki ga saman tambarin nakin baya wani kyalli sosai kamar igiyar ba ne? Kuma sarkar ma ba su yi iri É—aya ba, cox kawai dai chain É—in ne ya so ya yi kama, wannan sarkar mummy'n mu ne ta bamu, ina son shi sosai, na ki ma ya yi kyau sosai, in saya maki wani zaki sanya?". GyaÉ—a mashi kai ta yi alamar e
Shi dai Areef ido kawai yake bin su da shi ya wani riƙe masu waya kamar wani ɗan aikinsu.
"Tom shikenan zan sa Prof ya saya maki zinari mai shegen kyau irin namu sai ki saka, duk da na san da wuya a sami sak irin namu domin namu mummy da kanta ta je aka buga mata, ita ta zaɓi design da take buƙata da kuma time da date a jiki, amma dai ba za'a rasa mai kama da shi ba, da a ce ina free ma da na je da kaina company na basu nawa in ce a buga mani irin shi sai na zo maki da shi, amma dai yanzu ma ko an saya maki wani zan sanya a buga maki wani irin namu na zo maki da shi kin ji ko?".
Fuskarta É—auke da fara'a ta ce "E naji kuma ina godiya sosai da sosai".
Rimsha ya ambaci sunanta da wata iriyar murya wadda sai da ya sanya Areef kallonsa, ita ma dai ta yi mamakin yadda ya kwantar da muryarsa kasa kasa ya amsaci sunanta.
"Rimsha ki yi hakuri da abin da ɗan uwana ya yi maki kin ji ko? Kada ki riƙe shi a zuciyarki, ki yafe mashi dan Allah, shi haka yake, shi sarki ne, amma mu bamu son hakkin kowa ya kama shi, musamman ma hakkin ke ɗin nan, bana so ya kama shi, idan baki yafe mashi ba ina da tabbacin Allah zai bi maki hakkinki domin wannan a rubuce take, to dan Allah ki yafe mashi sannan kuma ina mai matukar farinciki da kika kasance ƴar uncle Hosain, na ji daɗi fiye da tunaninki, kuma ina matuƙar ji dake kema tamkar uncle, ki kula mana da kanki ƴar kanwar mu, banda rashin ji, ayi karatu sosai, daddynki yana can yana barcin gajiya, ni kuma zan tafi school yanzu ina da exams, yau zan yi na ukun karshe, so please pray for me kin ji ko gimbiyar TRIPLETS?".
Murmushi Areef ya yi, tana ƙoƙarin yin magana ya rigata da cewa "Aseef kana da sata fa, yanzu ina ruwanka da sunan da nake kiranta da shi da zaka sata mani? Kaima ka kawo naka sunan mana, daga na baka labari shikenan ka sace mani suna".
Kallon gefen ido ya yi mashi a yayin da idanun nasa suke a cikin glass. With full confidence ya ce "Ka gaya mani menene banbancina da kai? Idan ka gaya mani zan daina yin abin da kake yi". Hararar wasa Areef ya yi mashi kafin ya ce "Na fika kyau mana, kuma na fika karfi sannan na fika iya cin abinci".
Dariya sosai Aseef ya yi kafin ya ce "Kuma ka fini neman magana ba, ni ka bari Gimbiya ta yi mani magana zan wuce school time na tafiya". Kallonta Areef ya yi alamar ta yi magana Aseef na jiranta.
"Our Queen kin yafe wa ɗan uwana? Dan mu zaki yi ba dan shi ba kin ji ko?". Cikin sanyin murya, a nutse ta ce "Ni dama ban riƙe shi a zuciyata ba, na yafe mashi Allah ya ya fe mu tare". Wani haɗaɗɗen murmushi ya sakar mata kafin ya yi mata sallama ya miƙe daga saman table ɗin ya nufi waje yana sallamar Areef.
Bayan Areef ya katse kiran ne ya ce mata "Ki je ki É—auki abinci ki kaiwa Lion, ki kula sosai wajen zuba mashi abinci, nima ina nan zuwa bedroom É—in nasa yanzu, baya cin abinci sosai, dan haka kaÉ—an zaki zuba mashi, yanzu dai É—auko magani a cikin A box É—in can bari na shafa maki a ciwukan naki".
To ta amsa mashi da shi sannan ta miƙe ta ɗauko ta kawo mashi, har zai shafa mata sai kuma ya fasa domin idan ya shafa mata ta je zubawa Lion abinci ya ji warin maganin nan to wata azaban zai sake yi mata, shi idan zai ci abinci ya fi son ya ji iya kamshin abincin ne kawai, idan ya ji wani kamshi a wajen bayan wannan da kuma perfume to za'a samu matsala, shiyasa sojojinsa suke matukar taka tsantsan akan kada wani kamshi ya saɓa dana abincinsa idan za su kai mashi abincin, haka zalika bodyguards suma suna taka tsantsan sosai wajen gani babu wani kamshi a tattare da su idan za su zuba mashi abinci, abin da suke wanke mashi kwanikansa ma abu ne na daban, Lion yana da bala'in tsarine a rayuwarsa wadda duk wanda zai zauna da shi to sai ya kai zuciyarsa nesa kamar nisan sama da kasa kafin ya iya zama da shi.
Jiki ba kwari zuciyarta sai bugawa yake yi, haka ta hakura ta yunkura zata miƙe, ɗan riƙota ya yi ya shiga kara mata karfin gwiwa akan zata iya kada ta sare. Bai kyaleta ta tafiba sai da ya ji ta sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya alamar ta samu kwarin gwiwa kenan, sannan ya kyaleta ta fito ta nufi Kitchen.
Mark ta samu a kitchen É—in ya gama haÉ—a abincin Lion yana haÉ—a na Areef da na Imran, sannu ta yi mashi, bai amsa ba kuma ita ma bata damu ba domin dama ba wani son yi mashi magana take yi ba.
Wucewa ta yi zata É—auki abincin, wani irin tsawa ya daka mata wadda ya sanyata dafe saitin zuciyarta take yi mata barazanar faso kirjinta ya fito waje tsabar bugawa da yake yi da karfi karfi.
"Ke mahaukaciyar ina ce da zaki É—auki abincin oga ba tare da kin wanke hannayenki ba? So kike yi ki ja mani wata bala'in ko? Idan baki matsa mani a nan kin je kin wanke hannunki ba sai na É—auke ki da marin da sai ya sanya ki ganin mutuwa ido da ido!!".
Duk wannan magana da Mark yake yi bai fa juyo in da take ba bare ya kalleta, ta wutsiyar idanunsa ya kalli zata É—auki abincin, shi haka Allah ya yi shi, kusan irin Lion yake, idan yana abu baya É—auke kallonsa a kan abin da yake yi, baya da yawan magana kullum gum kamar kurma, kamar dai ogan nasa, haka zalika baya shiga shirgin kowa, aikin gabansa kawai yake yi, sai dai idan kai ne ka shigo gonarsa, sannan ne fa zaka yabawa aya zaÆ™, idan baku manta ba na gaya maku Mark renon Romeo ne, to fa shima sai a hankali kusan irin ogan nasa ne, sai dai ko rabin ogan bai kai ba a iya tsari, izza, izaya, ka'ida, da nuna isa akan koma waye.
Wucewa ta yi ta je ta wanke hannunta fes, sannan ta dawo ta É—auki abincin, yau ma da kyar kamar zata faÉ—in saboda nauyin tray É—in, Allah sarki bata saba ba. Ba'a kayan abincin jiya aka zuba mashi abinci ba, wasu sabbine launin sky blue, kayan abincin jiya ma a É—akinta ta barsu Imran ne ya fitar da su, kuma da ya fitar zai mayar Kitchen É—in sai ya manta ya barsu a saman table na palon sama.
Tun da ta doshi kofar É—akinsa gabanta ya kara tsananta bugun da yake yi, ziciyarta tamkar zata fito waje saboda tsoro.
Sallama ta yi mashi a bakin kofar ɗakinsa, kamar dai jiya shiru bai amsa ba, yana zaune saman sofa set dake a cikin ɗakin, ya yi shiru yana latsa wayarsa, jikinsa na sanye da three quarter launin Ash color, daga ta sama kuma yau army t-shirt ne a jikinsa, ba ƙaramin kyau ya yi wa kayan ba, ya saki dark black curly hair ɗin nan nasa har kafaɗarsa, kamar dai kullun sai tashin fitinannen kamshi yake yi, da alama kuma yau sarautar tasa ma ta fi ko yaushe, da alama dai akwai abin da ya faru, ko a gidansu na Washington DC ko kuma a wajen aikinsu, domin ya sanya a rufe mashi TGA a cikin ɗaki na tsawon kwanaki ana hora shi, dan Tga ya shiga gonarsa sosai a ƴan kwanakin, to yau da safe ya sanya a fitar masa da Tga ɗin domin dole ko da yana cikin rashin lafiya na horon da ya sha dole ya jagoranci tawagar da za su dimfari G.M.A jibi Friday, sannan ya sanya sojojinsa zarata mada katti guda biyu a kofar gidan Josephine akan su tsareta ko nan da kasuwa bai yarda ta je ba, da yake tasan halin ɗan nata, sai bata yi gardama da sojojin nasa ba, ta hakura ta zauna a gida, dan ta san ba ƙaramin aikin sa bane ma ya sanya a ɗaureta da sarka, kuma dole ta ɗauru tun da ta riga da ta zubar da girmanta na uwa a idanunsu, hakan yasa kawai ta hakura take bin ɗan nata sau da kafa kamar rakumi da akala.
(Kai gaskiya Lion duniya ne, anya akwai biyunka kuwa? Yanzu duk wannan bala'i da zafin rai na Josephine ka sanyata natsuwa bata shirya ba, shiru kake jin Josephine, kada ku mance labarinta da daddy ya bada lokacin da suke school, kunga kuwa mafaÉ—aciya ce sosai tun da har ta iya marin William a lokacin, sannan duk tsagerancin da Dangerous Boss wato William ya yi amma Lion ya nitsar da shi yanzu kamar ba dangerous Boss ba, Allah ku yarda da maganata, Lion É—an duniya ne na bugawa a jarida, ko da yake hakan ma ya fi tun da su suka riga da suka zubar da girmansu na matsayin iyaye a idanun yaran nasu, kuma dama mafi yawa kun san turawa haka suke da Æ´aÆ´ansu, wasu ma Æ´aÆ´an suke komawa iyayen suna bawa iyayen nasu umarnin tare da controlling É—insu, bare kuma abu ya haÉ—u da Kristanci, ai sai dai muce Allah dai yasa mu dace)
STORY
Da yake jiya taga bai amsa mata sallamarta ba, sai ta yi tunanin yau ma bari kawai ta shiga É—akin nasa kai tsaye.
Wani irin sanyi ta ji ya ratsa dukkannin ilahirin jikinta lokacin da ta sako kafarta a cikin ɗakin, ko'ina na ɗakin fes saboda Imran ya zo ya gyara mashi tun kafin ta tashi barci, da alama kuma sai ya hukunta ta na tsallake aikinta da ta yi na gyaran ɗakin nasa, domin time da Imran ya gyara ɗakin baya nan yana cikin toilet, da ya fito kuma sai da ya ce da Imran ɗin aikinsa ne da zai yi, kunga kenan zata karɓi hukunci domin duk abin da ya yi magana akai to ta shafe shi ne.
Yau daki kallon in da yake dan tana tsoron ya kamata tana kallonsa tun da baya son kallo, kuma da yake ya haÉ—u ne ma da yau yana saman sofa ne suna kusa, dan sofar kusa da carpet É—in da take ajiye abincin, shi ne ma ya kara sawa taki kallon nasa.
Tazo daidai zata wuce shi ta je ta ajiye mashi abincin ne, ya daka mata ƴar tsawa na cewa ya ce mata yana da buƙatar abinci ne, ko an gaya mata ana kawo mashi abin da bai bukata bane?.
Wannan tsawa da ya yi mata ne ya yi sanadiyar mugun tsoratata da har ta saki tray É—in abincin ya faÉ—i kasa komai na ciki ya tarwatse. BABBAR MAGANA.
Gaba ɗaya fruits dake a ciki sun watse, wani apple ne ya yi tsalle ya dake shi a kirjinsa kafin ya dawo ya bugi screen ɗin wayar hannunsa, da yake ba wani riƙe wayar ya yi sosai ba sai wayar ta faɗi kasa a saman carpet dake tsakiyar set ɗin.
Gaba ɗaya abincin sun zube kaza gudarta tana kwance mashi a tsakiyar ɗaki, ga shi jikin kazar duk kayan haɗi da akayi baking nata da shi. Tiles nasa fari tas sai kyalli yake yi duk ya ɓaci jaga jaga da miya.
Jikinta wani irin mugun kerma yake yi, ta kasa tsayawa akan kafafunta a in da ta durkushe a wajen domin tasan ba makawa zata hukuntu ba kaɗan ba, jiya ma da ba wani abin ta yi mashi ba ya azabtar da ita har haka, ina ga kuma yau da ta ɓata mashi ko ina na ɗaki, bayan haka kuma ta sanya apple ya dake shi a kirji sannan ya patale mashi wayar dake a hannunsa, ya ilahi ya lillahi, ita wlh ko da faɗuwar gaba da tsinkewar da zuciyarta keyi tare da bugawa ma kawai ya isa ya kasheta ba tare da wani hukunci nasa ba. Shi ne ta gudu ne ko ta tsaya? Idan ta gudu ma ina zata je a duniyar nan ta tsirawa hukuncinsa? Ya ilahi ya lalliahi!..
A zafafe ya É—ago kansa ya.................
Alhadulillah Alhadulillah Alhadulillah, Allah na gode maka da ka bani iko da dama na kammala book 2 na wannan littafin, kuskuren dake a ciki Allah ka ya fe mana, gyaran dake a ciki kuma Allah kasa mu yi amfani da shi, Allah ka ba mu dace wa, nan na kawo karshen book 2 sai mun haɗu a book 3 idan Allah ya kai mu nan ba da jimawa ba dan jin yadda wannan cakwakiya zata warware. Keep praying for me My people's, one love 💗 💘
SSG Palace Gujungu