Best Hausa Novels

Triplets Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: TRIPLETS BOOK 2.txt

Chapter 6 of 8

Cigaba da magana Areef ya yi "Me yasa kike saka irin wannan manyan kaya haka? Ga shi sai zufa kike yi" ya yi maganar yana nuna hijabin jininta.

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe, cikin muryar kuka ta ce "Haka muke yi a nan Nigeria, a kasar ku ne ko musulma sai dai ka ganta ba ɗan kwali bare hijabi, masu imani sosai ne sai kaga sun saka ɗan karamin hijabi, mu kam a nan har kasa muke saka wa mu rufe jikin mu".

Jinjina kai ya yi yana faɗin "Good, amma dai ya kama ku rinƙa sassautawa kanku dan wannan wahala ne ai" Shiru ta yi tana ɗan ɗari ɗarin amsar da zata bashi kada ya ɓata mashi rai, amma da ta tuna gaskiya ce zata faɗa, daga ƙinta kuma sai ɓata, sai ta daure ta ce "A'a Yaya Areef, wannan shiga ita ce daidai, ita ce annabi Muhammad (S.A.W) ya koya mana, gaba ɗaya jikin mace al aura ce, ya kamata ta rufe ko'ina nata, iya fuska kawai aka yarda ta bari a buɗe, shima ai kaga akwai dalili mai karfi, wannan shiga tamu ta nan shine shigar musulci, annabi ya ce mace ta sanya dogon hijabi, ta baya yana taɓa kasa, ta gaba kuma, ya kai idon sahu".

Sosai ya ji daÉ—in bayanan ta, kuma shi kanshi shigar tata ba karamin burgeshi ta yi ba, kawai dai dan ya ga tana haÉ—a zubane yasa ya yi mata magana, zufar kuma ta samo asaline saboda kukan da ta yi.

Sakin hannun nata ya yi yana faɗin "Ki yi mani addu'a na sami lafiya muje ki raka ni yawo a sassan kasar ku, dan ina son yawace koina da ina kafin mu koma kasar mu, ina son ganin kasar nan taku sosai, dan a yan kwana biyu da na yi a freedom nan, ba ƙaramin daɗin garin na ji ba".

Zata yi magana kenan Imran ya shigo bakinsa ɗauke da sallama yana ruƙe da wayar Lion a hannunsa, sai mirmishi yake yi yana kallon screen ɗin wayar, da alama video call yake yi da wani.

Kusa da Areef ya zo ya zauna tare da miƙa mashi wayar yana faɗin "Aseef want to see your face". Fuska ba ya bo ba fallasa ya karɓi wayar.

Wani irin kayatatcen Mirmishi ne ya bayyana akan face nasa lokacin da ya kawo wayar sai tin face nasa. Ba komai ne ya sanya shi wannan murmushi ba face ganin Aseef da ya yi zaune cikin library ga takardu a gabansa, da alama karatu yake yi tukuru, shima cool murmushi ne É—auke a saman face nasa.

"My blood Nigeria ya yi maka daÉ—i ko?" Aseef (Michael) ya tambaya. GyaÉ—a mashi kai Areef ya yi kafin ya ce "Over my blood over, idan akwai abin da ya fi over ma to shine, I really like Nigeria and Nigerians, they are good people's sosai".

Shiru Aseef ya É—an yi kafin ya ce "Okey i will join you In Sha Allah, but not now, I have exams next month, if am done, i will try to join you, am not happy at all, All of you kun tafi Nigeria kun barni, dan ma am together with uncle Musharraf yana É—ebe mani kewa, if not da kewa ya yi mani yawa sosai, a really missed guys".

Zuba mashi ido Areef ya yi na yan mintoci kafin ya ce "What is wrong with you?" Kara faÉ—aÉ—a mirmishi kan face nasa ya yi yana faÉ—in "Nothing blood".

"Am I your mate? Am i playing with you? I said what is wrong with you?" Ya yi maganar yana É—aure fuska sosai.

Cikin dariya Aseef ya ce "You're my mate and you're playing with me, what is next?"

Dafe kai Areef ya yi Aseef ya san takan tsiya, idan ya bi shi da karfi ba zai gaya mashi me yake damun shi ba, ga kuma damuwa karara akan face nasa bawan Allah, dan haka sai ya ajiye duk wata zafa ya fara yi mashi magana kamar sa'annin juna, suka koma TRIPLETS ɗin kawai, tun da ya ga yanzu Aseef ɗin ya warke garau tamkar bai taɓa yin ciwo ba, yanzu dole su goga kafaɗa.

"My blood you knew i really love you, and you knew am worried about you? Please tell me what is wrong with you, if not you will put me in to bad mood"

Yar dariya Aseef ya yi kafin kuma ya ɗaure fuska sosai, nan take yanayin sa ya sauya, yanzu dai cike da shagwaɓa ya fara magana "My James Uncle T ne yake bawa uncle Musharraf wahala, everyday idan na tafi school, before na dawo sai ya bashi horon sojoji, idan na tambayi uncle Musharraf ɗin what is happened to him sometimes nake ganin face nashi da kuma bodynsa somehow, sai ya ce mani nothing, kuma i knew there is something behind between him and uncle T dan na taɓa kama shi yana sanya uncle Musharraf ɗaga gun Ak, kuma tana cike da bullet sosai, ranar har ciwo sai da hannun uncle Musharraf ya yi, ina son gaya wa Lion amma bana son wata matsala ta faru a gidan kuma, kasan Lion zai bawa uncle T punishment mai tsanani, hakan kuma zai ɗaga wa daddy hankali, ina da tabbacin Lion yana busy this two days ɗin nan, i think that is the reason why baya bincinkan camarorin gida, da kuma abin da yake faruwa Kum......."

Bai kai karshen ba Areef ya dakatar da shi cikin tsawa "What uncle did to Uncle T da har yake ba shi horon sojoji Kuma?". "My blood you already knew that gaba É—aya yan gida they hate Muslim people's, so the reason why uncle T ke azabtar da shi kenan, because he is a Muslim".

Rai a matukar ɓace Areef ya ce "Ya zama dole uncle T ya karɓi hukuncin zalincin da yake yi, before na tafi sai da nace mashi ya sauƙe wannan rawanin zalinci dake a kansan nan ya ajiye, amma yaki, yanzu dai zan gayawa Lion please ya sanya a kawo mani uncle na nan kasar, idan na sami lafiya sai mu koma tare, in na dawo Allah sai na sanya uncle T ya kwance wannan rawanin zalinci dake a kansa ya ajiye...."

"My blood why zaka raba ni da uncle Musharraf, you know shi kaÉ—ai nake gani yake rage mani kewar ku fa". Girgiza kai ya yi yana faÉ—in "No Aseef ya zama dole na É—auki uncle, ko so kake na barshi uncle T ya cigaba da wahalar da shi ne?" Girgiza kai ya yi alamar a'a. "To ka gani, idan ka gama Exam ai kai ma zaka bi yo mu sai mu koma a tare, so kada ka damu, ka mai da hankali sosai akan karatu."

To Aseef (Michael) ya amsa da shi, daga nan suka cigaba da hira, sosai Areef ya bashi labarin Rimsha bai ɓoye mashi komai ba, dan dama haka suke, da James da Michael sirrin su kusan ɗaya ne, abin da ɗaya ya sani da wuya ka ji ɗaya bai sani ba.

Wani irin daɗi Aseef ya ji ya ce sam Areef sai ya nuna mashi a ina Rimsha ɗin take, ai kuwa bai hana shi ganin ta ba, da hannu ya yi mata alama da ta dawo gefensa ta saman pillow da yake kwance su yi magana da ɗan uwan shi, ba musu ta miƙe ta je.

Ba ƙaramin farinciki Michael ya ji ba, da alama ma ya fi Areef murna, dan har da dariya ne akan face nasa ba iya mirmishi ba.

Ita ta fara ce mashi good morning, sai daÉ—i yake ji, ga fara'a palala a face nasa, ya amsa mata gaisuwar tare da tambayar ya take, lafiya ta amsa mashi da shi, "My Name is Aseef what of you?" Farinciki yasa bakinta ya ki rufuwa "My name is Rimsha" ta bashi amsa.

"Wow Rimsha nice name, cos the way am seeing your face like you are under 15 years" Ya yi maganar yana tsareta da wayan nan brown eyes ɗin nasa, ba ƙaramin mamaki Imran ya sha ba, dan ya san halin Michael sarai lokacin da suke school, amma ya akayi yau yake magana da Rimsha haka? Abin da bai sani ba shine ƙwaƙwalwar Michael ta da da ta yanzu ba ɗaya hace, da kamar ma za'a ce ba shi bane, yanzu kuwa shine, cikakken mutun mai imani da natsuwa, yanzu ne ainahin wanene shi ta bayyana.

"Yah Yaya Aseef am under 15 years, am 14 by age" Shiru ya yi yana tunanin shekarun Lion da nata shekarun, anya kuwa hakan zata yi wu kuwa? Ya tambayi kansa, Areef ne ya katse shi da cewa "What are you thinking?".

Ɗaga kai sama ya yi tare da juya manyan idanun nan nasa, kai a ɗage ya dawo da kallonsa kan Areef ɗin, ya kashe mashi ido ɗaya tare da ɗaga gera ɗaya kamar wasu munafukai, Areef bai san time da dariya ta suɓuce mashi ba, dan ya gano hanyar da Aseef yake, wato idan Allah ya ƙaddara abin da suke fata, na Lion ya yarda ya auri Rimsha zuwa ɗaya zai yi mata ba dawo sai dai a ɗauki gawarta, wato ta yi mashi karama, hakan yasa Areef satar kallon ta, ita kam ba abun da ta gane, tama yi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.

Dawo da kallonsa kan Aseef É—in ya yi har lokacin yana É—age da kai sama yayin da idanunsa kuma suke a gefe yana kallon Areef É—in, da larabci Areef É—in ya fara magana bai san cewa Rimsha tana jin larabci ba, ba kuma ya son ta ji abin da suke cewa ne, shi James yana jin yaren china amma Michael baya ji, larabcin ma James É—in ya mance ne Michael baya ji, sai yana yi mashi kamar tare suka koyi komai.

"Kai Areef baka da kirki, me yasa zaka yi wannan tunani, ai zata girma...." Bai karisa maganar ba Aseef ya dakatar da shi da cewa "Which kind of language is this?".

Shafa fuskarsa ya yi sai lokacin ya tuna ashe Aseef fa yanzu yake koyan karatu, hakan yasa ya dawo magana da English ɗin kawai, tun duk wani baƙon yaren da yake ji Aseef baya ji sai English.

"My blood tayi ko? Kana ganin ta dace da Lion?" Cikin sauri Aseef ya jinjina kai yana faɗin "Yah sosai ma, saboda shi is so beautiful and she have innocent face, the way am looking at her like she is so silent, zata iya hakuri da mu, you knew yanzu wadda zata iya hakuri da mu ne muke buƙata, but seriously i pity her more than your expectations, saboda magana ta gaskiya you knew mu da muke TRIPLETS nasa ma, bamu taɓa gane ina ya dosa, kullun a murɗe yake, yana cikin gindayar da mutane, duk duniya ba wanda yake iya cankan ga abin da zai yi ko wanda ba zai yi ba, sai kana zaton shi a nan sai ka ga ya ma wuce nan, to be honest zata sha bakar wuya, ni for my on bana ji a jikina Lion zai bari ta zauna kusa da shi ma, bana jin wannan abin zai yi wu, amma anywhere shawarar da zan baku dai a nan ita ce, kada ku sanya yarinyar nan ta je kusa da shi ya yi mata kisan farat ɗaya, ku ɗauki alhakinta banza, wlh ni na sani idan ba wani kwakwaran dalili, kai in jin ko harbina da bindiga aka zo yi ta tare mani Lion ba zai barta a kusa da shi ba, ba zai yarda da ita ba, ko me zata yi mashi, amma zan taya ku thinking na wani solution ɗin wata kila mu dace, kuma ku yi tunani mai zurfi kada ku zo ku yi dana sani, for my on choice yarinyar ta yi sosai" dawo da kallonsa kanta daga kan Areef ya yi ya cigaba da cewa "My sister kin dai ji abin da na faɗa, iya gaskiya na gaya, ni bana karya, so is better for you ki iya takunki, ki ɗauki action mai kyau, dan bana son mu rasa wannan innocent face ɗin naki, ina ga ko daddy bai yi wa Lion irin sanin da ni na yi mashi ba, saboda ni nafi zama tare da shi, ko Areef ba zai gaya mani asalin wanene shi ba, duk da cewa nima ban san shi ciki da waje ba, dan ba komai zaka iya ganewa a tattare da shi ba, amma na san abubuwa da dama shiyasa kika ji na faɗi haka, so ki kula, idan da son samu ne ma, ki yi zaman ki sai na zo Nigeria sai mu san abin yi".

Areef ne ya tari numfashinsa da cewa "Yah Aseef abin da ka faɗa dukka gaskiya ce, ni kaina da abayane kace mani zan iya zama da mace haka mu yi hira, wlh zan ce karya ne kuma never in my life, so amma musulci ba wasa ba, In Sha Allah Lion zai so ta, ya yi aure muma mu yi aure, mu cika addininmu, amma na san ba nan kusa bane, yanzu ma abin da muke so ai ba zai ko kusan samuwa ba, shiyasa nace mata kada ta bari hanya ya rinƙa haɗa su, ta bari sai na sami lafiya, idan na sami lafiya shikenan, zan iya shiga ɗakin sa na kwanta kuma na kirata ta kawo mani abu, ko ta zo kuma ba zai ce komai ba, saboda kasan baya shiga abin da bata shafe shi ba, idan muna tare zan iya kiranta ba zai yi magana ba, amma yanzu dai bari na sami lafiya first".

Jinjina kai Aseef ya yi yana faÉ—in "Shawara mai kyau, hakan ma ya yi, kuma dama shiyasa nace ta bari sai nazo Nigeria, Lion baya kallon mutane da abubuwa, abin da yake gabansa kawai yake yi, amma ina da tabbacin idan tana yawan zama kusa da mu, wata rana dole zai so ganinta, kuma dole zai samu kwanciyar hankali a tattare da kasancewar a gidan, saboda idan ya ga muna tare da ita, zai ce e lallai tana da kirki, kuma zai so sanin wace ce ita da har muke tare da ita haka, zai yi bincike a kanta ko da bai gaya mana ba, kuma ina fatan daga nan shima zuciyarsa zata aminta da ita".

Jinjina kai shima Areef ya yi alamar gaskiya Aseef ya faÉ—a.

Kada ku mance duk wannan magana da suke yi, suna yi wa Rimsha kallon a matsayin kanwar Imran uwa É—aya uba É—aya ne fa, to ya kenan idan suka ji cewa shima Imran tsintota ya yi? Ba abin da ya haÉ—a su kuma bai san ina Æ´an uwanta suke ba, kuna tunanin za su yarda da ita kenan? Kuna tunanin za su bari É—an uwansu ya aure ta? Saboda fa kirkin Imran yasa suke sonta, dan kun ji sunce Imran mutumin kirki ne, suna son shi fiye da tunanin mai tunani, a cewarsu dukka family Imran mutanen kirki ne kamar shi, BABBAR MAGANA.

Miƙewa Imran ya yi ya nufi waje dan Akil ya kira shi yana kofar gida ya kawo kayan Rimsha.

Bayan ya karɓo ya dawo ne ya zo ya ce mata ta tashi ta je ta shirya zuwa school, to ta amsa mashi da shi, tare da yi wa Areef sallama da fatan samun lafiya sannan ta wuce ta barshi suna hira da Aseef nasa.

A gurguje ta yi wanka ta shirya cikin abaya blue color tare da hijabi ba mayafin rigar ba, time ya tafi almost 8:5 yanzu, sun zauna hira da su Areef, Imran ma bedroom nasa ya wuce dan ya yi wanka ya shirya ya zo ya kaita school.

Bayan ta gama shiri ne ta fito palo, wani irin nishaÉ—i ta ji lokacin da hancinta ya shako mata daddaÉ—ar kamshin perfume nasa, da alama ya wuce a palon, zama saman sofa ta yi tana rataye da hannu É—aya na school bag É—in ta a kafaÉ—a, ga hijabinta har kasa launin blue kalar rigarta, ta yi kyau sosai, ba wani make up ko kaÉ—an a face nata, soft skin É—in nan nata sai wani sheki yake yi, colan skin É—in nata ya kara fitowa sosai, sai wani murmushi take yi ita kaÉ—ai zaune shiru, idan ta tuna maganganun Aseef in da yake cewa mawuyacin abune Lion ya barta ta matso kusa da shi, sai ta ji gabanta na faÉ—u wa, me yasa kowa a cikin shawarar da zai bata sai ya ce mata kada ta haÉ—a hanya da shi? Ta tambayi kanta a cikin zuciyarta.

Bata kai ga samin amsar tambayar ba Imran ya fito yana faÉ—in "Let's go". Shirye yake cikin manyan kaya na wani haÉ—aÉ—en yadi mai kyau coffee colar, kayan sun mashi kyau sosai, shima yana da kyakkyawar saje irin na daddyn Jelly, daga wajen bakinsa kuma akwai kewayayyen gashi mai kyau sosai a wajen, kamar dai daddyn Jelly.

Gaba ya yi ta bi bayansa, a palon kasa suka hango Lion saman dining table yana latsa laptop ga kuma kayan abinci a gabansa, amma bai fara ci ba, sojan dake yi masu girki ne tsaye akansa yana jiran umarni kawai ya zuba mashi abincin. Shirye yake cikin wasu shegun tsadaddun kaya, wandon jeans ne ask color mai bala'in kyau, daga ta sama kuma high neck t-shirt ne white color, rigar ta kama jikinsa sosai hakan yasa kakkarfar surar jikinsa daga ta sama ta bayyana, ya É—aure kyakkyawar gashin kan nan nasa a baya, kamar dai kullun wannan guntu na gaban goshin nasa yana nan, while face nasa na sanye da black glass mai bala'in kyau, idan kaga lips É—in nan nasa, sai ka rantse da Allah yasa lips stick, har wani kyalli suke yi saboda yana É—an ciza su time to time, gaba É—aya kamshin perfume nasa ne ya gauraye gaba É—aya cikin palon.

Rimsha da aka ce kar tana yawan kallonsa, amma ta kasa É—auke idanunta daga kanshi, sai kallonsa take yi sosai, ji take tamkar ace ya zama nata, shi kuwa yana fuskartar gefe bai ma san suna yi ba, ya dai san mutane sun shigo palon, amma bai nemi sanin koma su waye bane.

Kasa kasa Imra ya ce mata ta je ta yi sallama da Areef yana zuwa bari su yi magana da Lion, to ta amsa mashi da shi sannan ya nufi ɗakin Areef ɗin, tana tafiya tana waigo Lion, ba ƙaramin tafiya da imanin ta ya kara yi ba, ya ruɗa mata kwakwalwa yau ɗin nan sosai da sosai.

Tana shiga ta sami Areef ya gama magana da Aseef yana latse latse a wayar Lion É—in, daga É—an gefa ta tsaya tana gaya mashi zata tafi school, dawo da kallonsa kanta ya yi kafin ya ce "Okey waye zai kai ki?" "Yaya Imran" ta bashi amsa.

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Idan ya kai ki dawowa yake yi ko?" Jinjina mashi kai ta yi alamar e, girgiza kai ya yi kafin ya ce "Haka ba zai yi wu ba gaskiya, dole ki samu tsaro sosai, saboda yanzu ke ba kamar sauran mata bane, nasan ba za'a rasa maza masu karan kwana da zaku yi maki magana ba, ni bana son haka, komai namu saboda ne wadda mu kaɗai muke fara amfani da shi, dan haka Lion ma sabuwar mace za mu sama mashi wadda ba wanda ya isa ko da sunan wasa ya yi gigin yunkurin tinkarar ta bare ma har ya ce yana sonta, bari Prof ya zo, sojan dake bakin gate ya kai ki school, Prof ya je ya nuna mashi school ɗin, kuma ya yi gadin ki sai an tashi ya dawo da ke, zan gayawa Lion ya karo wasu sojojin guda biyu wadda za su rinƙa tsaron bakin gate ɗin, daga yau wancan ya zama mai tsaron ki, kuma nasan a wannan gaɓar Lion zai yarda, domin ya sani cewa duk wanda yake tare da mu, idan bamu ba shi tsaro ba mun ɗauki alhakinsa, kuma ma yasan wannan dokar mu ce, kuddin mutun yana a karkashin mu to yana cikin tsaro".

To ta amsa mashi da shi tare da yi mashi godiya. Tana rufe baki sai ga Imran ya shigo bakinsa É—auke da sallama.

Kusan a tare ita da Areef suka amsa sallamar, kamar yadda ya gayawa Rimsha haka ya gayawa Imran, haka kuwa akayi, da sojan suka tafi, sai bayan sun tafi ne da Lion ya shigo karɓar wayarsa a hannun Areef ɗin, a nan ne yake sanar da Lion alfarman da yake nema, yana son abar wancan sojan ya rinƙa bawa sister Imran tsaro, shiru Lion ya yi bai yi magana ba, har ya gama abin da zai yi, zai fita ne sai ya ce "Idan sojan ya dawo ka sanar da shi nan da leƙa waje ban yarda ya sake yi ba, nan ba kasar su Prof bane? Before sister tasa ta zo nan waye ya ke bata tsaro? Ko a ƙarƙashin mu take ne? Idan ka sake yi mani irin wannan ranka zai ɓaci, ai ba a karkashin mu suke ba bare mu basu tsaro" Ya kai karshen maganar tare da ficewa abinsa.

Sai lokacin Areef ya tuna ashe ba kasar su ba ne, kuma ashe basu cike takardan zama a karkashin su ba, tunani ya fara yi ta yadda zai samawa Rimsha wannan takarda ta cike, idan ta cike shikenan tana karkashin kulawar Lion, ba zai bari wani abin ya same ta ba, addu'a ya fara yi Allah yasa Lion ya zo da takardan, idan ya zo da takardan wlh sai ya É—auko mata ta sanya hannu ko me zai faru, lokaci guda kuma wani tunani ya faÉ—o mashi, ina maman su Prof take da har ta bar sister Prof a nan, da ya ke kuma su yin hakan ma ba wani abu bane a wajen su, sai bai wani damu ba, bai kuma kawo komai a ransa ba, ya san su a wajen su ma yarinya tana iya barin gidan iyayen ta koma gidan saurayinta ta zauna, kuma iyayen suna gani ba wani action da za su É—auka akan hakan.

Tunani cike fal ransa har barci ya yi awon gaba da shi.

Imran kuwa suna fita sai da suka sayawa Rimsha abin da zata yi breakfast da shi, sannan ya bata 1k lokaci ya kure sun zauna hira da Areef bata yi girki abin da zata ci ba, tun da bata iya cin nasu ba.

Bayan sun je school É—in Imran ya dawo ya barsu ita da wannan sojan a school É—in, kowa sai kallonta yake yi, kowa yana son sanin wace ce ita, da soja yake gadin ta, sojan ma kuma Bature ga shi fari tas da shi kyakkyawa mai kirar jarumai, daga student har malamai sai kallonsu suke yi.

Da lokacin shiga class ya yi, har cikin class É—in sojan ya shiga, ya zauna a kujeran da malami yake zama yana fuskartar É—aliban, fuskar nan tasa babu alamar wasa ko kaÉ—an, shiyasa gaba É—aya É—aliban suka razana, class É—in ya yi tsit tamkar babu kowa, ga Rimsha yar firitu agab shi, dan bata kai kirjinsa tsawo ba, da kaÉ—an ta É—ara cikinsa tsawo, amma a haka yake bata tsaro, duk in da ta je yana biye da ita, kai Allah ka bamu arziki mai albarka.

A ɓangaren su Ayla kuwa, yau zata fara zuwa school, sosai mijinta ya shirya ta, kamar yadda yake shirya jelly ta tafi school haka ya shirya ta ita ma, ta yi kyau sosai, shima ya shirya cikin wata haɗaɗɗiyar yadi ash color, ya yi mashi kyau sosai da yake yana da haske.

Da farko ma cewa ya yi shi zai yi mata girki tayi breakfast, dan akwai kitchen a part É—in nasu, amma sai Aunty ta rigashi ta aiko masu da abinci, ba dan ya so ba, ya zuba mata girkin Auntyn tayi breakfast sannan suka fito suka nufi cikin gida, sun jero kamar wasu taurari.

A bakin kofar shiga palon su Abbi suka yi karo da Irfan yana fitowa, har wani faɗuwar gaba ya ji ganin su da ya yi a tare, bawan Allah har yar rama ya yi, kakalo mirmishi dole ya yi tare da miƙawa daddy hannu yana faɗin "Barka da safiya bappa".

Da fara'a daddy ya miƙa mashi hannu yana faɗin "Irfan baka da lafiya ne?" Girgiza kai ya yi kafin ya ce "A'a bappa lafiya ta lou, yanzu shiga na ciki ma sai da Sadiya ta tambaye ni ko bani da lafiya ne, wai me kuka gani kuke tambaya tane?".

Ayla ce ta caɓe zancen da cewa "Yaya Irfan ka rame ne mana, ina kwana?" Dogon numfashi ya ja tare da sauke wa a hankali kafin ya ce "Lafiya lou Aliya kin tashi lafiya?".

Lafiya ta amsa mashi da shi, sai wani kauce masu yake yi, baya son ganin fuskar Ayla, shi kuma daddyn jelly ya tsai da shi akan lallai sai ya gaya mashi menene yake damun sa, kafewa ya yi akan lallai shi ba abin da ke damun sa, haka suka hakura suka kyale shi ya wuce su kuma suka shige cikin palon.

Zaune suka isko Aunty saman dining table, cikin zolaya daddy ya ce "Sadiya kina cin ye mani kuɗi sosai fa, yanzu tun ban tashi barci ba kin haye saman table kin fara ciye ciye ko? So kike yi ki ja mani wata matsala ko? Wai ba ance kada ki rinƙa cin abubuwa masu nauyi ba har sai kin kara samun sauki ko? Shine kike ta ɗurawa da sanyin safiya salon ki jamin sake mai daki asibiti na kashe kuɗi na ko?."

Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce "Kai da nake renonka É—in ne zaka yi mani wata magana? Ni fa yanzu Aunty babba ce, ka zama kanina Yaya Maik tun da ka kame mani yar kanwata ka shige da ita part naku na zama aunty babba".

Harara shima ya wurga mata da manyan idanun nan nasa yana karisawa wajen table É—in, "Ina kwana?" Ta faÉ—a tana murmushi.

"Yanzu kenan kika tuna da gaisuwar ko? To ni dai kin shirya wa matata lunch box nata ne, ko kuma in shiga kitchen da kaina?".

Kai kallonta kan Ayla dake tsaye ta sunnar da kai kasa ta yi, sai wani Æ´an kame kame take yi, "Yaya Maik yanzu ni da nake Aunty babbama ni ce zan shirya maku lunch box ko?" ÆŠaukar apple ya yi kwara É—aya ya wuce ya nufi kitchen yana faÉ—in "Da dai ban iya girkin bane da sai ayi mani rigima, amma tun da na iya matata ta wuci gori".

"Eyeee irin wannan soyayya haka? To ni dai dawo na shirya mata, ai na san yau zata je school, dan haka na shiryawa yar kanwata komai da komai, Ayla wai kame kamen me kike yi ne? Ki je kitchen ki É—auko box É—in naki mana".

To ta ce tana ƙoƙarin nufar kitchen ta jiyo voice nasa daga ciki yana faɗin "No bari na ɗauko mata da kai na, sai ma na binciki me a ciki tukun nan, dan ita ba komai zata ci ba yanzu".

Murmushin kawai Aunty ke yi ta ce da Ayla ta zo mana me ya tsai da ta a can, ba musu ta kariso wajen table É—in cike da kunya suka gaisa, cikin raha kasa kasa dan kar daddy ya ji Aunty ta ce "Ke jiya da kika wani ce mani daddy da zafi baki ji kunya ba sai yau ko? A lallai yarinyar nan". Ta kai karshen maganar tana dariya.

Ita kuma Ayla hannu tasa ta rufe fuska tana tunanin a yaushe ta ce wa Aunty daddy da zafi kuma, bata san cewa a gigin barci ta yi maganar ba.

Lunch box É—in ya É—auko ya fito yana faÉ—in "Ina yaya Deen?" "Yana barci bai tashi ba" Aunty ta bashi amsa.

Hararar ta ya yi kafin ya ce "Ke kuma har kin tashi kin haye saman table ko?" "E mana ka sani ko dalili ya sanya ni hawa saman table É—in? Kai ma fa yaya maik wlh wasa wasa ka iya sa ido".

ÆŠan zaro ido ya yi kafin ya ce "Serious fa abin da nake tunani ne ya saki cin abinci da sassafen nan? Ba likita ya ce ba zaki sake iya É—aukar ciki ba?".

Guntun tsaki ta ja tana turo baki ta ce "Da farko dai ban san me yasa nake jin yunwa safe da dare daga jiya zuwa yau ba, na biyu kuma likita bai isa ya yanke hukuncin abin da ya shafi Ubangiji ke bayarwa ba, Allah ke bada haihuwa ba wani ba, so babu likitan da ya isa ya ce ba zan haihuba ko zan haihu, wannan hurumi ne na Aarahman".

"Haka ne zancen ki gaskiya, to Allah dai yasa abin da muke tsammani ne, mu dai mun wuce sai na dawo" ya faɗa yana barin wajen table ɗin tare da riƙo hannun Ayla da ɗayar hannunsa ɗayar kuma ya ruƙe mata lunch box ɗin suka fice daga palon, da kallo Aunty ta bisu har suka fita, sai fatan Alkhari take yi masu a zuciyarta.

Yau ma kamar daren jiya, da motar Abbi suka fita, tana zaune a front seat ta kwantar da kanta tana kallon hanya.

"Me babyn daddynta take tunani ne?" Ya tambaya yana kallonta ta cikin mirror motar, dawo da kallonta kan shi ta yi tana murmushi, "Daddy kai nake tunani mana".

"Da gaske?" Ya yi maganar cike da jin daÉ—i, kuma ya yi magar daidai lokacin da ya É—auki titin makarantar tasu.

"E daddy da gaske kai nake tunani".

Cool murmushi ya saki tare da jawota jikinsa yana kara gudun motar dan su isa da wuri ya samu ya rungumeta da kyau.

A kuwa cikin ƙankanin lokaci suka isa makarantar, yana kashe motar ya rungumeta da kyau a jikinsa yana faɗin "Baby zan yi kewarki sosai wlh, yanzu sai fa karfe ɗaya zaki dawo, kai anya zan iya kuwa?". Tana daga lafe a kirjinsa ta ce "Daddy nima fa ina jin kamar ba zan iya jimawa ban ganka ba".

Wani irin daɗi ya ji burinsa ya fara cika, haƙarsa ta fara cin ma ruwa, ɗago haɓarta ya yi tare da haɗe bakinsu waje guda, nan take suka shiga bawa juna hot kiss.

Sun shagala da kiss na juna agogon dake É—aure a hannunsa ta buga mashi karfe 8 ya yi, da kyar ya iya zame bakinsa daga nata tare da sake ta yana faÉ—i "Muje na kai ki". To ta amsa da shi, kusan a tare suka fito suka nufi cikin school É—in.

Cikin Æ´an mintunan da ba su wuci goma ba ya gama komai ya fito ya shiga motarsa zuwa gida ya bar ta a school É—in, har ga Allah yana kewarta fiye da tunanin mai tunani, haka ya koma gida ya kwanta cike da damuwa.

After some hours 👌

Gidan Lion.

Bayan Rimsha ta dawo daga school, tare da sojan nan, cikin gida ta nufa kafin ta shiga bedroom nata Imran ya dakatar da ita ya ce ta shirya da wuri su je gidan babbansa su yi wa daddyn Jelly murna ya yi aure. To ta amsa da shi, cike da zumuÉ—i ta shige cikin bedroom nata.

Tsabar murna zata fita anguwa a gurguje ta yi wanka ta shirya cikin wasu riga da wando masu ɗan karen kyau, rigar pink color ce zuwa gwiwarta ya tsaya mata kamar Pakistan, yayin da wandon kuma ya kasance fari tas mai stones a jiki, wandon dai pencil Jeans ne, while shi kuma rigar yana da ɗan faɗi daga ta kasa, da ta saman shi kuma ya kamata, gyalen kayan fari ne tas kalar wando, light make up ta yi ta gyara gashin kanta tare da ɗaure shi a tsakiyar kanta, sai tashin kamshi take yi, zubawa hannunta ido ta yi tana kallon yadda lallen hannun nata ya rage baki yake ƙoƙarin gogewa, da yake tana taɓa ruwa sosai, tunani ta fara yi dole yau ko gobe ta ce yaya Imran ya kai ta ayi mata wani. RIMSHA SARKIN SON LALLE DA GYARAN JIKI

Da wannan tunani ta É—auko farin hijabi daga cikin trolleynta ta fito Palon.

Babu kowa a palon, haka kawai ta ji cewa tana son ganin ɗakin Lion ɗin nan, ba ko tsoro ta lallaɓa izuwa bakin kofar ɗakin, bata kai ga leƙawa ba ta ji motsin Imran yana ƙoƙarin fitowa daga nasa ɗakin, da yake kusa ne hakan yasa ta ji motsin nasa.

A sukawane ta gudu ta koma saman sofa tana sauke ajiyar zuciya, Malika ce ta bayyana a gefenta tana faɗin "Ke Rimsha bakya jin magana ko? Wlh da kin leƙa ɗakin nan da yau kun yi ido huɗu da shi, domin kuwa yana zaune yana fuskantar kofar shigowa, da kuma hakan ta faru..." Bata kai ga karisa maganar ba ta ɓace abinta, dan ta isar da saƙon da take son isarwa, kuma ba sai ta karisawa Rimsha abin da zai iya faruwa ba idan da ta leƙa ɗakin, ta sani ita da kanta. Tana ɓacewa kuma Rimsha ta fara jiyo muryan Imran dake tsaye a ƙanta yana faɗin "Muje mana ina ta yi maki magana kin yi shiru".

Yar firgita ta yi tare da miƙewa tsaye tana faɗin "Kayi hakuri yaya Imran". Ba komai ya ce mata tare da wucewa gaba ta bi bayansa.

Ɗakin Areef suka fara shiga, yana zaune ya jingina da jikin headboard na gadon, yau ya sha wanka, har wani kyau ya kara, hasken fatarsa ta kara bayyana, yana sanye da singlet fara tas da shot, sai dai ya jawo bargo ya rufe cinyoyin sa, ba ƙaramin razana da kallon kyakkyawar surar jikinsa Rimsha ta yi ba (ni ko na ce dan ma baki ga na Lion ba, ai da sai suma!) Ta razana sosai, har wani kerma jikinta yake yi, shi kuwa zuba masu ido ya yi yana kare mata kallo, dan ɗazun yana kwance bai kalleta sosai ba.

A cikin zuciyarsa ya ce kai ashe karama ce sosai, tab akwai aiki a gabansu. Gefensa Imran ya zauna yana tambayar shi ya jiki, da sauki ya amsa, ita ma ta gai da shi, fuska ba ya bo ba fallasa ya amsa.

Sanar mashi da in da za su je Imran ya yi, shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Da ina da lafiya ai da munje tare" murmushi Imran ya yi ya ce "Ba komai idan ka samu lafiya zamu je, zai kai ka wajen dukka yan uwana" Sosai ya ji daɗi dan ba ƙaramin so yake yi wa Imran da ƴan uwansa ba, duk da bai san kowa daga cikin su ba, daga Imran ɗin sai Rimsha da yake yi wa ganin kanwar Imran ɗin ce, amma duk da bai san su ba, yana bala'in kaunar su sosai.

Sallama suka yi, suna yi mashi Allah ya kara sauki, shi kuma yana yi masu adawo lafiya, da haka suka wuce.

Da motar Imran ɗin suka tafi, a hanyane ya ce mata "Rimsha kina da farin jini sosai da sosai kowa son ki yake yi, kina burge duk wanda ya zauna dake" murmushi kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba. "Kina jin yunwa ko?" Ya tambaya yana sauƙa daga kan titin da suke zuwa na gidan su Abbi ɗin.

GyaÉ—a mashi kai tayi alamar e tana jin yunwa "To ki yi hakuri, an shirya mana abin ci a gidan Bappa zamu je mu ci, su Akila ma duk Akil ya kai su tun karfe 12 na rana, yanzu mu kaÉ—ai suke jira".

Wani irin daÉ—i ta ji, zata haÉ—u da Akila da Umaisha.

Suna isa gidan tun bai gama kashe motar ba ta fito, dan ita burinta kawai ta ga su Akila. Tsayuwa ta yi tana jiransa har ya kashe motar ya fito suka jera izuwa cikin gida.

Tun a bakin kofar palon suke jiyo hayaniya alamar suna haÉ—e a palon kenan, Imran ne a gaba tana bin shi a baya.

Da sallama ɗauke a bakinsu suka shiga cikin palon, wani ihu Ayla dake zaune kusa da daddy ta kurma tare da miƙewa ta nufeta tana faɗin "Rimsha!! Rimsha kece?!!" Ita ma Rimsha ihun sunan Ayla ɗin ta yi suka rungumi juna suna dariya kamar zautattu.

Malika dake tsaye a bakin kofar shigowa ba wadda ke ganin ta dan bata bayyana a yadda za'a ganta ba, da ɗan karfi ta ce "Rimsha ki ɗan yi nisa da Ayla dan kada wannan bala'in ya taɓa ki" a razane Rimsha ta zaro ido tana kallon ta.

Malika ta gane cewa karin bayani Rimsha ke so, dan haka sai ta ce "E abin da kika ji haka ne, akwai wadda ta bawa wani boka aiki shi kuma ya sanya aljanu yan uwa na yin wannan aiki, ba za su iya taɓa wadda aka ce ayi wa aikin ba, yana da riƙo da askar masu karfi, dan haka kan Ayla za su sauke wannan aikin nasu, bana son ki yi kusa da ita dan zata iya mutuwa akowani lokaci k.....

Sai mun haÉ—u Monday idan mai dukka ya kai mu

💖💖TRIPLETS💖💖

E 69-70

Malika ta gane cewa karin bayani Rimsha ke so, dan haka sai ta ce "E abin da kika ji haka ne, akwai wadda ta bawa wani boka aiki shi kuma ya sanya aljanu yan uwa na yin wannan aiki, ba za su iya taɓa wadda aka ce ayi wa aikin ba, yana da riƙo da askar masu karfi, dan haka kan Ayla za su sauke wannan aikin nasu, kuma kinsan a cikin aikin ma har da wadda duk macen da ta raɓe shi da sunan soyayya zata mutu, bana son ki yi kusa da ita dan zata iya mutuwa akowani lokaci, ko kuma wani mummunar abin ya sameta". Nan take Rimsha fara hawaye abin ya taba ta sosai da sosai, da yake sun jima suna kewar juna sai kowa ya yi tunanin kukan ɗaɗin haɗuwa da yar uwar tata take yi. Ita kuma tana son tambayar Malika amma tana tsoron yin magana kada su yaya Imran su yi mata kallon mahaukaciya tun da ba kowa ke kallon Malika ɗin ba.

Ganin tana kuka ne yasa Imran ya sanya hannu ya raba ta da jikin Ayla É—in, sai murmushi Ayla ke yi bakinta yaki rufuwa, ita kuma Rimsha wannan murmushi da Ayla ke yi, yana kara tayar mata da hankali ba kaÉ—an ba.

Gaba É—aya family suna haÉ—e a Palon, mazan sun yi shigar mayan kaya matan kuma abayas, Abbi, daddy'n jelly, Aunty, Irfan, Akil, Akila, Umaisha, Aafia, Ayla amarya, a gaba É—aya Æ´an gidan, Hajiya Khadijat ne da kuma Hanan sune basu a waje, ita Hajiya Khadijat ma bata gidan, ta tafi gidan Ummin Nawid wuni, ita kuma Hanan tana wanka.

Akila ce ta taso ta rungumeta tana rarrashinta, a haka suka karisa cikin palon suka zauna, saman sofa ɗaya Ayla da Rimsha suka zauna, while daddyn Jelly na gefensu, Aafia baiwar Allah da yake tana samun kulawa sosai wajen Akil har kumatu ta yi, saɓanin a gidan nasu da bata gaba bata baya, kullun a yadda take, ba cigaba, amma yanzu Akil na kula da ita sosai, hakan yasa kaso 70 cikin 100 na damuwar da take a ciki na rabata da budurcinta da aka yi ta ragu mata, a yanzu dai ta dai'na yawan tunanin sosai, ta fawwalawa Allah komai, ta dukufa da karatun dake a gabanta, Amarya Umaisha kam ba'a magana, dan ƙibar da ta yi ma a yan kwanakin nan ba kaɗan bane, kumatun nan sun ciko sosai, da yake dama tafi Aafia diri da kuma kiɓa, ita kuma Aafia ta fita tsawo, Umaisha akwai hips da breast sosai kamar Rimsha da Akila, su ukun nan shape nasu kusan ɗaya, sai dai wadda ta fi ƙiba a ciki afi yawan ganin nata.

Sai hira suke yi cike da annashuwa da farinciki, suna ta gaggaisawa da juna, ita kuma Hanan tana wanka, bata fito ba. Daddy'n Jelly bawan Allah tunanin Jellyn sa kawai yake yi, ga Æ´an uwanta sun haÉ—u amma bata nan, abin sam bai yi mashi daÉ—i ba, ya jefa shi cikin tunani.

Kasa hakuri Rimsha ta yi dan tana son yin magana da Malika, dan haka sai ta miƙe tana faɗin "Yaya Imran ina zuwa zan je wajen mota na dawo". Bata jira amsar shi ba ta fice da sauri abinta.

Tana fita Aunty ta fara tambayar a ina Imran ya samo yarinya kyakkyawa haka, wato magana suke akan Rimsha, bai ɓoye masu ba, ya gaya masu gaskiya yar Nawazudden ce, nan fa daga Abbi har daddyn Jelly suka fara godiya ga Allah da ya kawo masu ƴar Nawazudden har cikin gida, ashe da rabon su ramawa Nawazudden abubuwan alkhari da ya yi masu, ba ɓoye ɓoye da yake bappanun sune, hakan Imran ya fara basu labarin irin wahalar da Rimsha da Ayla suka sha kamar yadda Rimsha ta gaya mashi.

Duk cikin palon ba wanda bai matsa masu kwallaba, nan fa daddyn Jelly ya kara É—aura É—amarar kula da amaryarsa sosai, dan tasha wahalar rayuwa ba kaÉ—an ba.

Ita kuwa Rimsha tana fita waje ta fara Æ´an waige waige tana neman Malika, can jikin motar Imran ta hangota tana tsaye ta harÉ—e hannu a kirji tana É—an murmushi kamar kullun.

Da sauri Rimsha ta karisa wajen ta. Cike da tashin hankali ta fara magana "Malika menene yake faruwa? Dan Allah ki gaya Mani, wlh idan Ayla ta mutu zan iya shiga tashin hankali da zai iya zama sanadiyar rayuwata, kin dai ga nima bani da lafiya ko? To dan Allah ki tausaya Mani, yanzu haka da karfi karfi zuciyata ke bugawa, kirjina ciwo yake yi mani, dan Allah ki ji tausayin mu Malika". Tana magana idanuwanta cike tap da kwallah.

Matsowa Malika ta yi ta dafata tana faɗin "Rimsha bana son ganin ki cikin damuwa, bana son abin da zai taɓa ki, amma abin da na gaya maki akan Ayla gaskiya ce, ina son ki sani ba laifi na bane, kuma kema ba laifin ki bane, dan haka kiyi hakuri kamar yadda kika saba karɓar kaddarori da jarabobi to a wannan karon ma dagewa zaki yi ki karɓi mutuwar Ayla.

Tashin hankali, wani irin duhu Rimsha ta fara gani yana gilma mata ta cikin idanunta, jiri ta fara gani mai karfi yana ɗebanta, wani irin juyi duniyar yake yi mata, nan take ta fara ƙoƙarin zubewa kasa a wajen.

Cikin sauri Malika ta tareta tana faɗin "Rimsha kada ki faɗi, wai baki ji abin da Dr ya ce bane? Ko kin mance ne? Idan fa kika cigaba da sanya damuwa a ranki har kina yawan faɗuwa ki suma zaki sami paralyse, to dan haka ya kamata ki kula, ki zama mai karɓar kaddara a duk yadda ta zo maki, kuma ai ba ce maki na yi aikin ya kamata ba, bai kai ga kamata ba, a takaice ma bokan bai kai ga kammala aikin ba, so kinga akwai damar da za'a iya kuɓutar da ita, kin san fa wadda ta bada aikin cewa ta yi amata aikin da duk macen da ta raɓe shi da sunan soyayya to ta mutu, sannan kuma shi a sanya mashi son ta ita wadda ta bada aikin kenan, ita kaɗai zai so, to kinga aikin ba zai kama shi ba, ita kuma Ayla abin da yasa zai kamata ta mutu, saboda ta raɓe shi da sunan soyayya ne, dole aikin ya faɗi akanta.

Cikin sauri har tana haɗe words ta ce "Yanzu dai Malika ki gaya mani taya ya Ayla yar uwata zata kuɓuta daga hannun wayan nan azzaluman?"

A takaice Malika ta ce "E kuna da hanya biyu koma in ce ɗaya, domin ɗayar ba lallai ta yi amfani ba, bari na fara gaya maki wadda ba lallai ta yi amfani ba, askar, yin addua da zama da alwala shine hanya ta farko kuma shine ba zai yi amfani ba, abin da ya sa na ce ba lallai ta yi amfani ba, saboda Ayla ba zata iya ba, ba zata juri yi kullun ba, saboda bata saba ba, acikin askars da muke da su ma kwata-kwata guda uku Ayla ta iya, so yanzu ko kin ce mata ta rinƙa yi ba zata iya yin shi kullun ba, zata rinƙa mancewa, kuma Kinga bokan yana kan yin aikin, zai iya kammalawa ko wani time daga yanzu, wannan shine hanya ta farko, wadda ba zata yi wani amfani ba, hanya ta biyu wadda zata yi amfani kuma shine the best solution da kuke da shi a yanzu, domin daga yanzu zuwa ko wani lokaci bokan nan za su iya kammala wannan aiki, ina kara jaddada maki, wannan hanya dai ba wata bace fa ce a sami haɗuwa tsakanin Ayla da AbdulMalik, jininsu ya haɗu, ta haka ne za'a iya samin nasara, amma shima fa idan ba'a yi yadda ya dace ba ana iya samun matsala".

Kwata kwata Rimsha bata gane irin haÉ—uwar da Malika take nufi ba, dan haka sai ta ce "Ai yanzu ma suna haÉ—e gida É—aya, baki gani suna tare a palo bane? Ko dai ba AbdulMalik É—in a cikinsu ne? Ko ba su bane Æ´an uwan Ayla É—in?".

Nisawa Malika ta yi kafin ta fara bata labarin yadda akayi Ayla ta zo gidan da kuma wanene AbdulMalik sannan ta yi mata karin haske akan irin haÉ—uwar da take magana akai. Babbar magana shiru Rimsha ta yi tana tunanin ya za'ayi ta gayawa Ayla ga abin da Malika ta ce, kai ina hakan ma ba zai yi wu ba, to waye ya dace ta gaya mawa?.

Ganin haka yasa Malika ta saketa tana faɗin "Kiyi tunani mai kyau, ki nutsar da brain naki, ki ceci kawar ki ƴar uwan ki, na barki lafiya zan je gida, amma zuwa gobe zan dawo". Tana kai karshen maganar ta ɓace ɓat, hakan kuma ya yi daidai da fitowar Imran, dan ya ji ta shiru, ita da ta ce tana zuwa yanzu, amma shine ta je ta jima haka, shine ya fito duba ta, bayan shima ya gama gayawa su Abbi wacece ita ɗin.

Ganin ta wani sukuku ya sa ya tambayeta ko lafiya, me ya tsayar da ita a wajen nan?.

Ta kasa magana sai dai ta yi gaba ya bi bayanta, ta rasa waye zata fara tunkara da wannan maganar, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan ba magana ce da zata faɗu ga kowa ba, ta ya za'ayi ta fara tunkarar wani ta ce mashi me to? Ta ce tana son daddy'n jelly da Ayla su yi kwanciyar aure ne ko kuma dai me? Wannan magana tafi karfin ƙwaƙwalwarta, Malika ta kai ta ta barota a wannan fannin kam.

Suna shiga palo daddy'n jelly da Abbi har suna haÉ—a baki wajen cewa "Zo nan Rimsha" abin ya bata mamaki, ya akayi suke mata wannan kira haka har suna haÉ—a baki, bayan kuma É—azun da ta shigo banda mirmishi da suke yi mata, ba su wani kulata sosai ba.

Kusa da Abbi ta je ta zauna ta kasa wani motsin kirki kirjin ta sai dukan uku uku yake yi, wannan magana tafi karfinta, waye zata sanarwar? Ko Imran É—in ta sanar wa ba zai iya tunkarar daddyn Jelly da maganar ba, magana ce wace girmanta ya fi karfin katon dutse, har gara É—aukar katon dutse akan furta ta, ko abokan juna yana da wuyar furtawa a tsakanin su bare kuma ace ta gaya wa Imran shi kuma ya gayawa bappansa, to ta ina ma zaa fara? Su ce mashi ya kwanta da Ayla ne ko dai yaya?. Wanann shi babbar magana.

Su kuwa banda mirmishi ba wani abin da suke yi, sai hira ake zubawa, cikin dabara Irfan ya kira Akila akan ta zo ta raka shi waje, suna fita su Imran suka fara gulmarsu suna dariya.

Aunty ce ta ce kowa ya zo su haye saman dining table aci abinci, Akil ba kunya ya ce shi a kasa zai zauna ya ciyar da babynsa a baki, a saman table É—in nan ba zai ji daÉ—in bata abaki da kyau ba, salati Aunty ta yi tana tafa hannu, hararar ta daddyn Jelly ya yi yana faÉ—in "To zaki fara saka wa mutane ido ko? To wlh ki fita tun wuri, yau gabaÉ—ayansu ma a nan za su kwana".

Abbi ne ya caɓe zancen da cewa "Maik ina rabaka da shiga harkar matata! Ka kiyaye ni tom, idan ba ka yi wa Halima biyayya ba zaka shiga wuta!".

Gaba É—aya palon suka sa dariya, Aunty kuwa har da kara bubbuÉ—e hanci ita a dole matar yaya babba ce.

"Yaya Deen da gaske Sadiya Æ´ar sa ido ce, yanzu ba ga shi daga zuwan su Akil har zata saka masu ido ba".

Hararar shi Abbi ya yi yana faÉ—in "Ina Hanan É—ina ne? Naga kowa ban ganta ba".

Aunty ne ta ce "Hanan tana ɗaki tana wanka" jinjina kai Abbi ya yi yana faɗin "Gobe za mu je gidansu In sha Allah, idan muka dawo kuma kinga na haɗa yara uku kenan". Ɗan zaro ido Aunty ta yi yana faɗin "Ƴara uku kuma? Waye da waye?"

Da hannu ya nuna mata Rimsha yana faɗin "Da Rimsha da Hanan ɗin da kuma Aliya". Cikin sauri daddy'n jelly ya ce "A'a yaya Deen ni zan ɗauki Rimsha gaskiya, ka bari ni zan riƙe ta, a waje na zata zauna kafin mu nemo su mummynta da ƴar uwarta, idan ya so kai sai ka riƙe ƴar uwar tata".

Girgiza Abbi ya yi kafin ya ce "A'a kai da a yanzu baka da gida, kai ma fa riƙon ka nake yi tukun nan".

Dariya Aunty ta yi tana ƙoƙarin yin magana Akil ya rigata da cewa "Aunty wai ina abin cin ne? My wife tana jin yunwa".

Miƙewa Aunty ta yi ta nufi saman table tana faɗin "Bari naje na kawo wata kila baby ne ke jin yunwa ba wife ba, karna yi wa ɗan jikana rowa".

Rimsha kam miƙewa ta yi tare da riƙo hannun Ayla ta ce "Ayla ina ne ɗakin ki? Ina so ne in je ban ɗaki".

Satar kallon daddyn Jelly ta yi kafin ta ce "Muje na kai ki" ta kai karshen maganar tare da miƙe wa suka nufi sama.

"Baby ina zaki je ba tare da kin nemi izinin mijinki ba?" Cewar daddyn Jelly, da sauri ta juyo tana ƙoƙarin dawowa.

Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa "A'a raka mana first ladyn mu" kasa Rimsha ta yi da kai, ba abin da yake yi mata yawo a ƙwaƙwalwarta face zancen Malika, ga shi kuma shine kawai hanyar da za su bi wajen tseratar da Ayla.

Suna shiga É—akin ta rungume Aylar tare da fashewa da kuka, sosai ita ma Ayla ta rungumeta tana hawaye, ita duk a tunaninta kukan sun jima basu haÉ—u bane Rimsha take yi.

Sun ɗan jima a haka kafin su raba jikinsu su koma bakin gado suka zauna. "Rimsha ki je toilet ɗin mana?" Girgiza kai ta yi kafin ta ce "Ayla babu wani toilet da nake son zuwa, keɓewa kawai nake son mu yi, mu samu dama mu yi hira".

Sake rungumeta Ayla ta yi suna masu matuƙar jin kaunar juna.

A palo kuwa, sai hira suke yi, Akil babu kunya a gaban kowa da Aunty ta kawo mashi abin cin ya fara bawa Umaisha a baki, ita ma Umaisha ɗin da yake ta saba, yanzu ya koya mata, sai bata ji kunyar Abbi ba, sai cin abincin su suke yi, shi dai Imran daya ga haka sai ya miƙe ya fice waje bawan Allah.

Yana fita ya hango Akila da Irfan can wajen flowers suna hira, jikin motarsa ya koma ya tsaya yana hawaye, soyayyar Jelly ce ta dawo mashi sabuwa, Akil ya tuna mashi da lokacin baya idan ya je Kano, a baki yake bawa Jelly abinci, tana ci tana zuba mashi shagwaɓa, yanzu kuma da ya fito ya sake cin karo da su Irfan, sai ya sake tuna idan ya zo dawowa Kaduna yadda Jelly ke biyoshi waje tana yi mashi kukan shagwaɓa akan kada ya tafi ya kwana, hakan yasa shi hawaye, wani irin azababben son tane ke kara taso mashi, ji yake yi kamar zai mutu, zuciyarsa na mashi zafi sosai.

Yana tsaye a wajen bai ga lokacin da daddyn Jelly ya fito ba sai jin muryarsa ya yi yana faɗin "Dama nasan kuka ka fito yi Imran, tun da naga irin kallon da ka yi wa su Akil nasan sai ka tuna Jelly, saboda abin da kuka saba yi da ita kenan, ni kaina ina ganin Akil ya fara bawa Umaisha abinci kai da Jelly ne kuka faɗo mani a raina, kayi hakuri komai zai wuce In Sha Allah, idan har Jalila tana raye ina da kyakkyawar yaƙinin zata dawo gare mu, idan matar kace, to ba makawa sai ka aureta".

A zafafe Imran ya É—ago kai jin yau daddyn Jelly ya kira Jelly da sunanta kai tsaye wato Jalila, baya kiran sunan domin sunan wadda ta haifi mummyn Jelly É—in kenan, saboda ta yi mashi kara, ta yi mashi abubuwa da dama shiyasa ya yi mata takwara, familyn mummy'n Jelly basa son aurensa da Hajiya Umaima wato mummyn Jelly amma haka mamanta ta dage sai da akayi aure, wannan dalili yasa ya yi mata takwara kuma yake girmama sunan, harta mahaifin mummyn Jelly baya son auren, kuma kafin ya yarda ayi auren sai da ya kafa wa mummyn Jelly sharaÉ—in akan idan ta fita gidan shi ta fita kenan, kada ya sake ganin kafarta, haka saboda son da take yi wa daddyn Jelly ta ce ta amince, ta yarda, wannan shine dalilin da yasa daddyn Jelly baya zuwa gidan sirikansa, kuma hakan yasa ma yaki yarda ko hutu Jelly ta je gidan, domin yasan basu sonta, kakanta mace kawai ke sonta, sai kuma kawunta Ahmad wato A'A.

Goge hawayen fuskarsa ya yi kafin ya ce "Ba komai daddy ina hakuri ai, kuma ya zama dole na yi hakuri, amma dai idan na tuna ta dole zan yi kuka, ban taɓa son wani abu a rayuwata kamar yadda nake son jelly ba, tun tana ƴar shekara 2 zuwa 3 Allah ya zarabceni da sonta, na tabbatar mawuyacin abune na so wani abin kwatan makamancin son da nake mata, kullun sai na yi mafarkinta daddy, kullun na kwanta, daurewa kawai nake yi ina shiga cikin mutane mu yi hira da dariya, amma ni kaɗai na san me nake ji a cikin zuciyata, Allah ya gani ina kaunar jelly fiye da raina, ya Allah ya dawo mani da ita".

Yana magana wasu hawayen suna biyo kuncinsa. Tunani daddyn Jelly ya fara yi da ace ya aura mata Muneer da ba makawa Imran mutuwa zai yi, irin wannan kauna da yake yi mata tun ma bata san wace ce ita ba, lallai ba abanza Allah ya jarabci jelly da kaunar shi ba ita ma, Allah ne kaÉ—ai yasan dalilin da ya sanya ya sakawa Jelly sha'awar gudu ta bar gida dan kada ayi auren nan, Allah mai hikima mai iko.

Ya jima yana tunani shessheƙar kukan da Imran yake yi ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya faɗa, cikin sauri ya kariso wajen tare da rungumar shi yana ɗan bubbuga mashi baya a hankali yana rarrashinsa.

Irfan da Akila kuwa suna can gefe suna zuba hirarsu, while su Akil kuwa suna tsakar Palo shi da Umaisha yana bata abinci a baki tana zuba mashi shagwaɓa, Abbi kuwa ya haye saman table Aunty tana serving nasu shi da Aafia.

A ɓangaren su Rimsha kuwa, sun ɗan warware suna hira kenan Hanan ta fito daga toilet ɗaure da towel a kirjinta.

"Rimsha kece?" Shine abin da Hanan ta faɗa tana zaro ido, da sauri Rimsha ta miƙe tana faɗin "Hanan ke ce kuma a nan? Ina su yaya Yusuf da yaya Sadiq?".

Nan take fuskanta ya sauya jin an ambaci Yusuf da kuma Sadiq, ta tuna da gida ta kuma tuna mamanta, hawaye ta fara yi tare da tsugunnawa a wajen.

Da sauri Rimsha da Ayla suka kariso wajen suka fara rarrashinta.

Da kyar suka samu ta yi shiru, bayan ta yi shiru Rimsha ta tambayi me dalilin yin kuka, nan take ta bata labarin abin da ya faru da mutuwar mamanta da yadda akayi ta zo gidan.

Sosai Rimsha ta tausaya mata ta kuma bata hakuri.

Bayan wasu Æ´an muntuna Hanan ta gama shirinta cikin doguwar rigar Aafia sannan ta yi masu sallama ta fice waje izuwa Palo wajen su Abbi.

Tana fita suka dasa hirarsu, Rimsha tana son ta kwatanta gayawa Ayla wannan magana amma ta kasa, kuma abin da ya sanya ma bata karfafa akan ta faÉ—a wa Ayla É—in ba, ta san cewa ba wani abin da Ayla zata iya yi, hasalima ba zata fahimceta ba, tun da ba wani ilimi take da shi ba, ko da ma tana da ilimi ai ba zata je ta ce da daddyn Jelly ya kwanta da ita ba. Wannan maganar shi ya kamata a gayamawa, sai dai ba hanyar yin hakan.

Sai fara'a Ayla take yi tana gayawa Rimsha yadda take son mijinta, ita kuwa Rimsha banda to da a'a sai wani magana kuma ta É—an yi murmushi, banda hakan ba wani abin da take bin Ayla da shi.

Shi kuwa daddyn Jelly da kyar ya iya rarrashin Imran suka dawo cikin Palo, bayan sun je É—akin daddy ya wanke face nasa kenan.

Saman dining table suka haye, Aunty ta zuba masu abinci, da kyar Imran yake iya taunar abincin, ba dan kada ya ce ba zai ci abinci ba daddyn Jelly ya ɓata rai da ya cire hannunsa, shi kuma daddy yana son cewa a kira mashi matarsa ta zo ta ci abinci, amma ya kasa faɗa saboda Imran, baya son wani abin kuma ya jefa Imran ɗin cikin damuwa, hakan yasa ya hakura ya daure suka ci abincin a haka.

Bayan sun kammala daddy ya miƙe ya ce da Akil ya zo waje su yi magana, sai tsokanansu Aunty take yi daddyn Jelly na bata amsa har suka fita.

Suna fita daddy ya gayawa Akil ya kamata ya daina duk wani kulawa da yake bawa Umaisha a nan har sai sun koma gida, idan ba haka ba kuma to yana iya sawa su rasa Imran, sosai Akil ya ji tausayin É—an uwansa, kuma har ga Allah bai kawo a ransa cewa hakan zai iya haifarwa da Imran É—in matsala ba, a yanzu shima ya san zafin so, dan yana bala'in kaunar Umaisharsa, da abaya ne yake ganin kamar hauka kawai Imran yake yi, yanzu kuma ya gane cewa ba hauka bace, so na iya sanya mutun ya yi abin da ma bai san ya yi ba.

Bayan sun gama magana da Akil ya wuce ya samu Irfan da Akila, sai hira suke yi suna dariya.

"Akila wuce cikin gida Kinji?" Cewar daddy, kasa ta yi da kanta tare da wucewa da sauri. Bayan ta tafi daddy ya gaya mashi cewa kada ya rinƙa nuna soyayyar Akila a fili har sai Imran ya tafi, sunkuyar da kai kasa ya yi yana faɗin "Bappa bafa soyayya muke yi ba".

Wucewa daddy ya yi yana faÉ—in "Kai dai ka sani, ni kaga tafiya ta".

Murmushin Irfan ya yi tare da bin bayansa shima ya dawo cikin gida.

Saman table ya hango Akila ta zauna tana cin abinci, karisawa wajen ya yi shima ya zauna tare da fara magana ƙasa ƙasa "Heartbeat baki ce komai ba". Irfan kenan, shi kuma daddy'n jelly yana shigowa saman sofa ya zauna suka cigaba da hira shi da Aunty da Abbi. Su Umaisha kuma a lokacin sun wuce sama.

Kasa da kai Akila ta yi tana faÉ—in "Yaya Irfan ai ban san me zan ce bane". ÆŠaukar spoon ya yi ya fara cin abincin dake a cikin plate É—in nata kafin ya ce "To in gaya maki abin da zaki ce ne?" Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a.

"A'a kuma heartbeat?" Gera ta É—aga mashi alamar e, tana murmushi, su Abbi kam kamar ba su san da zaman su a saman table É—in ba, hirar su kawai suke yi.

Ɗan leƙo face nata ya yi yana faɗin "To shikenan ki ce wani abin ko kuma na gayawa Abbi kawai a ɗaura mana aure Friday mai zuwan nan" ajiye spoon ɗin hannunta ta yi ta miƙe da sauri ta haye sama tana murmushi, binta da kallo ya yi yana ƴar dariya shima, duk abin da suke yi Aunty na kallonsu, shi kuma Irfan ya mance ma da su Abbi a palon.

Akil kuwa an takura mashi yana son shan love kamar yadda ya saba, amma yau ba hali, domin wani abin ba zai yi wu ya yi shi a gaban Abbi ba, duk da yake bappansa amma ai uba ya wuci wasa, shi ya haifi Umaisha É—in komin yaya akwai kunya.

Akila kuwa tana hayewa sama ta fara duba wani É—aki su Rimsha suke ciki, sai da ta buÉ—e É—akuna biyu ana uku ne ta gane su, da gudu ta shiga É—akin tare da faÉ—a wa saman bed tana dariya.

Suna ƙoƙarin tambayarta ko lafiya sai ga Umaisha da Aafia da Hanan da suka fito daga ɗakin Aunty suma sun shigo.

Miƙewa Akila ta yi ta rungumo Aafia tana dariya kamar zautaciya. Rumgumeta Umaisha ma ta yi tana faɗin "Aunty Akila gaya mani me kuke kullawa da yaya Irfan? Naga yau har da dariya ya yi, shida kwata-kwata baya dariya, kullun zakiga face nasa a ɗaure, wlh tun ɗazun na tsaya a window ɗakin Aunty ina kallon ku".

Hararar ta Aafia ta yi kafin ta ce "Wato har ta zama Aunty Akila kenan saboda gulma, ke Umaisha wlh ni bansan ma a wani mataki zan ajiyeki ba"

Umaisha na ƙoƙarin yin magana wayarta dake a hannunta ya fara ringing, tana dubawa sai taga my life, cikin sauri ta yi picking tare da kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Yaya Akil har ka fara kewata ko?".

Daga ɗayar ɓangaren daddy'n jelly ya ce "Bawa auntynki wayar". Wani irin kunya Umaisha ta ji ya kamata jin voice ɗin bappanta ne ba mijinta ba.

Cikin sanyin jiki ta miƙawa Ayla wayar, karɓa Ayla ta yi tare da karawa a kunnenta ta ce "Hello".

Wani nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Baby zamu je masallaci an kira sallar la'asar, kafin na dawo ki kawo mani abinci É—aki na kuma ki zauna ki jirani, amma kafin nan ki yi Sallah tukun nan". Kamar dai kullun to ta amsa mashi da shi, sannan ya katse kiran ya bi bayan su Akil da tuni sun riga da sun wuce masallaci, shiyasa ma su Umaisha suka dawo cikin É—aki kenan, Aunty ta ce je ta ce masu su je su yi Sallah ga su Abbi can za su tafi masallaci.

A yanzu Aafia ta zama so silent kamar ba ita ba, kuma da alama har yanzu aikin da Rufee ta yi mata yana jikinta, da yake dai Rufeen bata nan ne bare ta bata command sai hakan yasa ba zaka gane akwai sihirin a jikinta ba.

Zama suka yi a saman bed ɗin suka fara hira, Hanan ne ta fara miƙewa ta ce bari ta yi sallah dama da alwalanta, cikin sauri Rimsha da Ayla suka miƙe a tare suma dan su je su yi alwala su yi Sallah, A'afia da Akila kuwa kwanciya suka yi wai basu Sallah yau, ita kuma Umaisha waje ta fice zuwa wani ɗakin da ta yi alwala tun da su Rimsha sun shiga cikin wannan toilet ɗin, daga Umaisha har Aafia ba wacce ta nemi Ommu a cikinsu, da alama ma sun mance da ita.

Umaisha tana fita kai tsaye wajen Aunty ta nufa, har kasa ta je ta duƙa ta bata hakuri tare da neman ta yafe masu duk abubuwan da suka yi mata abaya, a lokacin Aunty ta ɗauro alwala zata fara Sallah kenan, da fara'a akan face nata ta ce ta yafe masu ba komai, godiya sosai Umaisha ta yi mata sannan ta wuce cikin toilet na ɗakin auntyn ta yo alwala a cikin kafin ta dawo wajen su Rimsha suka yi sallah.

After 30min. Bayan sun idar da sallah meƙewa Ayla ta yi ta nufi kofar fita tana faɗin "Rimsha ina zuwa daddy ya ce na kai mashi abinci ɗakinsa" ta kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.