Best Hausa Novels

Triplets Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: TRIPLETS BOOK 2.txt

Chapter 3 of 8

Episode 43-44

This page dedicated👇

*Aisha baita Jiddah, Ruky Aunty, N Hidan, Hafiza ayuba*

Shiru A'afia ta É—an yi tana jujjuya kalaman matar, sun bata magani kenan suna da asibiti ne a nan wajen? Ta tambayi kan ta a cikin zuciyarta, kidnapers dama haka suke? Ta sake tambayar kanta.

Sake ɗagowa ta yi ta kalli matar sanna ta ce "To suna da likitoci a nan ne da za su bata magani?" Girgiza mata kai matar ta yi sannan ta ce "Ni dai tun da nake nan wajen yau tsawon wata uku ban taɓa ganin wani likita ba, sai dai idan suka ga baki da lafiya sosai sai kiga sun kawo maki magani, ban san daga ina suke samo maganin ba" "Wata uku!" A'afia ta maimai a fili tana zare ido, gyaɗa mata kai matar ta yi tana faɗin "E wata na uku a hannunsu, kuma sun karɓi kuɗin fansa daga wajen yan uwana har sau biyu amma sun ki su sake ni na koma gida" Zaro ido sosai A'afia ta yi domin bata taɓa tunanin hakan ba, ita a nata zaton idan suka kama mutun suna bashi kulawa saboda za su samu kuɗi, kuma tana tunanin da zarar an basu kuɗin fansa suke sakar mutun ya koma gida, bata taɓa zaton wajen nasu haka yake ba.

Jugum jugum su ka zauna abin gwanin ban tausayi.

Can kuma Aafia ta sake cewa "To amma ke meyasa basu barki kin koma gida ba tun da sun karɓi kuɗin fansa?" Wani dogon numfashi matar ta ja tare da sauƙewa a hankali sannan ta ce "E wannan ne ban san ni ba, abin da dai na sani shine da suka buƙaci kuɗin fansa sai suka ce mace ce zata kawo musu kuma macen ma babban ƴata mai shekara 17 shine yan uwana suka ki yarda suka ce mace ba zata zo wajen ba, sai aka bawa yayana kuɗin ya kawo, basu musa ba sai da yayana ya zo ya kawo musu kuɗin a in da suka yi da shi zai zo, bayan sun karɓi kuɗin sai suka sa bindiga suka harbe shi, wai dan saboda sun ce mace suke son ta kawo kuɗin yan uwana sun bujirewa umarnin su, haka yan uwana suka sake ba su hakuri suka rinƙa rokansu a kan su yi hakuri su sako ni, nan suka sake cewa sai an basu million biyu kuma kanina suke son ya kawo kuɗin, a cikin kannena ɗin ma sai suka zaɓi jarumin gidan mu, mai faɗa da kuma zafin rai, ni na rasa waye yake gaya musu family ka idan suka kamaka, sai kiga kusan komai naka sun sani, to da kanina ya kawo kuɗin sai suka yi ƙoƙarin jan ra'ayinsa a harkar dama haka suke yi, shiyasa suka yi yawa a cikin al'umma, idan sun ga namiji lafiyayyen mai karfin zuciya mara tsoro sai suyi ƙoƙarin jan ra'ayinsa, idan ya ki sai su yi mashi yankar rago, su yi video su turawa duniya amma ba za su taɓa faɗin abin da ya sanya suka yanka shi ba, sai dai suce ba'a kawo kuɗin fansan shi ba, abin da ya faru da kanina kenan, ya ce musu shi ba zai iya wannan harkarba, wlh a saman dutsen da suka karɓi kuɗin a nan suka ɗaure shi suka yi mashi yankar rago, sai bayan sun dawo suna magana na samu labari daga maganar da suke yi da ogan nasu, sannan dan su huce haushi suka zo suka ɗauki yarinyar nan suka tafi da ita shekaranta 14 a duniya amma haka shaiɗanunan suka lalata mata rayuwarta, na yi na yi su kashe ni na huta da wannan bakin ciki amma sun ki kula ni, kuma tun daga lokacin da suka yi wa wannan yarinyar aika-aikan nan ba su sake bi ta kai na ba, ni yanzu bani da wata bukatar da ta wuce su kashe ni, na yi kuka har hawayena sun kafe, yanzu zuciyata ta kekashe bana tsoro ko shakkar komai" Ta kai karshen maganar tana shafa kan yar tata dage kwance saman cinyarta gwanin ban tausayi.

Sosai A'afia take zubar da kwalla yau ta ji abin da ya fi karfinta, wannan rashin imani har ina, su sace mutane bayan haka kuma su rinƙa lalata musu rayuwa sannan suna kashe masu yan uwa, wannan bala'i dame ta yi kama, idan ba Allah maɗaukakin sarki ba ba wanda ya isa ya fitar da bawa daga cikin irin wannan bakin zalincin.

Dafata matar ta yi tana faɗin "Ki daina kuka domin kada hawayen ki su kare, abin kuka yana gaba, domin baki ga komai ba, tun kina da sauran hawaye har ma su ƙafe, ni yanzu addu'ar da nake yi maku Allah yasa kada su lallata maku rayuwarku, domin da wuya yanzu su ɗauko mace ba tare da sun kwana da ita ba su mai da ta, ɗazun da asuba ma naga sun kawo wasu mata sun zuba su cikin wancan ɗakin, an jima kaɗan za su zo su fitar da mu tsakar wajen cikin ciyayin can dan su azabtar da mu da rana, haka suke yi, idan rana ya yi sai su fitar da mu rana, idan yamma ya yi su dawo da mu, to idan sun fitar da mu sun haɗe mu waje guda ne sai kiga suna zaɓar mace da ta yi musu suna sanyawa yaransu na kasansu suna shigar musu da matan ɗaki, ina rokan Allah ya tsare ku yasa kada su lalata maku rayuwar ku, mu kam sun gama da mu saura su karisa mu kawai mu huta, ni na rasa ma me ya sanya basu kashe ni ba".

Banda kuka ba abinda A'afia take yi, ita kuma Rufee tuni ta sulale kasa ta kwanta kamar bata numfashi sai dai hawaye kawai zaka gani yana bin kuncinta.

(Toh fa su Aafia kuna cikin garari, na barku lafiya na tafi izuwa wajen Rimsha, kada ku manta part na Aafia True life story ne!)

A ɓangaren Rimsha kuwa, tare suka ci abincin ita da Akila, su na ci suna hira gwanin ban sha'awa, bayan sun kammala ne suka fito Palo, zaune suka isko Imran saman sofa, ya tattare komai na kwanikan abincin da ya ci, har da goge wajen ya yi bawan Allah.

Saman sofa mai zaman mutun 3 suka zauna Akila tana faÉ—in "Yaya Imran Aunty Aafia bata dawo ba fa, kuma yaya Akil ya ce idan ta je school ta dawo, to tun jiya bata dawo ba". Ba tare da kalle su ba ya ce "To bata da ra'ayin zama a nan É—in ne shiyasa, sai ku kyaleta ta zauna in da take so, ko ana dole ne?" Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a ba'a dole.

Shiru sukayi ba wanda ya sake magana, wayar Imran dake saman bed nasa a cikin bedroom nasa ne ta fara ruri tana neman agaji, da sauri Akila ta miƙe dan ta ɗauko mashi wayar, ɗagowa ya yi ya kalli Rimsha cike da kulawa ya ce "First lady gaskiya kin iya girki sosai kuma ina godiya, wlh na ji daɗi fiye da tunanin ki". Kasa ta yi da kanta tana murza yan yatsun hannunta, bata ce da shi komai ba, a haka akila ta dawo ta same su, hannunta ruƙe da wayarsa, miƙa mashi ta zo ta yi sannan ta koma saman sofar da ta tashi ta zauna tana murmushi.

Picking call ɗin ya yi tare da kara wayar a kunnansa yana faɗin "Hello Dr ya akayi ne?" Daga ɗaya ɓangaren Nawid ya ce "Wlh na mance ne ban bawa Rismha wayarta ba ga shi sai kiran layin nata ake yi zan bawa driver ya kawo muku". To Imran ya amsa mashi da shi sannan suka yi sallama ya dawo da kallon sa kanta "First lady dama kina da waya har yanzu ne?" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar E sannan ta ɗaura cewa "E wannan da nace maka ya taimaka mana a Ilorin shine ya saya mani wayar" yana ƙoƙarin sake yin wata maganar wayar tasa ta sake fara ruri, mai do da kallonsa kan wayar ya yi AA Salahuddeen shine sunan da ya bayyana akan screen ɗin.

Picking ya yi tare da karawa a kunnansa ya ce "Hello AA" daga ɗayan ɓangaren Ahmad ya ce "Prof ina cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali wadda yake yi wa rayuwata barazana". Zaro idanu Imran ya yi yana faɗin "A'A me ya yi zafi haka? Haba bana boss kada mu yi haka, tukun nan ma menene sila faɗi in ji, ba dai yarinyar da ka bani labarin nan bace?".

Tamkar Imran na a gaban shi haka ya yi ya gyaÉ—a kai yana faÉ—in "Wlh Prof ita ce, kwana biyu ina kiranta bata É—aga waya, sai yau da safe, shima muna magana ta katse ko gaisuwar kirki bamu yi ba, na sake kiranta sau ba adadi, amma bata É—auka ba, ni narasa ina zan saka rayuwata, duniyar gaba É—aya bata yi mani daÉ—i".

Jinjija kai Imran ya yi kafin ya ce "A'A na tausaya maka, amma ina son ka sani halin da ni nake ciki ko rabin shi baka shiga ba, matata shekara 15 muna tare ina kula da ita rana ɗaya na nemeta na rasa, ta ɓata, duk duniya idan ka cire iyayena ba wadda nake so biyunta, idan na tuna hakan jin zuciyata nake tamkar zata fashe ta fito waje, gara ma kai kana iya kiran wayar tata, ɗauka ne sai time to time take yi, ni kuma fa? In da take ma ban sani ba, bana jin Muryarta bana gani ba, bansan ai na zan ganta ba ya ilahi ya lillihi". Ya kai karshen maganar kamar zai yi kuka.

Zuba mashi ido Akila da Rimsha suka yi suna kallon shi gwanin ban tausayi.

"Yanzu Prof wani shawara zaka bani?" Shiru ya ɗan yi yana sauƙe ajiyar zuciya kafin ya ce "Shawarata a nan shine ka rabu da soyayya da gaibu, ka kama dahir, yanzu yaushe zaka shigo Kd? Idan ka shigo sai mu tsaida matsaya ko?" Jinjina kai Ahmad ya yi sannan ya ce "Toh shikenan zan shigo next week" to Imran ya amsa da shi, sannan suka yi sallama, ya miƙe zai wuce bedroom nasa dan AA ya fama mashi ciwon dake a cikin zuciyarsa, sallamar da akayi a bakin kofar shigowa ce ta dakatar da shi, amsawa ya yi tare da bada izinin shigowa dan ya san mai wannan sallamar, baba mai gadi ne.

Karisowa ciki mai gadin ya yi tare da dukawa kasa suka gaisa sannan ya miƙa mashi wayar Rimsha yana faɗin "Ga shi nan wai na baka in ji driver su Dr" karɓa Imran ya yi tare da yi mashi sannu ya juya ya miƙa wa Rimsha wayar sannan ya wuce ya nufi bedroom nasa yana faɗin "Akila zan ɗan kwanta zuwa la'asar domin kaina yana yi mani ciwo sosai" bai jira amsar su ba ya wuce ciki, shi kuma baba mai gadi ya miƙe ya koma bakin gate, su kuma suka miƙe suka wuce cikin ɗakin da ya kasance mallakin Rimsha a yanzu.

Saman gado suka kwanta Akila tana faÉ—in "Bari naga wayar taki". Lokaci guda suka yi sabo kamar sun jima a tare, saboda Akila akwai shiga rai ita ma sannan ga shi bata da mugunta tana son mutane sosai ga fara'a Masha Allah.

Miƙa mata wayar Rimsha ta yi, ta karɓa tare da kunna wutar screen ɗin, miss call ɗin Ahmad guda 20 ta gani, cikin sauri ta miƙa wa Rimsha wayarta tana faɗin "Ga shi nan yaya Ahmad naga ansa ya kira ki miss call har 20" karɓar wayar ta yi, kamar dama jira yake yi, tana karɓa sai ga kiran shi ya shigo, picking ta yi tare da kara wayar a kunnanta.

"Hello yaya Ahmad" nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Why my Queen why zaki azabtar da zuciya ta haka? So kike yi na mutu ko?" Cikin sauri ta girgiza kai tana faɗin "A'a yaya Ahmad bana so ka mutu" "To baki so na mutu me yasa kika ki ɗaukar wayata?" Ɗan satar kallon Akila da ta tsare ta da ido ta yi tana faɗin "Kayi hakuri wayar ne bata kusa da ni, ina wuni? Ya karfin jiki?" Shiru ya ɗan yi mata, can kuma sai ya fara magana "Lafiya lou Alhadulillah, amma dan Allah kada ki sake yin nisa da wayar nan, idan ba haka ba zuciyata zata iya fashewa" gyaɗa mashi kai ta yi kamar tana gaban shi, nan fa ya shiga zuba mata surutu tana bin shi da eh da kuma a'a, har ta ga ji shi kuma da alama yanzu ma ya fara.

Ganin haka yasa Akila ta karɓe wayar, ta kara a kunnenta tana faɗin "Yaya Ahmad amarya tana jin barci, ta gaji da magana ka rage mata maganar da zata yi maka anguma mana". Ta yi maganar cikin raha da wasa.

Ita kuwa Rimsha kamar wadda aka raba da ƙaya, Akila na karɓar wayar ta miƙe ta kwanta abinta, sosai Ahmad da Akila suka rinƙa zuba hira ta ce mashi ita sister Rimsha ce uwa ɗaya uba ɗaya, rashin sani ya fi dare duhu ai kuwa ya yarda har da cewa ta bawa mama waya su gaisa, nan fa ta sake shirga mashi wata karyar wai mama bata nan, ai kuwa nan ma yarda ya yi ya ci-gaba da bata labarin yadda suka haɗu da Rimsha da sauran tarihin rayuwarsa.

Rimsha kam bata ma san lokacin da suka gama waya ba, sai dai É—agowa Akila ta yi bayan ta gama wayar sai ta tarar ta yi barci, ajiye wayar ta yi saman bedside drawer ita ma ta kwanta a jefenta ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita, dama a gajiye ta dawo daga school.

A ɓangaren Jehan kuwa.

Ba wanda ya tashe su domin su yi sallar asuba, da yake ita ta saba tashi, time na cika ta farka, bayan ta yi alwala ta zo ta fara ƙoƙarin tashin su A'isha, amma ina sun ki tashi, cewa ma suka yi ba za su yi sallar ba, Adiva ce kawai ta tashi suka yi Sallah tare da Jehan ɗin, sai dai fa dukkansu biyu ba wadda ta san ina ne ainahin gabas a cikin ɗakin, kawai sun fuskanci in da suke ganin ya fi yi musu kama da Gabas ne suka gabatar da sallar su.

Bayan sun idar suka zauna suna askar har gari ya yi haske, still har lokacin ba wanda ya shigo É—akin da nufin zai tashe su ko wani abu makamancin hakan, abin ya bawa Jehan mamaki, kenan su a gidan nan ma ba ruwan su da kayi sallah da karka yi duk ubansu É—aya kenan, Allah ka tsare mu ka barmu da imanin mu, Jehan ta faÉ—a a cikin zuciyarta.

Sai Misalin karfe 8 Aisha da Maryam suka farka daga barci, wanka suka yi sannan suka fito suka shirya cikin kayan su mai bala'i kyau, riga da wando, ita ma Jehan wanka ta yi Adiva ta bata kaya, amma taki sakawa domin kayar gaba ɗaya ba na hankali a cikinta, duk kayan yan iska ne, kayanta da ta tuɓe shi ta ɗauka ta maida jikinta, ko wacce ta gyara gadonta.

Zama suka yi Jehan ta ce "Aisha ina jinki dan Allah ki ci-gaba da gaya mani menene tarihin wannan gida? Da kuma abubuwan da suke aikatawa a cikinta" gyara zama Aisha ta yi sannan ta fata magana tana dariya.

"Jehan sarkin sauri, ai da kin natsuma zaki ji komai, amma tun da kin matsa bari mu ci-gaba, akan Maganar yan lesbian, kin ga wannan part É—in na maki bayani yadda ya kamata sai dai in kina son karin haske a kai" Cikin sauri Jehan ta ce "Ni ina son ki gaya mani ainahin abin da yake saka matan aure zuwa irin gidan nan na Hajiyar daÉ—i ne?".

Guntun tsaki Aisha ta ja sannan ta fara magana kamar haka "Na gaya maki wasu matan auren wlh basu da raayi a kan ire-iren wayan nan abubuwa Hajiyar daɗi ke shiga jikinsu da sunan kawance, sai ta yi ta sakar masu kuɗi, sai sun saba sannan ta jawo ra'ayin su a hankali, idan ke mai kwaɗayin abin duniya ne to sai ki tsinci kanki a ciki dumu dumu, wani lokaci ma baki sani lokacin da zaki faɗa cikin harkar, saboda daɗin duniya, kafin ki farga sai kigan ki kin rufta ko in ce Hajiya ta ruftaki, wa su kuma su da kansu suke neman Hajiya da ta samo musu maza irin ƴan yara shekara 23 zuwa 25 haka, manyan mata fa, sai ki ga sun maƙalewa yara sa'annin ƴaƴan cikin su, irin Hajiyoyin nan ne da mazan su basa zama a gida, irin matan manyan nan, kin gane ai?" Gyaɗa mata kai Jehan ta yi alamar ta gane.

Ci-gaba da magana A'isha ta yi "Wa su matan kuma talaucine ya yi musu yawa, mazansu basu kula da su, basu basu ci da sha a wadace, ga kuma yara sannan ba su sauƙe musu sauran buƙatu da kuma hakkin da ya rataya masu akansu, haka za su sa kafa su fita su bar gida da yunwa ga yara, kinsan uwa kuma ba zata iya jure ganin ƴaƴanta suna kukan yunwa ba, sai kiga ta fita neman taimako, to kin dai san yadda taimakon kasar ta mu ta kasance yanzu, chuɗa ni in chuɗa ka ne, ban gishiri in baka Manda, dayawan mutane basu taimako saboda Allah, sai dai idan za su mori wani abin daga wajen ka suma, kamar wata mata da Zinariya ta zo tana gayawa Hajiya last week, ina jinsu ta ce wlh matar mace ce kyakkyawar gaske ga diri iya diri sai dai talauci ya yi musu katutu, yarta bata da lafiya ta kaita asibiti amma likitoci sun ki su kula yarinyar nan, yarinya kamar zata mutu, amma ba likitan ko Norse ɗin da ta kulasu, wai dan ba su yanki kati ba, kuma ko Naira biyar basu da shi, hakan yasa ta fita goye da yar ta mai shan nono da kuma ɗayar yarta yar shekara 10 dan su je neman taimako, Mahaifin ƴaran nata yana nan yana tura ruwa a kura, to yanzu kin san ruwa a kura ba kowa ke saya ba, yana iya bakin kokarinsa wajen ganin ya basu abin da za su ci, haka matar ta fita neman taimako, ta sha wahala har ta ga ji bata samu komai ba, saboda rayuwar ta yanzu sai a hankali kowa ta kai ta kai yake yi yana neman abin da zai sanya a cikinsa, haka taje wajen wani mutumi ya ce sai ta bashi kanta, da farko taki yarda daga baya da bata da mafita sai ta dawo wajensa ta yarda ta bashi kanta, ta sauƙe yarta na goye ta bawa karamar akan ta riƙe mata suka shiga cikin ɗakin mutumin, bayan ya gama biyan bukatarsa ya ɗauki Naira 500 ya bata ya ce idan tana son karin wani gobe ma ta dawo ya sake biyan bukatarsa ya bata wani 500 ɗin, idan kuma zata bashi wannan yar tata mai shekara 10 ita ma ya kwanta da ita, to zai ba su 1000, ƙinyarda ta yi ta ce ya bar mata yarta ta karɓi 500 tana kuka suka dawo asibiti......" Jehan ta kasa bari Aisha ta dire zance ta tari numfashi ta da cewa

"Iskancin banza dana wofi, bata zuwa ta nemi aikatau ne, sai ta bada kanta, to ba gara yarinyar ta mutuba akan abin da ta aikata, wlh ba duniya ce ta lalace ba zuƙatan mutanen duniyar ne ta mutu murus, ga aiki kala-kala Allah ya yi yawa da su a cikin al'umma, amma ta kasa zaɓar abu guda ta kama dan rufa wa kanta da ƴaƴanta asiri, wlh ban ga laifin mutumin nan ba, laifinta na gani akan me zata bada kanta? Na san cewa azamanin yanzu dama ba komai da komai namiji zai iya ɗauke wa mace ba, shiyasa dama abin da ya fi tun farko kada ki yi zaman banza ki kama sana'a, da ya kasance lokacin bikinki an zuba maki kaya a ɗaki gara abaki kuɗin ki fara sana'a, idan Allah ya sanya mashi albarka kyasayi abin buƙata, dama rayuwar yanzu waye yake ta kayan ɗaki, ku koyawa yara Sa'a a gida shine babban abin riƙewa, da shi za su riƙe miji har ku juya shi, domin idan kina da sana'a har dangin miji ba wanda zai yi gigin kawo maki raini, shima miji zaki ga har wani tarairayar ki yake yi, amma kunzo kun saki jiki an zuba muku kayan kallo idan kuka kafe Tv da ido bakwa tashi kuyi sallah a kan lokaci, ta ina za ku ga daidai? Ni bance maza basu laifi ba, amma mafi yawan laifin na mata ne, ko in ce na iyaye ba zaku binciki sana'ar mutun ba yana samu sosai ko yaya, zai iya riƙe yarinyar ku da abin da zata haifa ne ko yaya, yana da zuciyar nema ne ko zuciyar amace take, amma ku kuna saurin ku aurar da ita ku huta, to wlh in dai haka ne ba zaku taɓa hutawa ba a rayuwar nan, wahala wani na tafiya wani na zuwa, sai ki ga namiji bai da sana'ar arziki amma matansa biyu ko uku, sai ki rasa me iyayen matan suka gani suka aura mashi matar, wani fa ko mace ɗaya da take gidansa ya kasa riƙewa, amma za ki ga wai ya je neman wani auren, kuma sai iyaye su ɗauki yar su bashi, ko da ba abinci a gidan shi, ya je ya buɗe wa yarinya hanyar zina ya kasa riƙeta, ya sake su a gari suna nema suna ciyar da kansu, duk ba ga shi nan ina gani ba, kuma mummy tana bani labari ita da gwaggo wlh idan...." Bata kai karshen maganar ba Adiva ta rufe mata baki

(*Kada ku mance duk wannan surutu da Jehan ta yi, cikin harshen turanci ta yi shi, sannan abu na gaba kada ku mance, duk abin da za ku gani na rubuta dan gane da gidan Hajiyar daÉ—i ko abin da za su faÉ—a a cikinta True life story ne, da gaske ne sai dai akwai abubuwan da na kara a ciki dan ya kawata abun ciki kuma har da shi kanshi gidan Haniyar, amma dai duk wani abin da za ku ji ku gani dangane da gidan gaskiya ce ta faru ne*.)

"Jehan ke dai ba zaki bari mu gama jin labarin gidan nan ba ko?" Cewar Adiva guntun tsaki Jehan ta ja kafin ta ce "Allah Adiva abin ne ya ɓata mani rai talauci hauka ce".

Dariya A'isha ta yi sannan ta ci-gaba da cewa "Ni dai bari na baki iya labarin da ya sawwaƙa, ina ganin dai yanzu mu rufe babin matan auren nan ko..." Tun bata kai ƙarshe ba Adiva ta ce "A'a kada ki rufe ki cigaba da gaya mana".

Jinjina kai Aisha ta yi sannan ta cigaba da cewa "To matan auren dai abubuwa wajen kala huɗu ke kawo su nan, kun ji uku na farko Hajiyar daɗi ke janyo ra'ayin su da kuɗi, na biyu kuma mazansu basu kula da su, na uku kuma talauci, to abu na huɗun kuma wadda shine na karshe ni a iya nawa sanin da yake kawo matan aure cikin wannan harkar, shine masu auren namijin da baya son su, ko kuma mai biye-biyen mata, hakan yakan sa baya kula su baya biya musu buƙatar aure, idan sun ga ji sai su faɗo wajen Hajiyar daɗi neman mafita, wa su kuma kwaɗayin abin duniya, wayan nan sune ke kawo matan aure cikin wannan harkar, amma ni anawa ganin babbar matsalar shine mace ta zauna ba sana'a wato talauci, dan mafiyawancin wayan da Hajiya ke kawo wa nan zaki tarar talauci ya yi masu katutu, idan ka basu kyautar naira ɗari sai su ji tamkar ɗubu ɗari ka basu, saboda ba su samu, wata ma sai ta fi wata guda bata riƙe naira hansin nata na kanta ba, hakan shiyafi yawan kawo su cikin wannan harkar, da za'a samu su kama sana'a abubuwa za su yi sauƙi sosai, yanzu dai mu rufe babin matan aure mu shiga babin maza. Akwai maza a nan masu naman maza, wato yan luɗu, su kuma suna farowa ne daga wasu manya dake lalata su, misali kin ga akwai irin matsafa ko masu zuwa wajen boka, da boka zai ce masu sai sun yi luwaɗi da karamin yaro sannan za su sami biyan buƙatar da suka je nema, wani lokaci ma wani maganin boka ke basu akan su zuba wa karamin yaro a duburansa, to daga haka wasu mazan ke faro luɗu, idan wayan nan sun koya musu sun kuma tafi sun kyalesu basu samun biyan buƙata suna kashe kishin da suka saba da shi, to fa shine suma sai su shiga neman yara suna lallata su, da haka abin yake yawai ta, akwai maza je ma da suke da mata amma ba su son matan sai dai maza yan uwansu shine sai su bar mace tana gantale basu biya mata buƙata, saboda su sun samu sun biya nasu, wata macen sai ta fi shekara ba tare da sun kwanta da mijijta ba, kinga kuwa tunda ba dutse ke da akwai a kirjinta ba, dole ta fita neman mafita, to kin ji na maza kuma shine Hajiyar daɗi take tara su a nan dan saboda business ɗin ta ya kara karfi..." Katse ta Jehan ta yi da cewa "To mutanen ba su iya gudu su bar gidan ne?".

Shiru A'isha ta ɗan yi kafin ta ce "E ni dai ban taɓa jin ance ga wata ta gudu ba, ke gidan nan fa da kin shigo za ki ji baki son fita, wlh da kin yi ido biyu da Hajiya zaki ji ke fa ko mutuwa ba zaki so ta raba ki da gidan nan ba, kuma kin san gidan ne akwai daɗi, idan kin bawa hajiya goyon baya wlh har shopping zata rinƙa sanyawa ana ɗaukan ki kuje a sai miki mayukan gyaran jiki da kaya masu kyau dan saboda ki fito da kyau yadda masu kuɗi za su yi rububinki, babu abin da Hajiya bata saya mana, ni kam ai na sha zuwa shopping tare da ita ma, sau ba adadi, amma idan kika ki bata haɗin kai zaki sha wahala, ni sau ɗaya ma na taba ganin wadda taki yarda ta bawa Hajiya haɗin kai, amma daga baya yarinyar nan tafi kowa zaƙewa a cikin gidar nan, tana nan yanzu ma haka, sai dai yanzu tauraronta ya dishashe bata kawo wuta sosai, ba kowani Alhaji bane idan ya zo zai kwasheta.."

Shiru Jehan ta yi tana tunanin ta yadda zata bar gidan, dan wlh ba zata zauna ba. "Amma A'isha idan Alhaji ya É—auke ki fita kuke yi ne? Ko dai a cikin gidan nan ake gama yin komai?" Yar dariya A'isha ta yi kafin ta ce "Kai Jehan tunanin me kike yi da kika yi mani wannan tambayar?" Girgiza kai Jehan ta yi alamar ba wani tunanin da take yi.

"Akwai alhajin da zai ce fita za ku yi kuje ku yi kwana biyu, akwai kuma wanda zai ce a nan zai biya bukatarsa ya wuce" ajiyar zuciya Jehan ta sauƙe sannan ta ce "Amma Hajiya bata tsoron idan an fita da yarinya ta gudu?" girgiza kai Aisha ta yi tana faɗin "Ai hakan ma ba zai yi wu ba, kin manta na gaya maki duk wadda ta shigo gidan nan ba zata so fita ba? Saboda daɗin shi, sannan kuma ba haka kawai Hajiya take barin wani ya fita da yarinya ba, a'a sai idan ya ajiye maya makudan kuɗi da zata yanka mashi, idan ya dawo da yarinyar kamar yadda ya ɗauke ta, to sai ya karɓi kuɗinsa, idan kuma yarinyar ta sulala ta gudu, shikenan wayannan kuɗin sun zama na Hajiya a madadin yarinyar" "Amma Aisha su alazawan basu tada bala'i aba su kuɗin su?".

Wani irin dariyar shakiyanci Aisha ta yi kafin ta ce "Lallai Jehan baki san waye Hajiyar daÉ—i ba, ke dai kiyi fatar Allah yasa zuciyarta ta soki kema kuma ki sota, amma wlh ni banga wanda ya isa ya nunawa hajiya yatsaba, ke kinga yadda take zarewa manyan mutane ido kuwa? Amma fa kawata Afnan na É—akin gaban mun nan ta ce mani wai abin da yasa Hajiya take zare musu ido su ji tsoron ta wai magani take yi masu, amma fa ni baruwa na ban sani ba" Ta kai karshen maganar tana girgiza kai tare da yarfe hannu alamar ba ruwanta.

Shiru Jehan ta yi tana tunain yadda za'a yi ta bar gidan ita da Adiva.

A wannan hali Zinariya ta shigo cikin ɗakin ta same su, tana sanye da wata arniyar wandon jeans gundu zuwa cinya da yar karamar riga, kamar dai jiya ta ci uban make up kamar me, "Ke Aisha ku fita kuje kitchen ku karɓi abincin ku, sannan idan kun gama ci Aisha ki same ni a office na" tana kai karshen maganar ta wuce ta fita.

Miƙewa Aisha ta yi tana faɗin "Kuzo mu je mu karɓi abinci" "Abinci kuma?" Jehan ta maimaita, gyaɗa mata kai A'isha ta yi alamar e, "Waye mai sayan abincin?" "Kuɗin da muke samowa wajen alazawa mana, da shi Hajiya take bamu abinci mai rai da lafiya sau uku wata sain ma sau huɗu ga mayukan gyaran jiki, turarukan, da kayan sawa, ga su ice cream da su chocolate, shiyasa nace maki zaki ji daɗin zaman gidan nan komai akwai wlh, sai dai muce Alhadulillah, ban da kema da abinki idan Hajiya bata gyara mu ba, ta yaya zamu fito tsab har agan mu ace ana yi da mu".

Zubawa Aisha ido kawai Jehan da Adiva suka yi, ba shakka bariki ya zauna wa Aisha sosai, ta kware a duniyanci ba'a magana, wannan da ba dan sun tabbatar sheɗan shi kaɗai ne bai da yan uwa kanne da yayyuba, da sai su ce tabbas Aisha kanwar shaɗan ce, yarinya kamar shaiɗan ya mata fitsari a kai, wai badon ana gyara su ba ta ya za'a gansu a buƙace su, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Duk wannan zance Jehan ke yin shi a cikin zuciyarta.

Suna zaune a wajen har Aisha ta dawo hannun ta riƙe da plate na abinci sai tiriri yake yi, lafiyayyiyar jolof rice ce, ta ji kayan kamshi da kayan haɗi, ga kwai a gefe guda sai kayan ganye su cucumber and cabbage da sauransu, saman carpet ɗin dake a cikin ɗakin ta zauna tare da ɗaukan spoon ta fara ci, su dai ido kawai suka zuba mata. Ita ma Maryam da ta ga su Jehan ba su da niyar tashi sai ta tashi abinta ta nufi waje dan zuwa kitchen ɗin karɓar nata abincin.

Suna zaune shiru, ita kuma A'isha tana ta kai loma bakinta. Zinariya ce ta sake turo kofar ta shigo cikin dakin, kai tsaye wajen Jehan ta nufa, ba tare da ta yi musu magana ba ta riƙo hannun Jehan suka fice waje. Kai tsaye wani ɗaki ta kai ta, a nan ta zaunar da ita saman wani luntsumemen sofar mai bala'i taushi, bayan ta zaunar da ita sai ta koma saman table chair dake a cikin ɗakin ta zauna tana faɗin "Ki saki jikinki Hajiya ce ta ce kada a baki abincin da ake bawa yan gida, ta ce a rinƙa baki abinci na musamman har sai ta dawo, dan haka yar gold zata shigo maki da abinci yanzu".

"Me yasa ba za'a haÉ—a mu a bamu abinci iri É—aya ba?" Cikin sauri Zinariya ta waro ido tana kallon ta, mamakine ya bayyana karara a kan fuskarta anya yarinyar nan kanta É—aya kuwa? Har ki samu an yanta ki shine zaki yi wata magana, lallai wannan da zafin ki kika zo, amma zama ki yi sanyi ne, duk wannan zancen zuci Zinariya take yi.

Ganin ta yi shiru yasa Jehan ta ce "Duk abin da zan ci, shi Adiva zata ci, domin yar uwata ce ta jini, idan kuma ba za ku bata abin da za ku bani ba, to nima bana buƙata" ta kai karshen maganar tare da miƙewa zata bar wajen. Tsawa Zinariya ta daka mata wadda ya sanya ta dakatawa ba tare da ta shirya ba. "Koma ki zauna!!" shine abin da Zinariya ta ce.

Shiru ta tsaya tana tunanin ta koma ko kada ta koma. A wannan hali wata yar figaggiyar mata ta shigo wadda kuma da alama ita ce yar gold ɗin, domin kuwa ga shi ta yi kalar gold ɗin, fuska golden color kafa bakinkirin kamar zunubi, ta ci bleachin ta ƙoshi, har wani ɗayewa fatar kumatunta ya yi, tsabar ta shafa mai ɗin ya mata yawa, har wani ɗanye-ɗanye fatar fuskarta ta yi, kana iya ganin jan namar ciki, tana sanye da wani kafurin doguwar riga wadda ya matseta sosai, ga bayan nata a shafe kamar anyi pilastar dakali da siminti, ba ta da shape ko kaɗan, amma ba laifi kyakkyawa ce jinin hausa fulani, sai dai tana nan kamar bulala saboda sirranta, abin ba'a magana.

Hannunta ruƙe da ƙatuwar tray mai ɗauke da abinci mai ji da lafiya, fried rice ne ya ji su green beans carrot da sauransu, sai kamshi yake tashi, daga gefe kuma wani karamin plate ne mai ɗauke da haɗin salat, ga gasashen rabin kaza a gefe, sai hollandia ɗaya da ruwan swam water.

A gaban Jehan É—in ta zo ta ajiye tana faÉ—in "Ya na ganta a tsaye?" Fuska a É—aure Zinariya ta ce "Rabu da yar nema wai dole abincin da muka bata shi za mu bawa yarinyar nan da Hajiya ta turota shekaran jiya, wai yar uwarta ce dole ta re za su ci".

Zaro wayan nan shegun idanun nata yar gold ta yi, ga idanun nata saboda tsabar shaye-shaye sun sauya launi zuwa kalar fuskarta, wato golden color, dama kuma idanun nata ba farare bane, sannan gasu a tsaye a bushe kar. Tsawa ta dakawa Jenan "Ke wuce ki zauna ki ci abinci ko kuma na kira madaka katti su É—ura maki abincin nan tas!!".

Kare mata kallo Jehan ta yi tsab, fuska a yatsune ta ce "Idan kuma bani da niyar ci, na ce na ƙoshi fa? Akwai dole ne?" Wani irin bakin ciki yar gold ta ji, ranta a matukar ɓace ta wankewa Jehan fuskarta da mari. Cikin sauri ta dafe kuncin nata, idanuwanta suka ciko da kwalla yau shine karo na farko da aka taɓa marin wannan kyakkyawar face ɗin nata, ga shi marin ya shigeta sosai, tunani ta fara yi shin ta rama ne ko dai ta hakura sai ta gama sanin yadda gidan yake.

"Uban me kike kallo da kika tsareni da ido? Ko zaki rama marin ne? Idan rashin kunya kike ji da ita to gidan ta kika zo, ki wuce ki zauna ki fara cin abinci nan, idan ba haka ba mu yi maki dukan kawo wuƙa". Ba tare da ta yi magana ba ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin.

Damƙo rigarta yar gold ta yi ta janyota baya har sai da ta faɗi kasa, a fusace ta miƙe ta damki wuyar yar gold, domin ta kure hakurinta, ta ɓata mata rai sosai.

Zinariya na ganin haka ta yi maza ta taso suka haɗu suka fara naɗawa Jehan ɗan iskan duka domin su sauƙe mata wannan ji da kan nata, sosai Jehan ta yi ƙoƙarin kare kanta dan kada su ji mata ciwo, amma da yake su biyu ne, sai suka yi mata ɗan iskan dukar kawo wuƙa.

Tun tana iya kuka mai É—an sauti har kukan nata ya dai'na fita, sai da suka ga sun raunatata, sannan suka kyaleta suna mai da numfashi, Zinariya ta koma mazauninta ta zauna, ita kuma yar gold cike da izza da bada umarni ta ce

"Ki yi maza ki tashi ki ci abincin nan ko kuma na kara maki wani dukan wadda sai kin kasa motsi, har mu zaki buÉ—ewa ido? To tun kafin kizo duniya mukenan, iyayen ki ne mu a iskanci da rashin kunya, in dai a gaban mu kike to ba a ma haifeki ba a rashin kunya!!".

Ita dai Zinariya sai haki take yi kamar wadda ta yi tseren gudu, ba karya sun jibji Jehan iya san ransu, sun gwada mata karfin shekaru da iya bariki.

"Wai ba zaki tashi ba ina magana!!" Yar gold ce ta sake magana, ko gezau Jehan ba ta yi ba, kamar bata a cikin É—akin, tana kwance rashe-rashe a kasa tana hawaye tare da fitar da kuka mara sauti sosai.

Ganin taki tashi yasa Yar gold ta kariso wajen ta sanya hannu ta É—agota ta zaunar da ita tare da turo mata tray É—in abincin a gabanta, kin ci ta yi kamar ma bata ga abincin ba. Abin ba karamin fusata yar gold ya yi ba, cikin fushi ta É—aga hannu zata mareta, sai lokacin Zinariya ta sanya baki ta hanyar dakatar da ita, domin ta lura Jehan mace ce mai taurin kai ga kafiyar bala'i, idan suka biye mata to za su ji mata babban ciwo wadda idan hakan kuma ta faru to fa ba makawa sai sun biya Hajiya kuÉ—in da ta sayeta.

Miƙewa ta yi ta kariso wajen a ya yin da take sallamar Yar gold, gaban Jehan ta zo ta tsugunna tana faɗin "Shawarar da zan baki a nan shine idan zaki sauƙe wannan rashin kunya da wani jiji da kai to garama ki sauƙe tun wuri, idan ba haka ba, zaki ci bakar wahalane kawai a banza, domin duk wanda kika gani a gidan nan idanuwansa a buɗe yake, kowa shegen kanshi ne, so is better for you da ki natsu ki bi mu sau da kafa, domin ki zauna lafiya, yanzu ki ɗauki abincin nan ki ci!".

Tamkar babu Jehan a wajen haka ta yi shiru ta kyaleta, domin ta riga ya kafe a kan ba zata ci abincin ba. Ba yadda Zinariya bata yi ba, amma Jehan ta ki ta ci abincin nan, haka ta hakura ta kyaketa ta ce ta koma É—akin su.

Jikinta har kerma yake yi saboda dukan da suka yi mata, haka ta miƙe zuwa ɗakin nasu, tana shiga Adiva ta taso da sauri ta riƙe ta tana faɗin "Jehan lafiya? Me yafaru naga bakin ki a fashe?". Shiru ta yi masu ba magana, zama suka yi saman katifar gadon nasu, Aisha da Maryam dake cin abinci ma suka taso suka zo wajen. Aisha ce ta ce "Sun dake ki ko?" Gyaɗa masu kai Jehan ta yi alamar e.

Jinjina kai Aisha ta yi kafin ta ci-gaba da cewa "Ai in dai kina son zama lafiya da su, to fa sai dai ki yi hakuri ki zauna a yadda suke son ki kasance". Kuka Adiva ta fara yi tana faÉ—in "Jehan dan Allah ki gaya mani ina daddyna, na gaji da wannan bakar wahala, wlh tun da ya fita ya ce zai je gidan ku na jira shi, shikenan bai sake dawowa ba".

Ita ma Jehan É—in wani sabon kuka ta fara yi ba tare da ta yi magana ba.

Wai shin wace ce Adiva, Adiva ya ce É—aya tilo ga uncle Shitu wato abokin daddyn su Jehan, uncle Shitu yana bala'i son Adiva sosai da sosai ita kaÉ—ai Allah ya bashi, sosai abaya suna samun ciki kafin Adiva, wasu cikin zubewa suke yi, wasu kuma ana haifa yaranne basa zama suna mutuwa, Adiva ce kawai Allah ya bar musu, suna bala'i sonta.

Sai da Jehan ta yi kukar rashin mahaifi sosai yau, sannan ta goge hawayen da yake akan fuskar, sai hakuri su Aisha suke bata amma bata kula su ba, sai da ta yi mai isarta tukun nan ta yi shiru dan kan ta, kallon Adiva ta yi cike da kwarin gwiwa da kulawa ta ce "Adiva da daddyna da daddyn ki dukka Allah ya yi musu rasuwa, dan haka yanzu mu za mu yi faÉ—a domin rayuwarmu, dole ne mu san abinyi, su daddy ba za su iya zuwa in da muke ba bare su taimake mu, mu zamu tai maki kan mu da kan mu, yanzu ina son ki gaya mani ina mummy ki?". Sosai Adiva take kukan jin daddynta ya rasu, sun shaku sosai da shi, uncle Shitu ya bata kulawa fiye da tunanin mai tunani, rayuwar farinciki tun ranar da tasan wace ce ita, tun ranar da ta iya tantance mutun da dabba, yau rana tsaka ta yi wani irin rabuwa mai muni tsakaninta da iyayen ta, wannan wace iriyar rayuwace.

Rungume ta Jehan ta yi ta fara bata hakuri, tana bata hakurin ita ma tana hawaye, domin yau ta yi kukan rashin daddunta sosai, da ace daddynta yana nan da wayan nan shaiɗanun ba su isa sun dake ta ba. Sai basu hakuri su Aisha suke yi, amma ina sun ki yin shiru, su kaɗai suka san raɗaɗin dake a cikin zuƙatansu, su kaɗai suka san azabar da suke ji, bayin Allah duk wanda ya gansu a haka sai ya matse musu kwallah.

Sun kwashi mintuna 20 suna shan kukansu, sai da suka ji zuciyoyinsu sun musu sanyi sannan suka raba jiki dana juna, Jehan ta miƙe ta nufi toilet dan zuba ruwa, idan ba haka ba, zata iya sumewa a wajen.

Bayan ta fito Adiva ma ta shiga ta zuba ruwa. After some hours da basu wuci biyu ba. Zaune suke a saman gadon Adiva, dan Jehan ta ce ba zata rabu da yar Uwarta ba, haka ita ma Adiva É—in.

"Adiva ina mummynki?" Jehan ta tambaya tana tsareta da ido, kamar za ta yi kuka ta ce "Mummy ban ganta ba" "Kamar ya ya baki ganta ba? Ina ta je?!" "E naje school na dawo naga gida ba bu kowa sai masu aiki, dana tambayi baba mai gadi ya ce mum ta fita, na jirata har dare bata dawo ba, washe gari masu aiki suka yi girki na yi wanka na shirya zuwa school, na je na dawo ban ga mum ba, bata dawo ba, na tambayi mai gadi ya ce E bata dawo ba, haka har sati ɗaya ban sake ganin mummy ba, na kira layinta bata shiga, shine tun daga lokacin ban sake saka ta a ido na ba, ina cikin wannan hali wa su mutane suka zo wai banki na bin daddy kuɗi kuma lokacin biya ya yi dan haka mu fita a gidan za su yi gwanjon gidan, ni bansan in da zan ga kowa na yan uwan daddy ko mummy ba, kinga daddy shi ɗan Niger ne, mummy kuma ni ban sani ba, to alokacin ban wani damu ba domin ina tunanin kuna gida, haka na haɗa kayana abubuwan da nake buƙata tare da wayata na ce driver ya kai ni gidanku, haka ya ɗauke ni a mota muka nufi gidan ku, tun a bakin babban gate na ku ya sauƙe ni na juya kan motar domin har da motar a cikin gwanjon da za'a yi, na sha kuka lokacin da na je naga gidan ku a rufe, ba bu kowa, nan ne hankalina ya yi mugun tashi, zama na yi a kofar gate ɗin ku ina ta kuka, ban kawo komai a zuciyata na ɓatar daddyna ba, na yi tunanin ko sun yi tafiya da daddynku ne, tun da kunga suna yin hakan wani lokacin, da na zo naga gidan ku a rufe hakan yasa na kara gasgata cewa E tafiya kuka yi, na shiga tashin hankali domin bansan in da zan je in kwana ba, ina zaune a wajen har yamma, da dai naga dare ya fara yi sai na tashi na koma bakin hanya na tari abin hawa dan na koma gida, ina komawa na tarrar an sanyawa gidan mu kwaɗo an rufe shi, nasha kuka sosai shine na zauna a bakin gate ɗin, tun da bani da in da zan je, a nan wata mata ta zo ta same ni, shine ta ce na zo muje gidanta ga gidan nata a can, ita makwanciyar mu ce, ba musu na bita domin ina jin yunwa kuma na gaji. Da muka je gidan matar ta riƙe ni da amana, sai dai kuma mijinta ɗan iska ne, sai cikin dare yake lallaɓawa ya shiga ɗaki na, yana mini baraza idan ban yarda da shi ba sai ya yanka ni...." Cikin sauri Jehan ta katse ta da cewa "Kuma kika yarda?".

Girgiza mata kai ta yi ta ci-gaba da cewa "A'a Allah yana tsareni Allah yana taimakona, ina tserewa duk wani tarko nashi, toilet nake gudu na shiga, ba halin ya buga kofar matar zata ji, sai dai ya hakura ya tafi, daga baya na dawo rufe kofana da key idan dare ya yi, amma dai nasha wahala ba kaÉ—an ba, lokacin da Hajiyar ta gane cewa mijinta yana nemana, sai ta bani laifi ta koreni daga gidanta, haka na bar gidan na fita kan hanya ba ni da mafaka, ranar na sha kuka, kuma duk in na kira layin daddy bata shiga haka ita ma mummy layinta baya shiga, na sha wuyar tafiya a ranar, ga uban trolley da nake ja, to a hanya na haÉ—u da wata Hajiya ta kawo ni gidan nan" ta Kai karshen maganar tana goge hawayen da yake zubo mata akan fuskarta.

"Yanzu ina wayar taki?" Cikin sauri ta miƙe ta buɗe trolley ɗinta ta ɗauko wayar tare da dawo ta zauna ta miƙawa Jehan ɗin. "Dama kin zo da kayan sawar ki ne ɗazun kika bani kaya marasa hankali?" Girgiza kai ta yi kafin ta ce "An hana ni yin amfani da sune a gidan nan, iya kayan da Hajiya ta saya maki su kawai zaki sanya, shiyasa ban baki ba" guntun tsaki Jehan ta ja tare da miƙewa ta wuce izuwa wajen trolleyn, doguwar riga abaya pink color ta fitar tare da mayafinsa, ta ɗauka ta wuce toilet.

Jim kaÉ—an ta fito sanye da kayan a jikinta, da yake ta É—an fi Adiva tsawo, sai rigar bata kai mata har kasa ba

Kallonta Aisha ta yi ta bushe da dariya tana faÉ—in "Amma Jenan kin kai yar duniya, wato tun da an hana amfani da su, ke kin yi kena, wato dai ayi uban da za'ayi, wlh ina jiye maki ni dai". Bata bi ta kansu ba ta koma ta zauna tare da É—aukar wayar Adiva ta fara gwada layin daddyn Adiva wato uncle Shitu, layin akashe kamar kullun haka ma na mum É—inta shima baya shiga, shiru ta É—an yi kafin ta saka nata layin ta gwada shima shiru, mum É—in su shiru, har na daddyn su shima shiru a kashe, a fili ta furta "Wannan wace irinyar bala'i ce, kowa layin a kashe sai ka ce abin haÉ—in baki" Ta kai karshen maganar tare da ajiye wayar ta kwanta tana jin cikinta yana mata bala'i kugin yunwa, kuma ta rantse wannan abincin dai da suka bata ba zata ci shi ba matukar ba tare da Adiva za su ci ba.

Suma kwanciya suka yi suka fara hira, ita dai bata saka masu baki ba, ita ma Adiva da ido kawai take binsu, Aisha da Maryam ke ta zuba kamar kanya

(To fah Jehan kina tsaka mai wuya ni dai na haÉ—a kayana zuwa wajen Rimsha dan muga ya suka je shopping)

Karfe 8 daidai na dare, bayan sun yi sallar isha, sun ci abincin da Rimsha da Akila suka girka, Imran ya ɗauke su zuwa shopping ita da Akila da Umaisha, da farko Akil ya ce Umaisha ba zata je ba, sai daga baya da Imran ya ɓata rai shine fa ya hakura ya ce ta sanya nikaf su tafi.

Sosai Akila da Umaisha suka ɗebi kaya son ransu, ita kuma Rimsha sai nuƙu-nuƙu take yi, domin kunyar ɗibar kayar take ji, da Akila ta lura da hakan ne sai ta fara ɗebar mata, har da su chocolate suka ɗeba, kayan sawa sosai, da suka zo layin breziya Akila da tsiya sai ta juya tana kallon Rimsha ta gani ko dai ta ɗaukar mata ne ko bata fara ba.

Ganin haka yasa Rimsha ta kama kanta ta bar wajen, Imran na zaune daga É—an nesa da su, yana kallon su yana murmushi, abin gwanin ban sha'awa.

Ganin Rimsha ta gudu yasa Akila ta kwasan mata breziyar dozin biyu Æ´an madaidaita, bayan ta É—auka ne sai ta nufi wajen ta, nan ta same ta wajen kayan barci.

"Au a nan kika fi kauri kenan? Tom ni dai na fin son a rinƙa yi wa yaya Ahmad ciko" ko sannu Rimsha bata ce mata ba, dan bata ma gane me take nufi ba, sai dariya Umaisha take yi musu.

Daga nan suka wuce wajen always, kallon Rimsha Akila ta yi ta ce "Kin fara ne na É—ibar maki?". Duka Umaisha ta kai mata a baya tana faÉ—in "Me ta fara? Ke Akila kin lalace wlh, sai na gayawa yaya Akil ayi maza ayi maki aure kada ki wuce gona da iri". Turo baki Akila ta yi tana faÉ—in "Wai ke Aunty Umaisha na kasa da ke ne? Ni da kanwata nake magana, ba dole na tambayeta ta fara bane ko bata fara ba, ko so kike naje na kwaso mata abu kuma azo bata fara ba". Ita dai Rimsha ta rasa gane me ta fara, kwata-kwata ba ta fahinci akan me suke magana ba, domin hankalinta bai kai kan Always É—in ba, yana kan lotion da shower gel dake kusa da wajen, so bata lura da always É—in ba.

"Ke idan zaki É—auka mata gara ma ki É—auka mata, domin dai kin san dole zata fara, baki ga ma har kirjinta ya fara cika bane? To kirji ya cika kuma ai dole a fara".

Sake baki Imran ya yi yana kallonsu yana salati a cikin zuciyarsa, wai yaushe Akila da Umaisha suka iskance haka ne bai sani ba? Lokaci guda tunanin Jelly ya faÉ—o mashi a ransa, in dai Rimsha ta fara period to ba shakka Jellynsa ma ta fara, domin a irin ganin da yake yi wa Rimsha jelly zata fita shekaru, kuma haka ne Jelly ta girmi Rimsha, nan fa ya fara tunanin tare da addu'ar Allah yasa bata fara ba, Allah yasa a hannunsa zata fara, Allah ya bayyana mashi ita, lokaci guda mood nasa ta sauya, har ja idanuwansa suka yi, damuwa karara ya bayyana mashi a kan fuskarsa.

Su kuwa su Akila sai tsula tsiyarsu suke, basu yi tunanin yana ganin su kuma yana jinsu ba. Da suka gama da always sai suka wuce wajen pant, a nan ma sai da suka yi tsiya son ransu, har da wani cewa Rimsha ta fi su mazaunai dan haka ta juyo su gwadata karsu É—auki pant karami wadda ba zai isheta ba, tun Rimsha na nokewa bata biye masu, har ta fara biye masu, suna yi suna dariya, abin gwanin ban sha'awa.

Sai da suka gama kwasan duk abin da za su buƙata, sannan sa ka wuce wajen biya, keken ya cika tab da kaya, dogayen riguna kam ba'a magana, sun kwashesu iya son ransu.

Haka aka yi wa Imran bill ya biya, ma'aikatan wajen suka shirya musu kayan a bayan mota, daga nan suka wuce gida.

Suna zuwa ya wuce bedroom nasa, su kuma a É—akin Rimsha suka baje kayan saman gado, suka shiga rabawa kowa tana É—aukar nata, suna yi suna hira. Ba su suka rabu ba sai da Akil ya kira Umaisha a waya, sannan ta yi masu sallama ta kwashi kayanta ta wuce, ita kuma Akila sai da ta taya Rimsha suka jere kayan a cikin wall-drof sannan ta yi mata sallama tare da kwasan nata kayan ta wuce zuwa cikin gida, bata so rabuwa da Rimsha ba, ta so su kwana tare amma ba dama, domin Ammie ba zata yarda ba, Ammie zata je É—akin ta domin ta dubata, hakan yasa ta wuce ba dan ta so ba.

Ita kuma Rimsha Akila na tafiya ta miƙe ta shiga toilet, wanka ta yi ta fito, yau ga mayukanta da ta saba amfani da su lokacin da daddy yake nan, saman mirror chair ta zauna ta fara shafa Lotions ɗin, ga turaruka kala-kala, dama ba baya take ba wajen son kamshi, haka ta fashe jikinta sosai, sannan ta shirya cikin wasu riga da wando masu laushi na barci, ɗaya ne daga cikin kayan da suka sawo yanzu.

Bayan ta gama shiri, sai ta haye saman bed ta bi lafiyar gado, tare da jan lallausan bargo ta rufe jikinta, ta yi addu'ar barci ta lumshe idanu.

Ni kuma na haÉ—a kayana sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu a gidan daddy wato Washington DC bye

💖TRIPLET'S💖💖

E45_46

💖💖Washington DC💖💖

Zaune suke a palon kasa, Tga, John, Jay, da kuma daddy da Uncle Herry, Kamar dai kullum kowa da abin da yake yi, kowa hankalinsa na kan abin da yake yi, daddy da Uncle Herry suna shan black tea sun matso da glass table date tsakanin sofa set aky blue a gabansu, Jay da Tga suna aiki latsa waya da laptop, shi kuwa John yana kwance dan bai gama samun sauki daga horar da shi da Tga ya yi ba, yau ma kamar dai kullum É—in sharholiyar su suke yi, kowannansu kananan kaya ne a jikinsa, bare ma Tga da shi rigar tasa ma ji yake tamkar ya cireta, saboda dama shi baya san harkar zafi ko ya take, har daddy da Uncle Herry dukka su three quarter ne a jikinsu zuwa gwiwarsu, yanzu daddy baya wani damuwa da rashin James domin kullun sai sun yi waya amma fa a na shi tunanin ne yana waya da James, a zahiriya kuma da Lion yake waya ba James ba.

(To fah🤔)

Lion ke shirya mashi wannan basajan domin basu son abin da zai ɗaga mashi hankali har ya yi sanadiyar taɓa lafiyarsa.

Wani daddaɗar kamshin perfume suka ji, wadda basu taɓa jin irin wannan kamshin a gidan ba, har suna rige-rigen ɗago kai su kalli bene dan suga waye ne mai wannan kamshi, domin ta bene kamshin ke fitowa.

Subhanallah miƙewa Tga, Jay, da kuma John suka yi lokacin guda suna kallon benen, daddy da Uncle Herry kuma ajiye cups ɗin hannunsu suka yi tare da zuba mashi idanu suna kallonsa.

A hankali yake sauƙowa daga benen Musharraf na gefensa sun jero, sai murmushi yake yi. Sanye yake da wandon jeans, cikakken wando ba crazy ba, ba kuma guntu ba, har kasa kuma asalin Jeans wanda babu wani alkus a jikinsa, daga ta sama kuma yana sanye da Round neck polo shirt sky blue, yau ya yanke brown hair nan nasa, duk da cewa dama bata da wani tsawo sosai bata kai na Lion da James ba, baya barinta tayi tsawo dan tana takura mashi a cewarsa, amma yau ya yanketa kusan gaba ɗaya, wadda ta rage a kansa bata wuci kamar na yara kanana wayan da ake yi wa kitson roba ba, dan ko kusan kamuwa wadda ta rage a kansa nasa ba zata kamu ba.

Kafarsa na sanye da Booth sky blue mai bala'in kyau, sai tashin kamshi yake yi, ya sanya glass baka a idanuwansa, fuskar nan tasa har wani kyalli take yi tana curly kamar wadda ya shafa baby oil, yau ya yi dressing na cikakken mutun mai hankali da ilimin tare da class.

Shi ma Musharraf shigarsa kusan iri É—aya da Michael É—in, sai dai shi rigar sa fara ce.

Basu taɓa ganin Michael a irin wannan yana yi ba, ga shi wani irin sihirtaccen gwarjini na jikin William jacop ne ya bayyana akan fuskarsa, kai da gani kasan jinin Lion ne, ya zama cikakken mutun, hannunsa na ruƙe da wayarsa, cikin natsuwa yake takawa har suka sauƙo kasa.

"Hi uncle T, daddy, Uncle Herry hope you are enjoying your afternoon?" Shine abin da Michael ya faÉ—a, ya yi maganar cikin wata irinyar natsuwa kai ka ce Lion ne ke magana a wajen, saboda tsabar natsuwar da ya yi, da kuma yadda ya fito da words É—in, sai ka yi zaton James ne, dan shima James daga bayan nan ne ya fara magana ya É—aga murya, shima yana yi ne dan basaja, amma ba don haka ba, shima kasa-kasa yake magana cikin natsuwa.

"Uncle T why are you stearing at me like this? Why are you people starding? Jay, John hope you are okey?". Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da mamaki, domin yadda suka tsare shi da ido, ga shi sun mimmiƙe suna kallon shi, abin ya ba shi mamaki.

Ganin sun kasa magana ya sa ya ce "Uncle É—in James let's go" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi hanyar fita.

"Where are you going?" Tga ne ya tambaya cike da izza. Ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake yi ba ya ce "Uncle T am i a baby?" "Michael What do you mean by your statement?!" Cewar Tga.

Sai lokacin ya juyo a nutse ya ce " Yes Uncle am I a baby that you asked me where am I going". Tsabar haushi Tga ya ma rasa me zai ce mashi, wato shi ba yaro bane ya wuce a tambayi ina zai je, lallai Michael.

Wucewa ya yi ya barsu da mamaki, Musharraf ya rufa mashi baya, suna fitowa harabar gidan kamar kullun jibga jibgan sojoji ne ta ko'ina a cikin gidan, ko wannan su kuma riƙe da manya-manyan bugayen bindigu, wadda da ka gansu kasan sun wuce wane da wane su riƙe su, na manya ne domin kuma bawa manya tsaro.

Kai tsaye parking space ya nufa, yanzu Lion ya karawa gidan tsaro sosai saboda abubuwan da suka faru, kafin ka shiga parking space É—in sai wata na'ura dake a wajen ta yi scanning naka sannan ka shiga, haka idan zaka fito da mota kamar dai a baya sai na'uran jikin gate É—in ta faÉ—i kalar motar da aka fita da ita da kuma number motar kamar dai second gate, sannan idan ka je gate 2 É—in ma sai ta sake maimaitawa dan tsaro.

Haka Michael ya fito da wata sabuwar motar suka fito suka hau titi zuwa gate 2, sai da nauran wajen ta gama scanning na motarsu tsab, sannan gate ɗin ya buɗe kansa, yana buɗe wa Michael ya danna hanchin motar zuwa babban gate, ba ɓata lokaci jibga-jibgan security dake a wajen suka wangale masu katafaren gate ɗin, da gudun gaske Michael ya danna hanchin motar waje.

"Michael ka ta fi a hankali mana". Cewar Musharraf ya yi maganar cikin yana yi na tsoro, dariya Michael ya yi yana faÉ—in "Uncle É—in James kada ka damu, ko na yi gudu babu wani abin da zai faru, duk da cewa ma ban sanya alamar motar gidan mu bace, amma babu wani abu, bana son kuma na sanya ala'mar motar gidan mu ce saboda bana son magana ya koma gida akan an ganni a masallaci, idan haka ta faru nasan harbemu da gun za su yi mu dukkan mu biyu, shiyasa kaga na É—auko sabuwar mota ba nawa da aka sanni da ita ba".

Mamaki ne ya kama Musharraf, godiya sosai ya yi wa Ubangiji da ya sanya ƙwaƙwalwar Michael ta buɗu haka har yake iya fitarwa da kansa dabarar da zai bi ya tsirar wa wani abin.

A haka suka isa masallaci suna ta hira cikin nishaÉ—i. Babbar masallaci ne sosai, da kusan ma shine babba a gaba É—aya cikin Washington DC.

Kallon Musharraf ya yi kafin ya kashe motar a parking space na masallaci sannan ya É—auki face mask ya sanya a face nasa, ya juyo yana faÉ—in "Uncle É—in James idan na gaya maka nasan za ka yi mamaki, wannan mosque É—in fa Lion ya gina shi, da kuÉ—insa, da shi da wancan babban church da muka wuce a hanyar mu ta zuwa nan, dukka shi ya gina, shi kuma James nasa mosque É—in da church suna ta wajen jam street, nine kawai a cikinsu ban taba gina wajen wani bauta ba, amma In Sha Allah zan gina, su da suke Kristen ma sun gina bare Ni, zan gina very soon sai dai ni ba zan gina church ba gaskiya". Ya kai karshen maganar tare da buÉ—e kofar motar ya fito waje.

*Masjidil Al Sultan* shine abin da yake rubuce a saman masallacin, "Asif who is Al Sultan?" Shiru Michael ya É—an yi kafin ya ce "Like he is the one da yake control na mosque É—in, domin lokacin da aka gama ginin Lion ya bani kuÉ—i na kawo mashi wai za su sayi wasu abubuwa na masallacin, alokacin shikuma ya tafi church dan ranar akwai church, sai ya ce in kawo wa Sultan, da na zo na tambayi waye Sultan sai suka nuna mani shi, gently man ne, yana da innocent face, baya da yawan magana, but is an old man sosai". Shiru Musharraf ya yi yana tunanin da alama Lion ba zai yi wuyar shiga addinin Musulunci ba, domin yadda yake taimakawa musulmai, duk da cewa ba iya musulmai kawai yake taimakawa ba, har da addininsa wato Kristen da kuma yan bautar gunki da sauransu, duk wasu gidan bauta yana kai musu taimako, baya ware ko É—aya daga cikin su, amma Musharraf yana yi mashi kyakkyawar zato akan ba zai yi wuyar musulunta ba.

Yau dai a masallaci suka yi sallah cikin farinciki da annashuwa, cikin natsuwa.

Bayan sun idar da sallah suka fito waje, nan suka isko jama'a sosai a wajen harabar masallacin. Hannu Michael yasa a aljihunasa nan ya fito da kuÉ—i sosai, haka ya shiga rabawa musulman da suka fito Sallah a tare, ya zura É—ayar hannunsa cikin aljihun baya ya ciro wasu kuÉ—in ya bawa Musharraf dan shima ya raba sadaka. Allah sarki jinin William jacop ba dai kyautaba, gaba É—aya Triplets suna da kyau da akwairi sosai, ba su jin kyashi wajen bayarwa, haka zalika idan za su bada basu duba cewa wanna ba addininsu É—aya ba ba zasu ba shi ba, a'a duk da cewa basu son wata addini sai nasu hakan baya hana su bawa kowa kyauta idan suka ta shi. Ikon Allah kenan

Wani bawan Allah da Michael ya bashi kuɗin, duƙawa kasa ya yi ya fuskanci gabas ya yi sujudur shukur yana hawaye, taɓa Musharraf Michael ɗin ya yi yana tambayar sa me yasa wannan mutumin kuma ya yi sujjada ba lokacin sallah ba, a takaice Musharraf ya warware mashi me sujudur shukur yake nufi.

Jin haka yasa Michael ya duƙa suna fuskantar juna da mutumin, cikin mutuntawa ya ce da mutumin "Me yasa yake jin matukar daɗin dan ya ba shi wannan ɗan kuɗin?".

Mutumin yana hawaye ya fara magana "Yau tun da na shigo masallaci nake ta rokan Allah da ya bani abin da za mu ci ni da family na, lokacin da na yi sujjadar karshe a sallah har hawaye sai da na yi dan yau kwana biyu ba'a yi girki a gida ba, Alhadulillah, Allah shine arrahman mai rahama akan bayinsa, shine wadda idan ka roƙe shi da kyakkyawar niya da kuma yakinin bayan shi ba mai iya baka, to zai cika maka burinƙa cikin ƙanƙanin lokaci, sai ga shi ban bar masallacin ba Allah ya biya mani bukata ta da na roƙe shi, Alhadulillah Alhadulillah, Allah ne ya bani ta sanadiyar ka, ina godiya ɗan uwana" ya kai karshen maganar tare da miƙe wa ya nufi hanyar fita daga masallaci.

Dawo da kallonsa kan Musharraf ya yi domin ya yi mashi karin bayani dan gane da mutumin nan, ai kuwa tun bai tambaya ba Musharraf ya fara yi mashi karin baya ni, daga karshe ya rufe da cewa "Mutumin yana da karfin imani, idan da wani ne, kai zai ta zubawa godiya yana faÉ—in ka taimake shi ka bashi kuÉ—in sayen abinci, amma da yake wannan yana da imani ya san ya kamata, sai ya fara godewa Allah sannan ya gaya maka da bakinsa cewa Allah ne ya bashi ta sanadiyar ka, wannan shine gaskiya, idan da wasu ne cewa za su yi kai ka basu, irin mutanen nan basu da yawa sosai a duniyar yanzu".

Yana kai aya a maganarsa Michael ya jawo hannunsa suka nufi mota, bai yi magana ba dan yasan dole akwai dalilin da ya sanya Michael ya yi hakan.

Bayan sun shiga mota sai ya kunnata suka bar masallacin.

"Michael ina kuma za mu je? Ka mance cewa za mu jira sai anyi sallar la'asar ne kafin mu koma gida?" "Uncle ban mance ba, ai ba gida za mu koma ba, kai dai ka jira ka gani" to kawai Musharraf ya amsa da shi, sai gudu yake shararawa da motar har suka fita daga kan titi suka tsallaka cikin wata unguwa, wadda da ka ganta ka san yan unguwar nan takaici ya yi masu katutu.

Haka ya ci-gaba da kutsawa motarsa cikin wannan anguwar. Bakin wani gida wadda da ka ganshi kasan talauci ya yi masu katutu over, a nan ya juya kam motarsa suka sake fitowa daga unguwar suka nufi wata tampatsetsen Super market, wadda ya amsa sunan sa super market.

A bakin gate É—in shiga Super market É—in tambarin sunan James ne a wajen, hakan na nufin Super market É—in mallakin james ne.

Ciki ya kutsa motarsa, bayan ya yi barkin ya fito, suka shige cikin shopping É—in, kai da ga ganin wannan wajen kasan babu abin sa zaka nema ka rasa, mutun ne kawai basu saidawa.

Kayan abinci Michael ya fata loda da abubuwan amfani na gida, ciki har da fridge mai ɗan girma, sai binshi da ido kawai Musharraf yake yi, duk wani abin da yasan ɗan adam zai buƙace shi a gida sai ya nunawa ma'aikatan dake binsa a baya, masu kula da masu sayan kaya dan su taimaka masu ta in da suka gaza, idan ya nuna masu sai su fitar mashi.

Sai da ya lodi kaya har sai da Musharraf ya ce mashi ya isa haka nan, ina zai kai uban kayan nan haka? Bawan Allah tausayi ya rufe mashi ido, anguwar talakawan nan ya tayar mashi da hankali, mutumin da ya bawa kuɗi a masallaci nan ya tsaya mashi a ransa, kuma hakan yasa ya bi bayan mutumin har zuwa anguwar su, a nan ya ga tashin hankali, domin sosai ya rinƙa karo da yara ba takalmi a kafarsu, suna kuka riƙe da kwano a hannunsu alamar suna jin yunwa, kawai hakuri ya yi ya daure ya kawarda kansa domin ya bi bayan mutumin kada ya ɓace mashi, da suka je ya ga gidan ne sai ya juyo suka zo wannan shopping ɗin.

ÆŠaya daga cikin motoncin super market É—in ne ta kwashi duk kayan da ya saya, dama suna da manyan motonci masu baya wadda idan ka yi shopping É—in da motarka ba zata iya kwashe su ba, sai su É—aukar maka da motorsu su kai maka har in da zaka je, kuma kyauta ne shi wannan kai kayar.

ATM nasa ya bada suka ciri kuÉ—in kayan, sannan aka loda su a bayan motar, shi kuma shi da Musharraf suka shiga nasu motar suka yi gaba motar super market É—in ta rufa masu baya.

Kai tsaye kofar gidan wannan mutumin da ya bawa sadaka a masallaci suka nufa, a wannan karon daga É—an wajen anguwar ya yi parking na motarsa ya fito suka kariso da kafarsa da Musharraf, wancan karon da kyar ya iya fitar da motar tasa daga unguwar ne, shiyasa yanzu ya barta a waje.

Knocking na kofar gidan mutumin ya yi, kofar katako ce taci wuya sosai, wannan karamin yaro ma idan ya bugata da karfi zata ɓalle, ta sha ruwa sosai ga rana, duk ta zazzage.

Daga cikin gidan wata mata ta amsa da ana zuwa, komawa gefe ya yi ya tsaya yana jiran fitowar su, yan unguwa kuma sai kallonsa suke yi.

Mutumin da ya bawa kuɗin a masallaci ne ya fito, ganin su yasa ya fara ba su hakuri ya ɗauko kuɗin da Michael ɗin ya ba shi daga aljihunsa da nufi ya mai do musu da shi, dan a tunaninsa kuɗin su suka zo karɓa, Michael ya sanya face mask ga glass ba wanda ya gane wanene, nan take yan unguwa suka fara fitowa suna karisowa wajen dan su ji menene.

Mutumin nan kuka yake sosai yana gaya musu idan ma wani laifi ya yi mu su to dan Allah kada su taɓa mashi familynsa shi su hukunta shi, idan kuma kuɗin su suka biyo to ga kuɗin nan dama yanzu zai je ya sawo masu abinci, yana magana yana hawaye gwanin ban tausayi, dan a irin kallon da ya yi wa dressing ɗin jikin Michael yasan ko a ƴaƴan manyan kasar ma sai wane da wane za su saka irin kayan, hakan ne ma yasa ya kara tsorita sosai da sosai.

Matsowa kusa da shi Micheal ya yi ya rungume shi, dama shi ma ba baya ba wajen ruwan hawaye, nan take ya fara nasa hawaye, dan har ga Allah zuciyarsa ta yi mugun taɓuwa ganin mutanen nan cikin wannan hali, Allah sarki tun bai san menene falalar sadaka ba ma tukun nan, domin karatunsa bai kai nan ba, yana da tausayi sosai, dama ciwonsa ta mai da shi mara tausayi mara imani, ina da yakinin yawan sadaka da kyauta da yake yi ne ya sanya Allah ya cito shi daga duhun kafurci izuwa hasken musulunci.

Wayan su yaran mata kanana guda biyu ne suka fito daga cikin gidan, dukkansu mata ne ba za su wuci yan shararu 6 zuwa 8 ba, sakin mutun Michael ya yi ya riƙo hannun yaran yana tumbayarsu menene sunan su, tsoro ya hana su gaya mashi sunan su, sai kallon babansu suke yi, ciro handkerchief daga aljihunsa ya yi, ya gogewa mutumin hawayen da ke a kan fuskarsa, shi ya sanya face mask a fuskarsa nasa hawayen bai bayyana ba, sannan ko kaɗan bai ji kyamar mutumin ba, duk da yake talaka yana da tsabta sosai, jikinsa tsab, shiyasa ma ya rungume shi ba tare da ya ji kyama ba, haka kuma yasa ya goge mashi hawaye da handkerchief nasa ba tare da ya ji wani abu ba.

"Baba kana da yaro namiji". Michael É—in ne ya tambaya, sai kallon shi mutumin yake yi da ya yi magana, domin yana son gane wanene, amma Michael bai bari hakan ta faru ba, saboda bai son asan ya je masallaci, idan aka sani a gida, yana da tabbacin wlh kashe shi za su yi, sai dai su kashe shi suna kuka, amma sai sun harbe shi.

"E ina da yaro amma karamine 15 years yake da shi" to Michael amsa da shi sannan ya ce ya kira mashi yaron, wayan nan yara biyun da suka fitone, ɗaya daga cikin su baban ya aika ta kira mashi yaron, shi kuma Michael ya sanya wayan nan ma'aikata super market kwara biyu da suka biyo su akan su sauƙe masu kayan abincin.

Ba ɓata lokaci suka fara sauƙe abin cin, da kansa ya raba abincin ya nuna masu wadda za su shigar wa da baba cikin gidansa, saura kuma su rabawa mutanen unguwa, har kasa baba ya duƙa yana hawaye, ganin farincikin da yake a kan fuskar bawan Allah nan sai da ya sanya Michael zubar da wani hawaye, ba zai iya jure ganin yadda jama'a ke ta yi mashi ruwan hawaye suna duƙawa suna zuba mashi godiya ba, dan haka sai ya kama hannun yaron baba da ya fito yanzu suka ɗan koma gefe suka bar wajen.

"What is your name?" Ya tambaya yana shafa kan yaron, yaron ga shi kyakkyawa, ga innocent face irin na babansa, da gani ya samu tarbiya irin ta addinin Musulunci, ya samu ilimin addini sosai, a nutse sosai yake.

"My name is Aryan" yaron ya bashi amsa, maimai ta sunan Micheal ya yi yana kokarin tunano a ina ya taɓa jin wannan suna, sai bayan wasu yan sakannin sai ya tuna ashe sunan da Musharraf ya ba shi ne farkon musuluntar shi, yar murmushin ya yi, Micheal kenan duk gidan William jacop shi kaɗan ke murmushin, ko su John basu murmushin, shima ɗin da addinin musulunci ta ratsa shi ne ya san e murmushi Sunnah ce da fiyayyayyen halitta manzon tsira manzon Rahma Annabi Muhammad (SAW) hakan yasa yake yin murmushin sosai a yanzu, bayan shi ba wani mai murmushi a cikin su, Lion da Tga kam ai dama su sai dai ma ace zuciyar kafuran farko ce ko kuma dutse ne a kirjinsu saboda kwarewar su a zafin kai, zafin zuciya, da mugunta.

"Matakin karatun ka fa a ina ka tsaya?" Nan Aryan ya gaya mashi yana Jss 2 kuɗin makaranta ya kare ya dakata da karatu bai cigaba ba, shiru ya ɗan yi kafin ya sake cewa "Idan na buɗe maka business zaka iya zama har ka kula da shi ka taimaki iyayen ka da yan uwanka?". Michael kenan akwai kaifin basira, ya san cewa ka bawa mutun kuɗi ko abinci idan ya zo neman taimakon abin da zai ci ba shi ne ba, idan ka ba shi kuɗi ko abinci cikin ƙanƙanin lokaci zai cinye su, amma idan kana da hali ka taimaka mashi ka gina shi akan sana'a to nan ne ka yi mashi babbar taimako wadda koda million nawa ya samu agaba duk lokacin da ya taimaki wani ɗan adam da wannan kuɗi kai ma kana da lada sosai, kuma bashi sana'a da zaka yi hakan zai sanya zuciyarsa ta yi kwari ta ki mutuwa, zaka karfafa shi ya miƙe da kafafunsa, Michael akwai kwakwalwa wajen tunanin tun da Allah ya buɗe mashi ƙwaƙwalwarsa sanadiyar addua'o'i da Musharraf ke yi mashi, wa su addua'o'i ya tofa mashi a ruwan sha, wa su kuma a kan nasa yake tofa kashi, hakan yasa ƙwaƙwalwarsa ta fito da asalin kaifinta, gaba ɗaya yaran William jacop akwai su da kaifin kwakwalwar balai, har shi kan shi daddy yana da ƙwaƙwalwar domin lokacin da yake school kullun shine first class, mara kwakwalwa ba zai iya zama babban likita kamar shi ba, sai dai shaye-shaye da ya rinƙa yi bayan ya fara tsufa ce ta taɓa mashi lafiya, amma shima ba baya ba wajen kaifin basira.

Cikin sauri Aryan ya ce "E zan yi sana'a koma wace iriya ce" "To gaya mani idan ka samu kuÉ—i sosai a wajen business É—in me zaka fara yi da su?" Ba tunani ba komai kai tsaye Aryan ya fito da amsoshinsa, ta yadda zaka san abin yana ransa sosai.

"Zan mai da su Suhana school, zan je in biya masu school fees, daga nan in sawo abinci sosai in kawo gida, dan baba ya daina shan wahalar neman, kullun idan ya fita sai kaga ya dawo a gajiye, wata sa'an ma sai ya dawo ya shiga ɗaki ya yi ta kuka, kuma duk saboda abinci, saboda bai kawo abinci ba, su Suhana suna kukan yunwa, ina jin zafin hakan, tom abinci shine abu na biyu da zan kawo gida, na uku kuma kullun ranar Jumma'a zan rinƙa sawa ana girka abinci sosai ana kaiwa masallaci domin wayan da basu da shi su rinƙa samu suna ci a can, na huɗu kuma zan rinƙa koyawa kannena sana'a, ma'ana idan sun sami hutun makaranta akwai in da ake koyar da sana'o'in sosai, can zan je na biya kuɗi su rinƙa koya, dan karda su taso ba su iya wata sana'a ba, suce sun dogara da baba, bayan kuma shima fama da kansa yake yi, na biyar kuma...." Michael bai bari ya karisa ba ya rufe mashi baki yana faɗin "Irin ku ake bawa jari wayan da suka san abin da suke yi, ga shi yanzu a maganar nan taka kasa na samu karin wata haske, dole nima zan nemo kwararru wajen iya girki, arinƙa dafa abinci ana kaiwa masallatai dan marasa karfi su ci".

Sosai Aryan ya ji daɗin yadda Michael ya karɓe shi hannun bibbiyu, a wannan hali Musharraf ya isko su, nan ya tambayi meke faruwa, Michael ne ya labarta mashi yadda suka yi da Aryan, ba ƙaramin daɗi Musharraf ya ji ba, ya yi murna sosai hakan yasa ya kara karfafa masu gwiwa ta hanyar gaya masu falallar sadaka, duk masifar da musulmi yake ciki, matikar zai juri yin sadaka, tofa Allah subhanahu wata'ala shi ka kansa ya yi alkawarin ya ye mashi wannan damuwa, sannan aduk sadaka da mutun zai yi babu sadakar da ta fi falala irin sadakar abinci, tana da falala fiye da tunanin mai tunani, cikin kankanin lokaci Allah zai warware maka damuwar ka, matukar zaka juri yin sadakar abinci koma ya ya take.

Wani karin karfin gwiwa na musamman Michael ya ji a tattare da shi, lokacin guda ya ji zai iya karar da duk wani abin da ya mallaka akan sadaka da taimakawa bayin Allah.

Da wannan shawara Michael ya ce da Aryan gobe zai dawo su je ya duba irin sana'ar da zai iya sai ya buÉ—e mashi shago a kasuwa, sannan batun makaranta zai je har school É—in ya biya masu kuÉ—in makaranta, daga haka suka koma wajen baba, already ma'aikatan Super market É—in James sun gama rabon kaya sun shigarwa da baba nasa cikin gida, sun koma wajen aikin su, wato sun koma super market É—in, jama'a sun watse.

A kofar gidan Michael ya tsaya ya ce da Aryan ya kira mashi babansa suyi sallama, da sauri Aryan ya shiga cikin gida, shi kuma Michael É—in suka cigaba da hira da Musharraf, yana kara gaya mashi falalar taimako da sadaka.

A haka baba ya zo ya isko su, ya ce su zo su shiga cikin gida, fuska ɗauke da murmushi Michael ya ce a'a nan ma ya isa tafiya za su yi yana son sanin ko akwai wani abin da yake buƙata ne, cikin sauri baba ya ce a'a baya bukatar komai ya kara da zuba masu ruwan albarka da godiya sau ba adadi.

Ganin godiyar baba ba zai kare ba ya sa Michael ya yi musu sallama, Aryan ya raka su har wajen mota, Michael yana jin kaunar Aryan a ranshi tamkar ɗan uwansa na jini, tsabar farinciki har ya rasa me zai bawa Aryan, sai ya ɗauko ruwa daga cikin motar tasa roba ɗaya ya miƙa mashi, sai murmushi Musharraf ya ke yi, haka suka ja motarsu suka koma masallaci.

A ɓangaren Lion kuwa.

Sai karfe 8 na safe ya farka daga barci, a hankali ya waro dara-daran blue eyes nasa, sai wani kyalli fuskarsa take yi, wow yau ya sami barci mai daɗi, ga yanayin gari ga shi kuma yana wani irin yanayi mai daɗi wadda shi kaɗai ya san menene silar shigarsa wannan yana yi, a hankali ya janye lallausan bargon dake jikinsa, shiru ya ɗan yi na mintoci yana tunanin akan mafarkin mum ɗin su da ya yi daren ji, me yasa take yawan zuwa mashi a mafarki a cikin wata iriyar suffa mai wuyar gane wa, yana buƙatar amsa akan hakan.

Ya jima kwance yana ta zarin abubuwa guda biyu, na farko mum ɗinsa, na biyu kuma tafiyar da zai yi gobe. Bayan wani lokaci a hankali ya zuro kyawawan fararen kafafunsa kasa kafin ya miƙe gaba ɗaya, ya zauna a bakin gadon, bin ɗakin nasa da kallo ya fara yi, tun karfe shida na safe Tga ya gyara mashi ko ina ya feshe ko ina da daddaɗar air freshener sa mai bala'in kamshi da kyau da tsada, kasa tiles ɗin ɗakin tsabar haske kamar madubi, da yake tiles ɗin fari ne kana iya ganin kanka a ciki, ga shi yana samun gyara, sai ka rantse da Allah kafa bai taɓa taka shi ba saboda haske.

Jawo laptop nasa ya yi domin ya yi bincike a cikin camerar da ya sanyawa mum ɗin sa a kofar gate ɗin shiga gidan ta, saboda yana son gane gaskiya tsakanin ita da daddy, waye ya cuci wani, sannan kuma yana zarginta da shiga irin kungiyar su James, domin wayan can mutane guda biyu da ya taɓa kamawa, ya kama sune da manyan kwayoyin maye da kuma sun yi wa wata yarinya fyaɗe, daya tambaye su shine suka gaya mashi cewa kayan mayen Josephine za su kai wa, ita tayi oder su, sai ya yanke mu su gaba na fyaɗen da suka yi, ya kuma miƙa wa Tga su dan ya yi mu su hukuncin dillancin kayan maye da suke yi, wannan dalili yasa ya sanya mata camera a kofar gidan ta, domin shi baya yanke hukunci da kai kawai, baya yanke hukunci daga jin zance daga bakin wasu, no sai ya yi bincike yake hukunci.

Kunna laptop É—in ya yi yana wani lumshe dara-daran idanuwansa alamar akwai wani abin da yake tunawa.

Baki ɗauke da excuse Tga ya shigo cikin ɗakin, hannunsa ruƙe da cup mai bala'in kyau sai ɗaukan ido yake yi fari kal da shi, ɗan cup ɗin yana ɗaure ne saman wani kyakkyawan plate karami mai bala'in kyau, hot coffee ne a cikin cup ɗin, sai turiri yake yi.

Kusa da Lion ya zo ya zauna tare da miƙa mashi coffee ɗin, shiru Lion ya yi bai karɓa ba kuma bai juyo ba. Idan da sabo sun saba da halinsa hakan yasa ya ce "Good morning sir" nan ma shiru aikin da yake a gaban sa kawai yake yi.

Almost 10 mins sannan ya ɗan juyo da kallonsa kan Tga ɗin, calmly ya fara magana "Ni na ce maka ina buƙatar coffee ne?" Cikin sauri Tga ya ce "No sir kawai dan naga kasha jiya ne that is why na yi tunanin Maybe zaka buƙata a yanzu ma".

A maimakon ya ba shi amsa sai ya ce "Tafiyar sirri zan yi, ko daddy ba zan gaya ma ba, but idan ya tambaye ka just tell him the truth akan cewa na yi tafiya, and then ka kula da lafiyarsa sosai, ni kaɗai zan je za mu yi waya". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya shiga toilet, bin shi da kallo Tga ya yi yana mamakin hali irin na sa, tabbas ko a magana ba zaka taɓa gane in da ya dosa kai tsaye ba, yana magana ne a murɗe kamar yadda yake shima a murɗe, yanzu maganar da ya yi a nan wajen Tga ya kasa fahimter ina maganar ta dosa kai tsaye, zaman ka lafiya shine kawai idan ya ce ka yi abu, tofa kawai ka yi shi, idan ba haka ba, ka ce sai ka binciko ka gane asalin in da abin ya dosa, tofa zaka shekara babu abin da zaka fahimta, karɓar umarni ya fiye maka sauƙi in ba haka ba ƙwaƙwalwarka ta tarwatse.

Yana tsaka da tunani sai ya ji laptop ɗin Lion dake a gabansa ta yi yar kara, ɗaura cup ɗin ya yi saman bedside drawer ya jawo laptop ɗin ya fara dubawa, abin mamaki kuma abin al'ajabi da Tga bai taɓa sammani ba shine ya gani a cikin laptop ɗin.

Zaro idanuwansa sosai ya yi yana kallon abubuwan dake a ciki, É—ago kai ya yi ya kalli kofar toilet É—in, afili ya ce "Jinjina mai girma, a ya za dole ka yi tafiya, kuma ya zama dole jiya ka shiga yana mai daÉ—i" ya kai karshen maganar tare da fita daga wajen ya shiga bincike akan ina aka tsaya dan gane da wayan da suka kama James.

A wannan hali Romeo ya fito ya same shi ɗaure da towel a kugunsa, ga kuma wani ƙaramin a hannunsa yana goge dark black curly hair sa da shi.

Gaban mirror ya zo ya tsaya ba tare da ɓata lokaci ba ya shafe jikinsa da Lotions nasa masu kyau da tsada, da ga nan ya gyara gashin kansa tare da shafeshi da mayuka gashinsa masu kyau da tsada, ya fesa perfume nasa mai bala'in kamshin nan, wadda tun kafin ya iso waje perfume ɗin yake riga shi isa saboda bala'in kamshinta, already kamshin ta kama jikinsa, ko bai saka ba kamshi yake yi sosai, amma kullun sai ya sa, ya riga da ya saba.

Bayan ya kammala ya wuce dressing room nasa. Komai nasa a nutse yake yi daki daki, É—aya na bin É—aya, a nutse ya shirya cikin Ripped Jeans blue color da high neck t-shirt black color, ya É—aure gashin nan nasa a baya, ya bar wannan guntu na gaban goshin nasa, sai tashin fitinannen kamshi yake yi, ya yi wani masifaffen kyau, sai kyalli fuskarsa take yi, ga idon nasa wani irin idan ka gansu sai ka rantse da Allah kwalli yake saka masu saboda tsabar kyau.

Ko sannu bai ce da Tga ba da ya fito, wayarsa kawai ya É—auka ya nufi waje, palon kasan babu kowa a lokacin, kai tsaye waje ya nufa.

Yana fita dubbanin jibga-jibgan sojoji dake harabar gidan suka fara É—aga hannu suna sara mashi, ji kake dim sun buka kafa a kasa alamar girmamawa, ko mutun É—aya bai É—aga ido ya kalla daga cikin su ba, gaban sa kawai yake kallo, kai tsaye ya wuce cikin lambun daddy dake cikin gidan.

Akwai wata rumfa mai bala'i kyau da akaiwa daddy a cikin lambun dan hutawa, da zana irin na zamani aka yi shi, an jera wasu irin kujeru wadda aka yi su da wani irin abu kamar zana, kujerun nan sun haÉ—u ba kaÉ—an ba, launin dark brown suke, a tsakiyar su kuma sai aka sanya tables mai bala'in kyau shima, gaba É—aya rumfar kewaye take da wasu irin fitillu masu bala'in kyau suna bata hasken wuta kala biyu, su bada blue su kuma bada fari, ga shuke-shuke iri daban-daban a cikin lambun, akwai fruits kala-kala har da bishiyar tuffa wato apple abin ba'a magana sai wadda ya gani, amma dai lambun ya haÉ—u sosai.

A saman ɗaya daga cikin kujerun ya zauna tare da tura massage akan a kawo mashi fruits da maltina. Ai kuwa ba ɓata lokaci sai da jibga-jibgan bodyguard guda uku sun doso wajen, ɗaya hannunsa na ruƙe da kwanton fruits irin wanda ake yin sa kamar sakarnan, kwandon ba shi da zurfi sai faɗi, amma yana da bala'i kyau sosai, sun shaƙe shi da fruits kala kala wayan da ba'a yanka ba, ɗayan bodyguard ɗin kuma yana ɗauke da wani katon plate mai shaƙe da fruits kala-kala wayan da aka yanka su, bayan an yanka su kuma sai aka sanya fork spoon a cikinsu ta yadda mai sha zai rinƙa ɗauka kawai yana kaiwa baki, sannan an rufe plate ɗin da wani plate shima mai kyau, dan kar wani abin ya hau kan fruits ɗin, shi kuma bodyguard na karshe ɗauke yake da plate mai ɗauke da maltina guda uku sa glass cup mai ɗan karen kyau, irin dogayen glass cup ɗin nan ne, wanda kasansu yake a baje, a ɗayar hannunsa kuma yana riƙe da tissue a cikin abin sanya tissue ɗin.

Kai tsaye saman table ɗin gabansa suka zo suka ajiye mashi, sannan suka tsaitsaya a gefensa suna jiran umarni, ko kuma ko zai buƙaci wani abin. Kwantar da kansa ya yi a saman jikin bangon kujerar sannan ya ɗaga kan nasa sama tare da lumshe idanuwansa, bai ce da su ko uppan ba.

Almost 10mins suna a tsaye, daga karshe sai ya yi masu alama da hannunsa akan su tafi ba tare da ya buÉ—e ido ba, kuma bai yi magana ba, É—an dukar da kai kasa suka yi kafin su wuce cikin gida, a al'adar su yin hakan shine girmamawa.

Shi kuwa haka ya cigaba da zama shiru a wajen idanuwansa a lumshe da alama wani abin yake tunani.

(Ni kuma na haÉ—a kayana izuwa Nigeria dan naga yadda abin zata kaya, Lion sai na dawo, wata kila kafin lokaci ya É—an ci wani abin Bawan Allah)

Bari mu fara da maman Sadiq Katsina mu gani.

Sosai suka ji daɗin wannan kuɗi da Imran ya basu, zuwa maman Sadiq ta yi ta ɓoye kuɗin har sai da Sadiq ya dawo daga wajen aiki da daddare, bayan sun ci abinci sun yi sallah ne suka zauna take gaya mashi abubuwan da suka faru, sosai ya taya Rimsha murna, a cikin zuciyarsa kuma yana kukan rashin Jehan dan yana bala'in sonta.

Maman sa ne ta tambaye shi ya za su yi da kuɗin, nan fa ya kawo shawarar akan su kama hayar shagon nan da yake ɗan gaban layin nan nasu kaɗan, tun da ance za'a bada shi haya, kuma bashi da wani tsada 20k ne kuɗin hayar shekara, to su kama sai su sawo kayan provision da sauran 180k ɗin su zaba a ciki shigon, sai Yusuf ya rinƙa zama a ciki yana kula da shi, shi kuma sha'aban ya rinƙa bin shi suna tafiya gareji a tare, sosai maman Sadiq ta ji daɗin shawarar ta kuma karɓa hannu bibbiyu, shima Yusuf ya ji daɗi sosai ko ba komai zai bar zaman banza alayi, kuma zai rinƙa samu ɗan na kashe wa.

Da haka suka yi ta hirarsu cikin farinciki har can dare wuraren karfe 10 sannan suka yi sallama da juna suka wuce ɗakin su, ita kuma maman Sadiq ta miƙe ta rufe kofar ɗakinta ta haye yar katifar ta ta kwanta, cike da farinciki ta yi barci. Asuba ta gari.

A ɓangaren Su Rimsha kuwa.

Tun karfe bakwai na safe Akila ta baro part nasu zuwa nasu Rimsha É—in, domin yau babu school sai murna take yi za ta wuni tare da Rimsha.

A palo ta isko Imran yana zaune yana kallon News a Tv, kusa da shi ta zauna suka gaisa cike da kaunar juna, sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Rimsha tana gaya mashi ba wajen shi ta zo ba, dan haka ta tafi wajen wadda ta zo, sai murmushi kawai yake yi abinsa.

Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga bedroom ɗin, Rimsha sarkin son gayu da kwalliya, wani irin fitinannen kamshi ne ke tashi a cikin ɗakin, ta sha wankanta ta yi fes, tana sanye da doguwar riga fari tas mai bakai kyau, an yi mashi kwalliya da wasu duwatsu jajaye masu bala'in kyau, sannan ta gyare ko ina a cikin ɗakin nata, ba abin da ke tashi sai sanyin Ac da kuma kamshin air freshener sannan ga kamshin perfume dake a cikinta, sai suka haɗu suka bada kamshi na musamman, tana kwance saman lallausan bed nata ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, an samu duniya, komai ya daidai ta, tana ruƙe da wayarta tana latse-latse.

Jin sallamar Akila yasa ta É—ago tare da ajiye wayar, ganin Akilar yasa ta sakar mata wani irin cool murmushi wadda sai da fuskarta ya zaman tamkar tauraruwa mai walwalin haske a tsakiyar duhun dare, ga shi ta sanya lips balm a lallausan lips nasa, sai ta kara kyau sosai.

"Aunty Akila sannu da zuwa" ta faɗa a sanyaye, murmushi ita ma Akila ta sakar mata kafin ta ce "Wow First lady gaskiya kin yi kyau sosai, wai irin wannan ɗaukar wanka haka, dole yaya Ahmad ya ce mani ranar da ya fara ganin ki bai runtsa ba, wai irin wannan kyau ko nima ba zan runtsa ba bare shi, ya ce mani ranar kwana ya yi yana tunaninki Queen of beauty, gaskiya ya zaɓi sunan daidai dake" ta kai karshen maganar tare da hayewa saman bed ɗin ta cigaba da faɗin "Amma me yasa baki saka riga da wando da muka ɗauka iri ɗaya jiyarnan ba? Wlh ba karamin kyau zai yi maki ba, kin ga dai kin fi mu hips kayan za su zauna maki sosai wlh".

Miƙewa zaune ta yi fuska ɗauke da kayatatcen murmushi ta ce "Aunty Akila shi wannan dogon rigar bata yi bane?" Cikin sauri Akila ta girgiza kai tana faɗin "Sosai ma ya yi maki kyau, amma anjuma ki sanya riga da wandon sai mu yi anko, dan nima shi zan sanya idan na yi wankar rana" Gyaɗa mata kai Rimsha ta yi alamar to, sannan ta zuro kyawawan kafafunta kasa ta miƙe ta nufi Palo.

"Ina zaki je Rimsha?" Ba tare da ta dakata da tafiyar da take yi ba ta ce "Palo zan je dan naji kamar yaya Imran ya fito ne, ina son mu gaisa ne sai na tambayi me zan girka mana".

Da sauri ita ma Akilar ta miƙe ta bi bayan ta tana faɗin "Me za ki girma mana ne ko kuma me zamu girka? Ai abin da yasa ki ka ganni a nan yanzu kenan, dan na koyi girki". Ta kai karshen maganar lokacin da suke fitowa Palon.

Yadda Akila ta barshi É—azun haka suka fito suka same shi, zama suka yi saman sofa mai zaman mutun 3, suna fuskantar juna da shi, cikin girmamawa Rimsha ta É—aga mashi gaisuwa.

Cike da kulawa ya amsa mata gaisuwar tata, tare da tambayarta ya ta kwana, lafiya ta amsa mashi da shi sannan ta É—aura da tambayar me za su girka.

Sai lokacin ya ɗago ya kalleta, wani irin kyau ta yi mashi, fuska ɗauke da murmushi ya ce "Ki girka duk abin da kike son ci, ni bana zaɓen abinci, sannan idan ba damuwa anjuma da daddare Dr ya ce zai zo tare da kanwarsa dan ta dame shi su je yawo, to zai kawo ta nan, fatan zaku karɓeta hannu bibbiyu sannan ina son ku yi masu girki mai daɗi" cike da murna har suna haɗa baki wajen cewa "E zamu karɓeta kuma zamu shirya masu haɗaden girki".

Albarka ya sanya masu sannan ya É—aura da cewa "Rimsha baki gaya mani wani kasa kike son zuwa school ba?" Kafin Rimsha ta yi magana Akila ta rigata da cewa "Yaya Imran tare zaka kai mu, kuma Usa muke so" É—an murmushin ya yi kafin ya ce "To heartbeat an gama, amma dai banso Usa nan ba, amma ba komai zan san yadda zan yi". Ihu Akila ta kurma tare da tashi ta rungume shi tana dariya, yana bala'in son ganin farincikin Akila, dan haka sai ya kara da cewa "Za'ayi maku komai da wuri nan da next week ko two weeks zaku tafi".

Sosai Akila ta kankame shi, ita kuma Rimsha banda murmushi ba wani abin da take yi. Haka suka miƙe cike da farinciki suka wuce kitchen dan shiryawa kansu abincin safe mai rai da lafiya.

A ɓangaren Jelly da Ummi kuwa, tsab suka shirya suka nufi gidan Hajiya Khadijat wato maman su Irfan.

Suna zuwa ba ɓata lokaci suka wuce gidan su Irfan a tare dan suje suga gidan, da kuma tsarinsa.

Daga waje suka yi parking na motarsu sannan suka fito izuwa cikin gidan. A palo suka isko Aunty tana zaune tana kallo, ta ci wankanta ta sha kwalliya, dan yanzu jikinta Alhadulillah sauki na samuwa sosai sai dai muce Masha Allah.

Babu ko sallama suka faÉ—o cikin Palon, babu kowa sai Auntyn ita kaÉ—ai, daddyn Jelly da Ayla sun fita shopping, shi kuma Irfan yana part nasa yana barci.

Awannan karon Aunty bata wani damu ba, domin ta san ko su waye, fara zagaye palon Ummi ta yi tana faɗin "Kai Masha Allah Aunty Hadiza ki ce mini abin arziki kam har ya kai haka" ta yi maganar tana taɓe baki, kuma duk cikinsu ba wanda ya kuka Aunty har jelly dake a tare da su.

Wani shu'umin murmushi Ommu ta yi tana taunar chewing gum kas-kas-kas, cike da shakiyanci ta ce "Wlh kuwa kedai Turai bari da ana zaton na mutune za'a mamaye komai, sai Allah ya yi ina raye, kuma gida dai nawa ne, yanzu dai mu haura sama dan muga É—akunan yadda suke". Kai daga jin yadda Ommu ta yi wannan magana kasan da biyu ta yi shi, sannan kuma mawuyacin abune ayi zaman lafiya da ita, domin babu shi a tattare da ita.

Aunty baiwar Allah ita bama ta su take yi ba, Jelly kawai take kallo, dan taga ta yi mata kama da yaya maik wato daddynta, sai dai kash rashin sani yafi dare duhu, yau ga jelly har cikin gidansu amma Aunty bata santa ba bare ta gane ta, sai dai tabbas taga kamannin dake a kan fuskokinsu.

"Ke me kike wani kallona ido kamar na tsohuwa mayya" cewar Jelly ta yi maganar tana karewa Aunty kallo, ai kuwa maganar da ta yin nan ba karamin jefa Aunty cikin tunani ta yi ba, domin sak muryar daddynta ta ji, amma kuma bata kawo cewa Jellyn da suke nema bane, saboda ganinta da su Hajiya Khadijat da ta yi, ta yi tunanin cewa Æ´arsu ce, amma dai har cikin ranta ta jinjinawa wannan kamanni na daddy da jelly ga kuma murya shima iri É—aya, ita ma Hajiya Khadijat ta sha ruwan mamakin lokacin da ta ga Jelly, dan ita ma taga Kamannin, amma sai Hajiya Turai ta ce da ita ai yar uwan baban su Nawid ne, shiyasa ta bar zancen.

"Kai baby kin cika rigima wlh, ke kuma tsohuwar mayya me kike wani ganinta? To idan ma baby ce wlh a hir É—in ki ta fi karfinki, sai dai gani sai hange daga nesa" Cewar Ummi ta yi maganar cikin faÉ—a.

Ommu ne ta ce "Ke ma dai Turai me abin ɓata baki a nan? Ai wannan bata kai ku yi mata magana ba, ni fa bana ɗauka ma a gidan nan akwai mutun, dan haka mu wuce dan Allah, da ku tsaya ɓata bakin ku wajen yin magana da ita ba gara ku yi da bango ba, koba komai ya fita daraja". Shekewa da dariya suka yi tare da haurawa sama, Jelly na biye da su abaya tana wani turo baki kamar biro, da ido kawai Aunty ta bi su, tana ganin ikon Allah yau iya ganin idonta.

*Wannan Hajiya Hadizar ita ya kamata acewa kanwar sheÉ—an ba A'isha na gidan Hajiyar daÉ—i ba*

Aunty tana zaune a wajen har suka gama dube-duben su a sama, suka sauƙo suka fice suka bar gidan, ko uppan bata ce masu ba, sai ma addu'ar neman Ubangiji ya tsare ta daga sharrinsu da take yi a cikin zuciyarta. Baiwar Allah tana ganin rayuwa.

A ɓangaren Aafia kuwa babu wanda ya lura da ɓacewar tata, domin Abbi ya san tana gidansu Akil, shi kuma Akila a tunaninsa ta koma gida hakan yasa basu nemeta ba.

(*Tofa Aafia kinga ta kanki, wannan shine ɗaya daga cikin illar gida biyu, mutun ya kasance gida biyu yake, yau nan gobe nan, sai ya ɓata ba wanda zai farga da wuri har sai ma duk abin da zai faru ya faru kafin a farga, ni dai ina jajanta maki kuma na haɗa kayana sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu, dan jin yadda zata kaya*)

💖TRIPLET'S💖💖

47-48

Gidan Abba.

Sosai su Rimsha suka shirya haÉ—aÉ—en girkinsu mai rai da lafiya, bayan sun kammala suka jere a saman dining table, Sannan Akila ta wuce part nasu dan ta je ta yi wanka, ita kuma Rimsha ya wuce É—akin ta dan yin wanka.

After some hours da ba su fi biyu ba.

Zaune suke a palo sun baje suna cin abinci suna hira, Imran, Akila, Rimsha, tamkar sun saba sosai haka suka kasance, suna ci cike da nishaÉ—i da kuma santi, sai hirarsu suke yi.

Bayan sun gama cine, Akila ta ɗauko Alqur'ani mai girma a ɗakin Imran tana faɗin Rimsha ta kara mata karatu, dariya sosai Rimsha ta yi kafin ta ce "Aunty Akila ina da tabbacin kin wuceni a karatu" "A'a Rimsha Allah ban wuce ki ba ni dai ki kara Mani" to Rimsha ta amsa mata da shi sannan ta karɓi Alqur'ani ta fara karatu, kunna recording Imran ya yi a wayarsa yana recording na zazzakar murya nan nata.

Cikin suratul Maryam take karatun a nutse, a wannan hali Akil ya shigo ya same su, saman sofa ya zauna yana gaishe da Imran, da fara'a Imran ya amsa sannan suka yi shiru suna sauraron kira'ar Rimsha dake tashi, ga zazzakar murya nan nata ba'a magana.

Sai da ta kai aya sannan ta ce "Aunty Akila wani sura zan duba Maki?" Akila na ƙoƙarin yin magana Akil ya rigata da cewa "Yaya Imran wannan ita ce wadda ka gaya mani jiya a kan ka kawota gidan nan ko?" Gyaɗa mashi kai Imran ya yi alamar e.

Dawo da kallonsa kanta ya yi tun kafin ya yi magana ta rigashi da cewa "Ina kwana?" lafiya ya amsa mata da shi sannan ya É—aura da cewa "A ina kika tsaya da hadda?" Akil kenan yana bala'in kaunar ya ga mutun yana karatun Addini, ko da bai san mutunba matukar zai yi karatun addnin tofa zai taimaka mashi ba kaÉ—an ba.

Bayan ta gaya mashi ne, sai ya ce "To zan koma Madina nan da wata mai shiga, kafin na koma sai ku rinƙa zuwa ina kara maku har ma da na boko, kullun karfe 5 na yamma zuwa shida zamu yi lesson, yanzu ma bari na baku hadda koda shafi ɗaya ne, amma fa duk wacce ta yi wasa zan zane ta, bana son wasa da karatu". Sai murna suke yi suka amsa mashi da to, tare da kawo mashi Alkur'ani kowace ta faɗi daga in da zata tashi, nan ya kara masu shafi bibbiyu dan sun ce ɗaya ya yi masu kaɗan.

Bayan ya kara musu ne ya jaddada masu karfe 5 daidai su same shi a garden na gidan dan su kawo haddan su ya kara masu wani.

Sai daɗi suke ji suka amsa da to tare da miƙewa suka nufi bedroom ɗin Rimsha.

Suna shiga Rimsha ta ajiye Alqur'ani mai girma a saman mirror drawer, sannan suka haye gado suka fara zuba hira. Suna tsaka da hira Ahmad ya kira, cikin sauri Rimsha ta jawo wayar, tana ƙokarin yin picking kenan Akila ta ce "Kai Rimsha ki rinƙa jan aji mana kada ki ɗauka da wuri ki bari sai wayar ta kusa katsewa, idan ba haka ba yaya Ahmad zai ce kina da arha sosai, ko muna son abu ya kamata mu rinƙa jan aji akan shi". Harara Rimsha ta watsa mata kafin ta ce "Ni na ce maki ina son shi?" Yar dariya Akila ta yi tana faɗin "Ai ba ke kika ce ba, alama ce ta nuna, har da wani saurin ɗaukan kira, kai Rimsha, ki tasa Bawan Allah a gaba kina zuba mashi shagwaɓa da malamai har sai ya susuce maki ko? Wlh yaya Ahmad yana ruwa, thank God ni ba ni da saurayi amma fa duk saurayin da ya zama masoyina sunansa Sorry" ta kai karshen maganar tana dariyar iyashege.

Wayar har ta katse Rimsha bata É—auka ba ta biyewa Akila. "Aunty Akila ni fa abin da ya sanya zan É—auki wayarsa da wuri haka, saboda ina son tambayarsa number wannan yar uwar tawa Ayla da na baki labari jiya, shine fa yasa zan É—auki wayar".

Hararar gefen ido Akila ta yi mata cike da zolaya ta fara magana "To haka ne? Amma dai kada na ji an kashe murya, ayi mashi magana kamar yadda ake yi mani, idan ba haka ba zan mashi recording naki idan kina magana da ni, na tura mashi na ce ya ji muryar ki yadda kike yi mani magana, duk da cewa ma dai voice ɗin naki ƙarshe ne a daɗi" ta kai karshen maganar tana juyawa ta bata baya.

Rimsha tana ƙoƙarin yin magana kiran Ahmad ya sake shigowa a karo na uku kenan, cikin sauri ta yi picking tare da kai wayar kunnanta, a nutse ta fara magana "Assalamu alaikum Yaya Ahmad ina kwana?" Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya amsa mata da "lafiya Lou Alhamdulila My beauty ya kika kwana?" Lafiya ta bashi amsa sannan ta ɗaura da cewa "Dan Allah yaya Ahmad number Ayla nake son ka turo Mani" To ya amsa da shi sannan ya katse kiran ya turo mata number tare da sake kiranta.

Ba dan taso ba ta É—auki wayar suka fara hira, kamar dai kullun E da a'a shine kawai abin da take bin shi da shi, bai wani damu ba, shi dama burinsa kawai ta É—auki wayar.

Har Akila ta yi barci Ahmad bai ga ji da yiwa Rimsha surutu ba, sai da ya ji ta daina amsa mashi da e da a'a É—in ma, sai ya ce to za su yi waya anjuma, to ta ce mashi suka yi sallama.

Kamar jira take yi dama, yana katse kiran ta fata kokarin gwada layin Ayla, layin a kashe, ba dan ta ta so ba, ta ajiye wayar ta miƙe ta ɗauko Alkur'ani mai girma ta fara biya karatun da Akil ya kara mata, domin tana son kafin yamma ta haddace, ta yadda zata kai babu gargada, kuma tana son ya kara mata a yau ɗin, tana son rufe haddarta gaba ɗaya, a yanzu haka tana da izu arba'in a kanta, to tana son rufe ashirin ɗin gaba ɗaya.

Sosai ta dage tana karatu ita kuma Akila tana barci, ni kuma na haÉ—a kaya na zuwa wajen su Aafia.

🥺💔BANDIT'S💔🥺

Suna zaune cikin wannan bakin É—aki mai cike da bakin ciki da tashin hankali, babu wanda yake iya ce da É—an uwansa uppan, kowannensu bala'in yunwa yake ji sosai, gaba É—ayan su kusan buri É—aya ke a zuciyoyinsu. Wannan buri kuma ba wani buri bane fa ce a kashesu su huta, amma sai dai bandits É—in sun ki su kashe su.

Suna zaune a haka har bandits nan suka zo bakin kofar wajen suka ce da su su fito, da yake sun saba sai suka yi maza suka ta shi. Aafia ta sha ruwan mamaki ganin yadda suke rige-rigen wajen fita, har suna ture juna, abin ya É—aure mata kai, kamar waÆ´anda za'a bawa wani abin a wajen, sai mamaki take yi tana tafiya a hankali ta bar Rufee kwance a wajen. Bata ankara ba sai jin saukar wata shegiyar bulala ta yi a tsakiyar gadon bayanta, ihu ta kurma a guje ta bazama wajen sauran mata da suka yi gaban. Abin da yake faru wadda ita bata sani ba shine, idan bandits É—in suka ce ku fito, to kayi maza ka yi gaba, idan ba haka ba ka tsaya baka sauri to za su zane maka jiki da shaggun bulalun nan nasu, to ita bata sani ba, ta tsaya tana tunane-tunanenta, shiyasa ta sha bulala.

Can cikin wani ciyawa da suka kewaye da wasu kirare suka je suka zazzauna.

Wata mata dake zaune ɗan gefe da Aafia ne yaron ta na goye ya fara tsallara kukan yunwa, cikin saurin matar da ta zauna da Aafia a ɗaki ɗazun ta sanya hannu ta toshewa yaron baki, buge mata hannu uwar yaron ta yi tana faɗin "Baki da hankali ne ke? Kashe mani yaron zaki yi? Ya zaki toshe mashi baki yana kuka?" Kallon bandits dake kewaye da su matar ta yi kasa-kasa ta ce "Wlh idan kina son yaronki to ki sanya shi ya yi shiru, na lura ke bakuwa ce a nan, amma ni dai na gaya maki idan ba haka ba zaki rasa yaron nan, domin sun tsani kukan yara, last week suka kashe wani jariri a nan wajen, to kema ki yi da taka tsan......." Bata iya kai karshen maganar ba sakamakon wani bandit da ya shigo cikin wajen ya fisgo wannan yaro daga bayar uwarsa ya fice da shi, ihu uwar ta kurma ta miƙe zata bi bayansu, bandits dake tsaye a wajen ruƙe da bindiga ne suka yi mata barazana tare da dakatar da ita ta hanyar harba bindiga a in da take yunkurin saka kafarta, cikin wani irin gigita da kiɗima tare da matsananciyar tashin hankali uwar yaron nan ta ja burki tare da komawa baya.

"Koma gi zauna ko kuma yanzun nan na fasaki da bindigar nan!!" Cewar É—aya daga cikin bandits dake a wajen, jikinta sai kerma yake yi haka ta koma ta zauna tana hawaye.

Lokacin da suka saki wannan harbin bindigar tsabar tsorata yasa Aafia ta tamki matar da aka yiwa yarta fyaɗen nan wato maman Zahrau, nan take ta fara hawaye, bata taɓa jin karar harbin bindiga a gaske ba, sai dai a film, amma yau ga shi a gaban idanuwanta aka saki harɓi, abin ya gigitata.

Suna cikin wannan hali wani bandit É—in ya kariso wajen yana jan Rufee a kasa kamar shanuwa, da alama kuma ta suma, yana karisowa wajen ya wullota cikinsu ya juya ya bar wajen.

Sosai A'afia ta tsanan ta kukan da take yi mara sauti, abin ya ɗaga mata hankali fiye da tunanin mai tunani, wannan bala'i ma kawai ya isa ya sanya ƙwaƙwalwar mutun birkicewa, ɗaya daga cikin matar dake a wajen ne ta ce da matar da akayiwa yarta fyaɗen "Maman Zahrau ki sanya yarinyar nan ta yi kuka kasa-kasa ko kuma ta yi shiru, idan ba haka ba, ita ma tana gab da rasa tata rayuwar" Jin haka yasa A'afia ta yi saurin toshe hakinta da hannunta, jikinta sai kermar tsoro yake yi, abin gwanin ban tausayi.

Suna cikin wannan yanayi bandits guda uku suka kariso wajen hannunsu ruƙe da manya manyan tray masu ɗauke da shinkafa da miyar, layi-layi suka fara bi suna raba wa su Aafia abinci, ko da suka zo kan ta ƙin karɓa ta yi, wai ba zata iya ci ba, Mama Zahrau ce ta ɗan taɓa ta alamar ta karɓa, domin idan bata karɓa ba za su ce gidan su akwai kuɗi sosai dan haka idan dama millon ɗaya suka saka kuɗin fansa sai su kara dan kin ki cin abincinsu hakan ya nuna daga gidan daɗi kika fito kenan.

Jin maman Zahrau ta taɓa ta ne yasa ta karɓi abinci, wucewa suka yi suka ci-gaba da raba wa sauran abincin. Sai bayan sun gama rabawa sun ta fi ne Aafia ta ce ita kam ba zata ci ba, to kawai maman Zahrau ta bita da shi, sannan ta ɗaura mata da cewa "Kinga idan baki ci wannan abincin ba, wlh in baki yi Sa'a ba sai gobe yi war haka zaki sake ganin abinci, sau ɗaya suke bada abinci, sai wata Sa'a idan sun sami kuɗi sosai kamar idan an fanshi wasu nan ne za ki ga sun bamu abinci sau biyu a rana, kuma kada ki yi zaton iya mu da muke nan ne kawai suka kama, a'a akwai maza suna ta baya, akwai wasu matan ma ta baya, irin wajen nan uku suke da shi, kin ga suna da mutane da dama da suka kama, ba za su iya ciyar da mu sau uku a rana ba, wani lokaci ma ba mu samun ko sau ɗayar sai dai su bamu ruwa, shima ruwan kada ki yi zaton akwai shi available ne, A'a sau biyu suke bada shi arana shima, so dan haka is better for you da ki ci abincin nan".

Kallon abincin A'afia ta yi gaba ɗaya abincin dake cikin robar bai wuce ayi loma ɗaya da shi ba ya kare, amma a hakan idan suka ci kuma sai gobe, wannan wace iriyar bala'i ce, ya Allah ka kawo mana sauƙin wannan musifa da muke acikin.

Ita kuwa uwar yaron da aka kwace É—an, ta kasa ko da motsin kirki, burinta kawai taga ina yaronta yake, tana É—aya daga cikin bakin da aka kawo yau da safe, so bata san asalin halinsu ba, sai yar dube dube take yi ko zata hango yaron nata, amma ina shiru ba shi ba alamar shi, ko kukansa da ma yake yi ta daina jiyowa.

Su kuma sauran matan dake a wajen, tuni sun fara cin abinci, hannu baka hannu kwarya, ba za su Barka ka wanke hannu bama, kawai ci ake yi. Aafia tana son tashi ta isa ga Rufee dan ta dubata taga kamar bata motsi ne, amma ina tana tsoro, dan idan ka yi wata wargi tsab za su iya kashe ka.

Suna tsaka da cin abincin bandit ɗin da ya ɗauki yaron matar nan ya dawo wajen hannunsa na ruƙe da zanin matar jini na zuba da ga jikin zanin, ga abu kuma a ciki sun kunso shi.

Kai tsaye matar ya nufa, yana zuwa ya gefa mata yaron ya juya ya bar wajen, jikinta har kerma yake yi, da kyar ta iya buÉ—e zanin, wa iya zubillah yaron ne suka dafa shi, da alama cikin tafasasshen ruwa zafi suka sanya shi, gaba É—aya fatar jikinsa ta É—aye, sai tiririn hayaki ke fitowa daga jikin wannan yaron, gaba É—aya jikinsa ya kwaile fatar ta cire ya yi wani jawur da shi, daga bakinsa da hancinsa jinine ke zuba daga wajen, da alama a cikin tafasasshen ruwan zafi suka sanya shi, dan ga shi, duk wadda ya ga yaro nan idan bai suma ba, wlh sai ya matse mashi kwalla, sai dai idan zuciyar da babu wani imani ko É—igo a cikinta, innalillahi wa inna ilaihir rajiun uwar yaron nan a wajen ta yanke jiki ta faÉ—in, ba ita ka É—ai ba cikin wayan da suka suma harda A'afia da kuma bakin da aka kawo yau da safe a cikinsu akwai Hanan kanwar Sadiq Katsina.

Duk bakin da aka kawo yau da safe sai da suka suma ganin wannan tashin hankali, wayan da suka daɗe a wajen kuma masu kuka sun sha kuka, wayan da kuma zuciyarsu ta bushe ko alamar hawaye babu a idanunsu, sai dai ja da idanun nasu ya yi kamar wuta, alamar abin ya taɓa su suma, cikin wayan da ba su yi kuka ba har da maman Zahrau ita ma baiwar Allah zuciyarta ta bushe bata jin komai.

Wannan wace irinyar bala'i?, Wannan masifa dame ta yi kama? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya Allah ka kawo mana mafita, dayawa daga cikinmu sun saki Allah sun riki duniya gam, ya Allah ka jiƙan bayin ka ya Allah, innalillahi wa inna ilaihir rajiun astafirullah waatubu ilai.

Daya wa daga cikin mutanen dake a wajen, mu samman wayan da aka kawo yau, ba wanda ya iya cin abincin dukkansu kowa ya kasa ci da suka farfaɗo kenan, sai dai wayan da suka daɗe a wajen, suma ɗaiɗaiku ne suka iya cin abincin irin su maman Zahrau. Ya Allah ka kawo mana ɗauki, yanzu a naku tunanin ire-iren maman Zahrau da suka sanya zuciyarta ta bushe babu imani babu tausayi me kuke tunani zata iya aikatawa idan aka bata makami? Allah ma ya tsare da yake ba azzaluman bawa bane sai dai bawa zalunci kansa, sai zuciyar tata ta saura da son Allah da Manzonsa, bayan su ba wani abin dake a cikin zuciyar maman Zahra, ya ilahi ya lillillahi😭

Kasan cewar ogan su mai kiran waya baya nan hakan yasa suka wuni a wajen ba wadda aka kira iyayensa, domin duk cikin bandits É—in mutun biyar kawai ke da damar kiran waya, saura kuma aikinsu kamo jama'a ne kawai, da kuma kula da su, bayan haka ba wani abin.

Jugum-jugum suka zauna ba sallar azahar bare la'asar har karfe shida na yamma sannan suka sanya su a gaba zuwa cikin É—akunansu, dayawa daga cikin bandits É—in basa nan, da alama wani abin suka tafi aikatawa acikin gari, domin kusan rabi da kwatansu basu nan a wajen, yan kalilan suka rage, wadda ba su fi yawan mutanen dake a wajen ba.

Haka aka mai da su cikin ɗaki suka cigaba da zama jugum-jugum ita kuma Rufee da alama fa kamar babu rai ajikinta, domin ƙo motsi bata yi, kuma haka suke janta a kasa kamar shanuwa, a wannan dawo da su da suka yi, sun haɗa Aafia da kuma Hanan kanwar Sadiq waje guda, domin dama haka suke yi, idan sun tashi mai da ku, mafiyawancin lukuta suna canza maku ɗaki domin kada kudaɗe a waje guda har ku shirya masu wani abin, shayasa basu barin jama'a su sarara, tsabar rashin yarda da kai.

(To mun ji ɓangaren Aafia bari mu leƙa ɓangaren su Jelly dan jin yadda zata kaya mana.)

Sai murna take yi za su fita yawo da yaya Nawid, abin ba'a magana har wani kin magana take yi ma mutane, sai kauÉ—i take yi da rawan kai, ita adole za su fita yawo.

Bayan sun yi sallar isha ne suka zauna cin abinci, da sallama Nawid ya shigo palon, zaune ya isko su saman table Ummi na kokarin zuba masu abinci su ci, yau Abbo ba a part nasu yake ba, yana part É—in maman Afnan hakan yasa Ummi gaba É—aya bata son fitar da Nawid zai yi da baby, dan kada ya barta cikin kaÉ—aici.

"Baby ki tashi mu tafi mana, ba sai kinci abinci ba, za mu ci a can, Prof ya sa an shirya mana abinci". Ba tare da ta kalli in da yake ba, ta ce "Yaya Nawid kaza fa Ummi ta soya mani, ni gaskiya babu in da zanje sai na ci wannan kazar". Bin Ummi da ido ya yi, sai yanzu ya gane me matsalar da gangan Ummi ta kawo mata kaza dan bata son su fita saboda Abbo yana part É—in su Afnan, sanin haka yasa ya samu waje saman chair É—in tabla É—in ya zauna yana faÉ—in shima a zuba mashi abincin kawai ya ci.

Cikin sauri Ummi ta ce "Fitar fa ya zaku yi?" Rai a ɗan ɓace ya ce "Haba Ummi kinsan dai idan Baby ta samu kaza ba'a magana, bata kula kowa, bata kasancewa a duniyar mutane, dan haka a barshi kawai sai wata saan".

Cikin mayen kaza da kuma santi ba tare da ta kalli in da yake ba ta ce "Yaya Nawid ka faÉ—i gaskiya, aradu kaza tafi duniya daÉ—i, wai yaya Nawid ka cire wannan abin da aka rufe maka a kasar gadonka kuwa? Sannan na gaya maka wannan Abbon kwarto ne amma kaki yarda, to yanzu kuma ya zama É—an iska domin yana kallona sosai". Girgiza kai kawai Ummi ta yi babu wanda ya É—auki zancenta da gaskiya domin suna yi mata kallon mahaukaciya, bare kuma idan ta samu kaza ai shikenan kuma, sai ta kara haukacewa da gasken-gaske.

Ba wanda ya kulata suka zauna suka gama cikin abincinsu, ita kuma har lokacin tana fama da kaza, kamar wata mai aljanun kaza a kai.

A ɓangaren su Rimsha kuwa, kamar yadda Akil ya basu umarnin kawo hadda da karfe 5 haka suka shirya suka yi wanka, suka yi sallah tare da cin abincin rana da suka girka suka shiryawa kansu, a palon Imran suka zauna suna jiransa. Sai 5:10 ya shigo shi da Umaisha, sai murmushi suke yi wa juna, da alama dunuyar tana yi masu daɗi, daga gani kasan sun mace akan juna.

Saman sofa mai zaman mutun 2 ya zauna su kuma suka yi maza suka sauƙa kasa, Akila tana ruƙe da Alkur'ani mai girma, ita kuma Rimsha ta ce zata kawo da kai ba tare da Alkur'ani ba, sai dariya Umaisha take yi wa Akila da alama wani munafurcin suka haɗa, kasa ya ce ita ma Umaisha ta sauƙa, ba musu ta sauƙo kasa, kafin ya fara karɓar haddan nasu ne ya tambayi Akila ina A'afia bata dawo bane, E ta bashi amsa, shiru ya ɗan yi kafin ya ce to su kawo haddansu zai je gida ya same ta.

Da haka suka rufe babyn Aafia suka fara bada haddansu, dukkansu sun kawo daidai, kuma ya jinjina masu, kyautar maki mai girma ya basu, sai ya ce su kara tusawa domin ya zauna a ƙwaƙwalwarsu da kyau, sai zuwa gobe da safe zai kara masu wani shafin. Sai murna suke yi suna zuba mashi godiya, a tare suka miƙe za su tafi.

"Karatun boko da luttatafai fa?" Ya jefo masu tambaya, cikin sauri suka dawo suka zauna, Akila ce ta ɗauko takardunta suka fara koyan karatu, ita kuma Umaisha ta ɗauko masu littafai irin su Nahhu, muɗalaa, malumat, da dai sauran littatafan musulunci, zama suka yi suna ɗaukan karatu da kyau, har da ƙawa'idi, ahlari a ciki, sai karfe 6 kamar yadda ya faɗa suka tashi, cikin hanzari suka faɗa kitchen dan su shiryawa bakon yaya Imran girki kamar yadda ya faɗa.

A tare suka fara aikin, wannan ta kama wannan, wannan ta kama wancan, sai hira suke yi Akila tana bawa Umaisha labarin saurayin Rimsha, wato yaya Ahmad, É—an anachen Rimsha in ji ita Akilar, shine sunan da ta bashi, sai dariya suke yi, ita kuwa Rimsha ta tsare gida kam, babu alamar dariya ko wasa a tattare da ita, ta yi shiru sai ki rantse da Allah bata a wajen.

Fried rice suka yi ya ji kayan kamshi, su green beans da sauransu, Rimsha ce mai basu command, ita ma wani abin sai ta buÉ—e takardun girkin sannan take dubawa.

(Manya suna aiki fa.)

"Aunty Akila ke ki haÉ—a mana ganye, ke kuma Aunty Umaisha ki zuba abincin a kuloli ni kuma bari na haÉ—a pepper chicken" to suka amsa da shi sannan suka fara aikin da ta basu, abin duk wanda ya gansu sai sun ba shi sha'awa, sosai sun haÉ—a kansu kaman yan uwan juna, da yake Akila da Umaisha duk basu da matsala sai suka ja Rimsha sosai ajikinsu.

Bayan sun gama tsab, suka fito palo ana kiraye-Kirayen sallar mangariba, bedroom na Rimsha suka wuce, Akila ta ce a nan za ta yi wanka, ita kuma Umaisha ba dan ta so ba ta wuce Part nasu, Akil da Imran kuma sun tafi masallaci.

Rimsha ce ta fara yin wanka tare da É—auro alwala, bayan ta fito Akila ta shiga.

Zama Rimsha ta yi a gaban mirror ta shafe jikinta da mayukanta masu daÉ—in kamshi tsab, sannan ta feshe perfume nata masu daÉ—in kamshi, kafin Akila ta fito har ta gama shafa mayukan da duk wani abin da zata yi a gaban mirror, saura saka kaya, lokacin ita kuma Akila ta fito É—aure da towel a kirjinta, itakuwa Rimsha lokacin da ta fito, bayan towel da ta É—aura sai da ta sanya É—an karamin mayafinta da ta shiga da shi, wato gyalen abayar ta, dan bata son Akila ta ga zanen dake a kan kirjinta, shiyasa ta sanya mayafin a kanta ta rufe har kirjinta.

Riga da wandon da Akila ta ce su yi anko shi, shi ta ɗauko ta sanya, kayan sun karɓeta sosai da sosai, da rigar da wandon dukka masu kama jikine, sannan rigar zuwa gwiwarta ya tsaya mata, an zuba mashi kwalliya a gaba sosai, kai da gani kasan yana da tsada sosai dan ya haɗu over, launin pink color ne da milk, haka ta sanya su, amma kafin ta saka sai da ta sanya vest a ciki, domin wuyar rigar tana da ɗan girma, idan har bata sanya vest ba wannan zane na sunan Lion zai iya bayyana kowa ya gani, dama kuma saboda zanen yasa da suka je shopping ta ɗauki dozen na irin vest ɗin nan masu kama jiki sosai kamar roba, dan bata son kowa ya gani ma bare kuma ya tambayeta me yasa zata rubuta sunansa.

Bayan ta gama shiri sai da ta sake fesa turare sannan ta zura hijabi har kasa ta zauna a bakin gado tana jiran Akila, domin ta tafi sanya nata kayan ita ma.

Jiran minti goma ta yi sai ga Akilar ta dawo shirye cikin nata kayar irin É—aya suka yi anko, akalla Akila zata bawa Rimsha good 4 years da yan É—ori, amma da yake Rimsha tana da tsawo sai kansu ya yi kusan É—aya, da kaÉ—an Akila ta É—ara ta, dan suma Æ´aÆ´an Abba ba baya ba wajen tsawo. Yanzu Rimsha an fara zama Æ´an mata tula-tula sun fara girma.

A tare suka yi Sallah, bayan sun idar suka wuce palo dan su É—an yi kallo. Suna zama saman sofa Rimsha ta É—auki remote ta shiga News, Rimsha yarinya mai Sa'a duk time da ta shiga News zancen mutumin nata ake yi, yau ma ta yi Sa'a maganarsa ake yi, ga kuma hotonsa nan an kafe kamar kullum yana sanye da face mask.

Kamar ance ta kalli fuskarsa, ai kuwa idanunta suka sauƙa akan nasa, ba abin da ya faɗo mata a ƙwaƙwalwarta irin yadda taga idanuwansa a zahiri cikin mafarkinta, yadda ta gansu muraran, tuna hakan yasa ta runtse idanuwanta, tana tunanin yadda yake a zahiri, wannan idan ka ganshi zaka iya mutuwa.

Ji tayi ba zata iya ganin fuskarsa ba, koda kuwa a hoton ne, mugun razana ta yake yi, hakan yasa ta yi maza ta canja tasha. "A'a Rimsha me yasa zaki kashe mani jarumina ina tsaka da kallo?". Cewar Akila.

Ba tare da tayi magana ba ta miƙe da sauri ta koma cikin ɗaki, daidai lokacin aka kira sallar isha. Saman dadduma ta hau tana hawaye tana Sallah, ta rasa meke damunta, tana bala'in son wannan mutumi, amma kuma duk lokacin da ta kalli even pic nasa da glass ba iya face mask ba, sai ta yi mugun razana, sai ta fi awa uku tana takure waje guda tana razana, kamar wadda taga wani dodon ko wani abin, idan kuwa tana kwayar idonsa a hoton, ma'ana babu glass wunin ranar zata yi shine ba cikin walwala ba, ta rasa menene dalili, tana sallah tana kuka, ko da ta kai sujjada, ya jima sosai tana kuka tana rokan Allah da ya rabata da son wannan mutumi a zuciyarta, ta kuma yi danasanin rubuta sunansa a kirjinta.

A wannan hali Akila ta iskota, bata kawo komai a ranta ba, ganin tana sallama yasa ta yi tunanin kenan dama ƙiran Sallah da akayi ne yasa ta baro palo da gudu ta dawo ɗaki, da farko ta zaci ko wata matsalace, amma ganin tana sallah yasa ita ta tsaya kusa da ita tare da tada kabbara ta fara Sallah.

Rimsha bata bari Akila taga hawayen fuskanta ba, tana idar da sallah ta miƙe ta shiga toilet, lokacin kuma ita Akila tana raka'a na uku ne, tana shiga toilet ta wanke fuskarta sosai, sannan ta fito ta zauna gaban mirror ta ɗan gyara fuskar tata, ta miƙe ta nufi palo.

Bayan Akila ta idar da sallah ta yi addu'a sannan ta bi bayanta, daidai lokacin su Imran suka dawo masallaci, shi da Akil.

A palon suka baje suna hira da dariya, fito da wayarsa Akil ya yi ya kira Umaisha dan ta zo su yi hira a tare, aikuwa ba ɓata lokaci sai ga ta nan ta shigo, haka suka cigaba da hira cikin annashuwa, shi kuma Ahmad sai kiran layin Rimsha yake yi amma wayar na ɗaki ta sanya ta a silent. Sai wuraren karfe 9 da Imran ya samu sakon Nawid akan ba zai samu damar zuwa ba, saboda Jelly ta samu kaza, dariya Imran ya yi sosai ya ce "Ashe kuna da maganinta a gida ma ka tsaya kana wahalar da kanka, ai nan gaba idan ta dameka da ku fita yawo kaza kawai zaka saka Ummi ta soya mata sai ka haɗa ta da shi ka huta". Shima Nawid ɗin dariya ya yi, Imran duk ɗaukansa kanwar Nawid ɗin da ya ce an kawo ta da ga family Abbo ya zaci yarinya ce da bata wuci 8 to 10 years haka ba, shiyasa ma yake yiwa Nawid tsiya irin haka.

Haka suka yi ta hiransu na abokai daga bisani suka yi sallama da juna, Imran ya cewa su Rimsha su kawo masu abinci su ci, saboda Nawid ya ce ba zai samu zuwa ba, cike da murna suka kawo abincin Akil sai mamaki yake yi, yar yarinya kamar Rimshan nan ne ta iya girki, da farko ya ce ba zai ci ba, domin yana ganin kamar jagwalgwalo kawai suka yi, amma daga baya da Imran ya matsa mashi, sai ya ce a sanya mashi kaÉ—an, ai kuwa yana fara ci ya ce a kara mashi, sai dariya Akila ta ke yi mashi, ta ce "Wai yaya Akil ka manta ka ce duk mace da bata haura shekara talatin ba, ba zaka ci girkinta ba, domin ko masu shekara ashirin da biyar yara ne kamar mu, ba'a gama ya ye mu ba?". Harara ya wurga mata ita kuma Umaisha cewa ta yi "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun dama yaya Akil abin da ka faÉ—a kenan? Lallai ma, to wlh yanzu zan ko yi girki idan ba zaka ci nawa ba, ni ma ba zan ci na restaurant ba".

A kule ya ce "Idan kuma na bada umarnin ki ci dole fa?" Still dai fuskarta É—auke da murmushi ta ce "E sai na ci mana tun da kai kace, to bama dole na ba" Wani nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, Akil akwai bala'in son girma, wato tun da idan ya bada umarni zata ci shikenan ai ya huce, shi dai Imran, shi da Rimsha ban da murmushi ba wani abin da suke bin su da shi.

Bayan sun gama cin abincin sun yi komai, sun tattare wajen ne, suka yi wa yaya Imran sallama, Rimsha ta wuce É—akin ta, Akila da Akil da Umaisha suka wuce cikin gida, shi kuma Imran ya É—an jima a palon kafin nan ya tashi ya shiga bedroom nasa, ya yi wanka ya shirya cikin kayan barci, sannan ya kwanta.

Itama Rimsha wanka ta yi tare da shiryawa cikin tsadaddun kaya barcinta masu kyau launin pink color riga da wando, dan tana son pink color, sky blue, da kuma fari, sune best color É—in ta.

Bayan ta gama ne ta sake feshe É—akinta sa air freshener sannan ta haye gado ta ja bargo tare da jawo wayarta ta fara kiran layin Ayla, amma a kashe sosai ta fara shiga damuwa akan me ya samu Ayla. Haka tana ganin kiran Ahmad amma bata É—auka ba, saboda bata cikin yanayi mai daÉ—i, tana tunanin Ayla sosai. A wannan daren dai da kyar barci ya yi awon gaba da ita. Asuba ta gari.

Idan muka koma Washington DC kuma.

Kamar dai yadda suka tsara haka suka yi, sai da suka yi sallah la'asar sannan suka dawo gida, haka da mangariba tun karfe 6 suka fita gida, sai karfe 8 bayan sun yi sallar isha suka dawo gida, a palon Part ɗin Michael suka zauna dan yanzu dama ba su wani cika zuwa palon kasa ba, waya Michael ya yi akan bodyguard su kawo mashi kayan tea part nasa, haka kuwa a kayi ba tare da ɓata lokacin ba, sai ga bodyguard guda biyu, kamar kullun suna cikin dressing nasu na bakaken suit tare da bakaken glasa a kan face nasu, wato no respect.

Saman dining table dake a cikin palon suka É—aura kayan tea É—in tare da wani kyakkyawar flaks mai kyan gaske, kayatatcen tea ne wadda aka haÉ—a shi da ganyayyaki masu kara lafiya a jiki, shine a jikin flaks É—in, haka suka ajiye suka juya suka bar palon.

Kallon Musharraf Michael ya yi yana faɗin "Uncle ɗin James ka je ka haɗa tea ɗin ni bari na je na yi wanka na duba Lion yau tun safe da muka rabu a gym ba mu sake haɗuwa ba" To Musharraf ya bishi da shi, sannan suka miƙe a tare, Michael ya wuce toilet shi kuma Musharraf ya wuce saman table ɗin dan ya haɗa tea ɗin sa.

A ɓangaren Lion kuwa, lokacin da ya gama zaman shi a lambun sai ya miƙe ba tare da ya sha fruits ɗin ba, maltina kawai ya ɗauka kwara ɗaya da glass cup ɗaya ya fito daga wajen.

Ji kake dip-dip-dip wani jibgegen Bature soja fari tas ya nufishi a guje, yana zuwa ya karɓi maltinan da glass cup dake a hannunsa, cikin girmamawa ya ɗaga hannu ya sara mashi tare da buga kafa, ba musu Lion ya miƙa mashi maltina dan dama dan dole ya ɗauko su, yana jin yunwa amma kuma suna da zama a white house karfe 10 yanzu kuma har 11 ta kai bai je ba, hakan yasa ya fasa shan fruits ɗin dama kuma ba wani niyar sha yake da shi ba, kawai dai bai son cin abincin safe ne yasa ya ce zai sha fruits ɗin.

Kasa kasa ya yi magana kamar mai raɗa "Ku tashi motoci za mu wuce white house" da sauri sojan ya sanarwa da sauran sojojin dake a kusa, kan kace me sun haye saman bayan motoncin, wannan sojan da ya riƙe mashi maltinan shi ya buɗe mashi motarsa ya shiga cikinta, bayan ya shiga ne sojan ya zuba mashi maltina cup, cikin girmamawa ya miƙa mashi, girgiza kai ya yi alamar baya buƙata, sojan bai ji komai ba, domin idan da sabo sun saba ba zaka taɓa gane me yake so ba.

Da gudun gaske suka tashi motoncin suka fice daga gidan, kai tsaye white house suka wuce, kamar dai ko yaushe duk wata abin hawa dake a kan hanyar sauka take ta basu hanya su wuce.

Lokacin da suka isa white house, gidan a cike yake tab da jami'an doka sojoji manya-manyan yan siyasa da duk wasu masu faÉ—a a ji a kasar, gaba É—aya ko ina ka waiga sojoji da yan sanda ne cike makil a gidan, tun da jerin gwanon motocinsa suka shigo gidan, gaba É—aya sojojin dake a cikin gidan suka fara kamewa suna sara mashi, wani sojan kam ma, saboda kamewa sai ka rantse da Allah baya numfashin. Lion duniya

Kamar dai kullum kun san mai hali baya fasa halinsa, to haka ne, Lion dai bai kula kowa ba, ko kallon in da suke ma bai yi ba, ya sanya face mask a fuskarsa ya fito, kai tsaye fadar shigaban kasa ya wuce, sojojin sa kuma suka dakata daga bakin kofa.

Yana shiga cikin fadar ya wuce Roosevelt Room, nan ya isko kowa ya haɗu ana jiransa, da gani ran kowa dake cikin wajen a ɓace yake, domin Lion ya ajiye su suna ta jira, ga Tga nan tun ɗazun ya iso wajen, amma shi sai yanzu, kuma haka za su hakura ba yadda suka iya da ahi.

Daga gefe kuma ga yan jaridun white house, wato yan jaridu masu fitar da abin da ke faruwa daga fadar shugaban kasar, manya-manyan mutane suna zazzaune saman tsadaddun kujerun dake a cikin É—akin, wayan nan kujeru sun haÉ—u matika gaya, kuÉ—in wayan nan kujeru ba zai faÉ—u ba saboda tsadarsu, ta ko'ina Kamshi ke tashi a cikin fadar, amma Lion na shigowa kamshin perfume na jikinsa ya rinjayi gaba É—aya kamshin da yake a wajen, sai room É—in ya gauraye da irin kamshin perfume nasa, wani daddaÉ—ar sanyin Ac ne ke a cikin É—akin, wadda sanyin yana gudu daidai misali ba na wuce ka ida ba, ko wannan su akwai kayan sha masu bala'in sanyi a gabansu ga kuma kyawawan glasses cups a gabansu kusa da abin shan.

Shigowar Lion yasa gaba É—ayan su suka É—ago suka kalle shi, dayawa daga cikinsu kallo É—aya suka yi mashi suka kawar da kansu suna É—an satar kallonsa. Bai bi ta kan kowa ba, saman kyakkyawar kuma tsadaden kujerar kusa da His Excellency ya je ya zauna, shiru suka É—an yi kafin His Excellency ya buÉ—e masu taro da fara magana.

Kasa Lion ya yi da kansa dan bai ma san akan me zasu yi maganar ba, lokacin da aka kawo mashi takardan bai duba ba, yana wani aikin, sai dai Tga ya sanar mashi cewa karfe 10 za'a yi zaman, iya abin da ya sani kenan, kuma dama bai nemi sanin akan me za su yi taron ba, domin ba ɗaukar maganar su yake yi ba, abin da ya zo mashi a cikin ƙwaƙwalwarsa kawai yake aikatawa.

Kowa ya fara magana yana faÉ—an arbarkacin bakinsa akan kuÉ—in da za'a fitar dan kera manya-manyan makamai wadda karfinsu zai iya tashin state guda, ko uppan bai ce da su ba, kowa sai magana yake yi, shi hasalima ciwon kai suke sanya mashi wannan surutu da suke yi, ji yake yi tamkar ya bar wajen amma bai yi hakan ba, saboda akwai abin da yake son fahimtar a tattare da su.

An samu bambance bambancen ra'ayoyi dan gane da fitar da wannan kuÉ—in, wasu sun ce yes a fitar wa su kuma sun ce a'a kada za'a fitar yana da kyau a karawa yan kasa abun yi ne, ma'ana marasa aikin yi domin a ragewa kasa talauci, tun da suna da makamai sosai kawai a buÉ—e masana'antu companys da dama a É—ebi ma'aikata talakawa da ba su da abin yi domin kasar su ta sake tsabtatuwa daga cutar talauci, shi dai Tga ya tsaya akan gara a sayo kayan haÉ—a makamai domin sun fi mashi talakawan nan mahimmanci, shi kuma His Excellency hankalinsa ya fi rajaa akan gara a buÉ—e masana'antu saboda ba shi da burin da ya wuce kasarsa ta cigaba da zama super pawer ta duniya, ya fi son ya ga ya fi kowacce kasa komai.

Ganin sun dame shi da surutune yasa ya miƙe ba tare da ya ce komai ba ya nufi waje, bai kai ga fita ba His Excellency ya ce ina zai je ba su gama zama ba, shiru ya yi bai yi magana ba har sai da ya kai kofar fita sannan kasa kasa ya ce "Uncle please idan kasan irin wannan zama za ku yi kada ka sake kirana". Cikin sauri His Excellency ya ce "To yanzu dai gaya mani naka shawarar mu ji". A takaice ya ce a gina masana'antu, sannan ya wuce ya nufi waje abinsa, gaba ɗaya wajen tsit suka yi, domin sun san koda sun yi magana ma abanza ne tun da Lion ya ce masana'antu za'a gina tofa abin da za'a yi kenan, a ɓangaren His Excellency kuwa tuni ya yanke hukuncin abin da Lion ya faɗa shi za'a yi har ya fara shirye-shiryen rubutawa majalisa takarda dan a samu a saki kuɗaɗen da wuri a fara gabatar da aiki domin kawar wa da kasa talauci.

*Allah sarki manyan kasashen kenan kullun burinsu ta ya za'ayi kasar su ta ci gaba, burinsu a kullun kasarsu ta kasance ta farko a duniya wadda zata mulki ko wace kasa kuma ta juya su yadda take so, kuma sun san cewa kasarsu ba zata taɓa ci gaba ba, har sai sun raba yan kasa da talauci da mutuwar zuciya, da hanya ɗaya kawai zasu iya yin hakan, shine su rinƙa gina masana'antu suna bawa yan kasa talakawa aiki ana sarrafa abubuwa daga masana'antun ana fitarwa kasashen duniya ana sayarwa, su ci riba kuma sun raba matasansu da zaman banza zaman kashe zuciya, ya Allah ka sanya shuwagabannin muma su farka irin haka, Allah kasa su zama irin haka, ba wai bukatarmu a ɗauki kuɗi a bamu ba, a'a a gina mana abun da zamu rinƙa zuwa muna aiki a ciki muna samun halak ɗin mu ko ya yake, ya dai kasance kullun zamu je mu yi aikin mu samu, amma idan kuɗi za'a bamu kwana biyu kuɗin sun ƙare an koma gidan jiya😭 wani kuɗin ma idan aka baka abin ko karamar buƙatarka ba zai biya maka ba, please aikin yi muke so ba kuɗin da bai taka kara ya karya ba🥺😭🙏*

Lion yana fita gida ya koma ya yi wanka ya kwanta yana tunanin yadda tafiyarsa zata kaya, sai karfe 2 ya ci abinci Bawan Allah nan.

A ɓangaren su Musharraf kuwa, Michael na toilet yana wanka shi kuma ya fara haɗa tea ɗin sa don ya sha, domin bashi da wani abincin da ya wuci tea, bawan Allah, yana tsoron cin abincin gidan tun da ba musulmai bane kada ya je ya ci abin da Allah ya haramta mashi ci, hakan yasa ya kikaye kansa daga tea sai fruits kawai yake laptawa cikinsa.

Bayan ya zuba duk wani abin da zai bukata a cikin cup, sai ya ɗauki flaks ɗin ruwan tea ɗin, ya buɗe ya fara zubawa a cikin cup ɗin, sai zuba ruwan yake yi, amma cup ɗin taki cika, na cikin flaks ɗin kuma yaki karewa, idan ya cire flaks ɗin daga bakin cup ɗin zai ajiye sai yaga cikin cup ɗin babu komai, alamar ruwan tea ɗin bai zuba a ciki ba kenan, idan kuma ya sake mai da flaks ɗin yana zuba ruwan, tofa sai dai ya yi ta zubawa amma ba zai ga komai a cikin cup ɗin ba, abin ya ɗaure mashi kai, ya kuma tsorata shi sosai, yana tsaka da zubawa sai yaga ruwan tea ɗin ya canza kala daga brown zuwa jawur kamar jini, har wani yaukin jini yake yi, ihu ya kurma tare da sakin flaks ɗin ya yi baya zai faɗi, cikin sauri Michael da ya fito yanzu ɗaure da towel a kugunsa, ya yi maza ya riƙosa yana faɗin

"Uncle ɗin james lafiya kuwa?". Kasa magana Musharraf ya yi sai sunan Allah da yake iya kira a cikin zuciyarsa, amma ya kasa iya furtawa a bakinsa, ganin hakan yasa Michael ya zaunar da shi a saman ɗaya daga cikin chair ɗin table ɗin yana faɗin "Uncle ni bansan meke damunka this two days ba, sai ka rinƙa yi mana ihu yanzu kasa ni fitowa ba shiri" ya kai karshen maganar tare da komawa cikin bedroom nasa domin shiryawa, Allah sarki Musharraf shi ya ga abin da ya gani, a hankali ya ɗaga idanuwansa ya sauke su saman table ɗin, abin mamakin sai yaga komai ya koma yadda yake, duk wasu madara da ya zuba a cikin cup ɗin duk sun koma cikin robarsu, sai lokacin kuma ya samu damar kiran sunan Allah, yana kira kuma ya samu kwarin gwiwa ya tashi ya haɗa tea dinsa ya ɗauka ya nufi cikin bedroom ɗin, yana shiga ya samu Michael naɗe saman bed ya shige cikin bargo.

Da mamaki ya ce "Asif ya na ganka kana kwance? Ba wajen Lion zaka je ba ne?". Can kasa-kasa ya ce "Uncle dan Allah ka kyakeni sai da safe zan je wajen Lion ɗin, now I'm feeling sleeping over" Ya kai karshen maganar tare da janyo barkon ya rufe har kansa, abin ya kara ɗaurewa Musharraf kai, yanzu fa Michael ya fito lafiya Lou baya jin barci, amma daga shigowarsa ɗaki ba'a fi two mins ba wai barci yake ji, anya babu lauje a cikin naɗi kuwa,? Ya yi wa kansa tambayar da bashi da amsarta, ganin ba shi da amsa kuma ya sa ya ce "Asif abinci fa?" Shiru Michael bai amsa ba, da alama ya yi barci ne. Jin haka yasa ya miƙe ya koma saman sofa ya zauna.

Tas ya shanye tea É—in sa, ya mai da cup É—in palo, ya dawo shima ya yi wanka tare da shirin barci ya kwanta a bedroom nasa. Asuba ta gari.

Shima dai Lion kamar kullum wanka ya yi ya kwanta ransa fes sai tunainin James nasa yake yi, shima time to time ne dan yanzu tun da ya gano A.E.A bai sa wata damuwa sosai akan ɓatar James ɗin, jima yake yi tamkar ya dawo da James ɗin. Barci mai daɗi suka yi yau, mai cike da annashuwa, ga shi wuraren karfe 1 dare an tapka ruwan sama sosai, sai barcin ta kara armashi.

A NIGERIA KUWA.

Kamar kullum Rimsha na tashi karfe 6 na safe, ta zo ta gyare ko'ina tsab, daga bedroom nata har palo, sanna ta ɗaura masu abinci, yau Akila tana da glass karfe 10 tun karfe 7 ta zo suka fara aikin girki a tare, shima Akil ya bar Umaisha a kan ta zo ta rinƙa koyan girkin, dan ya ji daɗin abincin jiya sosai.

Kamar jiya yauma a tare suka yi girkin, bayan sun kammala, kamar yadda suka saba suka jere a Palo, ko wacce ta wuce É—akinta dan ta je ta yi wanka.

Bayan sun yi wanka sun shirya ne suka sake dawowa suka haɗu a Palo, Imran ne ya kira Akil a waya ya zo suka haɗu suka yi breakfast a tare, Akila ta tambayi Imran ko dai su rinƙa sakawa Ammi da Abba abinci ne, e ya amsa masu da shi tare da zuba masu ruwan albarka, sai murna suke yi suna amsawa da Amin.

Bayan sun kammala Rimsha ta ce Akil ya kara mata karatu shafi biyu, to ya ce mata sannan ta kara karanto mashi na jiya, sosai ya ji daÉ—i yadda take son karatu kuma take mai da hankalinta sosai a kan hakan.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.