Rashin Sani Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rashin Sani Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 4 of 7
part d'in Ganez suka fara shiga suka iske Nisah zaune kusa dashi,
Sanah tace " oh! ashe dai har yanzu ana tsinkar korawayen fure?
Duk sukayi dariya kana Ganez yace " a'a aini idan bada ku zan tsinki korayan fure ba,
ai a banza, Khulud tace " kinji shi zayyi mana wayo kullum yayi ta cewa idan ba mu ba sai rijiya,
Sanah tace " kuma yana tsoran matarsa ba,
Nisah tayi dariya kana tace " oh! kuji man yara,
wato kun saka mana ido, ai irin haka ake so,
Khulud tace " mijin ya rink'a jin tsoran matarsa?
Nisah tace " eh mana,
Sanah tace " ina fa dad'i miji ya zama mijin tace,
an dai mayar mana da kakanmu tace kawai,
Nisah tace " wannan ai kan tace ne ma,
duk sukayi dariya kana suka fita suka nufi part d'in Danish,
ganin Erum tayi kwalliya yasa su yin dariya,
Khulud tace " wato ke har yanzu baki dai na kwalliyya bako?
Erum tace " ina ni ina daina kwalliya,
Sanah tace " kici zamaninki kici na wasu ko?
"Sosai ma kuwa cewar Erum,
" a'a kace yau amare nane a gidan,
cewar Danish dake fitowa daga bedroom d'insa,
Sanah tace " mune, munzo a bamu abinda akaci aka rage,,
Danish yace " ku da kuke amare ina ku ina raguwa,
ai sai dai sabuwar dahuwa,
Khulud tace " ai dama kun saba yi mana wayo,
bayan duk tsoron matan ku kukeji,
Erum tace " ai irin wannan k'arshen ake so ayi yara,
ku ma kuyi addu'ar Allah ya baku ita mu,
Sanah tace " wai ma duk ba wannan ba,
ina zaku na ganku duk kunyi kwalliya?
" Mu da muke da walima yau har a tambaye mu inda zamu dan munyi kwalliya,
Erum tayi maganar tana dariya,
Khulud tace " a she walima ce daku,
a ina kuma?
Erum tace " sosai ma, kuma a nan gidan,
Sanah tace " tab wai wacce walimar kuke nufi?
Badai tamu ba ko?
Tayi maganar a lokaci d'aya,
Erum tace " walimar ku ko tamu?
"Ai muke da walima kuwa,
tunda mune manyan k'awaye,
tayi maganar tana dariya,
Khulud tace " mu dai bamu gayyace ku ba,
kuma bamu san gayyar sod'i ehe,
duk sukayi dariya kana suka fita,
part d'in Juju sukayi,
da sallama suka shiga,
Didi ya amsa musu cikin fara'a,
kana yace " 'yan candy ne yau a gidan namu?
Sanah tace " mu ne,
Didi ya kalli Juju yace " ina kika b'oye mana su ne?
Juju tace " wacce ni?
" Ai sai dai ka tambaye Mamun su,
ni tunda sukayi candy ban sa su ido na ba,
sai yau, ko irin kayan kayan candy nan ba'a kawo mana ba,
balle muce mu shaida anyi candy,
muce Allah ya sanya alkhairi,
Khulud tace " kai Juju Allah bamu zauna bane,
mu ta yawan zuwa saloon da k'unshi,
Sanah tayi dariya kana tace " Juju ku da zaku bawa wasu ma,
kayan candy kuma ga walima nan kun shirya ku da kanku,
sai ku shaida anyi candy kuyi addu'ar Allah ya sanya alk'airi,
Didi yayi dariya yace " wai Sanah baki abin magana,
ke dai ba'a tab'a k'ure ki ta wajen magana,
Juju tayi dariya tace " ai ni nayi shiru tunda an fini baki,,,
dama hausawa sunce dokin mai baki yafi gudu,
Didi ya kuma yin murmushi kana yace " Sanah yaushe jamb d'inku zata fito?
Sanah tace " naji ance this coming Monday,
Juju tace " wacce university kika cike?
"First choice BUK second kuma ABU Zaria,
Didi yace " masha Allah Ubangiji ya taimaka, Allah ya bada sa'a,
duk suka amsa da Amin,
har Khulud dabata zana jamb d'inba,
dan cewa tayi ita ta gama karatun boko har abada,
Juju ta kalli Khulud kana ta mayar da kallan ta ga Didi tace " 'yar Abbu da Mamu ita aure take so,
Khulud ta d'ago kanta da sauri suka had'a ido Juju tayi saurin sadda kanta k'asa tace " Allah Juju ba haka bane,
tayi maganar a shagwab'e,
Juju tace " idan ba haka bane to yaya ne?
Khulud tace " Allah ni ban san cigaba da karatun ne kawai,
ni kwata-kwata ban tab'a sha'awar yin karatun boko mai zurfi ba,
Juju zata kuma yin magana,
Didi yayi saurin cewa " haka ne ai kowanne mutum yana da nashi ra'ayin,
hakan ma da kikayi dai-dai ne dabaki yaudare iyayenki kin shiga jami'ar ba,
kana kik'i yin karatun ko wata matsala ta faru,
so ni ina ganin kinyiwa kanki da Abbunki adalci,
Allah ya zab'a maku abinda yafi alkhairi a rayuwarku,
ya haskaka rayuwarku ya sanya albarka acikinta,
duk suka amsa da Amin,
fita sukayi suka nufi wajen da aka tanada dan yin walimar da tuni k'awayensu sun fara zuwa,
sosai walima ta kankama haik'an,
aka ci aka sha sosai dan sosai Abbu ya saki bakin aljihunsa dan nuna tsantsar farin cikinsa na kammala karatun yaransa lafiya,
sosai aka rarraba kyaututtuka,
kana kowa ya watse cikin farin ciki aka gama walimar lafiya.
Sannu a hankali matsanannaciyar soyayyar Khulud tayi mugun kama Hanash,
ta addabi ruhi da gangar jikinsa,
kwata-kwata ya rasa sukuni da walwalarsa,
ya rame sosai dan raban dayaci ishashshen abinci ko ya samun bacci har ya manta,
kullum yana cikin bedroom ko parlor'nsa,
dan ko fituwa sosai ya dainayi sai dai ya fito ya gaida iyayshi ya koma,
yauma kamar kullum kwance yake a d'akinsa ya tsunduma duniyar tunaninta,
idanshi rufe babu abinda yake gani sai ita tsaye a gabansa,
tana sakar mishi k'ayataccen murmushinta,
jin knocking yasa shi bud'e shu'uman idanuwansa,
k'ofar ya zubawa ido na tsayin lokaci,
batare da yayi wani yunk'uri ba,
sake knocking akayi a karo na biyu,
dakyar ya iya cewa " waye?
Muryar Papu yaji yace " mu ne,
dan sun kasa jurewa ganinsa cikin wannan mawuyacin yanayin,
da sauri ya mik'e ya bud'e musu k'ofar suka shigo,
akan sofa duk suka zauna, a hankali Mimmee ta d'ora hannunta akan kafad'arsa,
had'i da zubawa d'an nata ido,
Papu ma ya zauna kusa dashi ya zuba masa ido,
kansa ya duk'ar dan ya san kwanan zancen,
muddin akace bashi da lafiya ko yana cikin damuwa to gaba d'aya gidan babu mai yin walwala,
a hankali Papu ma ya d'ora hannunsa akansa kana ya kira sunansa,
" Hanash,
"na'am, Hanash ya amsa cikin ladabi,
" meke damunka?
Cewar Papu a tak'aice,
murmushin k'arfin hali Hanash yayi kana yace " babu abinda ke damuna Papu,
yayi maganar while kanshi k'asa,
Mimmee ta shafa kansa kana tace " Hanash please karka b'oye mana abinda yake damunka,
ka daure ka sanar damu koda babu wani abu da zamu iya yi akai,
sai mu tayaka da addu'a,
ta fad'a cikin damuwa,
murmushi Hanash ya kuma yi kana yace " ba ni da lafiya ne,
Mimmee zazzab'i da ciwon kai ke damuna,
ido Mimmee ta zuba mishi tana nazarinsa dan ita kwata-kwata bata yarda da abinda yace ba,
Papu yace " kaje hospital?
Hanash yace " eh Papu,
"me sukace yana damunka?
Papu ya kuma tambayarsa,
d'an shiru Hanash yayi kafin yace " Malaria,
" to ikon Allah kai ko ina kaga sauron daya cije ka?
Mimmee ta fad'a tana kallan kwayar idansa,
murmushi yayi kana yace " Mimmee, cikin shagwab'a,
Papu yace " shi ciwo ai daga Allah ne, ba ta inda baya shiga jikin mutum ko son?
Yayi maganar cikin tsokana,
dan shima yadai ji Hanash ne kawai,
amma bai yarda da abinda ya fad'a ba,
babu yadda Papu da Mimmee basu yi akan Hanash ya sanar da su damuwarshi ba, amma yak'i yace babu abinda yake damunsa,
Papu yace " Allah ya sauwak'e,
ya amsa da " Amin, kana suka fita,
suna fita Hanash ya koma ya kwanta,
had'i da rufe idansa.
Ranar Monday jamb ta fito,
Sanah cikin murna da d'oki suka je ita da Aarib & Khulud suka duba,
a cafe, aiko taci sosai dan ta samu 251,
tsalle ta buga ta rumgume Khulud da Aarib cikin matsananciyar murna,
motar su nayin parking a harabar gidan ta fito,
ta shiga kwalawa Halan kira,
da gudu ta shiga part d'in Halan,
ta iske ta parlor zaune ita da Ziyad,
cikin murna ta fad'a kanta, ta ma manta da tsohon cikin dake jikin Halan,
Ziyad ya daka mata tsawa had'i da cewa " ke baki da hankali ne ko baki ganin abinda ke jikinta?
Bata kula da tsawar daya daka mata ba,
sai ma kiss datayi mishi a kumatu,
cikin murna tace " Yaya naci jamb,
ta fad'a tana tsalle,
dariya Halan tayi tace " kai masha Allah gaskiya nima nayi murna,
badan kayan dake gaba na ba,
da har dani za'ayi tsallan,
Ziyad yayi dariya yace " bani abu na inyaso sai kije kiyi tsallanki,
Halan ta kalleshi had'i da zumb'uro baki tace " Allah da ana bayarwa ai bama sai ka tambaya ba,
Sanah da Khulud suka fita da gudu suka nufi part d'in Mamu,
suna zuwa Sanah ta fad'a kan Abbu,
yace " kai Sanah ke dai baki girma,
naga alamar so kike ki karya ni tunda baki ganin na tsufa yanzu,
Sanah tayi mishi kiss tace " Abbu albishirinka,
yana dariya yace " goro,
tace " fari ko ja?
Yace " fari tass,
tace " Abbu na ci jamb,
Abbu yace " wai dole ayi murna,
Mamu tace " masha Allah,
saura waec & neco,
Abbu yace " suma duka za'a cinye su,
in sha Allah,
fita sukayi suka nufi part d'in Juju,
nan ma aka sanar mata anci jamb,
murna kam ba'a magana,
a week d'in waec ta fito,
Sanah ta samu result mai kyau,
result d'inta yayi mugun kyau,
bayan two weeks BUK ta kira su first UME,
bayan week nan ma result ya fito,
ta samu taci, suka bata Admission letter na BSC COMPUTER SCIENCE.
Kullum Hanash bashi da wani aiki sai mafarkin Khulud,
da tunaninta ko idansa ya rufe ita yake gani,
koyaya ya rufe idansa ita yake ya gani,
abun duniya duk ya dame shi,
ba shi da wani burin daya ce na sake ganinta a yanzu,
ko da sau d'aya ne a rayuwarsa.
Yau itace rana ta farko da Sanah zata fara hallartar BUK,
ta gama shirinta tsaf cikin riga da siket na material red color d'inkin yayi masifar yi mata kyau,
ya amshi jikinta sosai, ta saka high hill shoe ta yafa mayafinta mai kyau kalar flowers dake jikin material d'in black,
sosai Sanah tayi shegen kyau,
duk da ba wani make up tayi ba,
ta dayyi simple make up abinta,
wanda ya bayyanar da tsantsar kyauta,
har cikin makarantar Aarib ya kaita,
sai da yayi mata fad'a sosai kana ya tafi,
sannu a hankali take tafiya harta isa department d'insu,
tambaya tayi,
aka nuna mata, inda zasuyi lectures yau,
dayake tana da time table na duka courses & time d'in su,
a hannunta tasan Computer lectures zata fara attending,
zama tayi a inda taga students na zama,
zamanta ke da wuya ta fara jiyo hirar students,
" yau fa Sir Aryan ne damu,
kasan ko ba sauk'i, d'ayan yace " wallahi ko ni gaba na ma sai fad'uwa yake yi,
tun jiya dana duba naga shine damu hankali na yake a mugun tashe,
wani daga gefe yace " kai ai Malamin nan bai da kyau,
d'ayan yace " kaga fito sak a mutum kai tsaye kace bai da mutunci,
d'ayan yace " ni fa yana mugun ban mamaki shi ko irin na sauran lectures d'in nan bayyi,
d'aya yace " me?
" San mata mana,
d'ayan yace " kai tanan wajen ai Sir Aryan yayi wallahi,
ba ruwanshi da mata, duk kyanki yanzu zai yarfa ki,
ba kamar sauran lectures d'in ba,
shegu da sunga mata sai suyi ta rawar jiki,
idan mune 'yan uwansu maza tsakanimu dasu ba mutunci,
sai su rufe ido su karta mana,
amma shi kwata-kwata mace bata isheshi kallo ba,
naga 'yan mata dayawa sunyi mugun matuwa akansa,
d'ayan yace " aiya had'u ne ga kyau ga kud'i, kaga kuwa ai dole mata su matu,
tunda ready mate ne,
d'ayan yayi dariya yace " aiko suna shan dizgi da wulak'anci a wajensa ba,
dan yanzu zai kartawa mutum rashin m,
idan ta kama ma ya yarfa maka mari ba ruwanshi,
shege ga girman kai da d'agawa da jan aji dan sai kayi mishi magana goma amma dakyar idan yaga dama zai amsa maka d'aya ,
d'ayan yace " kai ai ya iya d'aukar wanka dacin uwar sutura,
yana zagin gizna ta asalimma,
ni na rasa uban me yake yi a makarantar wallahi,
"hmmmm ga babu ruwanshi da ke wai mace ce,
shi hukunci d'aya yake yi tsakanin mace da namiji,
idan ya riga ka shiga class ko waye ubanka kuma ko uban ya tsaya maka ya d'aure maka gindi baka shiga,
d'ayan ya duba agogo yace " sauran just 5 minutes ya shiga fa,
kusan kuma baya African time,
d'an tsaki Sanah tayi a hankali kana ta mik'e tabar gurin,
saboda duk gurin wajen mutum 100,
maganar mutum d'aya suke tayi Sir Aryan,
duk inda students sukayi d'an group,
maganar shi kawai sukeyi mata da maza,
daga maganar had'uwarsa kyansa, gayu, ajinsa,
sai ta wulak'anci da dizginsa da kuma girman kansa,
da yadda mata suka mato akansa yake wulak'antasu,
shiyasa duk randa yake da lectures dasu suke kaffa-kaffa.
Can gefe ta koma ita kad'ai ta zauna,
ita kad'ai kasancewar yaune farkon zuwanta bata san kowa ba,
tana daga zaune taga wata matsiyaciyar had'add'iyar mota ta danno kai cikin makarantar,
students na ganin motar suka kai duba zuwa number motar dan su tabbatar idan shi,
saboda baya hawa motar d'aya,
duk nacinka baka isa kace ga yawan motocinsa ba,
ta number motarsa kad'ai suke gane shi ne,
saboda sunan family d'in su ne a duka number motacinsa,,
ai students na tabbatarwa shine,
suka fara gudu maza da mata ana rige-rigen shiga class.
Yana yin parking, ya zare key d'in tare da komawa ya kishink'id'a jikin kujerar, ido ya lumshe tare da fesar da numfashi mai sanyi, a hankali ya kuma bud'e idon tare da sauk'e ajiyan zuciya, yana mai shak'ar k'amshin jikinsa dana mortar, a hankali ya sa hannun damanshi ya dafe saitin k'ahon zuciyarshi dan jin gabansa yana muguwar fad'uwa da k'arfi,
bugun zuciyarsa ya k'aru sosai,
zuciyarsa ta rink'a bugawa so past,
idansa ya kuma lumshe yana k'ara d'an kishingid'a akan kujerar motar,
a hankali ya furta " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
saboda yadda yake jin
duk ilahirin jikinsa ya mutu, gabansa na mugun fad'uwa zuciyarsa na bugawa da tsananin k'arfi, addu'ar yayi ta maimaitawa dan baya son ayi mishi African time shiyasa shima baya son yayiwa d'alibanshi, bere daga inda yayi parking yana iya hango yadda suke sassarfan shiga class, sharshesa ya fitar tare da d'an laso lips nashi, hadi da d'an cizawa dan kauda kasalar dake saukar mai a jiki,
a hankali ya b'alle marfin motar tare da zuro k'afarshi d'aya woje, baki ya d'an tab'e ganin yadda wasu matasa suka wuceshi da sassarfa, gudun karya rigasu shiga class, ya hanasu shiga, fitowa daga cikin motar tare da jawo laptop nashi, ya bud'eta tare da dorata kan hannunshi daya mik'ar, yana kuma d'an lallatsashi cikin k'orewa, ajiyan zuciya ya sauk'e tare da fara takawa zuwa class d'in yana mai jin dad'in iskar dake busawa sirrai da fawowi suna shawagi tsuntsaye na kai komo ga k'amshin furanni dake ratsashi.
Cikin takunsa na isassun maza masu haiba da kamala ga tarin nagarta yake tafiya cap-cap sautin takalminshi ke ratsa wurin in dalibai sun hangoshi sai suna rusunawa tare da ratse mishi.
Ganin yadda students ke gudu yasa Sanah kai idanta kan motar dataga kamar an saka MOLI'S 15,
amma data duba so sai taga kamar ba haka bane,
baki tad'an tab'e kana ta mik'e cikin takunta mai daukar hankali tabi bayanshi,
ta nufi class itama,
daga bayansa ya rink'a jin kamar takun mutum a bayansa k'at-k'at,
Fuska ya kuma had'ewa dan ya gane mace ce, daga k'asa ya kalli k'afarta data sha kunshi mai ja da bak'in lalle yayi masifar yi mata kyau,
gabansa ne yayi muguwar fad'uwa lokacin daya d'ora idansa akan k'afarta, sake had'e rai yayi , kana ya cigaba da tafiya,
yana tafiya tana binsa a baya,
har suka zo gaf da isa class d'in,
Kai ya d'an jinjina tabbatarwa da yayi class d'in sa zata shiga , hankalin shi na kan laptop d'inshi, hannunshi mai yin typing d'in ya d'an d'aga shi saman kafadarshi ta yadda zata gani, sanan ya had'e doguwar yatsarsa ta tsakiya da babbar yatsarsa ya kettasu sau d'aya ta yadda ya bada sauti, sannan ya had'e yatsunsa biyu ya kad'asu kamar mai buga fiyano ya mata nuni data tsaya inda take karta biyoshi,
batare daya juyo ya kalle ta ba bai kuma tsayaba yaci gaba da takunshi zuwa cikin class,
Itako Sanah bata gane abinda yake nufi ba,
dan haka taci gaba da binsa a baya,
Kai ya jinjina tare da yin gutun murmushi, mai dauke da alamar zaki gane kurenki,
kana ya cigaba da tafiya har suka k'arasa cikin class d'in,
Sanah tazo zata wuce mazaunin d'aliban, *"Keeh"* kamar daga sama sautin muryarsa ya ratsa shirun daya ratsa ajin,sai sautin takalminta dake amsakuwa, shirune ya sake ratsa ajin duk sunsha jinin jikin su, ita kuwa Sanah kai ta d'ago ta kalleshi ,Amman bata ga fuskarsa ba dan baya ya bata, sai gashin k'eyarsa da ta tsurawa ido ganin shi a kwance lub sai wani lauyewa a yayi ya bi k'eyan nashi yana Shek'i, tana cikin nazarin da me tayi mishi ta kuma jiyo muryarshi na ratsa ajin baki d'aya taji tajiyo muryarsa nacewa yana cewa, *"kneeling down,"*
ya fad'a still bai jiyo ya kalle ta ba,
juyawa tayi bayanta taga babu kowa sai ita kad'ai,
cikin mamaki ta kalli bayansa dan ita a iya saninta tasan ba'a saka Patick a jami'a.
Cikin mamaki ta kuma kallan bayansa,
batare daya jiyo ba taji yace *"ko bazaki kiyi bane?"*
Muryar dataji ta daki dodon kunnenta,
tasa gabanta mugun fad'uwa a razane ta kuma kallan bayansa,
babu damar taga fuskarsa saboda ya juya mata baya,
a hankali Sanah ta d'an zumb'uri baki kana tayi kneeling down d'in,
gaba d'aya students mamaki ya gama cika su,
duk da sun san halinsa, sun tabbatar zai iyin abinda ma yafi hakan,
dan sun san mari ko dizgi abu ne mai matuk'ar sauk'i a wajensa,
amma basu tab'a ganin yasa wata ko wani kneeling down ba,
sai yau kuma daganinta new comer ce,
students suka rink'a yin dogon wuya suna l'eka ta,
jin muryarsa ta fara explanations yasa duk suka shiga hankalinsu.
Sanah na nan har ya gama lecture tana ta zumb'ure-zumb'uren baki,
Cikin k'asaita ya fito zai tafi , ganin ya wuce ta gabanta amma bashi da niyyar ce mata komai,
yasa ta cewa *"Sir to ni wuni zanyi a nan ne? "*
Tsayawa yayi cak a inda yake,
kana ya juyo da fuskarsa a hankali ya zuba mata ido,
had'i da hard'e hannayensa a k'irji,
mik'ewa Sanah tayi batare daya bata umarnin tashi daga kneeling d'in ba,
kanta a sunkuye tana kakkab'e siket d'inta,
tana yin magana k'asa-k'asa, "eh wato kai zaka fece gidanku ko, ni kuwa in zauna a nan, sai kace baiwar gidan ku ka samu ko, hegen k'eya! da nad'edd'en gashi ,
hege mugu kawai , d'an masu k'aton kai."
dan ita a tunaninta ya tafi shiyasa ta d'anyi halin, baki ta murgud'a tare da mik'ewa tsaye,
d'ago kan da zatayi, keda wuya sexy eyes d'inta,
suka sark'e cikin na *SIR MOLI* dayake tsaye hard'e da hannuwa yana kallan ta..................
*_Aunty AISHA ALIYU GARKUWA_*
_kina tambayar inda nakai miki Sir Molinki to gashi nan na maido miki abinki_
~To fans masu tambayar ina nakai Sir Moli na b'oye har tsayin six years, gashi nan ya dawo~
~sai a cigaba da gashi a! d'ora daga inda aka tsaya~
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣0⃣
Ido ya d'an tsura mata na wani d'an lokaci,
yana mamakin yadda akayi har yanzu bata canja hali ba,
halinta yana nan babu abinda ta canza ko ya ragu,
sai ma abinda ya k'aru,
dan tuni Sir Moli ya gane Sanah,
tunda ya kalli k'afarta ya gane itace,
basarwa kawai yayi saboda halin muskilancinsa,
amma tuntuni ya dad'e da gane itace SANAH HAMRAZ,
itama Sanah ta gane shi tunda ta d'ora idanta akansa ta gane shine,
kallansa itama take yi ido cikin ido,
bata ko k'iftawa tana mamakin yadda ya canja, kyansa, kwarji da haibarsa ta kuma k'aruwa fiye da da,
fuska ya kuma tsukewa tare da cewa " Zo nan".
ya fad'a had'i da juyawa ya nufi office nashi,
baki ta turo kana tabi bayansa,
har suka isa office d'insa bai jiyu ya kalle ta ba,
shiga ciki yayi ya zauna akan kujerar zamansa,
ya d'ora laptop d'insa akan table d'in dake gabansa sannan ya maida hankalinshi kaco kam bisa laptop d'in yana sarrafata cikin k'warewa da, shiru ya ratsa office d'in sai sautin yatsunshi dake kan pins din system d'in yana typing,
Ita kuwa tana tsaye a gefenshi,
ta k'ura masa ido tana kallan yadda hutu da k'udi suka nuna k'arara a jikinsa,
da gani ba sai an fad'awa mutum ba kasan yana cikin jin dad'i da more rayuwa,
dogayen yatsunsa ta d'an saci kallon su, ido ta d'an juya ganin yadda skin d'inshi ya murje tsananin farinshi ya k'ara bayana,
kana ta kai duba zuwa kwantaccen gashin kansa,
wanda ya gangaro gefen fuskarsa zuwa hab'arsa yayi masa saje,
komai a fuskarshi mai kyau ne,
musamman idonsa da d'an k'aramin bakinsa mai d'auke da zayen tattausan suma da yayi mashi k'awanya sai jajayen lips d'inshi dake ta shek'i a tsakiyar kota million d'inshi,ga hak'ora farare tass,
ga dogon hancinsa, idan ka ganshi sai ka rantse ba indiyene,
musamman ma daya kasance fari tasss dashi dogo,
tun suna Roni yake mugun yi mata kama da Hiritik Roshan,
bata gama tantancewa da tsananin kamarsa da Hiritik ba sai yanzu,
dan idan aka jera maka Sir Moli da Hiritik baka isa ka banbance d'aya daga cikinsu ba,
dan har k'asunbar da Hiritik ya tara shima Sir Moli yana da ita,
har eye color d'in Hiritik datake brown color,
shima Sir Moli haka tashi eye color d'in take.
" har yanzu dai halin muskilanci da wulak'anci da girman kai d'in yana nan!
hmmm mai hali dai baya tab'a canja halinsa"
ta fad'a cikin ranta.
Shiko Sir Moli ya lura sarai da irin kallan mamakin da Sanah keyi masa,
wanda shima mamakin mugun kyau da girmanta yake yi,
musamman skin color & dimples da wushiryarta,
sunyi bala'in burge shi,
amma babu abinda yafi d'aukar hankalinsa a jikinta kamar sexy eyes d'inta,
da kuma structure d'inta,
girmanta ba k'aramin mamaki ya bashi ba,
duk da dama can tun tana yarinya tana da kyau,
amma dayake yanzu ta girma mak'erin 'yan matanci ya k'era ta sai yaga ta k'ara kyau,
sai ta zama kamar hurul'in (matan aljanna),
Idanshi nakan system d'insa yace " wannan kallan fa? Ko na miki sata ne ,kikaga abunki a guna da zaki tsareni da ido, ko ajiyan wani abunki kika bani yanzu kike so in maida miki?".
Da sauri ta d'auke idanta daga kansa,
"ko kin sanni ne?".
Ya kuma tambayarta batare daya d'ago kansa ba,
mamakin tambayar da yayi mata ne ya kamata,
danta tabbatarwa kanta ya gane ta sarai,
" halin za'a tab'a kenan,
tayi maganar cikin ranta,
a fili kuma cikin muryarta mai d'an tsiwa tace " a'a ban sanka ba,
ina zan sanka?".
Sosai shima yayi mamakin amsarta,
dan shima ya tambatar ta gane shi,
amma dayake yasan halinta sai ya basar,
yace: "
To meyasa zaki tsareni da kallon maita, cinyeni zakiyi ko?". Shiru tayi dan ta gane tijara zai mata ,
shi kuwa ganin tayi shiru yasashi ce mata,
"Me sunanki?".
Still bai d'ago ya kalle ta ba,
tace " SANAH HAMRAZ,
"wacce school kikayi?".
Ya kuma tambayarta idan shi nakan system,
tace " primary ko secondary?".
"Both, ya bata amsa a tak'aice, tare da tab'e baki,
A hankali tace:
" primary gate way nayi,
secondary school kuma Computer Girls Secondary school Roni na fara,
daga baya na koma Momy Speed na k'arasa a can"
"ba'a Roni kika gama ba kenan?
" Eh". ta bashi amsa,
"To meyasa?".
Ya kuma tambayarta,
rolling lulu eyes d'inta tayi kana tace " kawai haka nan".
yadda ta juya idanta yasa shi d'an d'agowa ya d'an kalleta a dai'ile, kana ya mayar da idansa ga abinda yake yi,
yace " wanne gari kike?".
"Kano, ta bashi amsa kai tsaye,
" wacce unguwa?
Ya kuma tambayarta while bai kalli inda take ba,
idanta na kansa tace " duk wannan tambayoyin fa na meye ne, ko cinye wani nai ake neman gidan mu?".
Ba tare daya kalle ta ba, yace " out!!!".
a tak'aice da sauri ta fita yadda kasan jira take,
a hankali ya d'ago kansa yabi bayanta da kallo,
still yana cigaba da mamakinta ,dogon tsaki yaja tare da rufe system d'in ya jingina da kurar tare da lumshe idonsa, yana fesa numfashi a hankali.
Sosai kewar Sanah ta dami Khulud kasancewar yau ne karo na farko,
kuma rana ta farko a duk tsayin rayuwarsu,
da suka yi nesa da juna har na tsayin hrs bama minutes ba,
dan tunda suke a rayuwarsu basu tab'a yin nesa da juna na tsayin lokaci haka ba sai yau,
dan haka Khulud taji gaba d'aya gidan yayi mata bak'i k'irin,
yayi mata mugun duhu, da girma,
ji take kamar gidan babu mutane,
gane take kamar ita kad'ai ce a gidan,
tunda Sanah ta tafi nata ko fito daga bedroom d'insu ba,
tana ciki k'unshe kamar mai taka ba,
ko part d'in Halan da Juju yau bata iya shiga ba,
dan tasan tsokarta zasu tayi har suka ta kuka daga k'arshe,
karo na farko a duniya dataji sha'awar cigaba da karatun itama,
dan sai da ta gwammaci dama itama ta shiga jami'ar koba komai tasan bazatayi nisa da Sanarta ba,
tasan zata kasance da ita,
duk bayan 2 to 3 minutes sai ta kalli agogo taja dogon tsaki,
dan ji take kamar Sanah tayi 1yr bata gidan,
gaba d'aya kewa da kad'aici ya dame ta ya addabi rayuwarta.
Zohal Mimmee ta aika ta kira mata Hanash bayan ta gama jera lunch a dinning table,
yana kwance akan sofa ya samu bacci ya d'auke shi,
cikin baccinsa yaji sama-sama ana knocking,
idansa cike da bacci ya bud'e su dakyar,
yace " waye?
Cikin muyar bacci,
Zohal tace " nice Yaya, Mimmee ce tace a kira za'ayi lunch,
idansa ya murtsuke kana ya kalli agogo,
a hankali ya mik'e zaune yace " jeki ce ina zuwa sallah zanyi,
"Ok tace " kana ta koma part d'in su ta sanar da Mimmee,
Mimmee tace " koma kice masa ina jiransa sai ya zo zanci abinci,
dan tare dashi nake san ci yau,
Zohal ta koma ta Sanar dashi,
mik'ewa yayi tsaye yana cewa " tom,
da sauri ya shiga bathroom ya watsa ruwa,
yayi brush kana ya d'auro alwala,
da sauri ya shirya yayi sallah ya fita,
kamar yadda Mimmee tace hakan ya gani,
tana zaune tana jiransa,
fuskarta d'auke da murmushi ta tare shi tace " son yau da kaina girka maka best food d'inka,
murmushi yayi yace " Mimmee me?
Fuska ta b'ata kana tace " bangane me ba?
Yace " sorry Mimmee tambaya fa nayi,
tace " lalle yaro na yana cikin damuwa tunda har ya manta abincin daya fi so,
kansa ya d'ora akan kafad'arta kana yace " no Mimmee ba mantawa nayi ba fa,
kawai dai na tambaya ne,
tace " traditional food mana,
murmushi yayi had'i dayi mata light kiss a kumatu yace " thanks best Mimmee of the whole world,
kansa ta d'an buga tana murmushi,
kana ta rik'o hannunsa taja shi zuwa dinning,
da kanta tayi serving d'insa tuwon shinkafa miyar taushe da naman rago ga man shanu da kunun aya a gefe,
"wow! Mimmee thank you so much,
yace yana dariya,
da sauri ya jawo abincin gabansa ya sanya hannu ya fara ci,
yana kai lomar farko bakinsa yaji babu dad'i,
a hankali ya d'an yamutsa fuska,
duk abinda yake Mimmee na kallansa,
abincin itama ta zuba ta fara ci,
ganin yana ta juya spoon d'in tun daga lomar farko bai k'ara ci ba,
yasa Mimmee cewa " wacece ita?
Ta fad'a batare data kalle shi ba,
ta jefa masa tambayar bazata,
da sauri ya d'ago kansa ya zubawa Mimmee shu'uman idanuwansa,
dan bai tab'a tsammanin wannan tambayar daga gare ta ba,
shiru Hanash yayi , yayi kamar bai ji abinda Mimmee tace ba,
Mimmee ta kuma cewa " wacece ita?
Ta kuma tambayarsa,
Hanash yace " wa kuma Mimmee?
Batare data kalle shi ba ta kuma cewa " nace wacece yarinyar da kake so?
Cikin shagwab'a Hanash yace " Mimmee,
Mimmee ta ture abincin da take ci gefe,
ta tattara dukkan hankali da nutsuwarta ga Hanash,
tace " Hanash babu wani hali dazaka shiga a duniya wanda zan kasa fahimta,
wanda bazan gane kona lura ba,
ka tuna nice mahaifiyarka ni na tsuguna na haife da kai na,
ni nayi goyon cikinka wata tara da kwana tara,
na shayar dakai daga gare ni,,
na raine ka, kayi wasa dani ka kuma yi kuka a jikina,
na sanka tun kafin kai kanka kasan kanka,
nasan damuwrka da matsalarka tun kafin kai kanka kansan damuwa da matsalar taka,
dan haka zan tambaye a karo na k'arshe wacece yarinyar da kake so?
Shiru Hanash yayi had'i da k'urawa Mimmee ido,
yana tsananin mamaki bai tab'a yarda da maganar da bahaushe ke fad'a akan uwa ba sai yau,
duk duniya babu wanda ya gane damuwarsa koya fahimci matsalarsa sai ita,
lalle uwa dabance rayuwa duk wanda ya rasa uwa yayi kuka,
"uhnnmmm ina sauranka Mimmee ta fad'a,
idanta yana kan Hanash,
'yar ajiyar zuciya Hanash ya sauke kana yace " Mimmee ni ma ban santa ba,
ya fad'a cikin sanyinsa,
"kamar yaya baka santa ba?
Mimmee ta fad'a cike da mamaki,
yace " Allah Mimmee ban santa ba,
"amma kake santa?
" So kuma Mimmee?
" Ba wani so kawai dai......
sai kuma yayi shiru,
Mimmee bana tunnin sonta nake yi,
"saboda me kace haka?
Ta tambashi idanta na kanshi,
Mimmee haka nan, kawai dai ina yawan ganinta a cikin mafarki na ko tunanina,
sannan tana yawan hana ni suku ni,
murmushi Mimmee tayi irin na manya kana tace " Hanash wannan ai shine san,
a hankali ya d'ora idansa akan Mimmee,
ta cigaba "Hanash kana santa,
kai ne dai har yanzu baka yarda kana santa nata ba,
ka yarda koda na rana d'aya ne ka bawa zuciyarka dama akanta,
ka saurari bugun zuciyarka a tun sanda ka ganta,
ko tazo maka,
daga yau zuwa gobe kawai zaka gane abinda nake fad'a maka,
yayi murmushi kawai, Mimmee tace " tashi kaje, amma gobe ka dawo bayan 24hrs.
Su Sanah basu gama lecture's ba sai wajen 6:30,
tayi muguwar gajiya,
tana fitowa ta hango Aarib zaune akan mota yana jiranta,
murmushi kawai tayi masa dan bazata iya magana ba,
saboda tsabar gajiyar data yi,,
Aarib da kansa ya bud'e mata motar ta shiga,
kana ya zagaya ya shiga ya ja motar,
duk abinda sukeyi akan idan Sir Moli,
baki ya tab'a kana yaja motarsa shima yayi waje,
Khulud na jiyo k'arar parking d'in mota ta lek'o ta window,
dama abinda take yi kenan tunda taga 4:00pm tayi,
ganin Sanah yasa ta fita da gudu ta tare ta,
tana zuwa ta fad'a jikin Sanah ta saka kuka,
Sanah tayi rolling sexy eyes d'inta,
tace " kai my Ulud daga dawowa ta,
sai kuka, so kike nima nayi kukan?
Khulud ta girgiza kanta kana goge hawayenta,
Sanah tayi murmushi itama tasa hannu tana gogewa Khulud hawaye,
parlor suka shiga tare Khulud rik'e da jakar Sanah,
sai da Sanah tayi wanka ta canja suka ci abinci tare sannan ta kwanta bacci mai nauyi yayi gaba da ita.
Aryan Rayyan cikekken Bababbare ne na asali,
d'an garin Maiduguri, wato k'asar barno,
suna zaune a unguwar polo dake garin Maiduguri,
General Rayyan Moli shine mahaifinsa,
mutum mai adalci da sanin ya kamata,
mai tsoran Allah, tausayi da taimakon talawa,
mutum kamili nutsatstse mai dattako,
General Rayyan Moli shine shugaban sojojin Nigeria har yau har gobe yana nan akan muk'aminsa bayyi retaya ba,
mutum ne daya samu lambobin yabo dama,
tau daga kan halayyarsa har zuwa nasoririn dayasamu a wajen aikinsa,
dan yana kan yiwa k'asarta aiki irin na mazajen jiya,
duk Nigeria babu wanda bai san MOLI'S FAMILY ba,
dan ko jika ne kai a gidan saikayi amfani da MOLI,
matarsa Hinah ba 'yar asalin Nigeria bace balarabiyar k'asar Kuwait ce,
suna da yara 9 mata 6 maza 3 Sir moli shine dansu na 5 yana da babban yayanshi wanda shine d'an farinsu sunashi Aliyu suna kiranshi Haiydar, Haiydar yanada mata har biyu da yara 6, sannan Sir moli yanada yayu mata 3 mai bin Haiydar Anty Kubra itace sai Anty Nina ta uku sai Anty Ayyam ta hudu, sannan shalelensun dan daga kan Haiydar basu kuma samun d'ana mijiba sai kan, ARYAN RAYYAN MOLI (SIR MOLI),
sai k'annenshi masu binshi MEELAH, da NAJMAH, sai d'an auta Jabeer
mai tsananin kama dashi,
dan suna muguwar kama dashi,
gidan su gida ne daya ginu akan turbar addinin musulunci,
da tarbiyyar da kuma wayewar boko dai-dai musali,
dan mahaifinsu da suke kira da HILWA
da kuma mahaifiyar su da suke kira da NAINAH,
mutane ne masu matuk'ar sauk'in kai,
Allah yayi mugun jarrabarsu da mugun san yaransu musamman ma Aryan, duk family nasu anfi ji dashi, yayunshi da k'annenshi suna mishi wani irin so na musamman, duk da halin miskilancin shi, suna mishi matsanaicin so sabida tsananin kamanshi da mahaifinsu, shi kuwa wani irin so yakewa yaran yayun nashi, suma yaran komai nasu zakaji suna Uncle Moli, dan shi kusan yafi gadar sunan inkiyar mahaifin nasu
Meelah da Najmah suna gama secondary school akayi usu aure,
mazansun suma barebari ne suna zaune a cikin garin Maiduguri,
a anguwar low cost.
Duk wata mota da zaka gani da sunan MOLI'S ta gidan suce,
Allah yayiwa MOLI'S tarin arziki,
wanda su kansu basu isa suce ga abinda suka mallaka a duniya ba,
yana da estate manya-manya a nan gida Nigeria dama sauran k'asashen duniya,
duk k'asar kaje kaga estates ko malls,
da sauraran abubuwa da sunan MOLI'S na General Rayyan ne,
Aryan Moli (Sir Milo) yayi karatun degree & master da PHD d'insa duka a Oxford University dake America,
bayan ya gama degree ne ya dawo Nigeria yayi service dan haka dokar k'asar take,
duk inda kaje kayi karatu dole ka dawo gida kayi bautar k'asa,
bayan ya gama service ne ya koma yayi master & PHD duka a America,
Aryan ya kasance mutum ne mai bin ra'ayin kansa,
shi kwata-kwata bai damu da tarin dukiyar da mahaifinsa keda da ita ba,
Aryan tun yana yaro yake mugun so da sha'awar yin aikin government,
musamman koyarwa, mahaifinsa bai hana shi ba, ya barshi dan shi mutum ne mai matuk'ar sauk'in kai,
bai san koyaya ne ya tauyewa mutum hakk'in shi.
Washe gari da safe bayan Sanah ta shirya dakyar Khulud ta barta ta tafi school,
dan harda kukanta, tare Aarib da Sir Aryan sukayi parking,
Sanah ta d'an jima a cikin motar kafin ta fito,
Hanash yayi kamar yadda Mimmee ta sashi,
ya kuma tabbatarwa kansa san Khulud yake yi,
a parlor ya iske Mimmee zaune,
tana ganinshi ta sakar masa murmushi,
har k'asa ya durk'usa ya gaida ita,
tana murmushi tasa hannun ta d'ago shi,
ta zaunar dashi a kusa da ita ,
tace " son ya ake ciki?
Murmushi yayi yana kallanta batare daya iya cewa komai ba,
"Son!
ta kira sunanshi cikin sanyin murya,
kansa k'asa ya amsa amsa mata " na'am,
tace " ya kaji yau d'in?
Ya kuma yin shiru,
tace " Son kayi man bayani mana,
murmushi yayi yana kallanta had'i da d'aga mata kai alamar "eh,
murmushin jin dad'i tayi tana shafa kansa tace " Alhamdulillah abinda muka dad'e muna jira yau yazo kusa,
to yanzu ina ne gidansu?
"Ban sani ba Mimmee ya fad'a kamar zayyi kuka,
kansa ta kuma shafa kana tace " ina kuka had'u?
Bayanin komai yayi mata tun daga farkon had'uwar su har zuwa last had'uwar da sukayi,
abu d'aya kawai ya b'oye mata,
marin da Sanah tayi mishi,
kai ta jinjina kana tace " babu wani abu da zaka iya tunawa akanta wanda zai baka damar gane ta?
Shiru yayi na wani lokaci kana ya d'ago ya kalle ta cikin alamun karaya ya girgiza mata,
yace " no Mimmee,
tace " try please,
ya k'ara shiru can yace " I can't,
"try ta kuma fad'a tana shafa kansa,
Mimmee ban iya tuna komai fa,
ta kalle shi cike da tausayawa,
tace " bakomai karka damu kaji Son idan har Allah yayi ita matarka ce babu makawa sai kun had'u,
so karka d'aga hankalinka kaji,
kansa ya d'aga mata cikin sanyin jiki,
kana yayi mata sallama ya mik'e zai fita,
har ya kai bakin k'ofa ya tuno ranar daya fara ganinsu,,
da irin uniform d'in makarantar su Zohal ya gansu,
da sauri ya dawo kusa da Mimmee yace " Mimmee na tuna wani abu,
tace " meka tuna?
"Ranar dana fara ganin su da irin school uniform d'in su Wajnah na gansu,
" yauwa Mimmee tace, kana ta shiga kwalawa Zohal da Wajnah kira,
da sauri suka fito daga bedroom d'insu,
Mimmee ta kalle su tace " yayanku ke nemanku,
suka mayar da kallansu kansa,
ido ya zaro yana kallan Mimmee yace " ni kuma Mimmee?
Mimmee tayi mishi alama da ido da yayi magana,
kana ta kauda kanta gefe,
ajiyar zuciya ya sauke had'i dayin gyaran murya yace " akwai wasu yara a school d'in ku,
d'aya tafi d'aya fari, wacce tafi farin tafi jiki,
sannan d'ayar doguwa ce sirirya,
tafi d'ayar tsayi, d'ayar tana da dimples da wushiya,
kun san su?
Duk shiru sukayi suna tunnani,
kana suka ce " gaskiya Yaya bamu gane su ba,
kuma kai baka san sunan su ba?
Shiru yayi yana tunanin,
ya jima sosai yana tunanin kafin ya tuno sanda Khulud tacewa Sanah,
"wai my Sanah meye haka ne,
lokacin daya watsa mata ruwan kwata,
tana yi mishi rashin kunya,
a hankali yace " sunan d'ayar SANAH,
da sauri suka zauna kusa dashi suna dariya,
kana sukace " oh! Sanah Hamraz & Khulud Rawan kake nufi ashe,
Mimmee dashi sukayi dariya,
Mimmee tayi saurin cewa " yaya halayyar su take?
Zohal tace " suna da kirki basu da wani munin hali,
sai dai ita Sanah tana da tsiwa da bak'ar zuciya,
sab'anin Khulud da babu ruwanta,
nan suka kwashe halayyarsu suka fad'awa Mimmee,
Mimmee taji dad'i sosai jin daga Sanah har Khulud basu da wani mugun hali na kyama wanda uwa zata hana d'ansu auren su,
Wajnah tace " ai ranar nan gidan su mukaje walima ma,
sune suka gayyace mu walimar,
class d'in mu d'aya,
Zohal tace " amma fa suna matuk'ar so da k'aunar junan su,
dan tunda nake a duniya ban tab'a ganin wad'anda suke san junansu kamar su ba,
wallahi idan d'aya bata san abu,
to duk sanda d'ayar keyiwa abun ta hak'ura dashi,
haka ma komai nasu iri d'aya ne,
hatta reborn ko color basu canjawa,
idan d'aya na kuka d'ayar ma sai tayi,
nan suka kwashe irin so da muguwar shak'uwar dake tsakanin Sanah da Khulud suka fad'awa Mimmee da Hanash,
har labarin abinda ya faru a Roni sai da suka basu labari,
dan sun samu labarin komai,
Mimmee ta jinjina kai tana mamakin irin wannan mugun son dake tsakanin su,
Hanash yayi shiru dan yaga tabbas da idansa yaga zahiri,,
amma duk da haka shi kansa sai da yayi mamakin son da suke yiwa junansu,
Zohal tace " bari na d'auko waya ta na nuna maka pictures d'in mu dasu a wajen walimar,
ta shiga bedroom d'insu ta d'auko wayar,
mik'a mishi wayar tayi ya amsa hannunsa yana kerrma.
Ido sosai ya k'urawa Khulud yana kallan yadda take murmushi da dariya,
kayan da kwalliyar sunyi mata kyau sosai,
kyanta ya fito, take yaji shi cikin matsananin farin ciki da walwalar daya dad'e bai tsinci kansa a ciki ba,
amma yana d'ora idansa akan Sanah lokaci d'aya yaji mugun bak'in cikin ya saukar masa,
ya nemi gaba d'aya walwalarsa ya rasa,
danba k'aramar tsana yayiwa Sanah ba,
yana jin tsanar ta har cikin ransa da zuciyarsa,
sosai Hanash yake jin k'iyayyar Sanah a cikin jinin jikinsa da tsokarsa,
tunowa da maganar su Wajnah yasa jikinsa yin sanyi yaji gabansa yayi muguwar fad'uwa,
lura da yanayin daya shiga yasa Mimmee cewa su Zohal "ku mik'oman wayar nima naga pics d'in walimar ku shiga ciki,
ba musu suka bata wayar, su kuma suka koma bedroom d'insu,
Mimmee ta kalli pics d'insu,
sosai taji tana matuk'ar k'aunar su gaba d'aya duk da bata san ainahin wacce Hanash yake san ba,
ta kalle shi tace " waccece a ciki?
Murmushi yayi kana ya mik'e ya koma kusa da ita,
ya nuna mata Khulud,
tace " wow! masha Allah she's so beautiful as so mush as I think bf,
yayi murmushi, ta kalle shi tace " meye naga duk yanayinka ya canja,
bayyi niyyar b'oye mata komai ba,
dan haka yace " Mimmee wallahi kwata-kwata ban san sister nan tata,
bata da kunya sosai, kinji ma su Zohal sun fad'a,
murmushi tayi kana tace " eh kamar yadda naji sun fad'i rashin jinta haka naji sun fad'i so da k'aunar dake tsakanin su,
dan haka muddin kana san Khulud dole ka b'oye k'iyayyar abinda tafi so a duniya,
inba haka ba ka rasa ta, dole ka daure ka rink'a pretending na kana santa,
murmushi ya kumayi kana yace " nagode Mimmee a ransa kuma yana tabbatarwa kansa muddin ya samu soyyayar Khulud har ya kai ga ya aure ta dole ne ya raba ta Sanah,
dan bai ko k'aunar ganinta,
kuma muddin ya bar Khulud tana mu'amula da Sanah yasan sai ta lalata ta,
ta watsa mata tarbiyyarta.
_Ni ko nace kuji man mutum da k'afin hali ka same su tare tsawon rayuwarsa kace zaka raba su, dacan bata lalata ko ta canja mata tarbiyyarta ta ba sai yanzu, tare fa gansu_
Mimmee tace " yaushe zaka je ka sanarta da ita?
Dariya yayi yace " da wuri haka Mimmee?
Tace " idan baka je yanzu ba sai yaushe zaka?
"Kasan bahaushe yace " a bari ya huce shike kawo rabon wani,
ka tabbatar yau ka shirya kaje ka sanar da ita,
yayi dariya kana yace " in sha Allah yau zani wajen 4:30pm,
"Allah ya taimaka ,Ubangiji ya kuma baka sa'a ya zama muku abinda yafi alkhairi a tsakaninku,
ya amsa da " Amin,
kana mik'e ya fita cike da farin ciki,
barin ma daya tura duka pictures d'in a wayarsa,
part d'in sa ya koma ya zauna a parlor yayi editing pics d'in,
ya cire Sanah, duk inda ta fito ya yanke ta,
yabar Khulud d'insa ita kad'ai,
4:00pm nayi ya tashi ya shiga wanka,
ya shirya cikin shiga ta alfarma,
kyansa da haibarsa suka fito,
sai da ya biya yayiwa Mimmee sallama tayi masa addu'a sosai,
kana ya fito, driven daya kai su Zohal gidan walimar yasa shi raka shi gidan,
ya saka shi gaba yana binsa a baya har suka isa gida,
kana ya sallame shi,
shi kuma ya shiga get d'in gidan,
get man ya aika akayi masa sallama da Khulud,
tana zaune kusa da Mamu cike da cewar Sanarta,
mai gadin yayi sallama a bakin k'ofa,
Mamu ta amsa kana ta bashi izinin shigowa,
bayan sun gaisa da Mamu kana yakai dubansa ga Khulud yace " manyan gobe ana sallama dake,
ido Khulud zaro had'i da cewa " ni?
Ya bata amsa da "eh ke yace,
" kai badai ni ba, dan ban kowa ba,
ka dai koma ka k'ara tamyarsa,
yace " ke yace manyan gobe,
zata kuma yin magana,
Mamu tace " jeka ce tana zuwa,
ya fita, kana ta mayar da kallanta ga Khulud tace" tashi kije,
Khulud tace " Mamu ni fa ban san kowa ba,
Mamu tace " ai da haka ake sanin kowan,
tunda kikaga yazo gidan ku, ya kuma ambaci sunanki,
ai ya sanki kenan,
dan haka tashi kije,
tayi shiru bata da alamar mik'ewa,
Mamu ta daka mata tsawa tace " dan ubanki ba magana nake yi maki ba?
Ta mik'e ta zari mayafi zata fita,
Mamu tace " haka zaki fita baki gyara fuskarki ba bakiyi komai ba?
"Dalla koma ciki ki canja kaya ki gyara fuskarki ki fesa turare,
Khulud ta d'an turo baki kana ta nufi bedroom d'insu,
shiru bata fito ba,
Mamu ta d'aga murya tace " zaki fito ko sai nazo na iske ki a d'akin nan?
Khulud ta fita, zata wuce Mamu tace " sakaran yara kawai,
kince bazakiyi karatu ba, so kike mu tasaku gaba muna kallo bayan kun isa aure,
har ita mai karatun idan ta samu miji aure zatayi,
duk mu aurar daku mu huta fargaba da tsoran mu ya k'are,
baku san duk mai 'ya mace cikekken bacci ma bai iya yi ba,
da ido d'aya yake bacci, har sai ya kawar da ita ya huta kana,
Khulud ta fita batare data ce komai ba.
A gajiye lik'is su Sanah suka fito daga second to the last lectures d'in su,
in badon lectures d'in Sir Moli ce next lactures d'insu ba, da dalibai da yawa zasu tafi gida, dan yadda suka gaji, ga yunwa ga yanayin garin da ya fara sauyawa, hadari ne daga k'asa ya fara shatawa sai iska dake dan busawa a hankali tana ratsa, illahirin bani adam dake wurin, sai d'aga kai students d'in suke yi, wasu suce "ruwafa za'ayi, wasu kuwa suce, hadarin zai fa watse, bakuji iska mai sanyi ke kadawa ba". haka dai suke ta hasashen su, gudun dai kar su taka k'aidar Sir Aryan (Sir Mili) shima ya tattakesu yasa dole, suke ,tsumayin lokacin zuwansa,
A hankali Sanah, ta d'an ja tsaki, dan yunwar da taji tana k'wak'wularta, hannu tasa ta d'an dank'i cikin nata, gyara zamanta tayi akan kujerun SUG, dake
a tsakiyar shuke-shuken dake zageye da department d'in nasu,
shiru tayi dan ita kadai keta green, kasan cewar har yau batayi k'awaba,
jin shirun ya mata yawa yasa ta zaro woyarta, ta fara lallatsawa, dan ta d'an d'ebe mata kewa kafin yazo,
tana cikin danne-dannen taji, motsi a saman bishiyar ayaban da take zaune cikin inuwarsa, ido ta lumshe, dan k'amshi da wurin yakeyi gaba d'aya, sabida bananan da ke zagaye da wurin, gasu sunyi sutu-sutu, dai-dai ci, Amman ba damar tab'awa, kamar dai irin dokar dibinon dake cikin G,S,U duk d'alibin daya tab'a ya tab'owa kanshi C/O. da sauri ta d'ago kanta jin motsin yayi yawa sosai, ido ta zazzaro woje, dan ganin wasu k'attin k'adangaru, suna hard'e da juna suna fad'a, cizo juna sukeyi harda jini, a firgice ta mik'e ,dan tsoron karsu rikito a kanta, har ta juya zata tafi, sai kuma taji gyalenta ya sule ya fad'in cikin tsoron, ta sunkuyo da sauri ta d'auke mayafin, tana mik'ewa tare da yafawa a jikinta, tana gama mik'e tsawonta kenan, suka rikito kanta, wani irin tsalle tayi tare da k'am-k'ame jikinta, ta bud'e hannayenta duka buying, tuni ta cilla woyarta gefe, ihu ta saki da iya k'arfinta tare da furta, "innalillahi". k'ara ta kuma cillarawa jin d'aya k'adangaren yabi wuyan rigarta ya shiga jikinta, tuni yabi tsakiyar k'irjinta yana neman wurin b'uya a jikinta, dan d'ayan ya fishi k'arfi duk ya jikkatashi, shiko d'aya k'aton sai huci yake yana kumbura kai, ya shimfid'e a fuskarta, kanshi na k'atsan idonta, ganin haka ya k'ara firgi tata tare da gigicewa,
cikin tsananin razane ta saki gigitacciyar k'ara,
wanda yajo hankalin students d'in dake zaune wajen,
gaba d'aya, sukayo kanta suka zagaye ta, suna zuwa kusa da ita kuma, sai suka fara ja baya-baya harda mazan, ganin abunda yake jikinta, dan ana iya hango, bindin wanda ke cikin rigarta d'inma a saman k'irjinta sai jujjuya bind'in yakeyi, tuni students suka fara tayata sowa, mata kam harda ihu, wasu har cewa suke "Wayyo Allah macizai nefa a jikinta, ku mazan ku taimaka mata mana, wayyo zasu sareta fa". su kuwa mazan da ake gani kamar sune jaruman sai cemata suke,
"Kiyi tsalle zasu fad'i".
suna fad'in hakan suna kuma k'ara matsawa baya-baya, duk sun cika wurin, sun kuma gaza taimaka mata, ita kuma, sai ihu takeyi da kururuwa da Andd'ar neman taimakon Allah.
Tun daga parking lord, yake jiyo yadda wurin ya rud'e, a hankali ya bud'e motarshi ya fito, tare da d'aga kanshi sama yana hago yadda dalibanshi sukayi dandanzo sunata ife-ife, ga kuma sikiwritis d'in makarantar ke tsaya sunyi cirko-cirko, baki ya d'an tab'e dan a zatonsa maciji ne suka gani suka gaza kashewa, tsaki ya d'an ja tare da yin kansu yana
tafiya cikin takunsa na isa da cikar haiba,
hango dandanzon students d'in nashi yayi a waje d'aya sun zageye juna,
Ita kuwa Sanah sosai take kukan fitar hankali tana ihuuu da tsalle,
karaf idanta ya sauka akan na Sir Moli daya iso wurin yanzu
a rud'e ta fara kwala masa kira tana kiran sunansa da iya k'arfinta da karaji,
Sir Moli! Sir Moli!! Sir Moli!!! please kazo k'adangaru zasu kasheni, wayyo Allah na!,
ganin yadda duk ta rud'e tana kuka yasa Sir Moli ya nufi inda take, students suna ta bud'a mishi hanya, tare da rusunawa suna gaidashi,
Gabanta ya tsaya ya tsura mata ido ganin yadda taketa tsalle da ihu da kururuwa, fuska ya tsuke tare da kauda kanshi gefe, A hankali yasa ............
*-Am so sorry Fans, kunjini shiru kwana biyu, abubuwane suka dan min yawa, Amman in sha Allah yanzu zamuci gaba, har sai in watan Ramadan ya kama zamu ajiye kuma sai bayan Salla-*
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣1⃣
Tana fita harabar gidan ta hango Hanash tsaye,
tsayawa tayi daga nesa kad'an yadda bazai ganta ba,
tana mamakin abinda ya kawo shi gidan su,
da yadda akayi ma har ya san gida,
a fili tace " ko dai k'arar my Sanah kawo?
Tayiwa kanta tambayar,
da sauri ta k'arasa gare shi,
tunda ya hango ta ya kafe ta da idansa, baya ko k'iftawa,
d'an gutun murmushi ya sakar masa,
ta mayar masa da martanin murmushin,
cikin nutsuwa tace " ina wuni?
" Lafiya Alhamdulillah, ya fad'a still idanshi yana kanta,
ganin yadda ya k'ura mata ido,
baiko blinking yasa ta yin k'asa da kanta,
jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago kanta,
aiko karaf idanuwansu suka sark'e cikin na juna,
tayi saurin mayar da kanta k'asa,
murmushi yayi mai sauti kana yace " ina san kunyar nan taki,
bata d'ago kanta ba, bare tace masa wani abu,
"magana nake sanyi dake please,
hope zaki ban dama?
Kanta k'asa tace " ok muje ciki,
gaba tayi yana binta a baya har suka k'arasa set room,
d'akin da aka tanada dan bak'i,
cikin sanyin murya tace " Bismillah ka zauna,
cikin nutsuwa ya zauna a d'aya daga cikin kujerun,
itama ta zauna,
zai fara magana suka ji sallamar mai aiki,
Khulud ta bata izinin shigowa,
ta shigo d'auke da tray fal da drinks ta ajiye a gaban Hanash kana ta fita,
zai kuma yin magana Khulud tace " kasha wani abun tukunna,
ta fad'a tana tsugunnawa agaban tray d'in,
rasa wanda zata bashi tayi dan haka tace " wanne zan baka?
Tayi maganar kanta k'asa,
murmushi yayi yace " any one,
d'aukar d'aya daga cikin drinks d'in tayi ta mik'a masa,
wajen amsar drinks d'in ya had'a da hannunta batare daya sani ba,
daga shi har ita wani mugun shock suka ji,
da sauri ta zame hannunta, shima yayi saurin sakin hannun nata da leman,
cikin nutsuwa ta aje masa drink d'in a gefensa,
kana ta koma ta zauna,
d'aukar drink d'in yayi ya kurb'a kana ya ajeye a gefe,
ya tattara dukkan nutsuwa da hankalinsa gare ta,
cikin sanyin murya ya kira sunanta " Khulud!
yana yin yadda ya kira sunan nata ne yasa ta kasa amsawa,
a hankali ta d'ago kanta ta zuba masa idanta dan jin abinda zaice,
d'an shiru yayi kana ya sauke numfashi ya soma magana,
" kin san komai yin Allah ne,
kuma Allah shike had'a mutum da mutum,
kowa yasan farkon alak'a amma babu wanda ya isa yasan k'arshenta,
kamar yadda kika fad'awa 'yar uwarki dukkanin mu bamu san zamu had'u ba,
amma Allah da kuma k'addara ta had'a mu,
d'an shiru yayi, ya kasa cigaba da magana,
sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yace,
tun ranar dana fara ganinki naji abu a raina game dake,
amma sai ban damu ba,
amma daga baya saina gane SO!!!ne,
cikin wata irin murya mai wuyar fassarawa yace " I love you,
ya fad'a cikin harshen turanci dan bai iya fad'a da Hausa.
Da sauri Khulud ta d'ago kanta ta kalle shi,
marairaice fuska yayi kamar zayyi kuka yace " please Khulud don't say no,
murmushi Khulud tayi tana kallanshi,
tace " ina ni ina amincewa wanda Sanah ta bata so,
ta kuma fi tsana sama da komai,
ban tab'a amincewa wanda baya shiri da My Sanah,
duk namijin dakaga na amincewa kona aura to ka tabbatar da my Sanah ce ta zab'ar min shi a matsayin abokin rayuwa ta,
duk sanda nakeyiwa abu muddin my Sanah bata sanshi nima ban sanshi,
kamar yadda nasan bazan tab'a san abinda bata so ba har abada,
zayyi magana tayi saurin d'aga masa hannu tace " kaje ka fara neman izinin yarda ta daga gare ta,
kaje wajenta ka nemo soyayyata,
muddin ta yarda ta kuma amince koda ban sanka nayi maka alk'awarin zan aure ka,
wani irin abu Hanash yaji tun daga tafin k'afarsa har zuwa cikin kwakwalwarsa,
k'ululun bak'in ciki ya takare masa zuciya da mak'ogwaransa,
take ya kuma jin sabuwar tsanar Sanah ta dirarmasa a ransa,
yaji ya tsane ta fiye da komai da kowa,
yaji tunda yake a duniya bai tab'a tsanar wani abu kamar yadda ya ji ya tsane ta ba,
leb'ensa na k'asa ya cija da k'arfe,
had'i da runtse shu'uman idanuwansa,
a ransa yake jin koda zai rasa Khulud,
kuma koda ciwon santa da k'aunarta zai zama ajalinsa bazai tab'a neman alfarma a wajen Sanah ba,
a hankali ya bud'e idansa da suka canja launi ya sauke su akanta,
ya jima yana kallanta yana jin mugun so da k'aunarta na k'ara ratsa duk wani b'argo, jini da jijiya dake jikin sa,
cikin sanyin murya yace " please Khulud wallahi ina iya mutuwa idan kika k'i amince man,
murmushi tayi tace " maganin cutar zuciyarka da mutuwarka,
yana hannunka, sai kayi maganin matsalarka da kanka,
zayyi magana tayi saurin cewa " please zan shiga gida,
my Sanah na hanyar dawowa ban san ta dawo ta iske ka,
dan nasan ranta zayyi mugun b'aci,
ni kuma duk abinda zan sanya ta cikin b'acin rai da damuwa ban san shi,
kullum bani da burin daya wuce na ganta cikin farin ciki da walwala,
tayi maganar tana mik'ewa, shima jiki a sanyaye ya mik'e yabi bayanta,
sallama tayi masa kana ta koma cikin gida,
bayanta yabi da kallo harta shige cikin gidan,
cikin motarsa ya shiga cike da bak'in ciki da damuwa,
har yayi hanyar gida ya tuna sak'on Papu daya aike shi BUK tun last week,
na yaje kan maganar Admission d'insu Zohal,
direct BUK ya nufa.
Sir Moli yace " cire mayafinki ki yar,
kanta ta girgirza masa alamar a'a,
yace " idan baki cire mayafinki ba, na kan fuskar taki ma zai shige miki cikin rigarki fa,
kallan taran jama'ar dake wajen tayi,
taga gaba d'aya hankalinsu na kanta,
kanta ta kuma girgiza masa cikin matsanancin kuka tace "ban iyawa,
tsawa ya daka mata cikin fad'a yace " wai badake nake magana bane?
"Dalla can cire mayafinki ki yar,
cikin kuka tace " I can't,
Sir Moli tsare ta da idansa yayi yana tunanin abinyi,
" kiyi tsalle da k'arfi zai fad'i,
ya fad'a while idanshi na kanta,
ba musu Sanah ta buga tsalle da k'arfi,
maimakon k'adangaren dake kan fuskarta ya fad'i k'asa sai ya shige cikin rigarta,
Sanah naji ya shige cikin jikinta ta kuma sakin gigitacciyar k'ara,
daga cikin jikinta taji k'adangaren yasa farcensa yana kartar fatar cikinta,
tsalle ta farayi sosai tana kuka,
gaba d'aya fuskarta tayi jajir,,
hawaye da majina sun had'e sun yiwa fuskarta faca-faca,
tsallan datake yi yasa k'adangaren yin k'asa yana neman hanyar shiga cikin siket d'inta,
tana jin yana neman hangar guduwa,
saboda shima a takure yake ,
farce ya saka yana kartar fatarta sosai,
tsoran da yayiwa Sanah yawa ne yasa,
numfashinta ya d'auke tayi luuuuuuu zata fad'i k'asa,
cikin zafin nama Sir Moli yayi wuf ya tare ta,
ta fad'a jikinsa a some,
jikinsa na kerrma da tsuma,
kansa ya kawar gefe had'i da runtse idanuwansa,
kana ya d'aga rigarta kad'an ya zura hannunsa ciki,
ya cire k'adangaren yayi jefa dashi,
jijjigata ya shiga yi had'i da kiran sunanta,
Sanah! Sanah!.
Amma batako motsa ba, controlling kansa yayi ganin agaban students yake,
dan haka ya had'e face ya sungume ta yayi office d'insa da ita,
students suka bi bayansa da kallo cike da mugun mamakinsa,
akan table d'in dake office d'insa ya kwantar da ita,
da sauri ya nufi fridge d'in dake cikin office d'insa,
ya d'auko robar faro,
hannunsa na rawa ya b'alle murfin ya zuba mata ruwan,,
ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi,
had'i da rirrik'e shi gam,tana cigaba da kuka,
ganin har lokacin bata dawo hayyacinta ba,
yasa shi cewa " ke dalla bud'e idanki,
yayi maganar a dak'ile,
jin muryarsa yasa ta saurin bud'e idanta,
ta zuba su cikin nasa tana kallan cikin kwayar idansa,
hannunta data rik'e shi yabi da kallo,
tayi saurin sakin shi, baya ya ja ita kuma ta mik'e zaune had'i da sanya hannunta tana shafa cikinsa,
jin wet yasa ta saurin ciro hannun ta kalli hannun,
ganin jini yasata zaro idanta,
jikinta na rawa ta d'aga rigar jikinta.
Kuka ta saka ganin sosai k'adangaren ya karce mata cikin ta da faratansa,
kallanta yayi yana mamakin yadda kuka bai mata wuya,
d'an tab'a baki yayi kana ya nufi inda yake ajiye first aid box,
ya d'auko, direct ya nufe inda take zaune tana kuka,
" kwanta, yace a tak'aice,
kallansa tayi cike da mamaki,
taga ya kauda fuskarsa gefe,
banza tayi dashi tayi kamar bata ji ba,
ya kuma cewa " kwanta,
" in kwanta kuma?
Ta fad'a tana kallan fuskarshi,
ganin ya had'e rai yadda kasan bai tab'a yin dariya ba,
yasa ta kwanciya kamar yadda ya umarce ta,
"d'aga rigar ce, yayi maganar yana bud'e box d'in,
da sauri ta kalle shi,
tace " kamar ya na d'aga riga ta mezakayi man?
Bai kulata ba " ya kuma cewa " nace ki bud'e rigarki ko?
Ya daka mata tsawa, mik'ewa tayi zaune,
while idanta nakan shi,
tsaki yayi "mtswwwww kana yasa hannunsa ya maida ita kwancen,
ya d'aga rigarta d'an sama kad'an,
kamar baya so ya fara yi mata dressing,
yana cewa " banza kawai zan za'a taimaka miki uban me zan gani?
"Kwaila dake har kina wani b'oye-b'oye,
ko uban me zan gani ajikinki oho,
yayi maganar cikin nutsuwa,
Sanah zatayi magana taji an turo k'ofar an shigo,
da sauri ta mik'e tana gyara rigarta,
tsawaye cak Hanash yayi had'i da k'ura mata ido na tsayin lokaci,
a ransa yace " wato wannan yarinyar bayan fitsara da rashin kunya,
ashe ta had'a harda iskanci?
Ya tambayi kansa, "haba ba mamaki shiyasa kwata-kwata bata jin tsoro ko kunyar uban kowa,
ya fad'a cikin ransa, d'an kwallinta da mayafinta dake k'asa yabi da kallo,
wanda itama sai lokacin ta lura dasu,
tasan kuma kanta babu d'an kwali,
hannun Sir Moli dake kan cikin Sanah yabi da kallo,
da sauri Sanah ta lura da hannun tayi saurin ture hunnun nasa gefe,
cikin sanyinsa Hanash yace " I'm sorry na katse muku hanzari ko?
Bai jira abinda zasu ce ba, ya fita,
Sanah ta runtse idanta da k'arfi had'i da dafe goshinta,
Aryan ya kalle ta yace " kin san shine?
"Eh tace,
yace " waye shi?
Ya kuma tambayarta idanshi na kanta,
baki tad'an tab'e kana tace " ba wani saninsa fa nayi sosai ba,
ta fad'a tana mik'ewa,
mayafinta da d'an kwallinta ta d'auka,
jingina yayi da table d'in, had'i da hard'e hannayensa a k'ijinsa,
ya zuba mata ido, yace " d'azu sunanwa kika kira?
Tana d'aura d'an kwalinta tace " Sir Moli, ta batare data kalle shi ba,
yace " waye shi, meye alak'arki dashi da kike kiran sunanshi?
Ido ta zaba masa tana mamakin tsantsar rainin wayonsa,
kana ta tab'a baki tace " bani da alak'ar komai dashi,
yace " kin san shi kenan?
Ya fad'a idansa na kanta,
"eh na sanahi wani mugun secondary school teacher d'in mu,
kwata-kwata bai da tausayi da imani,
ba ruwanshi da yarinta ko k'ank'antar shekarun yarinya,
ta fad'a idanta tarrr cikin nashi,
mamaki ne ya hana Sir Moli cewa komai,
" lalle yarinyar nan bata da kunya da tsoro,
ya fad'a cikin ransa,
a fili kuma yace " amma duk da wannan mugayen halayen nashi meyasa baki kira sunan kowa ba sai nashi?
" Bayan nasan kina da wad'anda suka fishi kusanci dake,
kallan shi tayi na wani lokaci,
kafin tayi rolling sexy eyes d'inta tace " hakan ya tab'a faruwa ne,
bawai saboda mahimci ko kusancinsa dani bane yasa ni kiran sunansa,
dan kwata-kwata bashi da wani kusanci ko alak'a dani,
dan ni na maanta dashi da rayuwarsa,
kawai dai naji sunansa yazo baki na ne,
ido ya zuba mata na tsayin lokaci kana yace,
"meyasa dance ki cire mayafinki kika k'i cirewa?
Sai da ta yamutsa fuska kana tace " Wani Malamin mu ne ya bani shawara,
still idanshi na kanta yace "Akan me?
Ya kuma tambayarta,
sai da ta juya idanta kana tace " yace na zama d'aya daga matan dako kashe su za'ayi basu tab'a bayyanar da tsiraicinsu ba,
bazasu tab'a zubar da k'ima da mutuncin su ba,
saboda yace man duk d'an Adam d'in,
daya rasa k'ima da mutunci dashi da dabba duk d'aya suke,
sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yace "waya fad'a miki duk wannan?
Air Moli ya fad'a yana kallanta,
murmushi tayi kana tace " wannan mugun Malamin namu ne dai,
murmushin takaici yayi kana yace " zaki iya tafiya,
tayi masa murmushin rainin wayo kana ta fita,
Sanah na fita taga garin da hadari sosai,
sai iske akeyi mai k'arfi,
ganin duk malamai da d'alibai nata tafiya gida,
masu yin hostal nayi,
yasa Sanah kiran Aarib a waya,
tambayarshi yana ina tayi,
ya amsa mata da yana office aiki yayi mishi yawa,
idan sun gama lecture's ne tahau adaidaita sahu.
Get ta nufa iska na neman kada ita,
tana ta fama da mayafinta,
shima ganin hadari yasa shi d'aukar brief case d'insa yayi hanyar fita daga office,
ya d'ora hannunsa akan handle ya bud'e k'ofar,
sukayi karo da Leem dake k'ok'arin shigowa cikin office d'in,
fuska Sir Moli ya tsuke had'i da jan tsoki,
yace " mtswwwww banza kawai ka wani shigo da k'arfi ka buge ni,
" dalla kai baka canja halinka,
koyaushe aka kanga rai a had'e kamar wanda akayiwa sammacin mutuwa,
kullum kai fuskarka babu fara'a da murmushi,
Leem ya fad'a yana dariya had'i da d'an dukan kafad'ar Aryan,
Sir Moli ya d'an basar,
Leem yace " to mu shiga mota mana,
kabarni yayyafi yana dukana,
murmushi Sir Moli yayi yace dalla matsoraci kawai,
ashe dai har yanzu baka daina shegen tsoran nan naka ba,
sai shegen tsoro kamar wata mace,
ko uban me ruwan sama zayyi maka oho,
" ba wani tsoro kaima ai kasan ban san ruwan sama zazzab'i da ciwon kai yake sani,,
muddin na bari ya dake ni ko yayane,
Leem yayi maganar suna shiga mota,
Leem na cewa " dama yanzun nan nazo gunka fa,
kwana da yawa bamu had'u ba,
kayi wuyar gani, yau na shigo kano shine nace yau dai bari na shigo mu gaisa ko'a tsaitsaya ne,
a gida ma nabar mota ta.
Sir Moli na driving,
Leem yace " kai dai ka nacewa kano,
kwata-kwata kak'i zaman Maiduguri,
wallahi kai dai banza ne,
ko uban me kake samu a kanon oho,
na rasa me ka gani a makarantar nan ka mak'alewa makaratar,
ko dai 'yan matan makarantar ke d'auke maka hankali kake san kayi ta kallansu?
Tsaki Sir Moli yayi had'i da tsuke fuska ya tab'e baki,
" to meye abin kallo ajikin 'yan mata?
" 'Yan matan har wasu ababen kallo ne?
" Bayan duk yawancin su tatsitsan yara k'anane,
duk kwalaye ne,
ku mata suka dama suke kuma gabanku da har kuke maganarsu,
Sir Moli yayi maganar kamar bayaso,
cikin dariya Leem yace " ah lalle kam ba ababan gani bane,
ai dama kai d'an banza ne, nasan dama baka tab'a d'aukar mace abar kallo ba,
mu dai da Allah ya jarrabe mu da san mata ya kuma bamu lafiya sai muyi tayi,
hankalin Sir Moli nakan tuk'in dayake yi yace " kamar ya ku da Allah ya bawa lafiya?
" Eh mana, in ba mara lafiya ba ya za'ayi cikekken namiji kamar ka ya tsani mata har ya rink'a cewa shi baiga abin kallo ajikin mata ba,
wallahi gwara kaje kaga likita tun kan kayi aure azo aji kunya,
a d'an gak'ile Sir Moli yace " haka kake gani?
"Sosai ma kuwa, dan ni na dad'e ina maka kallan mara cikekkiyar lafiya,
dan Allah kaje kaga Doctor karkayi aure ka rink'a cutar 'yar mutane,
murmushi Sir Moli yayi batare dayace komai ba,
sai wasa sukeyi suna dariya,
Sir Moli na gaf da fita get ya ganta sai sauri take yi, iska na neman d'aukarta,
ido ya zuba mata tun daga nesa har suka zo zasu wuce,
Leem nata magana yaji shiru,
inda Aryan ke kallo yabi da kallo,
Sanah ya gani sai faman sauri take yi,
Leem yace " yanzu fa kace baka kallan mata,
kuma a yanzun ka tsare wata da ido kamar tsohon maye,
ko ita wannan ba mace bace,
namiji ne?
A tak'aice Sir Moli yace " wannan d'in har wata macece?
Kallan Sanah Leem yayi cike tsantsar mamaki,
yaga duk inda mace mai tak'ama da kyau da body takai Sanah ta wuce nan,
dariya Leem yayi yace " au wannan ba mace bace namiji ne,
yayi maganar cike da rainin hankali,
Sir Moli yace " ni a waje na babu wani banbanci tsakanin mace da namiji duk d'aya nake d'aukarsu,
dan ni ban jin wani emotions ko feelings,
itama haka nake kallanta kamar namiji,
kuma ina da yak'inin lafiya ta lau,
Leem yace " shiyasa nace ai baka da lafiya wallahi,
kaje kaga Doctor,
guntun murmushi Sir Moli yayi kawai batare dayace komai ba,
Leem yace " to yanzu dai ita wannan d'in wacece danaka ka k'ura mata ido kana ta kallanta?
Sir Moli yayi dariya kana yace " she's my student tun daga Jss1,
sosai Leem yayi mamaki kana yace " ikon Allah,
kuma harka iya gane ta,
abokina kodai ka kamu ne?
Moli ya kuma yin dariya yace " kamuwa kuma?
"Da wa d'in?
" Lalle duniya ta lalace tunda aka fara kiran su Sanah mata,
kuma wacce zan so, tab that's impossible,
" to ya akayi baka mantata ba?
Leem ya kuma tambayarshi,
" she's very stubborn,
bata da kunya, fitsararriya ce no 1,
gata tsaurin ido da taurin zuciya,
ko ka tab'a ganin an manta d'alibin marar jin magana?
Dariya Leem yayi yace " ta shiga cases d'inka kenan?
Moli yace " sosai ma,
kana ya d'an bashi labarin Sanah in briefly,
sosai Leem yayi dariya kana yace " please mu koma kayi mata lift,
tunda abokiyar dramarka ce, ko ni ma Allah ya ci da ni ayi a gaba na,
nima in gani in shaida dan ba mamaki sharri kake yi mata,
batare daya kalli Leem ba yace " aiko indai wannan yarinyar ce tana iyayi a gabanka,
dan fitsararta ta wuce da saninka,
" naji yanzu dai mu koma kayi mata lift,
" wa zan bawa lift d'in?
Moli ya tambaya,
" dalla ban sani ba, wa muke magana yanzu?
" Dan Allah Malam ka tsaya ka rage mata hanya,
Moli yayi kamar baiji abinda Leem me fad'a ba,
"please mana abokina kaga macece ,,
kuma ga hadari a garin gashi har an fara yayyafi,
ba lalle ta samu abun hawan da zai kaita gida ba,
saboda idan ana ruwa yawancin masu abin hawan haya basu yin aiki,
still Sir Moli yayi banza da Leem,
" please Aryan,
Leem ya fad'a,
a d'an fad'ace Sir Moli yace " kai banfa tsayawa d'aukar yarinyar nan,
wai ina ma ruwanka da zaka damu da ita ne?
"Ina ko ruwa na tare fa na ganku,
Leem yayi tayi masa magiya amma Sir Moli yayi kamar bai jin shi,
ganin haka yasa Leem jan hand break d'in motar,
motar tayi wata irin k'ara k'uuuuuu,
Sir Moli ya zaro ido yana kallan Leem yace " dan ubanka kashe mu kake sanyi?
" Dan Allah ka koma ka taimake ta mana,
tsaki Sir Moli yaja had'i da yiwa motar key,
Leem ya kuma cewa " please mana,
bayyiwa Leem magana ba ya juya kan motar dan yasan muddin yana san zaman lafiya dole ya koma ya d'auko ta,
inko ba haka ba, yasan ya shiga uku wajen Leem,
dan gaba sai saka shi yayi tayi masa naci da magiya,
a gabanta yayi parking,
d'an tsayawa tayi kasancewar motar tintak ce,
bata ganin wanda ke ciki,
baki ta murgud'a had'i da watsawa motar harara ta zakagaye zata wuce,
Leem yayi dariya yace " lalle kam,
kai kaga yadda take hararar mota,
Moli yace " bakaga komai ba indai wannan yarinyar ce,
shiru Sir Moli yayi had'i da kauda kansa gefe batare dayace komai ba,
bai kulata ba saima uwar harara daya zuba mata,
Leem yayi k'asa da glass d'in motar ta yadda Sanah zata iya ganin Sir Moli,
kana yayi murmushi yace " k'anwata shigo mu kai ki gida,
kaita girgiza masa tana murmushi tace " no nagode,
Leem yace " ki shigo muyi miki lift kinga an fara ruwa fa,
cikin sanyin murya tace " a'a ka barshi nagode,
Leem zai kuma yin magana Sir Moli yayi sama da glass d'in motar,
yana cewa Leem " d'an iska idan so kake ka bata lift kaje ka d'auki motarka ka d'auke ta kayi mata lift d'in,
yana niyyar jan motar aka kece da ruwan sama mai k'arfi,,
walk'iya akayi had'i tsawa mai k'arfi,
da sauri ta bud'e motar batare datace komai ba ta shiga baya,
tana haki jikinta sai kerrrma yake yi,
tana addu'ar da bama tasan me take cewa ba,
duk addu'ar data zo bakinta kawai take yi،
dan Allah yayiwa Sanah mugun tsoran ruwan sama tun tana yarinya,
Leem yaso yin dariya amma ba dama,
sosai Sanah ta bawa Sir Moli dariya,
amma saboda tsabar muskilancinsa sai ya tab'e baki had'i da kauda kansa gefe yayiwa motar key,
Leem ya kalli Sanah yace " sannu naga kin tsorata sosai,,
ashe manya irinku ma na tsoro?
Murmushi kawai tayi masa batare datace komai ba,
Leem ya maida hankalinsa ga Sir Moli yace " wai yaushe zakayi aure ne Aryan?
Banza Sir Moli yayi masa,
Leem ya kuma cewa " wallahi na matsu naga wacece matar da zaka aura,
naga kalarta naga had'uwa da kyanta,
shiru still Sir Moli yayi saboda Sanah dake cikin motar,
" hmmm ashe wannan muskilancinsa nasa babu wanda baya yiwa,
ta fad'a cikin ranta had'i da tab'e bakinta,
duk abin takeyi idan Sir Moli na kanta ta cikin mirror,
Leem yace " please kayi koda soyayya ne,
a dak'ile Sir Moli yace " aini soyayya wahala da b'ata lokaci nake d'aukarta,
kawai dan rashin abin yi sai na tsaya ina wani soyayya,
ku ma gani kukayi zaku iya, dan haka sai kuyi ta fama,
Leem yace " hmmm kasan me Aryan?
Sir Moli yayi masa banza,
Leem ya cigaba" a wani tak'i na rayuwar mutum dole zai fuskanci soyayya,
nasan a yau ba lalle ka fahimci hakan ba,
amma wata rana zaka fahimci bakai ne kake yanke shawarar fad'awa a soyayya ba,
ita soyayyar ce take yanke lokacin faruwar hakan,
" akwai lokaci, Sir Moli ya fad'a kamar baya so,
Leem yayi dariya kana yace " to ai ita soyayya bakai ne kake yanke lokacin da zakayi ta ba,
faruwa kawai take yi,
Sir Moli ya kauda kansa gefe kana yace " to ai ni bana san ta faru dani,
Sanah sake zaune bayan mota tana jin hirar su,
ta tab'e baki cikin ranta tace " ka bata lokaci tabbas wata rana zata faru dakai,
ko dan girman kanka da halin wulak'ancinka,
nasan wata rana sai ka fad'a soyayya mai zafi,
wacce zata wahalar dakai kamar yadda ka wahalar da wasu,
cike da mamaki Leem ya juya ya kalleta,
Sir Moli ko ta cikin mirror ya k'ura mata ido,
sai a lokacin Sanah ta fuskanci a zahiri tayi maganarta,
ba acikin ranta tayi ta ba,
kuma ta fito fili sunji,
ido ta zaro had'i dasa hannu ta rufe bakinta,
cike da alamun tsoro,murmushi Sir Moli yayi batare daya ce mata komai ba,
ya mayar da hankalinsa ga tuk'insa,
Leem yace " yauwa k'anwa ta fad'a masa dai,
batare da Sir Moli ya tambayi Sanah kwantacen gidansu ko unguwarsu ba,
ya kaita har k'ofar gidansu,
a bakin get yayi parking batare dayace mata komai ba,
cikin matsanancin mamaki ta fito,
ta kalli Leem tayi masa guntun murmushi tace masa " nagode,
shima murmushin yayi mata yace " bakomai k'anwata,
harta juya zata shiga gida ta juya ta kalle shi tace " ya akayi kasan gidan mu?
Bai bata amsar tambayarta ba,
ya ja motarsa yayi gaba,
Sanah ta tab'e bakinta tace " Allah ya kyauta maka,
kana tayi shigewarta gida,
a parlor ta tarar da Khulud tana chart,
Khulud na ganinta tayi cilli da wayar gefe,
ta mik'e da sauri ta rungume ta,
kasancewar a matuk'ar gajiye Sanah,
take dawowa kullum yasa bata tab'a bawa Khulud labarin taga Sir Moli ba,
bugu da k'ari kuma bata damu dashi ba,
data bar makaranta take mantawa da Allah yayi ruwansa,
bata sake tunawa dashi sai idan ta ganshi.
Hanash na zaune Papu ya shigo parlor'n,
da sauri Hanash ya durk'usa ya gaida Papu,
Papu ya amsa cike da fara'a kana yace " Hanash kako je BUK wajen maganar Admission d'in Zohal?
Hanash yayi shiru ya shiga tunanin yadda yaga Sanah kwance wani k'ato na yadda yaga dama da jikinta,
ido ya runtse dan yayi masifar tsanar mace marar kamun kai,
mai sakarwa namiji jikinta anyhow,
Papu yace " yadai naga kayi shiru,
baka je ba ko?
Ya fad'a idanshi na kansa,
murmushi yak'e Hanash yayi kana yace " naje, amma banga mutumin ba,
Papu yace " kuma ka tabbata office d'in kaje?
Hanash yace " eh,
Papu yace " ka koma gobe,
Hanash yace" tom Papu Allah yakai mu,
Papu yayi murmushin jin dad'in biyayyar Hanash kana ya shafa kansa.
Washe gari wajen 4:30pm na yamma,
Sanah na zaune a cafeteria bayan sun fito daga lectures taje cin abinci,
drinks & snacks taci kasancewar Sanah tafi san heavy food,
a hankali ta bud'e hand bag d'inta ta d'auko table ta duba,
ganin Sir Moli ne dasu 4:30pm yasata kallan agogon hannunta,
ganin har 4:30pm d'in tayi ya sata mik'ewa da sauri had'i da cewa " oh! sheet!,
anan tabar abincin datake ci ta nufi class,
jikinta sai rawa da tsuma yake,
dan kwata-kwata bata san shiga track d'insa,
duk saurin da Sanah take dan kar Sir Moli ya rigata shiga class sai da ya rigada,
hango yadda take sauri yayi,
dakewa tayi ta saita kanta kana ta danna kanta ta shiga class d'in kai tsaye,
batare daya kalli inda take ba yace " kneeling down ya fad'a tak'aice,
idanta ta runtse dama tasan za'ayi hakan,
dan tasan kamar kad'an yake jira akanta,
a hankali tasa gwiwarta a k'asa tayi kamar yadda yace tayi,
yana fitowa daga lectures yace " ki same ni office,
yayi maganar batare daya kalli inda take ba,
Mik'ewa tayi ta kakkab'e jikinta ta shiga class,
tayi attending lectures.
Wanka Hanash yayi ya shirya cikin manyan kaya,
ya nufi BUK.....
Office d'insa ta nufa,
a hankali ta shiga bakinta d'auke da sallama,
iskewa tayi baya nan,
harta juya zata fita karaf idanta ya sauka akan talkami, agogo, da kuma rigarsa ta sama(cut) daya aje ya rataye a saman kujerar zamansa,
dariya Sanah tayi had'i da nufar kayan tasa hannunta ta d'auka tace " rayuwa kenan,
komai na duniya yana da lokacinsa,
babu wani abu dayake da da tabbas a rayuwa,
Allah karka kawo abinda bazai wuce ba,
d'an lek'awa tayi ta window taga bai taho ta,
dariya ta kuma yi kana ta nufi inda kayan ke aje a hankali sad'af- sad'af ta nufi inda ta hango hularsa dake aje a gefe,
da alama ba ranar ya shigo da ita ba,
dan yau cut ya saka a jikinsa,
ta d'auki hularsa ta saka a kanta d'an kwalinta ya zame ya fad'i k'asa,
kwantaccen gashin kanta bak'i ya zuba har gadan bayanta,
tace " ah wannan fa ya shanye k'aton kansa,
yanzu kansa ya k'ank'ance,
hannunta takai ta d'auki cut d'insa ta saka a saman kayan jikinta,
taga tayi mata zulum har kusan gwiwarta,
tace " kai yaron nan ya k'ara girma da tsawo ashe,
cire takalmin k'afarta tayi ta zura nashi,
tace " to mazurmi kenan, dama shi fa akwai k'afa,
k'afar nan dai tana nan har yau yadda take ada,
ita bata k'aru ba bata kuma ragu ba,
ta saka agogon a hannunta,
tana dariya sosai,
show glass d'in dayake aje perfume's & book ta nufa,
ta tsaya a gabanta had'i da sanya hannunta a hab'arta tana kallan yadda show glass d'in ke shak'e da turarurruka kala-kala,
kowanne turare da akwai lokacin saka shi,
dan taga an rubuta ranar sanya kowanne a jikin turarurrukan,
Friday to Thursday & na safe daban ya rana daban na yamma daban,
k'ara kallan turin littatafansa tayi tana mamaki,
tace " eh! yaran nan hancinsa kam yasan k'amshi,
bud'ewa tayi a hankali ta shiga fesa kowanne turare a jikinta,
sosai Sanah tayiwa jikinta b'arin turarurrukan Aryan,
tayi masa b'arnar Perfume's sosai,
gaba d'aya office d'in ya gauraye da k'anshin perfumes yadda kasan company had'a turaren,
k'amshin turarurrukan ya had'u da sanyin Ac ya bada wani irin yanayi mai wuyar fad'a.
K'afarta ta d'aya ta d'ora akan set d'in zamansa,
ta kwaikwayi maganarsa tace " kneeling down,
ta fad'a tana dariya,
juwayar da zatayi ta ganshi tsaye ya fito daga bathroom,
ya zuba mata rikitattun idanuwansa masu kamar yana jin bacci,
hannunta ta saka ta rufe bakinta............
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣2⃣
Hannunta ta saka ta rufe bakinta,
had'i da zaro sexy eyes d'inta waje,
a hankali cikin takunsa na cikakkun maza ya fara takowa gareta,
cikin tsoro Sanah ta fara ja baya tana yarfe hannu,
yana biyo ta ita kuma tana cigaba da yin baya har suka isa bango,
hannayensa ya saka ya dafe bango,
ya saka ta a tsakiyar hannayensa,
gaban rigarsa inda ya b'alle bottles d'in jikin rigar kyakkyawan k'irjinsa mai d'auke da yalwataccen kwantaccen gashi,
ta kalla, take taji gabanta yayi muguwar fad'uwa da k'arfi,
da sauri ta runtse idanta yayinda da k'irjinta keyin sama da k'asa da sauri-sauri,
lulu eyes d'insa ya zuba mata yana kallan yadda k'irjinta ke bugawa yana up an down da sauri,
yanayin k'amshin da sanyin Ac dake office d'inne suka saukar masa da wani irin yanayi a gaba d'aya ilahirin jikinsa,
yaji kasala ta saukarwa duk wata gaba ta jikinsa,
abinka kuma da yanayin damuna,
k'ara matseta yayi sosai a jikin bangon,
ta yadda k'irjinsu na gogar na juna,
da sauri Sanah ta bud'e idanta,
ta zuba cikin nashi,
ganin yadda lokaci d'aya gaba d'aya yanayinsa da kuma kamanninsa suka canja yasa zuciyarta ta shiga bugawa,
dayake ya fita tsayi yasa idan zata kalle shi sai dai ta d'aga idanta sama,
kanta na k'asa, idanta kawai ta d'aga tana kallanshi,
cikin wata irin kasalalliyar murya Sir Moli yace " kin tuna?
D'an kawar da kanta tayi gefe,
muryarta can k'asa tace " me?
Yace " alk'awarin da kikayiwa wannan mugun secondary teacher d'in naku,
muryarta na rawa tace " na manta,
"Ok bari na tuna miki, ya fad'a yana k'ara shegewa jikinta,
" please kaban last chance, idan na kuma yin laifi kayi man koma meye,
wallahi I promise ban k'ara yi maka laifi,
Allah idan na kuma kayi man komai kaga dama na yarda na d'auka,
duk abinda kaga damanyi kayi man,
ya fad'a bakinsa saitin kunnenta,
had'i da hura mata iskar cikin bakinsa a kunnenta,
kana yace " kin tuna yanzu?
Idanta na kansa ta d'aga masa kanta,
muryarsa can k'asan mak'ogwaro yace " kin san ban san d'aga kai ko?
Bakinta na rawa tace " eh!,
yace " good,
muryarsa bata fitowa sosai yace " shi kuma a lokacin mai yace miki?
Ya fad'a yana shinshinar wuyanta,
had'i da goga hancinsa a wuyanta,
kamar zatayi kuka saboda yadda duk yabi ya shege mata jiki,
tace " keep it in your mind,
I know one day you will pay for your promised,
"good yace , yana goga hancinsa a wuyanta,
" kince duk abinda naga dama nayi miki ko?
Ya fad'a muryarsa bata fita sosai,
"dan Allah kayi hak'uri Allah ban k'arawa,
yadda take maganar yasa shi k'urawa cutie lips d'inta ido,
still hannayensa na jikin bongon,
ita kuma tana tsakiyar hannayensa,
ya sanya fuskarsa a wuyanta yana goga mata,
kana a hankali ya fara goga mata fuskarsa akan tata fuskar,
sajensa yana gogar kumatunta,
k'irjinta na gogar na shi,
yadda k'irjinta ke yin sama da k'asa ya fara sa Aryan yin loosing control,
itako Sanah tsaron yanayin data ganshi ciki ne ya hanata yin koda kwakkwaran motsi,
idanshi na kanta yana karantar yanayin data shiga,
yasa hannu ya zame hularsa dake kanta,
ya cusa hunnunsa cikin gashin kanta,
bakinsa yakai cikin kunnenta ya rad'a mata,
kin shirya karb'ar punishment d'inki yanzu?
Ya fad'a muryarsa na creaking,
" kayi hak'uri tace , kuka na neman kwace mata,
yadda tayi maganar tana turo bakinta,
yasa Sir Moli had'e bakinsu waje d'aya batare daya sani ba,
ido Sanah ta zaro waje cike da tsoro jin abinda Sir Moli keyi mata,
gaba d'aya jikinsu ya d'auki rawa da tsuma,
kasancewar jin su a cikin wani irin yanayi da basu tab'a tsintar kansu ciki ba,
duk ilahirin jikinsu kerrrrrma yake,
musamman Sanah, da har hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta,
a hankali ya zagayo da hannunsa ya tallafe kanta yadda zaiji dad'in shan bakinta sosai,
had'i da cusa hannunsa cikin gashin kanta,
yana ya mutsuwa, still bakinsa na cikin nata,
d'aya hannun yakai yana shafa duk ilahirin jikinta,
hannu Sanah ta sanya a k'irjinsa tana k'ok'arin ture shi,
a hankali hannunta ya shege cikin rigarsa inda yake ya bud'e,
Sir Moli yana jin tattausan hannunta akan fatar k'irjinsa ya k'ara fita saga hayyacinsa,
jikinsa na kerrrma ya fara k'ok'arin neman zip d'in rigarta.
Hanash dake ta faman knocking a bakin k'ofar amma ba'a amsa ba,
ya d'an ja tsoki kana ya juya a hankali zai tafi,
bakinshi cikin nata tace " uhmm innnn amma ba damar yin magana,
saboda da gaske yake tsotsar bakin nata,
Hanash dake waje jin ance innnnn,
sai ya zata cewa akayi ya shigo dan haka ya danna kai cikin office d'in kai tsaye,
tsawa yayi cak ganin yanayin da suke ciki,
bakin Hanash na rawa yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
ya fad'a batare daya sani ba,
jin maganar Hanash ya sanya Sir Moli dawowa cikin hayyacinsa,
a matuk'ar kid'ime ya saki Sanah yayi baya,
cike da tsoro da kuma tsantsar mamaki Sir Moli yake bin Sanah da wani irin kallo,
yana tambayar kansa me yayi mata,
ido Hanash ya k'ura musu na tsayin lokaci,
yana kallan Sanah sanye da kayan Aryan a jikinta,
a hankali yabi cut da agogo da takalmin k'arfarta da kallo,
ya kuma kalli yadda gashin kanta ya barbaje,
kana ya mayar da kallansa ga Aryan dake dafe da kansa kwalla na neman gangarowa daga idansa,
yaga gaba d'aya jan bakin Sanah ya dame masa fuskarsa,
murmushin bak'in ciki Hanash yayi kana ya juya ya fita batare dayace musu komai,
durk'ushewa Sanah tayi had'i da fashewa da wani irin rikitaccen kuka,
kansa ya dafe dake barazanar tarwatsewa had'i da zuba mata idanuwansa da suka koma pure red color,,
muryarsa na rawa Sir Moli yace " me nayi?
" Meke shirin faruwa dani ne?
Yayi maganar idansa na kanta,
yana kallan yadda take ta faman kuka,
sai da taci kukanta ta k'oshi kana ta mik'e cikin sanyin jiki,
ta cire agogonsa ta d'ora masa akan table,
kana ta durk'usa ta d'auki hularsa dake yade a k'asa itama ta d'ora masa akan table,
ta cire takalmin ta aje a gefe,
kana ta d'auki d'an kwalinta ta d'aura,
ta yafa mayafinta, ta saita kanta sosai kana ta fita,
duk abinda take yi idansa na kanta,
tana fita ya naushi bango da k'arfi,
"oh! sheet! ya akayi nayi loosing control?
" Na aikata abinda ban tab'a yi ba,
zama yayi akan sofa dake cikin office d'insa yayi tagumi hannu bibbiyu yana san ya tuna abinda ya faru yanzu,
tana fita ta nufi get, ko ta kan lectures bata bi ba,
tafe take kawai batare data san inda take jefa k'afarta ba,
gaba d'aya hankalinta baya tare da ita,
ta fad'a duniyar tunnani,
a fili tace " shin da gaske ne abinda ya faru dani yanzu koko mafarki nake yi?
"Da gaske Sir Moli ne yayi abinda yayi man yanzu?
" Ashe dama d'an iska ne, mazinaci, fasik'i?
" Allah kad'ai yasan yawan matan dayayiwa abinda yayi man yanzu,
tana fita bakin get ta samu mai adai-dai sahu,
babu b'ata lokaci ta shiga ya kaita gida,
a harabar gidan ta iske Aarib yana k'ok'arin shiga mota,
yana hangota ya fasa ya tsaya yana jiran ta k'araso idanshi kanta yana yi mata murmushi,
"meyasa baki kira ni nazo na d'aukeki ba?
Ya tambaye ta,
kwata-kwata hankalin Sanah baya jikinta,
dan bama ta lura da wani Aarib ba,
kallanta yayi cike da mamaki kana yace " Sanah!,
amma shiru bata amsa masa ba,
tafiya kawai take yi, direct part d'in Halan ta nufa,
Aarib yabi bayanta da kallo, har yayi yunk'urin binta sai kuma ya fasa,
ya shiga mota yayi waje,
parlor ta shiga ta zauna akan sofa had'i da runtse idanta da k'arfi,
Halan na durk'ushe ciwon nak'uda ya dameta,
ji take kamar zata mutu, dakyar ta kira sunan Sanah,
amma shiru bata amsa ba,
cikin muryarta da bata fita sosai ta kuma cewa " Sanah!,
amma shiru bata amsa ba, dakyar Halan ta rarrafo tazo inda take tasa hannu ta tab'a ta,
firgigit Sanah tayi ta farka daga hang d'in da brain d'inta tayi,
ajiyar zuciya ta sauk'e da k'arfi kana ta kalli Halan dake ta faman cije baki tace " Aunty lafiya dai ko?
Dakyar Halan tace " kira yayanku,
Sanah najin muryarta tasan tana cikin mawuyacin hali,
da sauri ta mik'e jikinta ta kerrrma,
tayi kan Halan tana dialing number Ziyad,
sai da ta kusa yin cutting kana yayi picking,
bata jira taji abinda zaice ba tace " Yaya kazo gida yanzu Aunty Halan ba lafiya,
a kid'ime ya mik'e yana cewa gani nan,
wayar Khulud tayi dialing tana yin picking tace " ki zo part d'in Aunty Halan,
ina nan bata da lafiya,
da sauri Khulud ta mik'e tana cewa Mamu " Aunty Halan ba lafiya inaga haihuwa ce,
Mamu ta mik'e itama tace " Allah ya raba lafiya ki biya ki sanar da Juju,
kasancewar mutanen da akwai kara,
ita Mamu bata iya binsu hospital saboda ita ta haifi Ziyad,
dole zatayi kara,
Khulud na fad'awa Juju ta mik'e da sauri ta zari hijab sukayi part d'in Halan,
suna shiga Ziyad na shigowa bai wani ji kunyar Juju ba ya sab'i Halan yayi cikin mota da ita,
yana cewa " Khulud d'auko akwatin kayan haihuwa,
da sauri ta nufi d'akin ta d'auko,
Family Hospital d'in su ya kaita suna isa aka karb'eta aka shigar da ita labour room,
Sanah da Khulud suka yi cirko-cirko,
Juju da Ziyad na gefe.
A hankali ya mik'e ya sanya agogonsa da cut,
kana ya zira takalminsa ya zari brief case d'insa ya fita,
kasancewar yau Friday yasa Aryan nufar masallacin juma direct,
ana idar da sallah ya koma mota ya zauna,
dayake a yanayin damuna ne yana zaune cikin mota yaji an fara yayyafi,
ji yayi gaba d'aya hankalinsa yayi gida Maiduguri,
dama ya kai wajen 4 weeks baije weekend ba,
a hankali ya d'ago hannunsa ya kalli agogo yaga 1:30pm na rana,
ido ya lumshe yana jin sha'awar yin long journey a mota,
ya san kuma muddin Hilwa yasani bai barinsa ya tuk'o mota tun daga Kano har Maiduguri,
cewa zayyi dole sai yabi jirgi ko a aiko masa da Army Jet a d'auke shi,
kuma a ransa bai wani san tafiya a jirgi sosai,
musamman ma idan anan gidan Nigeria ne,
baya kuma san driver yafi san yayi tuk'i da kansa,
dan haka ya yanke shawarar tafiya kawai batare daya sanar da kowa ba,
sai dai yayi musu zuwan bazata,
a hankali yayiwa motar key ya d'auki hanyar Barno,
ya sakarwa motar wuta, dan Aryan akwai gudu da mota.
Halan takai 3hrs tana labour kana ta haifo yaronta,
mai kyau, nurse ta fito d'auke da baby Sanah tayi saurin amsar Baby tana murna,
Khulud ta kalli nurse d'in tace " ya Maman Babyn?
Nurse tayi murmushi kana tace " tana lafiya,
ai kaita d'akin hutu tana bacci,
nan da d'an wani lokaci zaku ganta,
a ranar da dare aka sallami su Halan kasancewar ta haihuwa lafiya babu wata matsala,
suka koma gida cikin murna da farin ciki.
Hanash na fita daga office d'in Sir Moli ya shiga mota,
ya kai wajen 10 minutes yana tunanin da bai san kona meye bane,
ji yayi ya k'ara jin tsanarta fiye da koyaushe a rayuwarsa,
tsoki yaja kana jiki a sanyaye yayiwa motar key yayi gida,
a parlor ya iske Mimmee zaune tana cin kwad'an Salad,
kusa da ita ya zauna, jikinsa duk ba dad'i,
kallo d'aya tayi masa tasan akwai abinda ke cikin ransa,
kallansa tayi tace " Son meke damunka?
Murmushi yayi kana yace " bakomai Mimmee,
d'an shiru tayi had'i da zuba masa ido kana tace " kamar ya bakomai?
Shiru yayi baice mata komai ba,
dan shi kansa bai san meke damunsa ba,
" ya kukayi da Khulud d'in?
Ajiyar zuciya ya sauke kana ya sanar da ita duk yadda sukayi,
bai b'oye mata komai ba,
shiru tayi na wani lokaci kana tace " kayi hak'uri,
in sha Allah I will pray for you kaji,
zan nemar maka zab'in Allah,
a sanyaye ya d'aga mata kansa,
tace " karka karaya kaji Son, ka cigaba da zuwa,
haba kai kamar ba namiji ba,
kai fa cikekken namiji ne, kayi amfani da basirarka da kuma wayonka,
ka sanya mata sanka,
"how!?
yace, " ban sani ba Mimmee ta fad'a a d'an hasale,
tana ture shi,
murmushi yayi kana yace " I promise you Mimmee I will try my best,
tayi murmushi kana tace masa good Son.
Aryan na shiga garin Maiduguri aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya,
wani mahaukacin katafaren gida,
wanda tun daga waje naga sojoji sunfi a k'irga suna kaikawo,
automatic get d'in naga ya bud'e kansa,
bayan yayi snapping number motar Sir Moli,
gaba d'aya habarar gidan babu komai sai dandazon sojoji dake kai kawo,
gidan yana da haukacin girma,
dan da gani filin da akayi gidan 300 by 300 ne,
gaba d'aya gidan zagaye yake da shukoki iri-iri,
a harabar gidan yayi parking batare daya fita ba ya kishingid'a,
Yara na gani a k'alla sun kai 7 suna wasa da ruwan sama a cikin farfajiyar gidan,
yayinda na hangi wasu yaran rakub'e cikin baranda,
da alama suma suna san yin wasan ruwa,
tsoro ne ya hana su,
d'aya daga cikin yaran dake tsaye a cikin baranda yace " Yaya kun fa san Uncle Aryan ya hana mu wasa a cikin ruwa ko?
D'ayan yace " kai zaka fad'a masa munyi wasan ruwan?
D'aya yaron yace " a'a amma kasan fa yace " idan mukayi zai gani,
kuma yace duk abinda muke yi yana ganin mu,
a duk inda yake,
d'ayan yace ba wani nan wayo yake yi mana,
kazo muyi ai babu wanda zai fad'a masa,
d'ayan yace " a'a ni banyi ni dai tsoro nake ji,
d'ayan zayyi magana Sir Moli ya bud'e mota ya fito,
gaba d'aya jikin yaran ya d'auki kerrrma da tsuma,
suka shiga rige-rigen guduwa,
wasu na take wasu, yadda kasan sunga dodo ko aljani,
wad'anda ke kan barandar suna ganin shi suka fito da gudu,
suka nufe shi suna cewa " ga Uncle Aryan ga Uncle Aryan,
oyoyo Uncle Aryan,
yaran naga ya kalla farare tass dasu,
masu kama da yaran turawa,
suna sanye da kaya na alfarma da gani kasan masu tsada ne,
murmushi yayi musu kana sunkuyo dai-dai tsayin su,
da gudu suka fad'a jikinsa, d'ayan yaron ya zagayo ta bayansa ya sak'alo wuyansa,
ya d'auki cutie Baby's d'in a hannunsa,
yayi hanyar part d'in Hilwa ya,
kasancewar yau ana suna a gidan yasan part d'in Nainah akwai mutane,
matar Yayanshi Haidar ta ce haihu,
yau ake suna,
a parlor'n Hilwa ya iske babban Yayanshi da auta Jabeer,
zaune suna hira,
Hilwa na ganinsa yayi saurin mik'ewa zaune daga kishingid'en dayake,
ya mik'e masa hannu alamar yazo,
yana dariya yadda kasan anyi masa bushara da aljanna,
annurin fuskarsa ya fad'ad'a ganin Sir Moli,
shima yana murmushi ya nufi mahaifin nasa mai tsananin so da k'aunarsa fiye da duk 'ya'yan daya haifa,
kwata-kwata Hilwa da Nainah basu iya b'oye tsananin son da suke yi Aryan a cikin yaransu,
yadda kasan shi kad'ai suka haifa a duniya,
kusa da Hilwa Aryan ya zauna yana fad'ad'a murmushinsa,
Hilwa ya shafa kansa yace " Soul shine kazo bako announcement,
dariya Sir Moli yayi yace " nasan baka bari na nayi driving ne,
ido Hilwa ya zaro yace " kai ka tuk'o motar tun daga Kano har Maiduguri?
Aryan yayi dariya yace " eh Love,
Hilwa yace " Moli (dayake haka yake kiransa wani lokacin saboda tsananin kamar dayake da shi,
shiyasa yake ganin kamar shine magajinsa),
"please ka daina wasa da rayuwarka kasan bazan iya jure rashinka ba ko?
Murmushi Haidar yayi kana yace " Hilwa ka hana mu gaisawa da d'an uwanmu ma,
Aryan yayi dariya yace " Big Bro ina wuni?
" Lafiya lau,yace yana dariya,
kana yace " ya aiki?
Sir Moli yace " aiki Alhamdulillah,
babban d'an Haidar ya shigo wanda zayyi sa'an Jabeer,
tare Jabeer da Noor suka gaida Sir Moli,
ya amsa fuska a sake,
hira sosai Hilwa da Aliyu & Aryan suka shiga,
yaran da suka tsorata sukayi cikin gida,
gidan suka shiga da suna cewa " Nainah, Ummi Uncle Aryan ya dawo,
"Uncle Moli ya zo (duk gidan suna kiransa da Moli)
Nainah tayi murmushi tace " zakin d'ana ya dawo,
dama indai na ganku kun shigo a firgice nasan shine,
manyan Yayyansa mata duk suka mik'e suna tambayar " ina yake! ina yake!?
Aunty Kubra ta d'auki wayarta tayi dialing number sa,
wayar na fara ringing Sir Moli ya kalli wayar,
kana yayi murmushi,
Hilwa da Haidar suka kai dubansu ga wayar,
Hilwa yace " hala har an kai musu labarin zuwanka,
murmushi ya kuma yi kana yayi picking wayar,
Aunty Kubrah tace " yanzu Mudah suka sanar mana ka zo,
kuma har yanzu bamu ganka ba,
"dariya yayi yace " ina part d'in Hilwa ni da Yaya,
"au ashe ko da gaske suke?
" Sannu kasha hanya bari yanzu na dawo maka ruwa,
"nagode yace had'i da yin dropping wayar,
gaba d'aya gida aka shiga munar dawowarsa saboda tsananin so da k'aunar da suke yi masa,
abinci Aunty Nina da Aunty Kubra suka shirya masa kala-kala,
Nainah, da Aunty Ayyam suka nufi part d'in Hilwa,
Jiya ta shigo da gudu a gabansa ta tsaya tana hakki tace " Uncle Aryan ina alk'awarin mu?
Jabeer yace " wallahi nima shi nake jira tun d'azu,
Sir Moli ya tsuke fuska had'i da cewa " bako gaisuwa,
balle ya hanya kinzo kin tsare kina tambayata alk'awarinki kamar wacce taban ajiya,
baki ta tab'a ta fara diddira k'afarta,
cike da shagwab'a tasan yin kuka,
tsawa ya daka mata had'i da cewa " karki soma dan ubanki,
sanin halinsa yasa jiya had'iye kukanta,
ta fad'a jikinsa tana dariya tace " I'm sorry Uncle,
ina wuni?
"Alhamdulillah, ya amsa yana d'agata sama,
dai-dai lokacin Nainah, Aunty Kubra, Aunty Nina da Aunty Ayyam,
suka shigo, gaba d'ayansu suka zauna kusa da shi,
suka zagaye shi suka sanya shi tsakiya,
Nainah ta jawo shi jikinta ta rungume tana shafa kansa tace " Life kasha hanya,
sannu Life,
Hilwa yace " kuma a mota yazo shine ma yayi driving,
Nainah ta zaro ido,
tace " Life meyasa?
Kansa ya k'ara kwantarwa a jikinta,
yace " sorry Nainah ban k'arawa,
tayi dariya tana d'ago shi tace " tashi kaci abinci,
nasan halinka da rashin san cin abinci,
mik'ewa yayi zaune yace " ai dole naci abincin gidan Nainah da Hilwa na yau dan nayi missing d'inshi sosai,
Aunty Ayyam ta jawo tray d'in abinci,
ta fara zuba masa, Aunty Nina na zuba masa drink a glass cup,
Haidar yace " uhmmm kaga d'an gatan Aunty's d'insa da Nainah,
ni dayake yau matana suna can wajen hidimar suna babu wanda ya kula dani ai,
aka barni da yunwa,
Nainah na ta hidimar da Hilwanta,
ni kun manta da ni,
ashe rabon naci da Brother na ne,
ya fad'a yana dariya, had'i da matsowa suka fara cin abincin tare,
Hilwa dayake soja ne bai san yaji,
abincin shima daban ake girka masa yace " ni ban iya ci da ku,
Jabeer da Jiya suka zauna kusa dashi a hankali suka ce " Uncle!
ya juya ya kalle su yace " meye kuma?
"Alk'awarin na mu,
kansa ya dafe had'i da cewa " oh my God,
Haidar yace " wai alk'awarin me kayi musu ne?
Aryan yace " Jiya laptop take so,
Jabeer kuma iPhone X yake so,
Hilwa yace " meyasa baku fad'a man na siya muku ba zaku damar man yaro?
Aryan yace " ai nama siyo musu suna mota,
Jiya da Jabeer suka shiga tsalle suna murna jin an siyo musu,
Jabeer yace " Yaya suna ina?
Sir Moli yace " suna mota, ungo key d'in ku d'auko ku barni na huta,
har ya basu key d'in ya tuna ana ruwan sama,
da sauri yace " yanzu ana ruwa ku bari sai an d'auke ruwan sannan,
ya fad'a yana amsar key d'in,
suna hira cikin so da k'auna,
sai da suka gama kana Sir Moli ya nufi part d'insa,
wanka yayi jikinsa duk a sanyaye,
ya rasa meke damunsa a duniya,
abinda yayiwa Sanah ya tsaya masa a ransa,
shi kunyarta ma yake ji, ji yake kamar bazai iya sake had'a ido da ita ba,
shi tsoransa d'aya ma karta d'aukeshi d'an iska tayi tunanin ko haka yake yiwa wasu matan,
wanka yayi ya shirya ya fita ya zagaya baya,
gani nayi ya b'ullo bakin swimming pool,
mai kyau da kayan k'awa,
gadon dake gaban swimming d'in ya hau ya kishingid'a,
wata 'yar kwararrawa ya danna naga wasu sojoji sun fito sanye da uniform iri d'aya a jikinsa,
batare daya d'aga kansa ba yace " a bani abu mai sanyi,
kai suka risina cikin girmamawa kana suka juya,
basu jima ba suka dawo d'auke da drinks kala-kala,
ya kai good 1hr anan kana ya mik'e ya nufi gym,
wata k'ararrawar ya danna sojoji suka fito,
a tak'aice yace " green tea,
sosai ya motsa jikinsa kana ya fita ya koma garden mai d'auke da flowers masu k'amshi da kyau,
ga tsuntsaye kala-kala suna kukan su mai dad'in sauraro,
tsayawa fad'ar had'uwar gidan Moli's b'ata lokaci ne,
saboda an kashe kud'i kamar ba gobe wajen tsara gidan,
duk wani abu na more rayuwar duniya akwai shi a cikin gidan,
abun da yafi ban mamaki shine,
duk wani ma'aikaci dake gidan soja ne,
dai-dai da masu aiki da wanki da guga duk they're sojan.
Aryan na kwance a bedroom d'insa,
Nainah ta shigo d'auke da fruits salad,
sallama tayi a k'alla takai sau uku,
amma Sir Moli baiji ba, a hankali ta ajeye tray d'in akan glass,
kana ta zauna kusa da shi,
hannun tasa ta kwantar da kansa akan cinyarta,
tana shafa kansa,
ajiyar zuciya ya sauke a hankali,
Nainah ta kira sunansa " Aryan!
a hankali ya amsa " na'am,
tace " meke damunka?
Tunda na d'ora idona akanka kasan kana cikin damuwa,
shiru yayi baice komai ba,
Nainah ta k'ara cewa " meke damunka Aryan?
"Bakomai heartbeat,
ya amsa mata,
" ya zakace bakomai bayan ga damuwar nan k'arara ta bayyana a tattare dakai,
murmushi yayi kana yace " nayi exercise da yawa na gaji ne,
murmushi tayi ta k'ara shafa kansa duk da bata yarda da abinda yace ba,
mik'ewa tayi a hankali ta d'auko fruits salad d'in ta shiga bashi a baki,
bata barshi ba sai da ya shanye tass,
dan tasan halin Aryan bai san cin abinci,
kansa nakan cinyarta tana shafa masa har yayi bacci,
a hankali ta mik'e ta d'auko Italian blanket ta rufe shi,
tayi masa kiss a kumatu kana ta fita,
sosai Moli's Family ke mugun so da tsananin k'aunar Aryan kamar ransu,
kowa yana nan-nan dashi kamar k'aramin yaron goye.
Washe gari da safe wajen k'arfe 11:30am na safe,
ya fito ya nufi part d'in Nainah,
dayake yasan 'yan taran suna duk sun tafi,
yasan babu sauran bare sai Moli's Family,
har ya kusa shiga part d'in ya tuna da alk'awarin su Jabeer,
komawa yayi ya d'auko sabuwar laptop da wayar duk a cikin kwalayen su,
kana ya nufi part d'in,
ganin ba kowa a parlor yasa shi nufar bedroom d'inta,
a can ya iske ta zaune tsakiyar Aunty's d'insa,
ana ta hira, Aunty Nina da Aunty Kubra na kan gado,
yayinda sauran ke zaune akan carpet,
kan gadon shima ya zauna had'i da tankwashe k'afarsa,
kana ya shiga gaida su,
Nainah ta k'urawa Aryan ido tana karantar yanayinsa batare datace komai ba,
Jabeer da Jiya suka zuba masa ido,
suna tsoron sake tambayarsa,
lura da irin kallan da su yi masa ne yasa shi mik'a musu,
cikin murna suka amsa suna da tsalle,
had'i dayi masa kiss a kumatunsa,
kana sukayi waje da gudu,
Aunty Ayyam tace " brother bari na kawu maka breakfast d'inka nan,
dariya yayi kana yace " thank you sister,
kunun gyad'a da zazzafan k'osai dayaji hanta da kwai ta kawo mishi,
" woww gaskiya nagode sosai Nainah,
ya fad'a yana kallan Nainah,
Aunty Nina tace " oh! mai yin wahalar daban wanda ake yiwa godiya daban,
yayi dariya yace " sorry Aunty, nagode sosai kema,
hira suka shiga yi sosai,
dan Moli's Family suna matuk'ar so da k'aunar junnansu,
gasu da had'in kai sosai kamar tsintsiya,
fuska ya d'an b'ata kana yace " wai Aunty me kuke har yanzu baku koma gidajenku ba?
Aunty Ayyam tace " kai kaga matsalarka ko,
kai sai ka juya fuska kamar kai ne babba akan mu,
fuska ya k'ara tsukewa yace " kowacce ta tashi ta shirya ta koma gidan mijinta,
miye dan suna kawai zaku zo ku zaune har ku sake kwana,
maza ku shirya yanzu ku tafi,
dayake Sir Moli akwai san girma idan yana wani abun sai ka rantse shine babba a gidan,
kuma dukda yana k'aramin su dukkan su suna jin shayinsa,
dan basa tab'a gigin kawo mishi rai,
shiyasa Hilwa yake ganin Aryan shine magajinsa,
Nainah tace " gaskiya kam nima tun jiya nake cewa su shirya su tafi,
suka k'i tafiya,
kai yanzu dayake kai ne daka tasasu a gaba ai dolansu su tafi,
Hilwa ma bai san suna nan sun k'ara kwana ba,
Sir Moli bai bar part d'in Nainah ba,
sai da ya tabbatar kowacce ta kwashi yaranta ta koma gidanta,
da daddare Sir Moli zaune kusa Hilwa a part d'insa,
Hilwa nayi fad'a akan rayuwa,
kan yaji tsoron Allah ya rik'e gaskiya da amana aduk inda yake,
Sir Moli yace " Hilwa gobe zan koma,
Hilwa yace " au gobe fa Sunday ko?
" Ni nama manta,
amma bazaka koma a mota ba,
ba zaka koma gobe ba, ka bari sai Monday,
sai jet ya kai ka da asuba,
ya amsa da to.
ranar Monday ana yin Sallar Asuba jet ya d'auki Moli yayi kano,
gidan yayi shiru kowa yana cike da kewarshi.
Ranar suna yaron Halan yaci sunan Didi Rawan, suna kiranahi da Khair,
yau tunda Khulud ta tashi ta tashi da matsanancin ciwon mara kamar zata mutu,
dan ko kanta bata iya d'agawa,
gashi ta kasa tashi balle taje tayi wanka,
Sanah kuma tun 7:00am ta tafi school kasancewar tana da lectures 8:00am,
tana kwance kamar zata mutu tayi shiru,
Hanash yau ma ya shirya cikin shiga ta alfarma,
yayi masifar kyau ya nufi gidan su Khulud,
yauma mai gadi yaje yayi sallama da ita,
sai lokacin Mamu ta shiga d'akin dubota,
dan tunda Sanah ta fara school,
ita kuma ta koma zaman bedroom,
shiyasa yau koda Mamu taga bata fito ba batayi tunanin wani abu ba,
ganin Khulud kwance tana ta murk'ususu,
yasa Mamu k'arasawa da sauri,
" ya Salam, Mamu ta fad'a tana d'agota,
" meke damunki?
Mamu ta tambaye ta,
dakyar tace " ciki na ne,
tana fad'ar haka Mamu ta gane period zatayi,
cikin tausayawa Mamu tace " dama yana yi maki ne?
Dayake su Mamu basu san Khulud bata fara ba,
shiru Khulud tayi bata bawa Mamu amsa ba,
kwantar da ita Mamu tayi ta mik'e ta shiga bathroom d'insu,
ta had'a mata ruwan wanka,
kana ta fito ta umarce data shiga dakyar Khulud ta mik'e ta shiga,
kafin ta fito Mamu ta fiddo mata kaya harda pad, pant & bra,
kana ta fita, cikin sanyi Khulud ta fito,
kayan da Mamu ta fiddo mata tabi da kallo,
kayan ta saka ta shirya sosai ,
ta d'auke pad d'in ta maidata cikin wardrobe,
bata jima da shiryawa ba, Mamu ta shigo d'auke da tray na abinci,
tea ta fara bata tasha dakyar,
Mamu ta matsa mata ta shanye tea d'in tsaf,
kana ta bata chips & miyar hanta,
ta d'anci kad'an kana Mamu ta bata magani tasha,
sosai Khulud taji ciwon ya lafa mata,
Mamu na zaune kusa da Khulud taji sallamar get man,
kai Mamu ta dafe tace " tab na manta tun d'azu kikayi bak'o fa,
Khulud ta d'an zumb'uro baki tace " Mamu ban jin dad'i ban iya fita,
Mamu tace " mutumin yazo tun d'azu yakai wajen awa d'aya da rab'i yana zaman jiranki amma ki k'i fita?
"Mamu please ki aika ace masa ban jin dad'i,
ta fad'a a shagwab'e,
Mamu tace " ki fita da kanki kije kiyi masa bayani,
zata kuma yin magana Mamu tace " no argument,
jiki a sanyaye Khulud ta fita,
iskewa tayi har an kai shi set room,
koda ta shiga taga kayan drinks & snacks jere a gabansa,
tana shigowa ya mik'e da sauri had'i da zubawa fuskarta ido,
a hankali ta zauna tana cije lips,
cikin sanyin murya tace " ina wuni?
" Alhamdulillah ya bata amsa yana kallanta,
ganin yadda take cije lips yasa shi cewa " meke damunki?
Muryarta na rawa tace " ciki na ke ciwo,
" innalillahi wa'inna ilaihirrajji'un yace,
cikin tashin hankali yace " tun yaushe?
" Tun safe ta bashi amsa,
cike da tension ya shiga jera mata sannu,
yadda kasan zayyi kuka yake magana muryarsa na rawa,
ido kawai Khulud ta zuba masa ganin yadda lokaci d'aya yanayinsa ya canja,
duk ya shiga cikin tashin hankali ya rud'e,
sosai Hanash yayi mugun bata mamaki,
yadda ya nuna damuwa k'arara a fuskarsa,
murmushi Khulud tayi tace "karka damu fa,
naji sauk'i ai,
kamar zayyi kuka yace " kamar ya karna damu?
Bayan kin san dole na damu, kin san abinda rai ke so ne ai,
shiru tayi bata kuma yin magana ba,
ganin haka yasa shi cewa " tashi ki ciki,
gobe na dawo naji ya jikin,
murmushi tayi kana tace" nagode,
yace " bakomai,
ya mik'e zai fita idansa ya sauka akan wayarta data manta,
da sauri ya koma ya zauna ya d'auki wayar,
to his lucky wayar babu pin,
pic d'in Sanah ya gani a screen sever,
in capital letter an saka my Happiness,
theme d'in wayar ma na pic d'in Sanah ne,
murmushin bak'in ciki yayi yana jin matsanancin kishin Sanah na shigarsa,
contacts d'inta ya shiga, my heartbeat yaga tayi saving number Sanah,
tsaki yayi kana ya saka number sa a wayarta yayi saving da MY LIFE,
kana yayi dialing dan ya samu number ta,
kiran ya shiga yayi saving number ta da My love,
kana ya bawa mai gadin wayar ya kai mata,
tun a motar ya kira ta,
tana zaune taga My life na kira,
cikin mamaki ta d'auki wayar tana mamakin waye,
har kiran tsinke aka kuma kira,
tana yin picking taji shine,
a ranar Hanash ya kira Khulud yaji ya jikinta yakai 10×,
Khulud na waya da Hanash taji k'arar parking,
da sauri cikin murna tace masa " my Sanah ta dawo,
bata jira amsarsa ba kashe wayar.
A ranar da daddare matsanancin ciwon mara ya hana Khulud sakat,
amma gudu karta tashi Sanah daga bacci yasa ta daurewa dan tasan da sassafe take fita,
sai wajen 3:00am period d'in Khulud yazo kana ciwon ya lafa mata,
sosai Hanash ya nunawa Khulud so da kulawa a rashin lafiyarta,
tun tana basar dashi harta fara sakin jiki dashi suna hira sosai,
sai dai duk rabin hirar labarin Sanah take bashi,
bata da wata magana ko labari daya wuce na Sanah,
bata san duk lokacin data ambaci sunan Sanah a kunnen Hanash daurewa kawai yake yi ba,
amma ji yake kamar tana watsa mishi wuta,
lokacin da Khulud ta sanar da Sanah da Halan ta fara period sosai sukayi murna da farin ciki,
satinta d'aya tana period tayi wanka,
Hanash ko kullum sai ya zo ba fashi,
dan ya dage sai ya sakawa Khulud matsananciyar soyayyar shi a zuciyarta,
kasancewar babu Sanah babu mai d'ebewa Khulud kewa,
yasata fara kula Hanash,
tun tana shashshare har dai ta fara kula shi,
sai dai ko zancen yazo hirar dai d'aya ce ta Sanarta,
daga my Sanah kaza sai my Sanah kaza,
sosai Hanash ya rink'a d'ebewa Khulud kewa, yana bala'in kula da ita sosai,
saboda yadda ya nuna damuwa da kulawa a gareta,
musamman ma da bata da lafiya,
ko kuma da tace abu yake yi babu musu,
duk abinda zayyi ya faranta mata shi yake yi,
yana kuma gudun duk abinda zai b'ata mata rai,
sosai yake nuna mata so da soyayyarta a zahiri,
sannu a hankali soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Hanash da Khulud,
suna yiwa junansu mugun so,
24hrs suna tare a waya, ko chart,
kasancewar Sanah da sassafe take fita school bata dawowa sai gaf da magrib,
idan kuma ta dawo bata da lokaci sosai datayi wanka taci abinci tayi sallah sai bacci ko karatu,
yasa kwata-kwata bata lura da abinda ke faruwa tsakanin Hanash da Khulud ba,
bata san komai ba,
ita kuma Khulud ba b'oye mata tayi ba,
dan bata samun lokaci ne yasa bata sanarda ita abinda ke faruwa ba,
sosai tsantsar soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Hanash da Khulud,
fiye da tunanin mai karatu,
ta yadda babu abinda d'aya zayyi batare da d'ayan sa ni ba,
kullum kuma ko yaushe suna manne da juna a waya,
sunyi masifar bawa junansu mahimanci fiye da tunani.
Tun bayan faruwar wannan al'amarin babu wanda ya k'ara ganin wani tsakanin Sir Moli da Sanah,
sosai suka shiga wasan b'uya,
a gajiye lik'is Sanah ta koma gida yau ma,
Khulud na waya da Hanash taji shigowar Sanah tayi saurin mik'ewa,
had'i dayin cilli da wayar,
Sanah ta zube akan sofa,
had'i da cewa " wassh Allah na gaji da yawa,
cikin tausayawa Khulud tace sannu My Sanah,
Hanash dake ta faman hello hello,
jin shiru, ya jiyo muryar Sanah,
tsaki yayi had'e da kashe wayar,
Khulud ta rik'e hannun Sanah tace " muje kiyi wanka,
ba musu Sanah tabi Khulud zaunar da Sanah Khulud tayi a bakin bed,
kana ta shiga bathroom ta had'a mata ruwanka,
ta fito tace " my Sanah shiga kiyi wankan,
Sanah ta mik'e ta cire kayan jikinta ta d'aura towel,
ta shiga tayi wankan ta d'auro alwala,
kafin ta fito Khulud ta fiddo mata kaya marasa nauyi da pant ta aje mata akan bed,
Sanah ta fito ta zauna gaban mirror tana shafa lotion,
cikin matsananciyar gajiya,
Khulud tayi dariya tace " ko inzo na shafa maki man?
Ta fad'a cikin tsokana,
Sanah tayi dariya tace " dako kin taimaka da yawa,
mai kawai Sanah ta shafa ta zura doguwar rigar bacci,
ta saka pant kawai bata saka bra ba dan bata bacci da bra,
perfume's ta fesa,
kana ta fara k'ok'arin hawa bed,
Khulud ta kalle ta tace " abinci fa?
Naga kina k'ok'arin yin bacci,
Sanah tace " kai bar abincin nan kawai,
Khulud ta turo baki kana tace " Allah sai kinci kefa nake jira ki damo mu ci,
Sanah tayi murmushi tace " sorry jeki d'auko mana muci,
Khulud ta mik'e ta fita tana cewa " yauwa ko ke fa,
wayar Khulud dake gefe ta ringing,
Sanah bata kula wayar ba harta katse,
aka sake kira, nan ma bata yi picking ba,
sai da kira na 5 ya shigo kana ta mik'a hannunta daga inda take kwance ta lalubo wayar,
sunan ta kalla taga anyi saving da My Life,
cikin mamaki ta tace " my life kuma, waye kuma my life?
Ta tambayi kanta,
jin wayar na neman katsewa yasa ta saurin yin picking,
"hello my happiness ina ta kira shine ba'ayi picking ba,
yayi maganar zazzak'ar muryarsa,
gaban Sanah yayi muguwar fad'uwa,
a hankali ta zame wayar daga kunnenta ta k'ara kallan screen d'in,
taga tabbas ba wrong number bace,
tunda gashi anyi saving, cikin mamaki ta k'ara mayar da wayar kunnenta,
muryarta na rawa tace " bata nan,
jin muryarta ya sashi sakin tsoki had'i da kashe wayar,
wayar Sanah ta k'urawa ido cike da mamaki,
Khulud ta shigo d'auke da tray d'in abinci,
ganin yadda Sanah ta k'urawa wayar ido tanaR juyata,
ya sata zama kusa da ita,
" lafiya?
Khulud tace, cikin sanyin jiki Sanah tace " waye my life?
Murmushi Khulud tayi tace " he's my love,
"your love?
Sanah ta maimata cikin mamaki,
Khulud tace " eh!, ban baki labarinsa bane saboda baki zama,
da kin dawo kike kwanciya bacci,
Sanah tace " yanzu dama Khulud har akwai wani abu da zamu b'oyewa junanmu, har akwai abunda zamuyi batare da sanin juna ba?
Khulud tace " My Sanah baki zama fa,
Sanah tace " saboda bana zama shine ya hana ki fad'a min,
wannan ai ba dalili bane, tunda ba mutuwa nayi ba, ba kuma garin na bari ba,
cikin sanyin murya Khulud tace " I'm so sorry, ban san na hana ki bacci ne,
shiyasa kika ga ban sanar dake ba,
Sanah " ok yanzu ai ina jinki,
Khulud ta mik'e tsaye had'i da d'aga murya cikin farin ciki tace " I love him,
I really love him so much,
I love him more & more most my Sanah,
ke kad'ai nafi so a duniya sama da Hanash,
ganin yadda Khulud ke farin ciki yasa Sanah yin murmushi tace " who is he?
Khulud tace " Hanash Waseef,
Sanah tayi rolling sexy eye d'inta tace " taya za'ayi na sanshi,
description d'insa gaki man yadda zan gane,
Khulud tace " ai kin san shi ma,
Sanah tace " na sanshi, a ina?
Khulud tace " wannan wanda kukayi fad'a,
Sanah tace " wai wa?
Khulud tace " wanda ya watsa maki ruwan kwata har sau biyu,
ke kuma kika mare shi,
a firgice ta mik'e tana kallan Khulud had'i da ja baya..............
_Banyi editing ba, so nasan akwai typing errors_
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣2⃣
Hannunta ta saka ta rufe bakinta,
had'i da zaro sexy eyes d'inta waje,
a hankali cikin takunsa na cikakkun maza ya fara takowa gareta,
cikin tsoro Sanah ta fara ja baya tana yarfe hannu,
yana biyo ta ita kuma tana cigaba da yin baya har suka isa bango,
hannayensa ya saka ya dafe bango,
ya saka ta a tsakiyar hannayensa,
gaban rigarsa inda ya b'alle bottles d'in jikin rigar kyakkyawan k'irjinsa mai d'auke da yalwataccen kwantaccen gashi,
ta kalla, take taji gabanta yayi muguwar fad'uwa da k'arfi,
da sauri ta runtse idanta yayinda da k'irjinta keyin sama da k'asa da sauri-sauri,
lulu eyes d'insa ya zuba mata yana kallan yadda k'irjinta ke bugawa yana up an down da sauri,
yanayin k'amshin da sanyin Ac dake office d'inne suka saukar masa da wani irin yanayi a gaba d'aya ilahirin jikinsa,
yaji kasala ta saukarwa duk wata gaba ta jikinsa,
abinka kuma da yanayin damuna,
k'ara matseta yayi sosai a jikin bangon,
ta yadda k'irjinsu na gogar na juna,
da sauri Sanah ta bud'e idanta,
ta zuba cikin nashi,
ganin yadda lokaci d'aya gaba d'aya yanayinsa da kuma kamanninsa suka canja yasa zuciyarta ta shiga bugawa,
dayake ya fita tsayi yasa idan zata kalle shi sai dai ta d'aga idanta sama,
kanta na k'asa, idanta kawai ta d'aga tana kallanshi,
cikin wata irin kasalalliyar murya Sir Moli yace " kin tuna?
D'an kawar da kanta tayi gefe,
muryarta can k'asa tace " me?
Yace " alk'awarin da kikayiwa wannan mugun secondary teacher d'in naku,
muryarta na rawa tace " na manta,
"Ok bari na tuna miki, ya fad'a yana k'ara shegewa jikinta,
" please kaban last chance, idan na kuma yin laifi kayi man koma meye,
wallahi I promise ban k'ara yi maka laifi,
Allah idan na kuma kayi man komai kaga dama na yarda na d'auka,
duk abinda kaga damanyi kayi man,
ya fad'a bakinsa saitin kunnenta,
had'i da hura mata iskar cikin bakinsa a kunnenta,
kana yace " kin tuna yanzu?
Idanta na kansa ta d'aga masa kanta,
muryarsa can k'asan mak'ogwaro yace " kin san ban san d'aga kai ko?
Bakinta na rawa tace " eh!,
yace " good,
muryarsa bata fitowa sosai yace " shi kuma a lokacin mai yace miki?
Ya fad'a yana shinshinar wuyanta,
had'i da goga hancinsa a wuyanta,
kamar zatayi kuka saboda yadda duk yabi ya shege mata jiki,
tace " keep it in your mind,
I know one day you will pay for your promised,
"good yace , yana goga hancinsa a wuyanta,
" kince duk abinda naga dama nayi miki ko?
Ya fad'a muryarsa bata fita sosai,
"dan Allah kayi hak'uri Allah ban k'arawa,
yadda take maganar yasa shi k'urawa cutie lips d'inta ido,
still hannayensa na jikin bongon,
ita kuma tana tsakiyar hannayensa,
ya sanya fuskarsa a wuyanta yana goga mata,
kana a hankali ya fara goga mata fuskarsa akan tata fuskar,
sajensa yana gogar kumatunta,
k'irjinta na gogar na shi,
yadda k'irjinta ke yin sama da k'asa ya fara sa Aryan yin loosing control,
itako Sanah tsaron yanayin data ganshi ciki ne ya hanata yin koda kwakkwaran motsi,
idanshi na kanta yana karantar yanayin data shiga,
yasa hannu ya zame hularsa dake kanta,
ya cusa hunnunsa cikin gashin kanta,
bakinsa yakai cikin kunnenta ya rad'a mata,
kin shirya karb'ar punishment d'inki yanzu?
Ya fad'a muryarsa na creaking,
" kayi hak'uri tace , kuka na neman kwace mata,
yadda tayi maganar tana turo bakinta,
yasa Sir Moli had'e bakinsu waje d'aya batare daya sani ba,
ido Sanah ta zaro waje cike da tsoro jin abinda Sir Moli keyi mata,
gaba d'aya jikinsu ya d'auki rawa da tsuma,
kasancewar jin su a cikin wani irin yanayi da basu tab'a tsintar kansu ciki ba,
duk ilahirin jikinsu kerrrrrma yake,
musamman Sanah, da har hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta,
a hankali ya zagayo da hannunsa ya tallafe kanta yadda zaiji dad'in shan bakinta sosai,
had'i da cusa hannunsa cikin gashin kanta,
yana ya mutsuwa, still bakinsa na cikin nata,
d'aya hannun yakai yana shafa duk ilahirin jikinta,
hannu Sanah ta sanya a k'irjinsa tana k'ok'arin ture shi,
a hankali hannunta ya shege cikin rigarsa inda yake ya bud'e,
Sir Moli yana jin tattausan hannunta akan fatar k'irjinsa ya k'ara fita saga hayyacinsa,
jikinsa na kerrrma ya fara k'ok'arin neman zip d'in rigarta.
Hanash dake ta faman knocking a bakin k'ofar amma ba'a amsa ba,
ya d'an ja tsoki kana ya juya a hankali zai tafi,
bakinshi cikin nata tace " uhmm innnn amma ba damar yin magana,
saboda da gaske yake tsotsar bakin nata,
Hanash dake waje jin ance innnnn,
sai ya zata cewa akayi ya shigo dan haka ya danna kai cikin office d'in kai tsaye,
tsawa yayi cak ganin yanayin da suke ciki,
bakin Hanash na rawa yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
ya fad'a batare daya sani ba,
jin maganar Hanash ya sanya Sir Moli dawowa cikin hayyacinsa,
a matuk'ar kid'ime ya saki Sanah yayi baya,
cike da tsoro da kuma tsantsar mamaki Sir Moli yake bin Sanah da wani irin kallo,
yana tambayar kansa me yayi mata,
ido Hanash ya k'ura musu na tsayin lokaci,
yana kallan Sanah sanye da kayan Aryan a jikinta,
a hankali yabi cut da agogo da takalmin k'arfarta da kallo,
ya kuma kalli yadda gashin kanta ya barbaje,
kana ya mayar da kallansa ga Aryan dake dafe da kansa kwalla na neman gangarowa daga idansa,
yaga gaba d'aya jan bakin Sanah ya dame masa fuskarsa,
murmushin bak'in ciki Hanash yayi kana ya juya ya fita batare dayace musu komai,
durk'ushewa Sanah tayi had'i da fashewa da wani irin rikitaccen kuka,
kansa ya dafe dake barazanar tarwatsewa had'i da zuba mata idanuwansa da suka koma pure red color,,
muryarsa na rawa Sir Moli yace " me nayi?
" Meke shirin faruwa dani ne?
Yayi maganar idansa na kanta,
yana kallan yadda take ta faman kuka,
sai da taci kukanta ta k'oshi kana ta mik'e cikin sanyin jiki,
ta cire agogonsa ta d'ora masa akan table,
kana ta durk'usa ta d'auki hularsa dake yade a k'asa itama ta d'ora masa akan table,
ta cire takalmin ta aje a gefe,
kana ta d'auki d'an kwalinta ta d'aura,
ta yafa mayafinta, ta saita kanta sosai kana ta fita,
duk abinda take yi idansa na kanta,
tana fita ya naushi bango da k'arfi,
"oh! sheet! ya akayi nayi loosing control?
" Na aikata abinda ban tab'a yi ba,
zama yayi akan sofa dake cikin office d'insa yayi tagumi hannu bibbiyu yana san ya tuna abinda ya faru yanzu,
tana fita ta nufi get, ko ta kan lectures bata bi ba,
tafe take kawai batare data san inda take jefa k'afarta ba,
gaba d'aya hankalinta baya tare da ita,
ta fad'a duniyar tunnani,
a fili tace " shin da gaske ne abinda ya faru dani yanzu koko mafarki nake yi?
"Da gaske Sir Moli ne yayi abinda yayi man yanzu?
" Ashe dama d'an iska ne, mazinaci, fasik'i?
" Allah kad'ai yasan yawan matan dayayiwa abinda yayi man yanzu,
tana fita bakin get ta samu mai adai-dai sahu,
babu b'ata lokaci ta shiga ya kaita gida,
a harabar gidan ta iske Aarib yana k'ok'arin shiga mota,
yana hangota ya fasa ya tsaya yana jiran ta k'araso idanshi kanta yana yi mata murmushi,
"meyasa baki kira ni nazo na d'aukeki ba?
Ya tambaye ta,
kwata-kwata hankalin Sanah baya jikinta,
dan bama ta lura da wani Aarib ba,
kallanta yayi cike da mamaki kana yace " Sanah!,
amma shiru bata amsa masa ba,
tafiya kawai take yi, direct part d'in Halan ta nufa,
Aarib yabi bayanta da kallo, har yayi yunk'urin binta sai kuma ya fasa,
ya shiga mota yayi waje,
parlor ta shiga ta zauna akan sofa had'i da runtse idanta da k'arfi,
Halan na durk'ushe ciwon nak'uda ya dameta,
ji take kamar zata mutu, dakyar ta kira sunan Sanah,
amma shiru bata amsa ba,
cikin muryarta da bata fita sosai ta kuma cewa " Sanah!,
amma shiru bata amsa ba, dakyar Halan ta rarrafo tazo inda take tasa hannu ta tab'a ta,
firgigit Sanah tayi ta farka daga hang d'in da brain d'inta tayi,
ajiyar zuciya ta sauk'e da k'arfi kana ta kalli Halan dake ta faman cije baki tace " Aunty lafiya dai ko?
Dakyar Halan tace " kira yayanku,
Sanah najin muryarta tasan tana cikin mawuyacin hali,
da sauri ta mik'e jikinta ta kerrrma,
tayi kan Halan tana dialing number Ziyad,
sai da ta kusa yin cutting kana yayi picking,
bata jira taji abinda zaice ba tace " Yaya kazo gida yanzu Aunty Halan ba lafiya,
a kid'ime ya mik'e yana cewa gani nan,
wayar Khulud tayi dialing tana yin picking tace " ki zo part d'in Aunty Halan,
ina nan bata da lafiya,
da sauri Khulud ta mik'e tana cewa Mamu " Aunty Halan ba lafiya inaga haihuwa ce,
Mamu ta mik'e itama tace " Allah ya raba lafiya ki biya ki sanar da Juju,
kasancewar mutanen da akwai kara,
ita Mamu bata iya binsu hospital saboda ita ta haifi Ziyad,
dole zatayi kara,
Khulud na fad'awa Juju ta mik'e da sauri ta zari hijab sukayi part d'in Halan,
suna shiga Ziyad na shigowa bai wani ji kunyar Juju ba ya sab'i Halan yayi cikin mota da ita,
yana cewa " Khulud d'auko akwatin kayan haihuwa,
da sauri ta nufi d'akin ta d'auko,
Family Hospital d'in su ya kaita suna isa aka karb'eta aka shigar da ita labour room,
Sanah da Khulud suka yi cirko-cirko,
Juju da Ziyad na gefe.
A hankali ya mik'e ya sanya agogonsa da cut,
kana ya zira takalminsa ya zari brief case d'insa ya fita,
kasancewar yau Friday yasa Aryan nufar masallacin juma direct,
ana idar da sallah ya koma mota ya zauna,
dayake a yanayin damuna ne yana zaune cikin mota yaji an fara yayyafi,
ji yayi gaba d'aya hankalinsa yayi gida Maiduguri,
dama ya kai wajen 4 weeks baije weekend ba,
a hankali ya d'ago hannunsa ya kalli agogo yaga 1:30pm na rana,
ido ya lumshe yana jin sha'awar yin long journey a mota,
ya san kuma muddin Hilwa yasani bai barinsa ya tuk'o mota tun daga Kano har Maiduguri,
cewa zayyi dole sai yabi jirgi ko a aiko masa da Army Jet a d'auke shi,
kuma a ransa bai wani san tafiya a jirgi sosai,
musamman ma idan anan gidan Nigeria ne,
baya kuma san driver yafi san yayi tuk'i da kansa,
dan haka ya yanke shawarar tafiya kawai batare daya sanar da kowa ba,
sai dai yayi musu zuwan bazata,
a hankali yayiwa motar key ya d'auki hanyar Barno,
ya sakarwa motar wuta, dan Aryan akwai gudu da mota.
Halan takai 3hrs tana labour kana ta haifo yaronta,
mai kyau, nurse ta fito d'auke da baby Sanah tayi saurin amsar Baby tana murna,
Khulud ta kalli nurse d'in tace " ya Maman Babyn?
Nurse tayi murmushi kana tace " tana lafiya,
ai kaita d'akin hutu tana bacci,
nan da d'an wani lokaci zaku ganta,
a ranar da dare aka sallami su Halan kasancewar ta haihuwa lafiya babu wata matsala,
suka koma gida cikin murna da farin ciki.
Hanash na fita daga office d'in Sir Moli ya shiga mota,
ya kai wajen 10 minutes yana tunanin da bai san kona meye bane,
ji yayi ya k'ara jin tsanarta fiye da koyaushe a rayuwarsa,
tsoki yaja kana jiki a sanyaye yayiwa motar key yayi gida,
a parlor ya iske Mimmee zaune tana cin kwad'an Salad,
kusa da ita ya zauna, jikinsa duk ba dad'i,
kallo d'aya tayi masa tasan akwai abinda ke cikin ransa,
kallansa tayi tace " Son meke damunka?
Murmushi yayi kana yace " bakomai Mimmee,
d'an shiru tayi had'i da zuba masa ido kana tace " kamar ya bakomai?
Shiru yayi baice mata komai ba,
dan shi kansa bai san meke damunsa ba,
" ya kukayi da Khulud d'in?
Ajiyar zuciya ya sauke kana ya sanar da ita duk yadda sukayi,
bai b'oye mata komai ba,
shiru tayi na wani lokaci kana tace " kayi hak'uri,
in sha Allah I will pray for you kaji,
zan nemar maka zab'in Allah,
a sanyaye ya d'aga mata kansa,
tace " karka karaya kaji Son, ka cigaba da zuwa,
haba kai kamar ba namiji ba,
kai fa cikekken namiji ne, kayi amfani da basirarka da kuma wayonka,
ka sanya mata sanka,
"how!?
yace, " ban sani ba Mimmee ta fad'a a d'an hasale,
tana ture shi,
murmushi yayi kana yace " I promise you Mimmee I will try my best,
tayi murmushi kana tace masa good Son.
Aryan na shiga garin Maiduguri aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya,
wani mahaukacin katafaren gida,
wanda tun daga waje naga sojoji sunfi a k'irga suna kaikawo,
automatic get d'in naga ya bud'e kansa,
bayan yayi snapping number motar Sir Moli,
gaba d'aya habarar gidan babu komai sai dandazon sojoji dake kai kawo,
gidan yana da haukacin girma,
dan da gani filin da akayi gidan 300 by 300 ne,
gaba d'aya gidan zagaye yake da shukoki iri-iri,
a harabar gidan yayi parking batare daya fita ba ya kishingid'a,
Yara na gani a k'alla sun kai 7 suna wasa da ruwan sama a cikin farfajiyar gidan,
yayinda na hangi wasu yaran rakub'e cikin baranda,
da alama suma suna san yin wasan ruwa,
tsoro ne ya hana su,
d'aya daga cikin yaran dake tsaye a cikin baranda yace " Yaya kun fa san Uncle Aryan ya hana mu wasa a cikin ruwa ko?
D'ayan yace " kai zaka fad'a masa munyi wasan ruwan?
D'aya yaron yace " a'a amma kasan fa yace " idan mukayi zai gani,
kuma yace duk abinda muke yi yana ganin mu,
a duk inda yake,
d'ayan yace ba wani nan wayo yake yi mana,
kazo muyi ai babu wanda zai fad'a masa,
d'ayan yace " a'a ni banyi ni dai tsoro nake ji,
d'ayan zayyi magana Sir Moli ya bud'e mota ya fito,
gaba d'aya jikin yaran ya d'auki kerrrma da tsuma,
suka shiga rige-rigen guduwa,
wasu na take wasu, yadda kasan sunga dodo ko aljani,
wad'anda ke kan barandar suna ganin shi suka fito da gudu,
suka nufe shi suna cewa " ga Uncle Aryan ga Uncle Aryan,
oyoyo Uncle Aryan,
yaran naga ya kalla farare tass dasu,
masu kama da yaran turawa,
suna sanye da kaya na alfarma da gani kasan masu tsada ne,
murmushi yayi musu kana sunkuyo dai-dai tsayin su,
da gudu suka fad'a jikinsa, d'ayan yaron ya zagayo ta bayansa ya sak'alo wuyansa,
ya d'auki cutie Baby's d'in a hannunsa,
yayi hanyar part d'in Hilwa ya,
kasancewar yau ana suna a gidan yasan part d'in Nainah akwai mutane,
matar Yayanshi Haidar ta ce haihu,
yau ake suna,
a parlor'n Hilwa ya iske babban Yayanshi da auta Jabeer,
zaune suna hira,
Hilwa na ganinsa yayi saurin mik'ewa zaune daga kishingid'en dayake,
ya mik'e masa hannu alamar yazo,
yana dariya yadda kasan anyi masa bushara da aljanna,
annurin fuskarsa ya fad'ad'a ganin Sir Moli,
shima yana murmushi ya nufi mahaifin nasa mai tsananin so da k'aunarsa fiye da duk 'ya'yan daya haifa,
kwata-kwata Hilwa da Nainah basu iya b'oye tsananin son da suke yi Aryan a cikin yaransu,
yadda kasan shi kad'ai suka haifa a duniya,
kusa da Hilwa Aryan ya zauna yana fad'ad'a murmushinsa,
Hilwa ya shafa kansa yace " Soul shine kazo bako announcement,
dariya Sir Moli yayi yace " nasan baka bari na nayi driving ne,
ido Hilwa ya zaro yace " kai ka tuk'o motar tun daga Kano har Maiduguri?
Aryan yayi dariya yace " eh Love,
Hilwa yace " Moli (dayake haka yake kiransa wani lokacin saboda tsananin kamar dayake da shi,
shiyasa yake ganin kamar shine magajinsa),
"please ka daina wasa da rayuwarka kasan bazan iya jure rashinka ba ko?
Murmushi Haidar yayi kana yace " Hilwa ka hana mu gaisawa da d'an uwanmu ma,
Aryan yayi dariya yace " Big Bro ina wuni?
" Lafiya lau,yace yana dariya,
kana yace " ya aiki?
Sir Moli yace " aiki Alhamdulillah,
babban d'an Haidar ya shigo wanda zayyi sa'an Jabeer,
tare Jabeer da Noor suka gaida Sir Moli,
ya amsa fuska a sake,
hira sosai Hilwa da Aliyu & Aryan suka shiga,
yaran da suka tsorata sukayi cikin gida,
gidan suka shiga da suna cewa " Nainah, Ummi Uncle Aryan ya dawo,
"Uncle Moli ya zo (duk gidan suna kiransa da Moli)
Nainah tayi murmushi tace " zakin d'ana ya dawo,
dama indai na ganku kun shigo a firgice nasan shine,
manyan Yayyansa mata duk suka mik'e suna tambayar " ina yake! ina yake!?
Aunty Kubra ta d'auki wayarta tayi dialing number sa,
wayar na fara ringing Sir Moli ya kalli wayar,
kana yayi murmushi,
Hilwa da Haidar suka kai dubansu ga wayar,
Hilwa yace " hala har an kai musu labarin zuwanka,
murmushi ya kuma yi kana yayi picking wayar,
Aunty Kubrah tace " yanzu Mudah suka sanar mana ka zo,
kuma har yanzu bamu ganka ba,
"dariya yayi yace " ina part d'in Hilwa ni da Yaya,
"au ashe ko da gaske suke?
" Sannu kasha hanya bari yanzu na dawo maka ruwa,
"nagode yace had'i da yin dropping wayar,
gaba d'aya gida aka shiga munar dawowarsa saboda tsananin so da k'aunar da suke yi masa,
abinci Aunty Nina da Aunty Kubra suka shirya masa kala-kala,
Nainah, da Aunty Ayyam suka nufi part d'in Hilwa,
Jiya ta shigo da gudu a gabansa ta tsaya tana hakki tace " Uncle Aryan ina alk'awarin mu?
Jabeer yace " wallahi nima shi nake jira tun d'azu,
Sir Moli ya tsuke fuska had'i da cewa " bako gaisuwa,
balle ya hanya kinzo kin tsare kina tambayata alk'awarinki kamar wacce taban ajiya,
baki ta tab'a ta fara diddira k'afarta,
cike da shagwab'a tasan yin kuka,
tsawa ya daka mata had'i da cewa " karki soma dan ubanki,
sanin halinsa yasa jiya had'iye kukanta,
ta fad'a jikinsa tana dariya tace " I'm sorry Uncle,
ina wuni?
"Alhamdulillah, ya amsa yana d'agata sama,
dai-dai lokacin Nainah, Aunty Kubra, Aunty Nina da Aunty Ayyam,
suka shigo, gaba d'ayansu suka zauna kusa da shi,
suka zagaye shi suka sanya shi tsakiya,
Nainah ta jawo shi jikinta ta rungume tana shafa kansa tace " Life kasha hanya,
sannu Life,
Hilwa yace " kuma a mota yazo shine ma yayi driving,
Nainah ta zaro ido,
tace " Life meyasa?
Kansa ya k'ara kwantarwa a jikinta,
yace " sorry Nainah ban k'arawa,
tayi dariya tana d'ago shi tace " tashi kaci abinci,
nasan halinka da rashin san cin abinci,
mik'ewa yayi zaune yace " ai dole naci abincin gidan Nainah da Hilwa na yau dan nayi missing d'inshi sosai,
Aunty Ayyam ta jawo tray d'in abinci,
ta fara zuba masa, Aunty Nina na zuba masa drink a glass cup,
Haidar yace " uhmmm kaga d'an gatan Aunty's d'insa da Nainah,
ni dayake yau matana suna can wajen hidimar suna babu wanda ya kula dani ai,
aka barni da yunwa,
Nainah na ta hidimar da Hilwanta,
ni kun manta da ni,
ashe rabon naci da Brother na ne,
ya fad'a yana dariya, had'i da matsowa suka fara cin abincin tare,
Hilwa dayake soja ne bai san yaji,
abincin shima daban ake girka masa yace " ni ban iya ci da ku,
Jabeer da Jiya suka zauna kusa dashi a hankali suka ce " Uncle!
ya juya ya kalle su yace " meye kuma?
"Alk'awarin na mu,
kansa ya dafe had'i da cewa " oh my God,
Haidar yace " wai alk'awarin me kayi musu ne?
Aryan yace " Jiya laptop take so,
Jabeer kuma iPhone X yake so,
Hilwa yace " meyasa baku fad'a man na siya muku ba zaku damar man yaro?
Aryan yace " ai nama siyo musu suna mota,
Jiya da Jabeer suka shiga tsalle suna murna jin an siyo musu,
Jabeer yace " Yaya suna ina?
Sir Moli yace " suna mota, ungo key d'in ku d'auko ku barni na huta,
har ya basu key d'in ya tuna ana ruwan sama,
da sauri yace " yanzu ana ruwa ku bari sai an d'auke ruwan sannan,
ya fad'a yana amsar key d'in,
suna hira cikin so da k'auna,
sai da suka gama kana Sir Moli ya nufi part d'insa,
wanka yayi jikinsa duk a sanyaye,
ya rasa meke damunsa a duniya,
abinda yayiwa Sanah ya tsaya masa a ransa,
shi kunyarta ma yake ji, ji yake kamar bazai iya sake had'a ido da ita ba,
shi tsoransa d'aya ma karta d'aukeshi d'an iska tayi tunanin ko haka yake yiwa wasu matan,
wanka yayi ya shirya ya fita ya zagaya baya,
gani nayi ya b'ullo bakin swimming pool,
mai kyau da kayan k'awa,
gadon dake gaban swimming d'in ya hau ya kishingid'a,
wata 'yar kwararrawa ya danna naga wasu sojoji sun fito sanye da uniform iri d'aya a jikinsa,
batare daya d'aga kansa ba yace " a bani abu mai sanyi,
kai suka risina cikin girmamawa kana suka juya,
basu jima ba suka dawo d'auke da drinks kala-kala,
ya kai good 1hr anan kana ya mik'e ya nufi gym,
wata k'ararrawar ya danna sojoji suka fito,
a tak'aice yace " green tea,
sosai ya motsa jikinsa kana ya fita ya koma garden mai d'auke da flowers masu k'amshi da kyau,
ga tsuntsaye kala-kala suna kukan su mai dad'in sauraro,
tsayawa fad'ar had'uwar gidan Moli's b'ata lokaci ne,
saboda an kashe kud'i kamar ba gobe wajen tsara gidan,
duk wani abu na more rayuwar duniya akwai shi a cikin gidan,
abun da yafi ban mamaki shine,
duk wani ma'aikaci dake gidan soja ne,
dai-dai da masu aiki da wanki da guga duk they're sojan.
Aryan na kwance a bedroom d'insa,
Nainah ta shigo d'auke da fruits salad,
sallama tayi a k'alla takai sau uku,
amma Sir Moli baiji ba, a hankali ta ajeye tray d'in akan glass,
kana ta zauna kusa da shi,
hannun tasa ta kwantar da kansa akan cinyarta,
tana shafa kansa,
ajiyar zuciya ya sauke a hankali,
Nainah ta kira sunansa " Aryan!
a hankali ya amsa " na'am,
tace " meke damunka?
Tunda na d'ora idona akanka kasan kana cikin damuwa,
shiru yayi baice komai ba,
Nainah ta k'ara cewa " meke damunka Aryan?
"Bakomai heartbeat,
ya amsa mata,
" ya zakace bakomai bayan ga damuwar nan k'arara ta bayyana a tattare dakai,
murmushi yayi kana yace " nayi exercise da yawa na gaji ne,
murmushi tayi ta k'ara shafa kansa duk da bata yarda da abinda yace ba,
mik'ewa tayi a hankali ta d'auko fruits salad d'in ta shiga bashi a baki,
bata barshi ba sai da ya shanye tass,
dan tasan halin Aryan bai san cin abinci,
kansa nakan cinyarta tana shafa masa har yayi bacci,
a hankali ta mik'e ta d'auko Italian blanket ta rufe shi,
tayi masa kiss a kumatu kana ta fita,
sosai Moli's Family ke mugun so da tsananin k'aunar Aryan kamar ransu,
kowa yana nan-nan dashi kamar k'aramin yaron goye.
Washe gari da safe wajen k'arfe 11:30am na safe,
ya fito ya nufi part d'in Nainah,
dayake yasan 'yan taran suna duk sun tafi,
yasan babu sauran bare sai Moli's Family,
har ya kusa shiga part d'in ya tuna da alk'awarin su Jabeer,
komawa yayi ya d'auko sabuwar laptop da wayar duk a cikin kwalayen su,
kana ya nufi part d'in,
ganin ba kowa a parlor yasa shi nufar bedroom d'inta,
a can ya iske ta zaune tsakiyar Aunty's d'insa,
ana ta hira, Aunty Nina da Aunty Kubra na kan gado,
yayinda sauran ke zaune akan carpet,
kan gadon shima ya zauna had'i da tankwashe k'afarsa,
kana ya shiga gaida su,
Nainah ta k'urawa Aryan ido tana karantar yanayinsa batare datace komai ba,
Jabeer da Jiya suka zuba masa ido,
suna tsoron sake tambayarsa,
lura da irin kallan da su yi masa ne yasa shi mik'a musu,
cikin murna suka amsa suna da tsalle,
had'i dayi masa kiss a kumatunsa,
kana sukayi waje da gudu,
Aunty Ayyam tace " brother bari na kawu maka breakfast d'inka nan,
dariya yayi kana yace " thank you sister,
kunun gyad'a da zazzafan k'osai dayaji hanta da kwai ta kawo mishi,
" woww gaskiya nagode sosai Nainah,
ya fad'a yana kallan Nainah,
Aunty Nina tace " oh! mai yin wahalar daban wanda ake yiwa godiya daban,
yayi dariya yace " sorry Aunty, nagode sosai kema,
hira suka shiga yi sosai,
dan Moli's Family suna matuk'ar so da k'aunar junnansu,
gasu da had'in kai sosai kamar tsintsiya,
fuska ya d'an b'ata kana yace " wai Aunty me kuke har yanzu baku koma gidajenku ba?
Aunty Ayyam tace " kai kaga matsalarka ko,
kai sai ka juya fuska kamar kai ne babba akan mu,
fuska ya k'ara tsukewa yace " kowacce ta tashi ta shirya ta koma gidan mijinta,
miye dan suna kawai zaku zo ku zaune har ku sake kwana,
maza ku shirya yanzu ku tafi,
dayake Sir Moli akwai san girma idan yana wani abun sai ka rantse shine babba a gidan,
kuma dukda yana k'aramin su dukkan su suna jin shayinsa,
dan basa tab'a gigin kawo mishi rai,
shiyasa Hilwa yake ganin Aryan shine magajinsa,
Nainah tace " gaskiya kam nima tun jiya nake cewa su shirya su tafi,
suka k'i tafiya,
kai yanzu dayake kai ne daka tasasu a gaba ai dolansu su tafi,
Hilwa ma bai san suna nan sun k'ara kwana ba,
Sir Moli bai bar part d'in Nainah ba,
sai da ya tabbatar kowacce ta kwashi yaranta ta koma gidanta,
da daddare Sir Moli zaune kusa Hilwa a part d'insa,
Hilwa nayi fad'a akan rayuwa,
kan yaji tsoron Allah ya rik'e gaskiya da amana aduk inda yake,
Sir Moli yace " Hilwa gobe zan koma,
Hilwa yace " au gobe fa Sunday ko?
" Ni nama manta,
amma bazaka koma a mota ba,
ba zaka koma gobe ba, ka bari sai Monday,
sai jet ya kai ka da asuba,
ya amsa da to.
ranar Monday ana yin Sallar Asuba jet ya d'auki Moli yayi kano,
gidan yayi shiru kowa yana cike da kewarshi.
Ranar suna yaron Halan yaci sunan Didi Rawan, suna kiranahi da Khair,
yau tunda Khulud ta tashi ta tashi da matsanancin ciwon mara kamar zata mutu,
dan ko kanta bata iya d'agawa,
gashi ta kasa tashi balle taje tayi wanka,
Sanah kuma tun 7:00am ta tafi school kasancewar tana da lectures 8:00am,
tana kwance kamar zata mutu tayi shiru,
Hanash yau ma ya shirya cikin shiga ta alfarma,
yayi masifar kyau ya nufi gidan su Khulud,
yauma mai gadi yaje yayi sallama da ita,
sai lokacin Mamu ta shiga d'akin dubota,
dan tunda Sanah ta fara school,
ita kuma ta koma zaman bedroom,
shiyasa yau koda Mamu taga bata fito ba batayi tunanin wani abu ba,
ganin Khulud kwance tana ta murk'ususu,
yasa Mamu k'arasawa da sauri,
" ya Salam, Mamu ta fad'a tana d'agota,
" meke damunki?
Mamu ta tambaye ta,
dakyar tace " ciki na ne,
tana fad'ar haka Mamu ta gane period zatayi,
cikin tausayawa Mamu tace " dama yana yi maki ne?
Dayake su Mamu basu san Khulud bata fara ba,
shiru Khulud tayi bata bawa Mamu amsa ba,
kwantar da ita Mamu tayi ta mik'e ta shiga bathroom d'insu,
ta had'a mata ruwan wanka,
kana ta fito ta umarce data shiga dakyar Khulud ta mik'e ta shiga,
kafin ta fito Mamu ta fiddo mata kaya harda pad, pant & bra,
kana ta fita, cikin sanyi Khulud ta fito,
kayan da Mamu ta fiddo mata tabi da kallo,
kayan ta saka ta shirya sosai ,
ta d'auke pad d'in ta maidata cikin wardrobe,
bata jima da shiryawa ba, Mamu ta shigo d'auke da tray na abinci,
tea ta fara bata tasha dakyar,
Mamu ta matsa mata ta shanye tea d'in tsaf,
kana ta bata chips & miyar hanta,
ta d'anci kad'an kana Mamu ta bata magani tasha,
sosai Khulud taji ciwon ya lafa mata,
Mamu na zaune kusa da Khulud taji sallamar get man,
kai Mamu ta dafe tace " tab na manta tun d'azu kikayi bak'o fa,
Khulud ta d'an zumb'uro baki tace " Mamu ban jin dad'i ban iya fita,
Mamu tace " mutumin yazo tun d'azu yakai wajen awa d'aya da rab'i yana zaman jiranki amma ki k'i fita?
"Mamu please ki aika ace masa ban jin dad'i,
ta fad'a a shagwab'e,
Mamu tace " ki fita da kanki kije kiyi masa bayani,
zata kuma yin magana Mamu tace " no argument,
jiki a sanyaye Khulud ta fita,
iskewa tayi har an kai shi set room,
koda ta shiga taga kayan drinks & snacks jere a gabansa,
tana shigowa ya mik'e da sauri had'i da zubawa fuskarta ido,
a hankali ta zauna tana cije lips,
cikin sanyin murya tace " ina wuni?
" Alhamdulillah ya bata amsa yana kallanta,
ganin yadda take cije lips yasa shi cewa " meke damunki?
Muryarta na rawa tace " ciki na ke ciwo,
" innalillahi wa'inna ilaihirrajji'un yace,
cikin tashin hankali yace " tun yaushe?
" Tun safe ta bashi amsa,
cike da tension ya shiga jera mata sannu,
yadda kasan zayyi kuka yake magana muryarsa na rawa,
ido kawai Khulud ta zuba masa ganin yadda lokaci d'aya yanayinsa ya canja,
duk ya shiga cikin tashin hankali ya rud'e,
sosai Hanash yayi mugun bata mamaki,
yadda ya nuna damuwa k'arara a fuskarsa,
murmushi Khulud tayi tace "karka damu fa,
naji sauk'i ai,
kamar zayyi kuka yace " kamar ya karna damu?
Bayan kin san dole na damu, kin san abinda rai ke so ne ai,
shiru tayi bata kuma yin magana ba,
ganin haka yasa shi cewa " tashi ki ciki,
gobe na dawo naji ya jikin,
murmushi tayi kana tace" nagode,
yace " bakomai,
ya mik'e zai fita idansa ya sauka akan wayarta data manta,
da sauri ya koma ya zauna ya d'auki wayar,
to his lucky wayar babu pin,
pic d'in Sanah ya gani a screen sever,
in capital letter an saka my Happiness,
theme d'in wayar ma na pic d'in Sanah ne,
murmushin bak'in ciki yayi yana jin matsanancin kishin Sanah na shigarsa,
contacts d'inta ya shiga, my heartbeat yaga tayi saving number Sanah,
tsaki yayi kana ya saka number sa a wayarta yayi saving da MY LIFE,
kana yayi dialing dan ya samu number ta,
kiran ya shiga yayi saving number ta da My love,
kana ya bawa mai gadin wayar ya kai mata,
tun a motar ya kira ta,
tana zaune taga My life na kira,
cikin mamaki ta d'auki wayar tana mamakin waye,
har kiran tsinke aka kuma kira,
tana yin picking taji shine,
a ranar Hanash ya kira Khulud yaji ya jikinta yakai 10×,
Khulud na waya da Hanash taji k'arar parking,
da sauri cikin murna tace masa " my Sanah ta dawo,
bata jira amsarsa ba kashe wayar.
A ranar da daddare matsanancin ciwon mara ya hana Khulud sakat,
amma gudu karta tashi Sanah daga bacci yasa ta daurewa dan tasan da sassafe take fita,
sai wajen 3:00am period d'in Khulud yazo kana ciwon ya lafa mata,
sosai Hanash ya nunawa Khulud so da kulawa a rashin lafiyarta,
tun tana basar dashi harta fara sakin jiki dashi suna hira sosai,
sai dai duk rabin hirar labarin Sanah take bashi,
bata da wata magana ko labari daya wuce na Sanah,
bata san duk lokacin data ambaci sunan Sanah a kunnen Hanash daurewa kawai yake yi ba,
amma ji yake kamar tana watsa mishi wuta,
lokacin da Khulud ta sanar da Sanah da Halan ta fara period sosai sukayi murna da farin ciki,
satinta d'aya tana period tayi wanka,
Hanash ko kullum sai ya zo ba fashi,
dan ya dage sai ya sakawa Khulud matsananciyar soyayyar shi a zuciyarta,
kasancewar babu Sanah babu mai d'ebewa Khulud kewa,
yasata fara kula Hanash,
tun tana shashshare har dai ta fara kula shi,
sai dai ko zancen yazo hirar dai d'aya ce ta Sanarta,
daga my Sanah kaza sai my Sanah kaza,
sosai Hanash ya rink'a d'ebewa Khulud kewa, yana bala'in kula da ita sosai,
saboda yadda ya nuna damuwa da kulawa a gareta,
musamman ma da bata da lafiya,
ko kuma da tace abu yake yi babu musu,
duk abinda zayyi ya faranta mata shi yake yi,
yana kuma gudun duk abinda zai b'ata mata rai,
sosai yake nuna mata so da soyayyarta a zahiri,
sannu a hankali soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Hanash da Khulud,
suna yiwa junansu mugun so,
24hrs suna tare a waya, ko chart,
kasancewar Sanah da sassafe take fita school bata dawowa sai gaf da magrib,
idan kuma ta dawo bata da lokaci sosai datayi wanka taci abinci tayi sallah sai bacci ko karatu,
yasa kwata-kwata bata lura da abinda ke faruwa tsakanin Hanash da Khulud ba,
bata san komai ba,
ita kuma Khulud ba b'oye mata tayi ba,
dan bata samun lokaci ne yasa bata sanarda ita abinda ke faruwa ba,
sosai tsantsar soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Hanash da Khulud,
fiye da tunanin mai karatu,
ta yadda babu abinda d'aya zayyi batare da d'ayan sa ni ba,
kullum kuma ko yaushe suna manne da juna a waya,
sunyi masifar bawa junansu mahimanci fiye da tunani.
Tun bayan faruwar wannan al'amarin babu wanda ya k'ara ganin wani tsakanin Sir Moli da Sanah,
sosai suka shiga wasan b'uya,
a gajiye lik'is Sanah ta koma gida yau ma,
Khulud na waya da Hanash taji shigowar Sanah tayi saurin mik'ewa,
had'i dayin cilli da wayar,
Sanah ta zube akan sofa,
had'i da cewa " wassh Allah na gaji da yawa,
cikin tausayawa Khulud tace sannu My Sanah,
Hanash dake ta faman hello hello,
jin shiru, ya jiyo muryar Sanah,
tsaki yayi had'e da kashe wayar,
Khulud ta rik'e hannun Sanah tace " muje kiyi wanka,
ba musu Sanah tabi Khulud zaunar da Sanah Khulud tayi a bakin bed,
kana ta shiga bathroom ta had'a mata ruwanka,
ta fito tace " my Sanah shiga kiyi wankan,
Sanah ta mik'e ta cire kayan jikinta ta d'aura towel,
ta shiga tayi wankan ta d'auro alwala,
kafin ta fito Khulud ta fiddo mata kaya marasa nauyi da pant ta aje mata akan bed,
Sanah ta fito ta zauna gaban mirror tana shafa lotion,
cikin matsananciyar gajiya,
Khulud tayi dariya tace " ko inzo na shafa maki man?
Ta fad'a cikin tsokana,
Sanah tayi dariya tace " dako kin taimaka da yawa,
mai kawai Sanah ta shafa ta zura doguwar rigar bacci,
ta saka pant kawai bata saka bra ba dan bata bacci da bra,
perfume's ta fesa,
kana ta fara k'ok'arin hawa bed,
Khulud ta kalle ta tace " abinci fa?
Naga kina k'ok'arin yin bacci,
Sanah tace " kai bar abincin nan kawai,
Khulud ta turo baki kana tace " Allah sai kinci kefa nake jira ki damo mu ci,
Sanah tayi murmushi tace " sorry jeki d'auko mana muci,
Khulud ta mik'e ta fita tana cewa " yauwa ko ke fa,
wayar Khulud dake gefe ta ringing,
Sanah bata kula wayar ba harta katse,
aka sake kira, nan ma bata yi picking ba,
sai da kira na 5 ya shigo kana ta mik'a hannunta daga inda take kwance ta lalubo wayar,
sunan ta kalla taga anyi saving da My Life,
cikin mamaki ta tace " my life kuma, waye kuma my life?
Ta tambayi kanta,
jin wayar na neman katsewa yasa ta saurin yin picking,
"hello my happiness ina ta kira shine ba'ayi picking ba,
yayi maganar zazzak'ar muryarsa,
gaban Sanah yayi muguwar fad'uwa,
a hankali ta zame wayar daga kunnenta ta k'ara kallan screen d'in,
taga tabbas ba wrong number bace,
tunda gashi anyi saving, cikin mamaki ta k'ara mayar da wayar kunnenta,
muryarta na rawa tace " bata nan,
jin muryarta ya sashi sakin tsoki had'i da kashe wayar,
wayar Sanah ta k'urawa ido cike da mamaki,
Khulud ta shigo d'auke da tray d'in abinci,
ganin yadda Sanah ta k'urawa wayar ido tanaR juyata,
ya sata zama kusa da ita,
" lafiya?
Khulud tace, cikin sanyin jiki Sanah tace " waye my life?
Murmushi Khulud tayi tace " he's my love,
"your love?
Sanah ta maimata cikin mamaki,
Khulud tace " eh!, ban baki labarinsa bane saboda baki zama,
da kin dawo kike kwanciya bacci,
Sanah tace " yanzu dama Khulud har akwai wani abu da zamu b'oyewa junanmu, har akwai abunda zamuyi batare da sanin juna ba?
Khulud tace " My Sanah baki zama fa,
Sanah tace " saboda bana zama shine ya hana ki fad'a min,
wannan ai ba dalili bane, tunda ba mutuwa nayi ba, ba kuma garin na bari ba,
cikin sanyin murya Khulud tace " I'm so sorry, ban san na hana ki bacci ne,
shiyasa kika ga ban sanar dake ba,
Sanah " ok yanzu ai ina jinki,
Khulud ta mik'e tsaye had'i da d'aga murya cikin farin ciki tace " I love him,
I really love him so much,
I love him more & more most my Sanah,
ke kad'ai nafi so a duniya sama da Hanash,
ganin yadda Khulud ke farin ciki yasa Sanah yin murmushi tace " who is he?
Khulud tace " Hanash Waseef,
Sanah tayi rolling sexy eye d'inta tace " taya za'ayi na sanshi,
description d'insa gaki man yadda zan gane,
Khulud tace " ai kin san shi ma,
Sanah tace " na sanshi, a ina?
Khulud tace " wannan wanda kukayi fad'a,
Sanah tace " wai wa?
Khulud tace " wanda ya watsa maki ruwan kwata har sau biyu,
ke kuma kika mare shi,
a firgice ta mik'e tana kallan Khulud had'i da ja baya..............
_Banyi editing ba, so nasan akwai typing errors_
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣3⃣
Tace " wannan kike nufi?
Khulud tace " eh shi My Sanah,
Allah ina sanshi dayawa,
Sanah tayi shiru tana karantar yanayin Khulud,
taga yadda take cikin farin ciki,
tana murna da tsalle, take fad'in she love him so much,
Sanah tayi shiru tana tunanin yadda akayi yasan gidansu,
da yadda akayi har soyayyar su da Khulud tayi zurfi haka batare data sani ba,
Khulud ta fad'a jikin Sanah tace " nasan kema zaki soshi saboda nima ina sanshi,
shima yana sanki sosai,
ya manta da duk abunda ya faru tsananin ku a baya,
kullum bamu da wata hira sai taki,
ko ban yi mishi maganarki ba,
shi sai yayi man taki,
murmushin yak'e Sanah tayi, cikin sanyin jiki tace " wow! My Khulud gaskiya nayi murna,
da farin ciki da jin wannan labarin,
kice kun dad'e kuna shan love?
Ta fad'a tana kallanta,
Khulud tace " ba wani dad'ewa mukayi sosai ba,
da bani da lafiya ne ya nuna kulawarsa sosai akaina,
kuma shine yake d'ebe man kewarki,
taja hannun Sanah suka zauna a bakin gado,
kana Khulud ta shiga bata labarin mafarin soyayyarta da Hanash tun daga farko har k'arshe,
" kai amma abin ya burge ni,
Sanah ta fad'a tana b'oye damuwarta,
saboda yadda ta hango soyayyar shi a cikin kwayar idon Khulud,
tasan kuma muddin ta nunawa Khulud bata sanshi,
bata kuma kula shi, sai dai idan tayi mata haka bata yi mata adalci ba,
musamman ma data fahimci shima yana bala'in san Khulud d'in,
kuma yana kula da ita sosai,
dan haka bazata tab'a b'ata musu farin cikin su saboda wani banzan dalilinta ba,
ta kuma yiwa kanta alk'awarin daga yau har abada bazata k'ara k'insa ba,
saboda soyayyar da yake yiwa Uludinta,
da kuma yadda itama Khulud take sanshi,
ta kuma d'aukarwa ranta komai zayyi mata,
bazata tab'a ramawa ba, zaici arzikin soyayyar Khulud,
zata kuma ta danne komai a ranta,
ta kawar da komai, ta rink'a kula shi tana bashi girma da mutuncinsa,
saboda Khulud,
kuma koba komai, ai yana d'ebewa Khulud kewa,
yana kuma sanyata cikin farin ciki da walwala,
jin shiru yasa Khulud tab'a tace " My Sanah lafiya naji kinyi shiru?
Sanah tayi saurin k'ak'aro murmushi tana girgiza kanta tace " bakomai My Ulud,
kawai ina jin dad'i da farin ciki ne,
Khulud ta kalle ta k'ura mata ido na wani lokaci kana cikin sanyin murya,
tace " My Sanah ko baki san alak'a ta da Hanash ne?
Sanah ta zaro idonta,
tace " kai injiwa?
Khulud tace " My Sanah nafi kowa saninki,
nafi kowa sanin wacece ke,
nafi kowa halayenki da d'abi'unki,
dan girman Allah ki sanar dani gaskiyar abunda ke ranki gami da Hanash please,
Sanah ta kuma yin dariya tana rik'o hannun Khulud cikin nata,
tace " my Ulud ki kwantar da hankali,
babu abinda ke raina, kawai dai ina mamaki ne,
"mamakin me?
Khulud ta tambaye ta idanta na kanta,
Sanah tace " yadda akayi my Uludina ta fad'a tarkon love,
Khulud tayi dariya tace " kai my Sanah,
Allah nima ban san yadda akayi na fara ba,
haka nan kawai na ji ni.....
d'an shiru tayi,
Sanah tace " kika ji me?
Khulud ta turo bakinta,
tace " nima ban sani ba,
Sanah tace " a'a ina za'ayi haka ai dolanki ki fad'a man abinda kika ji,
Khulud ta lura akwai abinda Sanah ke k'ok'arin b'oyewa dan haka cikin sanyin jiki tace " my Sanah!
Sanah ta kalle ta,
taga Khulud ta k'ura mata ido,
rolling idanta Sanah tayi kana tace " me?
Khulud tace " please kin ban damar cigaba da kula da Hanash,
Sanah ta d'an yamutsa fuska tace " sai yanzu za'a nemi izinina bayan aikin gama ya gama,
Khulud tayi dariya tace " ni dai please ni yes or no?
Sanah tace " hmmmm sai bayan kin gama yanke hukuncin fad'awa a soyayyar sa?
Khulud tace " my Sanah ba mutum ne ke yanke hukuncin fad'awa a soyayya ba,
ita soyayyar ce take lokacin faruwar hakan,
shiru Sanah tayi tana san tuna inda ta tab'a jin irin wad'annan kalaman,
Khulud tace " nasan ba lalle ne yanzu ki fahimci hakan ba,
amma akwai lokacin da ke da kanki zaki fad'awa wasu,
Sanah ta shafa fuskar Khulud tace " karki damu kinji My Ulud,
nayi farin ciki sosai da jin wannan labarin,
Allah ya sanya alkhairi, Ubangiji yabar ku tare,
ya kuma albarci soyayyarku,
ya baku zuria ta gari,
Khulud ta amsa da Amin, idanta yana kan Sanah,
Khulud tace " Yayan su Zohal & Wajnah Waseef ne,
Sabah tace " kai haba?
Khulud tace " Allah da gaske uwarsu d'aya ubansu d'aya su uku ne kawai a wajen iyayensu,
Sanah tayi dariya kana tace " kin san me?
Khulud tayi saurin cewa " a'a,
Sanah tace " naga Sir Moli fa,
cikin zumud'i Khulud tace " kai a ina?
Sanah tace " a makarantar mu,
lecturer ne a department d'in mu,
Khulud tace " kuma ya gane ki?
Sanah tace " ya gane ni ko na gane shi?
" D'an rainin hankali,
Khulud tace " zaki fara ko?
Sanah tayi dariya kana ta shiga bawa Khulud labarin had'uwarta da Sir Moli tun daga farko har k'arshe,
amma ta kasa sanar da ita abinda ya shiga tsakaninsu,
karo na farko a rayuwarta data b'oyewa Khulud wani abu,
haka nan kawai taji bata san sanar da ita,
Khulud tayi dariya kana tace " kai wallahi drmarku na birgeni,
ashe an d'ora daga inda aka tsaya,
dama ina nan dana sha kallo wallahi,
Sanah ta tab'e baki, tace " rabu da rainin sense shi so yake ni na fara nuna na sanshi ko na gane shi,
yadda zai samu damar wulak'anta ni,
ya farfad'a man bak'ak'en maganganu san ranshi,
cikin dariya Khulud tace " durk'usawa wada ai ba gajiyawa bane,
my Sanah in kin nuna kin sanshi sai me,
wani abun ne zai ragu daga jikinki?
Sanah ta nuna kanta tana tab'e bakinta,
had'i da yin rolling sexy eye d'inta,
tace " ni na zan nuna na sanshi God forbid,
ta fad'a tana nuna kanta,
Khulud tayi dariya kana tace " Sir Moli witch kawai,
Sanah ta zaro ido had'i da mik'ewa tsaye tace " what! ni?
Khulud tace " eh mana in ba ke ba da wa!?
Sanah ta d'auki pillow tana bin Khulud,
Khulud tayi baya tana dariya tace " Sir Moli witch,
Sanah ta bita da gudu tana jefa mata pillows,
Khulud ta hau kan bed tana yiwa Sanah kwalo, had'i da tare pillows d'in,
wayar Khulud ta soma ringing,
Sanah tayi saurin d'aukar wayar tace " sake fad'a inba tsoro ba,
Allah yanzu na taro miki March,
Khulud ta rik'e kunnuwanta had'i da d'an girgiza kanta tace " I'm so sorry,
ban k'arawa, Sanah tayi dariya kana ta mik'e mata wayar,
da sauri ta amshi wayar had'i dayin picking,
" hello my life, ya kike?
"Lafiya lau, Alhamdulillah, an u,
yace " ina lafiya kamar yadda kike,
kin ci abinci?
"Eh, kai fa, murmushi yayi mai sauti har dimples d'insa suka lotsa kana yace " yanzu Mimmee ta gama bani,
Khulud tace " dear wai meyasa baka san cin abinci?
Dariya yayi yace " ni ma ban sani ba,
Mimmee dai tace haka nake tun ina Baby,
idan kika zo sai ki wakilci Mimmee ki rink'a baki ko?
Ya fad'a cikin shagwab'a,
fuskarta ta rufe kamar yana ganinta,
tace " hmmmm,
yace " Papu yace nayi miki magana kan zasu zo wajen Abbu,
tun last week na sanar dake amma kink'i cewa komai,
murmushi tayi kana tace " dama jira nake ayi approving d'in mu kuma anyi,
cike da mamaki yace " approving!?
Tace " yes!
Yace " waye zayyi approving d'in?
Tace " My Sanah mana,
ji yayi kamar ta watsa masa wuta,
amma sai ya kanne yace " to tayi yanzu?
Tace " eh tayi, dama ai na fad'a maka bata tab'a kin amincewa da abinda nake so,
Allah baka ga yadda taji dad'i tayi murna da farin ciki ba,
" shegiya karuwa 'yar iska ba,
ai dole ta yarda saboda tana tsoran kar na tuna mata asirin iskancin da take yi,
ya fad'a cikin ransa,
a fili kuma yace " masha Allah,
kana yace " yanzu if she's saying no ,
shikenan our true love has been cancel,
da sauri tace " wallahi capital latter YES!,
dan ban ko k'ara kallan inda kake balle nayi maka magana,
so put it your mind albarkacin My Sanah kaci,
ido Hanash ya runtse da k'arfi yana jin kamar zai mutu,
yana jin yadda zuciyarsa ke k'una had'i da tafasa,
in banda yana mugun san Khulud da tuni ya rabu da ita,
amma rabuwa da ita dai-dai yake da fitar numfashinsa,
daurewa yayi yace " ok any way,
yanzu yaushe su Papu zasu zo?
" Bari na nemi izini wajen my Sanah,
zayyi magana yaji ta kashe wayar,
wayar kawai Hanash yabi da kallo yana sak'e-sak'e da tunani a ransa,
Khulud ta juya ta kalli Sanah tace " my Sanah!
"na'am Sanah ta amsa,
Khulud tace " wai iyayen su Hanash ne zasu zo,
Sanah tayi saurin mik'ewa zaune tace " kai haba, yaushe?
" Ai shine nace bari na tambaye ki,
Sanah tace " ok bari naje na sanar da Mamu,
in yaso sai ta sanarwa da Abbu ko?
Khulud tace " ni dai a'a kunya nake ji,
Sanah tace " to mu sanar da Aunty Halan inyaso saita sanarwa da Yaya Ziyad shi sai ya sanarwa Abbu da Didi,
Khulud tace " ni dai kunya nake ji,
Sanah tace " to za'ayi idan ba'a sanar da su ba?
"Ko haka nan kawai zasu ga mutane da ka?
Khulud zatayi magana Sanah ta mik'e,
Khulud ma tayi saurin mik'ewa ,
Sanah zata fita Khulud ta rik'o tace " no,
Sanah ta fisge ta fita da gudu,
Khulud tayi saurin bin bayan ta,
da gudu suka yi parlor,
Abbu da Mamu na zaune suka gansu da gudu,
Abbu yace " lafiya!?
Sanah zatayi magana Khulud tayi saurin rufe mata baki,
tana yak'e tace " bakomai Abbu,
Sanah na k'ok'arin kwace bakinta ta d'aga hannunta alamar k'arya take,
Mamu tace " wai ku meye haka?
"Kun girma amma baku san kun girma ba,
kuna abu irin na yaran goye,
Sanah ta kwace bakinta tana hak'i,
Khulud na k'ok'arin sake rufe mata bakin tace " iyayen Hanash zasu zasu zo,
Khulud na jin Sanah ta fad'a ta saka kuka,
Abbu yace " to ikon Allah meye abin kuka kuma?
"Zonan kinji d'iyata ya fad'a yana mik'awa Khulud hunnu,,
ba musu Khulud ta nufi wajen Abbu ta zauna kusa da shi,
cikin rashin fahimta Mamu tace " waye Hanash?
Sanah tace " saurayin Khulud ne,
shine iyayensa suka ce suna san zuwa,
shine tace wai kar a gaya maku kunya take ji,
da gudu Khulud tayi bedroom d'insu cike da kunya,
cikin mamaki Abbu ya kalli Mamu yace " dama kin san da maganar ne?
Mamu tace " eh!
Abbu ya kalli Sanah yana murmushin jin dad'i cikin murna yace " zanyi magana da Didi,
sai na sanar daku ranar da zasu zo,
Sanah tace " tom, kana ta nufi bedroom,
ta iske Khulud, Khulud na ganinta mik'e tana dukan Sanah cikin wasa,
Sanah tayi dariya tace " wannan duk murnar ce, uhnnn amaryar Hanash,
Khulud ta kuma kaiwa Sanah duka,
wayar Khulud ta soma ringing,
Khulud tayi banza da wayar cike da murna Sanah tayi picking,
tace " hello!
jin muryarta yasa shi jin zafi har cikin ransa,
" hello ta kuma cewa,
sai da ya runtse idonsa kana yace " ina mai wayar?
Sanah bata d'auki wani abu ba,
tace " gata nan kusa dani,
a dak'ile yace " bata,
jikin Sanah a sanyaye ta mik'awa Khulud wayar tana yak'e,
cikin ranta kuma tana mamakinsa,
Khulud ta amshi wayar kana tayi masa bayanin komai,
guntun murmushi yayi kana yace " kiyi mata godiya,
Khulud tace " gata kayi mata da kanka,
yace " no ba sai kin bani ba,
kiyi mata kawai,
nima sallah zanyi,
shiru Khulud tayi batare data ce komai ba,
yace " I love you, good night,
bata bashi amsa ba,
ta kashe wayar,
kana ta tura masa text,
_Ka sani ban tab'a auren mutumin da baya san my Sanah baya kuma shiri da ita duk son danake yi masa,_
_wallahi koda sanka zai zama ajalina muddin baka san my Sànàh ko babu good understanding tsakaninku zan iya hak'ura da kai,_
_na barka har abada na kuma manta da kai da rayuwarka_
_so gwara ma ka sani ka kuma lura,_
_muddin kana so na kana kuma san aure na ka kasance da ni har rai da mutuwa to ka fara koyar yadda zakayi kà so Sanah ka kuma yi mu'amula da ita,_
_dan ko a ranar d'aurin auren mu Sanah ta nuna bata amince da kai bà wallahi sai na fasa,_
Murmushin takaci Hanash yayi bayan ya gama karanta text d'in,
yana jin inama zai iya rabuwa da Khulud da ya rabu da ita ya hutawa ransa da rayuwarsa,
sai dai bai iya rabuwa da ita a yadda yake jin mugun santa har cikin kwakwalwarshi,
text ya tura mata shima,
_I'm so sorry if I hurt you_
_ba da wata manufa nayi hakan ba, amma kiyi hak'uri please,_
_gobe zanzo na baku hak'uri ke da our Sanah, I love you so much_
Murmushi tayi kana tayi cilli da wayar ta kwanta.
Washe gari da wuri Sanah ta shirya kasancewar suna da lectures da Sir Moli 8:30am na safe,
tun da wannan abun ya faru Sanah ta shiga taka tsantsan dashi,
data ga suna da lectures dashi take sauri ta shiga class ta samu can baya lungu ta zauna,
a hankali Sanah ta shiga cikin class d'in tana takawa a hankali,
ta samu wajen a baya ta zauna tana jiran lokaci yayi ya shigo,
kan motarsa ya danno cikin makarantar,
a parking space yayi parking,
ya kai wajen 15 minutes kana ya zuro k'afarsa d'aya waje,
kai da kanin k'afar sanye cikin takalmin Nike,
kasan mamallakin k'afar yana cin duniyarsa da tsinke،
a hankali ya zuro d'aya k'afar kana ya fito gaba d'ayan sa,
sanye yake cikin arnan Man material,
mai laushi, color blue black,
takalmi, agogo da hularsa black color,
cikin nutsuwa ya d'auki laptop & brief case d'insa,
ya fara takawa a hankali ya nufi class d'insu.
Sir Moli na gaf da shigà yà fara jiyo hirar su rose,
dan haka ya d'an tsaya kad'an,
Sanah na zaune a baya taji wasu Christians suna hira,
d'ayar mai suna Rose tace " ni fa ina mamakin Muslim,
d'ayar tace " mamakin me?
Rose tace " yadda suke bautawa wanda basu sani ba,
ba kuma su tab'a ganinsa ba,
d'ayar ta tab'e baki tace " nima abin nan yana bani mamaki fa,
yanzu da zaka tambaya su ina Allah su yake shiru zasuyi suyi tsuru-tsuru,
a zafafe Sanah ta mik'e ta nufi inda suke zaune,
tana zuwa bata jira wata-wata ba ta kifawa kowacce mari bibbiyu,
Sir Moli dake tsaye jikin window yayi saurin kallan Sanah cike da mamakin rashin tsoranta,
dan dukkannin su gidiga-gidiga ne,
masu k'irar k'atti babu wacce bazata iya sab'ar Sanah ta zagaye garin Kano kaf da ita ba,
Rose da d'ayar suka mik'e da sauri cike da mamaki,
suna kallan Sanah Rose dafe da kuncinta tace " kika mare mu?
Sanah ta zaro idanta kamar gaske tace " ni yaushe na mare ku?
Sir Moli ya gyara tsaiwarsa yana kallan ikon Allah,
Rose tace " yanzu fa kika mare mu,
Sanah tace " idan har da gaske kuke yi na mare ku,
ku nuna min marin,
Rose ta nuna kuncinta tace " gashi,
Sanah ta kalli kuncin had'i da sanya hannunta ta rik'e fuskokinsu tana duddubawa kamar gaske,
tace " ni fa banga komai ba,
gaba d'aya ajin akayi tsit kowa ya maida hankalinsa kansu,
Rose tace " kamar ya baki ga komai ba?
Sanah tace " eh banga marin ba,
amma ke tunda kina ganinsa kina iya nuna min shi na ganshi,
d'ayar tace " ke karki raina mana wàyo,
Sanah ta sanya hannunta ta rik'e hab'arta had'i yin sautin da bakinta,
tana kallansu cike da rainin hankali,
" in banda rainin hankali dama ana ganin mari ne?
D'ayar ta fad'a,
Sanah tayi murmushi kana tace " au dama ba'a ganin mari?
Rose tace " tayaya za'a ga mari?
Sanah tace " to yaya kika san na mare ki?
Rose tace " naji shi ne,
Sanah tace " yauwa anzo wajen,
kin tabbata ba'a ganin mari,
amma ana jinsa,
dana mareki baki ganshi ba amma kinji shi har cikin kwakwalwarki da zuciyarki,
to kamar yadda bakiga marin nan ba,
amma kika yarda akwai shi, zuciyarki da kwakwalwarki suka amince suka kuma gaskata shi gaskiya ne,
haka Allah Ubangijin mu mai komai da kowa yake,
shi dayake shine Ubangijin gaskiya shiyasa ba'a ganinsa,
amma zuciya, rai ,ruhi , kwakwalwa, duk suka yarda suka kuma amince akwai shi,
zati da k'udurar Ubangijinmu tafi k'arfin ido ya ganshi,
yafi k'arfin zuciya ta siffatanshi,
yafi k'arfin rai ya misaltashi,
kana ta kalli jakarta tace " yanzu Rose idan kika shigo ajin nan kika ga ba kowa sai wannan jakar kad'ai,
kin san akwai mai ita,
akwai kuma wanda yake mallakinsa ce,
sannan kin tabbatar akwai wanda ya k'era ta ko?
Rose tace " haka ne, duk wani da kika gani akwai meshi,
Sanah tace " good, to kamar haka be akan duniya,
Rose ko kwano kika gani ajiye kin san akwai meshi,
balle kuma duniya da abinta ke cikinta,
ke kanki kin san akwai mai ita,
saboda babu abinda yake halittar kansa
komai kika gani a duniya yinsa akayi,
idan kika kalli shuke-shuke da ruwa, jini da mutum kad'ai ya isa ya tabbatar miki akwai Ubangijin gaskiya,
so please ku bar irin wad'annan maganganun a cikin al'umma saboda hakan yana iya haifar da fitina,
ayi ta kashe rayukan da basu ji ba,
basu gani ba,
ba su Rose kad'ai ba, duk wanda ke wajen sai da jikinsa da zuciyarsa tayi sanyi,
Sanah ta koma inda take zaune ta zauna kamar babu abinda ya faru,
Rose ta kalli Sanah tace " I'm sorry,
then thank you so much,
Sir Moli dake tsaye yayi guntun murmushi,
yau karo na farko da Sanah tayi abu a rayuwarsa yaji ta burge shi,
sosai yayi mugun mamakin basira da hikimarta,
a hankali ya taka ya shiga class d'in,
sai da ya gama koyar da su as usual kana ya fita.
Hanash sai da ya tabbatar Sanah ta tafi makaranta kana ya shirya cikin Man lace,
ash color, takalmi, agogonsa gucci,
hularsa kalar aikin jikin kayan yayi masifar kyau,
idan ka ganshi sai ka rantse bai san Hausa ba,
dama abinka da bafulatani usul back and front,
duk inda kake tunanin had'uwa ko kyan namiji Hanash ya kai koma in ce ya wuce,
yana da bala'in kyau kamar aljani,
dan da yawa wad'anda sukayi karatu tare basu yarda d'an Nigeria bane,
waya ya ciro daga aljihunsa ya sanar da ita yazo yana set room,
itama tayi kwalliya cikin riga da skirt na atamfa tayi simple make up,
bakinta d'auke da sallama ta shiga,
har k'asa ta durk'usa ta gaida shi,
ya amsa fuska cike da fara'a,
a hankali ta zauna akan sofa had'i da satar kallanshi,
karaf suka had'a ido,
tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa,
yayi murmushi cikin nutsuwa yace " ya dai ake satar kallo na,
a fito kai tsaye a kalle ni mana,
kiga angon naki sosai, kar sai daga baya kice nahi,
tayi murmushi,
yace " ina our Sanah,
tana ji yace " our Sanah, tayi saurin d'ago kanta ta kalle shi cikin jin dad'i,
tace " tana makarata,
kansa ya d'an dafe yace " oh! zuwa fa nayi na bada hak'uri,
ance jiya nayi laifi,
dariya tayi had'i da saka hannu ta rufe face d'inta,
yace " ya kukayi da Abbu yau?
Tace " ai my Sanah bata dawo ba,
dole sai idan ta dawo zamu ji komai,
sannan koma meye kayi magana da ita kawai, duk abinda tace is okey to me,
murmushi yayi yana danne abinda ke ransa,
sosai sukayi hira kana da zai tafi ya mik'o mata laida,
k'in amsa tayi,
dan dama sun saba haka duk lokacin da zai mata kyauta sai ya sha fama kafin ta amsa,
yace " to zaki fara ko?
"Wannan ai ba naki bane ke kad'ai,
ke da our Sanah ne,
jin yace harda Sanah ta amsa had'i dayi masa godiya,
har bakin mota ta raka shi ya fita,
tana shiga gida ta aje kyautar tak'i b'ud'ewa tana jiran Sanah ta dawo.
Ko da Abbu yajewa da Didi da maganar masu neman auren Khulud zasu zo,
cewa yayi shi ina ruwansa ai shine ubanta yayi duk abinda ya dace kawai,
hakan da Didi yayiwa Abbu yasa Abbu yaji dad'i sosai,
Didi yana komawa gida ya sanar da Juju,
jikinta a sanyaye tace " to ita Sanah fa?
Didi yace " itama Allah zai kawo mata,
mu dai addu'a ce tamu,
Abbu ya sanar da Mamu ta fad'awa su Sanah cewa su zo ranar Friday,
kana Abbu ya Sanar da Ziyad da Zafran,
ko da Ziyad ya sanar da Halan itama cewa tàyi Sanah fa,
Sanah yau da wuri ta dawo daga school,
wanka tayi kana tayi sallah taci abinci,
sai data gama komai kana Khulud ta d'auko ledar da Hanash ya kawo musu,
tace " My Sanah Hanash yazo ganinki baki nan,
amma yabar sak'o,
Sanah tayi dariya kana tace " ayya dan Allah ki bashi hak'uri,
Khulud tace " ai badamuwa ya fahimta yace zai dawo da weekend sai ku gaisa,
Sanah ta amshi ledar ta bud'e wasu arnan perfumes suka gani masu shegen kyau da k'amshi,
da gani kasan masu shegiyar tsada ne,
Sanah tace " wow! amma gaskiya naji dad'in kyautar nan,
please kice masa nagode sosai,
Khulud tace " in ce masa kodai ki kira shi kiyi masa godiya da kanki,
Sanah zatayi magana Mamu ta shigo,
a bakin bed ta zauna kana ta kallesu tace " to ku sanar da su suzo ranar juma'a,
Khulud tasa hannu ta rufe fuskarta,
Mamu tace " kwaji dashi dai 'yan nema,
ta fita tana dariya,
Sanah tace " kira shi a fad'a masa,
ba musu Khulud tayi dialing number sa,
kashewa yayi ya kira ta, tayi picking sai da ta gaida shi kana tace " magana zakuyi da my Sanah,
yayi murmushin k'arfin hali yace " ok bata,
Sanah ta amsa tana murmushi ta gaida shi,
ya amsa ba yabo babu fallasa,
godiyar perfumes ta fara yi masa,
kana ta sanar dashi sak'on Abbu,
yayi d'an murmushi yace " nagode,
a tak'aice, itama murmushin tayi kana ta mik'awa Khulud wayar,
suka shiga shan love,
suna gama wayar Hanash ya nufi part d'insu Mimmee,
a parlor ya tararda su,
har k'asa ya durk'usa ya gaida su,
suka amsa cikin so da k'auna,
zayyi magana Papu yace " ya kukayi a BUK?
Kansa ya shafa kana yace " Papu ban samu ganin shi ba,
Papu yace " kamar ya baka ganshi ba?
Hanash yace " naje har sau biyu amma ban samu ganinshi ba,
kana yace " wai Papu dole ne sai su Zohal sun cigaba da karatu?
" Mai zai hana ayi musu aure kawai,
Allah yawancin malaman jami'a 'yan iska ne,
basu da wani aiki sai lalata yaran mutane,
a d'an hasale Papu yace " saboda baka san suyi karatun shiyasa kak'i maida hankali?
A hankali Hanash yace " kayi hak'uri Papu ban san magana ta zata b'ata maka rai ba,
kayi hak'uri in sha Allah ranar Monday zan koma,
zan kuma yi iya bakin k'ok'ari na,
zuciyar Papu tayi sanyi jin kalaman Hanash,
cikin sanyi Papu yace " yauwa nagode Allah yayi maka albarka,
Ubangiji ya baka zuri'a ta gari,
Allah ya albarkaci rayuwarka,
Hanash da Mimmee suka amsa da Amin,
Papu ya kalle shi yace " naga kamar da magana a bakinka ko?
Hanash ya d'an shafa kansa kana yace " eh!,
Papu ya karkata hankalinsa gaba d'aya gare shi,
yace " ina jinka,
baki Hanash ya d'an turo kana yace " to ka daina kallo na Papu,
yayi maganar cike da shagwab'a,
Papu yayi dariya yace " nama rufe ido na,
Hanash yace " iyayen Khulud ne suka ce ku je ranar juma'a,
Papu da Mimmee suka bud'e baki cikin matsananciyar murna,
Papu yace " kai masha Allah, rabon danaji labari mai dad'i irin wannan har na manta,
Hanash yasa hannu ya rufe fuskarsa wai shi kunya,
Papu yace " kayi min text d'in details na gidan,
Hanash yace " tom,
Mimmee ta mik'e zata fita,
Papu yace " ina zaki?
Tace " wajen Jadda mana a sanar mata abin farin ciki,
abinda ta dad'e tana jira,
Zohal da Wajnah dake lab'e suka fito da gudu suka yi waje suna dariya,
sukace " Mimmee mu zamuyi mata albishirin,
koda suka sanar da ita bata yarda ba,
sai da tazo har part d'in Mimmee,
suka fad'a mata da kansu kana ta yarda,
dan murna har rawa ta taka.
Kamar yadda aka tsara ranar Friday iyayen Hanash suka je,
Yayyan Papu biyu da abokinsa ne suka je,
an karb'e su hannu bibbiyu, cikin mutunci da girmamawa,
suka gabatar da kansu, ashema sun san juna sosai,
Papu abokin Didi da Abbu ne tare sukayi primary da secondary,
set d'in su d'aya, sosai sukayi farin cikin sake ganin juna rayuwarsu,
dan sun nemi juna har sun gaji da neman junansu har sun hak'ura,
dayake an san juna Abbu yace karsu damu zai sanar dasu duk halin da ake ciki,
a cikin kwana biyu Abbu yayi bincike sosai akan Hanash dama gidansu,
babu wani abun k'i a tattare dasu,
sai ma yabo da suka samu daga wajen mutane,
sosai Abbu da Didi sukayi farin cikin jin yabon da al'umma keyiwa Wassef,
duk da dama sun san halayyarsa,
Abbu ne ya kira a waya cewar sun gama duk abinda ya kamata,
mutanen da suka zo da farko su suka k'ara dawowa,
duk abinda ya kamata sunyi,
sun kawo goro da alawa da kud'in neman aure,
goro da alawa kad'ai Abbu ya amsa shima dakyar,
yace " sadaki kawai zasu kawo shima sai ranar d'aurin aure,
aka sanya bikin wata biyu kad'ai,
shima dan Mamu ta dage ne,
saboda tanasan shirya 'yarta sosai,
amma da wata d'aya aka saka.
Tafiya kawai take a matuk'ar gajiye lik'is,
dan dakyar take iya d'aga k'afarta,
ga yauma Aarib yana busy bazai samu damar zuwa d'aukarta ba,
fita tayi daga get tana neman mai adai-daita,
daga gefenta taji haushin kare,
a hankali ta juya taga wasu tik'a-tik'an karnuka guda biyu,
suna lasar harshe,
da k'arfi gabanta ya fad'i, jikinta ya d'auki kerrrma,
saurin tafiyarta ta k'ara,
taga karnukan sun mik'e daga kwancen da suke, suna kallanta,
juyawa tayi taga lungun babu kowa,
dan haka tsoro ya k'ara kama ta,
ta fara gudu-gudu sauri-sauri,
ganin yadda jikinta ke tsuma yasa karnukan zaton ko bata da gaskiya,
san haka suma suka fara binta a hankali suna haushi,
jin haushinsu yayi masifar gigita ta,
dan haka ta tattare doguwar rigar material dake jikinta,
ta zage iya k'arfinta ta soma gudu,
aiko karnukan suka ce dawa Allah ya had'a mu,
suka bi bayanta a guje,
ganin sun biyota yasata yin cilli da mayafinta datayi rolling dashi,
gaba d'aya gashinta kanta ya zubo bayanta ya barbaje,
ya hargitse,
tayi kuma yin cilli da takalmi da jakarta,
tana gudun tana kuka,
tana kuma juyawa baya tana kallan yadda karnukan ke binta,
direct baya Sanah ta koma ta nufi cikin makarantar,
karnukan suka bi ta,
a hankali ya fito daga office d'insa,
ya nufi motarsa cikin takunsa na izza,
cikin nutsuwa ya bud'e d'ayan b'angaren ya ajiye laptop da brief case d'insa,
kana ya zagayo zai shiga motar,
hangota yayi tayiyo kansa gadan-gadan,
American dogs na biye da ita,
bako d'an kwalli bare takalmi da mayafi,
sai iska dake faman kad'awa tana yin baya da rigar jikinta,
had'i da d'aukar gashin kanta yayi sama ya barbazu,
ganin direct shi ta nufo yasa shi zaro ido,
had'i da girgiza mata kansa alamar no,
saboda yadda compound d'in ke cike da students,
ganin bata fasa nufo shi ba,
yasa shi ce mata " a'a fa,
amma kafin yayi aune ta fad'a kansa,
daga shi har ita sukayi baya,
suka fad'i k'asa,
shiya fad'i a k'asa ita kuma ta kansa, gashinta ya bazu ya rufe musu fuska,
fuskarta kan tashi,
bakinta kan nashi, hancinta na gogar nashi,
hannayenta duka akan k'irjinsa,
ita kuma gaba d'ayanta akan jikinsa................
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣4⃣
Gaba d'aya Malamai da students dake wajen,
suka tsaya cak had'i da sanya hannu suka rufe bakin su,
cikin tsantsar mamaki,
suna tunanin wanne irin hukunci Sir Aryan zai yiwa Sanah,
gashin Sanah ya rufe musu fuskarsu ta yadda babu mai iya ganin fuskokin su,
eyeball to eyeball suke kallan junansu,
dukkan su sun shagala suna kallan juna,
daga shi har ita babu wanda yayi motsi balle suyi k'ok'arin tashi,
karnukan kuwa yadda kasan anyi musu magana suka juya suka koma,
bakin Sanah nakan na Sir Moli,
sun k'urawa juna ido basu ko blinking,
Leem dake tsaye ya zuba musu ido fuskarsa d'auke da murmushi,
d'an gyaran murya Leem yayi had'i da cewa " a compound dai ake,
da saurin Sanah ta mik'ewa tsaye had'i da duk'ar da kanta k'asa cike da kunya,
shima mik'ewa yayi had'i da tsuke fuskarta,
ya had'e rai tamau, yadda kasan bai tab'a yin dariya ba,
a hankali ta d'ago kanta cikin rawar murya tace " kayi hak'uri,
ta fad'a tana gyara gashin kanta,
daya zubo mata, tasa hannu ta mayar dashi baya,
harara ya watsa mata batare dayace mata komai ba ya shiga motar,
gaba d'aya mutanen dake wajen tsananin mamaki ne ya hana su yin koda kwakkwaran motsi ne,
Leem ya kalli Sanah yace " shiga mu tafi,
kai ta girgiza masa alamar a'a,
Sir Moli ya kalleta cikin takaici yaga yadda jama'a ke kallanta,
wasu ma sun shagala da kallanta,
sun k'ura mata ido kamar mayu,
gata jikinta babu ko d'an kwali babbe mayafi,
jajayen idansa, dasuka gama komawa pure red saboda tsabar b'acin rai,
ya d'ago ya kalle ta dasu kawai,
ta gane abinda yake nufi,
jikinta na kerrrma ta bud'e bayan motar zata shiga,
cikin masifa yace " driver ki ne ni?
Da sauri ta rufe k'ofar baya ta bud'e ta gaba ta shiga,
Leem zayyi magana Sir Moli ya figi motar cikin b'acin rai,
batare daya kalli inda take ba yace " ina kika zubar da kayanki?
Cikin rawar murya tace " waccen lungun ta fad'a tana nuna masa lungun da hannunta,
bai kuma magana ba, yayi hanyar data nuna masa,
parking yayi a inda yaga jakarta da mayafinta,
bayyi mata magana ba ta fita da sauri,
jikinta na rawa ta d'auki mayafinta ta yafa,
kana ta d'auki takalmi da jakarta,
ta bud'e motar ta shiga,
kanta a k'asa,
dan tayi mugun tsorata dashi,
musamman yadda kalar idansa ta canja kala in few sec,
a k'ofar gidan su yayi parking batare dayace mata komai ba,
ya kauda kansa gefe, jikinta a sanyaye ta bud'e motar ta fita,
zatayi magana ya bugi motar yayi gaba,
bayan motar tabi kallo kana ta shiga gida.
Tana shiga cikin harabar gidan,
ta iske motar Hanash, daga bayanta taji Khulud na kiranta,
da sauri ta juya bayanta,
Khulud ta nufo ta cikin fara'a,
tsayawa tayi cak tana bin jikin Sanah da kallo,
kana tace " my Sanah lafiya?
Ta fad'a tana bin jikin Sanah da kallo,
itama jikinta tabi da kallo kana tayi dariya tace " karnuka ne suka kusa murmushe ni,
Khulud ta zaro ido tace " wayyo a ina?
Sanah ta bata labarin duk abinda ya faru,
Khulud tayi dariya tace " baki tashi sanin Sir Moli sai kinga bala'i,
wallahi in nine shi banko kallanki,
Sanah ta tab'a bakinta tace " shi ya sani,
Khulud ta rik'o hannun Sanah tace " Hanash tun d'azu yake jiranki kan maganar shirye-shiryen biki,
Sanah tace " ayya to muje,
tabi bayanta,
tare suka shiga set room d'in,
hannunsu sark'e cikin na juna,
Sanah tayi dariya tace " ango kasha k'amshi,
ayi man afuwa na bar ango da kansa yana zaman jira,
yayi murmushi yana bin kayan jikinta da kallo,
" iskancin yarinyar nan fa ya wuce tunanin,
wato har a k'asa take kwanciya wannan shegen d'an iskan ya hau kanta,
a fili kuma yace " ah ai girmanki ne,
ba damuwa, kuma naga yanzu kika dawo, kamar ma a gajiye kike ko?
Tayi murmushi tana zama akan sofa,
tace " badamuwa our groom manta da gajiya,
ya kuma yin murmushi mai sauti wanda har sai da dimple d'insa suka lutsa,
yace " badamuwa our Sanah kije ki huta,
tunda yau Friday kinga gobe weekend ne muna da free time sosai,
sai in dawo muyi magana ko?
Khulud na tsaye gafe ta k'ura masa ido,
tana jin sansa da k'aunarsa yana ratsa duk wata gab'a da jijiya dake jikinta,
tana jin zata iya bada rayuwarta akansa,
ta rasa meyasa yake yi mata bala'in kama da Seif Ali Khan,
ido kawai zai fi Saif Ali Khan,
da yake Hanash akwai manyan ido dara-dara,
shi kuma Saif abu d'aya zaifi Hanash d'inta,
shine fari, da yake Hanash ba fari bane sosai,
skin color d'insa chocolate color ne,
mai shegen kyau, wanda wasu mutanen ma suke ganin kamar sunfi fararen fata kyau,
fakaitar idan Sanah yayi, ya kashewa Khulud ido d'aya dan ya lura da irin kallan datake yi masa,
da sauri ta kawar da kanta gefe tana murmushi,
Sanah tace " to in baku waje ne?
Dan ta lura da abinda ke faruwa a tsakaninsu,
Khulud tayi saurin cewa " me akayi my Sanah?
Sanah ta kalle ta tana dariya tace " oho maki ban sani ba, karki raina man wayo,
Hanash yace " a'a our Sanah karki tafi,
Sanah tace " to ai gani nayi an kira ni an zaunar dani ana shan love,
ba'a ko jin kunya ta balle ayi man kara da kawaici,
" hmmm kaji shigiya wai ita 'yar duniya,
kowa zata nunawa ita ta Allah ce,
fasik'a kawai shegiya,
ya fad'a cikin ransa,
a fili kuma yace " ayi mana afuwa kin san abun ne ba'a iya b'oye shi,
wad'anda suke yin haramtacciyar soyayya ma suke bainawa duniya,
ba kunya ba tsoran Allah, balle mu tamu mai tsarki,
daga Sanah har Khulud babu wanda ya fuskanci abinda yake nufi,
duk sukayi dariya, saboda Sanah tabar wajen ya kuma cewa " our Sanah kije kiyi wanka ciki abinci goben sai na dawo muyi magana,
" badamuwa in dai hakan yayi maka,
yak'e Hanash ya kuma dan ya gaji da ganinta da kuma magana da ita,
Allah Allah yake yi tabar wajen,
yace " badamuwa kije,
tayi dariya kana ta mik'e tayi mishi sallama tayi cikin gida.
Direct part d'in Halan ta nufa,
ta iske su zaune a parlor ita da yaran Khair sai rigima yake yi,
Sanah tace " kai dai wannan yaro anyi jarababbe,
kai ke nan kullum bakinka baya shiru?
Halan dariya tace " ya za'ayi bakinsa yayi shiru bayan jinin Sanah na yawo a jikinsa,
Sanah ta d'an turo baki tace " kwaji dashi, kowacce yaronta yake kuka sai kuce ni ya biyo,
sai kace ni kad'ai keda bakin magana,
Halan tace " ai dole muce ke suke biyowa,
tunda kinfi kowa bakin mai da magana,
Sanah ta mik'e tayi hanayar bathroom tana cewa " ku ai ta kunne kuke magana,
Halan tayi dariya,
wanka Sanah tayi ta zura doguwar riga mara nauyi,
taci abinci ta kwanta.
Washe gari Hanash bayyi niyyar zuwa ba,
amma saboda kar ya b'atawa Khulud rai yasashi zuwa,
cikin shadda brown color yazo,
yayi masifar kyau, a waya ya kira Khulud ya sanar da ita yazo,
ta kalli Sanah tace " to oganniyya tashi ki shirya Hanash yana waje,
ba musu Sanah ta mik'e ta zura dogon hijab,
suka fita a set room suka iske shi zaune as usual gabansa an jera masa kayan motsa baki,
Khulud ta durk'usa har k'asa ta gaida shi,
Sanah ta kalle shi cikin mamaki,
baki tad'an tab'e batare dasun ganta ba,
kana ta zauna akan sofa, tace " ango ina yini?
Fuskarsa a sake ya amsa da lafiya lau,
amma deep down yana jin kamar ya shak'eta,
yace " ya kike?
ta amsa da " Alhamdulillah,
yace " dama kan shirye-shiryen biki ne,
nace ko kuna da wasu abun da kuke san kuyi?
D'an kallan Khulud Sanah tayi,
Khulud tayi mata alama da tayi magana,
Sanah ta d'anyi gyaran murya kana tace " to mu dai har yanzu bamuyi wani plan ba,
amma ina ganin kar muyi bidi'a a bikin,
saboda neman albarkar aure da kuma zuria ta gari,
duk auren da zakaga an zage anyi bad'ala baya albarka saboda duk an gama janye tallafi da albarkar auren tun daga waje,
so ina ganin muyi walima da wa'azi kawai zaifi ko?
"Shegiya munafuka uwar tsari,
a fuska da baki kamar ta Allah,
amma a zuciya da bad'iri ko fir'auna albarka,
ya fad'a cikin ransa,
yak'e yayi kana yace " Alhamdulillah da ra'ayin mu yazo d'aya,
dama nima bani da ra'ayin bidi'a a biki,
saboda duk abinda Allah yace kar ayi,
to bashin shi shine abinda yafi a'ala da masalaha (alkhairi),
amma idan aka k'iji aka k'i bin dokar Allah,
aka kauce hanya saboda ra'ayin mu,
to za'aga ba dai-dai,
shiyasa auren yanzu yawanci baya albarka,
daga wannan sai wannan,
miji na fama, mata na fama suma iyayen ba'a barsu sun zauna lafiya hankalinsu ya kwanta ba,
so nima dai ina ganin muyi bikin mu cikin bin dokin Allah,
muyi walima kawai kamar yadda addini ya tanadar,
mu kuma yi wa'azi dan fad'akar da al'umma.
Sanah tace " gaskiya dai nima ina ganin hakan zai fi,
yace " to maganar lefe fa?
" Shi kuma ya kuke ganin za'ayi dashi?
Sanah tace " duk yadda kukayi dai-dai ne,
mu bamu da matsala,
yace " ok zanyi magana da Mimmee sai muji ta bakinta,
Sanah tace " hakan ma yayi,
yace " maganar hidimomin biki nawa ne zai isheku?
Sanah tace " no karka damu Abbu yace " kar mu karb'i komai daga gareka,
dan kaima d'ansa ne, ko ba gidan nan kake neman aure ba,
shi zai tsaya maka,
dan haka duk abinda muke so mu tambaye shi,
Hanash yayi murmushin jin dad'i,
a ransa yace " kowa a gidan mutum kirki ne,
amma banda wannan shegiyar,
kodan dama ance a duk zuri'a sai an samu zakka,
a fili kuma yace " ai hakk'i nane dan haka dole nima nayi wani abun,
Sanah zatayi magana yayi cewa " please! ku barni nima nayi iya yina,
"Ok tace kana suka cigaba da maganar shirye-shiryen biki.
Bayan Hanash ya tafi direct part d'in Halan suka nufa,
tana kitchen tana aikin abincin dare,
suka shiga, amsar aikin sukayi sunayi Sanah na sanar da ita yadda sukayi da Hanash,
itama Halan sosai ta goyi bayan tsarin da sukayi,
sai da suka gama girkin kana sukayi part d'in Mamu suka sanar da ita komai,
itama taji dad'in hakan,
dan haka ta tashi ta nufi part d'in Juju ta sanar da ita,
ita dayake bata cewa komai,
sai dai tabi su da addu'a,
shima Hanash yana komawa gida ya sanar da Mimmee da Papu yadda sukayi,
tace " eh gaskiya wannan tsarin yayi,
waye ya kawo tsarin, baki ya tab'a kana yace " Sanah,
yana fad'a ta gane wacce basa shiri ce,
tayi dariya tace " kai amma yarinyar tana da hankali da tunani,
wallahi har naji ta burge ni,
Hanash yace " hmmmmm Mimmee baki san wacece Sanah bane,
tayi murmushi batare datace komai ba,
yace " Mimmee ya maganar laifi?
Tayi murmushi tace " in sha next week za'aka kai,
kaga saura 3 weeks kenan lokacin,
ya amsa da Allah ya kaimu,
tace " Amin ya Allah.
Sannu bata hana zuwa sai dai a dad'e ba'aje ba,
rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya,
duk abinda aka sakawa lokaci komai daren dad'ewa zai zo koda shekara dubu ne,
yau gaba d'aya gidan Hard'o ya kacame da girke-girken tarbar 'yan kawo lefe,
kasancewar yau ne ranar kawo lefen,
sosai ake ta aikin girki, an shirya abinci da snacks kala-kala,
manya-manyan tray aka shirya wajen guda 30 d'auke da samosa, spring grl, pepper chicken,
donut, meat pie cincin, duk anyi raping d'insu da foil papers,
an ajiyesu a gefe wad'anda za'a bawa masu kawo lefen ne idan sun tashi tafiya,
su tafi dashi as tukwici,
a part d'in Mamu aka shirya amsa lefen,
dan haka su Khulud suna part d'in Halan,
yayinda gaba d'aya mutanen gidan suka hallara a part d'in Mamu ana jiran su,
wajen k'arfe 5:00pm na yamma lumtsuma-lumtsuma motoci suka fara parking,
a harabar gidan, had'add'un mata 'yan boko suka fito,
su Halan ne sukayi musu iso har part d'in Mamu,
aka tare su hannu bibbiyu cikin sakin fuska,
saitin akwatuna biyu na company Victoria Secret,
k'irar 2019,
new design aka shigar dasu part d'in Mamu,
jama'a 'yan amsar lefe suka shiga bud'awa,
komai na cikin akwatin dozin biyu ne 24,
har da key d'in Range Rover da tikect na d'in America & Dubai,
na zuwa honeymoon,
kowa ya yaba da lefen sosai,
bayan an gama ganin lefen kana aka shiga cin abinci da shaye-shayen drinks,
da suka tashi tafiya aka basu tray d'auke da snacks.
Sosai ta kowanne b'angare aka shiga shirye-shiryen biki haik'an,
Mamu ta dake sosai wajen shirya d'iyarta,
ta shiga tsumata da magunguna kala-kala,
aka fara yi musu gyaran jiki dilka da halawa,
daga Sudan Mamu ta d'auko mai gyaran jikin Sanah da Khulud musamman,
aiko nan da nan suka shiga shek'i suna k'alli,
kyansu ya k'ara fitowa sosai,
tunda biki ya taho gadan-gadan Sanah ta daina zuwa makaranta,
saboda sunyi busy da yawa kullum suna faman yawan kasuwa,
har Halan bata zama kullum tana nan da can,
bayan an bugo invitation card,
Khulud ta mik'awa Sanah tace " gasu nan ko kina da wanda zaki gayyata d'aurin aure,
Sanah tace " bani da wanda zan gayyata,
Khulud tace " har Sir Moli,
tayi maganar idanta yana kan wayarta,
Sanah ta zaro ido waje tace " wa kika ce?
Khulud tace " Sir Moli nace, tayi maganar idanta yana kan phone,
Sanah ta jefa mata pillow tace " kinyi magana kinyi kamar bake kikayi ba,
Khulud tace " eh meye a ciki?
"Cewa nayi ki gayyato Sir Moli yazo d'aurin aure,
in kuma baki gayyatarsa ni zan kai mishi IV da kaina,
Sanah tace " tab so kike ya samu damar cimin mutunci kenan,
Khulud tace " dan Allah ki gayyace shi,
Sanah tace " ke! wai meye haka ne,
Allah ban gayyatarsa,
Khulud tace " shikenan ni zan gayyace shi,
kuma Allah sai kin raka ni har office d'insa gobe na kai masa,
Sanah tace " indai wannan ne ba damuwa muje zan raka ki Allah ya kaimu goben,,
Khulud ta amsa da " amin.
Washe gari wajen 10:30am suka shirya suka nufi BUK,
har cikin makarantar Aarib ya kai su,
yace " na tafi kona jira ku?
Sanah tace " no ba dad'ewa zamuyi ba,
yace " ok badamuwa ina jiranku,
Sanah na sanye da riga da skirt na atamfa,
d'inki yayi masifar yi mata kyau,
yabi jikinta, ta yafa mayafi a kafad'arta,
sai shek'i suke abinka dama da amsu kyau,
balle kuma yanzu an k'ara da gyaran jiki har kala-kala,
sai shek'e suke suna d'aukar ido,
a k'ofar office d'insa suka tsaya,
Sanah ta kalli Khulud tace " sai kiyi knocking ko?
Khulud tayi murmushi tace " tarihi ya maimaita kansa kenan,
Sanah tace " me?
Khulud tace " kin manta a Roni mun tab'a yin irin haka,
Sanah tayi dariya tace " haka ne,
ranar da kika matsa sai muje ko?
Khulud tayi murmushi kana tayi knocking had'i dayin sallama,
tunda suka tsaya Sir Moli na hango su ta cikin glass,
yana kuma yijo hirarsu,
sosai ya k'ura musu ido yana kallansu,
muryarsa a dak'ile yace " waye?
Still idanshi na kansu na cikin glass,
rolling sexy eye d'inta tayi had'i da tab'e baki,
Khulud tayi murmushi had'i da girgiza kanta tace " Sanah ce Sir,
Sanah ta zaro ido waje, tace " meyasa zaki ce ni bazaki ce ke ba?
Khulud tace " yadda zaifi ganewa mana,
idan nace mishi Khulud ce sai yayi dogon nazari kafin ya gane,
amma danace Sanah zaifi saurin ganewa,
duk abinda suke yana jinsu,
cikin izza yace " wacece Sanah?
Sanah ta kalli Khulud had'i da zare mata ido,
tana yi mata alamar kin gani ko?
Khulud tace " Sir nice Khulud Rawan your student,
" in.. yace a tak'aice,
zaune suka iske shi akan sofa,
Khulud ta durk'usa har k'asa ta gaidashi,
ya amsa fuskarsa a sake,
yace " masha Allah su Khulud an girma,
tayi murmushi,
Sanah na daga tsayen tace " ina wuni?
Banza yayi da ita baiko kalli inda take ba,
Khulud ta kalli Sanah tace " ki bashi to,
Sanah " au to kana ta ciro IV daga cikin jaka ta mik'a masa,
ya amsa batare daya kalli inda take ba,
Khulud tace " katin d'aurin mu ne,
shine nace kai zamu fara gayyata,
katin ya sub'uce daga hannunsa,
yayi saurin d'auka cikin fara'a yace " masha Allah,
na tayaki murna Ubangiji ya sanya alkhairi,
Khulud ta kasa amsawa sai Sanah ce tace " Amin,
baiko kalli inda take ba,
Khulud tace " Sir kullum sai na tambayeka,
yayi murmushi yace " ayya ni ma ina sane dake, naso na tambaye ki,
sai dai babu wanda zan tambaya,
Sanah ta gane abinda yake nufi,
da ita yake, wato girman kanshi bazai barshi ya iya tambayarta ba,
Khulud tayi murmushi tace " Sir dan Allah kazo,
yace " in sha Allah zanzo,
waye ango?
Sanah tace " wannan wanda ya shigo office d'inka 2 times unexpected,
of head, with out your permission,
ya gane wanda take nufi,
wanda ya shigo ya ganshi yana goge mata cikinta,
da lokacin daya shigo ya kamasu yana shan bakinta,
amma sai yayi kamar bai ji ta ba,
ya kalli Khulud ya kuma cewa " waye angon?
Khulud tayi murmushi tace " sunanshi Hanash Waseef,
Sir Moli yace " Allah ya kaimu lokacin,
suka amsa da amin,
Sanah na tsaye ji take kamar zata fashe saboda dizgin da yayi mata,
Sanah ta kalli Khulud tace " sai ki tashi mu tafi ko?
Khulud ta kuma yin murmushi kana tayiwa Sir Moli sallama suka tafi,
suna fita ya bud'e IV d'in yaga saura just 4 dayas d'aurin auren,
Sanah ko masifa taitayiwa Khulud wai ta kawo ta an wulak'anta,
bayan kwana biyu ana saura kwana biyu d'aurin aure 'yar Sudan ta zana musu arnan k'unshi mai matsiyacin kyau,
mai black and golden color,
aka gyara musu gashin kansu,
suka fito d'asss dasu kamar amaren indiyawa,
ranar alhamis akayi walima ana gobe d'aurin aure,
Hanash k'in zama gida d'aya dasu Mimmee yayi,
d'aya daga cikin gidajen Papu dake Nasarawa GRA Kano,
aka gyara, gidan yayi masifar had'uwa kamar gidan film d'in hate story 3,
sosai gidan ya had'u, Abbu yayi bajibta dan zagewa yayi sosai ya fitar da 'yarsa kunya,
daga China yayi oder komai,
even spoon daga China aka shigo masa dashi,
Royal bed d'aya aka saka sai Dubai bed d'aya,
da Italian bed d'aya,
ya kama 3 bedroom, 2 parlor,
including kitchen daya gaji da had'uwa shima and dinning table,
gidan kam ya had'u iya had'uwa,
ranar juma'a aka shirya za'a d'aura aure da safe da yamma ayi wa'azi then akai amarya.
Ranar Friday da misalin k'arfe 10:30am na safe,
dubbun mutane suka shaida d'aurin auren Khulud Rawan & Hanash Waseef,
akan sadaki 1 million naira,
dakyar Abbu ya karb'i sadakin,
dan shammatarsa ma sukayi,
ango Hanash sanye cikin matsiyar shadda wacce a k'alla kud'inta zai kai 300k,
takalmi da agogonsa duk designer,
sai gaisawa yake yi da mutane,
idanshi ya sauka akan Sir Aryan Moli,
dake tsaye yana gaisawa da mutane shima fuskarsa d'auke da fara'a,
ji yayi ransa ya b'aci,
" wato sai da wannan shegiyar yarinyar ta gayyato min abokin fasik'ancinta wajen d'aurin aure,
ya fad'a cikin ranshi,
Sir Moli na sanye cikin normal yard,
fari tasss kana hango har singlet d'in jikinsa,
yayi masifar yin kyau sosai,
yana niyyar shiga mota Aarib ya hangoshi,
ya k'arasa wajensa da sauri,
hannun Aarib ya mik'a masa suka gaisa kana yace " malaminsu Sanah ko?
Dan ya sanshi tun a Roni ya kuma gane shi,
murmushi Aryan yayi kana yace " eh,
Aarib yace " mu shiga ciki mana,
Sir Moli yace " no ba sai na shiga ciki ba,
tafiya zanyi, Aarib yace " no please ka shiga ciki na turo maka su ku gaisa,
dakyar Sir Moli ya yarda ya shiga ciki,
part d'in Seeya ne bakowa, dan haka can Aarib ya nufa da Sir Moli,
a parlor ya zaunar dashi kana yace " bari naje na turo maka su,
Sir Moli ya amsa da "to,
Sanah data shiga wanka a part d'in,
kasancewar sauran part d'in ciki yake da jama ta fito d'auke da gutun towel,
hannunta rik'e da wani towel d'in tana tsane ruwan kanta,
gashin kanta duk ya mammanne mata a jiki,
tana wak'ar Celine Dion new day has come,
tana wak'ar tana rawa tana kad'a boom-boom d'insa,
kwata-kwata bata lura da Sir Moli ba,
shi ko tunda ta fito daga bathroom idansa yake kanta,
hand drear ta d'auko ta gyara gashin kanta yayi masifar kyau,,
kana ta fara shafa lotion a jikinta,
tana shafa man tana rawa da d'an tsalle,
tana yarfa gashin kanta, tana cigaba da yin wak'ar,
sai da ta fesa body spray a jikinta,
kana ta d'auko pant zata saka,
tana k'ok'arin sakin towel d'in dake jikinta,
taji muryarshi can k'asan mak'ogwaro yace " no please,
ya fad'a kamar mai koyan magana,
a firgice ta juyo danta tabbatarwa kanta gaskiyar abinda taji,
zaune ta ganshi akan sofa idanuwansa sunyi canja kala ,
sunyi masifar yin jajir, kamar gauta,
wata mahaukaciyar gigitacciyar k'ara ta saki da gaba d'aya gidan sai da ya amsa,
dai-dai lokacin Hanash ya shigo parlor'n.............
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣5⃣
Sir Moli gyara zamansa yayi ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya,
yana bin dukkan su dan kallo,
Hanash dubansa yakai kan pant da bra d'in Sanah dake zube a k'asa,
kana ya bita da kallo tun daga sama har k'asa,
kansa ya girgiza kana yace " Allah ya kyauta,
ya juya ya fita, yana tunnanin why Khulud ta kirashi tace su had'u a part d'in,
kiran Khulud ya shigo wayar Hanash,
sai da ya d'an saita kansa kana yace " hello Mrs Hanash Waseef,
murmushi tayi kana tace " please ka d'an jira in ina zuwa yanzu part d'in,
da sauri yace " no ni ma banje ba,
ina cikin mutane ki bani nan da 20 minutes idan na gama zan kira ki,
ya fad'i hakan ne dan kwara-kwata baya san b'ata musu wannan mahimmiyar ranar,
mai cike da tarihi gami da farin ciki,
dan yasan muddin Khulud taga abinda ya gani yau sai Allah,
yasan zata kasance bak'ar rana kuma mummunar rana a gareta,
wanda shi bazai tab'a san ranar auren su ta zame mata bak'ar rana ba,
ni ko nace hmmm Hanash wannan a naka tunanin kenan,
tsakanin Khulud da Sanah sun wuce haka,
"ok Khulud tace, kana ta rufe wayarta.
Hanash na fita Aryan Moli ya mik'e cikin takunsa na isa da tak'ama ya nufe ta,
tsaye take cak ta kasa koda motsi,
ganin ya nufo ta direct yasa ta saurin juyawa da gudu zata shiga bedroom,
cikin zafin nama yayi wuf ya rik'o ta,
baki ta bud'e tana da niyyar yin ihuuuu,
yayi saurin sanya hannunsa ya rufe mata bakinta,
had'i da tura ta jikin bango ya matse ta,
still hannunshi nakan bakinta,
ido suka zubawa juna na tsayin lokaci,
yayinda gaba d'aya jikin Sanah ke kerrrma ga ba damar yin magana dan ya rufe mata baki,
matseta ya k'ara yi sosai a jikin bangon,
while yana kallanta ido cikin ido,
muryarsa can k'asa yace " meyasa baki da kunya?
Da ido tayi mishi alamar me nayi?
Yace " abinda kikayi yanzu,
da idanta ta kuma bashi amsar " a gidan mu nake,
"ok anyway, yace had'i d'age kafad'arsa,
irin I don't care,
sakinta yayi ya juya zai tafi,
tsoki taja had'i da rolling sexy eyes d'inta,
ta girgiza kanta ta juya da niyyar shiga bedroom da sauri,
santsin tails ne ya kwashe ta tayi baya zata fad'i,
cikin zafin nama Sir Moli yayi saurin tare ta ta fad'a jikinsa,
tana niyyar sakin ihuuuu ya had'e bakinsu waje guda,
ido Sanah ta zazzaro waje had'i k'ok'arin hankad'a shi baya,
amma ina bata iyawa namiji da mace ba d'aya suke ba,
yadda take kallansa ido cikin ido,
idanuwanta duk waje yasa shi sanya d'ayan hannunsa ya rufe mata ido,
a hankali shima ya lumshe idanuwansa yana cigaba da tsotsar lips d'inta,
sai da yasha bakinta san ransa,
ya gaji dan kansa kana ya saki bakin nata,
had'i da zame hannunsa daya rufe mata ido,
ya k'ura mata ido na tsayin lokaci,
suka kallan juna ido cikin ido,
gaba d'aya kammaninsa sun gama sauyawa,
idanuwansa sun rikid'e sun koma asalin jajaye,
duk da sanyin Ac dake parlor'n gume karyo masa yake tako'ina,
itama ido ta k'ura mishi tana mamakinsa,
yadda lokaci d'aya yanayinsa ya sauya,
ganin yadda yake kallanta yasa tabi idanshi,
taga inda yake kallo,
jikinta ya k'urawa ido musamman slink skin d'inta,
a tsorace ta zaro ido waje,
dan ita tama manta daga ita sai towel,
nuna shi da yatsanta tayi had'i da yin kwafa batare datace komai ta shige bedroom,
murmushi yayi had'i da girgiza kansa ya cusa hannunsa cikin kwantaccen gashin kansa,
kana yayi hanyar fita.
Sir Moli yana niyyar fita Khulud ta shigo,
fuskarta d'auke da murmushi,
baya ya d'an ja dan ya bata hanyar shigowa,
Khulud ta shigo ciki tana murmushi tace " Sir da tafiya zakayi baka gammu ba?
Murmushi yayi kana ya koma ya zauna batare dayace komai ba,
itama Khulud d'in zama tayi akan sofa,
Khulud zatayi magana Aarib ya shigo tare da 'yar aiki d'auke da tray,
agaban Sir Moli ya umarce ta data aje,
kana ya zauna kusa da Sir Moli,
Aarib ya kalli Khulud yace " ina Sanah?
Khulud ta juya tana d'an dube-dube kana tace " ni ma ita nake nema,
rabo na da ita nakai 1hr,
Aarib yana k'ok'arin yin magana Sanah ta fito cikin arniyar kwalliya,
sanye take cikin riga da skirt na material lace,
yayi masifar yi mata kyau,
d'inkin yayi d'assss a jikin ta,
fuskarta tasha make up,
da sauri Aarib ya mik'e had'i da zuba mata ido,
cikin ransa yace " love of rest of my life,
a hankali Sir Moli ya d'aga kansa ya kalle shi,
dan yaji abinda Aarib yace,
tana murmushi ta k'araso ta zauna kusa da Khulud,
Khulud tayi murmushi tace " kinyi kyau sosai my Sanah,
Aarib yace " ai dama ita mai kyau ce ko ba make up,
Sir Moli ya tab'e bakinsa had'i da kansa gefe,
Sanah tayi murmushi tace " da gaske Yaya?
Aarib yayi dariya yace " kina da kyau sosai ma,
gaki da manyan ido farare tass,
masu d'aukar hankali, ga dimple both side, then wushirya da farare hak'ora a jere,
ga dogon bak'in gashi har gadon baya,
ga........
d'an tari Sir Moli yayi dan kwata-kwata ba san hirar yake yi ba,
Sanah tayi murmushi tace " thank Yaya,
karaf idan Khulud ya sauka akan pant & bra d'in Sanah,
ido ta zaro had'i da kallan Sanah,
da ido Sanah tayi mata alama da meye?
Itama Khulud da ido ta nuna mata pant & bra d'in,
ido Sanah ta zaro had'i da satar kallan Aarib da Sir Moli,
wanda duk abinda suke yi yana kallansu,
Sanah tayi yak'e kana ta sanya k'afa zata ture su,
Khulud ta zaro ido had'i da girgiza mata kai,
Sanah ta cije hak'ora had'i da zaro ido,
ta motsa lips d'inta ta yadda babu wanda zai gane abinda tace,
tace " ya kike san ayi to?
Khulud tace " kina tab'awa zasu gani,
Aarib yace " me?
Dan ya ji abinda Khulud d'in ta fad'a,
da sauri sukayi murmushin yak'e kana sukace bakomai,
Sanah ta kuma cije hak'oranta alamar kin gani ko?
Khulud tace " me?
Aarib yace " a ina?
Suka kuma yin yak'e had'i da cewa " bakomai,
Sanah tayi rolling sexy eye d'inta tace " ki kwashe,
ta fad'a yadda babu wanda zai ji ta,
da k'arfi Khulud tace " tabb! ni?
Aarib ya kalle su tare cikin alamar tambaya,
Sir Moli yana sane da duk abinda suke yi basarwa kawai yayi had'i da kauda kansa gefe,
ganin yadda duk sukayi tsuru-tsuru yasa Sir Moli yin murmushin gefen baki kana ya mik'e,
da sauri Aarib ma ya mik'e Sanah na ganin sun mik'e tayi saurin sa k'afa ta tura su k'ark'ashin sofa,
ajiyar zuciya suka sauke a tare,
kana suma suka mik'e,
hannu Sir Moli ya mik'awa Aarib sukayi musabaha kana yace " zan tafi,
Aarib yayi dariya yace " ok mun gode sosai,
kana ya kalli su Khulud yace " my Sanah ku raka shi,
Sanah turo baki kana tace " Yaya shifa ba yaro bane,
ai yasan hanya,
Khulud tace " Sanah!
Sanah ta kalleta kana tayi gaba,
Aryan yayi murmushi kana ya fita,
Khulud tabi bayansa,
suka jera da Sanah suka bi bayansa,
sun kusa isa bakin motarsa Halan ta kira Khulud,
Khulud ta kalle shi tace " Sir mun gode sosai,
Allah ya nuna mana naka,
Allah ya maida kai gida lafiya,
murmushi yayi mata kana yace " amin,
Khulud ta juya zata tafi Sanah na k'ok'arin bin bayanta,
Khulud tace " kije ki raka shi mana,
Sanah ta turo baki tace " ni dai a'a,
Khulud ta k'ura mata ido had'i da cewa " Sanah!
Sanah ta kuma turo baki kana tabi bayansa,
yana sane da tana biye dashi amma bai ko juya ba,
ya shiga motarsa ya fige ta, kamar zai taka ta,
tabi motar da harara kana ta ja tsoki ta juya ta koma cikin gida,
Hanash na tsaye yana kallan duk abinda suke yi,
yaja tsoki kana yace " dan daraba ba'a iya hak'uri na yau kad'ai,
sai an zo har gida anyi, iskancin ma yanzu ya wuce ayi a makaranta.
Bayan sallar la'asur Malamar addini tazo tayi wa'azi akan zamantewar
aure,
tayi musu nasiha sosai mai ratsa jiki da jijiya,
sosai nasihar ta shiga jikin duk wanda ya halarci wajen,
tun daga wajen wa'azin Sanah da Khulud ke ta faman kuka kamar ransu zai fita,
dama mutane sun san za'ayi haka,
dan kowa yasan rabuwar Khulud da Sanah akwai ganin ikon Allah,
d'akinsu suka shiga suka rufe suna ta faman cin uban kuka,
ana yin sallar Magrib Abbu ya aiko a kira masa Khulud da Sanah,
babban parlor'n gidan Halan ta shiga dasu,
India suka iske kowa da kowa harda kakanninsu ciki,
fad'a aka yiwa Khulud sosai kan zamantakewar aure,
kusan kowa sai da yayi mata fad'a,
inda zuciyar kowa ke cike da tsantsar tausayin su,
musamman ma Sanah,
Abbu ya kalli su Mamu yace " a fad'awa mutane babu kai amarya,
sunna zanyi ni da kaina zan kai 'yata,
daga ni sai Mamu, Halan da Sanah,
duk mai san zuwa yaje daga baya,
Didi yayi murmushi yace " wama zaije?
"Uba da kansa zai kai 'ya d'akin miji?
Abbu yayi murmushi yace" eh sunna zamu raya,
kana ya kalli Halan yace " kuje ku shirya nan da 10 minutes zamu tafi,
Khulud da Sanah najin haka suka k'ara fashewa da sabon kuka,
Halan ta mik'e rik'e dasu ta fita,
basu fi 10 minutes d'inba suka fito rik'e da juna gam,
suna ta kuka, har suka sanya zuciyar mutane karyewa,
motar Abbu suka shiga, Sanah da Halan suka saka Khulud a tsakiyarsu,
Abbu da Mamu na gaba,
tunda suka shiga cikin motar baka jiyo komai sai sautin kukan su,
sun rirrik'e juna kamar za'a raba su har abada,
a harabar gidan Khulud Abbu yayi parking suka fito,
Abbu da kansa ya rik'e hannun Khulud ya shigar da ita cikin gidan,
da suka zo shiga main cikin gidan Abbu ya tsaya a bakin k'ofar shiga,
ya shiga biya mata addu'a Khulud na maimaitawa kana yace " ki shiga da k'afar dama,
bismillah tayi kana ta shiga da right leg d'inta,
zama Abbu da Mamu sukayi akan sofa,
yayinda Khulud, Sanah da Halan ke zaune akan Italian carpet,
addu'o'i Abbu ya kuma yi kana ya sake yi mata fad'a sosai,
sai da ya gama ya kalli su Halan yace " ku tashi muje,
Mamu da Halan suka mik'e amma banda Sanah,
Khulud ta rirrik'e ta gam suna cigaba da kuka,
Abbu ya kalli Sanah cike da tausayawa yace " tashi mu tafi,
cikin muryar kuka Sanah tace " Abbu zan tsaya saboda siyan baki,
tunda bamu da wasu k'awaye dole ni zan jira,
shiru Abbu yayi kana yace " ok tom,
har ya kai bakin k'ofa ya juyo yace " karki sake ki kwana,
dan wallahi idan kika kwana sai ranki ya b'aci,
yayi commanding d'inta,
cikin muryar kuka ta amsa da " tom,
kana su Abbu suka fita,
shiru kawai Abbu yayi yana driving amma a k'ark'ashin zuciyarsa yana mugun tausayawa Sanah,
while itama Mamu da Halan tunanin da suke yi kenan har suka isa gida.
Su Abbu na fita Sanah ta kalli Khulud cikin muryar kuka tace " yanzu shikenan bazamu k'ara kwana tare ba,
bazamu kuma cin abinci, muyi wasa tare ba?
Khulud tace " meyasa?
Ta fad'a still crying,
Sanah tace " gashi kuwa aure ya raba mu,
daga yau ni kad'ai zan rink'a kwana,
ni kad'ai zan rink'a yin komai a rayuwata,
Khulud tace " mutuwa nayi?
Sanah tace " ai ko baki mutu ba aure ya raba mu,
shikenan munyi nesa da juna,
ta fad'a cikin matsanancin kuka,
Khulud tace " dan Allah my Sanah ki daina kukan,
ta fad'a itama tana kukan,
Sanah tace " dole nayi kuka,
daga yau zan kasance komai nawa ni kad'ai,
gwara ke kina da mijinki ma, zai rink'a d'ebe maki kewa ta,
amma ni babu kowa,
Khulud tace " duk duniya babu mai d'ebe min kewarki my Sanah,
you still alone in my heart baki da kishiya a zuciya ta, har yau har gobe ke kad'aice,
murmushi Sanah tayi tana gogewa Khulud hawaye tace " thank you so much,
Khulud tace " nayi miki alk'awarin har abada babu abinda zai raba mu koya shiga tsakanin mu,
Sanah tace " ni ma nayi miki alk'awarin bazan tab'a barinki kiyi kuka ba,
Khulud tayi dariya tana goge mata hawaye,
Hanash bai shigo gidan ba sai around 9:00pm na dare,
dan yayi tsammanin 'yan kawo amarya ne suka kawo ta,
shi kad'ai ya shigo kasancewar shima ba wasu abokai ne dashi ba,
rik'e da ledoji,
fuskarsa d'auke da murmushi,
ganin Sanah yasa shi yin turus,
kana ya k'ak'aro murmushin dole,
yace " ana nan ana ta faman kukan ko?
"Ni dai a taimaka man kar ayi ciwon kai,
Khulud ta d'ago red eye d'inta ta kalle shi,
ganin ya shigo shi kad'ai yasa Sanah cewa " Ango ina 'yan siyan bakin?
Murmushi yayi kana yace " bana da abokanai ai,
tana mik'ewa tsaye tana goge fuskarta tace " aiko na tsaya ne saboda kar 'yan siyan baki su zo su iske babu kowa,
yace " ok shikenan sai ki kwana anan,
Sanah ta zaro ido tace " in kwana a ina?
Abbu yace " kar in sake in kwana,
Hanash ya d'anyi shiru kana yace " Ok shikenan muje na maidake gida,
Khulud najin ance za'a mayar da Sanah gida ta k'ara fashewa da matsanancin kuka,
jikinsa ya jawota ya rungume ta yasa harshe yana lashe mata hawayen,
babu wani jin kunyar Sanah na tsaye,
cike da mamaki Sanah ta kawar da kanta gefe,
Khulud tayi saurin kwace jikinta,
ta ruga ta rungume Sanah gam,
sai dakyar Hanash ya sa Khulud ta saki Sanah,
dukkan su suna ta faman kuka kamar zasu mutu,
da gudu Sanah ta fita daga parlor'n tana cigaba da kuka,
a harabar gidan ta tsaya had'i da jingina jikin motarsa,
a hankali ya tako wajen cikin takunsa na izza,
ya zuba mata ido,
yace " do you think zan d'aukeki a motata ne?
Ya fad'a yana yi mata wani irin kallo mai cike da kyama,
" so idan ma kina tunanin hakan ki daina,
dan ban tab'a d'aukar mazinaciya fasik'a cikin motata,
wallahi kin ban mamaki duk irin tarbiyyar gidanku,
da halin mutumci da kirkinsu ke kin fita zakka,
saboda tsabar ke kwararriyar karuwa ce,
duk iskanci da kike yi cikin makaranta bai isheki ba,
sai kin kawo k'ato har cikin gidan ubanki,
ranar d'aurin aurin 'yar uwarki,
haba ashe shiyasa baki da kunya kwata-kwata,
nayi mamakin yadda kika iya d'aga hannu kika mari cikekken namiji kamata,
a kan titi a cikin bainar jama'a,
ina 'yar mutumci zata iya irinka,
ai dama idan kaga haka sai rikakk'un karuwai,
banza 'yar iska kawai, wallahi dana d'aukeki a motata gwara a sace gaba d'aya motocin dana mallaka,
kuma baki kwanar min a cikin gida tunda ba gidan ubanki bane,
sai kira shi abokin fasik'ancin naki ya maidaki gida,
kinga kun sake samun wata damar kuna iya yin abunku cikin mota,
ya k'arasa maganar yana kallanta,
cike da kyama,
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
dama kallan da Hanash yake yi mata kenan?
Ta fad'a cikin ranta,
wato kallan karuwa, mazinaciya, fasik'a yake mata,
a hankali ta shiga tunani,
tabbasa ya ganta da Sir Moli har sau uku,
na farko ya ganta kwance kan table a office d'insa,
babu d'an kwali, ya kuma d'age mata riga,
na biyu ya gansu cikin wani yanayi,
har Sir Moli na shan bakinta,
kuma tana sanye da kayansa,
na uku ya ganta d'aure da towel a gabansa,
tabbas dole yayi zargin wani abun,
tunda su ba ma'asumai bane,
dole yayi tunanin akwai wani abu tsakaninsu,
tunda shima d'an Adam ne kamar kowa,
yana da zuciya kamar ta kowa mai sak'a alkhairi da sharri,
dole zayyi musu mummunan zato,
tunda shi ba daban yake da kowa ba,
saboda ko ita ce ta kanshi da mace kamar yadda ya ganta da Sir Moli dole tayi masa mugun kallo,
kuma ko shi Sir Moli ya ganta da wani kamar yadda Hanash ya ganta dole zayyi zargi,
musamman ma har sau uku,
d'aya daga ciki kuma yana shan bakinta,
kuma su ba waliyyay bane,
sai lokacin wasu abubuwa da dama suka shiga dawo mata cikin kanta,
ashe dayace wad'anda suke yin haramtacciyar soyayya ma basu b'oyewa ko jin kunya da ita yake?
Ashe saboda wannan dalilin ne ya rungume Khulud a gabanta,
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
ta fad'a had'i da rutse idanta, dan tasan bata da bakin wanke kanta,
tasan duk duniya duk wanta ya ganta haka dole yayi tunanin wani abu,
tasan ko Mamu da Abbu da suka haife ta ,
suka fi kowa sanin halinta da ciwonta,
suka ganta kamar yadda Hanash ya ganta dole suyi zargin akwai wani abu,
" tab! tace a ranta,
tana jin zafin abun,
tana jin tuk'ok'in bak'in ciki a zuciyarta,
" ya Salam! ta kuma fad'a
idanta ta runtse hawayen bak'in ciki da takaici na zubo mata,
a hankali ta bud'e idanta ta ganshi still yana tsaye hard'e da hannuwa yana kallanta,
hawayenta ta goge ta kalle shi ido cikin ido tarrr,
had'i da nuna shi da yatsa,
cikin rashin tsoro da tsiwa ta bud'e baki zatayi magana,
alk'awarin datayiwa Khulud ta tuna,
" _nayi miki alk'awarin daga yau har abada duk abinda zai yi man ban kuma ramawa,_
a hankali ta sauke hannunta data nuna shi da shi,
kana ta juya zata tafi,
murmushi Hanash yayi mai sauti kana yace " iskanci da fitsarar naki da kika saba zaki kuma yi man,
batare data jiyo ko tayi magana ba,
ta fice daga gidan,
murmushin jin dad'i yayi kana ya juya ya koma cikin gidan.
A parlor ya iske Khulud kamar yadda ya barta tana ta faman kuka,
a hankali ya zauna kusa da ita had'i da jawo ta jikinsa ya rungume,
cikin muryar kuka tace " My Sanah! fa?
Ya gane abinda take nufi dan haka yace " nasa driver ya maida ta gida,
shiru tayi tana jin gabanta na fad'uwa,
haka nan taji tsoro da fargaba sun shigeta,
cikin nutsuwa Hanash ya mik'e ya shiga kitchen ya d'auko plate da cup,
a hankali ya jawo ledojin daya jigo dasu,
ya bud'e su,
ya kalle ta yace " my queen me zaki ci?
Cikin kuka tace " my Sanah!
Shiru yayi had'i da k'ura mata ido yana nazarin yanayinta,
a cikin idanuwanta ya hango rashin yarda,
da kuma rashin kwanciyar hankali k'arara,
wato idan ya fahimta jikinta ya bata akwai wani abu,
mamakin tsananin soyayyar dake tsakanin su yake,
murmushi yayi kana yace " me?
Shiru tayi batare data amsa ba,
a hankali ya kuma jawo ta jikinsa,
ya manne ta da k'irjinsa ya shiga lallashinsa,
sosai Hanash ya lallashi Khulud kana ya bata abinci taci kad'an,
sai fresh milk data d'an sha,
mik'ewa yayi da ita a hannunsa ya nufi bathroom,
ganin ya nufi bathroom yasa Khulud fara mutsu-mutsun sakkowa daga jikinsa,
k'in ajeta yayi sai da ya kaita har cikin bathroom d'in,
kana ya dire ta cikin tub bath,
yana yi mata wani irin kallo yace " wanka zamuyi,
cikin tsoro Khulud ta zaro ido waje tace " kai da wa?
Yayi murmushi kana yace " with my wife,
murmushi tayi tace " ok tom,
ta fad'a tana k'ok'arin fitowa,
dariya yayi mai sauti kana ya mayar da ita cikin tub bath d'in,
Khulud ta kwab'e fuska tana san soma kuka,
tace " please ka barni nayi,
yana dariya yace " wannan duk tsoron mijin ne haka?
Kuka ta soma yi cike da shagwab'a,
yayi dariya yace " sorry bari na fita,
kiyi wanka ki d'auro alwala,
ya fad'a yana fita,
direct bedroom d'insa ya shiga ya shiga wanka,
ya fito ya shafa lotion & body spray kana ya fesa perfumes kala-kala,
ya shirya cikin arnan kayan bacci ya nufi bedroom d'inta,
itama tuni tayi wankan ta d'auro alwala,
ta shirya cikin kayan bacci so slink,
doguwar rigar har k'asa,
ta shafa turaruruka da body spray kala-kala,
ta d'auki k'amshi ta ko'ina,
ta zura hijab har k'asa,
tana gama shiryawa ya shigo,
bakin gado ya zauna yasata ta shinfid'a musu prayer mat,
ya ja su Sallah bayan sun idar ya dafa kanta ya shiga kwararo addu'o'i kamar yadda sunnah ta koyar.
Suna idarwa ta fara hamma,
ya kalle ta yace " bacci ko?
Kanta ta d'aga masa tace " eh!
"ok yace kana ya mik'e ya d'auke ta cak ya nufi kan bed da ita,
kwantar da ita yayi kana shima ya kwanta ya jawo ta
jikinsa,
yana shigewa jikinta mata kamar wani k'aramin yaro,
a hankali ya sanya hannunsa yana shafa jikinta,
cikin wayo ya fara k'ok'arin cire rigar jikinta,
da sauri ta rik'e masa hannu,
duk ilahirin jikinta kerrrma yake yana tsuma,
yadda kasan ana kad'a mata gangi,
cikin wani irin salo yakai bakinsa saitin kunnenta,
muryarsa na rawa yace " please ki bari muraya daren yau,
ya k'arasa maganar yana hura masa iska cikin kunnenta,
da sauri ta runtse idanta, while jikinta na cigaba da rawa,
bakinsa da nata ya had'e ya shiga tsotsar bakinta,
yayinda hannunsa ke yawo a jikinta yana shafa ko'ina,
a hankali Hanash yayi sama da hannunsa zuwa k'irjinta,
ya shiga wasa da k'irjinsa,
still bakinshi na cikin nata,
a hankali ya zame rigar jikinta ya mayar da ita naked,
kana shima ya cire kayan jikinsa,
duk abinda yake yi bakinsu manne,
cikin nutsuwa ya gangaro da bakinsa zuwa k'irjinta,
had'i da cusa hannunsa cikin gashin kanta,
yayinda d'aya hannun keta faman shafa ta,
ganin gaba d'aya ya rud'e ya gama fita daga hayyacinsa,
duk ilahirin jikinsa kerrrma yake,
yanayinsa da kamanninsa sun sauya,
yasa Khulud k'ara rud'ewa tsoronta ya k'ara k'aruwa,
taga kamar ba Hanash d'inta ba,
cikin muryar kuka tace " no please,
muryarsa na rawa yace " dan Allah,
still bai bar abinda yake yi ba,
sai da yayi romancing d'inta sosai,
ya tsotse tass in an out kana,
a hankali ya burkitata,
ya hawaye kanta,
ya fara k'ok'arin neman hanyar shiga,
azaba tasa Khulud fashewa sa matsanancin kuka tana tureshi da iya k'arfinta amma ina,
ya sakar mata gaba d'aya nauyinsa,
a hankali ya bita harya samu k'ofar shiga,
Hanash jinshi a duniyar dabai tab'a ziyara ba,
yasa shi zagewa iya k'arfinsa yana kashe arna,
bai sarara mata mata ba, sai da ya samu nutsuwa,
kana ya d'agata ya koma gefe,
had'i da jawota jikinsa ya rungume ta tsam,
itako sai ajiyar zuciya take saukewa cikin wahala.
Kasancewar unguwar su Hanash unguwar manyace,
layukan duk kusan iri d'aya ne,
yasa Sanah kid'imewa ta kasa gane takamaiman hanyar fita bakin titi,
tafiya kawai take tana waige-waige cike da tsoro da fargaba,
gashi dare yayi sosai, dan yanzu 11:00pm na dare,
awa biyu kenan tana ta tafiya tana neman abun hawa,
amma ta rasa, tunda ta fito ko mota d'aya bata gani ba,
ga Sanah ba saba tafiyar k'afa tayi ba,
ga dare yayi sosai, duk ta rud'e tsoro ya cika ta fall,
tana tafe tana kuka,
da zarar ta shiga wannan layin sai taga kamar ta koma baya,
haka idan ta kuma shiga wani layin sai taga kamar ta kuma komawa baya,
haka taitayi tana bulayi ita kad'ai cikin unguwar,
kowanne gida rufe,
sai faman haushin karnuka da take jiyowa daga cikin makamakan gidajen,
sauk'inta d'aya dayake unguwar manyan mutane ce,,
ko'ina a haskake yake da wuta,
babu duhu kwata-kwata,
wajen so silent,
k'arar motar taji tazo wucewa shuuuuuu,
d'agowar da zatayi hasken motar ya dalle mata ido,
ta yadda bata iya ganin komai,
kafin ta ankara sai taga motar tsaye a gabanta,
a tsorace Sanah ta d'ago kanta fuskarta cike da hawaye,
fuskar tayi jajir, a kid'ime ta mik'e tayi baya da aguje,
ta fara gudu iya k'arfinta,
a hankali matuk'an motar suka bi bayanta da motar cikin wani irin gudu,
da gudu aka sha gabanta da motar,
ganin da gaske gudu take yasa matuk'in motar fitowa،
da sauri ya rufe mata bakinta,
had'i da d'aukarta cak ya dannata cikin motar ya rufe....................
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣6⃣
Da k'arfi ya rufe motar kana ya zagaya ya shiga mazaunin driver,
da k'arfi Sanah ta shiga dukan glass d'in motar tana ihuuun kuka,
had'i da neman ceto,
" Keeh! ni ne,
taji muryarsa ta daki dodan kunnenta,
ajiyar zyciya ta sauke da k'arfi kana ta cigaba da kukanta,
da gudu yake jan motar dan dama shi baya tuk'in mota a hankali,
jin har lokacin batayi shiru ba,
yasa shi ganganrawa gefen titi yayi parking,
ya kashe motar, had'i da kishingid'a ya lumshe idansa, ita kuwa sai kukan take cikin disashewar murya, ido ta zura mushi tana me k'ara sautin kukanta ciki, tsananin rauni tace,, "Ka kaini gida Abbuna zaimin fada dere yayi, meyasa zaka tsaya?. "
muryarsa can k'asan mak'ogwaro yace " idan kin gama kukan sai mu cigaba da tafiyar,
ya fad'a kamar baya san yin magana,
shiru tayi masa batare data ce masa komai ba ta cigaba da kukanta,
cike da tsantsar bak'in ciki da takaici,
shiru motar tayi babu abinda ke tashi sai sautin kukan Sanah da takeyi sosai kamar ranta zai fita,
idonsa lumshe yana sauraran kukanta babu abinda ya dame shi,
a hasale Sir Moli ya juyo yace " wai baki gama bane?
Ganin yadda take kukan yasa shi yin tsaki had'i da bud'e motar da k'arfi ya fito,
a fusace ya bud'e bayan motar inda Sanah ke zaune kamar zai b'alla murfin,
ya fisgota waje, yayi wurgi da ita gefe ,
kana ya bud'e motar cikin zafin zuciya ya shiga yayi mata key,
ya fige motar yadda kasan zai tashi sama,
yayi tafiyarshi, durk'ushewa Sanah tayi wajen had'i k'ara fashewa da rikitaccen kuka,
takai wajen 10 minutes durk'ushe a wajen tana ta faman kuka,
ta hangi motarsa na dawowa,
a gabanta yayi parking batare daya fito ba,
ya kai wajen 5 minutes tsaye gabanta cikin motar,
amma ko alamar motsi bata dashi,
ganin haka yasa shi fitowa ya taka a hankali zuwa inda take durk'ushen,
yasa hannu ya d'ago ta kana ya nufi motar ya bud'e ya saka ta a baya,
shima ya shiga bayan kusa da ita ya zauna,
yakai wajen 6 minutes zaune kusa da ita babu wanda yayiwa wani magana,
while tana cigaba da kukanta,
ido kawai ya k'ura mata yana kallan yadda take kuka kamar ranta zai fita,
a hankali ya jawota jikinsa ya rungume ta tsam had'i da d'ora kanta a saitin zuciyarsa,
batayi musu ba, saboda itama tana neman wanda zai lallasheta,
dan haka ta lafe a jikinsa, tana sauraran bugun da zyciyarsa keyi da sauri da sauri,
while bata daina kukan da take yi ba,
sun dad'e a haka kana cikin rawar murya yace " meye?
Cikin sheshshekar kuka ta d'ago kanta tana kallansa,
tace " ARYAN! mun shiga uku!
ta fad'a cikin kuka,
cikin tsantsar mamaki Sir Moli yake kallanta,
jin yau rana ta farko Sanah ta kira sunansa,
dan shi a iya saninsa bata tab'a ambatar sunansa ba,
sai idan taga bala'i ko tana neman taimako,
amma haka nan bata tab'a kiranshi ba,
amma yau sai gashi ta kira shi da real name d'insa,
bai nuna mata mamakinsa a fili ba,
yace " kamar ya mun shiga uku!?
Ya tambaye ta,
cikin kuka tace " ni dai kai wallahi mun shiga uka,
da k'arfi k'irjinsa ya buga,
amma ya dake kamar bakomai yace " meyasa!?
Ya tambaye ta a tak'aice,
cikin matsanancin kuka jikinta gaba d'aya na kerrrma gami da tsuma still tana kukanta tace " zargin mu akeyi,
"zargin me?
Ya fad'a idanshi na kanta,
jikinta na rawa tace " zargin mu yakeyi,
Hanash mijin Khulud zargin mu yake yi,
yana yi mana mummunan zato,
wani irin kallo yake yi mana,
ta k'arasa cikin matsanancin kuka,
cikin rawar murya yace " zargi akan me!?
Kuka ta k'ara fashewa da shi kana tace " wai muna....
shiru tayi ta kasa k'arasawa,
Sir Moli ya gane abinda take san fad'a,
amma yayi kamar bai gane ba ya kuma cewa " muna me?
" Wai muna....
kukan dayaci k'arfinta ne ya hana ta k'arasawa,
fuska ya tsuke kamar bai gane abinda take san fad'a ba,
yace " wai meye, muna me!?
Kin dame ni da muna! muna! kawai,
idanta ta rutse da k'arfi tana cigaba da kuka, tace " wai muna ZINA!!!,
ta fad'a cikin mahaukacin kuka na fitar hankali,
yayinda gaba d'aya jikinta rawa yake,
ta gama rud'ewa sosai ta fita daga hayyacinta,
jin yayi shiru yasa ta d'ago kanta ta kalle shi,
gani tayi ya zuba mata ido kawai yana kallanta,
babu alamar damuwa ko razana a tattare dashi,
ganin yadda ta rud'e sosai jikinta nata faman kerrrma,
yasa shi maida ita jikinsa ya rungume,
Sir Moli daurewa kawai yayi bai nunawa Sanah yaji maganar ba,
amma maganar tayi masifar shigarsa har cikin kansa,
ya daure ne kawai saboda karya k'ara d'aga mata hankali,
dan yasan muddin taga wani reaction a tattare dashi sai ta k'ara tsorata,
amma deep down ji yake kamar an watsa masa wuta,
jin zuciyarsa yake kamar ana dafata da narkarkiyar dalma,
sosai ransa yayi masifar b'aci,
k'irjinsa nayi masa zafi kamar ana zuba masa ruwan zafi,
mak'ogwaronsa nayi masa k'ona da zafi,
gaba d'aya yawon bakinsa ya koma masa tamkar mad'aci,
ji yake kamar ya mutu,
amma a zahiri dayake namijin gaske ne kai baka isa ka gane halin dayake ciki ba,
shiru yayi batare dayayi magana ba,
ya sanya hannu yana shafa kanta had'i da bubbuga bayanta,
sun kai a k'alla 5 minutes a haka kana yayi controlling temper sa,
"meya ce miki?
Jikinta na rawa ta shiga bashi labarin abinda ya faru tsakaninta da Hanash tun daga farko har k'arshe,
idanta ya runtse da k'arfi yace " kiyi hak'uri, ita dama rayuwa ta gaji haka,
wata rana fari wata rana bak'i,
wata rana zuma wata rana mad'aci,
yayinda wata rana zakayi kuka wata rana kuma kayi dariya,
so karki tab'a yin abu dan mutane su gani su yabeki,
komai zakiyi kiyi shi kanki tsaye,
saboda baka tab'a iyawa mutanen duniya,
duk yadda kakai da kyan hali,
da kyawawan d'abi'u sai wani ya kusheka,
koda kullum karatun Qur'an kake yi,
kana kwana fatawa, sai ka samu masu ya aibataka,
suna zaginka, so kibi rayuwa da mutane a sannu,
karki tab'a yin komai dan kowa,
duk abinda zakiyi kiyi dan Allah,
ki kuma saka tsoran Allah a ranki,
ki kyautatawa mutane zato,
ya fad'a idansa lumshe,
kanta ta girgiza masa alamar to,
idansa lumshe yasa hannunsa dayake bubbuga mata baya,
yana shafa jikinta a hankali da niyyar lallashi,
d'aya hannun kuma yana shafa kanta,
a hankali Sanah ta d'ago kanta had'i da kafe shi da sexy eyes d'inta bata ko blinking,
shima ido ya k'ura mata while yana cigaba da abinda yake yi.
Sun juma suna kallan juna kana a hankali ya sanya hannunsa ya zame mata d'an kwallinta,
cikin wani irin salo ya sanya hannunsa ta k'ark'ashin wuyanta,
ya zame reborn d'in data d'aure gashin kanta dashi,
ya saki gashin ya zuba gadan bayanta,
while idansu na cikin na juna,
cikin nutsuwa ya zura duka hannunsa ta k'ark'arshen wuyanta,
ya tallafe fuskarta, a hankali yayi k'asa da kansa,
ya had'e bakinsu, ya shiga tsotsar bakinta,
yana shan harshensa had'i da tsotsar lips d'inta,
idanuwansu duka lumshe daga shi har ita,
a hankali yanayinsu ya fara sauyawa,
suka fara mance a duniyar da suke,
hannunsa ya sanya yana shafa jikinta ta ko'ina a gaggauce kamar wani mara hankali,
while d'aya hannun yana cikin gashin kanta yana aikin yamutsawa,
k'asa yayi da hannunsa ya d'aga rigarta ta k'asa ya zura hannunsa,
yana shafa shafaffen jikinsa,
kana cikin salo yayi baya da hannunsa yana shafawa a hankali,
bayanta ya shiga shafawa ya sanya yatsansa cikin kwarmin bayanta,
yana yi mata tafiyar tsotsa had'i da shafawa,
still bakinsu na manne dana juna suna aikin tsotsar lips da harshen junansu,
idansu duk rufe suna sauke nauyayyan numfashi,
had'i da ajiyar zuciya kamar wad'anda sukayi tsare,
gaba d'aya basa cikin hayyacinsu,
sun dad'e da shigewa cikin wata duniya ta musamman,
hannunsa ya ciro daga cikin rigarta,
ya zaya yana neman zip zai zuge,
a hankali ya fara yin k'asa da zip d'in,
while baibar abinda yake yi ba,
hannunsa d'aya na cikin gashin kanta,
bakinsa kuma yana tsotsar nata,
hannunsa ya zura ta cikin zip d'in,
yana shafa gadan bayanta cikin salo mai mantar da mutum duniyar da yake,
bakinsa ya zame daga cikin nata,
ya mayar wuyanta ya shiga tsotsar wuyanta zuwa saman k'irjinta,
yayinda d'aya hannun ke aikin shafa gadon bayanta zuwa cikinta da cibiyarta,
babu abinda suke fitarwa sai nishi,
da wani irin sauti,
sama Sir Moli yayi da hannunsa ta bayanta cikin salo yana k'ok'arin b'alle bra d'in jikinta,
dan gaba d'ayansu basu cikin nutsuwarsu,
daga waje akayi knocking glass d'in motar,
daga shi har ita babu wanda yaji,
k'ara kwankwansa glass d'in akayi a karo na biyu da d'an k'arfi,
wanda yasa Sanah dawowa cikin hayyacinta,
aiko a zabure tayi saurin yin baya,
had'i da d'ora hannunta akan bakinta ta rufe cikin tsoro,
k'ara biyota Sir Moli yayi yana k'ok'arin sake had'e bakinsu,
hannunta ta saka a k'irjinsa ta tura shi baya,
idanuwanta duk waje saboda tsoro da fargaba,
yana k'ok'arin sake matsowa kasancewar har lokacin bai dawo cikin hayyacinsa ba,
yaji an kuma buga k'ofar da k'arfi,
wanda yasa shi dawowa cikin nutsuwarsa,
red eyes d'insa ya d'ago ya kalleta,
ganin irin kallan datake yi masa a tsorace ne yasa shi,
d'an matsawa baya kana ya gyara jikinsa,
ya saita kansa da nutsuwarsa.
Muryarsa na rawa yace " koma gaba,
ya fad'a a tak'aice, da sauri ta mayar da ribbon d'inta ta d'aure gashinta,
kana ta d'aura d'an kwalinta had'i da yafa mayafinta,
jikinta na kerrrma kamar mazari ta fita ta koma gaba kamar yadda ya umarce ta,
sai ta zauna kana ya bud'e bayan ya fito,
sojoji ya gani tsaye, suna ganinshi yasa sukayi saurin sara masa had'i da cewa " sorry Sir bamu san kai ban.........
hannu ya d'aga musu kawai batare dayace komai ba,
yayi shigewarsa cikin mota yaja,
kasancewar motar tint ce yasa basu ganshi ba,
a hankali Sanah ta saci kallansa tana mamakin dalilin dayasa shi fitowa yanzu cikin daren nan,
dan taga dare yayi sosai,
tana mamakin meyasa duk sanda ta shiga cikin matsala Allah yake turo mata shi dan ya ceceta,
tunani taitayi cikin ranta tana yiwa kanta tambayoyi ganin babu mai bata amsa yasata tab'e bakinta had'i da cewa " anyway komai dai yaya ne shi kamar GARKUWA ta ne,
saboda Allah yana kawo shi gare ni a lokacin daya dace,
ta fad'a cikin ranta,
" kinci abinci!
ya tambaye ta,
kanta ta d'aga ta kalle shi taga kamar bashi yayi maganar ba,
dan haka itama ta share, bai kuma yi mata magana ba,
yayi parking a k'ofar USA restaurant,
batare dayace mata komai ba ya fita,
oder ya bayar kana ya tsaya yana amsa wayar,
tana daga cikin motar ta k'ura mishi ido,
duk da bata jiyo abinda yake cewa,
wani mutum taga ya zo batare da yayi mishi magana ba,
ya mik'a mishi wani abu, kamar splash disk kamar memory card,
dayake tana daga nesa yasa bata ga ko meye sosai ba,
shima Sir Moli taga ya amsa batare da yayiwa mutumin magana ba,
mutumin ya juya da sauri yabar wajen,
shi kuma Sir Moli ya nufo motar,
tambayar kanta tayi waye wannan mutumin?
"Me ya bashi?
" Ko shine dalilin fitowarsa cikin dare?
tambayoyi taitayiwa kanta, wanda babu mai bata amsarsu,
motar ya bud'e ya shiga ya zaune had'i da lumshe idanuwansa yace " ke bakiga inda nazo bane?
Kanta ta d'aga kana tace " na gani,
yace " meya hanaki fitowa ko ni kike so na zab'ar mike abinda zaki ci?
Ya fad'a still idanshi rufe, banza tayi dashi bata bashi amsa ba,
can wajen 5 minutes dayin maganar yace " daga yau idan kikaga na fita kema ki fita dan ban san yawan magana,
idanta na kanshi ta amsa masa da " to!
bai kuma cewa komai ba,
har aka kawo masa oder da yayi,
baya bud'ewa wanda ya kawo ya aje a bayan motar,
kana yaja motar, a k'ofar gidansu yayi parking,
baiko d'aga kanshi ya kalle ba,
" nagode tace, cikin sanyin murya,
bai kalle ta ba, yace " ki d'auka ya fad'a a tak'aice,
tace " me!?
Bayyi mata magana ba, ya kalle ta,
baki ta tura had'i da cewa " ni fa ban gane abinda kake nufi ba,
" gasu nan a baya,
ya fad'a yana kallanta,
" kabarshi nagode, ta fad'a,
tsawa ya daka mata a zafafe yace " ke! ni sa'anki ne, ko abokin wasanki ne?
Jikinta na rawa ta bud'e bayan ta d'auka,
kana ta shiga gida,
part d'in Mamu Sanah tayi direct ta shiga bedroom d'insu,
taga yayi mata girma sosai, take kewar Khulud ta dawo mata sabuwa fil,
kan bed ta fad'a had'i da fashewa da kuka ta jawo pillow ta rungume,
sai da tayi kuka mai isarta kana ta mik'e ta shiga bathroom tayi wanka ta sanya kaya mara nauyi,
ji tayi duk jikinta ba dad'i dan haka kwanciya tayi batare databi takan abincin ba.
Sir Moli yayi parking a makeken harabar gidansa,
ya fito da nufin shiga cikin gida,
daga bayan motar yaji waya na ringing,
cike da mamaki ya koma ya d'auki wayar,
wayar ya zubawa ido yana kallanta,
har kiran ya tsinke aka sake kira,
sunan wanda ke kiran wayar ya kalla yaga Yaya Aarib,
baki ya tab'e kana ya shiga gida,
shima wanka yayi ya shafa lotion ya sanya boxer ya kwanta kan makeken royal bed d'insa,
har ya kwanta ya tuna da wayar Sanah,
a hankali ya mik'e ya d'auko wayar ya dawo ya kwanta,
pictures ya shiga, yana kallan pictures,
dariya yayi sosai ganin irin tab'arar datake tsulawa,
wasu daga ita sai bra,
wani saga ita sai bom short da half best,
wasu daga ita sai towel, wasu 3 quarter,
wasu sleep dress nema kad'ai a jikinta,
videos ya shiga nan ma yaga yadda take tsula tsiyarta san ranta,
yayi dariya sosai.
Tsakar dare yunwa ya tashi Sanah,
ta farka a gigice kasancewar duk yinin ranar bata ci komai ba,
da sauri tayi bathroom ta wanke bakinta,
ta dawo fresh milk d'in ta fara sha sosai kana taci gashashshan naman daya siyo mata,
sosai yayi mata dad'i,
tana gama ci ta baje ta cigaba da bacci,
da safe da Sir Moli zai fita ya biya ya kaiwa me gadin su Sanah wayarta,
karb'a yayi ya kai mata cikin gida,
ya bawa Mamu, tayi mamaki amma bata tambayeshi ya akayi wayar tazo hannunsa,
takai mata cikin bedroom, koda Sanah ta tashi daga bacci taga wayarta kusa da ita batayi tunanin komai ba.
Rungume da Khulud Hanash ya kwana a kirjinsa yana ta faman lallashi,
da tarairayarta,
da asuba da kanshi ya tashi ya had'a mata ruwa,
ya gasa ta sosai kana yayi mata wanka sukayi sallah,
da gari ya waye daga gidan Mimmee aka kawo musu breakfast,
mai rai da lafiya sai da suka sake wanka suka shirya cikin shiga ta alfarma,
kana sukayi breakfast,
kasancewar Hanash ya gasata sosai yasa ta warke,
tare suka yini Hanash yana lallab'a ta,
yana nan da nan da ita kamar ransa,
da yamma ya shirya zai fita zaije gaida su Mimmee,
ya kalleta yace " my zanje gaida su Mimmee,
fuska ta kwab'e kana cikin shagwab'a Khulud tace " nima zani,
ido ya zaro waje yace " da wannan tafiyar taki?
" Kamar kina koyan tafiya, kin rufa mana asiri kar su Mimmee su gane,
baki ta d'an tura tace " ni dai zan je please,
ido ya zuba mata kana yace " to tafiyarki taki fa?
Baki ta kuma turowa had'i da sanya hannunta ta rufe fuskarta tana murmushi,
shima murmushin yayi kana ya shiga bedroom ya d'auko mata hijab,
da kanshi ya saka mata kana d'auketa cak,
bai aje ta ako'ina ba sai sai cikin mota,
kana yayiwa motar key,
bai tsaya ko'ina ba sai harabar gidansu,
tana k'ok'arin fitowa yayi saurin dakatar da ita,
kana ya zagayo tana ganin yana niyyar d'aukarta,
tayi saurin girgiza mishi kanta,
bai saurare ta ya sungume ta cak,
tana ta mutsu-mutsu had'i da waige-waige,
Jaddah na kallansu ta window,
murmushi tayi had'i da cewa " yaran zamani babu kunya,
tana ganin yana k'ok'arin shiga main parlor da ita tayi saurin direwa tana dariya,
dariya shima yayi suka shiga ciki,
a parlor suka iske Mimmee tana ganinsu tayi saurin mik'ewa,
had'i da nufar Khulud tayi hugging d'inta,
cike da murna tace " you are welcome dear,
murmushi Khulud tayi kana ta zame har k'asa ta gaida ita,
Mimmee na murmushi ta d'agota had'i da zaunar da ita akan sofa,
kana ta kwalawa su Zohal kira,
da dugu suka fito suna ganin Khulud sukayi wajenta suna murmushi had'i da cewa " Khulud Rawan,
tsawa Mimmee ta daka musu had'i da cewa " kul! karna sake ji, Anuty sunanta daga yau,
jikinsu a sanyaye suka amsa da " to,
kana ta umarce su dasu akawo mata abinci,
kana Mimmee ta mik'e ta nufi sama wajen Papu,
Hanash na ganin Mimmee ta tabar wajen ya dawo kusa da Khulud ya zauna,
ya mik'a hannunsa zai jawo ta jikinsa,
tayi saurin zaro ido had'i da d'an matsawa,
tace " please ka koma can ka zauna kar Mimmee ta dawo ta ganka anan,
" to sai me?
" Ba kusa da matata na zauna ba?
Zatayi magana Papu da Mimmee suka sauko,
a hankali ta fara k'ok'arin mik'ewa Mimmee data gane halin datake ciki tayi saurin dakatar da ita,
" a'a ba saikin mik'e ba, kiyi zamanki,
ta fad'a suna zama ita da Papu kan sofa,
har k'asa Khulud ta durk'usa ta gaida Papu,
ya amsa cikin fara'a yana tambayarta ya bak'unci,
ta amsa da Alhamdulillah,
Papu ya kalle ta yace " Khulud! ta d'ago kanta a hankali ta kalle shi,
" na'am ta amsa,
yace " ki d'auke ni tambakar Abbu da Didi,
saboda duk d'aya ne ni da su, abokaina ne tun na yarinta,
tare muka taso dasu, ki d'auke ni kamar su,
ni ma zan d'aukeke ki tamkar Zohal da Wajnah bawai surukata ba,
ki tambaye ni duk abinda kike so,
nayi miki alk'awarin zan yi miki duk abinda kike so in sha Allah,
a hankali ta amsa " to Papu in sha Allah zanyi yadda kace,
yayi murmushin jin dad'i,
Mimmee zatayi magana Jaddah ta shigo,
" to daba'a je an gaidani ko ankai min amaryar ba,
ni nazo ganinta da kaita,
Hanash yayi saurin mik'ewa had'i da zuwa inda take ya rik'o hannunta,
yana dariya yace " yi hak'uri na d'auka kina bacci ne,
shiyasa ban shiga ba, kema kin san ai bazan tab'a wuce ki nazo nan ba,
kece fa ta k'arfen,
ya fad'a yana dariya, dariya itama tayi kana tace " kaji sarkin wayo,
nice ta k'arfen ka d'auko matarka,
da sauri Khulud ta rufe fuskarta,
cikin jin kunya, Papu ya mik'e yana dariya yabar wajen,
Jaddah ta zauna kusa da Khulud ta dafata kana tace " amarya Allah ya sanya alkhairi,
Ubangiji ya bada rabo mai amfani,
fuska Khulud ta sunne, cikin jin kunya,
Jadda tace " ai kima daina jin kunya dan nayi miki maganar haihuwa,
dan babu abinda nake san gani kamar yaran Hanash a duniya,
dan haka ki shirya haihuwa duk shekara,
Hanash yayi dariya kana yace " Jadda itama tasan muna san yara dan tasan babban burin Hanash shine yaga yaransa,
Jaddah ta mik'e had'i da cewa " atoh! kama gaya mata ta shirya dan in sha Allah ban mutuwa sai na ga yaran Hanash,
ta fad'a tana k'ok'arin fita, har takai bakin k'ofa ta juyo tana dariya,
tace " yanzu ma sai ka d'auke ta,
Hanash ya mik'e yana dariya yace " tom Jaddah yanzu kuwa,
ya fad'a yana k'ok'arin d'aukar Khulud,
ido Khulud ta zaro had'i da girgiza mishi kanta,
fuskarta kamar zatayi kuka,
Jaddah tace " jama'a kuji man yaro mara kunya,
cikin dariya Hanash yace " kefa kika ce na d'auke ta,
sai dare su Hanash suka koma gidan su,
ranar ma Hanash bai sararawa Khulud ba sai da yayi,
sai da akayi sati biyu kullum daga gidan Mimmee ake kawo musu abinci,
kana bayan 2 weeks Khulud ta fara girki,
yayinda kullum suna cikin waya da Sanah ko chart,
a rana sai suyi waya fiye da goma.
Tuni Sanah ta koma makaranta ta cigaba da attending lectures,
dan ta yanzu tafi san zaman makarantar fiye da gidan,
danma yanzu ta fara sabawa,
yau basu gama lectures ba sai magrib,
suna fitowa ana kiran sallar magrib,
ga hadari ya had'o sosai garin yayi bak'i k'irin,
saboda hadarin daya had'o,
a matuk'ar gajiye ta nufi get tana tafiya tana hard'ewa kamar zata fad'i saboda tsananin gajiya,
ga bak'ar yunwa data addabeta,
matarsa ce ta tsaya a gabanta batare daya kalleta ko yayi mata magana ba,
yayi parking,
idanta tayi rolling kana ta zagaya ta bud'e gaban motar a hankali,
ta shiga batare da sunyiwa juna magana ba ya ja matar yayi waje,
yayyafi aka farayi mai d'an k'arfi,
hannunsa rik'e da drinks yana sha,
mik'a mata lemun yayi batare daya kalleta ba,
yace " sha!
a tak'aice, kallansa tayi kana ta kalli sauran lemon dayake sha wanda ya mik'o mata,
tace " me!?
"Sha! ya kuma fad'a mata,
still bai kalli inda take ba,
kallanshi tayi cike da mamaki kana tace " me d'in zan sha?
Kallanta yayi kana ya kalli lemon batare da yayi magana,
" na koshi tace, bai kalle ta bai kuma janye hannunsa daga mik'a mata sauran lemon ba,
idanta ta juya kana tasa hannu ta amshi robar lemon MIWADI,
(drink d'in dayafi kowanne lemo tsada a duniya)
bakinta takai ta kurba, taga har lokacin bai janye hannunsa ba,
kallansa tayi tace " me! kuma?
"Bani! yace a tak'aice,
" oh! God tace kana ta mik'a masa lemon,
bakinsa taga ya mayar ya cigaba da sha cikin nutsuwa kamar bashi yayi ba,
ruwa aka kece dashi mai k'arfi,
kamar da bakin kwarya harda k'ank'ara,
da gudu yake jan motar,
yana gaf da wuce danja,
danjar ta tsaidasu, gudun karya taka doka ya sashi saurin taka burki da k'arfi k'uuuuu,
sosai Sanah ta tsorata tayi saurin fad'awa jikinsa had'i da rirrik'e shi,
lemon hannunsa ya kufce ya zube masa jikinsa,
ya b'ata masa gaba d'aya jikinsa,
gashi farin yadi ne a jikinsa,
jikinsa yabi da kallo,
yaga gaba d'aya ya gaba b'aci,
d'an tsoki yaja, wanda yasa Sanah d'agowa daga jikinsa,
amma still bata sake shi ba,
inda ta rik'e shi yabi da kallo,
itama wajen ta kalla, da sauri ta sake shi had'i da komawa mazauninta,
kanta k'asa tace " kayi hak'uri,
bai amsa mata ba, ya karya kan motarshi ya nufi gidansa,
gatafaren gidansa dake Lamid'o Crescent,
ya nufa, gani tayi get d'in ya bud'e kansa da kansa bayan yayi snapping number motarsa,
tun daga waje taga sojoji na kai kawo a k'ofar gidan,
take tsoro ya kamata yayi masifar cika mata ciki,
a hankali ta d'ago kanta ta kalle shi,
da niyyar tambayarsa inane nan,
taga ya had'e ranshi sosai kamar bai tab'a yin dariya ba,
ganin ba fuska yasata sadda kanta k'asa jikinta na kerrrma,
sosai ake yin ruwan saman kamar da bakin kwarya,
parking yayi harabar gidan wanda ke d'auke da motoci kusan 15,
kowacce mota private number ce a jikinta,
*MOLI'S!*,
a hankali ya zuro k'afarsa k'asa,
kana ya fito gaba d'ayansa,
sojojin dake harabar gidan suka nufo shi jikinsu na rawa,
dakatar dasu yayi ta hanyar d'aga musu hannu,
zamanta ta gyara cikin motar da niyyar cigaba da zama,
tunowa da gargad'in da yayi mata kan duk sanda taga ya fita itama ta fita tabi bayansa,
ya sata saurin fita tabi bayansa,
Sanah na fitowa daga mota k'arfin ruwan saman dakeyi ya k'aru kamar me,
ta shiga inda taga ya shiga,
Sir Moli na shiga cikin gidan ya cire kayan jikinsa tun a parlor ya shiga bathroom,
a hankali ta shigo tana sand'a kamar b'arauniya,
girma da had'uwa parlor sunyi masifar bata mamaki,
yadda kasan irin gidajen nan na turawa ko manyan masu kud'in indiyawa,
duk wani abu na jin dad'i da more duniya akwai shi a parlor,
sofa ma set 3 ne a parlor'n b'angare d'aya,
royal, b'angare d'aya American,
d'aya b'angaren kuma Paris chairs,
sai makeken dinning, ga wani irin bed daga gefe cikin parlor'n,
dabata tab'a ganin irinsa a rayuwarta ba,
da gani daga turai yake,
duk da kallo d'aya zakayiwa gidan kasan komai daga k'asar waje akayi oder sa,
even tails dan glops & sucket na waje ne,
gidan a gyare tsaf dashi yadda kasan a turai,
k'amshe kawai ke tashi
a hankali wayarsa dake cikin aljihun rigarsa ta soma ringing,
kasancewar yasan babu kowa a gidan sai shi d'aya kuma yasan ya barta a mota,
jin wayarsa na rori yasa shi fitowa daga shi sai d'aure da towel a k'ugunsa,
turus yayi ganinta zaune a parlor'n,
a hankali ya juya yana k'ok'arin komawa bedroom da sauri,
jin taku ya sata d'agowa a hankali,
ganin yadda yake yasata saurin mayar da kanta k'asa ta sunyar,
gaba d'aya jikinta ya d'auki rawa da kerrrma,
wani irin gigitacciyar tsawa akayi da k'arfi gami da walk'iya mai hasken gaske,
kana ruwan yayi wani irin kece shaaaaaa kamar da da bakin kwarya ya b'alle,
cikin tsananin firgici da kid'ima ta mik'e ta nufi shi, jikinta na tsuma ta fad'a jikinsa had'i da rirrik'e shi gam................
*Al'bishirinku fans ku tsumayi page 27 nanda awa biyu*
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣7⃣
Fatar jikinsa na had'uwa da tata yaji wani irin abu dabai tab'a jin irinsa ba a rayuwarsa,
tsikar jikinsa ta tashi had'i da yin yarrrr gaba d'aya k'ofofin gashin jikinsa, suka rink'a buduwa, suna shigarmai da wani bak'on yanayi,
sandarewa yayi a wajen batare daya iyayin koda kwakkwaran motsi ba,
gaba d'aya jikinsa ya d'auki kerrrma, jin k'afafunshi na rawa, bazasu iya daukar nauyin jikinshi da nataba yasashi, tattaro sauran k'arfin shi ya fara motsawa,
a hankali ya zagayo da ita gabansa,
saboda ta bayansa ta rungume shi,
ido ya k'ura mata yaga gaba d'aya a mugun tsorace take, sai kerma take ta rufe idonta gam, sai k'ara k'wak'umarsa takeyi,
a hankali yaja hannunta ya nufi kan sofa da ita, tafiya yake kamar yau yake koyan takawa da k'afafunshi, cikin kasala ya zame bisa sofar,
zama yayi ya jingina da kujerar, kana ya zaunar da ita saman cinyarsa,
had'i da rungume ta tsan a jikinsa,
kamar wani zai kwace ta,
sai da ya d'auki tsawon lokaci a haka, ba abinda yakeyi sai sauk'e nannauyan ajiyan zuciya tare da shak'an k'amshin furannin dake zagaye da gidan,
kana ya d'ago kanta dake saman k'irjinsa,
ya kalleta da jajayen idansa,
har a lokacin a tsorace take,
jikinta sai kerrrma yake ta tsuke d'an bakinta ta cinnoshi sama, yayinda lips dinta sukayi jazir,
in slowly Sir Moli ya lumshe idansa, sai kuma ya sake bud'esu da sauri ya zubasu kan Red lips d'inta, cikin Rashin sani da wani irin fisga da shauqi keyi masa, ya ajiyan zuciya had'i da kai bakinsa kan nata,
ya had'e su ya ya lik'a lips enshi da nata ya shiga tsotsar leb'enta da harshenta,
ita kuwa idanta ta rufe da k'arfi dan tsananin bugawa da k'irjinta keyi, wani irin kasala ya rufeta ya hana ta k'ok'arin hana shi abinda yakeyi matan,
ta rasa meyasa bata iya dakatar dashi daga tab'a mata jikinta,
ta rasa dalilin dayasa bata kwace kanta ko yi mishi gardama aduk lokacin dayake yi mata makamanta irin wad'annan abubuwan,
tasha zama tayi tunanin why ,
danganta abin tayi da rudun shaidan ,kamar yadda annabi yace, matuk'ar mace da namiji da ba muharramaiba suka keb'e to cikon na ukunsu shaid'an ne, dan haka take ji wannan hudubar shaid'an ne,
tana son tureshi Amman ta gaza ko yanayin yadda yake komawa a duk lokacin dayake cikin irin yanayin ne yake sawa yake fin k'arfinta, dan gaba d'aya yake juyewa kamar ba Sir molin da ta sani bane,
Shi kuwa cikin zuciyarshi, fargaba yakeji da tsananin kunyar mahaliccinshi da tsoron laifin da yake shirin kusanta kanshi da aikatawa, amman ya kasa tsaida hannunshi,
a hankali yakai hannunsa ya zame d'an kwallinta,
had'i da baza gashin kanta kana ya cusa hannunsa ciki,
while yana cigaba da shan bakinta,
d'aya hannunsa ya saka a muyanta yana shafa duk ilahirin jikinta,
jikinsa na kerrrma ya d'ago hannunsa ya d'ora saman k'irjinsa,
a hankali ya zame bakinsa daga cikin nata,
muryarsa na rawa yake cewa, "Ma. Maatsa, ta. ta tashi a jikina". ya k'arishe maganar cikin fizgo numfashi tare da k'ara matsota jikinshi, ikon Allah sai kallo, yana ta tashi a jikinshi yana kuma k'ara matseta, cikin k'arfi da ficewar numfashi ya sake cewa, "Tashi. "
ya fad'a a tak'aice,
ba musu saboda a tsorace take ta dashi dan haka ta shiga yunk'urin kwace kanta daga matsar da ya mata, kici-kicin da takeyi dan k'wace kanta , shi kuma sai yakejin kamar shafa faffad'an k'irjinsa mai kwantaccen gashi takeyi,
d'aya hannunta ya rik'o ya sanya cikin suman kansa kana cikin muryar raunieyace " Ki tashi",
ya fad'a kamar mai koyan magana,
nan ma Sanah ta fara yin yadda yace,
cikin salo ya kai bakinsa wuyanta yana tsotsa had'i lasar kunnenta yana hura mata iska ciki,
had'i da gogo k'asumbarsa a saman fuskarta,
a hankali Sanah ta lumshe idanta,
tana yunk'uri had'i da cusa hannunta cikin sumar kansa,
tana cigaba da mik'ewa,
wuyanta ya sank'alo tare da jawota jikinshi, yana kuma Allah wadaran abinda yakeyi a cikin zuciyarsa, manneta yayi da jikinshi,
take jikinsu duka ya d'auki rawa da kerrrma,
daga ita har shi tsuma sukeyi kamar mazari,
idansa yayi masifar yin jajir,
duk da sanyin Ac da ruwan saman da akeyi gumi Sir Moli yake yi,
dukkansu sun fita daga cikin hayyacinsu,
baka jin komai sai sautin fitar numfashinsu,
dake fita da sauri da sauri,
a hankali ya zura hannunsa ta k'asan rigarta,
ya shiga yin wasa da cibiyarta,
had'i da zura hannunsa cikin kwarmin cibiyar yana shafawa,
d'ayan hannunsa ya zagaya dashi bayanta,
yana shafa tsakiyar bayanta, zuwa cikinta,
a hankali yayi sama da hannunsa zuwa k'irjinta,
jin hannunsa saman booms d'inta,
yasa gabansa muguwar fad'uwa da k'arfi, yana mai zubda k'ollar bak'in ciki, yana tuna ayoyin dake hani da kusanta zina, hawaye yake zubdawa sosai daga idonshi yana tuno ayoyin forko-forkon suratul Noor, amman duk da haka ya gaza control din kanshi
abinka da wanda bai tab'a ba, itama tana jin hannunsa saman booms d'inta ta saki naunauyan nishi,
a hankali ya mik'e had'i da d'aukarta cak ya nufi kan bed d'in dake parlor'n,
kwantar da ita yayi idanuwanta lumshe tana fitar da numfashi da sauri k'irjinta nayi sama da k'asa.
A hankali ya birkita bayanta ya zuge zip d'in rigar,
bayanta ya bayyana,
sai da ya rumtse idansa da k'arfi kana a hankali ya yasa harshe yana lasar gadon bayanta,
yayinda hannunsa ke faman yawo a sassan jikinta,
cikin salo yasa hannunsa ya ya sab'ule rigar jikinta,
kana a hankali ya b'alle bra d'in jikinta,
ya d'ora hannunsa saman booms d'inta,
batare daya zame bra d'in ba,
a hankali yasa harshensa yana lasar saman booms da k'irjinta zuwa wuyanta,
while hannunsa bai bar yawo a jikinta ba,
zame towel d'in jikinsa yayi ya rage daga shi sai boxer,
a hankali ya ya kwanta ya d'orata saman jikinsa,
k'irjinta saman nashi, booms d'inta na gogar k'irjinsa,
tana daga saman nashi ya cigaba da shafa yana shan bakinta,
had'i da tsotsar harshenta,
sosai Aryan ya gigice ya d'imauce sosai,
ya fita sosai daga hayyaci da nutsuwa,
gaba d'aya jikinsa kerrrma da tsuma,
joy stick d'inshi ta mik'e samb'al,
kamar taci babu dan yunwa da azabtuwa da take tsawon shekaru tana dakon abincinta.
Parlor'n yayi tsit baka jin komai sau k'arar ruwan sama,
da gurnaninsu,
a hankali Sir Moli yakai hauununsa yana k'ok'arin cire bra d'in jikinta gaba d'aya.
wayarsa ce ta d'auki rori ta cika parlor'n gaba d'aya!,
jin k'arar wayar ya dawo da Sanah cikin hayyacinta,
da sauri ta yunk'ura ta fara k'ok'arin tashi,
da k'arfi Sir Moli ya mayar da ita kwance,
had'i da juyewa ya mayar da ita k'asanshi,
ya danne ta, saboda har lokacin ya kid'ime yake,
kana ya zura hannunsa k'asan skirt d'inta yana shafa cinyoyinta,
k'ara yunk'urawa Sanah tayi had'i da sanya hannunta da niyyar ture shi,
sakar mata gaba d'aya nauyinsa yayi,
had'i da zame bakinsa daga cikin nata,
yakai bakinsa saitin kunenta muryarsa na creaking,
yace "Wa iyazubillah!
ya fad'a yana lasar kunnenta,
kanta ta fara girgiza mishi had'i da saka kuka,
tace " ni dai a'a dan Allah,
ta fad'a cikin kuka,
" Sakeni". ya kuma fad'a,
kamar mai koyan magana muryarsa can k'asan mak'ogawaro,
kana mayar da bakinsa cikin nata,
yana cigaba da shafa saman booms d'inta,
ido Sanah ta bud'e ta bishi da kallo taga daga shi sai boxer,
abinda bata tab'a ganin a rayuwarta ba,
tsiraicin babba,
kana tabi jikinta da kallo taga jikinsa babu riga an zame ta k'asa,
wajen k'ugunta, skirt d'in dake jikinta ma an tattare shi sama,
da k'arfi ta saki gigitaccen kuka,
wanda ya dawo da Sir Moli duniyarsa ta ainahi,
da sauri ya d'agata had'i da hantsilawa baya a gigice,
a kid'ime ya dafe kansa yana bin jikinshi da kallo kamar mai tabbayar kansa me yayi, ido ya rumtse da k'arfi yana furta, LA'ilaha'illa anta subahaka innikuntu minazzalumin, azubullahi minashaidani rajin,"
jikinsa ya kuma kalla yaga yadda yake,,
hannu yasa ya dafe kansa da tsananin k'arfi, yana mamakin kansa da abubuwan da yake yi a cikin kwanakin nan,
ya rasa meyasa daya ganta koya keb'e da ita yake loosing control,
cikin tsananin dana sanin abinda yayi , ya mik'e da da sauri ya d'auki towel d'insa ya d'aura,
kana cikin sauri da maimaita addu'o'in ya shiga toilet ya sakarwa kanshi ruwa, tare da rumtse idonshi yana mai zubda zazzafan hawaye da jin kunyar kanshi da mahaliccinsa, bedroom ya fito tare da shirya. A kunyace ya fito,
koda ya fito ganinta yayi yadda ya barta, a durk'ushe tana ta faman kuka,
Ido ya kawar tare da tsuke fuska da neman tsari daga sharrin shaid'an yace, "Keeeh wai a nan zaki kwana nane?".
Kallonshi tayi tana cigaba da kukan,
" Tashi in meda ke gida, ya fad'a muryarsa na rawa kamar kuka zai kwabce mai,
bata ko kalli inda yake ba ta cigaba sa kukanta, murya can k'asa cike da madame yace,
*" kiyi hak'uri!*
red eyes d'inta ta d'aga ta kalle shi cike da hawaye tace " hak'uri!?
Kansa ya kawar gefe cikin tsananin jin haushin kanshi da nadama, kana yace " Wallahi ni ma ban san yadda akeyi hakan na faruwa ba, Wallahi Allah ba halina bane".
batayi mishi magana ba,
ta mik'e dan gani take hankali yake san kuma raina mata,, gyara rigarta da skirt d'inta,
tayi hanyar fita bata ko kalli inda yake ba,
ganin k'ofar akwai password yasata tsayawa cak,
batare data juya ko tayi mishi magana ba,
mik'ewa yayi ya nufi inda take,
ganin ya nufo ta gadan-gadan yasa ta matsawa had'i da kauda kanta gefe,
bayyi mata magana ba,
tissue ya d'auka a gefe ya mik'a mata batare dayace mata komai ba,
kanta ta kuma kawarwa gefe ,
fuska ya tsuke ya kuma tare da d'aga kafad'arsa, alamar i don't care,
kana ya tab'e bakinsa ya zauna akan sofa had'i da d'ora k'afarsa d'aya kan d'aya,
yace " anyway! ni bazaki kwananmin a gida ba."
kallansa tayi taga kwata-kwata babu abinda ya dame shi, sai ma yadda yake wani reacting kamar itace mai laifin,
cikin rawar murya tace " amma dai kasan kallo da zargin da akeyi mana ko?
" Ko so kake mu tabbatar da mummunan zato da zagin da ake yi mana?
" So kake ni in zama karuwa, fasik'a mazinaciyar daya ambace ni dasu?
" Ko so kake yi mu zama MAZINATAN da gaske?
Take launin idansa ya canja,
ya dawo asalin Sir Aryan Moli,
fuskarta tayi jajir yadda kasan ta watsa mishi wuta,
idansa ya runtse batare dayayi magana ba,
" dan Allah ka tashi mu tafi, ko ka bud'e min k'ofar na tafi,
kaga dare yayi har anyi sallar ishshsha,
idansa ya bud'e da suka koma pure red,
ya zuba mata su, batare daya motsa daga inda yake zaune ba,
kallansa ya mayar ga tissue d'in,
yayi alama da idansa data d'auka ta goge fuskarta,
sanin matuk'ar bata d'auka tayi abinda yace ba,
sai dai su ta zama anan,
yasata d'aukar tissue d'in ta goge fuskarta,
bayyi mata magana ba ya mik'e ya bud'e k'ofar,
da sauri ta fita yadda kasan ana hankad'a ta,
bayanta yabi da kallo yayi wani irin ajiyar numfashj had'i girgiza kansa kana yabi bayan ta.
K'ofar gidan su yayi parking batare daya bud'e k'ofar motar ba,
k'ok'arin bud'e k'ofar motar ta shiga yi,
taji ta a kulle, kallansa tayi had'i da zuba masa ido batare datace masa komai ba,
kansa ya kauda gefe yana kallan waje,
muryarsa can k'asa yace *kiyi hak'uri,"*
yayi maganar kamar bashi ya fad'a ba,
kallansa tayi cikin mamaki kana tace " akan me?
"Ki yi hak'uri, ya kuma fad'a yana kallan waje,
murmushin yak'e tayi dan tasan idan ta tsaya zasu iya kwana nan,
tace " bakomai, Allah ya yafe mana gaba d'aya,
bayyi magana ba, yayi unlocking k'ofar,
fita tayi da sauri tana mamakin yau Sir Moli da kanshi ya bata hak'uri,
kallanta yayi yaga yadda take sauri kana yaja motar yabar wajen.
Duk duniya yanzu babu abinda ya damu Khulud kamar kewar Sanahrta,
wayarta dake gefe ta d'auka tayi dialing number Sanah,
wayar na fara ringing Sanah ta d'aga,
tana dariya tace " uhmm kaga amarya Hanash Waseef,
Khulud ta turo baki kamar Sanah tana kallanta tace " my Sanah Allah nayi fushi,
Sanah ta zaro ido tace " me kuma nayi?
Khulud tace " oho ban sani ba,
Sanah tace " please mana,
Khulud " amma yau fa 2 weeks nake dashi a gidan nan baki zo ba,
Sanah tayi dariya tace " ai barinki nayi kici amarci,
Khulud tace " amarcin banza,
ni dai yaushe zaki zo,
Sanah tace " ki bari sai weekend sai nazo na yini,
Khulud tace " a'a ni dai kizo yau,
Sanah tace " yau yamma tayi ki dai bari sai gobe,
Khulud tace " are you sure zaki zo goben?
Sanah tace " in sha Allah,
hira sukayi sosai kana sukayi sallama,
washe gari ta shirya ta nufi gidan Khulud,
tana shiga harabar gidan taga Hanash na k'ok'arin shiga mota,
yana ganinta ya fasa shiga ya tsaya had'i da hard'e hannunsa a k'irji,
ya kafe ta idansa,
nufarshi tayi tana dariya kamar wani abu bai faru,
cikin fara'a tace " ango!
" ke! uban me ya kawo ki gida na?
Shiru tayi batayi masa magana,
yace " ko gidan ubanki ne?
Still shiru tayi, ya kuma cewa " kina da gado cikin gidan?
Ido kawai Sanah ta zuba masa batare datace masa k'ala ba,
yace " ni gida na ba gidan 'yan iska da karuwai bane,
dan haka karki kuma zuwanmin gidan,
in ba haka ba, wallahi duk abinda nayi miki ke kika ja,
ba musu Sanah ta juya ta fita zuciyarta tayi mata k'ona kamar zata fashe,
sai da Sanah ta koma gida kana ta kira Khulud,
tayi mata k'aryar suna da test,
tayi hak'uri next week zata zo.
Yau kimanin wata d'aya da sati biyu kenan da zuwan Sanah gidan Sir moli har wannan zuwan ya zama sanadin da yayi romancing da ita, tun daga wannan ranar har yau Sir moli azumi yakeyi da isiqfari da neman yardar Allah, yayi niyar bazai bar yin azumin nanba har sai yaji a jikinsa ubangijinmu ya yafe mishi, ya kuma k'ara dagewa da azumin da addu'o'in Allah ya sassauta mishi wani abun da yake yawan ji matuk'ar yana tare da Sanah, Sir moli bawan Allah ne tsarkakekke bai taba kusanta kanshi da zina ba ko saudaya a rayuwarsa duk da zama cikin turawa da yayi, shiyasa yanzu da haka ta faru yake matuk'ar jin kunyar kanshi da tsoron abinda ya aikata, shiyasa kullum yake azumi sai ran jumma'a-jumma'a yake hutawa.
Khulud na kitchen tare da Hanash tana girki yana taya ta,
ya motsa jikinta ya rungume ta baya yace " Allah yasa nan da 8 months mu samu baby,
ido ta zaro tace " 8 months kuma?
Yace " eh! man, ai nasan zuwa yanzu na saka kwai na,
ya fad'a yana shafa cikinta,
dariya tayi tace " da wuri haka?
" To me zamu jira!?
Tace " wai meyasa kai kullum baka da wata magana sai ta haihuwa da yara,
kab'arsa ya d'ora bisa kafard'arta yace " wallahi Khulud bani da burin daya wuce naga yara na a duniya,
ina mugun san yara da yawa Allah,
kinga ma Jadda kullum bata da wata magana sai ta samun yara,
kullum tambayarta matarta nada ciki,
murmushi tayi kana tace " Allah ya bamu masu albarka ya amsa da " Amin,
girgikin ta gama ta zuba a food flask,
ta juyo ta kalle shi tace " to ga na my Papu,
dariya yayi yace " shiyasa kullum babu bashi da wata magana sai taki,
dariya tayi tace " ai haka ake so,
to mu gama cin abincin sai mu kai musu ko?
Cikin zumud'i tace " da ni zakaje,
"eh! yace , yana fita da abincin,
sai da suka gama kintsawa kana sukayi gidan Mimmee,
part d'in Jaddah suka fara shiga saboda kar tayi musu k'orafi,
zaune suka iske ta a parlor,
tana ganinsu ta mik'e idanta nakan cikin Khulud,
tayi murmushi tace " mai ciki da kanki, meyakun kiyi mana waya mu muzo?
Dariya Khulud tayi tana sunne kanta,
Jadda tayi murmushi tace " kin ganni nan harna fara siyan kayan haihuwa ta fad'a jawo wata leda,
bud'ewa ledar tayi ta shiga ciro kayan jarirai kala-kala,
Hanash yayi dariya yace " kai Jadda wannan ai har kin fimu zamud'in haihuwar,
tana dariya tace " ai dole d'an Hanash guda,
ai duk ranar da aka haife yaron nan zaiga gata,
ji nake kamar na jawo watannin haihuwar,
murmushi sukayi kana sukayi mata sallama,
suka shiga part d'in Mimmee,
babu kowa a parlor'n, dan haka Hanash yayi sallama da k'arfi,
Papu ya fito daga gyms room,
yana murmushi cike da so da jin dad'in ganinsu,
dan harga Allah Papu yana mugun san Khulud,
yana jinta har cikin ransa, yana jin babu abinda bazai iya yi mata ba,
kullum cikin tambayarta abinda take so yake,
amma amsar d'aya ce babu,
har jiran ranar dazata nemi wani abu daga gare shi,
har k'asa suka durk'usa dukkansu suka gaidashi,
ya amsa cikin fara'a,
Hanash yace " Mimmee fa?
Papu yace " sun tafi kasuwa dasu Wajnah,
Hanash yace " dama 'yar gaban goshinka ce tayi maka girki,
Papu yayi murmushi yace " masha Allah, a zubo min naci,
Khulud ta mik'e ta shiga kitchen ta d'auko plate da serving spoon ta zuba masa sakwara da miyar agushi data gashi dajin dry dish da sukunbiya had'i da ganda,
Papu yace " kai masha Allah gaskiya nagode sosai,
Papu ya zage yaci abincin sosai ya k'oshi,
ganin har yamma su Mimmee basu dawowa yasa su Hanash tafiya.
Su Khulud na tafiya kiran Sanah ya shigo,
da sauri tayi picking amma batayi mata magana ba,
Sanah tace " hello my Ulud!
Khulud tayi mata banza,
Sanah tace " kiyi hak'uri idan laifi nayi,
still Khulud batayi mata magana ba,
Sanah tace " kiyi man magana please,
fashewa da kuka Khulud tayi wanda yasa Hanash saurin yin parking,
yace " lafiya my wife,
bata kalle shi ba, tace " haba my Sanah ace har shiga wata na biyu amma baki zo kin ganni ba,
d'an tsoki Hanash yaja jin dailin kukanta kana yaja motar,
Sanah tace " kiyi hak'uri gobe zan zo na yinar miki kinji my Ulud,
cikin murna Khulud tace " Allah da gaske goben zaki zo?
Sanah tace " Allah nayi miki alk'awarin zanzo na yini ma,
cikin zumud'i Khulud tace " me zan dafa miki?
Sanah tace " no karki bawa kanki wahala,
ki bari idan nazo sai mu girka tare Khulud tace " OK badamuwa,
har suka isa gida Sanah da Khulud na waya.
Washe gari da wuri Sanah ta shirya,
driver ne ya kaita a k'ofar gidan ta sauka ta shiga cikin gidan,
tsaye ta ganshe sanye da jallabiya,
da gani yasan da zuwan nata ita yake jira,
"sannu da zuwa mayya makwawaciya,
uwar naci da jaraba,
an kore ki an kore amma dan tsabar jaraba da naci kin dage sai kin zo,
wannan wanne irin naci da jaraba ce,
bata kula shi ba, ta rab'e ta gefensa zata wuce,
da k'arfi Hanash yasa hannunsa ya fisgo ta ya dawo da ita baya,
kana yace " ke! ni sa'an uban ki ne da ina yi maki magana zaki wuce?
" Ko gidan da kike k'ok'arin shiga gidan uwarki ne?
Idanuwan Sanah sukayi jajir saboda tsabar ruwan bala'i,
amma ba damar yin magana,
ga abun gudu sai da ba gurin zuwa,
a cikin kwayar idanta ya hango tsantsar b'acin rai da ruwan masifar dake cinta,
murmushi yayi yace " oh! na manta da tantiriyar fitsararriya mara kunya nake magana,
idanta ta runtse a hankali, sannan ta bud'e had'i da had'iye abinda take ji ,
ta zagaye shi zata wuce,
da k'arfi ya kuma jawo ta had'i da kifa gigitaccen mari,
kana ya hankad'a baya ta fad'i k'asa,
nunata yayi da yatsa yace " wallahi kika kuma k'ok'arin shiga cikin gidan nan sai nayi miki jahilin bugu dan ubanki,
shegiya kamar gidan ubanta ko da gadanta cikin gidan,
still batayi mishi magana ba ta mik'e ta kakkab'a jikinta,
ta kalle shi ido cikin ido tace " kaci darajar masu daraja,
kaje kaci albarkacin alk'awarin daya yiwa Khulud,
kuma duk d'an halak cikekken mutum baya karya alk'awari,
k'ara d'auke ta yayi da mari,
sai da ta kifa saboda k'arfin marin,
kana yace " lalle 'iskanci da rashin kunyarki sun rik'a in banda haka kizo har cikin gida na ki nemi gaya mana magana,
to bari kiji matuk'ar san da kikewa Khulud gaskiya ne,
matuk'ar kina san farin ciki da walwalarta su d'ore kiyi nesa da ita da gidanta,
zatayi magana yasa hannunsa ya rik'o hannunta ya soma janta a da k'arfi har tana fad'uwa yana fizgota
sai da ya kaita har waje kana yacewa mai gadi " duk ranar daka k'ara barin wannan ta shigo a bakin aikinka,
Ita kuwa Khulud na parlor zaune tana zaman jiran Sanah,
haka kawai taji gabanta na fad'uwa,
a hankali ta mik'e ta shiga bedroom wajen Hanash,
ganin baya nan yasa ta lek'awa bathroom nan ba baya nan,
a hankali ta juya zata fito,
karaf idanta ya sauka akan Hanash dake tsaye bakin get yana zazzaga ruwan bala'i,
a kamar mutun ta hango a durk'ushe a gabansa,
a hankali ta k'ara lek'awa dan taga wanda ke durk'ushen amma bata gane ba,
bata wani damu data gani ba, dan haka tayi komawarta parlor ta zauna,
d'an tsoki taja had'i da kallan agogo,
a hankali tace " kodai my Sanah bazata zo ba?
Ta tambayi kanta,
baki ta tab'e kana tace " Hanash ko shida wa oho!
yake ta bambami,
gabanta ne yayi muguwar fad'uwa tunowa da tayi Sanah,
da sauri ta mik'e ta koma bedroom d'insa ta kuma l'ek'awa ta window,
ganin still bata ganin wanda ke durk'ushen yasa juyawa ta fita da gudu ta nufi harabar gidan...................
*Alhamdulillah wata ya tsaya, inai mana fatan muyi azumin Ramadan lfy, Allah kuma ya amsa mana ibadunmu*
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
_DIDECATED TO_
*MY AUNTY AYSHA ALIYU GARKUWA*
(```GARKUWAR MARUBUTA```)
~MY UWAR ROOM~
2⃣8⃣
Khulud ba ko takalmi ta k'arasa harabar gidan,
shi kuma dai-dai lokacin ya juyo yana niyyar shiga cikin gidan,
a tsakiyar compound suka had'u,
kallanta yayi kana yace " lafiya?
" Lafiya ta bashi amsa tana hangawa bayansa,
bayan nasa shima ya juya ya kalla kana ya mayar da idansa kanta,
yace " me kike dubawa?
" My Sanah ta bashi amsa,
" oh!, yace yana rik'o hannunta,
da nufin shigar da ita cikin gidan,
k'in binsa tayi ta tsaya cak, tana kallansa a marairaice,
yace " me kuma?
" Ina My Sanah ta tambaye shi,
wata muguwar fad'uwa gabansa yayi,
amma ya dake kamar babu komai yace " kamar ya?
Tace " bada ita na ganku yanzu kuna magana ba?
Murmushi yayi had'i da sungumarta cak,
yayi cikin gidan da ita, cikin sanyin murya tace " please my Sanah!,
murmushi ya kuma yi yace " oh! wannan duk d'okin ganin our Sanah ne?
Zata kuma yin magana yayi saurin had'e bakinsu,
yana cewa muje na gaisa da baby na,
dan nasan idan our Sanah tazo ba'a da lokaci na,
ya fad'a yana tura k'ofar bedroom da k'afarsa,
dole tasa Khulud yin shiru amma badan taso ba,
dan gaba d'aya hankalinta yana kan Sanahrta,
kwantar da ita yayi a kan bed yana cigaba da shan bakinta,
had'i da shafa jikinta, a hankali ya rabata da kayan jikinta,
kana ya kashe arna, Hanash bai wani samu yadda yake so ba,
dan Khulud bata sakar mishi jikinta yadda ya kamata ba,
bata kuma taimaka mishi wajen bashi hakk'in nasa ba,
dan kwata-kwata bata cikin hankali da nutsuwarta,
dama ko ba yanzu ba,
yana fuskantar irin wannan matsalar daga wajen Khulud,
dan kwata-kwata bata da wayewa a wajen sex,
kwanciya takeyi kamar ruwa sai dai shi ya sarrafa ta,
amma even romance Khulud bata iya yi mishi,
farko-farko ya d'auka kunya da rashin sanin, da kuma rashin sabo da abun ne ke damunta,
amma yanzu gashi kusan 3 months da auren su,
amma still bata san komai ba,
gashi shi ba abokanai ba balle ya kaita wajen matan su suyi mata bayani,
kuma shi kunyarta yake ji bai iya yi mata bayani da kansa,
dan gani yake kamar cin fuska da wulak'anci ne,
shi yadda ake fad'ar ana mugun jin dad'in sex shi bai wani ji,
dan wani lokacin ma sai yayi da gaske yake yin releasing,
tun abun bai damunshi har abun ya fara damunshi sosai,
wani lokacin koda yana cikin buk'ata hak'ura yake yi,
dan bai san shan wahala a banza,
bayan komai ya lafa tsakanin Hanash da Khulud ya jawo ta jikinsa ya rungume ta tsam a k'irjinsa.
Yana shafa kanta, deep down kuma yana sak'e-sak'e a ransa,
yana jin inama zai iya fitowa ya fad'a mata gaskiyar abinda ke ranshi,
sun kai 15 minutes a haka kana ta mik'e ta shiga bathroom,
tayi wankan tsarki ta shirya,
wayarta ta d'auka da nufin kiran number Sanah,
Hanash yayi saurin cewa " my love yunwa nake ji bani abinci naci,
ido ta zaro waje tace " yanzu fa kaci abincin,
yayi kyakkyawan murmushinsa kana yace " bakiga uban aikin danayi yanzu ba?
" Ai dole naji yunwa tunda kin zuk'e abincin dana ci,
bata kuma cewa komai ba saboda kunyar abinda ya fad'a,
ta juya da sauri ta nufi kitchen,
tana fita yayi saurin d'aukar wayarta ya sanya number Sanah a black list,
bata jima da fita ba ta dawo d'auke da tray,
sai da yaci abincin sosai kana ya shiga wanka.
Sai da Sanah ta tsaya a bakin get d'in da Hanash ya hankad'o ta,
taci uban kukanta sosai, kana ta share hawayenta,
ta mik'e ta nufi bakin titi,
tana tafe hawayen bak'in ciki na sake zubo mata,
Allah ya taimake ta tun kafin ta k'arasa bakin titin ta samu mai napep,
da sauri ta tsaida shi ta shiga ta zauna,
sai da ta zauna kana ta fad'a masa inda zai kaita,
sai da ta tsaya a bakin get d'in shiga gidan su,
ta saita kanta kana ta shiga, dan bata san kowa ya fuskanci abinda ke faruwa tsakaninta da Hanash,
bata tsaya shiga part d'in Halan ba tayi shigewarta part d'in Mamu kai tsaye,
a parlor ta iske Mamu tana jera abinci a dinning,
kallo d'aya Mamu tayi mata ta fuskanci da akwai matsala,
da sauri Mamu ta nufe ta tana cewa " ke lafiyarki?
Murmushin k'arfin hali Sanah ta k'ak'aro kana tace " meye Mamu?
Mamu ta kalle ta cike da mamaki tace " ban gane me ba?
" Bayan ga fuskarki nan da idanki sun nuna kinyi kuka,
rolling sexy eyes d'inta tayi kana tace " kuka kuma Mamu?
Mamu tace " ke ban san rainin hankali,
zanci ubanki wallahi, ni kike san yiwa yawo da hankali dan gidan ku?
Sanah ta zumb'uro baki kana tace " ni fa babu komai Mamu,
Mamu tace " wai tsaya ma, ba gidan Khulud kika tafi ba?
Sanah tace " ni kuma?
Ta fad'a tana zaro idanta waje,
" ni bance zani gidan Khulud ba,
Mamu tace " kan uba!, ke ni kike san maidawa mahaukaciya ko me?
" Idan ba gidan Khulud kika ce zaki ba, gidan ubanki kika ce zaki?
Sanah tace " a'a ni test naje nayi,
Mamu tace " oh! ni Allah na, Ubangiji ya kawo mu wannan lokacin,
yanzu Sanah ni zaki yiwa yawo da hankali dan ubanki yanzu kina nufin har kinje BUK,
kinyi test kin dawo ko me kike nufi?
Ta fad'a tana kallan Sanah a k'ufule,
Sanah tace " kai Mamu dan Allah kiyi hak'uri ki kwantar da hankalinki mana,
cikin fad'a Mamu tace " a gidan ubanki zan kwantar da hankalin nawa,
kin fita kin kuma dawo min gida kina kuka,
sannan kina neman raina man hankali,
amma ina zuwa,
ta fad'a tana nufar inda ta ajeye wayarta,
ta d'auka had'i dayin dialing number Khulud,
da sauri Sanah ta k'arasa inda Mamu ke tsaye fuskarta d'auke da tsoro tace " me zakiyi Mamu?
Mamu bata kula ta ba,
ta maida hankalinta ga abinda take yi,
Khulud na zaune kusa da Hanash taji wayarta na ringing,
bai wani damu ba saboda ya san ya saka number Sanah a black list,
da sauri Khulud tayi picking ganin number Mamu,
cikin girmamawa Khulud ta gaida Mamu,
Mamu ta amsa kana tace " Khulud ba gidanki Sanah tazo yanzu ba?
Sanah najin Khulud Mamu ta kira tayi saurin zaro ido,
Khulud tayi shiru ta rasa amsar da zata bayar,
a hankali tace " lafiya Mamu?
Mamu tace " 30 minutes back tayi man sallama tace " ta tafi gidanki,
amma yanzu ta dawo cikin damuwa kuma da gani taci uban kuka sosai,
ido Sanah tayi rolling,
itako Khulud idanta ta zaro tana yiwa Hanash kallan zargi،
kana ta cewa Mamu bani Sanahr,
Mamu tace " kamar ya na baki Sanah?
" Karku had'u kuyi min yawo da hankali,
tambayarki nayi dan haka ki bani amsa,
cikin sanyin murya Khulud tace " eh nan tazo,
Mamu tace " meya faru da har tayi kuka?
Khulud tayi shiru na d'an wani lokaci kana tace " wai cikinta ke ciwo,
Mamu tayi tsaki kana tace " Allah ya shiryeku,
cikin sanyin Khulud tace " Mamu bani ita please,
Mamu tace " ai kina da phone number ta ki kira ta mana,
Khulud zata kuma yin magana Mamu ta kashe wayarta,
bata k'ara bi takansu ba ta cigaba da subgoginta,
cikin sanyin jiki Khulud tabi wayar da kallo na wani d'an lokaci,
kana ta k'urawa Hanash ido tana karantar yanayinsa,
" me!?
Yace, yana kallanta, yayinda gabansa ke fad'uwa,
idanta na kansa tace " me kayiwa My Sanah?
Da sauri ya mik'e zaune kana yace " kamar ya menayi mata?
Idan Khulud na kansa still tana karantarsa tace " please me kayi mata?
" Wani abun tace nayi mata?
Ido ta kafe shi dashi batare data kuma cewa komai ba, shima shirun yayi bai ce komai ba,
wayarta ta d'auka,
tayi dialing number Sanah amma sai taji not reachable,
bata kawo komai a ranta ba ta aje wayar,
itama Sanah nacan na faman neman layin Khulud amma busy yake nuna mata.
Tunda Sir Moli ya lura matuk'ar ya keb'e da Sanah yana loosing control,
yasa shi yin nesa sosai da ita,
ya gujewa duk wani abu da zai keb'anta shi da ita,
dan shi kansa yana mugun mamakin kansa,
ya rasa meyasa yake shiga wani yanayi idan yana tare da ita,
ya rasa meyasa yake mance kansa idan yana tare da ita,
shi dai yasan a iya tsayin rayuwarsa bai tab'a kusantar zina ba,
ya zauna da turawa, larabawa, indiya da sauran jinsunan duniya,
amma bai tab'a tsintar kansa da irin haka ba,
sai akanta,
sosai ya dage da yin azumin nafila da istigfari,
saboda neman tsira dan gani yake kamar ya aikata babban laifi.
Yauma bayan sun gama attending lectures,
bata fito ba sai gab da magariba,
ganin yanayin garin na damuna ga kuma dare na neman kawo kai,
yasa Sanah yin sauri sosai,
tun daga nesa ya hangota,
yayinda dashi ke zaune cikin motarsa k'irar ferrari,
yana driving,
idansa ya lumshe lokacin dayazo zai wuce ta dai-dai ita,
yana san taimaka mata ya d'auke ta,
amma baijin zai iya yin haka,
dan gudu da kaucewa duk abinda zai kai shi ga keb'ewa da ita,
balle har a samu sab'anin da zai iya kawo shigar wani abun a tsakaninsu,
motar Sanah tabi da kallo had'i da tab'a bakinta tace " kai dai ka sani.
Hanash kwance akan k'ayataccen royal bed d'insa,
ya fad'a duniyar tunani,
idan da abunda yafi damunsa yanzu a duniya bai wuce na rashin gamsuwa da jin dad'in sex da bayayi ba,
saboda kwata-kwata baya samun ishashshiyar gamsuwa,
ba wai dad'i ko ruwan ni'ima ne Khulud bata dashi ba,
tana da ni'ima sosai kamar me,
dan ruwan ni'imarta har mamaki yake bashi wani lokacin idan yaga yadda take b'ulb'ulo da ruwa daga k'asanta,
shi abinda ke damunsa
kwata-kwata bata iya sex ba,
bama tasan yadda zata yi sex d'in ba,
ga rashin samun had'in kanta wajen sex,
da rashin taya shi, kwata-kwata bata iya komai ba,
ba kuma tasan komai,
shi kad'ai yake kid'ansa yake rawarsa,
ko romance bata iya ba, gashi bata iya sex styles and irin kukan kissa da nuna irin tana enjoying sosai ba,
sai dai ta kwanta kawai kamar ruwa,
shi zayyi komai ya sauka,
wannan abun yana matuk'ar damunsa,
dan tun abin baya damunsa yanzu har abun yazo ya zame mishi babban matsala,
dan wasu lokutan ma yana bala'in jin haushinta,
dan ji yake kamar ya rufe ta da duka,
ita ko irin shigewa jikin miji, da nanik'ar miji batayi,
ko irin zama akan cinyarsa batayi,
kwata-kwata ba romantic girl bace,
shi kuma gashi so hot romantic,
yana bala'in san irin rayuwa da soyayyar turawa,
yana san koyaushe ya kasance matarsa tana nanik'e dashi,
yana bala'in san mace mai san jiki,
da iya love, & romancing,
sosai yake cikin damuwa, ya rasa ta inda zai b'ullo mata,
ya rasa ta hanyar da zai bi yayi mata bayani,
yana tsaka da tunaninsa ta shigo,
zama tayi a bakin bed d'in fuskarta d'auke da murmushi tace " breakfast is ready Sir,
idanshi na kanta yace " ji babu ko d'an sexy abu balle romantic,
babu even kiss, just breakfast is ready,
ya fad'a cikin ransa,
a fili kuma yayi mata guntun murmushi,
kana ya mik'e ya shiga bathroom batare dayace mata komai ba,
mik'ewa tayi ta fita ta koma parlor,
yana jin fitarta ya tab'e baki had'i da cewa " even wanka da miji bazata iya ba,
dan duk wad'annan abubuwa babu yadda bayyi ya koya mata ba amma tak'i ta d'auka,
sai da yayi wanka ya shirya kana ya fita parlor'n,
a parlor ya same ta zaune, tana ganinshi tayi saurin mik'ewa tana murmushi,
shima murmushin yayi mata kana suka zauna a dinning table,
serving d'inshi farfesun kayan ciki da soyayyar doya da miyar kwai tayi,
sama-sama ya d'an tsakuri abincin ya mik'e,
da sauri ta kalle shi ta kalli abincin tace " wai kana nufin har kayi me?
Murmushi yayi mata yace " Alhamdulillah na k'oshi,
bata kuma yin magana ba ta mik'e rik'e da brief case d'insa,
" ba ko tarairayar miji, ko irin ta saka ni gaba tana yi man shagwab'a tana tarairayata akan dole sai naci abincin babu,
ina cewa nak'o shi shikenan, bayan tasan ba iya abinda na saba ci kenan ba,
ya fad'a cikin ranshi,
har bakin mota Khulud ta raka shi ya shiga kana ta koma cikin gida.
Kullum sai Khulud tayi ta
faman kiran number Sanah amma not reachable,
haka itama Sanah kullum cikin kiran number Khulud take amma busy,
dukkansu basu kawo komai a ransu,
dan haka suka cigaba da harkokinsu,
haka ma sau uku Sanah na zuwa gidan Khulud mai gadi yana hanata shiga,
daga k'arshe ma rok'arta yayi akan dan Allah karta k'ara zuwa saboda mai gidan yace zayyi asarar aikinsa,
dole Sanah ta hak'ura ta daina zuwa gidan Khulud,
haka duk sanda Hanash zai kai Khulud gida,
sai ya tabbatar da Sanah bata gidan,
sannan zai kaita, kafin ta dawo kuma sun bar gida,
haka suka cigaba da rayuwa lokaci na tafiya har Khulud tayi wata hud'u da aure,
amma ko sau d'aya basu tab'a had'uwa da Sanah ba,
tun bayan aurenta,
su dukkansu basu tab'a tsammanin zasuyi kwana d'aya a rayuwarsu batare da sunga juna ba.
Su Khulud na zaune a parlor'n Mimmee ita dasu Zohal,
Mimmee ma na zaune gefensu,
Zohal ta kalli agogo tace " kinga har 3:30pm na rana tayi,
muyi sauri mu fita kafin Yaya ya dawo,
yanzu daya dawo sai yace yamma tayi babu inda zamu mu bari sai gobe,
Khulud tace " gaskiya kam muyi sauri dan nima ina san zuwa saloon d'in nan wallahi,
Mimmee tace " ta ku tashi kuyi sauri ku shirya mana,
kun tsaya kuna surutu, Khulud tace " mu ai mun shirya Wajnah kawai muke jira,
Mimmee tace " ina Wajnah nan?
Zohal tace " tana bedroom tana ta faman k'ak'ale-k'ak'ale kema ai kinsan halin shirinta,
Mimmee tace " ikon Allah ta kuje ku kirata mana,
kafin suyi magana Wajnah ta fito tana cewa " gani ma na fito ai,
babu wanda yayi magana duk suka mik'e Mimmee ta bisu da kallo d'aya bayan d'aya,
suna k'ok'arin fita Jaddah ta shigo,
tana binsu da kallo, kana tace " ina zuwa?
"Saloon cewar Zohal,
kallan Khulud Jaddah tayi kana tace " wajenki fa nazo,
Mimmee ta kalli Jaddah cikin mamaki batare da tace komai ba,
Khulud ta durk'usa har k'asa tace " ina yini?
Jaddah bata amsa gaisuwarta ba,
tace " ke wai har yanzu ba wani labari ne?
Khulud ta kalleta cikin rashin fahimta,
tace " me Jaddah!?
Jaddah tace " watan ku hud'u kenan da aure amma har yanzu banji kin fara 'yan amaye-amaye,
da rashin lafiyar laulayi ba,
ko har yanzu babu komai,
ni fa kin san babu abinda nafi so sama da ganin yaran Hanash ato kima dage,
Khulud durk'ushe agaban Jaddah kanta na k'asa,
daga Mimmee har su Wajnah babu wanda yace k'ala,
dan sanin halin Jaddah sarai,
Papu dake sakkowa daga samansa yace " Jaddah ba sai Allah ya kawo ba tukunna,
ai basu isa su bawa kansu ba,
sai idan Allah yaga dama ya basu tukunna,
kallan Papu tayi cike da mamaki dan hakan bata tab'a faruwa ba,
tunda take dashi bai tab'a mayar mata da magana ba sai yau akan Khulud,
Khulud ta kalla kana ta juya zata fita,
harta kai bakin k'ofar fita ta kuma juyowa tace " ni dai na fad'a miki,
kana tasa kai tayi ficewarta,
Papu ya k'arasa shigowa cikin parlor'n,
a hankali Khulud ta juya tana gaida Papu,
cike da fara'a ya amsa kana yace " kiyi hak'uri kinji?
Murmushi tayi tace " lah bakomai Papu,
yayi murmushi shima,
kana suka fita.
Washe gari Sanah bata shiga makaranta ba sai around 10:30am na safe,
saboda bata da lafiya zazzab'i da ciwon kai ke damunta sosai,
a hankali take tafiya dan ji take kamar zata fad'i saboda jirin dake d'ibarta,
in banda suna da test da Sir Moli babu abinda zai kawo ta makarantar,
tana shiga class Rose ta nufo ta da sauri ganin yanayin datake ciki,
dan tun da suka samu d'an sab'anin nan suke shiri,
Rose tace " meke damunki,
murmushi Sanah tayi kana tace fever & headache,
cike da tausaywa Rose tace " ayya sorry,
gashi har anyi test baki nan,
da sauri Sanah ta d'ago kanta tace " Sir Aryan har yayi test d'in!!?
Rose tace " yes! tun around 9:30am na safe,
kai Sanah ta dafe had'i da cewa " ya salam!
shiru tayi na wani lokaci kana ta kalli Rose tace " please ki raka ni office d'insa,
Rose ta zaro ido waje cike da tsoro tace " am sorry sister babu abinda zaki tambaye ni na kasa yi maki,
amma ban iya rakaki office d'insa,
shiru Sanah ta kuma yi,
batare data kuma cewa Rose komai ba,
ta nufi office d'insa,
sallama tayi ya bata izinin shigo,
a hankali ta tura k'ofar ta shiga,
yana kishingid'e akan sofa,
idanuwansa lumshe,
ta durk'usa a gabansa,
saboda ji take kamar zata fad'i,
cikin muryar marasa lafiya tace " Sir!,
bai ko motsa ba balle ya bud'e idansa ko yayi mata magana,
muryarta na rawa ta kuma cewa " Sir!
a dak'ile yace " fad'i,
"Sir banyi test ba,
" sai akayi yaya?
Ya fad'a bai motsa daga inda yake ba,
" bani da lafiya ne, ta fad'a muryarta ba creaking,
" me zanyi miki to?
Ya kuma fad'a bai motsa ba,
"dan Allah kayi man tawa!
ta fad'a tana kallanshi,
shiru yayi baice komai ba,
Khulud na kwance a parlor Hanash na gefenta zaune,
tayi saurin mik'ewa ta,
a hankali Hanash ya d'ago kansa ya kalleta,
yace " lafiya naga kin zabura!?
"Ki rink'a bi a hankali saboda unborn d'ina,
dariya tayi tace " kai komai Baby,
shima dariyar yayi kana yace " shine babban buri na a duniya,
wallahi komai za'a bani bai kai na samu Baby ba,
bani da wani sauran buri ko muradi daya wuce na ganni da d'a ko 'ya nawa na kaina,
idan naga Baby na bani da sauran buk'ata a duniya,
murmushi tayi had'i da cewa " Allah ya bamu basu albarka,
ta fad'a tana nufar bedroom d'inta,
wayarta ta d'auko ta dawo parlor ta zauna had'i da kunna data ta shiga WhatsApp,
ta shiga sunan Sanah jikinta na rawa dan basirar yi mata voice note bai tab'a zo mata ba sai yau,
muryarta na rawa tace " My Sanah kina kusa please?
"Idan kina kusa kiyi man magana,
Sanah na durk'ushe gaban Sir Moli taji notification na WhatsApp,
kamar bazata duba ba, sai kuma ta duba,
ganin Khulud ce yasa ta saurin kunnawa a speaker,
Sanah tayi murmushi kana tace " ina kusa my Khulud,
Khulud na rik'e da waya tana jiran amsa,
taji k'arar shigowar sak'o, da sauri ta duba,
kuka Khulud ta saka had'i cewa " me nayi miki My Sanah?
Sanah tayi playing, a hankali ta lumshe idanta jin Khulud tana kuka,
kana tace " meye my Ulud?
Khulud tace " au meye ko?
Sanah tace " eh mana,
cikin kuka Khulud tace " haba my Sanah yanzu fa na shiga 5 months da aure amma baki tab'a zuwa inda nake ba,
tunda nayi aure bamu sake had'uwa ba,
wallahi ko a mafarki aka fad'a min zamuyi 5 months bamu had'u ba ban yarda,
matuk'ar muna raye a duniya,
musamman ma a cikin gari d'aya,
dan Allah idan wani laifin nayi miki ki fito ki sanar dani sai na gyara,
na kuma baki hak'uri,
idan kuma akwai abinda ke faruwa please ki sanar da ni,
dan Allah hukuncin nan yayi man tsauri,
Sanah na danne kukanta tace " kiyi hak'uri kinji my ulud,
komai na duniya muk'addari ne kuma yana da iyaka,
Khulud tace " dan Allah kizo yau please,
Sanah ta lumshe idonta hawaye na zuba,
tace " kiyi hak'uri my Ulud ban iya zuwa dan bani da lafiya,
Khulud ta tura mata amsa cikin tashin hanakali " subhanallah meke damunki?
Sanah tace" fever & headache,
Khulud tace " kina ina yanzu?
Sanah tace " ina makaranta,
Khulud tace " yaushe zaki dawo gida?
" Sai dare, Sanah ta fad'a while hawayen bai bar fita ba,
Khulud tace " to dan Allah gobe karki je ko'ina zanzo,
Sanah tace " tom zan jira ki in sha Allah,
sai da sukayi hira kana sukayi sallama,
Hanash na jinsu, suna gama wayar ya jawo ta jikinsa ya rungume batare dayace komai ba,
suna gama chart d'in Sanah ta saka kukan da take dannewa,
Sir Moli yana nan yadda yake baiko matsa ba, idanuwanshi lumshe,
sai da taci kukanta ta k'oshi kana ta mik'e zata fita,
har takai bakin k'ofar fita,
yace " meke faruwa tsaninku ku ukun?
Cak ta tsaya had'i da juyowa a hankali,
red eyes d'inta ta d'aga ta kalle shi,
taga yana nan yadda yake,
batayi niyyar b'oye masa komai ba,
dan haka ta fad'a masa tun daga zuwanta na farko gidan har zuwanta na k'arshe bata b'oye masa komai ba,
idansa rufe yace " yanzu kina san zuwa ganin Khulud d'in?
Ido ta k'ura masa batare datace komai ba,
a hankali ya bud'e idansa had'i da mik'ewa zaune,
yana kallanta yace " tambayarki nake,
cikin sanyin jiki ta d'aga masa kai,
yace " amma kin san ban san nodding kai ko?
Cikin sanyin murya tace " sorry،
ya kuma cewa " kina san zuwa ganin Khulud?
"Eh! tace tana kallanshi,
a hankali ya mik'e batare daya kuma kallanta ba,
ya zura talmi da hularsa,
kana yace " muje,
da sauri ta kalle shi tace " ina?
" Ban sani ba, yace yana fita daga office d'in,
bayansa tabi a hankali kasancewar jikinta babu kwari,
office d'in ya rufe kana yayi gaba batare daya kalle ta ba،
binsa tayi a baya har suka isa motarsa,
bayyi mata magana ba ya bud'e ya shiga,
tsaye tayi bakin motar tana kallanshi,
harara ya watsa mata,
ganin hararar dayiyi mata yasa ta zumb'urar baki kana ta bud'e motar ta shiga,
Sir Moli bai tsaya ko'ina ba sai a unguwar su Khulud,
dai-dai inda yaga Sanah da daddare,
batare daya kalle ta ba yace " ina ne gidan?
Nuna masa ta shiga yi har suka k'arasa bakin get,
sosai gaban Sanah ke muguwar fad'uwa saboda bata san abinda zai jawowa Khulud matsala a zamantakewar aurenta,
dandai babu yadda zatayi da Sir Moli ne,
yasa ta biyo shi, musamman ma da irin zargin da Hanash yake yi musu,
horn yayi mai gadin ya lek'o, kasancewar motar tine tac ce yasa bai ga Sanah ba,
kuma daya ga motar babbar motace d'auke da private number yasa shi,
tsayawa yana tunani dan shi ba'a sanar dashi akwai bak'i ba,
ganin haka yasa Sir Moli zuge glass d'in motar a hankali,
ya lek'o da kansa yace " bud'e,
ya fad'a a tak'aice,
ba musu mai gadin ya hangame get d'in,
Sir Moli ya danna motarsa cikin gidan kanshi tsaye,
lura da yadda Sanah take yasa shi cewa " fita،
fuska ta kwab'e kamar zatayi kuka tace " please mu koma,
bai kalle ta ba, yace " nace ki fita ko!?
Yayi maganar a d'an hasale,
a hankali Sanah ta kwab'e fuska had'i da cewa " to dan Allah karka tafi ka jira ni,
bai amsa bata ba, ya kawar da kanshi gefe,
a hankali Sanah ta bud'e motar ta fito,
mai gadi na ganin Sanah, ya nufo ta da sauri,
jikinsa na kerrma, yace " Hajiya dan girman Allah ki taimaka min karki shiga,
Yallab'ai yana nan, kuma a gabanki yayi min gargad'i,
Sanah zatayi magana Sir Moli ya bud'e motar ya fito,
ya jingina da jikin motar had'i da hard'e hannayensa a k'irjinsa,
yace " gargad'in me yayi maka?
Muryar mai gadin na rawa yace " Yallab'ai ne yace muddin na kuma barinta ta shiga cikin gidan a bakin aiki na,
"Ok Sir Moli yace kana ya mayar da kallansa ga Sanah yace " shiga,
fuska ta kwab'e kamar zatayi kuka tace " please!
mai gadin yayi saurin cewa " dan Allah ku taimaka min،
ina da yara k'anana,
da mata, sannan ga iyaye na,
ga yaran d'an uwana daya mutu,
duk a k'ark'ashi na suke,
ni kuma da wannan aikin kad'ai na dogara,
Sir Moli yace " idan ya koreka kazo zan baka aiki mai kyau,
ya fad'a batare daya kalli inda mai gadin yake ba,
mai gadin yace " ni dai dan Al.........,
hannu Sir Moli ya d'aga masa,
yace " please Baba kayi shiru nace idan ya kure ka zan baka aiki,
kuma dama matsalarka bata aikin bace,
idan kuma aikin ne baka so zan baka jari mai kyau,
shiru mai gadin yayi saboda kwarjinin da Sir Moli yayi masa,
karaf idan Sir Moli ya sauka akan Hanash dake nufar d'aya daga cikin motocin dake jere a harabar gidan,
da alama bai lura da su ba,
daga Sanah har mai gadin babu wanda ya lura dashi,
Sir Moli ya kalle ta yace " karna sake miki magana,
da sauri ta nufi hanyar shiga part d'in,
Sir Moli ya tsaya jikin motarsa had'i da hard'e hannuwansa a k'irjinsa,
ya zubawa Hanash ido,
yana nazarinsa,
shi dai a fuska baiga wani mugun hali ko alamar munana d'abi'u a tattare dashi ba,
sai nutsuwa da kalama had'i da suffar nagartattun mutane,
daya gani tattare da Hanash d'in,
abinda da marar lafiya Sanah na fara takawa tayi taku na uku,
k'afarta ta gurd'e kasancewar takalmin k'afarta mai tudu ne,
jiri ya d'ebeta tayi baya luuuuuu zata fad'i,
cikin matsanancin zafin nama Sir Moli yayi saurin tare ta,
ta fad'a jikinsa,
a tsorace Sanah ta saki 'yar k'ara,
saboda ta gama sadak'arwa ta fad'i,
k'arar da Sanah tayi ce tajawo hankalin Hanash kansu,
ya sauke idansa a kansu dai-dai lokacin da Sanah ta fad'a jikin Sir Moli.
A hasale Hanash ya juyo yana kallansu cikin matsanancin b'akin rai yace " hey! nan ba hotel ko club bane,
ba kuma gidan karuwai da 'yan iska bane,
idan zakuyi iskancinku kuje can kuyi,
tsabar rainin hankali kuzo man har cikin gidana kuna iskancin da kuka sabo yi,
ko an gaya maku nan gidan 'yan iska ne?
Da sauri Sanah ta fara k'oka'rin kwace jikinta daga na Sir Moli,
amma Sir Moli ya k'ara manneta da jikinsa,
idansa akan Hanash yana kallan cikin kwayar idansa,
yana karantar yanayinsa,
had'i da san fassara abinda yake hangowa cikin kwayar idan nasa,
ran Hanash ya kuma mugun b'aci cikin mugun takaici yace " get out from my house,
kwaratan banza, 'yan iska fasik'ai kawai,
guntun murmushi Sir Moli yayi yana k'ara shigewa jikin Sanah,
had'i da shinshinar wuyanta yana goga hancinsa a kumatunta,
ita ko Sanah sai k'ok'arin kwace kanta take yi,
amma ta kasa sai nuk'u-nuk'u take,
tana k'ifk'ifta idanuwa,
ido Hanash ya runtse cike da tsantsar bak'in cikin ganin abinda Sir Moli yake da mace kuma har cikin gidansa,
cikin b'acin rai Hanash yace " I said get out from my house,
nan ba hotel bane, gidan ma'aurata ne,
Sir Moli yayi dariya kana ya saki Sanah ya maida kallansa ga Hanash yacewa Sanah " jeki shiga,
tsayawa Sanah tayi bata ko iya d'aga k'afarta ba,
idan Sir Moli nakan Hanash ya had'e rai sosai,
yadda kasan bai tab'a yin dariya ba yace " nace ki shige ko,
Hanash tsaiwarsa ya gyara yana kallan Sanah,
yace " tazo ta wucen inta isa ita tacacciyar mara kunya ce,
cikin kuka Sanah ta kalli Sir Moli tace " please mu koma na hak'ura da ganin Khulud d'in,
gigitacciyar tsawa Sir Moli ya daka mata cikin b'acin rai yace " nace ki shiga ko!?
Jikin Sanah na kerrrrma saboda tsawar da Sir Moli ya daka mata
bawai saboda tsoran Hanash ba,
ta nufi hanyar shiga gidan,
Khulud dake zaune a parlor ta mik'e ta fito da sauri kasancewar gigitacciyar tsawar dataji Sir Moli ya daka,
dama tun d'azu take jiyo maganganu k'asa-k'asa,
Khulud na fitowa harabar gidan dai-dai lokacin Sanah ta rab'a ta gefen Hanash zata wuce,
a k'ufule Hanash ya maka mata kyawawan marika gudu biyu a jere,
wad'anda sukata zubewa k'asa ba shiri,
karaf akan idan Khulud........
cikin tsananin b'acin rai da zafin zuciya Sir Moli ya.........
Ya azumi da ibada?
Ubangiji ya amshi ibadun mu,
Allah yayi mana rahama da rahamarsa,
yaji k'anmu da jin k'ansa,
Allah yasa muna daga cikin wad'anda za'a yafewa a wannan watan mai albarka.
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
2⃣9⃣
Take duk ilahirin jikin Sir Moli ya d'auki kerrrma da b'ari,
zuciyarsa ta shiga tafasa tana yi masa k'una,
cikin matsanancin zafin rai da k'unar zuciya Sir Moli ya makawa Hanash kyawawan marika guda hud'u a jere,
had'i da sakar masa gigitaccen naushi a cikinsa,
zafin naushin ne yasa Hanash dafe cikinsa had'i da durk'ushewa ya saki k'ara,
Khulud tsaye tayi cak ta kasa koda motsa k'afarta,
ta k'ame a tsaye,
saboda tsantsar mamaki,
Sir Moli ya sunkuya ya d'ago Sanah had'i da manna ta da k'irjinsa,
kallo d'aya zakayiwa Sir Moli kasan ransa yakai k'ololuwar b'aci,
idanuwansa sunyi masifar yin jajir dasu,
ya kalli Hanash yace " kayi gangancin tab'a ta a gaba na,
how dare you da hannunka zai tab'a jikinta?
"Ko an gaya maka ita irin matan nan ce da kowanne Tom and Jerry yake tab'a su,
kaje kaci darajar masu daraja,
amma badan haka ba da sainayi maganinka,
Sir Moli ya fad'a cikin matsanancin zafin rai
a hankali Hanash ya d'ago had'i da nufar Sir Moli gadan-gadan,
cikin zafin nama Khulud tayi saurin shan gaban Hanash,
cikin bak'in ciki da suyar zuciya ta jefa idanta cikin nashi,
yayinda hawaye ke rubdugun zubo mata,
ta kallanshi idanta tarr cikin nashi tace " ashe dama haka kake?
" Wannan itace true color ka?
"Dama na dad'e ina zargin akwai wani abu k'asa,
dan nasan haka nan banza bazai tab'a yiyiwa Sanah ta iya jura getting to 5 months batare data zo ta ganni ba,
Hanash ka ban mamaki, ashe duk abinda kake fad'a k'arya ne?
Baki ta bud'e zatayi magana amma kukan dayaci k'arfinta ya hanata cigaba da magana,
da gudu Baba mai gadi ya rugu ya zabe a gaban Hanash,
had'i da cewa " Yallab'ai kayi min rai,
wallahi ba laifi na bane, sai da nayi musu bayani amma suka k'i ji,
tazo wajen sau biyar ina hanata shigowa,
cike da mamaki Khulud ta tsaida kukanta,
ta maida kallanta ga mai gadin tace " meye Baba?
Cikin rawar murya mai gidan yayi mata bayanin komai,
had'i da cewa " dan girman Allah kayi hak'uri,
ido Khulud ta runtse cike da bak'in ciki,
kana ta nufi Sanah,
Sanah da har lokacin tana manne jikin Sir Moli,
saboda rashin kwarin jikin data ke fama dashi ya hanata kwace jikinta daga gare shi,
duk ilahirin jikinta kerrrma yake,
ganin Khulud ta nufo ta yasa ta saurin barin jikin Sir Moli,
cikin kukan bak'in ciki Khulud ta rungume Sanah tana kuka,
tace " please my Sanah kiyi hak'uri wallahi kwata-kwata ban san abinda ke faruwa ba,
nayi sake da sakaci dana kasa tsayawa na maida hankalina na lura da abinda ke faruwa,
ta k'arasa maganar tana k'ara fashewa da gigitaccen kuka,
Sanah ma tana zubar hawaye dan bata da k'arfin yin kuka mai k'arfi ta shiga girgiza mata kai,
cikin bak'in ciki Hanash yace " ni ka daka ko!?
Ya fad'a yana nuna kansa,
cikin isa da tak'ama Sir Moli yace " an dake ka d'in,
kayi duk abinda zakayi,
kaci sa'a ma daban illata kaba,
akanta babu abinda zaban iya yi ba,
a hankali Sanah ta d'ago kanta ta kalli Sir Moli jin abinda yace,
Hanash yace " saboda tsabar rainin hankali da rashin sanin shari'a da hakk'in d'an Adam shine zaka shigo har cikin gidan ka dake ni?
Gyara Tsaiwarsa Sir Moli yayi kana yace " ko kana buk'atar k'ari ne?
Hanash yace " wallahi sai naga uban waye ubanka,
sai naga uban da ya d'aure maka gindi,
shege d'an iska fasik'i karuwan namiji kawai,
Sir Moli yayi guntun murmushi kana yace " kai inda kasan waye uban nawa,
da baka soma yin marmarin cewa zaka ganshi ta wannan hanyar ba,
kuma da kake maganar shari'a,
da sanin hakk'in d'an Adam kai abinda kake yi dai-dai ne?
"In banda rashin sanin daraja da k'imar mace,
har zaka iya saka hannu ka mareta,
har kana wani fiffik'a kana nuna k'arfi,
waya fad'a maka ana nuna k'arfi akan mace?
" Idan k'arfi kake da buk'atar nunawa kaje ka tari maza 'yan uwanka mana,
amma saboda kai lusarin namiji ne,
wanda ya rako maza duniya,
wanda bai san mutunci da k'imar kansa ba,
bai kuma san darajar da Allah yayiwa 'ya mace ba,
shine har kake fiffik'ar dukan mace,
Hanash yace " au kai har maganar k'ima da sanin darajar kake yi?
"Kai yanzu inda kasan kunya har zaka kalle ni kayi man maganar sanin mutuncin kai,
lalle kamm!
kodan dama ance 'yan iska basu data ido,
banzaye 'yan iska fasik'ai kawai,
wad'anda basu da aikin yi sai yad'a b'arna a doran k'asa,
then da kake cewa inda nasan waye ubanka banzanyi marmarin ganinsa ba,
waye shi!?
Kana ya mayar da kallansa ga Sanah yace " karuwa! fasik'a kawai,
Sir Moli ya matso daf dashi ta yadda har suna iya juyo mumfashin juna,
had'i da kallansa ido cikin ido,
ya nuna masa yatsansa yace " kul karka sake ci mata karuwa,
inba haka ba... ya cije lips d'insa da k'arfi had'i dayin kwafa,
sannan idan kana san sanin waye ubana sai ka nemi ganin nashi kamar yadda kace,
kana Sir Moli ya juya cikin takunsa na isa ya nufi mota,
Khulud ta kalli Hanash tace " karka kuma ce mata karuwa,
dan ba karuwa bace,
ido Hanash ya runtse da k'arfi kana ya kalli Khulud yace " please karki saka kanki cikin wannan maganar,
a hankali Khulud ta saki Sanah ta nufi Hanash,
Sanah tayi saurin rik'o ta,
amma ta fizge,
ta taka har gabansa ta kalli cikin kwayar idansa tace " ban gane kar na saka kaina cikin wannan maganar ba, me kake nufi Hanash?
"Yama za'ayi a gaba na kuma ina tsaye ka rink'a kiran Sanah da karuwa fasik'a,
wallahi in banda arzikin aure da kuma matsayinka na mijina,
had'i da girman igiyoyinka dake kaina,
dana nuna maka mai hak'uri bai iya fitina ba,
kai da kake da k'anne mata, kuma kake neman haihuwa har kake aibata 'ya'yan wasu,
kamar yadda k'annanka suke mutane haka Sanah da Sir Moli suka mutane,
masu cikekken gata,
Hanash kabi a hankali dan haihuwa zakayi,
kuma shi ciki mai haife-haife ne,
ba'a san abinda zai haifu ba,
ka daina zagi kana aibata 'ya'ayan wasu,
dan baka san kaima abinda zaka haifa ba,
ina jiye maka tsoran kada Ubangiji yayi maka jarawar da zata fi k'arfinka,
jarabawar da zara gigitaka,
Hanash ka kiyayi duniya da rayuwa,
dan ita duniya tamkar mace mai ciki ce ba'a san abinda zata haifa ba,
haka kuma k'addara mace ce mara tabbas da akoyaushe tana iya canjawa,
hannu Hanash ya yarfe cike da takaici ya kalli Khulud,
yace " idan ba karuwar bace mecece?
" Ko kin san sau nawa ina kama su da ido na,
suna aikata masha'a?
" Sau hud'u ina ganin su, biyu a office d'in abokin karuwancin nata,
d'aya ranar d'aurin mu,
sannan da ido na naga ya kaita gidansa,
lokacin Papu ya aiki ni gidan abokinsa a unguwar,
tsaiwarsa ya gyara kana ya kuma cewa " sai ki fad'a man yanzu duk macen da take bin namiji har zuwa gidansa mecece?
Shiru Khulud tayi tana kallan Hanash cikin takaicinsa,
murmushi yayi yace " baki da amsar bani ko?
" To idan baki da amsa ni ina da amsa,
sunan macen dake bin namiji har zuwa gidansa KARUWA!, FASIK'A!!, MAZINACIYA!!!,
dan haka wad'annan sunayen duk sunanta ne ya fad'a yana nuna Sanah,
cikin zafin rai Khulud ta d'aga hannu da niyyar kifawa Hanash mari,
tsaida hannun nata tayi a dai-dai fuskarsa,
ta kasa k'arasa abinda tayi niyya,
hannunta dake kerrrrma Hanash yabi da kallo,
cikin tsantsar mamaki,
yace " what! Khulud da marina zakiyi danna fad'i gaskiya?
Hannunta ta yarfe had'i da durk'ushewa kasa,
ta fasa gigitaccen kuka mai cin rai,
a hankali Sanah ta tako inda Khulud ke durk'ushe tana kuka tasa hannu ta d'ago ta,
tana zubda hawaye itama,
a hankali Khulud ta d'ago kanta ta kalli Hanash tace " Allah ya isar musu,
ya kuma saka musu a bisa zargin da kake yi musu,
Hanash yace " wai baki yarda ba kome?
"Kina nufin sharri da k'arya nayi musu?
" Ko kina nufin k'age nayi musu?
" Ko so kike kice ba karuwar bace?
A fusace Sir Moli ya juyo cikin k'araji yace " i said don't dare you call her karuwa!
ya fad'a yadda kasan anyi masa sammacin mutuwa,
cikin sanyin jiki Khulud da Sanah suka mik'e tsaye rungume da junansu,
Hanash ya kuma gyara tsaiwarshi,
cike da dagara yace " if i repeat it again what will you do!?
Tsaiwa Sir Moli ya gyara had'i da tattare hannun rigarsa,
kana ya zuba hannunsa cikin aljihun wandansa,
had'i da jefa idansa cikin na Hanash yace " ok k'ara fad'a inka isa kai cikken mara kunya ne,
Hanash yace " I said it in capital letter she's *KARUWA!!!*,
yadda kasan mahaukacin zaki Sir Moli ya nufi Hanash gadan-gadan,
yana wani irin takun k'arfin,
had'i da fitar da huci mai zafin gaske,
kai da ganinsa kasan ransa yazo iya wuya,
ran 'yan maza yayi mugun b'aci,
shima Hanash nannad'e hannunsa rigarsa,
yayi yana jiran k'arasowarsa,
ganin abinda ke shirin faruwa yasa Sanah saurin shan gaban Sir Moli tana kuka kamar ranta zai fita kana tace " please no!
a harzuk'e Sir Moli ya zagaye ta yana k'ok'arin k'ara nufar Hanash,
da sauri ta kuma shan gabansa,
had'i da sanya hannunta a saman k'irjinsa tana k'ok'arin dakatar dashi,
cikin kuka tace " a'a dan Allah,
jajayen idansa ya zuba cikin nata,
na tsayin lokaci, batare dayace komai ba,
ya dad'e yana kallanta ido cikin ido,
kana cikin zafin rai ya furzar da iskar bakinsa,
had'i da naushi motar dake kusa dashi ta Hanash,
inda ya daka a jikin motar ya lotsa,
hannunsa daya naushi motar yaji ciwo,
ya shiga zuwar da jini,
cikin furgici Sanah ta zaro ido had'i da saurin rik'o hannun,
tace " kana bleeding, ta fad'a cikin tashin hankali,
ganin yadda ta kid'ime yasa shi kafe ta da shanyayyun idanuwansa,
da sauri ta zame d'an kwalin kanta,
ta d'aure mishi hannun while tana cigaba da kukanta,
a hankali Sanah ta rik'e hannun Sir Moli ta jashi cikin mota,
ta bud'e mishi ya shiga, Sanah ta zagaya zata shiga cikin motar Khulud tace " my Sanah jira ni na d'auko hijab mu tafi gidan tare,
murmushi Sanah tayi kana tace " ok maza jeki d'auko,
a hankali Khulud ta juya ta shiga cikin gidan,
Sanah na ganin ta shige tayi saurin bud'e motarta ta shiga,
cikin muryar kuka tace " zaka iya driving d'in?
Baice mata komai ba yayiwa motar key,
jikin Baba mai gadi na rawa ya bud'e get,
Sir Moli yazo zai fita ya tsaya ya d'auko card d'inshi ya mik'awa mai gidan,
yace " ka kira ni letter, cikin rawar jiki Baba mai gidi ya amsa,
had'i da yin godiya, Sir Moli bai kuma yin magana ba yaja motar,
sai da ya fita daga gaba d'aya unguwar kana yayi parking a gefen hanya,
had'i da kwantar da kujerar motar ya kishingid'a gami da lumshe idansa,
yana fitar da huci had'i sauke ajiyar zuciya akai-akai,
ido Sanah ta k'ura mishi tana mamakin abubuwa da dama,
abu na farko daya tsaya mata yadda yayi akanta,
da yadda gaba d'aya yayi loosing control,
akan ance mata karuwa, dan taga yadda kalar idansa ta canja,
ta kuma hango tsananin b'acin rai acikin kwayar idansa,
ta tabbatar in banda tayi gaggawar shiga tsakiyarsu da Allah ne kad'ai yasan me zai faru,
can k'asan mak'ogwaranta ta maimata,
kalmarsa _akanta babu abinda bazan iya yi ba_,
sake kallan yadda yake ta faman huci tayi،
yana fitar da numfashi had'i da sauke ajiyar zuciya,
a ranta tace " yanzu wannan duk akai na ne?
"Idan akai na ne yayi wannan abun me hakan ke nufi?
" Idan dan ance man karuwa ya shiga cikin wannan matsanancin halin,
yanayinsa ya canja haka, to meye manufar yin hakan!?
Tana cikin yin zancan zuci taji yace " meyasa idan yayi maki abu baki iya ramawa!?
Yayi maganar batare daya motsa ba,
idanta na kansa cikin muryar kuka tace " nayiwa my Ulud alk'awarin duk abinda yayi man ban kuma ramawa,
"Ok tasan yana yi miki hakan kenan?
" A'a bata sani ba!
ta fad'a still idanta na kanshi,
" idan bata sani ba ya akayi kikayi mata alk'awarin?
Cikin sanyin jiki Sanah ta bashi labarin komai,
tun daga farkon had'uwarsu a ranar da sukayi graduated har zuwa ranar data yiwa Khulud alk'awarin bata kuma yi mishi komai har abada,
" ashe rashin kunyarki ce ta ja maki?
Ya fad'a yana bud'e idansa a hankali,
" yanzu in banda tsabar rashin kunya ina ke ina marin namiji?
" Duk abinda yayi maki ma dai-dai ne wallahi,
damma yana da sauk'in kai da sauyin zuciya,
inda irin mu ne hmmm ya k'arasa maganar yana yin murmushin gefen baki,
ido cikin ido Sanah ke kallan Sir Moli,
tana kallan cikin kwayar idansa,
wani irin abu take gani daga cikin kwayar idan nasa,
mai kamar brown color,
idan kuma ta kalli farin cikin idansa sai taga yayi mata wani iri,
kwata-kwata ta kasa fassara abinda take hangowa cikin kwayar idansa,
shima cikin kwayar idanta yake kallo,
jin yanayinsa ya fara canjawa yasa shi saurin kauda idansa,
daga kallanta ya mayar da kansa gefe,
ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi,
kana ta kalli hannunsa, a kid'ime tace " har yanzu yana bleeding fa,
dan Allah muje hospital, ta fad'a tana k'ok'arin rik'o hannun,
saurin janye hannunsa Sir Moli yayi had'i da tsuke fuska,
" please muje hospital kaga still yana bleeding,
a hankali ya kalle ta, yaga duk ta marairaice masa,
ta zama wata kalar tausayi,
key yayiwa motar batare dayace mata komai ba,
suna fara tafiya Sanah tace " amai nake ji,
bayyi mata magana ba ya gangara gefen hanya yayi parking,
yana tsaida motar ta fito da sauri tun kafin ta tsugunna ta fara shek'a aman,
a hankali ya bud'e motar ya fito,
ya zagoyo inda take,
a hankali ya tallafo ta cike da tausayi ya shiga mata sannu,
sai da ta gama yin aman kana,
ya bud'e mota ya d'auko ruwa ya zuba mata ta wanke jikinta,
jikinta sai kerrrrma yake yana rawar sanyi,
a hankali ta mik'e tsaye jiri na rib'arta,
ganin tana neman fad'uwa yasa shi d'aukarta cak ya sakata cikin mota,
kana shima ya zagaya ya shiga,
kwantar mata da kujerar motar yayi,
kana ya kashe Ac saboda yadda take rawar sanyi.
Direct standard hospital ya nufa da ita,
yayi parking a harabar asibitin bayyi mata magana ba,
ya zagayo ya bud'e motar ya tallafo ta,
a hankali Sanah ta zuro k'afafunta waje,
cikin sanyin jiki ta shiga takawa zuwa cikin asibitin,
while Sir Moli yana tallafe da ita,
da sauri nurses suka tare su,
suka amshi Sanah daga hannun Sir Moli,
but bai sake ta gaba d'aya ba,
yana rik'e sa ita ta d'aya b'arin,
office d'in Doctor aka nufa dasu,
a hankali suka zaunar da ita akan kujera,
Doctor ya mik'e da sauri yana murmushi yace " sannu!
kai kawai ta d'aga masa,
Doctor yana shirin fara dubata ta kalli Sir Moli tace " please kaje ayi maka dressing hannunka,
kallanta yayi batare dayace mata komai ba,
ta k'ara marairaicewa tace " please!
yace " bari a fara dubaki tukunna sai inje,
Sanah zatayi magana, Doctor tace " wow! amazing lovers gaskiya kun burgeni,
da yadda kuke bala'in so da kula da junanku,
Sir Moli zayyi magana Nurse d'in tayi tayi dariya tace " bari kaidai Doctor they're wonderful and best couples of the whole world wallahi,
sunyi masifar dacewa da junansu,
d'aya nurse d'in tace " saboda yab'ar yadda yake caring da san matarshi yama bari mu rik'e ta k'i yayi,
Doctor yace " Allah yasa dai Baby ne,
inyi maka babban albishir, dan da ganinku sabon aure ne,
kuma akwai soyayya a wajen,
kaga idan Baby ne amarci yayi kyau,
d'aya nurse d'in tace " aiko da gani ma laulayin ne,
d'ayar tace " aiko da kaya na zan kwaso na dawo gidanku ganin ikon Allah,
dan nasan akwai abu a goyon cikin nan.
Tunda suka fara magana idan Sir Moli yana kan Sanah yana karantar yanayinta,
bai iya gane yanayinta ba saboda halin rashin lafiyar datake ciki,
kallansa ya maida ga Doctor da nurses d'in,
yayi musu murmushi batare dayace komai ba,
kana ya fita ya nufi dressing room.
Da gudu Khulud ta fito hannunta rik'e da trolley,
ganin babu motar su Sanah yasa ta fashewa da kuka ta nufi hanyar fita,
Hanash dake tsaye yadda tabarshi,
baiko motsa ba, cike da tsantsar bak'in ciki da takaici,
yayi saurin shan gaban Khulud,
ya marairaice face yace " please kiyi hak'uri,
ban k'arawa,
bata ko kalli inda yake ba ta cigaba da nufar get tana kuka,
rik'eta yayi tayi saurin fisge jikinta,
tace " karka kuma tab'a ni,
da sauri ya janye hannunsa had'i da cewa " na bari,
dan Allah kiyi hak'uri kinji,
kallansa tayi tace " wallahi kaban mamaki Hanash,
na yarda dakai 100%,
idan wani ne ya fad'a man zaka yi duk wannan wallahi ban tab'a yarda,
na d'auka kai mai gaskiya ne,
na zata kai daban ne a cikin millions of millions na maza,
ban tab'a k'in yarda ko gaskata ka ba,
ban tab'a yin kokonto akanka da magarka ba,
Hanash na yarda dakai sosai,
meyasa zakayi haka!?
"Meyasa zaka tarwatsa duk yardar danayi maka?
" Meyasa zaka kawo kokwanto da zargi a zamantakewar mu?
"Mai yasa zaka zama mai fuska biyu?
" Why kake k'ok'arin raba ni da Sanaha, why Hanash! ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka,
muryarsa na rawa yace " wallahi Khulud nima ban san meyasa nake yin haka ba,
amma dan Allah kiyi hak'uri,
kallansa tayi tace " ina ai ba maganar hak'uri Hanash,
idan baka manta ba tun farkon alak'armu na fad'a maka,
cewar Sanah itace komai nawa,
ina matuk'ar santa fiye da komai da kuma kowa,
na fad'a maka bana k'aunar duk wani abu dazai shiga tsakani na da Sanah,
dan haka rabuwa dakai ta zama dole Hanash,
ta fad'a tana jan trolley d'inta,
da sauri Hanash ya fara k'ok'arin karb'ar trolley'n hannunta,
cikin tsawa tace " live me alone,
da sauri ya sake ta ya d'aga murya yacewa " Baba mai gadi " karka sake ka bud'e mata get,
kar bari ta fita,
jin abinda yace yasa Khulud durk'ushewa a wajen ta saki gigitaccen kuka,
a hankali Hanash ya durk'usa a kusa da ita,
cikin rawar murya yace " dan Allah kiyi hak'uri,
ki tashi mu shiga cikin gida,
red eyes d'inta ta d'ago ta kalle shi,
tace " wallahi ko yunwa da rana zasu kashe ni ban shiga cikin gidan da aka haramtawa my Sanah shigarsa,
sosai Hanash ya shiga lallab'a ta yana bata hak'uri,
amma fafur tak'i ko sauraronsa,
sosai Hanash yayi mugun mamakin taurin kan Khulud,
a ransa yace " dama ance masu hak'uri basu iya fushi ba,
ganin tak'i sauraronsa yasa shi mik'ewa cikin sanyin jiki yace " tashi muje na kaiki gidan da kaina,
babu musu Khulud ta mik'e, da kanshi ya bud'e mata gaban mota,
amma tak'i shiga ta bud'e bayan motar ta shiga ta zauna,
murmushi yayi had'i da girgiza kansa,
kana ya zagaya ya shiga motar yayi mata key,
tunda ya fara tuk'i yake kallanta ta mirror yana bata hak'uri had'i da rarrashinta,
amma tayi masa banza,
ta cigaba da kukanta,
har suka k'arasa gidan yana ta faman bata hak'uri,
a harabar gidan yayi parking,
da sauri ya fito jikinsa na rawa ya zagaya b'angarenta,
fitowa tayi itama tana jan trolley,
dai-dai lokacin Abbu da Didi suka fito,
turus sukayi a harabar gidan suna kallan ikon Allah,
cikin nutsuwa Hanash ya k'arasa inda suke had'i da durk'usawa har k'asa ya gaidasu cikin girmamawa,
cikin fara'a suka amsa masa,
Khulud ta k'araso inda su Abbu ke tsaye ta durk'usa ta gaida su,
Abbu bai amsa gaisuwar ba yace " lafiya na ganki da akwati?
Shiru Khulud tayi had'i da sunkuyar da kanta k'asa,
Abbu yace " tambayarki nake yi,
lafiya na ganki da akwati, me kikazo yi gidan harda zuwa da akwati?
Abbu yace " biki ake yi ko suna a gidan?
Kan Khulud na k'asa tace " a'a,
Abbu yace " to uban me ya kawo gidan?
Cikin kuka Khulud tace " Abbu na dawo gida ne?
Abbu yace " ban gane kin dawo gida ba?
"Me kika dawo yi?
Shiru Khulud tayi batace komai ba,
Abbu yace " magana nake yi miki,
cikin kuka Khulud tace " ban kuma zama dashi,
Abbu yace " shiwa?
Khulud tace " Hanash!
Abbu yace " akan wanne dalilin?
Khulud tayi shiru,
Abbu yace " ci da sha ne baya baki ko hakk'ink'i na auratayya ne baya biya miki?
"Ko mutuncinki ya kasa karewa, ko kuma nauyinki dake kansa ne bai saukesu!?
Cikin sanyin murya Khulud tace " a' a!
Abbu yace " Allah yake sab'awa,
ko kuma mashiriki ne?
"A'a Khulud tace,
" giya yake sha ko lud'u yake yi?
" A'a!
Abbu yace " a cikin sharadd'an rabuwar aure da Allah ya gindaya akwai d'aya a tsakaninku?
A hankali Khulud tace " a'a!
Abbu yace " auren dole mukayi miki ko mu muka kawo miki shi muka matsa maki kika aure shi?
"A'a tace tana zubar da hawaye,
Abbu yace " mu muka had'aki dashi?
Nan ma Khulud tace " a'a,
Abbu yace " ke kika wo kayanki kikace kina so ko?
Tace " eh!
" To shine dan iskanci daga yin auren dududu wata biyar zaki kwaso kaya kice kin dawo gida?
" Ni dai dan Allah Abbu ku raba ni das.......
gigitaccen marika Abbu ya maka mata guda biyu a jere,
cikin fad'a yace " dan ubanki mu zaki maida k'ananan mutane,
daga yin auren zaki dawo, ki dawo gidan kiyi uban me?
" Tunda kike cikin gidan nan kin tab'a ganin anyi yaji?
"Ko tunda kuke dasu Mamu kin tab'a ganin sun kwashe kayansu sunce sun koma gidansu?
" Kin tab'a ganin su Halan sun fita ko k'afar gida da sunan yaji, ko so kike yi ke ki fita zaka kibar tarihi?
" Idan baki sani ba, gwara ki sani haka dokar Hard'o family take,
idan suka aura ko aka aure su babu saki ko yaji sai dai mutuwa ta raba da yardar Allah,
ki bud'e kunne dakyau kiji ni daga yau duk ranar da kika sake d'auko k'afa da sunan yaji to ki nemi wani gidan da kuma uban ba ni ba,
zan cire ki daga jerin yara na,
kinji ko baki ji ba, cikin kuka ta amsa " naji! dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa,
ajiyar zuciya ya sauke kana yace " yauwa good girl,
Allan yayi miki albarka kinji aje ayi ta hak'uri,
duk wacce kika gani gidan mijinta zaman hak'uri da juriya takeyi,
duk matar datace maki bata da matsala gidan mijinta k'arya take yi,
da zarar anyi aure so da soyayya sun k'are sai dai ayi zaman hak'uri,
idan kika bar mijinki na yanzu saboda wani dalilin,
kin san wanda zaki sake aura?
"Ko shi kin san halinsa, kin san nashi d'abi'un?
" Kinga baki san hannun wanda zaki kuma fad'awa ba,
dan haka kiyi hak'uri kinji my daughter,
nasanki da hak'uri da juriya had'i da kawar sa kai da saurin yafiya fa,
Abbu ya fad'a cikin tsokana, kanta ta kuma sunkuyarwa k'asa,
Abbu yace " maza tashi ki koma d'akinki kinji,
mik'ewa tayi a hankali kana ta kalli Abbu tace " bari na gaida su Mamu,
Abbu yace " a'a ba sai kinje ba,
suma zaune suke a gidajen mazajensu suna hak'uri,
dan haka kema ki koma naki gidan mijin,
kyazo ki gaida su daga baya cikin dad'in rai,
ba musu Khulud taja trolley d'inta ta koma mota,
Hanash ya mik'e tsaye had'i dayiwa su Abbu godiya sosai,
Abbu yace " kai ma kayi hak'uri,
kasan mata 'yan a lallab'a ne,
sai anyi hak'uri dasu, muma duk abinda mukeyi kenan har yanzu,
shiyasa kaga ankawo har tsayin wannan lokacin ana tare,
kansa ya sunkuyar had'i da cewa " in sha Allah Abbu,
sallama sukayi kana suka tafi,
Didi dake tsaye bayyi magana ba,
har su Khulud suka tafi kana ya sauke ajiyar zuciya yace " oh! yaran zamani dai ba hak'uri daga yin auren har an kwaso rigid'i-rigid'i,
an taho yaji gidan,
Abbu yace " kadai bari,
Didi yayi murmushi yace " uban 'ya anyi fad'a an dawo kuma ana rarrashi,
Abbu yace " yaran yanzu ne sai da hakan milkin soja zalla ba yayi musu,
dole sai an had'a mulkin farar hula anyi musu siyasa kana,
ina murna na kusa gama aurar da yara na lafiya,
tana neman d'aga min hankali,
ta tada man zaune tsaye,
Didi yayi dariya,
kana suka nufi part d'in iyayensu dan dama can suka fito zasu.
Sai da aka gamawa Sir Moli treatment kana ya koma inda ya bar Sanah,
Doctor na ganin shi yayi dariya yace " master of love,
murmushi Sir Moli yayi had'i da cewa " how is she?
Doctor yace " gaskiya bata da lafiya sosai,
Sir Moli yace " meke damunta!?
Doctor yayi murmushi had'i da mik'ewa Sir Moli takardar batare da kawo komai aranshi ba ya amshi takardar,
karaf idansa ya sauka akan abinda Doctor ya rubuta da sauri Sir Moli ya mik'e had'i da cewa " what!,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.................!
MOMYN ZZARAH
[7/7, 4:42 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
3⃣0⃣
"What! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
badai kwantar da ita zakuyi ba?
Fuskar Doctor d'in d'auke da tausayawa,
yace " eh! dan gaskiya koda zamu sallame ta sai ya kai zuwa gobe,
" meke damunta?
Zazzab'i ne da ciwon kai, kuma dole sai anyi mata k'arin ruwa da allurai,
"tana ina?
Sir Moli yace a tak'aice,
" muje Doctor ya fad'a yana fita daga office d'in,
a baya Sir Moli ya bishi har zuwa d'akin da aka kwantar da Sanah,
hannunta d'auke da drip,
bakin gadon yaje ya tsaya had'i da k'ura mata,
Doctor yace " anyi mata allurar bacci ne,
dan ta samu hutu, dan ta jigata sosai,
ajiyar zuciya Sir Moli ya sauk'e had'i da yiwa Doctor godiya sosai,
sallama Doctor yayi mishi kana ya fita,
a hankali Sir Moli ya zauna a bakin gadon had'i da k'ura mata ido,
sai lokacin ya hango 'yar ramar da tayi,
fuskarta tayi firit, ga haske data k'ara,
cikin nutsuwa ya kai hannunta saman goshinta ya shafa,
a hankali ya rink'a shafa saman goshinta zuwa kanta,
cikin bacci Sanah ta saki ajaiyar zuciya,
had'i da motsawa ta kamo hannunta Sir Moli ta rungume a k'irjinta,
cikin sand'a Sir Moli ya fara k'ok'arin zame hannunsa daga jikinta,
idanta rufe still tana baccin, ta tura baki,
had'i da k'ara k'ank'ame hannun a k'irjinta,
kana ta k'ara gyara kwanciyarta,
murmushi yayi kana ya zame hannunsa,
baki Sanah ta kuma turawa had'i kwab'e fuska kamar zatayi cikin shagwab'a,
ita a dole anyi mata ba dai-dai ba,
a hankali ya mik'e daga bakij gadon,
kan sofa ya koma yana tunanin abinyi,
ya sandai bai kamata ace ta kwana hospital ba tare da sanin Family'nta ba,
so dole ya sanar da su,
to amma ta yaya?
Ya tambayi kanta, shiru yayi na tsayin lokaci yana tunanin abinyi,
wayarta daya bari cikin mota ya tuno,
a hankali ya mik'e yaje bakin gadon,
ya ja mata blanket sama ya rufe ta,
kana ya juya zai fita, caraf yaji ta rik'o hannunshi cikin nata,
juyawa yayi had'i da zuba mata ido,
gani yayi still dai baccin take yi,
cikin bacci Sanah ta k'ara rik'e hannunshi gam cikin nata,
tace " please karki tafi ka barni,
fa fad'a tana yamutsa fuska alamun shagwab'a,
murmushi yayi had'i da cire hannunta,
ya shafa kanta had'i dayi mata light kiss a goshi kana fita,
tun daga nesa yayi using remote ya unlocking motar,
yana daga waje ta b'angaren zamansa ya zura kansa da jikinta ya d'auko wayar,
kana ya rufe mota ya koma cikin hospital d'in,
gudun kar ya shiga cikin d'akin yayi waya ta tashe ta,
yasa shi tsayawa daga k'ofar d'akin ya kunna wayar,
luckily babu pin a wayar yayi mamakin ganin wayar babu pin dan wancan karon ma haka ya gani,
wayar ya shiga juyawa a hannunsa yana kallanta,
had'i da tunani,
dan yasan is so hardly kaga wayar 'yan mata da samari a wannan zanin babu password,
a ransa yace " ta yarda da kanta kenan,
ya fad'a yana dialing number Abbu,
daya gani a jeren missed call,
tana soma ringing Abbu yayi picking,
cikin girmamawa Sir Moli yace " Assalamu Alaikum,
d'an shiru Abbu yayi jin muryar namiji,
sai da Sir Moli ya sake maimaita sallamar kana Abbu ya amsa,
gaidashi Sir Moli yayi Abbu ya amsa cikin sanyin jiki,
a nutse Sir Moli yayi mishi bayanin shi Malamin su Sanah ne,
kuma yanzu haka suna asibiti bata da lafiya har an kwantar da ita,
cikin tension Abbu yace " subhanallahi a wanne hospital akan kwantar da ita?
Cikin nutsuwa Sir Moli yayi masu bayani,
sosai Abbu yayiwa Sir Moli godiya kamar me,
kana Abbun yace gasu nan yanzu,
bayan Abbu ya kashe wayar ya kalli Mamu yace " dama Sanah bata lafiya kika barta ta tafi makaranta?
Mamu tace " wallahi ban sani ba meke faruwa?
Abbu yace " lecturer sune ya kira ni yanzu yake shaida man an kwantar da ita a asibiti,
a kid'ime Mamu ta mik'e tana salati tace " a wanne asibitin! meke damunta?
Abbu yace " kwantar da hankali yace man zazzab'i ne kawai,
yanzu zanyiwa Didi waya yaje,
Mamu ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,
Abbu yayi dialing number Didi,
bayan sun gaida Abbu yace " 'yarka ce ba lafiya, an kwantar da ita a hospital,
" subhanallah a wanne asibitin?
Didi ya fad'a cikin tension,
Abbu yayi masa bayani,
kana ya kashe wayar,
da sauri Didi ya mik'e yayi parlor wajen Juju,
a gaggauce yayi mata bayani kana yace ta shirya abinci yanzu,
itama da sauri ta mik'e ta shirya suka fita,
a compound Didi ya had'u da Ziyad da Zafran ganin yadda suke sauri yasa su nufarsu,
suna tambayarsu lafiya,
a gaggauce Didi yayi musu bayani,
kana ya shiga mota suka tafi,
Ziyad yacewa Zafran jeka shirya kazo mu tafi,
Zafran ya amsa da " OK,
koda suka shiga su Halan cewa sukayi sai sun bisu,
haka rungud'uma suka tafi gaba d'ayansu,
Sir Moli yana gama wayar ya koma cikin d'akin ya zauna akan sofa,
ba'afi 20 minutes ba su Didi suka k'araso,
number Sanah Didi ya kira Sir Moli yayi picking Didi yace " gamu mun k'araso,
Sir Moli ya fita ya shigo dasu,
su Juju basu jima da zuwa ba su Ziyad suka k'araso,
gaba d'ayansu hankalinsu a matuk'ar tashi yake,
jikinsu sai kerrma yake, duk sukayi cirko-cirko a bakin gadon da Sanah ke kwanciya,
Halan sai shafa kanta take,
yau kam Sir Moli yaga yadda Sanah keda gata,
ake kuma mugun santa a cikin Family'nsu,
dan kowa ka gani a cikinsu yadda kasan zai d'ora hannu aka ya kurma ihuu,
ganin dangin Sanah sunzo yasa Sir Moli yi musu sallama,
sosai su Didi, Ziyad, Zafran da Juju sukayi mishi godiya kamar me,
sai lokacin hankalin Halan ya kai kansa,
tayi mamakin ganinsa sosai,
har k'asa Halan ta durk'usa ta gaida Sir Moli cikin girmamawa,
shima ya amsa cikin mutuntatawa,
har bakin motarsa Ziyad da Zafran suka raka,
kana suka kuma yin musabaha had'i da sallama ya tafi,
bayan ya basu wayar Sanah.
Tunda Khulud ta shiga mota ta zauna take ta faman kuka kamar ranta zai fita,
abu ya had'u yayi mata yauwa ga mari ga tsinka jaka,
shiru Hanash yayi baice komai ba,
motar tayi tsit babu abinda ke tashi sai sautin kukan Khulud,
a harabar gidan yayi parking ya fito da sauri ya zagaya b'angaren Khulud jikinsa na rawa ya sunkuya da niyyar d'aukarta,
duka hannayenta biyu Khulud ta sanya ta tura shi baya,
cikin masifa tace " don't dare you touch me again,
ta fad'a tana fitowa daga motar idanta tarr cikin nashi,
sororo Hanash yayi yana kallanta,
kasancewar shi ba mutum bane mai san hayaniya da fad'a yasa shi tsayawa yana kallanta,
yama rasa abinyi har ta shige cikin gidan ta barshi,
bayanta yabi da kallo yana matuk'ar mamakinta,
dan da fad'a mishi akayi Khulud tana da wannan zafin ran bai tab'a yarda,
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kana ya taka yabi bayanta,
koda ya shiga cikin gidan iskewa yayi harta shege bedroom d'inta ta rufe k'ofar,
bedroom d'insa ya wuce yayi wanka,
ya zura kaya marasa nauyi kana ya fito,
yadda ya bar k'ofar haka ya dawo ya iske ta,
bai wani tsaya yi mata magana ba yayi ficewarsa,
bai dawo ba sai dare wajen k'arfe 9:00pm،
rik'e da ledoji dan yasan ba lalle idan tayi girki ba,
kamar yadda yayi tsammani haka ya tarar,
yadda ya fita yabar k'ofar haka ya dawo ya iske ta rufe,
bakin k'ofar yaje ya tsaya yana tunanin abinyi,
daga bakin k'ofar ya rink'a jiyo sautin kukanta,
ba k'aramin mamaki Hanash yayi ba,
ganin har lokacin Khulud na, kuka,
cikin mutuwar jiki yayi knocking k'ofar,
amma shiru, daga wajen yace " dan girman Allah kiyi hak'uri ki bud'e man,
still banza Khulud tayi dashi bata ce mishi komai ba,
Hanash ya kai wajen 20 minutes tsaye bakin door yana ta faman bata hak'uri,
had'i da rok'onta kan ta bud'e masa k'ofar,
amma bata amsa masa koda sau d'aya bane,
ganin haka yasashi komawa kan sofa ya zauna had'i da ciro wayarsa cikin aljihu,
yayi dialing number Mimmee bugu d'aya Mimmee tayi picking,
cikin sanyin murya ya gaida ita,
ta amsa masa, yanayin yaffa taji muryarsa yasa ta cewa " lafiya dai Son!?
" Muryarsa na rawa yace " please Mimmee ki kira Khulud kice ta bud'e man k'ofa,
cike da mamaki Mimmee tace " kamar ya?
Yace " ni dai please Mimmee kawai kice mata ta bud'e man k'ofar,
Mimmee tace " fad'a kukayi?
Shiru yayi baice komai ba,
a d'an hasale Mimmee tace " uban me kayi mata?
Yace " banyi mata komai ba,
nima yanzu na dawo gidan na iske ta shiga d'aki ta rufe k'ofa tana ta faman kuka,
Mimmee tace " subhanallah bari na kira ta,
kashe wayar Mimmee tayi kana tayi dialing number Khulud,
sai da wayar ta kusa tsinkewa kana Khulud tayi picking,
cikin muryarta da bata fita sosai,
ta gaida Mimmee, Mimmee ta amsa cikin fad'uwar gaba dan ta fahimci akwai matsala,
Mimmee tace " Khulud lafiyarki?
Khulud tayi shiru bata yi magana ba,
Mimmee tace " Khulud meke faruwa tsakaninki da mijin naki?
Khulud tace " bakomai Mimmee,
babu yadda Mimmee batayi kan Khulud ta sanar mata abinda ke faruwa tsakaninta da Hanash ba,
amma Khulud tak'i, tace babu komai,
ajiyar zuciya Mimmee ta sake cikin ranta kuma tana jin dad'i dan ta fahimci Khulud macece mai matuk'ar sirri,
da alama bazata tab'a fallasa tsakaninta da mijinta ba,
bazata tuna sirrinsu ba,
Mimmee tace " to koma miye kiyi hak'uri,
saboda ita rayuwar aure ta gaji haka,
duk macen da kika gani gidan mijinta zaman hak'uri takeyi,
sosai Mimmee tayiwa Khulud fad'a da nasiha masu ratsa jiki da zuciya,
ta nusashsheta abubuwa da dama kan zamantakewar aure,
daga k'arshe Mimmee ta ba k'ara da bata hak'uri sosai,
kana tace " ki daina yawan kuka gaban miji indai bana shagwab'a,
ko na kissa bane, dan yawan kuka yana kawo rai tsakaninku,
sannan yana sa namiji k'osawa dake,
ko ya daina tsoro da shayin yi maki laifi,
Khulud ta amsa da " to,
kana ta umarce ta kan taje tayi wanka taje wajen mijinta,
cikin sanyin jiki Khulud tace " to Mimmee in sha Allah zanyi duk yadda kikace,
murmushin jin dad'i Mimmee tayi kana tace " yauwa 'yata nagode sosai kinji,
Allah yayi muku albarka ya baku zuri'a ta gari,
kasa amsawa Khulud tayi saboda kunya,
kana sukayi sallama Mimmee ta kashe wayarta,
Mimmee na kashe wayar Khulud ta mik'e cikin sanyin jiki,
ta shiga wanka, dan nasihar Mimmee tayi masifar shiga jikinta,
bata dad'e ba ta fito, ta shirya,
dayake tayi sallah ، tana gama shiryawa ta bud'e k'ofar ta fita parlor.
zaune ta iske kan sofa, yana ganinta ya mik'e da sauri jikinsa yana rawa ya nufi,
ya shiga k'ara bata hak'uri,
ta d'an saki ranta ba yabo ba fallasa,
dakyar Khulud ta d'anci abinci,
a hankali Hanash ya rungumo ta jikinsa ya kwantar da ita saman k'irjinsa,
yana shafa kanta, yana cigaba da bata hak'uri.
K'arfe 11:30pm na dare Sanah ta fara motsi,
a hankali ta sanya hannunta wanda ke sanye da calular ta dafe kanta,
had'i da bud'e idanta a hankali a hankali,
bakinta d'auke da salati,
da sauri Halan ta mik'e taje kusa da Sanah,
ganinta ta farka yasa Ziyad fita da sauri ya fita kiran Doctor,
tare Doctor da Ziyad suka shigo tare,
duddubata Doctor ya kumayi kana ya bada umarnin a bata abinci taci,
cikin lallab'awa Halan ta kama Sanah ta zaunar da ita,
muryar Sanah na rawa tace " sallah zanyi,
batare da b'ata lokaci ba, Halan ta kama ta ta kaita har cikin toilet kana ta fito had'i rufe mata k'ofar,
kafin Sanah ta isar da sallah Juju ta had'a mata tea da abinci,
ruwan tea Sanah ta fara sha kana daga baya Juju ta matsa mata taci farfesun kaji,
kana tasha magani,
sosai Sanah taji dad'in jikinta,
ta wartsake, ta shiga hira da su Mimmee kamar ba itace patient d'in ba,
sai dare su Halan suka koma gida suka bar Juju ta kwana tare da Sanah,
duk da Halan taso kwana Didi ya kad'a su suka koma gida,
washe gari da safe su Halan suka dawo,
suka iske Sanah ta warke garau,
bayan tayi breakfast Doctor yazo ya k'ara dubata kana ya sallame ta,
duk abin nan da ake hankalin Sanah yana kan Sir Moli,
badan komai ba sai dan ciwon dake hannunsa,
k'arfe 12:00 na rana suka isa,
Halan da Juju suka raka Sanah part d'in Mamu har cikin bedroom d'inta.
Kasancewar ranar Friday aka sallamo Sanah yasa ta samu ishashshen lokacin hutu,
dan Saturday and Sunday babu makaranta,
tun da Sanah ta dawo gida ta shiga tunanin ko ya Sir Moli yake?
ko ya jikin nasa yake?
ga bata da number shi balle ta kira shi,
cikin ranta tace " Allah sarki duk sanda nake cikin wani hali ko matsala sai Allah ya kawo man shi ya taimake ni,
ganin tunanin ba kai mata zayyi ba yasa ta mik'ewa ta shiga bathroom ta watsa had'i dayin alwala tayi sallah kana ta kwanta.
Ranar Monday da wuri Sanah ta shirya ta tafi makaranta,
office d'insa tayi niyyar fara shiga tayi masa godiya amma ta fasa,
dan ganin baifi 10 minutes left a shigo masu lectures ba,
tana shiga class Rose ta taso da sauri ta tare,
had'i da rik'e hannun Sanah taja ta waje,
can gefe Rose taja Sanah inda babu kowa,
Rose ta kalli Sanah tace " ina kika shige ne ina ta nemanki?
Sanah tace " rashin lafiya nayi shiyasa kikaga kwana biyu ban shigo ba,
Rose tace " ayya sorry dear,
Sanah tace " thank you,
Rose tace " kin tuna maganar da mukayi dake kwanaki akan Muslims?
Sanah tace " eh!
Rose tace " maganganun da kika fad'a a wannan lokacin sunyi tasiri a zuciya ta,
sun kashe min jiki sosai, dan haka naje nayi tunani sosai,
daga k'arshe nayi binci mai zurfi akan addininku na muslunci,
so in fact I want converted to Islam,
cikin matsananciyar murna da farin ciki Sanah ta rungume Rose,
yayinda hawayen farin ciki suka shigo zubowa Sanah,
na tayi sanadiyyar musluntar da wani,
da sauri Sanah taja hannunta zuwa office d'in Sir Moli,
saboda tsabar murna da farin ciki Sanah bata tsaya neman izinin shiga ba,
ta danna kai cikin office d'in kanta tsaye,
zaune suka iske shi akan kujera yana aiki a system,
fuska ya tsuke kana yace " ubanwa ya baki izinin shigo man office kai tsaye?
Bata kula da maganarsa ba tace " Sir wajenka muka zo,
a tsawace yace " get out!,
ya fad'a a yana nuna mata k'ofa,
a d'an tsorace Sanah taja baya kana tace " Sir Rose ce take san musulunta,
jikin Sir Moli yayi sanyi,
a hankali ya mayar da kallansa ga Rose yace " are you sure you want converted to Islam?
"Yes Sir Rose tace tana murmushi,
" Alhamdulillah Sir Moli yace,
a nutse Sir Moli yayi hanyar fita had'i da cewa " ina zuwa,
Sir Moli bai jima ba, ya dawo da manyan malaman addinin mulunci dake BKU,
had'i da shuwagabanin makarantar,
kowa fuskarsa d'auke da murmushi,
d'aga daga cikin Malaman ya kalli Rose yace " kin tabbatar musulunta zakiyi da zuciya d'aya?
" Eh Rose tace,
Malamin ya kuma cewa " me yaja ra'ayinki zuwa ga musulunci?
Rose ta basu labarin abinda ya faru tsakaninta da Sanah,
da yadda tayi ta bincike da neman k'aramin bayani akan musulunci,
gaba d'aya malaman sun jinjinawa basira da hikimar Sanah,
anan cikin office d'in Sir Moli aka musuluntar da Rose,
Sanah nata hawayen farin ciki,
yayinda itama Rose d'in hawayen farin cikin takeyi,
Malamin ya bata zab'in d'aya daga cikin sunan musulunci,
Rose ta zab'i sunan Fatima,
cikin Malaman wani yace " Alhamdulillah Fatima yanzu kin zama cikekkiyar musulma,
wanka kad'ai ya rage miki,
then what about your family issue?
Rose wacce ta koma Fatima tayi murmushi tace " family na basu da matsala dan Brother ne ya fara musulunta last year,
bai kuma fuskanci matsalar komai ba,
kuma sai da na sanar da parents d'ina,
su suka amince min kamar yadda suka amincewa Yaya na,
Alhamdulillah Malaman sukace,
kana sanar da ita sun sakata a d'aya daga cikin islamiyoyinsu ta rink'a zuwa karatu,
dan ta san abubuwa cikin addinita,
Fatima ta amsa da to,
bayan Sanah ta koma gida cikin murna da d'oki ta sanar da 'yan gidan su labarin musuluntar Fatima,
sosai 'yan gidansu Sanah sukayi murna,
Abbu yace ta kawo mishi ita zayyi mata kyau.
A b'angaren su Khulud sun dai-daita sosai,
dan Hanash hak'uri yayi ta bata,
yana rarrashinta,
had'i da kwantar mata da hankali yana fad'a mata dad'ad'an kalamai masu kwanatar da zuciya,
yayinda da kullum Khulud da Sanah sai sun nemi juna a waya amma basu samun juna sai dai suyi magana ta WhatsApp,
hakan yasa kullum kuma koyaushe suna cikin chart da juna,
dan dukkan su babu wanda yayi wani tunanin.
Ranar Friday bayan an tashi daga lectures,
around 4:30pm na yamma Sir Moli zaune cikin motarsa ya kishingid'a had'i da lumshe idanshi,
jin zuciyarshi na bugawa da tsananin k'arfi yasa shi bud'e idanshi a hankali,
yana bud'e idan ya hangota tana tafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,
da ganinta kasan babu abinda ke damunta cikin rayuwarta,
ido ya k'ura mata sosai, tun daga nesa har ta wuce shi,
ido ya sake lumshe ya bud'e had'i da sauke ajiyar zuciya,
kana yayiwa motar,
gabanta ya tsaya batare dayayi mata magana ko ya bud'e motar ba,
tsayawa tayi ta kama k'ugunta,
tare da yin rolling sexy eyes d'inta,
a nutse Sanah ta taka ta bud'e motar ta shiga,
daga shi har ita babu wanda yayiwa wani magana,
sai da aka d'an lokaci kafin Sanah tace " ina wuni?
Banza yayi da ita bai amsa ba,
murmushi Sanah tayi tace " dama ni kake jira ko?
Jin abinda tace yasa shi juyowa a hankali ya kalli cikin kwayar idanta,
na seconds kana ya mayar da kallansa ga tuk'in da yake yi,
rolling sexy eyes d'inta ta kuma yi, kana tace " deaf!
kallanta ya kuma yi batare da yayi maganar ba,
Sanah tace " ah yau inaga ciwon baki da azumin magana yake yi,
" talkative! yace batare daya kalle ta ba,
murmushi tayi tace " ashe dai yana magana!
fuska ya tsuke yadda kasan anyi mishi sammacin mutuwa,
had'i da kauda kansa gefe,
ganin ba hanyar gidansu ya d'auka ba yasata kallanshi da niyyar yin magana,
ganin kwata-kwata babu fuska dan ya had'e fuskarsa yasha mur sosai yasa ta yin shiru dole,
A harabar wani k'ayataccen park mai shegen kyau yayi parking,
wajen ya k'ayatu sosai kamar a k'asar waje,
bayan yayi parking a wajen ya bud'e motar ya fito batare daya ko kalli inda take ba bare yayi mata magana,
baki ta zumb'uro had'i da bin bayansa da harara,
kana ta bud'e motar tabi bayansa,
wata hanya taga yabi tayi saurin bin bayansa sai da sukayi 'yar tafiya kana suka b'ulle,
tsayawa Sanah tayi cak had'i da furta " wow! masha Allah,
ganinta a tsakiyar lambu wanda ya gaji da had'uwa,
daga hannun dama kwantaccen ruwan ne kwance a k'asa,
daga b'angaren hagu kuma table ne guda d'aya tak d'auke da kuje biyu,
a saman table d'in akwa babbar kwalbar lemon mai kama da giya,
sai glass cups guda biyu a gaban kowacce kujera,
hannu Sanah ta d'aga sama had'i lumshe idanta,
ta d'aga kanta sama tana juyi a wajen had'i da shak'ar dadd'an k'amshen furannin dake zagaye da wajen,
yayinda sassan iska mai sanyin dad'i ke kad'awa,
hannu Sir Moli ya hard'e a k'irjinsa had'i da zuba mata ido,
fuskar Sanah d'auke da murmushi ta bud'e idanta ta sauke su akan Sir Moli tace " wow! wajen ya burge ni sosai,
ta fad'a cikin kwanciay hankali,
bayyi mata magana ba ya k'arasa inda kujerun suke ya zauna akan d'aya daga ciki,
cikin nutsuwa itama ta taka ta zauna tana cigaba da sauraren dadd'an kukan tsuntsayen sake tashi cikin lumbum,
ga sautin ruwa mai dad'in sauraro,
idanshi na kanta ya kafe ta da shu'uman idanuwansa,
bai ko k'iftawa,
ta wata k'ofa wani matashin sauri ya fito a hankali yazo ya bud's drinks ya zuba cikin cups d'in,
kana ya d'an rusuna yabar wajen,
cikin k'asaita Sir Moli ya d'auki cup d'in gabansa yakai baki,
ya d'an kurba kana ya aje,
itama d'aukar cup d'in tayi takai bakinta ta kurb'i lemun ciki,
Sir Moli yace " it's bar!
cikin tsoro da firgici Sanah ta zaro idonta waje,
tace " what! mekace?
Kamar bazayyi magana ba,
sai kuma yace " yes! ai nasan kinji ni,
a kid'ime Sanah ta mik'e tsaye cikin tashin hankali ta d'auki kwalbar tana dubawa,
nannauyan ajiyar zuciya ta sake,
had'i da komawa ta zauna akan kujerar,
har lokacin idashi na kanta bai ko k'iftawa,
idanta ta jefa cikin nashi tace " meyasa!?
Sai da ya d'auki lokaci kana yace " nace miki ki sha ne?
Idanta cikin nashi ta girgiza mishi kanta had'i cewa " a'a,
yace " to akan me zaki sha?
kanta ta kunyar k'asa batare datace mishi komai ba,
yace " wata rana idan kina irin haka sai kin sha wani mugun abun,
cikin shagwab'a Sanah ta turo baki had'i da cewa " to ai naga kasha ne,
bayyi mata magana bai kuma d'auke idanshi daga kanta ba,
jin notification yasa ta bud'e hand bag d'inta ta d'auko wayarta dan tasan Khulud ce,
video taga Khulud d'in ta turo mata dan haka tayi saurin yin playing,
short comedyn film d'in na mamajo na marigayi Rabilu Musa Ibro (Allah yayi masa rahama),
ta gani, tun kafin ta gama gani ta sanya dariya sosai kamar me had'i da sanya hannunta saman bakinta ta rufe bakin tana cigaba da yin dariya,
Ido Sir Moli ya k'urawa Sanah yana kallan yadda take yin dariya sosai yayi,
a bazata tammakar saukar aradu Sanah taji muryarsa can k'asan mak'ogwaro yace " *I LOVE YOU SANAH!!!*
MOMYN ZARAH
[7/7, 4:44 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
3⃣1⃣
Cak ta tsayar da dariyarta had'i da sandarewa a yadda take bata ko motsa ba,
balle ta iya cire hannun daga bakinta,
takai wajen 3 minutes a haka kafin ta sauke hannunta a hankali had'i da juyowa ta zuba masa ido,
hannayensa zube cikin aljihun wandonsa,
cikin salo Sir Moli yayi saurin basarwa had'i da kawar da kansa gefe yana kallan kwantaccen ruwan fake gefensu,
kamar bashi ne yayi maganar ba,
baki ta tab'e had'i da kawar da idanta daga gare shi,
cikin ranta tace " dama nasan kunne na ne ya jiye man ba dai-dai ba,
ruwan itama ta zubawa ido tana cigaba da yin zancen zuci,
ganin ta kawar da idanta gefe yasa shi mayar da kallansa kanta,
yana karantar yanayinta, d'an gutun murmushi yayi mai mai sauti,
kana yace " ina sanki Sanah!
da sauri Sanah ta kuma juyowa ta kalle shi,
still basarwa Sir Moli yayi kamar bashi ne ya fad'a ba,
ido ta kafe shi dafe dan san tabbatarwa kanta abinda kunnuwanta suka ji,
ganin ta tsare shi da ido yasa shi mayar da,
idanshi kanta yana kallan cikin kwayar idanta,
eyeball to eyeball suke kallanta junansu batare da d'aya daga cikinsu ya k'ifta idansa ko ya d'auke kansa ba,
cikin sassanya kuma zazzak'ar muryar da Sanah bata tab'a jinsa da ita ba taji yace " I love you!,
cikin tashin hankali Sanah ta zaro idonta waje kamar wacce taga mutuwarta ta had'i da mik'ewa tace " what!?
Zamansa ya gyara had'i da hard'e hannayensa a k'irji yace " yes am madly in love with you Sanah,
I really really love you more and more most,
cikin firgici da kid'ima Sanah ta fara marin kanta a hankali,
taba cewa " please wake up Sanah daga wannan mugun baccin mai tattare da bak'in mafarkin,
cikin nutsuwa ya mik'e tsaye still idanshi na kanta hannuwanshi hard'e a k'irjinsa,
jikin Sanah na kerrrma ta nufi bakin ruwan dake kwance k'asa a gefensu,
ta durk'usa tasa hannunta tana d'iba tana zubawa fuskarta,
had'i da cewa " wake up please Sanah,
cikin takunsa na isa da tak'ama ya tak'o gabanta ya tsaya,
ya kai wajen minti biyu zuwa uku tsaye a kanta yana kallanta,
ganin yadda duk ilahirin jikinta ke kerrrma da tsuma yasa shi,
sunkuyawa a hankali ya d'ogota ya tsaida ita a gabansa bisa k'afafunta,
hannunshi duka biyun kan kafad'unta,
Yana kallan cikin kwayar idanta,
cikin kid'ima Sanah tace " mafarki ne ko?
" Please kace man mafarki ne,
kace man abinda kunnawa na suka ji ba gaskiya bane,
ta fad'a idanta cikin nasa,
fuskarsa d'auke da murmushi yace " no Sanah ba mafarki kike ba,
sannan abinda kunnuwanki suka ji gaskiya ne ba k'arya ba,
INA SANKI! ya k'ara fad'a yana matsa kafad'arta,
sai lokacin Sanah ta k'ara tabbatarwa kanta abinda kunnanta suka ji gaskiya ne ba wai mafarki take ba,
a hankali tasa hannunta ta zame hannunsa dake kan kafad'arta yana faman aikin mammatsa mata,
idanta cikin nashi take kallansa tana ja baya had'i da girgiza masa kanta,
hawaye na zubowa daga idanta,
ta kasa koda furta kalma d'aya ,
sai k'ifk'ifta ido take yi ,
da sauri Sir Moli ya nufi inda take,
da sauri ta dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu,
cikin muryar kuka tace " ni kake so?
Ta fad'a tana nuna kanta, still tana cigaba da yin baya,
tana kuma girgiza kanta,
"yanzu ni Sanah kake so?
" Ni kake furtawa kalmar so?
" Kai fa Malami nane tun daga secondary school ko ka manta ne?
Zayyi magana ta k'ara d'aga masa hannunta,
ba musu yayi shiru yana kallanta cikin tashin hankali da firgici,
" please don't reject me, dan Allah karki ce a'a please,
idan kika k'i k'arb'a ta wallahi ina iya mutuwa,
Sanah baki san tsawon lokacin dana d'auka ina fama da dakon soyayyarki ba,
wallahi nasha wahala sosai akan ki,
ya fad'a kamar zayyi ihuuu,
Sanah ko ido ta k'ura masa cike da tsantsar mammakinsa,
kasa magana tayi sai faman girgiza masa kanta take,
tana yarfa hannu,
hannunta ya rik'o tayi saurin fisgizewa,
ya kuma rik'o hannunta gam cikin nashi had'i kafeta da ido kamar zayyi kuka sai " please! please!! please!! yake cewa,
ido ta runtse da k'arfi hawaye na zubowa daga cikin idonta tana cigaba da girgiza masa kanta,
cikin rawar murya tace " kayi hak'uri amma gaskiya ban tab'a yin soyayya da kai balle har na iya aurenka,
tana fad'a ta juya ta d'auki jakarta da wayarta tayi hanyar fita,
da sauri Sir Moli ya juya da niyyar bin bayanta,
hannunta ta d'aga masa batare data jiyo ba had'i da cewa " wallahi ban tab'a yin soyayya da kai,
juyawa Sir Moli yayi ya sunkuya had'i da dafa table,
cike da bak'in ciki ya busar da iska had'i da cusa hannunsa cikin sumar kanshi,
yana daga sunkuyan ya juya ya kalli bayanta,,
cikin takaici ya bugi table d'in da k'arfi,
glass table d'in ya tarwatse sakamakon dukansa da Sir Moli yayi,
hannunsa ya yanke take hannun ya shiga zubar da jini,
k'arar bashewa glass table d'in ce tasa Sanah juyawa ta d'an kalleshi kana ta juya ta cigaba da tafiya,
bayanta Sir Moli ya kafe da ido harta b'ace masa,
iska ya k'ara busarwa had'i da dafe goshinshi da hannunsa d'aya,
d'aya hannunsa kuma ya cusa cikin kwantaccen gashin kansa,
batare daya kula da uban jinin da yake zubarwa ba.
A ransa kuwa ji yake kamar zai mutu,
yana jin idan duniya da abinda ke cikinta zasu taru babu wanda ya isa ya hana shi mallakar Sanah sai Allah,
dan yasan rabuwa da Sanah tamkar rabuwa da ransa da rayuwarsa ne,
har ya gwammaci numfashinka ya d'auke daya rasa Sanah,
yana jinta har cikin ransa, da zuciyarsa da duk wata gab'a jini da jijiya dake jikinsa,
duk numfashin daya shak'a yana shak'arsa ne da ita muddin aka raba shi da Sanarsa hakan dai-dai yake da muturwa,
ya kai 30 minutes a wajen yana zancen zuci kana ya mik'e yana tafiya yana had'a hanya ya nufi waje,
dakyar ya k'arasa inda motarsa ke aje ya bud'e ya shiga ya had'a kai da sitiyari sai da ya d'auki lokaci mai tsayi kafin yayiwa motar key cikin mutuwar jiki ya nufi gidansa dake Lamid'o Crescent.
K'afarta take jifawa kawai batare datasan inda take jefa ta ba,
cike da tsantsar mamakinsa had'i da jinjina al'amarin cikin ranta,
wai yau ita Sir Moli ke furta yana santa,
ba kunya ba tsoran ido kai lalle maza sai a barsu,
ita babu ma abinda yafi d'aure mata kai sai yadda ya marairaice mata yana neman yi mata kuka,
jin horn d'in mota ne ya dawo da ita cikin hayyacinta,
da sauri ta kalli gabanta,
a tsakiyar babban titi ta tsinci kanta,
cike da tsoro ta zaro ido tana kallan traffic (go slow) d'in data had'a,
mutane sai magana suke yi mata,
wasu ma fad'a suke yi hannu ta d'aga masu tana basu hak'uri tana gangarawa gefen titi,
mai adai-dai ta sahu ta tare ta shiga,
batare data fad'a masa inda zai kaita ba,
shiru mai adai-daitan yayi yana jiran ta sanar da shi inda zai kaita,
ganin bata da niyyar yin magana ne yasa shi cewa " Hajiya ina zan kai ki ne?
"Hmmmm tace had'i da sauke nannauyan ajiyar zuciya tace " Jan bulo BUK Road,
"kin san kud'inki ko?
Mai adai-daitan ya fad'a yana kallanta ta cikin mudubi,
" badamuwa muje!
ta fad'a tana kallan titi, ba musu yaja suka tafi,
har k'ofar gida ya kaita ta sauko a hankali kana ta bud'e jakarta ta d'auko 1k ta mik'a masa,
yana k'ok'arin bata canji yaga ta juya zata shige gida,
da sauri yace " Hajiya canjinki fa?
"Ka barshi, ta fad'a tak'aice batare data jiyo ba,
cike da murna ya shiga yi mata godiya had'i da kwarara mata addu'o'i dan kwata-kwata tafiyar batafi 150 ba,
bata k'ara bi ta kansa ba tayi shigewarta cikin gida,
bata tsaya shiga part d'in Halan ba,
tayi wucewarta part d'in Mamu direct bedroom d'inta ta shige ta fad'a kan bed rigingine tana kallan ceiling,
Sir Moli yana komawa gida yayi parking a harabar gidan ya bud'e motar ya fito,
bai ko tsaya rufe motar ba ya shiga cikin gidan direct bathroom ya shige ya sakarwa kansa shower had'i da dafe bango da duka hannayensa,
idansa rufe ya d'aga kansa sama ruwan yana sauka kan fuskarsa,
batare daya cire kayan jikinsa ba.
Sai da ya dad'e cikin bathroom kana ya cire kayansa ya fito d'aure da towel,
cikin sanyin jiki ya kwanta a akan bed yana tunane-tunane,
ya jima a haka kafin ya mik'e ya gabatar da sallar magrib da ishsha,
jin cikinsa na k'ugi yasa shi mik'ewa ya nufi parlor ko kallan abincin dake jere akan dinning table wanda kukunsa ya girka masa bayyi ba,
fridge ya nufa ya bud'e ya d'auko fresh milk ya kafa tsukakken bakinsa,
bai ajiye ba sai da ya shanye tass,
kana ya ajiye rubar ya koma bedroom ya zube kan bed yana tunanin muddin Sanah tak'i amincewa da shi yaya ne makowar rayuwarsa,
a haka bacci b'arawo yayi awon gaba dashi.
Itama ta dad'e a kwance kana ta mik'e ta fad'a bathroom tayi wanka had'i da d'auro alwala ta fito ta sanya kaya marasa nauyi tayi sallah,
kana ta fita parlor Mamu na zaune hannunta rik'e da waya,
Sanah na fitowa Mamu ta kalle ta tace " au dama kin dawo?
Gudun kar Mamu tayi mata fad'an tayi dare yasata cewa " wa ni!?
"Ai tun d'azu na dawo har nayi bacci na tashi nayi wanka ma,
Mamu tace " to amma banji shigowarki ba,
yanzu ma ke nake kira a waya fa,
dariya tayi tana zama kusa da Mamu tace " Mamu yunwa nake ji,
da gatse Mamu tace " to kwanta abincin yazo har inda kike ya same ki,
ta d'an turo baki tace " kai Mamu,
Mamu tace " Sanah ko dai ni kike so na tashi na d'ebo maki abinki na kawo maki ne?
Ido ta zaro tana dariya ta mik'e tace " wace ni rufa man asiri Mamu,
Mamu tace " to ai alamar hakan na gani,
ta shige kitchen tana dariya,
shinkafa da wake da mai da yaji ta zuba a plate sai had'i salad da kwai data zubo gefe,
ta sanya cikin tray kana ta d'auko fanta ta fito ta koma parlor'n ta zauna kusa da Mamu,
Mamu ta kalli d'an abincin da Sanah ta zubo kana ta tab'e baki tace " gulma!
idan wani yaji kina cewa yunwa yunwa sai ya d'auka zaki iya cinye duniya,
amma ji d'an abincin da kika zubo kamar zaki bawa baby,
Sanah tayi dariya tana cin abincinta babu abinda ya dameta dan harta manta da wani Sir Moli,
tace " yanzu kuma da cin abinci ne dani da yawa a sani gaba,
yanzu kuma bana ci da yawa kowa ya saka ni gaba,
Mamu tace " ubanwa zai dame ki keda cikinki?
Idan kinci kanki idan ma baki ci ba kanki,
bata kuma cewa komai ba harta gama cin abincinta ta kwashe kayan ta maida kitchen ta wanke kana ta dawo parlor kusa da Mamu ta zaune,
Mamu ta ture ta tana cewa " to mage uwar san jiki ke baki da aiki sai zama jikin mutum duk kibi ki nanik'e mutum,
shigewa jikin Mamu ta kuma yi tana dariya tace " to Mamu idan ban nanik'i jikinki ba jikinwa zan nanik'a my sweet Mom,
Mamu tace " hmmm baki abin magana wato yaran yanzu Allah yayi muku wayo duk ta inda aka biyo muku sai kun b'ulle ko?
Sanah tayi dariya tana k'ara shigewa jikin Mamu,
murmushi Mamu tayi had'i da girgiza kai batare datace komai ba,
nan jikin Mamu Sanah ta fara bacci,
sai wajen k'arfe tara Mamu ta tasheta ta shiga d'aki tana had'a hanya,
tana shiga d'aki ta fad'a kan bed ta cigaba da baccinta,
around 2:30am na dare Sir Moli ya farka,
daga wahalallan baccinsa mai cike da tarin mafarkanta,
juye-juye yayi tayi ya kasa komawa baccin saboda tarin tunanin da sukayi mishi yawa,
ganin ya kasa komawa baccin yasa shi mik'ewa cikin sanyin jiki ya shiga bathroom,
ya d'auro alwala, bedroom d'insa ya koma ya zura jallabiya,
had'i da shinfid'a sallaya ya riga jera nafilfili,
bai sallame sallar ba sai da yaji an fara kiran sallar farko kana yayi sallama,
ya d'aga hannayensa sama yana kwararo addu'a akan Allah ya bashi nasara akan Sanarsa ya kuma d'ora shi akanta,
ta so shi koda kwatankwacin yadda yake santa ne,
sai da yaji an kira salla kana ya shafa addu'ar,
a hankali ya mik'e ya fita masallacin dake manne da jikin gidansa......
bayan sun idar da sallar sai da ya tsaya yayi karatun Qur'an,
had'i da k'ara yin addu'o'i kana ya koma gida,
har ya kwanta kan bed yaji yana san jin muryarta,
batare da yayi wani kokonta ba ya mik'e ya d'auko wayarsa,
kana yayi dialing number ta dan ya dad'e da mallakar number ta,
jin wayar ta soma ringing yasa gabansa fad'uwa da k'arfi,
cikin ransa yace " ya salam yau ni ne da tsoran mace,
Sanah na kwance cikin duniyar dadda d'an baccinta taji ringing d'in wayarta,
bata ko motsa ba har kiran ya tsinke,
kamar bazai sake kira ba sai kuma ya sake yin dialing,
sama-sama cikin bacci ta kuma jiyo ringing d'in wayarta,
tsaki tayi kana ta shiga laluban wayar batare data motsa kota bud'e idanta ba,
cikin bacci tayi picking had'i da kara wayar a kunnenta,
" hello tace cikin muryar masu bacci,
ido ya lumshe had'i da dafe saitin zuciyarsa saboda yadda ta buga da tsananin k'arfi da jin sautin muryarta,
cikin bacci ta kuma cewa " hello!,
jin anyi shiru yasa Sanah cire wayar daga kunnenta ta bud'e idanta dakyar ta kalli screen d'in wayar,
tana gyara gashin kanta daya zubo ya rufe mata fuska,
special number ta gani,
wayar ta kuma mayarwa kunnenta tace " hello!,
sai da ya d'auki lokaci kafin
a hankali ya bud'e idansa had'i da saita kanta yace " tashi kiyi sallah ya fad'a cikin sanyin murya kamar ba Sir Moli ba,
jin muryar Sir Moli yasa ta saurin bud'e idanta tarr had'i da cire wayar daga kunnenta ta k'ara kallan wayar cike da mamaki,
cikin zazzak'ar muryarsa yace " ki tashi kiyi sallah,
a hankali ta mayar da wayar kunnenta,
tana gyara kwanciya tace " ina ka samu number ta?
Bai bata amsar tambayarta ba yace " I said wake up & pray,
zata kuma yin magana yace " nace ki tashi kiyi sallah ko!?
Ya fad'a a tsawace,
baki ta turo kamar yana ganinta cikin muryar bacci tace " to!
yace " ke! ni kike turowa baki!?
Ido ta zaro had'i cire wayar daga kunnenta ta kuma dubawa kana ta mayar da wayar kunnenta tace " ni kuma?
Yace " a'a ni,
shiru tayi batace komai ba, tana lumshe ido saboda baccin bai sake ta ba,
yace " tashi!
cikin sanyin murya tace " na tashi ai,
yace " tashi zaune to,
mamaki ne ya k'ara kamata na yadda akayi yasan bata tashi zaune ba still tana kwance,
"mamaki ko?
Ido ta kuma zarowo zatayi magana yace " tashi zaune,
a hankali Sanah ta tashi zaune,
yace " tashi tsaye nan ma ba musu ta mik'e tsayen kamar yadda ya umarce ta,
yace " shiga bathroom, "to tace tana murza idanta dake cike da bacci sai da yaji k'arar bud'e k'ofar bathroom kana ya kashe wayar batare da yayi magana ba,
alwala ta d'auro kana ta fito ta shinfid'a prayer mart ta zura hijab,
kana ta tada sallar, sai da alfijir ya keto kana ta shafa addu'ar ta koma ta kwanta,
shiko yana kashe wayar kashingid'a yayi had'i da lumshe idansa har bacci yayi awon gaba dashi,
k'arfe 8:00am na safe alarm d'in dake kan bedside drawer ya hau ruri,
a hankali ya mik'e hannunsa ya kashe alarm d'in,
ya d'an jima kwance kafin ya juya a hankali,
dakyar ya bud'e idansa kana ya mik'e ya shiga bathroom,
wanka yayi ya shirya cikin d'anyar gizna dark blue takalminsa cover shoe na kamfanin nike agogon hannunsa rolex ya d'ora hula black,
kasancewar shi fari fat sai kayan sukayi mugun amsar shi sukayi mashi kyau,
designer perfumes ya fesa kala-kala,
kana ya fito parlor iskewa yayi har kukunsa ya gama jera masa abinci akan dinning table,
baiko kalli inda abincin yake ba ya fita,
k'arfe tara dai-dai na safe motarsa tayi parking a harabar makarantar,
sai da ya d'auki lokaci cikin motar kafin ya zuro k'afarsa d'aya a hankali k'asa,
sai da akayi seconds kana ya zuro d'aya k'afar,
nan ma sai da aka d'an d'auki lokaci mara tsawo,
kafin ya fito gaba d'ayansa,
hankalin gaba d'aya jama'ar dake wajen yayi kansa,
"Woooow! OMG! cewar gaba d'aya mutanen dake wajen,
" Allah yayi halitta anan wata yarinya ta fad'a,
cikin takunsa na isa da tak'ama had'i da izza ya shiga takawa zuwa office d'insa,
yayinda gaba d'aya hakalin kowa yana kansa ba iyakacin mata kad'ai ke kallansa ba har maza sun kafe shi da ido,
sai da ya shige office kana kowa ya maida hankalinsa jikinsa,
yana shiga cikin office d'insa ya zauna kan sofa had'i da jan tsoki yace " mayu kawai،
aiki Sir Moli ya fara yi a cikin system d'insa kasancewar next week za'a soma second semester exam,
duk bayan minti d'aya biyu sai Sir Moli ya d'ago kai ya kalli get ta window had'i da duba agogon hannunsa,
aikin kawai yake yi amma gaba d'aya hankali da nutsuwarsa yana wajen Sanah,
ganin har k'arfe sha d'aya na safe Sanah bana shigo makaranta ba,
yasa shi mik'ewa ya koma kan sofa ya kishingid'a had'i da lumshe idonsa,
idansa lumshe ya ciro wayarsa daga cikin aljihu had'i da bud'e idansa a hankali ya sauke a kan wayar ya d'auki lokaci yana kallan wayar had'i da juyata a hannunsa,
yana tunanin ya kirata ko karya kira ta,
inda daga k'arshe ya yanke shawarar kiranta,
batare da b'ata lokaci ba yayi dialing number ta.
Sanah na kitchen tana girkin rana ta jiyo wayarta na ringing a parlor,
hannunta ta goge da towel kana ta nufi parlor'n da sauri gudun kar kiran ya yanke,
ganin number Sir Moli ce yasa ta jan tsoki had'i da maida wayar ta aje ta koma kitchen ta cigaba da aikinta,
har wayar ta tsinke k'ara kiran wayar akayi a karo biyu,
Mamu tace " wai ni Sanah wannan ba wayarki bace ake kira?
" eh, race,
Mamu tace " shine kuma dan iskanci kina ji ana kiranki bazaki d'aga ba?
Shiru Sanah tayi batace komai ba,
a fusace Mamu tace " dan ubanki zo ki d'auki wayar nan tun kafin na sab'ar miki,
baki ta turo had'i da goge hannunta da towel ta fita,
sai cika take tana batsewa ta d'auki wayar,
" hello tace,
sai da ya lumshe ido kana yace " me kike ina kira baki yi picking ba,
fuska ta kuma had'ewa kana tace " abinda ya dace,
idansa dake lumshe yayi saurin bud'ewa yace " ke! ni kike fad'awa haka,
halin naki zaki fara ko?
Baki ta cuno kana tace " wanne irin hali ne dani?
"Bak'in hali ya bata amsa kai tsaye,
murmushi tayi mai sauti kana tace " a hakan dai,
ya gane abinda take nufi dan haka yayi murmushi amma sai gyara muryarsa yace " uban me ya hanaki zuwa makaranta yau?
Jin yadda yake magana a dak'ile kamar an sashi dole yasata tab'e baki tace " bamu da lectures yau,
yace " to idan baku da lectures sai k'i zuwa kiyi karatu bayan kinsan next week zaku fara exam d'in second semester,
" zanzo gobe in sha Allah ta fad'a cikin k'osawa da wayar,
" ki tabbatar kinzo yau dan zanyi CA,
dariya ce ta kwace mata dan ta gane wayon Sir Moli so yake ya ganta,
batare da ya kuma yin magana ba ya kashe wayar yana murmushi,
dan shi kansa ya bawa kansa dariyar.
Washe gari tun around 9:30am na safe Sanah ta shigo makaranta,
Aarib na ajiyeta shima motarsa nayin parking ya juma a cikin motar yana kallanta,
kana ya fito ya nufi office d'insa batare daya ko kalli inda take ba,
itama bata kalli inda yake ba ta nufi class d'insu,
tana gaf da shiga class d'in taji wayarta ta soma ringing tsayawa tayi cak had'i da kallan screen d'in wayar,
ganin Masifaffe D'an Anace dan haka tayi saving number Sir Moli,
yasa yin rolling sexy eyes d'inta kana tayi picking,
"zo! yace a tak'aice, batare daya jira amsarta ba ya kashe wayar,
tsoki taja kana ta nufi office d'insa,
sai da ya bata izinin shigowa kana ta shiga,
kishingid'e ta same shi akan sofa idanuwanshi lumshe,
takai wajen minti 10 batare daya ko motsa ba,
ganin haka yasata cewa " gani!
banza yayi da ita batare daya motsa ba,
baki ta turo ta kuma cewa gani nazo,
" ni kike zumb'uruwa baki!?
Kallansa Sanah tayi taga still idanshi rufe suke,
yace " duk sanda na kuma yi maki magana kika zumb'uro min baki,
sai na murd'e bakin ya fad'a batare daya bud'e idanshi ba,
ganin an kuma d'aukar lokaci bayyi mata magana ba yasa ta cewa " ko in tafi ne?
" Da ni na kira ki!?
Kallanshi tayi cike da mamakin rainin hankalinsa, kanta ta kawar gefe tak'i bashi amsa,
" tambayarki nake yi?
A dak'ile tace " kai ne?
A hankali ya bud'e idansa ya sauke su a kanta yace " wana aika ya kira ki?
Banza tayi dashi bata bashi amsa ba,
yace " uhnnn ke nake sauraro,
" yanzu fa ka kira a waya kace nazo,
ido ya zaro kamar gaske yace " wa d'in ni!?
Ya fad'a yana nuna kansa,
kallansa kawai tayi batare datace komai ba,
yace " ni ban kira ba, amma muga number data kira kin, ya fad'a yana mik'a mata hannu,
k'in bashi wayar tayi ta kauda kanta gefe danta lura hankali yake san raina mata,
ido ya kafe ta dashi still bai janye hannunsa ba yace " bani wayar,
sosai Sanah ta had'e ranta murtuk yadda kasan anyi mata sammacin mutuwa,
kamar bazata bashi ba sai kuma ta mik'a masa,
ya amsa had'i da yin dialing number shi,
bai san sanda dariya ta kufce masa ba,
ganin tayi saving number shi Masifaffe d'an anace,
kallashi tayi fuskarta had'e murtuk tace " me!?
Screen d'in wayar ya juya mata,
cike da jin kunya Sanah ta sunyar da kanta k'asa,
yana dariya yace " ashe ni d'an anace me?
" Kuma masifaffe ko?
Ya fad'a yana kallanta,
instead of ta bashi amsa sai tayi k'asa da kanta tana wasa da 'yan yatsunta,
a hankali ya mik'e ya nufeta daf da ita yaje ta yadda suna jiyo numfashi da bugun zuciyar junansa,
had'i da jefa idanshi cikin nata,
yana kallan cikin kwayar idanta,
sexy kallan dayake yi mata ne yasa ta saurin sunkuyar da kanta k'asa,
hannu yasa ya d'ago hab'arta while idanshi na kanta bai ko k'iftawa,
muryarshi can k'asan mak'ogwaro yace " bazan canja yadda kikayi saving number ta da hannuna ba,
but I promise you zan saka hannun daya rubuta hakan ya canja da kanshi ya mayar da my sweet ko my heart, ko my heartbeat,
ko hub, ko my life etc,
a hankali ta d'ago kanta tayi murmushi had'i da cewa " never!
murmushi yayi shima kana ya sanya hannuwansa ya dafe bango ya sanya ta tsakiyarshi,
had'i da sunkuyo da kansa yakai bakinshi saitin kunnenta,
muryarshi can k'asa yace " kefa kika ce na bawa soyayya dama ko my soul!?
sexy eyes d'inta zuba mishi,,
yadda yake yi mata wani irin kallo yasa ta saurin mayar da idanta k'asa,
maryarshi bata fita sosai yace " to na bata dama yanzu kamar yadda kika ce Mol'is happiness an princess,
ya fad'a yana goga hancinsa saman wuyanta,
ido Sanah ta runtse da k'arfi kana ta bud'e,
cikin kerrrmar jiki ta sunkuya tabi ta gefenshi yana k'ok'arin rik'ota tayi saurin bud'e k'ofa ta fita jikinta na tsuma,
a k'ofar office d'in ta tsaya had'i da jingina da bango tana mayar da numfashi,
mayafinta ta sanya tana goge gumin dake zubo mata,
shiko tana fita ya zube kan sofa had'i da runtse idanshi da k'arfi yana sauraron yadda zuciyarshi ke bugawa da tsanannin k'arfi,
shi kanshi yana mamakin mugun son dayake yi mata da harya ke yin tasiri mai k'arfi a kanshi yake sanya shi losing control idan ya ganta koya kasance tare da ita.
Da daddre around 9:00pm Sir Moli ya kira Sanah tak'i yin picking,
ya k'ara yin dialing amma tak'i d'agawa,
murmushi yayi ya tura mata text,
_cikar mutum shine wanda yasan dad'in SO yasan d'acin K'I, ba burgewa bane ka nace akan abu d'aya mutum wayayye kuma mai ilimi shike bam-bamce tsakanin aya da tsakuwa, ki gwada yin Soyayya dan ki san inda duniya ta dosa, ki jarraba amincewa da soyayyata dan ki san dad'in rayuwa_
haka ya kwanta cike da bak'in cikin rashin jin muryarta,
Sanah na kwance a bedroom taji k'arar shigowar text a hankali ta lalubi wayar,
ta bud'e ta karanta tsoki taja had'i dayin cilli da wayar,
da asuba ma ya kira ta 3 times amma tak'in yin picking,
bayan ya idar da sallar asuba ya tura mata text,
_So yafi yunwa zafi, yafi guba da gobara illa, yakan lahanta duk inda yake in har bai samu matsugunni da masauki ba, nasan baki san SO ba Sanah amma ina san ki bani dama dan na d'and'ana miki zak'in SO, na tabbatar zakiyi alfari da ni_
wayar na gefen ta yayinda da take zaune kan sallaya bata duba text d'inba sai da ta dama azkar,
tsoki taja bayan ta gama karanta text d'in kana ta haye kan bed tayi kwanciyarta,
koda ta tashi da safe wani text d'in ta sake gani ya turo mata,
_I can't live with you, without you what's my worth, if I get separate from you then I'll get separate from self (my world), because you are the 1 I most love madly, you're the only 1 my eyes want to see, my ears want hear her voice, I LOVE YOU MORE MOST SANAH_
" Hmmm Allah ya kyauta muku wasu mazan kam basu da kunya wallahi ta fad'a tana fita daga bedroom d'in,
tun daga ranar Sanah bata k'ara shiga makaranta ba, haka duk kiran da Sir Moli zayyi mata kwata-kwata bata yin picking,
ba kuma ta tab'a yi mishi replaying text d'in shi ko sau d'aya ba,
shiko bai tab'a fashin kiran ta ba a rana yana kiranta wajen 5 tyms,
text kam ba'a magana dan Allah ne kad'ai yasan yawan text d'in dayake turo mata,
sosai hankalin Sir Moli yayi mugun tashi ganin kwata-kwata Sanah tak'i sauraransa,
ya shiga cikin matsananciyar damuwa ko a abinci ya baya iya ci,
babu abinda ke damunta sai wutar santa dake faman azalzalar zuciyarsa koyaushe tana k'ara ruruwa yana jin koza rasa ransa bazai tab'a iya rabuwa da ita ba..........
Sanah bata k'ara shiga makaranta ba,
sai ranar da zasu fara exam din second semester,
kasancewar a late ta shiga school d'in yasa ta yin sauri kamar zata tashi sama,
tako yi sa'a ba'a shigar musu ba,
kusa da Fatima (Rose) taje ta zauna,
Fatima ta mik'a mata hannu had'i dayi mata sallama,
Sanah ta amsa fuskarta d'auke da murmushi,
Fatima tace " kin kusa yin late fa!
Sanah zatayi maka supervisor d'insu ya shigo, hakan yasata yin shiru,
su Sanah basu fito daga exam ba sai 5:30pm na yamma,
Sir Moli na ganin 'yan department d'in su sun fara fitowa yayi saurin mik'ewa ya sab'i system & phones d'insa ya fita,
office d'insa ya tsaya ya rufe kana ya nufi motarsa cikin takunsa na izza,
a ransa yana murnar zai ganta yau dan ita ya tsaya jira ya gama abinda yake yi 3:00pm na yamma,
ita ya tsaya jira ta fito,
a matuk'ar gajiye su Sanah suka fito,
ita da wani d'an department d'in su suka jero suna tafiya suna hira,
fuskokinsu d'auke da murmushi kai da kallansu kasan basu da wata damuwa a duniya,
Sanah sai murmushi take yi masa shima yana yi mata suna kallan juna,
a hankali Sir Moli ya bud'e bayan motarsa ya saka system da wayoyinsa cikin motar ya ajesu kan kujera,
cikin nutsuwa ya juya ya zagaya mazaunin driver motar ya bud'e da niyar shiga,
key d'in motar ya kufce daga hannunshi ya fad'i k'asa cikin nutsuwa ya sunkuya ya d'auki key d'in,
d'agowar da Sir Moli zayyi idanshi ya sauka akan su Sanah,
take bak'in kishi ya saukar masa,
duk ilahirin jikinsa ya d'auki kerrrma da tsuma,
zuciyarsa ta shiga bugawa da tsananin k'arfi,
tana harbawa had'i dayin tsalle kamar zata fasa k'ijinsa ta fito,
ji yayi gaba d'aya yawon bakinsa ya k'afe,
mak'okwaransa ya shiga yi masa d'aci yayinda k'irjinsa ke yi masa soya,
launin idanuwansa suka canja daga farare zuwa asalin jajaye jijiyon kansa suka tashi rud'u-rud'u,
ido ya runtse da k'arfi yana san saitin kansa da nutsuwarsa,
amma ko da ya rufe ido Sanarsa ya cigaba da gani tsaye gaban wani k'ato suna kallan cikin kwayar idan juna,
tana sakar mishi murmushi,
Sanah ko bama tasan yana yi ba balle tasan halin daya shiga,
takalmin k'arfarta ne ya gurd'e tayi bayi luuuuuuuu zata fad'i cikin matsanancin zafin nama matashin sauyin yayi wuf ya rik'o ta fad'a jikinsa,
dai-dai lokacin Sir Moli ya bud'e idanshi had'i da sauke idanshi a kansu,
tashin hankali wanda ba'a saka maka rana,
_*RASHIN SANI*_ wanda hausawa sukace yafi dare duhu shine yasa matashin saurin tare Sanah,
dan daya san abun da zai biyo baya daya barta ta fad'i k'asan koda zata karye,
take Sir Moli yayi losing control ya fita fit daga hayyacinsa,
cikin rawa da kerrrmar jiki ya nufe su gadan-gadan..................
MOMYN ZARAH
[7/7, 4:47 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
3⃣2⃣
Cikin rawar jiki da matsananciyar kerrrma ya nufe su gadan-gadan,
Sir Moli na zuwa bayyi wata-wata ba ya makawa matashin saurayin gigitattun marika har guda hud'u a jere ji kake kauuuuuu,
a kid'ime Sanah ta d'ago kanta tana gyara tsaiwarta,
shiko yaron durk'ushewa yayi a wajen,
take jin sa da ganinsa suka yi d'aukewar wucin gadi,
yakai wajen minti biyu zuwa uku kana saurayin ya dawo normal,
cikin zafin rai saurayin ya d'ago cikin matsananciyar zafin zuciya ya d'aga hannunsa da niyyar rama marin da Sir Moli yayi masa,
cak ya tsaida hannunsa ganin wanda ke gabansa tsaye cikin wani irin yanayi,
a d'an tsorace saurayin ya zaro ido waje,
had'i dayin baya yana sauke hannunsa,
a k'ufule Sir Moli ya kalle shi da jajayen idanuwanshi,
yace " do you want hit me!?
Ya tambayi yarin yana k'ara matsawa kusa da shi,
sadda kansa k'asa yaron yayi cikin alamun tsoro yana ja da baya,
" oya hit! me Sir Moli ya fad'a a tsawace,
" I'm sorry Sir ban san kai bane,
" I said hit! me Sir Moli ya kuma fad'a cikin d'aga murya da hargowa,
maganar da Sir Moli yayi da k'arfi ce ta jayo hankalin sauran jama'ar dake wajen,
kowa ya tsaya cak had'i da mayar da hankalin su gare su dan ganin abinda ke faruwa,
a kid'ime saurayin ya bud'e baki da niyyar yin magana Sir Moli ya k'ara maka masa gigitattatun marika biyu,
take bakin saurayin ya fashe jini ya fara zuba,
ganin jinin yasa Sanah zaro ido had'i da sanya hannayenta ta rufe bakinta cike da tsoro,
" sorry Si........!
kafin yaron ya k'arasa Sir Moli ya k'ara maka masa mari,
yana cewa " am I your mate?
Kai yaron ya girgiza masa cike da tsoro dan yanayin Sir Moli kad'ai ya isa ya d'imauta yaron,
mari Sir Moli ya k'ara maka masa yace " dan uwarka ba magana nake yi maka ba?
Yaron zayyi magana Sir Moli ya k'ara d'auke shi da mari,
daga yaron har sauran jama'ar dake wajen babu wanda yasan takamaiman laifin da yayi masa,
ganin Sir Moli yana niyyar illata yaron da gigitattun marikansa yasa Sanah saurin shiga tsakaiyarsu,
ta tare Sir Moli hawaye na zuba daga idonta ta take girgiza masa kanta had'i da cewa " no please!
d'ago jajayen idanuwansa yayi ya zuba cikin nata yana kallan cikin kwayar idonta,
" move! ya fad'a a fusace...
" please! ta kuma fad'a kuka na neman kufce mata,
da k'arfi Sir Moli yace " I said move!
yadda yayi maganar yasa duk ilahirin jikinta d'aukar tsuma da kerrrma,
sosai bala'in tsoro yayi masifar shiga jikin Sanah,
zagaye ta yayi yana sake nufar yaron dake durk'ushe yana goge jinin dake zubo masa,
dakewa Sanah tayi had'i da sake zagayawa ta shiga tsakiyarsu,
ta jefa idanta cikin nashi tana kallanshi tarrr ido cikin ido,
cike da tsantsar tsiwa tace " wai meyasa kai azzalumi ne?
"If I say I love him what will you do?
Ta fad'a k'asa-k'asa yadda babu mai jinta sai shi kad'ai,
ido ya zuba mata cikin takaici da tsananin zafin da zuciyarsa ke yi masa,
cikin tsiwa Sanah tace " I hate you and I love h.......
tassssss tassss Sir Moli ya d'auke ta da gigitattun marika itama,
babu wanda yaji abinda tace masa sai k'arar marin da yayi mata suka ji,
cikin zafin rai Sir Moli ya k'ara nufar yaron gadan-gadan,
da sauri Sanah ta kuma shan gabansa hannunta dafe saman kuncinta,
tace " wallahi matuk'ar ina raye baka isa ka sake tab'a shi ba,
abinka da mai bak'ar zuciya,
wanda yake dama a k'ufule aiko cikin zafin rai ya rik'o hannunta ya jefata gefe,
Sanah ta zube k'asa, da sauri ta kuma mik'ewa ta k'ara nufarsa tana k'ok'arin k'ara tare shi,
dan kar ya kuma dukan yaron,
amma kafin ta k'arasa har ya isa ga yaron ya cakumo wuyanshi ya k'ara kifa masa mari,
da k'arfi cikin tsiwa Sanah tace " I HATE YOU!!!,
and I will never accept you as a lover,
cak Sir Moli ya tsaya had'i da sakin yaron ya fad'i k'asa,
baya yayi ya koma jikin motarsa,
ya kifa kansa yana ji kamar yayi hauka,
a hankali ya d'ago yasa hannunsa ya dafe motar had'i da sunkuyawa yana kallan saman motar daga gaba.
Sai lokacin matashin saurayin da sauran jama'ar dake wajen suka fahimci abinda ke faruwa tsakanin Sanah da Sir Moli,
mik'ewa tsaye Sir Moli yayi had'i da rik'e k'ugunsa da hannu d'aya,
ya cusa d'aya hannun cikin kwantacciyar sumar kansa,
da sauri Sanah ta mik'e ta nufi inda Yaron yake durk'ushe,
yana faman goge jinin dake zubo masa daga bakinsa,
k'ok'arin goge masa jinin ta fara yi,
Yaron yayi saurin ja da baya cike da tsoro,
k'ara binsa Sanah tayi takai hannunta saitin bakinsa tana goge masa bakin tace " am sorry nice na jawo maka,
ta fad'a cike da tausayawa tana kallan yaron,
kallo d'aya zakayi ma Yaron ka tabbatar a matuk'ar firgice yake,
duk ilahirin jikinsa kerrrma yake,
kamar zaka ce masa k'et! ya ruga,
ido Sir Moli ya zufawa Sanah yana jin zuciyarsa kamar zata fashe saboda tsananin rad'ad'i,
da k'una had'i da zugin da take masa,
glass d'in motar ya daka da k'arfi,
aiko glass d'in ya warwatse yaji ciwo sosai a hannunsa jini sai zuba yake,
fuskarsa a had'e yadda kasan anyi masa mammacin mutuwa,
ya kalle ta yace " zo ki shiga mota mu tafi,
ko kallan inda yake Sanah batayi ba balle tasan Allah yayi ruwansa,
a tsawace yace " nace ki shiga mota ko?
Motar dake kusa da shi idan ta motsa kota kalli inda yake to Sanah ta motsa,
ko gezau batayi ba, ji yayi tamkar ya tsaga k'irjinsa ciro ya zuciyarsa,
ya huta akan abinda yake ji,
bak'in ciki ne yasa Sir Moli nufar Sanah,
ganin yadda ya nufo ta gadan-gadan,
yasa gabanta dukan uku masifaffan tsoro ya dirar mata a ranta,
amma ta dake kamar ma bata san yana tahowa ba,
yana k'arasowa bai tsaya yi mata magana ba,
ya damk'i hannunta, ya fara janta da k'arfi,
turjewa Sanah ta fara yi tana cewa " meye haka Malam!?
" Ina zaka kai ni ne!?
" Ni ka sake ni, ka wani rik'e ni, sai kace uban.........!
tassssss tasssss Sir Moli ya maka mata mari,
bata san lokacin data fasa gigitaccen kuka had'i da dafe kuncita ba,
ko ta kwanta bai bi ba ya cigaba da janta,
yana isa ga motar ya bid'e ya danna ta ciki kana ya zagaya ya shiga had'i da yiwa motar key ya figeta kamar zai tashi sama,
cike da tsantsar mamaki students suka bi bayan motar da kallo har ya b'ace masu,
kana kowa ya watse suna maganganu k'asa-k'asa,
sosai Sanah ke kuka kamar ranta zai fita,
cikin kuka ta kalle shi tace " ka fara takura man! ka fara shiga rayuwa ta! ka fara matsawa duniya ta kana d'auke man fari ciki,
haka nan ka kama d'an mutane ka daka danka fishi gata da kud'i had'i da k'arfi,
saboda tsabar zalunci,
kai ubana ne da zaka zab'a man mutanen da zanyi huld'a dasu?
" Wallahi baka isa ka hanani kula da wanda naga dama ba,
nace ban sanka ban sanka ko ana so dole ne?
" Ko kana tunanin wad'annan abubuwa dake su zasu na so ka na amince dakai?
" Idan ma kana tsammanin mallakar zuciyata,
ko zan so ka, to tun wuri ma ka sake tunani dan Allah ban tab'a aurenka ko maza sun k'are babu abinda zanyi da kai,
tuk'in kawai Sir Moli yake yi amma kwata-kwata bai san inda kansa yake yi ba,
ji yake kamar ya fasa ihuuuu yayi ta kururuwa ko zai rage masa azabar da zuciyarsa keyi masa,
idanshi sun kad'a sunyi jajir kamar gauta,
zuciyarshi sai tsalle take tamkar zaga tsaga k'irjinsa ta fita,
maganganunta suna masifar dukar masa zuciya,
" ban sanka ban kuma tab'a sanka ARYAN!,
I hate you ARYAN,
mahaukacin burgi Sir Moli ya taka k'uuuuuuuu,
batare daya kalli inda take ba yace " fita!
hawayenta ta goge kana ta kalle shi zatayi magana,
sanin duk abinda zai fita daga bakinta ba kalma ce mai dad'i ba,
kuma ya tabbatar muddin ta k'ara furta bata sanshi koda sau d'aya ne,
a halin yanzu dai-dai yake da mutuwarsa,
dan take numfashi zai d'auke zuciyarsa ta tarwatse,
dan haka yace " I said get out from my car!
ya fad'a a matuk'ar tsawace,
batare da ya kalle ta ba,
jikin Sanah na rawa ta bud'e motar ta fita,
da wani irin mahaukacin gudu ya figi motar kamar wanda ke shirin barin duniyar,
ya bule ta da k'asa yayi gaba,
jin bazai iyayin driving d'in ba,
yasa shi gangarawa bakin hanya yayi parking,
had'i da kifa kanshi jikin sitiyarin motar yana sauke numfashi kamar mai ciwon asma.
Mayafinta ta gyara tana bin bayar motar da uwar harara tace " Allah ya isa na mugu kawai,
ta fad'a tana tsaida adai-daita sahu,
tunda ta shiga adai-daitan take faman magana ciki-ciki har suka k'arasa gida,
biyanshi kud'inshi tayi kana ta shige cikin gida,
part d'in Mamu ta wuce directly,
tayi sa'a bata tadda kowa a parlor'n ba,
dan haka ta wuce cikin bedroom d'inta,
jaka da mayafinta tayi cilli dasu gefe ta fad'a kan bed tayi rub da ciki,
tsoki taja tace " azzalumi haka nan ka kama d'an mutane kayi ta jibga kamar ka samu yaronka,
ta fad'a tana shiga bathroom, tayi wanka ta fito d'aure da towel,
doguwar riga ta zura had'i da shafa lotion ta fesa body spray ta sanya pad kasancewar bata sallah,
harta zauna a bakin bed sai kuma ta mik'e tayi hanyar parlor,
a kitchen ta jiyo motsin Mamu dan haka ta nufi kitchen d'in,
batare da Mamu ta juya ta kalle ta ba tace " kin dawo ashe?
"Eh, Mamu har ma nayi wanka,
ta fad'a tana amsar aikin da Mamun keyi,
ba musu Mamu ta sakar mata tana cewa " bari na shiga ciki nayi wanka da sallah Abbu ya kusa dawowa,
idan kin gama abincin ki jera a dinning table kinji ko?
"To Sanah tace tana cigaba da aikin, Mamu kuma ta fita,
bayan Sanah ta gama girkin ta zuba nata a plate kana ta zuba abincin takai dinning table ta jera kamar yadda Mamu ta umarce ta,
ta d'auki nata abincin ta nufi bedroom d'inta,
kan carpet ta zauna taci abincinta hankalinta kwance babu wata damuwa tattare da ita,
jin ta k'oshi yasata ture plate d'in ta mik'e taje ta wanke hannunta cikin bathroom,
kana ta dawo ta baje saman bed dan mugun bacci take ji,
tsoki Sanah ta ja tunowa da Sir Moli datayi tace " wicked & selfish man,
ta fad'a tana lumshe idanta bata jima a haka ba bacci yayi awon gaba da ita.
Sir Moli yakai wajen 30 minutes tsaye a wajen cikin mota,
a hankali ya d'ago kansa ya kai dubansa gefen hanya,
ya kalli mutanen dake zaune kowa yana harkokinsa cikin kwanciyar hankali,
babu wanda yake tattare da wata damuwa sai annashuwa suke cike da tsantsar farin ciki,
kanshi ya jingina jikin kujerar mota had'i da runtse idanshi da k'arfi,
ya d'an jima a haka kana ya bud'e idon had'i da furzar da iska daga cikin bakinshi,
" hmmmm soyayya! ya fad'a yana sauke nannauyan ajiyar zuciya,
a hankali yayiwa motar key ya jata,
bai tsaya ko'ina ba sai a harabar gidanshi,
cikin nutsuwa ya bud'e motar ya fito ya taka sannu a hankali ya shiga cikin gidan,
tun a parlor ya cire kayanshi yayi naked ya fad'a bathroom ya sakarwa kanshi shower.
Ya dad'e cikin bathroom ruwan shower na hau kanshi kana ya fito d'aure da towel a k'ugunsa,
kansa dayaji yana sara masa sosai ya kuma tabbatar bayan damuwar dayake ciki harda yunwa ma,
yasa ya nufi parlor still yana d'aure da towel d'in a k'ugunsa,
a hankali ya shiga bud'e sahan d'in dake jere saman dinning table,
wanda ke d'auke da abinci kala-kala,
a k'alla sunkai kala bakwai kamar bana cikin mutum d'aya ba,
Sir Moli ji yayi kwata-kwata abincin ya fita ransa bai iya cin komai daga cikin,
fuska ya yamutsa had'i da tab'e baki yana takawa zuwa bakin fridge,
a hankali ya sunkuya ya bud'e ya ciro fresh milk ya b'alle murfinta ya kafa a d'an tsukakken bakinsa,
fresh milk d'in na sauka kan harshensa yaji tamkar mad'aci ya zuba,
sanin idan bai sha ba yunwa tana iya illata shi yasa shi runtse idanshi,
ya kwankwand'a haka nan badan ranshi naso ba,
bai aje rubar ba sai da shanye tassss kana ya jefa rubar cikin dosbin,
cikin nutsuwa ya koma cikin bedroom d'insa ya haye saman bed,
ya kwanta rigingine idanshi na kallan ceiling,
ajiyar zuciya ya sauke da k'arfi yana mik'ewa tsaye had'i da furzar da iska yace " hmmm love!
hannu ya mik'a ya d'auko system d'inshi kana ya dawo kan bed ya kwanta ya bud'e ta,
makeken photon Sanah naga ya bayyana,
sosai nayi mamakin ganin photon,
ba wai dan photon Sanah bane a'a,
sai dan ganin photon Sanah tun suna Roni,
sanye cikin hostel ware, tana dariya,
mamaki na anan, shin tun su Sanah na Roni dama Sir Moli ke santa ko kuwa ya akayi!?
Nasan dai babu amsa tunda ni kai na na kasa fahimtar abinda ke b'oye,
wata folder naga ya shiga wacce gaba d'ayanta babu abinda ke ciki sai pictures d'in Sanah,
anan tsananin mamaki ya dad'a kamani kai na yayi masifar d'aurewa,
dan pictures d'in sun kai 5k har na ranar da ta fara zuwa BUK lokacin daya sanya ta kneeling down,
da lokacin da k'adangare ya fad'a mata jiki a BUK,
da pictures d'inta tun tana Roni,
wasu tana sanye da uniform wasu kuma hostel wares,
har da wad'anda take sanye da kayansa da hularsa da takalminsa a Roni,
dana BUK kai har da wanda take sanye da kayan game d'in Roni,
dana bikin Khulud dana ranar walimar su,
wasu daga cikin pictures d'in tasan anyi su amma wasu da yawansu da alama ba bata sanin lokacin da ake yinsu (d'aukarta),
Hmmmm nace ina kallan Sir Moli cike da tsantsar mamakin wannan al'amari,
ina san na tambaye shi amma tsoron karya kore ni daga cikin bedroom d'insa yasani tsuke baki na,
lalle *_RASHIN SANI......._* ya fi dare duhu!.................
Sir Moli yana cikin kallan pictures d'in yana murmushi bacci ya d'auke shi,
kyakkyawar fuskarshi d'auke da k'ayataccen murmushi.............
Tun da al'amarin nan ya faru tsakanin Sanah da Sir Moli bata k'ara bari ya ganta ba balle har ta kai ga sun keb'e ba,
kullum cikin wasan b'uya take dashi,
duk wata hanya ko huld'a da zata had'ata da Sir Moli Sanah tabi ta rufe ta ruf,
sosai hakan ya haifarwa da Sir Moli matsannanciyar damuwa cikin ranshi da zuciyarshi,
kallo d'aya zaka yi mishi kasan yana cikin muguwar damuwa dake barazanar illata masa ruhi da gangar jikinsa,
ya k'ara komawa so silent yayi muguwar rama ya k'ek'ashe,
ya zama kamar bashi ba idan ka ganshi sai ka rantse bashi ne real ARYAN RAYYAN MOLI ba,
ya sha zama bakin get yana jiranta amma bai tab'a riskar sa'a ya sami ko da ganin ta ba,
wani lokacin har department d'in mu yake zuwa haka nan dan ya samu ganinta amma ko sau d'aya bai ganinta ba,
abun yayi mugun damunsa,
gashi ko zai kwana yana kiranta a waya bata d'agawa,,
ko replay text d'inshi bata tab'a yi mishi ba,
a rana sai ya kira ta sau 10 amma bata d'agawa text kam ba'a magana,
shi babban tashin hankalin shi ma yau zasu gama exam kuma daga yau hutu zasu tafi dan da zarar sun dawo zasu shiga level 2,
itako a nata b'angaren babu abinda ya dameta hankalinta a kwance yake sosai,
dan ko tuna shi ma bata yi, abinda ma bai sani ba,
shine ta dad'e da maka number shi a block list,
text ko idan zai shekara yana turo mata bata ko bud'ewa balle ta karanta.
Sir Moli kwance saman sofa yana tunanin mafita dan yasan yau ne last chance d'inshi,
dan daga yau shikenan sai idan an dawo hutu,
ya dad'e yana tunani kafin wata shawara ta fad'o masa,
da sauri ya mik'e ya fita dan ganin saura baifi 5 minutes ya rage musu su fito daga exam ba,
a hankali cikin tafiyarsa ta isa da tak'ama ya taka ya shiga cikin class d'insu,
sosai ya d'aure fuska kwata-kwata babu alamar wasa,
daga bak'in k'ofa ya tsaya bayan sun gama gaisawa da supervisor d'in su,
ya kalle ta a wulak'ance yace " ke!,
cikin nutsuwa ta d'ago idanta ta kalle shi kawar da idanshi yayi daga kallanta dan gudun kar yayi losing control,
yayi abin kunya gaban students d'inshi,
a dak'ile yace " ke! kinyi CA d'in course d'ina?
Idanta na kanshi tace " eh! nayi,
cikin ko in kula yace " to banga taki ba idan kina da buk'artar cin course d'in sai kizo ki sake wata,
idan kuma baki da buk'ata kina iya bari,
ya fad'a yana fita daga class d'in,
baki Sanah ta tab'e tana bin bayanshi da kallo,
office d'inshi ya koma ya zauna had'i da had'a kai da gwiwa,
yana tunanin zata zo ko bazata zo ba,
duk bayan minti d'aya sai ya kalli agogo had'i da sauke ajiyar zuciya,
kwata-kwata Sanah bata yi tunanin wayo Sir Moli yayi mata ba,
dan haka suna gama exam ta nufi office d'inshi,
daga bakin k'ofa ta tsaya tayi sallama,
jin mutyarta yasashi mik'ewa zumbur kamar wanda aka tsikara da allura,
da sauri ya bud'e mata k'ofar ta shigo fuskarta a tsuke,
k'ofar ya mayar ya rufe had'i da danna mata key,
idonta d'aya da girarta d'aya ta d'age tana tab'a baki,
tace " gani!,
idonshi na kanta yace " have a site please ya fad'a yana nuna mata sofa,
fuska ta k'ara tsukewa ta kauda kanta gefe tace " bani questions d'in,
fuska ya marairace ya koma kalar tausayi,
a hankali ya nufe ta yaje daf da ita ya tsaya cikin raunanniyar murya yace " please Sanah ki taimaka man ki so ni,
ko kwatankwacin yadda nake sanki ne,
danna san har abada bazaki tab'a yi min irin sanda nake yi maki ba,
fuskarta ta kawar gefe batare datace komai ba,
cikin mutuwar jiki ya rik'o hannayenta cikin nashi,
saurin fizge hannunta tayi tace " don't touch me again!
da sauri yace " I'm sorry!
"wallahi Sanah ina sanki ina maki mugun sonki please karki ce a'a ki kalle yadda na canja,
na shiga damuwa sosai Allah ko abincin ban iya ci,
kwata-kwata ban iya yin bacci please my love ki tausaya min ki karb'i soyayya ta,
wallahi kikace a'a ina iya mutuwa zuciyata gaf take da tarwatsewa,
ya fad'a yana dafe saitin zuciyarshi,
cikin tsiwa Sanah ta kalle shi ido cikin ido tace " I said i hate you kuma i can repeat it in millions times in front of any body,
ban sanka ban kuma tab'a sanka har abada ko ana so dole ne?
A hankali Sir Moli ya zame k'asa yayi knelling down a gabanta,
idanshi d'auke da hawaye gwiwoyinsa a k'asa ya durk'usa a gabanta idanshi yana zubar da hawaye...................
MOMYN ZARAH
[7/7, 4:48 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
```DEDICATED TO```
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
_(GARKUWAR MARUBUTA)_
3⃣3⃣
Cike da tsantsar mamaki Sanah tabi Sir Moli da kallo,
tsoro da fargaba suka shige ta,
a hankaki ya rik'o hannunta cikin nashi,
yana kallan cikin kwayar idanta,
while hawaye na cigaba da zubo masa,
yace " wallahi kece rayuwata kece farin cikin duniyata,
muddin baki tare dani ni ba komai bane,
ina sanki so na gaskiya da hak'ik'a ki tausayawa rayuwata Sanah,
ina iyayin komai akan ki dan Allah karki ce a'a My Fiance,
ya k'arasa maganar yana langwab'ar da kanshi gefe,
hawayen dake zubo mata ta sanya hannunta ta goge,
kana ta girgiza masa kanta cikin muryar kuka tace " ka tashi please!
" ban tashi har sai kin ce you love me too,
kuma kin amince zaki aure ni,
"kayi hak'uri ban iya yin soyayya dakai,
" why!?
Ya fad'a cikin raunanniyar murya,
" hmmmm har ka manta abubuwan da suka faru a baya?
" plPlease ki manta da baya mu fuskanci gaba yanzu an if i made mistake at back ki fad'a man zan baki hak'uri na kuma gyara,
Allah nayi miki alk'awarin duk abinda baki so banyin shi,
abinda kike so kawai zanyi please accept me,
" ni dai a'a gaskiya abubuwa sun faru da yawa,
" meye suka faru bayan wanda zai hana ki so ni ko ki aure ni?
" Hmmm tace tana kallanshi durk'ushe gabanta,
" ni dai ka tashi please,
" ban tashi har sai kin amsa min,
" I can't tace tana goge hawayenta,
ranshi ne yayi mugun b'aci jin tace she can't,
cikin b'acin rai ya mik'e ya juya mata baya yana cije lips d'inshi da k'arfi,
had'i da runtse idanshi, d'aya hannunshi ya cusa cikin sumar kanshi,
d'aya hannun kuma ya rik'e k'ugunshi,
yakai 5 minutes a haka kana yace " why Sanah?
Muryarta na rawa tace " kai fa Malami na ne,
how zanyi soyayya da Malami na?
Da k'arfi ya daki table d'inshi yace " dan ni malaminki ne sai akayi yaya?
"Allah ya haramta aure a tsakanin mu ne?
" Wai mai yasa mutane suke san mai da al'ada addini?
"Suke san mai da halak haramun?
" Suke haramtawa kansu abinda Allah ya halarta musu,
kawai dan ina Malaminki shikenan bazaki so ni ko ki aure ni ba?
bayan Allah bai haramta hakan ba,
saunawa akayi haka nasan kema kin sha jin Malami ya auri student d'inshi,
Sanah idan baki so na ne kawai ki fito ki fad'a man kai tsaye har ki d'orawa aiki na,
ta yadda zakisa na tsani aikin,
kuma idan ma aikin ne baki so wallahi a yau zan bar aikin,
dan Allah Sanah kice kin amince dani,
a hankali ya taka zuwa gabanta ya dafa kafad'unta,
ya marairaice fuska sosai yana shirin yi mata kuka yace " please my hope!
" Allah ban iyawa ta fad'a kanta k'asa,
sakinta yayi ya naushi bango da k'arfi,
cikin b'acin rai yace " kina tunanin yanzu na fara sanki?
"Ko kina tunanin sai da naga kin zama mace kin mallaki komai na d'iya mace nake sanki?
Ya fad'a idanshi kanta,
bata bashi amsa ba ta kawar da ganta gefe gabanta yana fad'uwa,
yace " idan dan jikinki ne, na samu dama a kanki yakai sau uku zuwa hud'u,
wacce idan wani abun naki nake so da tuni an dad'e da wuce wajen,
ko a cikin office d'in nan naso keta maki haddi na samu damar yin hakan,
yana maganar yana tafiya inda system d'inshi ke ajiye ya jawo ya bud'e ta,
ya kunna ya shiga folder danaga ya sanyawa sunan heartbeat,
a tsorace Sanah ta zaro ido ganin pictures d'inta,
wanda idan za'a kashe ta bazata iya fad'a adadinsu ba,
pictures d'inta na Roni ya bud'e mata,
a hankali ta fara bin pictures d'in da kallo a trorace gabanta na dukan uku-uku daga b'angare d'aya kuma mamaki ne fal ranta,
wasu tana zaune a cikin class a Roni wasu tana yin game sanye cikin kayan game,
wasu kuma cikin hostel ware,
wasu tana cikin office d'inshi,
har da wanda aka d'auke ta lokacin data saka kayan shi a Roni,
wasu kuma duk a BUK aka d'auke ta,
har da wanda ranar data fara zuwa BUK ne,
wasu tana cafeteria wasu tana zaune cikin garden wasu a office d'inshi dana bikin Khulud,
har da na walimar su wasu kuma tana cikin bedroom d'inta wasu tana parlor wasu ma a part d'in Halan aka d'auke ta,
cike da mamaki had'i da tsoro dan ta fara tunanin Sir Moli ba mutum bane,
bakinta na rawa tace " wad'annan duk tayaya suka faru?
Guntun murmushin gefen bakin baki yayi,
had'i da hard'e hannayenshi a k'irjinshi yana kallanta,
yace " idan kina tunanin saboda yanzu kin zama mace ki mallaki booms & hips,
nake sanki kinyi kuskure Sanah,
dan tun kafin ki mallaki komai nake fama had'i da d'awainiya da ciwon sanki,
since before ki zama matured,
tun kafin ke kanki kisan wacece ke,
tun ranar dana fara d'ora idona akanki na fara sanki،
da farko banyi tunanin sanki nake yi ba,
nayi tsammanin wani al'amarin kawai daban,
hakan ne yasa duk abinda zakiyi man a Roni ban iya dukanki,
sai daga baya a hankali a hankali na fara jin abun na sauyawa,
ban tabbatar da sanki nake yi ba sai ranar da kika suma ranar da Khulud bata da lafiya,
anan na tabbatarwa kai na sanki nake yi,
dan ji nayi kamar nayi hauka,
tun da kuka bar Roni na tsinci kai na cikin k'unci da damuwa,
nayi haukan nemanki kamar hauka a duniya Sanah,
nasha bak'ar wahala wajen nemanki da gidanku amma na kasa samunki,
na koma Roni wajen sau uku neman address da phone number gidanku,
amma ban samu ba, asalima ko wanda yasan sunan unguwarku ban samu ba,
kullum addu'a ta Allah ya k'ara nuna man ke a rayuwata ya kuma mallaka man ke,
kwatsam rana d'aya na ganki a BUK,
kuma a department d'in dana ke koyarwa,
hmmmm kin san meyasa nasaki knelling down ranar?
Hmmmm Sanah kam ba baka sai kunne saboda tsantsar mamaki,
cigaba da magana yayi " saboda na rink'a ganinki sosai,
wallahi ranar ban san me na koyar ba,
koyarwar kawai nayi,
bayan na koma office kasa daurewa nayi saboda tsantsar farin ciki kuka nayi sosai saboda murnar kawai na ganki,
ranar kwana nayi ina sallah da godewa Allah,
a ranar nayi rabon kud'in dani kai na ban san ko nawa bane,
naje gidanjen marayu na bada taimako,
wallahi ina yin parking mota ta a makarantar,
nasan kina cikin BUK a lokacin,
kin san dalili?
Ido kawai ta zuba mishi batare datayi magana ba,
murmushin bak'in ciki ya sake yi yace " tun kina Roni muddin kina waje ko kina kusa da inda nake,
ko kina tahowa ko kuma kina kusa dani bugun zuciyata yake canjawa zuciyata ta shiga bugawa da tsananin k'arfi kamar zata fito,
muddin naji haka nasan kina wajen,
shiyasa ranar dana shigo BUK naji bugun zuciyata ya canja nasan kina kusa dani,
kin san a lokacin me nayi?
Sanin bata da bakin yin magana yasa shi cigaba da magana batare daya jira amsarta ba,
" runtse ido na nayi da k'arfi had'i da dafe saitin zuciyata tace " Ya salam!
wallahi lokacin dana d'ora ido na kanki kusan zaucewa nayi,
dan kad'an ya rage na fad'i k'asa,
idan baki manta ba lokacin sai da na dafe bango,
cikin nutsuwa Sir Moli ya tako zuwa gabanta ya d'ora hannunshi saman kumantunta,
ya tallafe fuskarta had'i da marairace fuska yace " ina sanki fiye da komai da kowa a duniya,
ina sanki fiye da yadda nake san kai na da rayuwata,
saboda ke na fara so a rayuwata,
you're my first love and daga kanki babu wata dan zuciyata a kulle take,
bata ji bata ganin kowacce mace a duniya sai ke kad'ai,
kuma nayi miki alk'awarin ke kad'ai zata cigaba da so har ranar da zata tsaya cak,
nasha bak'ar wahala akan ki nayi yawo da bulayi cikin duniya nemanki amma na kasa samunki,
ranar da kika sake shigowa rayuwata,
a ranar na bi bayanku a mota har zuwa gidan,
lokacin nasan gidanku idan baki manta ba
ranar dana fara d'auki cikin mota ta,
ni da Leems ai kai tsaye na kaiki gidanku har kike tambaya ta ya akayi na san gidanku,
please kema ki so na! ya fad'a yana kallanta ido cikin ido,
muryarta na rawa tace " ina ka samu duk wad'annan?
Murmushi yayi yana kallan cikin kwayar idanta yace " wasu ni da kai na ke d'aukarki,
wasu kuma cikin wayarki na samu,
pictures d'in walimarku da wad'anda kikayi cikin gidanku su cikin wayarki na same su,
na bikin Khulud wasu cikin wayarki na samu wasu kuma ni da kai na d'auke ki,
ina sanki da yawa da yawa ko?
Ya fad'a cikin shagwab'a yana langwab'ar da kanshi gefe,
baki ta tab'e had'i da gyara mayafinta,
tace " ina question d'in?
" Dama babu wani CA da zakiyi,
na fad'i hakan ne dan na samu ganinki,
shiru tayi had'i da kafe shi da idonta,
cikin zuciyarta kuma tana mamakinsa,
ta d'an d'auki lokaci tana kallanshi ido cikin ido,
kafin ta juya batare datace masa komai ba,
ta fara k'ok'arin bud'e k'ofa zata fita,
da sauri yasha gabanta muryarsa na rawa yace " Allah ina iya mutuwa idan baki amsa man ba,
please ki taimaka ki bani amsa,
batare data kalle shi ba tace bud'e man k'ofa,
" please ya fad'a yana had'e hannunsa alamar rok'o,
" I said ka bud'e man k'ofa na fita,
ta fad'a a d'an zafafe,
" please karki yi man haka Sanah,
idan kika k'i ni mutuwa zanyi dan Allah kice man yes and you love me too،
dan Allah ka bud'e man k'ofa kar wani yazo shigowa yaji k'ofa rufe yayi tsammanin wani abu,
" to sai me?
"Duk wanda zayyi tsammanin wani abun ya dad'e bayyi ba,
ni akanki ban gudun komai zai faru ya faru ban tsoro da fargabar komai,
shiru tayi had'i da kauda kanta gefe,
marairacewa ya k'ara yi yace " dan Allah ki taimaka kar sanki ya kashe ni,
idan kika ce a'a ban san yadda zanyi ba,
nasan dai mutuwa zan yi,
a fusace tace " to ka mutun mana idan ka mutu ina ruwan wani,
wanda yayi asara shi yayi ka dame ni da mutuwa zakayi idan nace a'a,
to tace a'a ban sanka ban kuma tab'a sanka ko ana soyayya dole ne,
haba kaji ni da mutum ka saka ni gaba ka dame ni,
shiru yayi yana kallanta harta kai k'arshe,
zayyi magana tayi saurin cewa " nace ka bud'e man k'ofa ko?
" Ki bud'e yace muryarshi na rawa,
had'i da nuna mata key d'in kan sofa,
tsoki taja kana ta d'auki key d'in ta bud'e k'ofar ta fita had'i da banko mishi k'ofar,
cikin mutuwar jiki Sir Moli yayi baya ya zube kan sofa,
gami da had'a kai da gwiwa ji yake kamar yayi hauka ko ya fasa ihuuu,
ya gwammace yayi kuka akan irin azabar da zuciyarshi keyi masa,
idanshi ya kad'a yayi jajir jijiyoyin kanshi sun fito sunyi rud'u-rud'u,
ji yayi gaba d'aya garin kano ya fice mata fit a rai,
mik'ewa yayi jikinsa na rawa ya d'auki system da wayoyinsa kad'ai ya fita,
anan cikin makantar yabar motarshi ya hau adai-adaita ya nufi Airport kai tsaye ko gidanshi bai je ba,
kasancewar Moli's Family sanannu ne a k'asa yasa yana zuwa aka tashi jirgi na musamman saboda dashi zuwa Maiduguri,
dan lokacin dayaje babu jirgin Maiduguri a k'asa.
Tana fita daga office d'inshi ta nufi get,
tana gaf da fita tajiyo muryar Aarib a bayanta yana cewa " princess baki ganni bane?
Cak ta tsaya had'i da k'ak'aro murmushin yak'e,
tace " lah a she kazo Yaya?
"Eh tun dazu nazo ina nan inata faman jiranki,
na kira number ki switch up,
kai ta dafe had'i da cewa " opss! na manta ban kunna wayar ba,
kasan idan zamu shiga exam dole sai mun kashe wayar mu,
ido ya k'ura mata yana karantar yanayinta,
idonta tayi rolling tace " Yaya wannan kallan fa?
Murmushi yayi yana bud'e mata k'ofa yace " princess lafiya kike kuwa?
Zama tayi cikin motar shima ya zagaya ya zauna mazaunin driver,
d'an kallanshi tayi kana tace " me ka gani?
" yanayinki naga ya canja kuma kamar jikinki ma yana rayuwa,
" hmmm tace tana kallan waje,
" please fad'a man abinda yake damanki,
"hmmmm ta kuma cewa tana kallan waje,
bata k'ara magana ba har suka k'arasa gida,
babu rok'o da magiyar da Aarib bayyi mata kan ta sanar dashi damuwarta ba amma tak'i amsa masa,
dan ita kanta idan za'a kashe ta bata san hak'ik'anin abinda yake damunta ba,
haka nan take jin jiki da zuciyarta babu dad'i,
take jin jikinta yayi mata mugun sanyi,
koda suka k'arasa gida bata san ma sun isa cikin gida har yayi parking ba,
a hankali Aarib ya d'ora hannunshi kan nata,
had'i da kiran sunnanta cikin sanyin murya " Sanah,
bata motsa ba dan bata jira ba,
k'ara kiran sunanta yayi still bata amsa ba,
ido Aarib ya k'ura mata na tsayin lokaci,
kafin ya d'an matsa hannunta da k'arfi had'i da cewa " Sanah!,
'yar k'ara ta saki a hankali tana yarfa hannun,
cikin shagwab'a ta kalli shi tace " kai Yaya!,
hannun Aarib ya ruk'o yace " sorry da zafi ko?
"Eh tace tana cigaba da yarfa hannun,
" mugani Aarib yace,
bata kula shi ba ta zunb'uro baki had'i da bud'e k'ofar ta fita,
bayanta yabi yana dariya had'i da kiran sunanta,
ko juyowa batayi ba tayi shigewarta part d'in Mamu,
kanshi ya girgiza yana murmushi kana ya shige part d'in shi,
Mamu na zaune a parlor Sanah ta shigo,
kan sofa ta zauna tana yarfa hannun cikin shagwab'a ta fara k'ok'arin yin kuka,
Mamu tace " ke kuma ke da wa?
"Yaya Aarib ne yayi man mugunta,
tsoki Mamu taja tana cigaba da kallan tv,
abinka da wanda ke jiran k'iris dan dama a wuya take tana neman dalilin yin kuka,
haka nan take jin ranta da zuciyarta babu dad'i,
ta tsinci kanta cikin matsanancin bak'in ciki,
ganin abinda Mamu tayi mata yasa ta fasa kuka,
had'i da mik'ewa ta shige bedroom d'inta,
bayanta Mamu tabi da kallo،، tana mamakinta dan kallo d'aya tayi mata ta fuskanci akwai abinda ke damunta,
ba abinda Aarib yayi mata bane yasa ta kuka ba,
dan idan da sabo sun saba,
kamar zata mik'e tabi bayanta sai kuma ta fasa ta mayar da hankalinta ga kallan da take yi,
tana shiga bedroom ta fad'a kan bed had'i da sakin rikitaccen kuka mai cin rai da zuciya,
ta jima tana cin uban kuka da idan za'a kashe ta bata san dalilin yin sa ba,
asalima bata san abinda yake damunta ba,
mik'ewa tayi ta shige bathroom tayi wanka had'i da d'auro alwala,
doguwar riga kawai ta zura ko lotion bata shafa ba,
ta koma tayi kwanciyarta batare data bi takan abinci ba.
Jirginshi nayin landing a Maiduguri yayi saurin mik'ewa,
Maiduguri bata tab'a yi mishi nisa irin na yau ba,
dan babu abinda yake so illa ya ganshi cikin gidansu gaban family da iyayenshi,
ko ya samu sassauci,
yana fitowa ya d'auki shatar taxi ya nufi gida,
a bakin get ya sauka ya biya mai taxi kana ya nufi cikin gidan,
tun daga bakin get sojojin dake tsaye suka shiga sara mishi,
suna k'amewa had'i da sandarewa,
ko ta kansu bai bi ba ya shige cikin gidan,
direct part d'in Nailah ya nufa,
a parlor ya iske ta zaune saman sofa,
tsayawa yayi daga bakin k'ofa ya jingina bayanshi da bango,
had'i da kafeta da ido, jin k'anshin d'anta yasa Nailah d'aga kanta a hankali ta kalli bakin k'ofar,
bisa mamakinta ta ganshi tsaye ya kafe ta da ido yana kallanta,
ganin yadda yanayinsa ya canja ya firgice lokaci d'aya ya zama kamar ba Aryan Moli ba,
yasa ta cewa " bata amince ba ko?
Ta fad'a cike da tausayawa instead of ya bata amsa sai ya nufe ta da sauri,
ya zauna k'asa kan tails had'i da d'ora kanshi saman cinyarta,
yana zubar da hawaye yana sauke ajiyar zuciya,
cike da tsantsar tausayawa Nailah ta d'ora hannunta saman kanshi tana shafawa ta kuma cewa " bata amince ba ko?
K'ok'arin yin magana ya soma amma ya kasa furta koda harafi d'aya,
ruwan sanyi tasa mai aiki ta kawo mishi,
da kanta ta karb'a ta bud'e ta bashi yasha,
sai da ta bari ya d'an lafa kana,
tace " meyasa bata amince ba?
Dakyar cikin muryar kuka wacce bata fita sosai yace " bata sona Nailah!,
" kuma ka sanar da ita irin mugun son da kake yi mata?
Kai ya d'agawa Nailah alamar eh,
d'an shiru Nailah tayi tana shafa kanshi,
" Aryan na san kana san yarinyar nan sosai tunda ka d'auki tsawon lokaci kana faman nemanta da jiranta,
Nailah ta fad'a cikin tausayi,
" ai bama ke kad'ai ba kowa yasan irin matsannancin son da Aryan keyiwa Sanarsa,
duk wanda yasan Aryan koda na kwana d'aya ne dole yasan Sanah,
duk kunya da kawaicin Aryan har ya kasa b'oye san da yake yi mata,
wannan kad'ai ya isa ya shaidawa duniya yana santa,
Hilwa ya fad'a yana zama kan sofa,
Haidar dake shigowa yayi dariya,
yace " yau dai ga jarimin d'an Nailah da Hilwa yana kuka kan mace,
tab kuka kan mace andai ji kunya,
duk k'ababa da tak'amar taka anan suka k'are?
Sir Moli baiko kalli inda Haidar dake tsaye yana dariya had'i da tsokarsa ba,
Hilwa yace " karka damar man d'a, kabar shi ma da abinda yake ji,
karka k'ara mishi zafi akan wani zafin,
kai waya san mekayi akan taka soyayyar,
kuma wanda yasha wuya kan so da soyayya had'i da mace sai yafi wanda bai sha ba sanin darajar su,
Nailah tace " karka damu kaji Son,
kira man ita,
muryarshi na creaking yace " bata picking wayata koda zan shekara ina kiranta,
" ka gwada kiranta yanzu,
" me zaki ce mata Nailah?
Ya fad'a kamar mai koyon magana,
" kai dai ka kira min ka sani ko sa'ar soyayyarka a hannu na take,
kaga ka kasa nemo soyayyarka da kanka kenan sai dai a nemo maka,
bayyi mata magana ba ya mik'o mata wayarshi bayan ya fito mata da number,
dariya Haidar ya kuma sakawa yana cewa " Moli's in dangerous & blind love,
wai waga d'an Hilwa da soyayya,
da lokacin da ake cewa ka fad'a mata kana santa tun kafin kayi sake,
wani yayi maka k'afa ba cikin tak'ama da gadara kake cewa Sanah taka kai kad'ai bace,
dan kai aka halicce ta ba, you make sure she love you as much as you love her
gashi nan yanzu ka gani ai dama hausawa sunce a bari ya huce shike kawo rabon wani,
cikin shagwab'a Sir Moli yace " Hilwa ka ganshi ko,
Hilwa yace " rabu dashi kaji my son,
in sha Allah you will be
succeeding,
dialing number Sanah Nailah tayi a wayarta,
tana shafa kan Aryan da d'aya hannunta,
Sanah na kwance cikin damuwa da bata san dalilin yin ta ba,
taji wayarta na ruri tsaki tayi had'i da juyawa wayar baya,
cikin ranta tana jin zuciyarta kamar zata fashe,
katsewa wayar tayi, ba'a jima ba aka k'ara kira,
tsoki ta kuma ja kana ta mik'e hannu tana daga kwancen ta lalubo wayar,
ganin bak'uwar number yasata sharewa,
kamar bazata yi picking ba sai kuma ta d'aga wayar a hankali,
bakinta d'auke da sallama a hand free Nailah ta sanya wayar jin Sanah tayi picking,
cikin sanyin murya ta sake yin sallama,
da sauri ya d'ago kansa daga kan cinyar Nailah,
yatsa Nailah ta d'ora akan lips d'inta had'i da cewa " shhhhhhh alamar yayi shiru kar yayi magana,
sallama Sanah ta sake yi a karo na uku,
take Nailah taji yarinyar ta k'ara shiga ranta,
dama tunda ta ganta cikin picture taji yarinyar ta burgeta sosai,
jin Sanah na niyyar kashe wayar yasa Nailah saurin cewa " amin wa'alaikissalam,
" ina wuni?
Sanah tace daga d'aya b'angaren,
cikin fara'a Nailah ta amsa gaisuwar,
d'an shiru Sanah tana jiran taji kowaye,
" mahaifiyar Aryan Moli ce Nailah ta fad'a,
da sauri Sanah ta mik'e zaune tana cewa " lah yi hak'uri ban sani ba,
" bakomai Nailah ta fad'a tana murmushi,
sake gaidata Sanah tayi cikin faran-faran yadda kasan babu komai tsakaninta da Sir Moli,
Nailah zatayi magana network ya fara season da sauri Sanah ta fara cewa " hello! hello!,
ita Nailah na jin Sanah ita ce dai bata jinta,
" ya salam ta fad'a tana dafe kanta,
Allah yasa dai ba wani abun ne ya same shi ba,
murmushin manya Nailah tayi jin abinda Sanah tace kana ta kashe wayar,
ido ya lumshe yana jin mugun dad'i na ratsa shi ta ko'ina,
idanshi ya bud'e yace " Nailah sake kiranta please,
murmushi ta kuma tace " ko da ban kira ta ba ita da kanta zata kira ni,
cike da mamaki yace " that's impossible,
bata so na fa!
ya fad'a yana langwab'ar da kanshi gefe,
" inji wa ya fad'a?
"Ita da kanta ta fad'a yakai 10 times,
murmushi Nailah ta kuma yi kana tace " wallahi tana sanka,
tana yi maka mahaukacin so ma,
wanda ita kanta bata san hakan ba,
" how!
yace cike da tsantsar mamaki,
" baka ji lokacin dana kira ta muryarta ta nuna tana cikin damuwa ba,
daga ji tana cikin damuwa akan abinda ya faru tsakaninku ne d'azu,
then dana ce maka mahaifiyarka ce baka ji yadda ta amsa min ba faran-faran,
idan bata sanka bazata karb'i mahaifiyarka haka ba balle harta mutunta ba,
saboda duk mutumin da bai sanka to bai san jininka da kowa naka,
even friend & nervous d'inka bai tab'a sansu,
wannan ya tabbatar min da itama tana sanka ta dai fad'i bata sanka ne kawai,
amma deep down tana sanka,
Haidar yace " kuma daga k'arshe baka ji abinda tace ba?
Kallan Haidar yayi batare dayace komai ba,
Haidar yace " at last cewa tayi ya salam Allah dai yasa ba wani abun ne ya sake ka ba,
wanda yake sanka ne kad'ai zayyi gudun kar wani mugun abun ya same ka,
kuma shi ne zai shiga damuwa da tashin hankali har yaji babu dad'i idan yaji wani abun ya same ka,
amma wanda bai sanka ko ajikinshi,
asalima sai dai yaji dad'i yayi murna da farin ciki,
kawai dai bazata karb'i soyayyarka bane saboda wasu dalilan,
amma kaje kayi tunani ka gano wad'anne dalilan.......
shiru yayi jin wayar Nailah na ringing,
murmushi tayi had'i da d'ago mishi wayar tace " you see!
murmushi yayi cikin matsanancin farin ciki yace " pick Nailah,
d'an duka Nailah ta kai mishi tace " mara kunya,
ka bari ta katse mana, da sauri ya zaro ido yace " what ta katse fa kika ce?
" Eh sai na kira ta da kai na ba,
daga jin muryarta tana da hankali da cikekkiyar tarbiya da nutsuwa,
" ki kira ta Nailah wayar ta katse,
dak'uwa tayi mishi kana ta sake dialing number ta,
tana soma ringing tayi picking cikin nutsuwa,
bakin ta d'auke da sallama,
d'an shiru Sanah tayi tana jiran taji abinda Nailah zatace,
" daughter ya kukayi da Aryan ne?
Cikin alamun jin kunya Sanah tace " bakomai,
Nailah tace " Sanah Aryan yana mugun sanki sosai,
ya sha wahala sosai akanki tunda nake dashi bai tab'a zama yace man yana san mace ba sai akanki,
kece mace ta farko daya kasa b'oye soyayyar ki cikin ranshi,
ya fito da ita kowa ya sani duk family d'inmu babu wanda bai sanki ba,
babu wanda baida labarin mugun son da Aryan yake miki,
gaba d'aya bangon part d'in shi picture's d'inki ne ta ko'ina,
saura biyar muna kawo mishi mata ya aura cikin family yana k'i saboda ke tunda muka haife shi bai tab'a yi mana musu ko gardama ba sai akanki,
bai tab'a sab'a umarnin mu ba sai akanki,
Aryan yaro ne mai taurin rai da k'arfin zuciya amma ya zauna yana kuka gaban kowa kanki,
bawai dan he's my son nake fad'a maki haka ba,
a'a saboda ke 'yata ce nake fad'a maki hakan,
dan wallahi Allah idan kika rasa wanda yake sanki kamar Aryan,
bazaki tab'a samun wanda zai soki koda kwatankwacin nashi bane,
ki auri wanda yafi sanki shine riba,
dan sai yafi lallab'aki yafi gudun b'acin ranki,
I know him and I know he love you so much,
Sanah ina baki sharawa akan Aryan amma kiyi tunani kinji daughter,
cikin sanyin jiki ta sauke ajiyar zuciya a hankali,
kana tace " nagode sosai in sha Allah zanyi tunani akai,
murmushi Nailah tayi kana tayi mata sallah kana ta kashe wayar,
a hankali Sir Moli ya d'ago kai ya kalli Nailah yace " thank you so much Mom like no other,
Haidar yace " mu fa?
Zayyi magana Hilwa yace " kyale shi kaji Son je kayi wanka kazo muci abinci,
Haidar yayi dariya yace " rago mai kuka kan mace kawai,
daga yau an daina cika mana baki ana mana k'ababa,
kallan Haidar yayi yace " akwai ranar bada amsa'a ya fad'a yana fita,
yana shiga part d'in shi ya zube kan sofa yana sauke ajiyar zuciya.
Aarib kwance saman bed d'inshi idanshi kan ceiling da gani tunani yake mai zurfi,
ya dad'e haka kana ya sauke ajiyar zuciya,
a fili yace " tabbas akwai abinda ke damun my Sanah kuma na tabbatar abin ya shafi soyayya,
saboda daga office d'inshi ta fito,
kuma yadda jikinta ke rawa da yadda yanayinta ya nuna ya nuna yanayin soyayya ne,
mik'ewa yayi zaune had'i da tallafe hab'arsa yace " karfa nayi sake,
karna tsaya kallan ruwa kwad'o yayi man k'afa,
aiko ban tab'a bari wani yazo rana tsaka daga sama ya kwace man ita,
Allah ya sani ina san Sanah tun tana yarinya k'arama nake ta faman dakwan soyayyarta,
ya fad'a yana nufar window shi,
a hankali ya d'aga labule ya lek'a,
Abbu da Dide had'i da Gahez & Danish ya haugo zaune a harabar gidan,
dama wani lokacin suna zama haka musamman ma idan suna da mahimmiyar maganar da zasu tattauna,
murmushi yayi yana sakin labulen yace " ga dama ta samu ta neman auren Sanah,
nasan idan na bari wannan damar ta wuce kafin na k'ara samun wata kamar ta za'a dad'e,
da sauri ya nufi k'ofa ya fita bibbiyu ya rink'a taka steps jikinshi na rawa ya fita harabar gidan ya nufi su Abbu dan gabatar da neman auren Sanah.....................
MOMYN ZARAH
[7/7, 4:54 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
3⃣4⃣
Yana k'arasawa ya durk'usa har k'asa ya gaida su,
yana niyyar yin magana Dide yace " yauwa dama yanzu nake shirin tashi,
tunda Allah ya kawo ka shikenan,
d'auko man wayata tana kan side table a parlor,
ba musu Aarib ya mik'e dan shi yaro ne mai tsananin jin magana da biyayyar iyaye,
parlor ya shiga ya fara dudduba wayar a inda Dide yace masa amma bai ganta ba,
ganin ya dad'e bai dawo ba yasa Dide mik'ewa yana ce musu bari naje na d'auko wayar nan,
kasan wani bai ganin ajiyar wani,
Abbu yayi murmushi batare dayace komai ba,
parlor'n Dide ya iske shi yana dube-dube,
wayar Dide ya kalla kana ya mayar da kallanshi ga Aarib yace " yanzu idan maganar gani akayi muku,
sai kuce kun fimu gani saboda mun tsufa,
ya fad'a yana d'aukar wayar,
murmushi Aarib yayi yace " ban kula da ita ba, kuma fa har wajen na duba,
Dide yace " kai dai ka yarda baka gani sosai,
dan haka kaje ayi maka medical glass,
ya fad'a yana fita a baya Aarib ya bishi shima yana nufar inda su Diden ke zaune,
tsayawa Dide yayi had'i da juyowa yace " lafiya naga kana bi na?
Kansa ya shafa had'i da sunkuyar da kanshi k'asa yace " eh,
" me zakayi?
Shiru Aarib yayi cike da kunya,
tsaiwa Dide ya gyara yace " naga kamar da magana a bakin,
fad'i ina jinka,
k'ara k'asa yayi da kanshi had'i shafa kanshi yace " dama magana nake san yi daku!
cikin mamaki Dide yace " magana! wacce irin magana?
Kanshi ya shafa cike da jin kunya yace " dama akan Sanah ne,
" me sanar tayi?
Dide ya fad'a duk da ya dad'e da fahimtar Aarib yana san Sanah,
Aarib ya d'an k'ara yin k'asa da kanshi yace " d..a..m..a! d'an shiru yayi kana ya kuma cewa " d...a...m...a!!,
ya fad'a muryarshi na rawa,
Dide yace " kai ban san rainin wayo ka tsayar dani ka sani gaba kana ce man dama dama,
dama me?
K'eyarshi ya d'an sosa kana yace " dama zanje na fad'a muku ne zan aure ta,
ya fad'a cikin matsananciyar kunya da rawar murya,
tsaiwa Dide ya gyara kana yace " kun dai-dai ta junanku ne?
Aarib yace " a'a,
Dide ya kuma cewa " ta san zaka zo ka nemi aurenta?
"A'a, Aarib ya kuma fad'a cikin jin kunya,
Dide yace " kana nufin baka fara neman soyayyarta da yarda ba?
"Eh, yace yana shafa kai,
Dide yace " shine zaka zo ka nemi aurenta kai tsaye,
auren dole kake san ayi mata?
"A'a, yace cikin sanyin murya,
a d'an hasake Dide yace " to me kake san ayi maka yanzu,
kasan muddin ka furta maganar nan gaban Abbu da Baffa (Gahez Baban Abbu Kakan Sanah),
sai an aura maka ita koda bata sanka,
wanda hakan yana iya kawo ruguwar zumuncin da mu kan mu tasowa mukayi muka tarar da iyayen mu nayin shi,
bazan so d'an dana haifa da ciki na ya kawo k'arshen alak'armu ba,
dan haka kaje ka fara neman yardarta da soyayyarta,
idan ta amince ni zanfi kowa farin ciki,
kanshi ya shafa had'i da cewa " in sha Allah zanyi yadda kace Dide,
" yauwa Dide yace yana juyawa,
shima juyawar yayi cikin sanyin jiki ya nufi part d'in shi,
har Dide ya fara tafiya ya kuma juyowa yace " Aarib!,
cikin nutsuwa ya juyo had'i da amsawa " na'am!,
nayi maka gargad'in karka sake ka fitar da maganar nan har sai ta amince,
saboda bana san abunda zai kawo lalacewar zumuncin da iyayen mu suka gino akai,
har mu da ku muka iske, dan Allah ko bayan ran mu duk abinda zai kawo lalacewar zumunci ku gujeshi,
idan har ka gaya mata ta nuna bata sanka ko ta fad'a maka tana da wanda take so,
ko kuma kai da kanka ka fahimci tana da wanda take so please ka bar maganar cikin ranka,
cikin sanyin jiki Aarib yace " tom!,
" Allah yayi muku albarka,
" Amin ya Rabbi.
A hankali Sir Moli ya mik'e ya shiga bathroom ya sakarwa kanshi ruwa,
" hmmm dama haka soyayya ke da zafi?
"Dama haka so yake?
Haka Seeya da sauran masu sona ke ji?
" Allah sarki amma na tausaya masu,
please forgive me ban san haka soyayya take da illa ba,
ya fad'a cikin sanyin murya yana cigaba da wankan,
karo na farko kenan a rayuwarshi daya tausayawa Seeya da sauran mata masu sanshi,
a hankali ya mik'e hannu ya d'auko towel,
ya d'aura a k'ugunsa yana fitowa,
daga shi sai towel d'in ya zauna akan sofa had'i da jingina kansa da bayan kujerar,
idanshi yana kallan ceiling ya dad'e a haka kafin ya sauke ajiyar zuciya,
idanshi lumshe ya lalubi wayarshi ya d'auko,
a hankali ya bud'e idon kana ya shiga rubuta mata text,
_Sanah hasken idanuwa na bazasu tab'a gajiya da kallan ki amatsayin abu mafi k'awatuwar kallo ba, danna tabbata yin hakan bazai tab'a sawa suji sun kaji ko k'osawa da kallanki ba, kece mallakar idaniyar ruhi na, ina sanki my hope_
yana gama rubutawa yayi mata sending,
bata zato ba tsammani yaji k'arar shigowar text wayarshi,
sai da ya d'an yamutsa fuskarshi kana ya duba dan bai tab'a saka ran zata turo mishi reply ba,
da sauri ya zaro ido ganin itace,
cikin rawar jiki ya mik'e zaune had'i bud'ewa,
" Nagode sosai da soyayyarka a gare ni, ya jikanka?
ya karanta text d'in ya kai wajen sau 5,
tsalle yayi cikin murna da tsananin farin ciki,
jikin shi na rawa ya saka kaya ya fita ya nufi part d'in Nailah har yana tuntub'e ,
a tsaye ya iske Nailah da Hilwa suna magana,
cikin d'oki ya fad'a jikinta yana cewa " I'm done nayi sa'a yau she replayed my text Nainah,
Hilwa yace " sake ta kada ka kada man ita ka yawo man aiki,
"thank you so much ya fad'a yana kissing d'inta,
dariya tayi tace " Alhamdulillah yanzu babu sauran kuka kenan,
nayi nawa aikin sauran kuma ya rage naka sai ka dage,
ka k'ara zage dantse,
" thank you best mom in the whole world, I love you mom,
kiss itama tayi mishi had'i da shafa kanshi,
" I love you too son, maza zauna na baka abinci kaci,
ba musu ya nufi kan kujerar dinning d'in ya zauna,
Hilwa ya kalla Haidar yace " oh! mu da muka taya da addu'a kaga ba'ayi mana godiya ba,
balle a rungume mu ayi mana kiss,
Haidar yace " kyale shi Hilwa in ba yau ai akwai gaba,
kuma gaba ai tafi baya yawa,
" wacce gabance tafi baya yawa,
ni yaro na mace d'aya zai aura ban barinshi ya tara mata ya tsofe da wuri kamar su ......... ,
ta fad'a tana kallan Haidar,
Haidar zayyi magana Hilwa yace " a'a rabu dasu kaji, karka ce komai,
kuma aure ai sunnah ce mai k'arfi tun da aka tashi karan farko ma,
cewa akayi mu auri mata bibbiyu ko uku-uku ko hurhud'u,
idan bazamuyi adalci ba mu auri d'aya,
amma bari nima zan raya sunnah na k'ara auren nan nima,
ya fad'a cikin tsokana yana kallan Nailah,
baki ta tab'e had'i da cewa " kuma dai kanku ake ji, idan ka tashi sai ka nemar mata wanj gidan ba wannan ba,
Hilwa da Haidar sukayi dariya,
Haidar ya zagaya b'angaren Nailah had'i da dafa kafad'unta,
yace " daina had'e rai our Nailah babu wata mace da zata shigo daga ke babu k'ari,
Hilwa yace " inji wa!?
Hararsa tayi had'i da cewa " da akwai kenan?
Da sauri Hilwa yace " a'a wane ni babu ke kad'ai ce ya fad'a cikin barkwanci,
a hankali Aryan ya mik'e ya nufi Hilwa ya rungume shi,
had'i da cewa " thank you so much Sweet Hilwa,
d'an ture shi Hilwa yayi yana cewa " ni matsa ka bani guri ba dai ni kayiwa haka ba,
mun b'ata,
kunenshi ya rik'e da duka hannayenshi biyun tare da cewa " I'm sorry, ya fad'a yana d'ora kanshi saman kafad'ar Hilwa,
dariya Hilwa yayi gami da rungume shi,
Haidar yace " oh! ni ne kad'ai a bayiwa godiya,
ko me nayi oho?
Dariya yayi gami da nufarshi ya rungume shi yace " sorry babban Yaya magajin Hilwa,
cikin dariya Haidar ya k'ara matse shi da jikinshi yace " ina ni ina zama magajin Hilwa bayan ga Aryan,
ai babu magajin Hilwa sai kai,
duk suka saka dariya.
Bedroom d'inshi ya koma ya fad'a saman bed ya baje,
yana sakin murmushi kamar mahaukaci sabon kamu,
murmushin ya kuma yi had'i da kifa kanshi saman foam yana shafa kwantacciyar sumar kanshi,
" thank you God for everythings,
ya fad'a while yana sakin murmushi,
yana daga kwancen ya mik'a hannunshi ya lalubo wayar had'i dayin dialing number ta,
idanshi lumshe, har kjran ya tsinke bata d'aga ba,
yana k'ok'arin sake kiranta text ya shigo wayarshi,
ganin number ta yashi saurin tashi zaune,
yana duba text d'in,
_" sallah zanyi idan na gama kuma zan d'an taya Mamu aiki after that I will call you back_
murmushi yayi gami da tura hannunshi cikin yalwataccen gashin kanshi,
kana yayi mata reply ya tura mata amsa,
_" OK badamuwa I'm waiting_
yakai 2hrs yana jiran kiranta amma shiru,
duk bayan minti biyu sai ya duba agogon Rolex dake d'aure a hannunshi,
yana haka bacci yayi awon gaba dashi rik'e da phone a hannunshi,
a b'angarenta kuwa tana idar da sallar ta mik'e ta nufi kitchen,
sai da suka gama aikin tsaf kana ta koma bedroom,
tana shiga ta zarce bathroom,
ta watsa ruwa ta fito d'aure da towel,
bata wani tsaya shafe-shafe ba,
body spray da roxena kawai ta shafa had'i da zura rigar bacci,
harta kwanta ta tuna da kiranshi da zatayi,
a hankali ta mik'e ta d'auko wayarta,
ta koma bakin bed ta zauna had'i dayin dialing number shi,
2 missed call tayi mishi bayyi picking ba,
wayar ta aje saman bedside drawer ta kwanta,
bata dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita.
Sama-sama cikin baccinsa yaji ana kiraye-kirayen sallah,
a hanlaki ya d'an motsa had'i da juyawa,
ya bud'e idanshi kad'an kana ya mayar ya rufe,
jin an kuma kwala kiran sallar ya sashi bud'e idanshi tarrr,
dan ya tabbatarwa kanshi abinda yaji,
jin kiran sallar da gaske ne ya sashi tashi yana shafa kanshi,
" oh! yanzu daga wannan yar kishingid'ar har bacci ya d'auke ni,
lokaci ya ja haka, ya fad'a yana kallan agogo gami da niyyar mik'ewa,
tunowa da ita da yayi ya sashi komawa ya zauna da sauri,
tare da zaro ido waje, da sauri ya mik'e hannu ya d'auki wayar yana dubawa,
ido ya kuma zarowa had'i da cewa " ya salam har 2 missed call,
bacci baka yi ba wallahi, kaja man asarar jin my sweet voice,
ya fad'a yana mik'ewa cikin sanyin jiki,
cikin nutsuwa ya cire a gogon hannunshi ya aje kana ya shiga bathroom,
alwala ya d'auro ya fito ya nufi masjid,
cikin ranshi sai tsoki yake ja,
bayan an idar da sallar sai da ya tsaya yayi azkar da karatun Qur'an,
kana ya nufi gida, yana shiga bedroom d'inshi ya zauna saman bed had'i da d'aukar wayarshi yayi dialling number ta,
tana soma ringing tayi picking,
" hello! tace cikin sanyin murya,
da baya ya fad'a kan bed had'i da lumshe idanshi,
yace " hello ko dai Assalamu Alaikum!,
" yi hak'uri Assalamu Alaika!
ido ya kuma lumshewa kana yace " amin wa'alaikissalam ya wife to be in sha Allah,
shiru tayi bata ce komai ba,
" dama kiranki nayi ki tashi kiyi sallah,
d'an murmushi tayi kana tace " ai na tashi tuni har ma na idar azkar nake yi yanzu,
ranar nan ma dan a gajiye nake sosai shiyasa na makara,
" kina tashi kiyi mana addu'a kenan?
" Hmmm wazayyi sake da lokaci mafi mahimmaci,
da asuba ne fa ake raba duk arzikin duniya da lahira,
ido ya lumshe yana jin dad'in abinda take cewa,
" masha Allah na zab'awa yara na uwa ta gari,
ya fad'a cikin salon jan hankali,
" hmmm tace,
zayyi magana tace " ban k'arasa yin azkar ba,
" OK tom kiyi mana addu'a Allah ya bamu zuri'a ta gari,
" hmmm ta kuma cewa cikin jin kunya,
" I love you, yace,
tace " nagode, ya kuma cewa " I love you,
ta kuma cewa " nagode,
cikin shagwab'a Aryan yace " ni dai a'a ban yarda sai ance man I love you too,
dariya tayi had'i da kashe wayar,
shima dariyar yayi gami da rungume wayar a k'irjinshi idanshi lumshe.
Washe gari tana mik'ewa bathroom ta fad'a tayi brush ta wanke jikinta,
kana ta fito kaya ta canja daga na bacci zuwa riga da zani na tamfa,
har zata fita ta hango wayarta ta koma ta d'auka,
text taga ya turo mata,
a hanlaki ta bud'e ta soma karantawa,
_Not 4 a moment can I stay away from you, I live every day only for you, the way I devoted my self to you, the shade of sorrow ، that it will take a white to pale, I surrender to you now my beloved, you did gv a shade over me like rains , you drenched me in happiness like storms, you have taken away with my sense's my fiance I love you with all my heart_
murmushin jin dad'i tayi a karo na farko data ji dad'in text d'in shi,
har kuma ta murmusa,
kana ta tura mishi reply,
_" thanks for the caring_
kana ta fita iskewa tayi parlor babu kowa da alama Mamu bata tashi ba,
kitchen ta shiga ta had'a breakfast,
ta kawo dinning ta jere agogon dake manne a parlor'n ta kalla taga har 11;20am na safe,
jin gidan yayi mata shiru yasata fita ta nufi part d'in Halan,
a parlor ta iske halan zaune ita kad'ai tana kallan ocean 8 Hollywood film,
kusa da ita Sanah ta zauna had'i da gaida ita, ta amsa cikin fara'a,
gami da tambayarta ya karatu, ta amsa da Alhamdulillah.
Sir Moli yana kwance samun d'an gadon dake gefen swimming pool,
dake cikin gidansu, idanshi lumshe,
yana sak'ar k'amshin furannin dage zagaye da wajen,
musamman k'anshin bishiyar ayaba da vanilla flower,
dan Allah yayi shi da san k'amahin furanni musamman ayaba,
iska ya burar had'i da bud'e idanshi ya zuba cikin swimming pool d'in yana kallan kifayen dake lilk'aya cikin ruwan,
deep down kuma yana jin farin ciki na ratsa duk ilahirin jikinshi ta ko'ina,
cocktail d'in dake gefen shi cikin designer glass cup,
ya kai hannu ya d'auka had'i da kaiwa d'an k'aramin bakin shi ya kurb'a,
kana ya mayar ya ajiye,
a hanlaki ya k'ara lumshe idanshi yana shafa kwantaccen gashin k'irjinshi,
kasancewar babu riga a jikinshi,
daga shi sai 3 quarter kad'ai, jin k'arar shigowar text ya sashi bud'e idanshi a hankali,
cikin nutsuwa yakai hannu ya d'auki wayar gami da bud'e sak'on,
karanta sak'on yaron shi yayi gami da tura mishi amsa,
yana k'ok'arin maida wayar ya ajiye yaga sak'onta,
da sauri ya bud'e yaga wajen 1hr 30 minutes da turo sak'on,
murmushi yayi kana yayi dialing number ta,
yana komawa kwancen,
suna hira da Halan taji wayarta na ringing,
ganin shine yasata yin picking,
" Assalamu Alaikum!
cikin nishad'i ya amsa mata,
tace " ina wuni?
"Lafiya lau ke fa?
" Alhamdulillah,
" I misses you so much just 2 days danayi ban ganki ba ji nake kamar nayi 100yrs,
gaskiya ina sanki da yawa,
ya fad'a cikin shagwab'a,
" nagode tace,
" please even once say you love me dan Allah,
ya fad'a kamar zayyi mata kuka,
" with time, tace,
" haba wanne lokaci kuma muke jira,
bayan kina so na nima ina sanki,
ido ta zaro kamar tana gabanshi tace " inji wa yace ina sanka!?
" baki so na?
Ya fad'a cikin sanyi murya,
shiru tayi bata bashi amsa ba,
dan harga Allah ita kanta bata da tabbacin yes ne ko no,
" to kin gani, aure kad'ai ya rage mana,
idon ta kuma zarowa tace " what!?
Dariya yayi sosai kana yace " yes mana baki ganin Khulud tana gidanta,
murmushi tayi tace " ai kowanne mutum da irin tashi k'addarar,
murmushi yayi yace " haka ne kam,
Allah yasa mu dace,
" Amin ya Allah, tace
yace " shine jiya kika yi man wayo ko?
"Wayon me!? fad'a cikin rashin fahimta,
" Zaki fara ko?
" Me!?
" Halin naki mana,
" wanne irin hali ne dani?
" So kike na fad'a nayi laifi ki samu abin fakaicewa kiyi fishi ko?
Murmushi tayi tace " hmmm kuma dai,
yanzu dai ya Nailah?
Dad'i yaji ya k'ara ratsa shi jinta tambayi mahaifiyarshi,
murmushi yayi yace " tana lafiya lau, tace in fad'a maki ta dank'a amanata a hannunki,
murmushi tayi tace " kace mata ina godiya,
amma ban amsar amanar rigimamme,
ido ya zaro yana dariya yace " tab! ai ke kinfi ni rigima,
tace " na yarda na fika amma ban da akan love,
had'i da saurin kashe wayar,
kai ya dafe yana dariya yace " shikenan fa na bani,
Halan dake gefanta tana sauraronta,
tace " ke kuma dawa kike waya!?
" Sir Moli ne,
Halan tace " yauwa dama ina so na tambayeki,
Sanah tace " me!?
Halan tace " ina kika kuma samo Sir Moli?
Zaro ido tayi had'i da cewa " kamar ya ina na samo shi?
"Eh ba shine naga ya kai ki hospital ba?
D'an yamutsa fuska tayi tace " eh shine, ai lecturer ne a BUK,
dariya Halan tayi tace " tab! kice tarihi ya maimaita kansa,
ashe kun jone da abokin tsamarki da shan caftarki amma shine baki tab'a labarta mana mun je kallo ba,
baki ta tab'e kana tace " ba sai ka damu da abu kake bashi mahimmanci har kake bada labarinsa ba,
da zarar na bar makarantar nake mantawa da Allah yayi shi,
murmushi Halan tayi tace " yanzu mahimmanci kika bashi kenan da kike bani labarinshi?
Banza Sanah tayi da ita tana latsa wayarta,
Halan tayi dariya tace " ya kuma akayi farkon had'uwarku ya gane ki?
Baki ta kuma tab'ewa tace " tab! wannan d'an wulak'ancin da shegen girman kan ne zai nuna ya sanni,
idan yayi haka ai bai cika shi d'in bane,
" to ya kuka yi ki ban labari mana,
Sanah tayi d'an murmushi kana tace " ai lokacin daya fara gani na yi yayi kamar bai tab'a sani na a rayuwarshi ba,
dan tsabar rainin hankali fa har sunana da old secondary school d'ina ya tambaye ni,
Halan ta tuntsure da dariya sosai,
cikin dariya tace " please ban labarin yadda kukayi complete,
Sanah ma na dariyar ta bata labarin dramar da sukayi da shi,
sosai Halan tayi dariya kamar ranta zai fita,
kana tace " kuma har yanzu bayyi aure ba?
" To ni ina zan sani,
" aiko ke zakifi kowa sani dan duk wanda yake neman informations akanshi ke zai samu ya tambaya nan zaiji komai,
" saboda ga k'anin uba na ko?
Halan na dariya tace " a'a ni dai bance ba,
kawai naga kinfi kowa kusanci dashi,
a d'an tsorace ta zaro ido waje kamar zasu fad'o k'asa,
tace " kam! ke ki jiki da wata magana saboda ga miji na ko kuma wanda yake aure na,
Halan tace " eh mana ai ba k'arya nayi ba, dan kinfi kowa dad'ewa dashi,
fuskantar Halan neman magana da san tunzurata take yasata mik'ewa ta nufi kitchen,
Halan tabi bayanta da kallo tana dariya,
had'i da d'aukar wayar Sanah tana duddubawa,
sosai Halan tayi mugun mamaki ganin groups a wayar Sanah,
na WhatsApp wanda a k'alla zasu kai 30,
daga na novels sai na koyar da rayuwar aure had'i da zamantakewar aure,
wasu daga cikin groups d'in suna koyar da rayuwar aure ne a bud'e babu abinda suka b'oyewa ko sakayawa,
fayyace komai suke har yadda mace zata gyara farjinta,
da yadda mace zata kwanta da mijinta,
da magungunan mata kala-kala,
groups d'in akwai harkar ilimi da k'aruwa sosai dan suna koyar da zamantakewar aure, da girke-girke, had'i da hak'uri, juriya, kula da miji, kissa da tarairayar miji,
koda ta shiga Instagram & Facebook d'inta nan ma haka yake,
dan har su jaruma empire tayi following,
da ire-irensu sai dai kwata-kwata babu harkar iskanci da maza cikin groups d'in komai ka gani na karuwa ne,
fitowa tayi daga kitchen hannunta rik'e da tray d'auke da plate an tea cup,
kusa da Halan ta zauna had'i cewa " Aunty Halan me kika shagala kina kallo ne haka?
Ajiyar zuciya ta sauke had'i da cewa " ikon Allah nake kallo cikin wayarki,
cup d'in takai bakinta ta kurb'i tea d'in,
tace " wanne irin ikon Allah kuma?
" Sanah me kike yi da duk wad'annan groups d'in?
Sai da ta kurb'i tea d'inta kana tace " ilimi nake koyo akan rayuwata,
da yadda zan gyara duniya da lahira ta,
ta fad'a in I don't care manner,
Halan tace " shegiya kice zamu zo d'aukar darasi danna kula nema kike ki fimu ilimi a wannan fannin,
murmushi tayi tace " a jami'a fa nake,
" tab aiko ina tausayawa duk wanda ya aure ki,
irin wad'annan abubuwa haka ga manyan mata nan irin AYSHA ALIYU GARKUWA,
da manyan malamai mata masu fad'akarwa kan zamantakewar aure suna ta baku darussa,
harda su magungungunan mata,
tab wannan ai sai buzun Sir Molin namu ina tausaya masa aradu idan ya shiga hannun manyan mata,
d'an tab'a baki tayi kana tace " abinda kuka fi kwarewa akai kenan magungunan mata kad'ai,
to wallahi ba anan take ba, iya gyara farji da kuma iya bada shi shine mace,
kya gama shan magungunan matan naki da jik'e-jik'e aje a auro miki wacce bata shan komai ta fiki wajen miji,
dan haka ki mayar da hankali wajen gyara shi sosai ki kuma kware wajen badashi,
ido Halan ta zuba mata tana mamakinta,
itako ko a kanta yadda kasan ba'ita keyin maganar ba,
Halan tace " to ai gyaran shine maganin matan,
Sanah tace " a'a wallahi gyara daban maganin mata daban,
shi gyara yana nufin ki tsaftace HQ ki rink'a taka tsan-tsan da kaffa-kaffa da toilet infection,
da duk wani abu da kika san zai tab'a wajen ko rage miki testing,
ki rink'a zama da pant kina kuma yawan canjawa,
da dare kuma ki rink'a kwana babu pant dan wajen ya rink'a shan iska,
kin san kamar d'anyan nama yake,
idan kika rufe shi 24hrs dole zayyi bashi-bashi,
shiyasa zakiji idan wata ta cire pant yana mugun yin wari,
koma kiji gaban nata na tashi,
kamar baki ne idan kika kwanta bacci ko kina azumi ba wari yake yi ba?
" To saboda kin rufe shi babu iska yasa yake yin warin,
ajiyar zuciya Halan ta kuma saukewa tana kallan Sanah tamkar bak'uwa a wajenta,
Halan tace " gaskiya na gamsu da maganarki amma maganin mata da 'yan dabaru sun zamar mana dole,
d'an d'aga ido da gira Sanah tayi ta kalli Halan had'i da tab'e baki,
tace " babu dole wallahi amma ga wad'anda suka saka kansu su ya zamewa dole,
fruits & muski da ruwan zafi ,kanunfari ma idan mutum ya rik'e ya ishe shi,
" wato ke kin yarda da kanki kenan?
"Kin san Allah yayi ni'ima a wajen,
kice our teacher zai sha dad'i,
" babu yarda da kai ai duk mace, mace ce kawai ki iya bada shi shine,
dariyar Halan tayi tace " to ikon Allah iya bada shi kamar yaya kuma?
Sexy eyes d'inta tayi rolling kana tace " sex styles mana and sex emotions, show you enjoying and sex sound,
ta fad'a kanta tsaye,
" kam! tab! hmmmm wai Allah na,
gaskiya Sanah kin waye da yawa, idanki ya bud'e,
zan fad'awa Dide da Abbu su aurar mana da ke,
ta fad'a cikin tsokana tana dariya,
juyar da kanta tayi irin bama tasan tanayi ba,
Halan ta sauke ajiyar zuciya idanta kan Sanah tace " hmmmm kwal uba nan!,
manyan mata!,
" wai miye kike ta wani abu kamar wacce taga wani mugun abun tashin hankali,
kinga ni dai karki kaini inda banje ba,
barima kiga nabar miki gidanki,
ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa,
da sauri Halan ta rik'ota tana dariya tace " dawo ki zauna ai bamu magana da ke ba,
Sanah tace " ai gani na yi kina neman d'aure ni,
ta fad'a tana komawa kan sofar ta zauna,
Halan tace " dama ina san nayi miki magana kan Khulud please,
da sauri Sanah tace " lafiya!?
" Ke kwantar da hankalinki lafiya lau,
kan maganar da mukayi yanzu ne,
kin san dai Khulud bata kai ki shiga mutane da faram-faram ba,
sannan bata da wasu k'awaye balle su wayar da ita idanta ya bud'e tasan abubuwa masu mahimmanci kan aure,
kuma kin san ita irin wad'annan abubuwan da shige-shigen ba damunta sukayi ba,
kuma idan ni naje nayi mata magana kunya ta zata ji,
bazata iya sakewa muyi magana sosai ba,
so shine dama nake san yi maki maganar tunda ke you're so wise,
dan Allah ki taimaki 'yar uwarki,
kije kiyi mata magana ki koya mata abubuwa da dama ki wayar mata dakai,
ki bada number ta a sakata a irin wad'annan groups d'in please,
kin san halin mazan yanzu sunfi d'aukar sex da mahimmanci sama da komai a zamantakewar aure,
wallahi duk yadda mace takai da kyau, kwalliya, kissa, biyayya da hak'uri idan bata san kanta wajen sex ba mazan yanzu a banza suke d'aukarta,
basu bata daraja da k'ima sai kiga an auro maki wacce ko kashin gindinki yafi ta amma ta kwace maki miji ta fiki a wajenshi,
abinda yasa nace ke kije kiyi mata magana,
saboda kinfi kowa kusanci da ita,
kinfi sabawa da shak'uwa da ita,
ita kanta zatafi sakewa tayi maganar dake kan mu,
dan Allah kije gidanta kuyi magana da ita sosai,
abinda yafi k'arfin sani da tunaninki sai kiyi man magana,
naje gidan na sameta na k'ara wayar mata dakai please Sanah,
d'an shiru Sanah tayi tana tunani kana ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi,
tace " gaskiya haka ne maganarki Khulud tana da mugun sake da nuna rashin ko'in kula ta wannan fannin,
bata chart da kowa sai family's,
amma bari next week zanje,
" ni na rasa mai yasa baki san zuwa gidan Khulud duk sanda akayi miki maganar kije ko za'a aike ki gidan sai kin kawo uzuri,
duk wannan soyayyar taku ya kuke neman watsar da ita ne,
karfa kuyi sake ku bari wani abun ya shiga tsakaninku har kuyi nesa da juna,
yanzu fa Khulud tayi kusan 1yr da aure,
dan girman Allah ki shirya kije gidan gobe maganar tana da mugun mahimmanci,
murmushi tayi had'i da cewa " Allah ya kaimu goben zanje,
" yauwa kinga tunda kina hutu ma sai ki d'an yi mata koda kwana biyu ne, nasan zata ji dad'in hakan.
Da daddare tayi wanka ta gama shirin kwanciya tsaf,
ta haye saman bed d'inta tana shirin bacci taji wayarta ta soma ringing,
tasan shine dan ta san babu mai kiranta dai-dai wannan lokacin,
cikin nutsuwa tayi picking bakinta d'auke da sallama,
cike da so ya amsa sallamar kana ya tambaye ta ya take,
ta amsa mishi da lafiya lau,
hira sukayi sosai sun kai 2hrs suna hira,
cikin tsatsar soyayya, daga k'arshe Sanah tace " gobe fa zan fita,
face ya had'e kamar tana gabanshi yace " ina zaki?
D'an murmushi tayi dan taji yanayin muryarshi ya canja tace " zani gidan Khulud ne,
shiru yayi na d'an wani lokaci kafin yace " tana lafiya dai ko?
"Eh lafiyarta lau, tana ta mita wai tunda tayi aure banje ko sau d'aya na kwana ba,
wai zuwa na ma d'aya gidan gashi harta kusa yin 1yr,
" to ki gaina ta ya fad'a cikin sanyin murya,
" lafiya naji muryarka ta canja ko baka san naje ne?
" Wane ni da raba hanta da jini, ai ba mai raba zumuncin Allah sai shaid'an,
idan mutum bayyi k'ok'arin sada zumunci da had'a shi ba kar yayi k'ok'arin rabawa,
ke da Khulud soyayyarku daga Allah ne,
sosai taji dad'in kalamansa har cikin ranta,
cikin jin dad'i tayi murmushi mai sauti tace " to meyasa murka ta canja?
" Hmmm kawai dai ban san kije babu escort ko guardian ne,
saboda kinga baku shiri da Hanash a gaban idona ma ji abinda yayi ina kuma ga babu kowa,
" bakomai ai akwai Allah, kuma yanaji yana gani yana kuma tare da kowa,
tayi maganar cikin nutsuwa,
" please ni dai idan ba wani serious issues ne zai kai ki ba ki bari sai na dawo na kaiki da kaina if it's possible please my love,
ya fad'a yana langwab'ar da kanshi gefe kamar tana ganinshi,
karka damu babu komai kaji ta fad'a tana hamma had'i da lumshe idanta,
dan bacci ya fara cinta sosai,
" ni dai please ki bari na dawo gobe kawai jibi sai na kaiki,
ko goben na biyo jirgi da sassafe nazo, kinga wajen 11:00am na safe sai na kaiki ko?
Shiru tayi bata bashi amsa ba dan sama-sama take d'inshi,
murmushi yayi yace " bacci ne sweetheart,
"Unnnnn tace cikin bacci,
" OK bye good night my wish sweet dream with me an you,
cikin bacci da muryar masu bacci tace " I will....
wani irin jahilin dad'in yaji ya ratsa shi tun daga tafin k'afarsa har cikin kanshi,
take yaji tsikar jikinshi ta tashi yarrrrrrrr,
idanshi ya lumshi had'i da cewa " I wish to hear when you say you love me too,
can't wait for this day dear,
that day hmmm ina ga sai nayi..........
cikin sanyin murya yace " I love you more & more & more heartbeat,
batare data sani ba cikin bacci tace " *I LOVE YOU TOO MY HOPE!!!*
ta fad'a cikin bacci had'i da sakin wayar ta fad'i k'asa.................
```KU KASANCE DA SIR ARYAN MOLI NEXT PAGE```
MOMYN ZARAZARAH
[7/7, 4:56 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
3⃣5⃣
Tamkar rugugin tsawar ruwan sama yaji kalmar ta sauka cikin dodon kunnenshi,
ta daki zuciyarshi da kwakwalwarshi,
komai dake cikin duniyar tsayar mishi yayi cak,
kwakwalwarshi tayi hooking na d'an lokaci,
shiru yayi yana jin abin kamar a mafarki,
tunanin abinda ya faru ya fara yi,
had'i da k'ok'arin san tuna abinda ya farun,
cikin kid'ima da firgici Sir Moli ya mik'e tsaye,
had'i da cewa " say it again!,
shiru yaji tayi bata yi magana ba, hannunshi na kerrrma,
while duk ilahirin jikinshi na tsuma ya cire wayar daga kunnenshi ya kalli screen d'in wayar,
yaga batayi dropping ba, da sauri ya mayar da wayar kunnenshi,
jikinshi na rawa yace " please say it again,
I want hear it in millions time's from you,
kamar mahaukaci ya cire wayar daga kunnenshi yana dukan screen d'in yana cewa " say it again please!,
ki k'ara fad'a say you love me dan Allah,
amma ina ita bama tasan ta fad'i na farkon ba balle ta kuma fad'a a karo na biyu,
kanshi ya rik'e da hannu d'aya ,
d'ayan hannun kuma ya cusa cikin gashin kanshi,
bakin shi yak'i rufawa sai murmushi yake yana cewa " Alhamdulillah! ya Rabbi thank you,
nagode ma Allah finally yau Sanah ta furta man abinda na d'auki tsayin lokaci,
shekara da shekaru ina jira,
dariya ya saka had'i da fad'awa kan bed,
" wai anya kuwa ba mafarki nake yi ba?
D'an marin kanshi yayi had'i da cewa " tashi Aryan,
pillow ya rungume tsam yana dariya yace " ba mafarki nake yi ba it was real!,
am not deeming, thank God,
haka yayi ta sambatu yana juye-juye yana jiran gari ya waye,
dan ya nunawa Allah godiyarshi,
ya kuma nunawa mutane da duniya tsantsar farin cikin da yake ciki,
kwana yayi bai runtsa ba yadda yaga rana haka yaga dare,
sai da aka kira sallar asuba ya shiga bathroom yayi alwala ya fita masallaci.
Tun daga masallacin ya fara rabon bandir na 100k,
ranar duk wanda yaje ya samu sai da ya bawa kowa,
bayan ya dawo haka yayi ta bin ma'aikatan gidan yana yi musu b'arin kud'i,
duk da gaba d'aya ma'aikatan gidan they're soldiers,
cikin farin ciki ya koma bedroom d'inshi ya zube saman bed,
idanshi na kallan ceiling kyakkyawar fuskarshi d'auke da murmushi,
I'm done......!
"Alhamdulillah Allah abin godiya,
juyawa yayi ya gyara kwanciyarshi,
" Sanah ta zama Mrs Aryan Rayyan Moli,
" masha Allah nice name and match name,
idanshi ya lumshi yana hango irin kwawawan yaran da zasu haifa,
yana cikin wannan hali bacci yayi awon gaba dashi,
kasancewar bai samu bacci da dare ba,
bai farka ba sai 11:00am a hankali ya bud'e idanshi ya kalli agogon bango,
kanshi ya dafe da hannunshi yana mik'ewa zaune,
yakai 5 minutes a haka kana ya mik'e ya shiga bathroom,
shower ya sakarwa kanshi, runwa ya dad'e yana sauka jikinshi,
kana yayi wanka ya fito direct wajen wayarshi ya nufa,
ya d'auka yayi mata sending text,
_kin sanya ni cikin farin cikin daban tab'a tsintar kai na ciki ba I love you MRS ARYAN MOLI_ ,
wayar ya jefa saman bed kana ya shirya cikin d'anyan material na maza,
white color ya saka takalmi da hula & agogo silver color,
yayi masifar kyau tamkar wata daren sha hud'u,
fuskarshi cike da annuri ya nufi part d'in Nailah,
gaba d'aya ya iske su saman dinning suna breakfast,
fuska ya gwab'e cikin shagwab'a yace " shine ko a taso ni!,
hannu Hilwa ya mik'e mishi yana dariya,
yace " you look so handsome and classic my son,
ina zuwa haka?
Fuskarshi d'auke da murmushi an sosa mishi inda yake yi mishi k'aik'ayi yace " finally Hilwa she said it,
cikin fara'a Nailah tace " what! ?
" She said she love me!
dariya duk sukayi kana Hilwa yace " I she must said it dan yaro na ba banzan namiji bane,
irinsu dubban nan mata suke nema ido rufe,
Haidar yace " kai dai Hilwa banda cika baki ta dawo tace ta fasa,
kaga b'arin hawaye da ragonta,
matar Haidar tace " ai ko yanzu data amsa dai taja shi k'asa ta nuna mishi ita mai tsada da aji ce,
tunda har kuka mutum yayi wiwi,
cikin shagwab'a yace " Hilwa......!
yana kallan Haidar da matarshi,
Hilwa yace " kai rabu dasu kaji kai ma ka kusa kawo mai shigar maka,
murmushi yayi yace " wallahi kam dan akwaita da tsiwa,
Haidar yace " ba wani ka fito kace bata da kunya mafad'aciya ce,
ka tsaya kana yiwa haram kwaskwarima,
murmushi yayi yana kai coffee bakinshi,
yace " today is happy day in my life,
dan haka ban bari ka b'ata man ita,
idan ma so kake ka tsoka ne ni ko ka tun zura ni,
Nailah tace " yauwa my good boy,
yi breakfast d'inka ka kyale su kaji,
" yauwa my happiness!,
yana gama breakfast d'in gidan marayu ya nufa yakai musu taimako mai yawa,
yaran sukayi tayi misha addu'a suna yi mishi godiya haka ma manyan, kana yayi government hospital nan ma yaje yayi musu b'arin kud'i,
sosai yayi ta kai taimako guraran da suka dace suka kuma cancanci taimakon,
ko a hanya yaga almajiri da nakasashshe sai yayi parking yayi mishi kyautar dashi da bara har abada,
sai da ya gama tsaf kana yayi hanyar gida,
dan shi ba mutum bane mai yawo,
dan ko abokai bai da su.
Bata tashi ba sai wajen 10:20am na safe,
da sauri ta mik'e ta fad'a bathroom tayi wanka da sauri ta fito ta shirya,
cikin riga da normal zani na lace,
ta d'anyi heavy make up, wayarta ta d'auka danta tabbatar ya kirata ko ya turo mata text,
sororo tayi a tsaye bayan ta gama karant text d'in,
cike da mamaki tace " menayi masa?
" Allah dai yasa ba wani abun nayi kona fad'a cikin bacci batare dana sani ba,
cikin 'yar fad'uwar gaba tayi dialing number shi,
sai kuma ta fasa ta zura wayar cikin hand bag d'inta tayi parlor,
a parlor ta iske Mamu zaune tana kallo,
" ina kwana?
" Lafiya Alhamdulillah ina zaki na ganki da jaka?
" Kai Mamu badai har kin manta ba?
" Na manta, sai kin tuna min,
" gidan Khulud mana, jiya fa na fad'a maki har kika ce kina sak'on da zaki ban na kai mata,
"Oh! na shafa'a ne,
har kin shirya sai tafiya yanzu?
" Eh! fitowar nan ma danayi tafiyar zanyi,
Mamu tace " aiko na manta da zakije gidan Khulud yau har tarko abinci mai wuya,
" uhnnnn ki kira Juju ko wad'an can tsofaffin su tayaki mana,
" wad'anne tsufi?
" Ga su can suna zaune meye amfanin su, in ba su rink'a tayaku aikin ba,
ku rink'a danna musu aiki suna yi maku ke da Juju,
kuma kinga suna da yawa har su hud'u fa,
hannu Mamu ta tafa had'i da zaro ido tace " uwaki Sanah yanzu iyayen namu ne tsofi?
Baki ta turo tace " to basu tsufan ba?
" Dak'uwa Mamu tayi mata tace " zanci gidanku wallahi Sanah idan baki fita daga ido na,
kin kiyayar mana iyaye ba,
" kai Mamu danna ce masu tsofaffi kike fad'a?
" Wallahi idan kika b'ata man rai babu inda zaki,
cikin sigar lallashi tace " haba Mamu kakanni na ne fa ai munfi kusa yanzu da zasu ji ni zasu shigarwa suce ina ruwanki,
" idan zaki musu kiyi musu can idan babu idon mu,
" tom naji na daina, ta fad'a dan kar a hana ta fita,
mik'ewa Mamu tayi ta nufi bedroom d'inta tana mita,
magungunan mata ta d'auko ta bawa Sanah,
tace " ki kai mata kice maganin basir da shawara ne tasha da fresh milk ko peak milk,
dariyar dake shirin kufce mata ta danne,
jin Mamu ta mayar da ita yarinyar goye,
ko ta manta a jami'a take ne oho?
Kuma ko ba jami'a ai yanzu akwai social media,
amsa tayi while tana danne dariyar tace " aiko akwai peak milk bari na d'auko ni ma nasha dan basir da shawara na damuna,
cikin dakewa Mamu tace " a'a wannan nata ne dan ita tayi magana,
ita kad'ai na amsowa ke miyasa da can bakiyi magana an amso miki ba,
" ai naga magungunan na da yawa zasu isha nima nasha tunda ba wani da yawa zan sha ba,
" a'a karki sha wannan ki kai mata,
idan kin dawo ina da saura sai na baki cikin nawa,
" ok badamuwa nasha a can idan naje gidan nasan ai bazata hana ni ba,
d'aure fuska Mamu tayi tace " wai ni sa'arki ce Sanah ko kuma wasa nake dake?
" Da ina magana kina yi min gardama,
" yi hak'uri my sweet Mom bazan sha ba idan na dawo kya bani nakin,
nakin ma sai ya fi man dad'i,
" ato ya dai fi maki, maza tashi ki tafi, a dawo lafiya Allah ya tsare,
" Amin ya Allah my sweet......!
wayarta dake cikin jaka ta soma ringing,
da sauri ta zuge hand bag d'in ta d'ako wayar,
bata san sanda ta saki murmushi ba,
ganin shine, jakarta da mayafinta ta bari nan tayi bedroom d'inta da gudu tana dariya,
saboda yadda Mamu ta kafe ta da ido,
sai da ta saita kanta kana tayi picking,
bakinta d'auke da sallama,
ido ya lumshe had'i da amsa sallamarta yana kishingid'a kan sofa,
" ina wuni?
tace tana kwanciya rigingine saman bed,
Alhamdulillah dear, ya kike?
" Lafiya lau, kai fa?
Idanshi ya lumshi yana sauke ajiyar zuciya,
yace " ni yau ai ina cikin matsanancin farin ciki da annushuwa,
yau komai mutum zayyi man bai tab'a man rai,
" masha Allah meya sanya ka cikin farin ciki haka?
" You said it!
Ido ta zaro had'i da cewa " me!?
" You love me,
" what! ni d'in?
"Eh ke da kanki da bakinki,
kuma nasan koda kin ce a'a ba haka bane,
nasan kin fad'a ne kawai amma ba gaskiya bane,
saboda duk abinda mutum ya fad'a cikin bacci da maye gaskiya ne,
cikin shagwab'a ta gyara kwanciyarta,
tana cewa " ni dai Allah a'a bance ba,
kawai dai wayo kake san yi man,
yama za'ayi nace maka I love you,
" wow! kinji yadda kalmar I love you d'in ta fito daga bakinki?
Idonta ta lumshe had'i da k'ara juyawa tace " ko!?
" Yes! Sweetheart kuma ko da baki fad'a jiya ba yanzu gashi nan kin fad'a ai,
" me d'in?
" I love you d'in mana,
murmushi tayi tace " hmmm wayo ko?
" No ba wayo zanyi maki ba, seriously kin fad'a,
kuma naji dad'i sosai dan yanzu nasan ba san maso wani nake yi ba,
" hmmmm karka sa nayi yamma bari idan na k'arasa zan kira ka,
" ina zaki kuma!?
" Lah badai har ka manta ba?
" Me!?
" Ba na ce maka yau zani gidan my ulud ba?
Kanshi ya dafe had'i da cewa " ops...! Allah na manta jin dad'i yasa ni mancewa,
please ki kular man da kanki kinji?
" In sha Allah fiye ma da yadda zaka kula da ni,
ta fad'a ciki tsokana,
" wad'in never wallahi Sanah kin san yadda nake jin ki cikin rai na kuwa?
"Hmmmm tace,
yace " Wallahi idan kika d'auke Hilwa & Nainah nafi sanki fiye da kowa cikin duniyar nan,
zan iya bada rai na da rayuwata da duk abinda na mallaka akanki,
ya k'arasa maganar cikin sanyi,
" nagode sosai ,karka damu kaji my...!
shiru tayi cike da jin kunyar abinda tayi niyyar fad'a,
" no dan Allah said it karki fasa fad'a man abinda kika yi niyyar,
"hmmm ni dai zan tafi kar yamma tayi idan gamma tayi Mamu bata bari na fita,
murmushi yayi yace " ok badamuwa my happiness sai kin dawo,
please close your sexy eyes ban san ki kalli kowanne namiji,
murmushi tayi mai sauti tace " ina da kamar ka wanne irin namiji kuma zan kalla?
Saboda tsabar rawar jikin da yake yi sai da wayar ta sub'uce daga hannunshi,
da sauri ya d'auki wayar daga k'asa ya mayar kunnenshi,
had'i da lumshe idanshi yace " thank you sweetheart for make my heart happy,
I love you, ya fad'a cikin sanyin murya,
iska ta d'an busar daga hancinta kana tace " bakomai ai yiwa kai ne, bye!
da sauri ya bud'e idanshi yace " no no no please kice man I love you too,
cikin sanyin murya tace " ban iyawa,
" ok, rufe idanki, a hankali ta rufe idan kamar yadda ya umarce ta,
" ki sauke ajiyar zuciya yanzu,
ba musu tayi,
yace " ki bud'e zuciyar ki,
cikin sanyin murya tace " uhnnn,
yace " ki saurari bugun zuciyarki,
d'an shiru tayi tana sauraron bugun zuciyarta ta,
yace " now say it,
shiru tayi bata bashi amsa ba,
yace " I love you so much my sweet,
kai tsaye cikin sanyin murya tace mishi " I love you too my eyes shinning,
ta fad'a tana a yadda take batare data bud'e idan ba,
dukkansu sun kai 1 minutes shiru babu wanda yace " k'ala,
kana ya sauke nannauyar ajiyar zuciya thank you heartbeat,
dan Allah karki tab'a juya man baya a kowanne irin hali,
" karka damu Sanah taka ce har abada,
tana fad'ar haka ta kashe wayar,
ta kai 5 minutes rik'e da wayar a hannunta idanta rufe tana sauraron bugun zuciyarta,
tana jin tamkar ta tsaga zuciyar ta ciro ta,
a hankali ta bud'e idonta had'i da cewa " I love you!, I love you so much,
cikin nutsuwa ta fito parlor, ta tarar da Mamu nan yadda ta barta,
sallama ta k'ara yi mata kana ta fita,
driver yana hangota ya taso cikin rawar jiki,
" manyan gobe ina zuwa! gidan Khulud ta bashi amsa fuskarta d'auke da murmushi,
" to to muje ko...........
" a'a yi zamanka Baba driver zan kai ta,
Aarib ya fad'a yana kallanta cikin matsananciyar soyayyarta dake azabtar da rayuwarshi,
murmushi tayi mishi tace " kana ciki dama?
"Eh man yau ban fita ko'ina ba,
ya fad'a yana bud'e mata k'ofar,
zama tayi tana cewa meyasa Yaya?
Zama yayi had'i da yiwa motar key yaja suka fita،
kana yace " tunaninki ne yake hana ni sukuni,
ya fad'a yana kallanta,
rassssss! gabanta yayi muguwar fad'uwa,
amma sai ta dake ta k'ak'aro murmushin k'arfin hali tace " kamar yaya ban gane ba?
Murmushi yayi yana kallanta,
fuskarta ta d'an tsuke had'i da kawar da kanta,
babu wanda ya kuma cewa " komai har suka isa gidan Khulud,
bata tsaya yi mishi magana ba,
ta bud'e motar zata fita had'i da cewa " nagod.......!
bata k'arasa ba taji hannunshi saman nata,
a hankali ta kalle shi kana ta kalli hannun,
da sauri ya janye hannunshi ya bud'e baki yana k'ok'arin yi mata magana,
tayi ficewarta batare data tsaya ta saurari abinda zaice mata ba,
murmushi yayi yabi bayanta da kallo harta shige cikin gidan,
kanshi ya girgiza had'i da cewa " I love you!......!!,
Khulud na kwance parlor saman 3 setter taji sallamarta,
cikin rawa da kerrrrmar jiki ta mik'e har tana k'ok'arin fad'uwa ta nufi k'ofa,
jikinta na tsuma ta bud'e k'ofar ganin Sanah yasata tsayawa cak,
ido ta zuba mata na d'an lokaci kana ta fad'a jikinta had'i da fashewa da kuka,
" meye kuma na kukan?
" Allah ko kiyi shiru kona juya,
d'an dukan Sanah Khulud tayi tana cigaba da kuka tace " ba sai ki koman ba,
cikin tsokana Sanah tace " to tana k'ok'arin juyawa,
dariya Khulud tayi fuskarta d'auke da hawaye,
tace " hali dai yana nan,
cikin dariya tace " to ina zashi hali ai zanin dutse ne,
ta fad'a suna shiga cikin gidan,
saboda tsabar farin cikin ganin Sanah Khulud rud'ewa tayi ta rasa me ma zatayi,
mema zata bata, ina zata kaita,
duk ilahirin jikinta kerrrma yake,
kallanta Sanah tayi tana dariya tace " oh! ikon Allah wannan duk rawar jikin ganin Sanah ne!?
Khulud bata amsa ba ta kalli gabas tayiwa Allah sujjada,
kana ta d'ago tana cewa " Alhamdulilla,
yau dai Allah ya amshi addu'a ta ya had'a ni da Sanah ta,
ita kam ido kawai ta zuba mata tana kallanta sai sakin murmushi take yi,
Khulud tace " my Sanah me zaki ci na shiga kitchen na dafa miki yanzu?
" Kai daga zuwa na ko hira bamu yi ba sai maganar ci,
Khulud tace " eh ai ban san na barki da yunwa ne,
hannunta Sanah ta kamo ta zaunar da ita kusa da ita,
tace " zauna muyi hira kafin mu shiga kitchen d'in,
hira suka shigayi sosai sai labarai suke bawa juna,
sai da sukayi takai ta wajen 1hr kana Sanah ta dafa kafad'ar Khulud tace " my Khulud I'm in love fa!
ido Khulud ta zaro tana murmushi tace " with who!?
"Hmmmm kedai bari kawai I'm deadly fell in love,
wallahi ina jinshi har cikin rai na zuciya ta,
ji nake kamar nayi hauka ban kuma san ina san nashi ba,
sai yau, yau d'in ma yanzu yanzu da zanzo gidanki,
yau ya tabbatar man da ina sanshi,
" woow please who is that lucky man?
" *SIR ARYAN RAYYAN MOLI*
I love him, I really really love him,
ta fad'a cikin matsanancin farin cikin da shauk'i,
da sauri Khulud tace " wa!? Sir Moli kike nufi?
" Yes! My Khulud she dai,
murmushi Khulud tayi had'i da cewa " Masha Allah, Alhamdulillah gaskiya naji dad'i sosai,
ya abin ya kasance?
Ba wani b'oye-b'oye Sanah ta bawa Khulud labarin komai tun daga farko har k'arshe,
Khulud ta sauke ajiyar zuciya had'i da cewa " dama wallahi na dad'e ina tunan sanki yake yi,
ranar da kuka zo har sukayi fad'a da Hanash ranar na k'ara tabbatarwa kai na yana sanki,
Sanah tace " hmmmm! ni ina na sani,
wallahi ban tab'a tunanin so na yake yi ba,
Khulud tace " ke ma dai ai alamomi da dama sun nuna Sir Moli sanki yake,
kuma shi so ai bai tab'a b'oyuwa,
ko gangar jiki da fusuka sun b'oye baki ya kasa furtawa,
kwayar ido da ruhi bazasu tab'a b'oyewa ba,
" hmmmm ni fa har yanzu mamaki nake yi wai I'm in love with him,
" hmmm ni kuma kin san meke ban mamaki har yanzu?
" A'a! sai kin fad'a!
"yadda ya cire girman kai, isa da tak'ama gami ji da kanshi,,
yayi kneeling down yana rok'on soyayyar mace,
wallahi in wata ta fad'a man ban tab'a yarda,
" hmmm gumu da bala'in love yaji!
duka suka sanya dariya,
cikin dariya Khulud tace " wallahi zan so naga idan Sir Moli yana shan love,
naga yadda zayyi tashi kalar soyayyar,
in ga in da dai zai kai had'e fuska da izzar da tak'amar nan tashi,
murmushi ta kuma tace " tashi mu shiga kitchen kar mijinki ya dawo na k'ara yin laifi wajen shi,
yace yau saboda nazo kika k'i dafa mishi abinci kika barshi da yunwa,
ki k'ara shafa man kashin kaji,
ta fad'a tana dariya,
dariya itama tayi kana suka mik'e suka shiga kitchen,
Khulud ta kalli Sanah tace " me zamu dafa ne?
Rolling idanta tayi kana tace " I think muyi sakwara da miyar ganye & dry fish da ganda,
" Ok Khulud tace, kana suka fara aikin,
Khulud tace " amma my Sanah anan zaki k'arasa hutunki ko?
Murmushi tayi tace " idan mijinki bai min haushi ya kore ni ba,
"au wato ma haushi yake yi miki,
saboda kin maida man miji kare ko?
" Yo in ba kare ba wake haushi,
a haka kamar na Allah yadda kasan idan aka saka mishi hannu baki bai iya cizawa,
amma idan ya fitittike yana tajira da ruwan bala'i kamar me!
duk sukayi dariya, basu fi 1hr ba suka gama abincin tsaf suka jere saman dinning,
" to je kiyi wanka kinji my Ulud,
" ban san na barki ke kad'ai ne ai,
dariya tayi tana tura ta cikin bathroom d'in, had'i da jawo mata k'ofa,
parlor ta dawo ta zauna had'i da d'aukar wayar Khulud ta shiga black list,
dan ranta da zuciyar ta sun dad'e suna bata a black list Hanash ya sanya number ta,
dan matuk'ar ba haka ba babu yadda za'ayi ace number ta ce kad'ai bata shiga koda zata shekara tana kiran juna,
tana shiga taga number ta cikin block list,
murmushi tayi had'i da cewa " shege tijararre ja'iri d'an nema,
kana ta cire wayar daga block list d'in,
Khulud bata jima ba ta fito ta gama shiryawa tsaf!,
Sanah ta kalle ta sama da k'asa tace " ke ko meya had'aki da riga da zani cikin gidanki da dare nan?
Cikin mamaki Khulud ta kalle ta tace " bangane ba!
" hmmm ai dama bazaki gane ba, please jeki cire ki saka sexy kaya,
kamata yayi ki rink'a yawo kusan tsirara cikin gidanki, ke da baki ma da yaran da zasu takura miki,
wallahi ni idan duniya na haifa bazasu hana ni sakewa da miji na ba,
nayi kwalliya, abinda yasa matan waje ke kwace maku miji kenan,
kalle ki fa ki kinganki duk kinbi komai kin rufe kamar mai shirin zuwa gidan mutuwa,
ki rink'a yadda tsiraici ciki gidanki ba haramun bane saboda kija hankalin mijinki gare ki,
sakatoto Khulud tayi tana kallan Sanah harta dasa aya,,,,
kana tace " hmmmm zan gyara in sha Allah,
baki ta tab'e had'i da cewa " ya dai kamata kam,
in ma ba ke ba mai zai had'i ki da manyan kaya cikin gidanki harda su bra,
dariya tayi had'i da cewa " gaskiya my Sanah kin waye da yawa,
kodan ai jami'a kike,
" hmmmm wallahi ba wani jami'a,
'yan mata nawa ne a JSS amma idansu tarrrr,
kuma 'yan mata nawa ne a jami'a kansu yake cikin duhu,
" hmmmm ni dai taso muje muci abinci yunwa nake ji,
" wai kina nufin baki jiran mijinki?
" Ikon Allah kuma dan zan jira shi sai na barki da yunwa kome?
" Kinga ni ki barni naci amma ke sai kin jira shi,
" please tashi muje mu ci abinci,
ta fad'a tana rik'o hannunta,
saman dinning d'in suka zauna had'i da yin serving junansu,
kana suka fara cin abincin,
basu dad'e da soma cin abincin ba ya shigo,
yana ganinta ya murtuke fuskarshi murtuk yadda kasan an aiko mishi sak'on mutuwar Mimmee,
batare daya kalle su ba, ya shigo zai wuce,
da sauri Khulud ta tare shi tana yi mishi sannu da zuwa,
fuskarshi d'auke da murmushi ya amsa,
had'i da rungume ta,
d'an kallanshi tayi tace " ina wuni?
Banza yayi da ita kamar bai ji ba,
ta kuma cewa " ina wuni,
still bai amsa na, shiru tayi bata kuma yi mishi magana ba,
Khulud tace " my sweet bakaga our Sanah bane!?
Itama shiru yayi mata,
ta kuma cewa " wai baka ji our Sanah na gaida ka bane!?
" No!, out of correction! your Sanah dai,
ta ina ta zama our, ke da wa ta zama our?
Ya fad'a fuskarshi a tsuke,
" to amma baka ji tana gaida ka bane?
"Na ji mana, in naji sai me?
" sai akayi yaya ko kuma cewa akayi kowanne kucakin yayi maka magana sai ka amsa?
Ido Khulud ta lumshe hawaye na zubowa kan kuncinta,
Sanah tace " please my Ulud karki yi kuka,
idan ba haka ba zan tafi yanzu wallahi,
a fusace yace " ke ban san iskaci da karuwanci,
abinci ne dai ya kawo ki gashi nan sai kiyi tacin mai mai dad'i shegiya kwalamammiya,
muryarta na rawa saboda k'ok'arin danne kukan da take yi,
tace " amma kasan gidan mu babu yunwa ko?
" Dan ina da tabbacin kana d'aya daga cikin wad'anda suka san mun fi k'arfin komai a rayuwarmu,
hannu ya d'agawa Khulud cikin b'acin rai had'i da cewa " enough please!
ya fad'a yana shigewa cikin bedroom d'inshi,
sakwaf Khulud ta zube kan sofa tana k'ok'arin fasa kuka,
Sanah tace " kikayi kuka ban k'ara zuwa gidanki,
ni abinda yake yi man bai damuna,
dan idan da sabo na saba,
da sauri Khulud ta goge hawayenta jin Sanah ta rantse,
a hankali ta mik'e ta dawo kusa da Khulud ta zauna had'i da dafa ta,
jakarta ta d'auko ta bud'e ta ciro magungunan matan da Mamu ta bata ta kawo mata ta bata tace " da peak milk ko fresh milk zaki rink'a,
dan ta bawa Khulud dariya tace " kin san meya faru tsakani ma da Mamu?
Cikin sanyin jiki ta girgiza mata kai,
Sanah ta bata labarin yadda sukayi kan magungunan matan,
Khulud ta kwashe da dariya harda tuntsirawa,
" kai my Sanah baki da dama wallahi,
yanzu har Mamun tamu baki kyale ta ba?
" To ji nayi tana neman mai da ni jaririya,
ganin Khulud ta sake harda dariya sosai yasa taji dad'i,
had'i da tattara nutsuwarta dan yi mata takamaiman maganar data kawo ta,
tace " Aunty Halan ce fa ta aiko ni,
" to lafiya dai ko!?
" Ke lafiya lau karki d'aga hankalinki,
idon Khulud yana kanta tace " ina jinki,
guaran murya tayi kana tace " dama akan maganar sex n........!!
"idan an cewa mutum d'an iska fasik'i ace ba haka ba,
yanzu wannan meye in na karuwanci ba?
" Budurwa dake wacce ko saka mata rana ba'a tab'a yi ba amma kina maganar sex!,,,
a fusace Khulud ta mik'e had'i da kallanshi ido cikin ido tace " dama haka kake Hanash haka halinka da d'abi'unka suke!?
Bayyi mata magana ba idanshi na kan Sanah,
tace " wai meyasa kake yiwa my Sanah haka ne?
'Hanash ka tuna ba haka mukayi dakai ba,
tun ranar daka fara zuwa waje na sai da na fad'a maka wacece Sanah a gare ni،
amma kana wasu abubuwa tamkar ka tsane ta,
idanshi ya mayar kanta yace " yahhh!,
cikin tashin hankali ta zaro idanta waje tace " meye yahhh! kana nufin ka tsane ta?
Cikin d'aga murya yace " yes I hate her! na tsane ta ban santa ban k'aunar ganinta,
tun farko saboda ke da son da nake yi miki,
yasa nake danne k'inta da k'iyayyar danake yi mata,
amma,
Khulud na tsani Sanah! so what?
A hankali Khulud ta soma ja baya tana girgiza kanta,
duk ta rud'e duk ilahirin jikinta kerrrrma yake yi,
da sauri Sanah ta mik'e ta nufe ta had'i da cewa " karki damu da duk abinda zayyi min,
dan bani yake yiwa ba kanshi yake yi...........!
tassssss!!!! tassssss!!!! Hanash ya d'auke Sanah da gigitattun marika,
a rud'e ta dafe kuncinta da hannunta,
yayinda jinta da ganinta sukayi d'aukewar wucin gadi,
a razane Khulud ta kalli Sanah kana ta mayar da kallanta kanshi,
muryarta na rawa tace " what! marin Sanah kayi!?
"Ok yayi kyau ni bazan rama mata da kai na ba,
saboda albarkacin igiyoyin aurenka da ke kai na,
a hankali ta mayar kallanta ga Sanah tace " ni kikayiwa alk'awarin cewa duk abinda yayi maki baki k'ara ramawa har abada ko!?
" Ni kika yiwa alk'awarin duk abinda zayyi miki zaki shanye ko!?
" To daga yau kuma yanzu na yafe wannan alk'awarin naki,
ya yafe duniya da lahira Allah yana shaida,
a yanzu nace ki rama marin da yayi maki,
tun da shi baiga darajata a matsayi na,
na matarshi ta sunna ba, bai ga darajar su Abbu da Dide ba,
yake duk wad'annan abubuwan har ya iya d'aga hannu ya mare ki,
dan Allah dan Annabi Sanah idan har so da soyayyar da kike man gaskiya ne,
a yanzu a nan take ina san ki rama marin da Hanash yayi miki.......................
MOMYN ZARAH
[7/7, 5:03 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
```DEDICATED TO```
*NAFISA SHEHU SADNAF*
~(UMMU AFFAN)~
3⃣6⃣
Tsaye yayi hard'e da hannunshi a k'irji,
yana kallanta,
duk ilahirin jikin Khulud kerrrrma yake had'i da tsuma,
kallo d'aya zakayi mata ka hango tsantsar ruwan bala'in dake cikin kwayar idanta,
tarrrr take kallanshi ido cikin ido,
while tana yi mishi wani irin kallo mai wuyar fassara,
cikin zafin rai tace " nace ki rama marin da yayi miki please,
ta fad'a cikin hargowa,
Sanah dake durk'ushe cikin zafi da k'unar zuciya,
tana jin ranta tamkar wuta yake ciki,
tunda Hanash keyi mata abubuwa babu abinda ya tab'a b'ata mata rai,
ya tab'a zuciyarta kamar yau,
amma gudun karta tun zura Khulud yasata dakewa,
had'i da d'agowa ta kalli shi ido cikin ido take kallan cikin kwayar idanshi,
tace " a'a my Ulud mu mu nuna masa mun san daraja da k'ima,
muna da d'a a ta yadda koda karen gidan mu bamu tab'a wulak'antawa,
kuma koda dabba ta rab'emu harta zo inda muke bazamu tab'a k'ask'antar da ita ba,
balle mutum d'an Adam mafi girman halitta,
wanda Allah ya girmama shi fiye da kowacce halitta a duniya,
yaje yaci arzikin masu dajara,
ta fad'a still bata d'auke idanta daga cikin nashi ba,
zuciyar Khulud na tafasa tayi kwafa had'i da kallan shi,
tace " Hanash meye manufar aure na dakayi?
" Me kake nufi a tsakani na da Sanah?
" Idan har kana tunani ko san raba mu ne,
to kayi babban kuskure da har tunaninka, zuciyarka da ranka suka baka zaka iya raba gangar jiki da ruhi,
dan raba ni da Sanah tamkar raba gangar jiki da ruhi yake,
wallahi Allah zan iya rabuwa da kowa a duniya,
nayi nesa da kowa a rayuwa har abada amma banda SANAH,
ciki kuwa har da kai kanka,
kai yanzu bazaka ji kunya aje gaban Abbu a fad'a mishi abinda kake yiwa 'yarsa ta cikinsa ba?
"Ya zakayi duk ranar da Abbu yasan abinda kake shukawa 'yarsa?
" Wallahi in banda Abbu yace duk ranar dana k'ara komawa gida,
babu shi babu ni ba, kuma na nemi wani uban ba shi ba,,,
da wallahi banga abinda zai hana ni tafiya in barka maka wannan gidan naka ba,
haba ayi mutum kwata-kwata babu yafiya bai mantuwa,
ina amfanin wannan hali da bak'ar zuciya,
cikin zafin rai Hanash ya d'aga hannu zai mari Khulud,
cikin zafin nama Sanah tayi saurin rik'e hannunshi,
tsaye yayi cak yana kallanta cike da mamaki dan tunda yake marinta bata tab'a tarewa ba,
sai yau da zai mari Khulud,
tarrrrrr take kallanshi idonta cikin nashi,
tace " 'a'a karka soma wannan gangancin a gaban Sanah,
ta fad'a tana yin jefa da hannun nashi gefe,
" dan ka saba mari na ina kyale ka shine kayi tunanin hali na ya canja!?
"Ko ko kana tunanin tsoranka nake ji!?
" To bari in fad'a maka babu d'aya daga cikin wad'annan biyun,
darajar Khulud kake ci, ka kuma godewa Allah dana san darajar alk'awari,
ba dan haka ba.......!
ta cije tab'enta da k'arfi had'i da nuna masa yatsa,
" amma duk da haka idan kana san ganin ainihin wacece Sanah,
ka gwada tab'a Uludinta a gabanta,
cikin fad'a yace " idan na gwada tab'atan mezakiyi!?
Guntun murmushin gefen baki tayi mishi tace " a nan ne zaka gane kuranka!,
harta juya zata tafi ta juyo tace " idan ma so kake ka raba mu ko in dai na zuwa,
to kasa ni bazan tab'a baka wannan damar ba,
kuma daga yau every weekend sai nazo,
sai naga yadda zakayi, idan kuma ka sake kayi gigin tab'a ni,
gwarzo kuma jarimin namiji,
cikekken namiji mai ji da komai zai koya maka hankali,
dan yanzu ina da mai shigar man ya kuma d'auren man gindi,
murmushi yayi had'i da cewa " cikekken namiji! waye shi!?
Idanta cikin nashi tayi murmushi had'i da cewa " wanda yazo har cikin gidanka,
ya dake ka, ya kuma fita lafiya,
babu abinda ka iya mishi,
zayyi magana tayi saurin cewa " ai kaji k'arfin naushin shi ko!?
" Tunda naga har durk'ushewa kayi,
gadan-gadan ya nufo Sanah cikin zafin rai,
Khulud tayi saurin shiga tsakiyarsu,
tace " wallahi Allah daga yau duk ranar daka kuma kuskuren tab'a Sanah ko ka mare ta,
wallahi ka tab'a aurenka ko da zanyi kwanan titi da kwararo had'i da bola,
ban kuma kwana gidanka, ban kuma k'ara aurenka,
ido ya k'ura mata na tsayin lokaci,
kana ya mayar da kallanshi kan Sanah,
murmushi tayi masa had'i da kashe mishi ido d'aya,
cikin bak'in ciki ya fita fuuuuuuu!.
Duk suka bi bayanshi da kallo,
cikin kuka Sanah tace " please my Ulud kiyi hak'uri nayiwa mijinki rashin kunya!....,
itama cikin kukan tace " abinda kikayi shine dai-dai my Sanah,
nasan in banda darajata da Hanash yake ci dabai isa yayi maki haka,
ki kyaleshi ba, nasan shi kanshi ya san hakan,
dan farkon had'uwarku zai tabbatar mishi da hakan,
amma dan girman Allah kiyi hak'uri my Sanah,
hawaye ta sharewa Khulud tace " bakomai my Ulud karki damu kinji!,
abu d'aya nake nema daga gare ki dan Allah,
da sauri tace " meye shi?
" Please kiyi man alk'awarin bazaki tab'a canjawa Hanash kan wannan abun daya faru ba,
kiyi man alk'awarin ko a fuskari baki tab'a nuna mishi,,,,
zaki mishi yadda kuka saba bazaki rage komai ba,
then..! kiyi man alk'awarin daga yau duk abinda zayyi man baki k'ara yin kuka koda d'igon hawayen ki bai k'ara zuba,
shiru Khulud tayi tak'i yin magana,
ta kuma cewa " matuk'ar kina san na cigaba da zuwa!..,
ki d'aukar man wad'annan alk'awarirrika!....,
ajiyar zuciya ta sauke had'i da cewa " na yarda zanyi amsa miki alk'awarin ki amma ni ma sai kinyi man alk'awari biyu,
" ina jinki...!!
" na farko kiyi min alk'awarin baki daina zuwa zaki cigaba da zuwa,
Sanah tace " yes! I do!
" then..!?
" then...! daga yau duk abinda Hanash yayi maki baki k'ara rangwanta mishi,
baki kuma kyale shi zaki rama...!,
shiru itama tayi idanta kan Khulud,
" amma my Ulud......!!!
" no but..! kawai kiyi accepting ke ma!
shiru Sanah ta kuma yi na d'an lokaci kana tace " da dai an taimaka man an canja man wani sharad'in idan da hali,
" no way! tace, kana ta fara k'ok'arin mik'ewa tana cewa " ki barshi kawai,
da sauri Sanah ta ruk'o hannunta had'i da cewa " yes! I do!
" a'a cewa zakiyi kin yarda kin amince,
cikin sanyin jiki tace " na yarda na amince!....
" good Alhamdulillah yanzu hankali na zai kwanta!
kana tace " taso muje mu k'arasa cin abincin mu,
" a'a gida zan tafi Mamu tace kar nayi dare fa!
" kai my Sanah yanzu Mamu ce tace miki karki yi dare!?
"Eh! tace tana d'aukar jakarta,
b'ata fuska Khulud tayi had'i dacewa Allah baki tafiya yau sai kin kwana,
ido ta zaro tace " wai rufa man asiri ki barni na tafi tunda sauran mutunci na,
in ba so kike tsakar dare mijinki ya watsa ni ta window ba,
" amma ke fa kika ce anan zaki k'arasa hutunki,
dan Allah ki kwanar man koda kwana biyu ne kawai,
" kiyi hak'uri my Ulud kin san ban zo da kaya ba,
ki bari next week zanzo na kwana,
" to baga kaya na nan ba sai ki saka,
" a'a ni dai Allah ki barni na tafi,
Allah zan dawo next week tare da Hub! zamu zo!
" meye kuma Hub!?
Murmushi tayi har simples d'inta suka lotsa,
tace " Hub yana nufin MASOYI ko SO ko SOYAYYA (LOVE!),
da harshen labarinci,
" wato shi kanshi ne soyayyarta ki kenan?
"Eh man dan ma bance mafi K'ALB! ba,
" again!..! meye K'ALB?
" Mean Zuciya (heart),
cikin sanyinta tace " to ni dai dan Allah da gaske zaki zo next week d'in?
" In sha Allah!
" to tsaya na zuba maki sakwarar ki kaiwa Mamu da Abbu,
" wa d'in...!?
" Tab! ni zan d'au abincin Hanash nakai gida?
" Yadda zaiji dad'in fad'in magana kenan,
yanzu ma da ba'a d'auka akai ba yana cewa cin mai dad'i ne ya kawo ni,
ina kuma da ana d'iban abincinsa ana kaiwa gida,
ba ruwa duk ranar da zaki gida sai ki girka da kanki ki kai masu,
amma ni babu hannu na ciki,
then kince duk abinda yayi mani na rama,
and kuma kina neman had'a mu!
ido ta zaro had'i da cewa " ni ke san had'a kun.....!?
"Eh! man yanzu idan ya ganni da abincin nan ya fad'a man magana fa?
" Kuma kince na rink'a ramawa idan na rama kinga ai mu kuma tsokane shi kenan,
" to naji shikenan! yi hak'uri, ta fad'a cikin sanyi,
murmushi tayi tana yafa mayafinta,
tace " tom! ni nayi nan sai next week d'in,
" dan Allah kizo fa karki shanya ni please,
ta fad'a kamar zatayi kuka!
" Allah zanzo karki damu kinji my Ulud!
"to muje na raka ki!
" a'a kiyi zamanki tunda kinga ni sai na fita zan samu abin hawa,
harta juya ta juyo tace " and please karki nuna masa komai even a face d'inki,
ki tuna kinyi alk'awari, kuma nasan kin san girman shi,
kai ta d'aga mata tana jin kamar tabi ta,
kana sukayi sallama ta fita,
tazo fita bakin get! mai gadi yayi saurin tasowa,
jikin shi yana kerrrma yace " ranki ya dad'e ina yini?
Cikin sakin fuska ta amsa " lafiya lau,
ya aiki Baba!?
" Alhamdulillah, d'an shiru yayi yana san yin magana nauyi da kunya sun hana shi,,,
tace " naga kamar da magana a abinka,
" uhnnnn hmmmm dama!.......,
dama........! shiru yayi yana 'yan kame-kame,
tsaiwarta ta gyara tace " karkaji komai kaji Baba kayi magana,
ka fad'i abinda ke ranka mun san darajar d'an Adam mu bamasu wulak'anta mutane bane,
" dama kwanaki mijinki yayi min alk'awari har ya ban number waya,
idan na kira kuma bata shiga,
d'an shiru tayi tana tunani kafin ta tuna lokacin da suka zo da Sir Moli,
yayiwa mai gadin alk'awari har ya bashi katinshi,
ta san shima k'ilan mantawa yayi,
murmushi tayi tana kallan mai gadin,
kana tace " ayyya Baba mun manta ne,
kayi hak'uri kaji,
" haba Hajiya meye na bada hak'uri kuma,
dama nasan kun manta ne shiyasa nace bari nayi tini,
" kana da waya!?
"Eh yace yana d'auko baby Nokia daga cikin aljihunshi,
cikin rawar jiki ya mik'a mata,
had'i da cewa " gata Hajiya, ya fad'a yana rusina mata,
" dan Allah karka k'ara durk'usa man Baba,
kai fa babba ne ni ya kamata na rusuna maka,
murmushi yayi batare dayace komai ba,
account balance d'inshi ta duba taga akwai 15 naira,
dan haka tayi dialing number ta,
dan ta d'auki number shi, tasan ko ta tambaye shi,
ba lalle ya sani ba,
saving number tayi kana tace " na d'auki number ka in sha Allah zan kira ka,
godiya yayi mata sosai kana ta fita,
tun kafin ta kai bakin titi Allah ya taimake ta ta samu mai napep ta hau!,
ta fad'i mishi sunan anguwar da zai kaita,
a bakin get ta sauka ta biya shi kana tayi shigewarta cikin gida,
a harabar gidan taga Aarib yana k'ok'arin shiga mota,
hangota da yayi yasa shi fasawa,
had'i da nufo ta fuskarshi d'auke da murmushi,
itama guntun murmushin tayi mishi,
batare data yi mishi magana ba,
" har kin dawo princess!?
"Eh...! tace mishi a tak'aice dan a matuk'ar gajiye take,
" kuma shine ko ki kira ni nazo na d'auke ki?
Dariya tayi tace " nayi zaton kana wani abu ne,
" no bana komai yanzu shan ice cream zani ko zaki bi ni!?
In banda a gajiye take da babu abinda zai hana ta binshi,
kai ta langwab'e tace " please ka bari sai gobe muje yau a gajiye nake mutuk'a,
" ok badamuwa Allah ya kai mu goben sai na kaiki, amma yanzu ina san zuwa naci shawarma da ice cream,,,
" are you sure goben zaka kai ni?
" Zan kai ki koda kullum kina san na rink'a kai ki sau 100 ne,
murmushin jin dad'i tayi tace " thank you bro like no other,
murmushi shima yayi mata,
yace " nima take away zanyi na dawo gida,
" ok sai ka dawo, ta fad'i tana shigewa part d'in su,
duk abinda suke yi Juju da Dide na kallansu,
Juju tace " naga alama fa kamar d'an Abbu yana san 'yar mu,
murmushin manya Dide yayi yace " au ke sai yanzu kika fahimta?
" A'a na jima ina zargin hakan a raina,
ganin bai magantu bane yasa ni yin shiru,
Dide yace " ya magantu ai,
cikin d'oki tace " to Alhamdulillah amma naji dad'in wannan abu,
zumunci zai k'ara k'arfi da dank'o kenan,
amma waya fad'iwa!..?
Hankalinsa ya tattara gaba d'aya ya mayar kanta,
kana ya bata labarin yadda sukayi da Aarib,
kana Dide ya d'ora da cewa " na fahimci kamar akwai wanda ke nemanta,
dan sau uku ina ganinshi yana kawo ta gida,
daga makaranta kuma naganshi wajen d'aurin auren Khulud,
sannan ranar da bata da lafiya ma shine ya kaita asibiti,
Juju tace " shine wanda muka je muka tarar wajenta?
"Eh shi, kuma na fahimci kamar akwai soyayya mai k'arfi tsakaninsu,
shiyasa na dakatar dashi na fara cewa ya je ya fara neman amincewarta tukun,
" to amma meyasa baka sanar dashi akwai wanda take so ba?
"Tab! lalle mata sai a barku,
kuma kawai matsayi na na uba ni da kai na zan fad'a mishi haka,
idan kuma a fahimta ta ne kawai ba soyayya suke yi da wancan d'in ba fa,
kamata yayi yaje wajenta da kanshi,
koma me kenan ta sanar mishi da kanta,
cikin sanyin jiki Juju tace " Allah ya tabbatar da alkhairi,
"Amin ya Allah,
tana shiga ta tarar parlor'n babu kowa,
bata tsaya parlor ba ta wuce bedroom d'inta,
jakarta ta d'ora saman gado kana ta cire mayafinta,
ta ninke ta mayar cikin wardrobe,
ta cire d'an kunnenta da takalmin suma ta mayar dasu mahallinsu,
ta cire kayanta ya rage daga ita sai bra & under,
kana ta zuge jakarta ta ciro wayarta ta juna a ciji,
ido ta zaro ganin 15 missed call d'inshi,
da sauri ta zauna gefen bed had'i da cewa " I'm sorry Hub!,
ta fad'i tana dialing number shi,
tana soma ringing yayi rejecting,
a d'an tsorace ta zaro ido dan a zatonta fishi yayi,
tana k'ok'arin sake dialing number shi kiranshi ya shigo,,,
kwanciya tayi rigingine saman bed,
had'i da lumshe idanta kana tayi picking,
" amincin Allah ya tabbata ga ruhin Aryan,
wani irin sanyin dad'i taji yana ratsa duk ilahirin jikinta,
idanta lumshe tace " amin tare da kai Hub!,
shima idan ya lumshe yace " meye " Hub! My heart?
Fuskarta d'auke da murmushi tace " kai Hub Allah nasan ka sani kana dai tsokata ne kawai,
ku da ke tare da shuwa, kuma yawancin 'yan Maiduguri suna jin larabci,
ido ya lumshe kana yace " thank you sweetheart, ko ni ma da larabcin za'a zab'ar min sunan da zan rink'a kiranki,
'yar dariya tayi tace " kai ai ne bature dan haka sai ka kira da turanci,
dariya mai sauti yayi yace " ikon Allah bature aka mai da ni kuma!?
" Yes! haka ne,
" tom ni dai zab'ar man sunan da zan rink'a kiranki da larabcin nima,
d'an shiru tayi kana tace " K'ALB yayi?
" To shi meye ma'anar shi?
" Ko kuma kace " K'ALBI, duk d'aya ne yana nufin zuciya ta,
"wow! that's wonderful name,
daga yau kin koma K'albi, dariya tayi tace " tom nagode sosai Hub!,
" tom yanzu bani labarin abinda akayi gidan Khulud,
zatayi magana sheshshekar kukan datayi d'azu ta hana ta,
a hankali ta sauke ajiyar zuciya,
" K'albi kinyi kuka ko?
Cikin mamaki tace " meka gani Hub!?
"Please fad'i man gaskiya kinyi kuka ko bakiyi ba?
Shiru tayi ta rasa abinda zatace mishi,
da k'arfi ya bugi bango yace " I know something must happen in har kika je gidan nan,
shiyasa nace maki karki je ki bari sai na dawo na kaiki da kai na,
cikin sanyin murya tace " ni fa banyi kuka ba,
deep down kuma tana mamakin yadda yake fahimtar yanayin datake ciki idan suna waya,
dan sometime ko baki ta zumb'ura mishi yana ganewa,
cikin b'acin rai da zafin zuciya yace " meyayi maki?
" Allah bakomai karka damu Hub!,
ya zaki ce karna damu, bayan kin san dole hankali na ya tashi,
please fad'i man abinda yayi miki dan Allah,
" bakomai tayi maganar cikin sanyi,
" K'albi ban san tun yanzu ki fara man k'arya kina yi man b'oye-b'oye,
na sanki tun kina k'arama nasan baki k'arya,
then ina so mu gina soyayyarmu da rayuwarmu bisa gaskiya da amana had'i da yarda,
kuma kece zaki taimaka wajen yin hakan,
ban san ki rink'a yi man k'arya, dan ban san gaba ki fad'a man magana na rink'a kokwanto akanta gaskiya ne ko k'arya ne,
idan har aure babu yarda aciki to babu aure,
dan zargi ya shiga,
duk inda kika ga al'umma mai kyau ingantacciya to an gina ta ne bisa gaskiya,
kuma hakan tana samuwa ne tun farko daga tushe,
matuk'ar muna san zuri'ar mu da mu kan mu mu ginu mu zama ingantacciyar al'umma dole sai ni da ke munyi k'ok'arin gina alak'armu bisa gaskiya, amana, yarda, had'i da jin tsoran Allah,
so please fad'a man meya faru,
ya fad'a cikin tausasa harshensa
take duk ilahirin jikinta yayi sanyi,
taji ya kashe mata jiki,
cikin sanyin murya tace " zan fad'a maka amma dan Allah karkace zakayi mishi komai ko kace zaka d'auki mataki,
maganar ta wuce, abarta please,
" ina jinki......!
shiru tayi ta rasa ta inda zata fara yi mishi bayani,
cikin taushin magana yace " ya mare ki ko?
Kamar yana kallanta ta d'aga mishi kanta,
shiru yayi tuk'ik'in bak'in ciki da takaici na cinsa,
ji yake tamkar ya fasa ihuuuu wani k'aton banza ya marar masa Sanarsa a wofi,
sai da ya runtse idanshi kana yace " uhnnn ina jinki, ya fad'a cikin wata irin murya da tasa Sanah fahimtar ranshi yayi mugun b'aci,
ta bud'e baki zatayi magana taji Aarib yana kwala mata kira daga parlor had'i nufo bedroom d'inta,
a firgice Sanah ta mik'e had'i da saurin cewa " Yaya Aarib karka shigo I'm naked ina zuwa,
wani k'ululun bak'in ciki da takaici ne suka taru suka tokare k'irjin Aryan,
komawa yayi saman bed ya kwanta had'i da runtse idanshi da k'arfi,
jikinta na kerrrrma ta zumbula zubulelen hijabin sallar ta,
kana ta bud'e k'ofar murmushi yayi mata had'i da mik'a mata ledar,
yace " ban iya ci batare da kema kinci ba,
karb'a tayi tana murmushi tace " thank you bro like no other,
har ya juya zai tafi tace " shikenan mun fasa fita goben kenan?
" A 'a bamu fasa ba, zan kai ki duk inda kike so,
ki shirya da wuri dan mu sha yawo sosai,
cikin jin dad'i tace " nagode sosai Yaya,
kana ta koma ciki wayarta rik'e a hannunta,
ya ji duk abinda suka ce,
k'ofar ta dannawa key, tana cewa " tab daya shigo kai tsaye daya kenan,
daga ni sai bra & under ta fad'a tana ajiye hijab d'in saman bed had'i da d'ora ledar take away saman bedside,
da sauri ta mayar da wayar kenenta gami da cewa " au daman baka kashe ba?
In stead of ya bata amsa sai yace " ke da waye?
"Yaya Aarib,
meya kawo maki?
" Ni bamma duba ba, amma nasan bai wuce ice cream & shawarma,
" ina zaku gobe?
Ya kuma tambayarta idanshi rufe,
batare da tasa komai a ranta ba tace " yawo da shan ice cream,
cikin zafin rai ya bud'e idanshi yace " what!?
" Kin san yadda nake sanki nake kishinki kuwa?
" Yanzu fa in banda Allah ya kiyaye da kai tsaye zai shigo miki bedroom ya ganki haka babu kaya,
" amma Hub! naga Yaya na ne fa,
a hasale yace " idan yayanki ne sai akace babu aure tsakaninku?
Shiru tayi tana tunanin ya akayi yayi mata mugun sani haka,
yasan komai nata da rayuwarta yasan every movement & family issues d'inta,
ya akayi Aryan yasan Aarib ba d'an uwana uwa d'aya uba d'aya bane?
" Saboda ina sanki, ya bata amsa,
bata san maganar da take yi ta fito fili yaji ba,
" to ai babu komai tsakanin mu dashi fa,
jin ranshi da zuciyarshi yake kamar zasuyi bombing,
saboda yadda yake jin tsananin zafi da k'una had'i da rad'ad'i,
sanin idan yace zayyi magana a halin dayake ciki yanzu,
yana iya b'ata farin cikin su da suka soma,
yasa shi cewa " ina zuwa....!
ya fad'a muryarshi na shak'ewa,
bai jira jin abinda zatace ba yayi dropping wayar,
komawa yayi ya kwanta had'i dayin pillow da hannunshi,
while d'aya hannun ya d'ora saman kanshi had'i da rufe idanshi,
yana jin yadda zuciyarshi ke tafasa tana azalzalarshi,
cikin ranshi ya shiga fad'in " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
abinda yayi ta maimaiwa cikin ranshi kenan,
har ya samu yaji zuciyarshi ta fara yin sanyi,
yadda yayi maganar ya tabbatar mata yana cikin wali hali,
da matsananciyar damuwa,
ji tayi gaba d'aya hankalinta yayi mugun tashi,
taji kamar tayi hauka, a hankali ta kwanta saman bed d'in had'i da rufe idanta tana jin gaba d'aya duniyar tayi mata bak'i k'irin.........!
Ta jima a haka kana ta mik'e ta sanya kaya,
ta koma ta kuma lafewa saman bed,
shina kwance yake kawai ya fad'a duniyar tunani
abu ya taru yayi mishi yawa,
ga abinda Hanash yayiwa Sanah,
ga Aarib na neman shigar mishi rayuwa,
ya shiga mishi hanci da k'udundune,
a hankali ya mik'e zaune had'e da tallafe hab'arshi da suka hannayenshi,
akwai abinda yake ta k'ok'arin san tunawa kan Aarib d'in amma ya kasa,
haka nan kawai yaji gabanshi na fad'u,
ajiyar zuciya ya sauke had'i da mik'ewa a hankali,
yana gaf da shiga bathroom ya tuna abinda yake ta k'ok'arin tunawa,
ranar d'aurin auren Khulud yaji lokacin da Aarib d'in,
yace " love of my life, I love you,
lokacin da Sanah ta fito daga cikin bedroom,
tab! take yaji k'irjinshi yayi muguwar bugawa da k'arfi,
take yaji gaba d'aya hankalinshi,
yabar Maiduguri yayi Kano ta dabo,
a ranshi yace " dama nima nayi sake, ban gama gina soyayyata ba,
na barta gashi nan ina neman yiwa kaina sakiyar da ba ruwa.
Aarib nacan nata faman juyi saman bed ya kasa bacci,
dan ya tabbatarwa kanshi lokacin daya je kai mata ice cream,
waya take yi da namiji, kuma da idanshi yaga lokacin data bawa masu gadi shawarmar,
numfaashi ya fitar da k'arfi had'i da mik'ewa zaune,
yace " gobe za'ayita ta k'are kawai,
zan same ta na fad'a mata ina santa, na kuma fad'a mata zan aure ta in 1 week,
ya fad'a yana komawa kwancen,
itama tana can kwance ta kasa runtsawa.
Washe gari da safe haka ta tashi sakaka,
duk wanda ya ganta yasan tana cikin damuwa,
duk ta zama shiru-shiru da ita,
tana zaune saman dinning table gabanta plate an tea cup,
hannunta rik'e da tea spoon tana juyawa a hankali,
idanta kan tea d'in ta tsura mishi ido tana tunani,
ya shigo cikin d'anyan wanka kyanshi da k'uruciyarshi sun fito sosai,
cikin nutsuwa ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun dinning d'in,
had'i da kafe ta da ido, yayinda ita bama tasan ya shigo ba,
iska ya hura mata saman face d'inta,
a hankali had'i da kiran sunanta cikin wata irin murya,
firgigit tayi ta farka,
tunanin me akayi haka!?
Ajiyar zuciya ta sauke tana k'ak'aro murmushin k'arfin hali,
ido ya zuba mata yana karantar yanayinta,
kafin yace " meke damunki princess?
Murmushi ta kuma yi kana tace " bakomai,
idanshi na kanta yace " kinci shawarmar jiya!?
Kai tsaye tace " a'a,
" meyasa!?
"Kawai! ta bashi amsa a tak'aice,
bai damu da yadda take amsa mishi maganar shi ba,
d'an shiru yayi kana yace " magana nake san muyi dan Allah,
hankali ta gaba d'aya ta mayar gare shi tace " ok ina jinki Yaya,
shiru ya kuma yayi kana ya sauke ajiyar zuciya yace " kiyi man alk'awari zaki amince da abinda zan fad'a miki,
" matuk'ar bai sab'awa addini da al'adata ba nayi maka,
" kiyi man alk'awari duk abinda na fad'a miki kona tambaye ki Eh zakice no saying no,
d'an shiru tayi kana tace " ina jinka,
ajiyar zuciya ya kuma saukewa kana cikin sanyin murya yace " ina sank...............
MOMYN ZARAH
[7/7, 5:13 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
```DIDECATED TO```
*ZUWAIRAT UMMU MARYAM*
*(UWAR D'AKIN SAFWAN)*
3⃣7⃣
Cikin sanyin murya yace " ina sank..........,
bai k'arasa fad'ar abinda yayi niyya ba,
wayar ta dake gefe saman dinning ta soma ruri,
" ina zuwa! tace tana d'aukar wayar,
ganin shine take duk ilahirin jikinta ya soma b'ari,
cikin rawar jiki tayi picking,
Aarib sandarewa yayi akan kujerar had'i da zuba mata ido,
yana san jin wanda ke kiranta da har jikinta ke tsuma haka,
cikin d'oki tayi picking " hello Hub..!,
ta fad'a cikin rawar murya, murmushi yayi cike da tsantsar farin cikin jin zanzak'ar muryarta,
yace " na'am! K'albi!,
cikin shagwab'a tace " jiya fushi kayi ko?
Murmushi yayi mai sauti wanda ya k'ara bayyanar da kyan fuskarshi,
yace " wane ni da yin fushi da ruhi na,
cikin shagwab'ar ta kuma cewa " to meyasa kak'i k'ara kira na,
kuma dana kira ka bakayi picking ba?
"I'm sorry K'albi! yanzu baga ni gare ki ba,
murmushi tayi had'i da sauke ajiyar zuciya tace " Allah ka sani cikin wani hali jiya da kewar muryarka na kwanta,
kuma na kasa yin baccin ma, ka ganni nan na sanya abinci gaba na kasa ci,
" meyasa K'albi.....!?
" Ba bai bane! kaja naji ban san komai,
" tom ayi hak'uri ban k'arawa,
" ai baka laifi koma kayi an yafe maka tun kafin kayin,
murmushi ya kuma yi had'i da cusa hannunshi cikin gashin kanshi,
yace " kina ina..!?
" Gida mana, baka hana ni fita ba?
"Lek'o kiga wani abu,
" ina zan lek'o...?
" Harabar gidanku, da sauri ta mik'e,
ta fita da gudu kunnenta manne da wayar,
tabar Aarib zaune anan kamar mutum mutumi,
yayi shiru yadda kasan an zare mishi kuzari da lakar jikinsa,
ya kasa kwakkwaran motsi saboda tension,
kwata-kwata ta manta dashi,,,
tsaye ta ganshi jikin motar shi k'irar Benz 2019,
sanye cikin lace na maza white color,
d'inkin mai shegen kyau agogon hannunshi k'irar Paul newman Rolex,
takalminshi na kamfanin Valentino,
sai hula daya d'ora saman kanshi,
ido suka zubawa junansu suna kallan juna,
fuskar kowanne d'auke da k'ayataccen murmushi,
can k'asan mak'ogwaranta tace " My Man!!,
murmushi yayi mata had'i da kashe mata ido,
dan yaji abinda tace ta cikin wayar,
bata san sanda ta nushi da gudu ba,
ido ya zaro ganin yadda ta fito kuma ga ta nufoshi da gudu gaban masu gadi da drivers,
kanshi ya shiga girgiza mata had'i dayi mata magana da ido,
da ido yayi mata alamar ta kalli jikinta ta kuma kalli mutanen dake wajen,
tsayawa tayi had'i da kallan kanta,
dan ita ta manta daga ita sai 3 Quarter da mata da body hug,
wacce gaba d'aya wuyanta da bayanta ke bud'e,
kanta babu d'an kwalli sai reborn data tufke gashin kanta dashi,
da sauri ta juya ta koma ciki tana dariya,
tana shiga gidan Dide ya fito, da alama fita zayyi,
cikin nutsuwa Aryan ya gaidashi,
Dide ya amsa cikin fara'a da sakin fuska,
" Sanahr bata fito bane?
Dide ya fad'a yana kallan Sir Moli,
kanshi ya shafa " eh,
" ta san da zuwanka?
" Eh dama test zasuyi a makaranta kuma inata kiran wayarta bata shiga shine nace bari nazo na sanar da ita,
" ah to mun gode sosai, bari nasa Aarib ya kaita to,
" idan ba damuwa sai mu tafi tare na aje ta dan nima makarantar zan koma,
d'an shiru Dide yayi kana yace " ok badamuwa,
zaune ta iske Aarib ya rafka uban tagumi hannu bibbyu,
ji yake kamar yayi ta ihuuuu yana buga kanshi da bango,
" please Yaya Aarib kayi hak'uri mu bar maganar sai anjima,
yanzu my love he's out yana jira na,
bata jira amshi kota kula da yanayin dayake ciki ba,
ta shige bedroom d'inta da sauri ta canja kaya ta zura doguwar rigar material lace mai shegen kyau da tsada,
ta d'anyi heavy make up,
had'i kafa d'aurin d'an kwali....,
wayar ta kawai ta d'auka ta zura takalmi tayi waje,
yadda tabar Aarib haka ta dawo ta iske shi,
" Yaya kazo ku gaisa da My life mana,
ta fad'a tana cigaba da tafiyar,
kanshi duk'e a k'asa bai d'ogo ba,
tun da ta fito idansu ke sark'e cikin na juna fuskarsu d'auke da murmushi,
" masha Allah, Alhamdulillah Ubangiji yayi halitta anan,
ya fad'a cikin ranshi, in banda cikin gidan su suke da babu abinda zai hana shi rungume ta,
" I love you so much my everything,
ya fad'a mata lokacin data k'araso,
cikin farin ciki tace " I love you too Hub!,
zuwan bazata ko..!?
" Eh man bagashi bakinki yak'i rufuwa ba,
nasan idan nayi miki zuwan bazatan sai kin fi jin dad'i,
" ai kowanne irin zuwa zakayi zanyi farin ciki sosai Hub!,
hannunshi ya sark'e saman k'irjinshi,
idanshi kanta yace " kina da kyau my K'albi dan ban cewa kinyi kyau,
saboda kinfi shi kanshi kyau kyan,
murmushi tayi cike da jin dad'i tace " kai ma haka,
yace " dana barki da hakan zaki fito k'arti su gane man mata?
" To ba kai bane! ta fad'a cikin shagwab'a,
" danayi me?
" Ka rud'a ni mana, ganin ka yasa ni mantawa da komai,
dariya yayi yace " oh! da ashe ana so na ake kauda kai ana had'iyar yawo,
har ake gara ni ana jana k'asa,,,
dariya itama tayi tace " hmmm ya ka baro Nailah da Hilwa?
" Suna lafiya sunce na gaida ki sosai,
" ina amsawa...!
" muje ko?
Da idonta ta tambaye shi ina...,
" saida ki zanyi,
" da kafi kowa shiga damuwa,
dan nasan har kwanciya hospital sai mutum,
ko a saka man Nainah da Hilwa gaba ana kuka,
dariya yayi sosai yace " ni ko hmmm nagode,
ya fad'a yana bud'e mata motar,
" wai ina zamu?
"Ai ta tambayi izinin fita dake,
" wajen wa?
"Dide yanzu na tambaye shi ya kuma yarda,
" mekace mishi?
Dariya yayi kana ya fad'a mata yadda sukayi da Dide,
"Ok bari na sanar da Mamu, ta fad'a tana juyawa,
bata jima ba ta dawo ta shiga, shima ya zagaya ya shiga, yaja sukayi waje,
duk abinda ke faruwa kan idan Aarib,
dakyar ya iya mik'ewa yaja k'afarshi ya koma part d'inshi,
ya zube k'asan tails yana ruzgar kuka wiwi.
A wani had'add'an park mai shegen kyau,
wanda ya gaji da had'uwa, ya tsaro sosai kai da ganin ginin da tsaruwar wajen,
kasan turawa ne suka gina shi,
LAGOSA park and garden wajen zuwan manyan mutane masu kud'i,
sosai wajen ya k'ayatu sosai kamar k'asar waje yake,
a hankali ya bud'e motar ya fita,
ya zagaya b'angarenta ya bud'e mata motar,
had'i da mik'a mata hannunshi,
babu gardama ta d'ora hannunta saman nashi,
idansu cikin na juna suna sakarwa juna k'ayataccen murmushi,
idan ka gansu sai rantse they're Arabian couple's,
sunyi shegen kyau had'i da dacewa da junansu,
cikin nutsuwa suka fara takawa,
cikin wata k'ofa ya shigar da su,
suna shiga taga anyi rubutu da manyan bak'i,,
_"You are welcome my K'albi Mrs Aryan Rayyan Moli_
kallanshi tayi suka yiwa juna murmushi,
daga gefe da gefe na k'ofar wasu kyawawan yara ne jere ,,,
hannunsu rik'e da couples spray,
suna k'arasa shiga cikin k'ofar yaran suka shiga fesa musu spray d'in suna murmushi,
murmushi tayiwa yaran had'i da shafa kawukansu,
a hankali idanta ya sauka kan wani k'aton frame wanda girmanshi zai kai rabin bangon da yaje lik'e jiki,,,
d'auke da makeken hotanta tana murmushi,
daga saman hotan an rubuta..!
_" how can I tell you I'm in love with you? My love I'm not able to tell you what's left in my heart, but my eyes has been explain it to you, the dream are still under my eyelids with you my K'ALBI..........!!!_
kwata-kwata bakinta yak'i rufuwa saboda farin ciki,
hannunta cikin nashi yace " mu je ko my K'albi!?
Bin shi tayi suka cigaba da tafiya,
bai fi taku goma sukayi ba,
taji flowers na sauka jikinta daga sama,
baki ta bud'e cikin mamaki ta d'aga kanta sama,
fuskarta d'auke da murmushi har side dimple d'inta na lotsawa,
kanta ta d'aga sama had'i da lumshe idanta tana shak'ar k'amshin flowers d'in,
tsaye yayi yana kallanta cikin so da tsantsar k'auna,
" I love you so much Hub! ta fad'a cikin farin ciki,
bayyi mata magana ba, ya sake yin gaba,
cikin wani babban hall suka suka b'ulla,
hall d'in yasha decoration irin na wajen bikin Indian sak,
tun daga bakin k'ofar har zuwa inda zata zauna flowers ne zube a k'asan,
a tare suka d'ora k'afafunsu kan flowers d'in suka taka har inda zasu zauna.
Daga gaban bangon da zasu zauna still k'aton hotanta ta gani,
manne jiki anyi rubutu daga k'asan shi,
_I live every seconds, every minutes, every hours, every week, every months and every years only you my K'ALBI........!!_
eyeball to eyeball suke kallan juna,
in slowly Aryan ya ciro zuben diamond cikin aljihunsa,
had'i da durk'usa gabanta yace " will you marry....!?
Cikin tsananin farin ciki ta sanya hannu ta rufe bakinta,,,,
tana murmushi had'i da d'aga mishi kanta tace "yes I will,
a hankali ya rink'o hannunta ya saka mata goben,
hannun daya sanya mata zoben ta d'aga ta kalla tace " very soon I will be come MRS ARYAN RAYYAN MOLI,
ta fad'a muryarta ta rawa saboda tsantsar farin ciki,
a hankali ya rink'o ta ya zaunar saman lap d'inshi,
had'i da d'ora goshinta saman nashi,
yace " I love you so much, ina sanki fiye da rai na da rayuwa ta,
don't separate with me please,
kissing kumatun shi tayi kana ta kalle shi tace " I will never ever,
murmushin jin dad'i yayi kana ya nuna mata goshin shi yace " saura nan,
da ido ta tambaye shi me....!
shima da idanshi ya nuna mata lips d'inta,
murmushi tayi had'i da yin kissing goshin nashi,
kumatunshi ya nuna mata nan ma tayi ba musu,
d'aya kumatun ya kuma nuna mata,
ta kuma yin kissing d'in,
ya nuna mata hancinshi,
nan ma tayi,
ya nuna mata hab'arshi, tayi,
cikin salo idanshi cikin nata yanayi mata wani irin kallo mai saukar da kasala,
ya d'ora hannunshi saman lips d'inshi ya nuna mata,
had'i da cewa " saura nan...!,
hararar shi tayi had'i da d'an dukan kafad'arshi tana dariya,
ta mik'e, mik'ewa shima yayi had'i da rik'o hannunta,
cak ta tsaya batare data jiyo ba,
cikin salo ya juyo da ita had'i da manna ta jikinshi ya d'ora hannunshi bayanta,
idanshi cikin nata, a hankali ya mayar da kallanshi kan cutie lips d'inta,
itama nashi lips d'in ta kalla,
while duk su biyun suna fitar da numfashi da sauri da sauri,
ganin yana k'ok'arin had'e bakin su yasata mayar da kallanta,
kanshi ta kafe shi da idonta,
murmushi yayi had'i da sanya tafin hannunshi saman fuskarta ya rufe mata ido,
shima ya lumshe idanshi kana ya dad'e bakinsu, ya suka shiga tsotsar lips d'in juna,
had'i da fitar da numfashi, sun d'an jima haka kana a hankali ya zame bakinshi daga nata,
yana murmushi, kanta ta sunyar cike da kunya,
" have a site please a hankali ta zauna, shima ya zauna,
" murmushi ya kuma yi yace " shyness girl!
bata kalle shi ba tayi murmushi,
" I love you ya kuma fad'a mata,
a hankali ta d'ago kanta ta kalle shi,
" mu je yace yana mik'ewa had'i da mik'a mata hannunshi,
cikin nutsuwa ta sanya hannunta cikin nashi kana ta mik'e,
gaban wasu glasses suka je,
shawarwa, pizza & Burger ta gani cikin kowanne kala-kala na k'asashe daban-daban,
a jikin kowanne glass an rubuta sunan na k'asar wajen kala 20,
daga gefe kuma ice cream ne different flavors,
kallanshi tayi tace " wannan fa?
" Naki ne duk ke d'aya,
zatayi magana yayi saurin d'ora finger d'inshi saman lips d'inta,
yace " shhhhhhhhh!
" fad'a man wanda zakici nayi serving naki,
vanilla flavor ta nuna masa na ice cream,
kana ta nuna mishi Arabian shawarma & American burger,
da kanshi ya zuba ya kai kan table,
ya rink'a bata a baki harta ci ta k'oshi,
" Allah na k'oshi ta fad'a cikin shagwab'a,
" kad'an fa zaki k'ara,
" ban iya k'arawa,
" to shikenan ya fad'a yana ture abincin gefe,
tace " kai fa..!?
"Me?
" Baka ci ba kai ?
" Murmushi yayi yace " azumi nake yi,
hararashi tayi tace " kana azumin kuma......!
shiru tayi ta kasa k'arasawa,
ya gane abinda tayi niyyar fad'a,
dariya yayi sosai yace " nayi me?
Baki ta turo cikin shagwab'a tace " Allah nasan ka gane,
cikin dariya yace " ni ban gane ba,
ganin yana neman jan maganar yasata,
cewa " shikenan tunda baka gane ba abar maganar,
" a'a ni ban yarda ba sai kin fad'a man,
" kana azumin kayi man kiss,
ta fad'a kamar an fuzgi maganar daga bakinta,
" ai banji komai ba, kawai dai nayi miki ne dan naga kina so,
ya fad'a in a funny way,
ido ta zaro tace " wad'in?
"dariya yayi sosai kana yace " a'a wancan ya fad'a yana nuna mata pic d'inta,
baki ta turo tace wayo ko?
Sosai sukayi hira kana ya mayar da ita gida,
babu yadda bayyi da ita tafi da kayan ba,
amma tak'i d'aukar koda ice cream,
lokacin data koma gida taci sa'a su Mamu sun tafi islamiyya,
part d'in Halan ta shiga, ta iske ta zaune cikin parlor tana kallan shirin kwana cas'in a tashar Arewa 24,
kallanta Halan tayi ta ganta cikin annuri sosai,
a hankali ta zauna kusa da Halan,
Halan tace " daga ina haka?
" Daga unguwa nake,
" ina kika je na ganki cikin walwala da farin ciki?
" Fita mukayi da Sir Moli,
wai su Halan anji gulma,
da sauri ta jiyo sosai tana kallan Sanah tace " wa!?
"Eh! ai nasan kinji wa nace,
" eh naji abin ne naji kamar kunne na yayi man k'arya,
" a'a ba k'arya kunnanki yayi miki ba,
soyayya muke yi da Sir Moli sosai,
muna kuma san junanmu kamar mu mutu,
cikin dariya Halan tace " a'a ku taimaka karku mutu,
tab! kice mun kusa shan biki!?
" A'a bikin nan ba yanzu ba fa,
duk da naga shima zumud'in da yake tayi kenan,
magana d'aya biyu aure,
" tohhh ikon Allah Sanah meye amfanin soyayya?
"Ai naga kamar auren shi yafi tun da kuna san junanku,
" eh zamuyi amma so nake sai nashi level 3 ko 4,
dan ban san Baby su hana ni karatu,
saboda na lura yana san yara da yawa, bai tab'a yarda muyi planning,
" a'a Sanah babban burin kowacce mace ta ganta gidan mijinta,
karfa kiyi sake,
baki ta tab'e tace " saken me! akan wa! badai Aryan ba?
" A'a nidai shawara kawai nake baki,
idan haihuwa ce baki so kiyi mishi magana ku tsara rayuwarku idan ya yarda sai musha biki,
"tab wallahi fad'a zamuyi wannan mai shegen san yaran,
k'ilamma yace " ban san shi shiyasa ban san haihuwa dashi,
" ki gwada yi mishi maganar, ba direct zaki fito kiyi mishi maganar ba,
ta baibai zaki b'ullo mishi ki bugi cikinshi,
" wai Sir Moli zan yiwa wayon?
" Kema ma fa kin san shi kin san halin shi kin san waye shi,
sai dai ma ki bawa wani labarinshi,
duk ta inda aka biyo mishi sai ya gane,
" wallahi ni so nake na ganki cikin gidan auren ki kema!
" ke dai ba kina cikin naki gidan auren ba?
" To sarkin fad'in bak'ar magana,
dariya tayi tana mik'ewa tace " bari naje na d'ora abinci kafin Mamu ta dawo,
nayi wanka kuma kafin lokacin waya yayi,
" tom Mrs Sir Moli baki ban labarin yadda kukayi da Khulud ba?
" wow perfect name tace tana kad'a boom boom,
" hmmm Allah ya nuna mana lokacin muga k'arshen rawan kan nan,
" amin tace tana k'ok'arin fita,
Halan tace " bafa ki fad'an ba!
" kamar dai yadda kikace man haka akayi,
ki bari zan shigo sai muyi maganar,
ta fad'a tana fita da gudu dan ta waske saboda bata san takamaiman abinda zata ce mata ba.
Tana komawa gida ta saka wayarta a caji,
ta shiga kitchen ta d'ora abinci,
cikin sauri-sauri take aikin dan haka tayi saurin gamawa
ta zuba cikin food flak takai komai da komai kan dinning table ta shirya,
kana ta d'auki wayarta ta shige bedroom d'inta,
wayar ta wulla saman bed ta fad'a bathroom,
tayi wanka had'i da alwala ta fito ta shirya kana ta tada sallah,
sai da ta gama komai kana ta koma parlor dan ta jiyo muryar Mamu,
" sannu naga kinyi girki ko?
"Eh nayi,
" me kaki dafa?
" Tuwon semovita da miyar d'anyar kub'ewa,
" Alhamdulillah kamar kin san yau tuwo muke sanci,
Allah yayi miki albarka ya saka miki da alkhairi ya baki miji nagari,
"Amin my Mamu,
har Mamu takai bakin k'ofa ta juyo tace " jeki kira yayanki yazo yaci,
" wanne daga ciki?
"Aarib! tace tana shigewa bedroom,
" tabbbb!! Sanah tace dan sai lokacin ta tuno da Aarib,
da sauri ta fita ta nufi part d'inshi,
knocking tayi daga bakin k'ofar had'i dayin sallama,
takai 5 minutes tana knocking had'i da sallama,
amma ba'a amsa mata ba,
har ta juya zata tafi tajiyo nishinshi cikin d'akin,
da sauri ta tura k'afar ta danna kai,
batare data lura da privacy d'inshi ba,
kwance ta iske shi saman tails yana nishi,
a firgice ta k'asara inda yake had'i da d'ago shi,
" Yaya lafiya! meke damunka?
Dakyar iya bud'e idanshi jin muryarta,
ido ya k'ura mata hawaye na zubo masa,
cikin muryar kuka yace " mutuwa zanyi princes I lose her,
ban iya rayuwa idan babu ita, ina santa sosai ina matuk'ar santa,
tun tana yarinya nake fama da azababbiyar soyayyarta,
amma ina ji ina gani wani ya same ta,
an kwace man ita an raba ni da ita,
sarai ta gane da ita yake dan ta fahimci abinda yayi niyyar fad'a d'azu,
amma sai tayi kamar bata gane ba,
tace " kayi hak'uri Yaya wani bai tab'a auren matar wani,
haka wani bai tab'a haihuwar d'an wani,
komai daka gani a rayuwa rabo da k'addara ne,
babu wani d'an Adam daya isa ya kaucewa k'addararsa,
may be tun farko Allah ya riga ya tsara itan ba rabonka bace,
ba matar aurenka bace, kayi addu'a Allah ya baka wacce ta fita komai,
kuma Allah yasa haka ne ya fiye muku alkhairi gaba d'ayanku kai ita,
duk abinda kaga ya samu daga Allah ne,
dan shike da ikon tsarawa kowa rayuwa,
babu wanda ya isa ya kaucewa hukucin Allah, da k'addarar shi,
ta fad'a cikin tausayawa,
ido ya k'ura mata dan shima ya fahimci ta gane da ita yake,
cikin rawar murya yace " shikenan yanzu bazata tab'a tausaya man ba?
" Bazata taimaki rayuwa ta ta so ni ba?
" Ka fahimce ta itama ka tausaya mata,
zai iya yiwa ta riga ta fara san wancan,
ta fara mishi mugun son da bazata tab'a iya rayuwa babu shi,
may be rabuwa dashi tamkar rabuwa da numfashinta ne,
kaga bai yiyiwa ta taimake ka ita kuma ta watsa rayuwarta ba,
ta rayu cikin k'unci da rad'ad'i had'i da azabar so,
kuma kai ma da laifinka mai yasa tun farko baka sanar da ita ba?
A hankali ya gyara zamanshi sosai,
kana ya mayar da kallanshi kanta,
yace " shikenan bakomai!
" dan Allah ka tashi kayi wanka na kawo maka abincinka nan kaci kasha magani,
kanshi ya kawar gefe alamar bai tashi,
dakyar ta sashi ya mik'e ya shiga wanka,
d'akin ta gyara mishi sosai ta share ko'ina tsaf,
ta jona bonar turaren wuta, kana ta fita,
yana jin ta fita ya fito d'aure da towel,
gudun karta dawo ta same shi naked yasa shi gaggauta shiryawa,
ya tada sallah,
ita ko zama tayi dan ta bashi ishashshen lokacin da zai shirya,
sai da akayi 20 minutes kana ta d'auko abinci data jera mishi saman tray,
had'i da Panadol extar-pain relief ta koma bedroom d'inshi,
sai da ta tsaya tayi sallama ya bata izinin shigowa kana shiga,
da kanta ta bashi abincin yaci sosai ta bashi maganin yasha,
ta umarceshi ya kwanta ta rufe shi da bargo kana ta mayar da wutar d'akin dum light ta fita.
Tare da Abbu da Mamu suka ci abincin,
suna hira cikin farin ciki har suka gama,
kana ta kwashe kayan ta wanke ta gyara wajen tsaf,
ta shige bedroom d'inta ta kwanta,
dan tun shigowarta d'aukawa Aarib abinci tayi sallar ishsha,
a hankali ta mik'e ta cire kayan jikinta ta saka na bacci,
tana ninke wanda ta cire kiran shi ya shigo,
murmushi tayi had'i da d'auka,
aminci da yardar Ubangiji su tabbata ga ruhin Moli,
" amin ya Allah tare dakai,
" an gama shiryawa ko?
" Eh kai kawai nake jira,
dariya yayi yace " gani gare ki,
" yanzu dai kaci abinci danna sanka baka san cin abinci?
" Idan ana san na rink'a cin abinci akan lokaci sosai a aure ni mana,
" za'a aure ka in sha Allah very soon ma kuwa,
" yauwa K'albi yanzu naji batu,
ki rink'a haifo man 'yan uku-uku masu kama dake,
" tab! ya zanyi da 'yan uku ni dasu wazai reni wani?
Sosai maganarta ta bashi dariya,
" ki bari idan kika haifa zaki san yadda zakiyi dasu,
kuma baga ni ba,
" kai da zaka rink'a tafiya wajen aika ka barni dasu,
" a'a babu inda zani ina manne da matata,
idan masu kuka ne kuma tab...!
" idan na rarrashi su suka k'in yin shi sai na saka su gaba muyi kukan tare,
dariya ce ta kucfe mishi sosai jin abinda tace " iya rigima kenan,
" yanzu gaya min mekika ci?
" Tuwon semovita miyar d'anyar kub'ewa,
" ni ko kinga fresh milk da fruits kawai naci,
" ayya Hub! meyasa baka san cin abinci sosai?
" Bani da mai a baki kuma wani lokacin abincin kuku bai man dad'i sosai,
" ayya Hub kayi hak'uri kaji da munyi aure ka huta ko?
" In sha Allah K'albi,
sai da suka kai k'arfe 2:30am na dare suna waya cike sa shauk'in junansu,
" kije ki kwanta kinga yanzu dare yayi sosai,
" ayya ban tab'a gajiya da yin waya da kai,
baccin ma bai zuwa idan ina jin dadd'ar muryarka,
murmushi yayi idanshi lumshe,
yace " wallahi ni zan iya k'are rayuwa ta a haka,
ina sauraron muryarki,
murmushi tayi tace " gud 9t Hub! I love you more & more & more,
ta fad'a cikin d'aga murya da k'arfi,
dariya yayi yace " I love you too K'albi,
muuuuuuuuuhhh yayi mata kiss ta cikin wayar itama ta mayar mishi kana suka kashe wayar,
dukkan su suka kwanta cikin tsantsar farin ciki,
while Aarib na can sai juyi yaje ya kasa bacci dan maganganun Sanah,
sun tabbatar mishi daya rasa ta har abada,
amma bakomai ya san meye mafita,
ya san abinda zayyi ,
zayyi abin da dole dole abashi ita ya aura,
ko da zai rabu da kowa a duniya.
A b'angaren su Khulud kam tun ranar da abin ya faru ya shiga wasan b'uya da ita,
dan yasan yayi mata lefi tana fushi dashi,
tana zaune a parlor da daddare,
ya shigo gidan, dan yana zaton tayi bacci,
rai a had'e yana k'ok'arin shegewa ciki,
amma bisa mamakinsa yana shigowa ta tare shi fuskarta d'auke da murmushi,
had'i dayi mishi sannu da zuwa,
kwata-kwata babu alamar wani abu ya faru tsakanin su,
murmushi yayi cikin jin dad'i da tsantsar farin cikin,
ya rungume ta, yayi kissing goshenta yace " Allah yayi miki albarka,
" Amin ya Allah, muje kaci abinci,
kan dinning table d'in ta kai shi ta zaunar dashi,
tayi serving d'inshi, kana ta shiga bashi abincin a baki, kasancewar abincin yayi mishi dad'i sosai,
yasa shi zagewa ya ci ya k'oshi,
sai wani rawar kai yake yi a zatonshi,
ya fara cin nasara ne, bai san hakan da ake mishi umarnin Sanah bane,
bedroom ta kai shi ta had'a mishi ruwan wanka,
ya shiga, ita kuma ta fito, ta bud'e wardrobe ta fiddo mishi kayan bacci ta ajiye saman bed,
kana ta fita ta kwashe kayan abincin ta gyara wajen,
itama tayi wankan, ta shirya kana ta kwanta saman bed,
dan bata jin zata iya zuwa bedroom d'inshi yau,
hakan ma datayi mishi saboda tayiwa Sanah alk'awari ne,
fitowa yayi daga wankan bai iske ta ba,
baki ya tab'e yana cewa " yanzu da ita wata ce kamata yayi ta tsaya ta tsane ni da towel kana ta taya ni shiryawa,
amma ita kwata-kwata bata san irin wad'annan abubuwan ba,
biyayya da girki kad'ai tasani,
tsoki ya ja kana ya saka kayan data fito mishi dashi,
ya shirya sosai ya fesa turarurruka masu k'amshi da tsada,
ya nufi bedroom d'inta, tana jin motsinshi tayi saurin rufe idanta,
dan bata san ya neme ta, saboda bata iya hanashi hak'k'inshi,
tsayawa yayi bakin gadon yana kallanta,
yasan ba bacci take yi ba, a hankali ya kwanta saman ta,,,
had'i da goga fuskarshi saman tata,
kana yace " nasan idanki biyu,
k'in bud'e idanta tayi balle tayi mishi magana,
ganin haka yasa shi yin murmushi had'i da had'e bakinsu,
a hankali ya zura hannunshi cikin rigarta,
jin bra yashi jan tsoki cikin ranshi,
amma a fili bai nuna mata komai ba,
shi da kanshi ya cire mata rigar,
kana ya shiga romancing d'inta,
yana wasa da boobs d'inta while yana shafa ko'ina na jikinta,
kamar yadda ta saba as usual tayi kwance kamar ruwa,
sai dai shi ya sarrafa ta yau ma hakan tayi,
shi kad'ai yayi komai ya hau yayi ya sauka,
ba tayi wani yi mishi komai ba,
no participating no sex sound,
gefe ya koma ya kwanta cike da tsantsar bak'in ciki da takaici,
in banda tsoki babu abinda yake ja cikin ranshi,
har bacci ya d'auke shi.
Washe gari da safe bayan ta gama had'a breakfast,
tayi wanka ta k'afe tsaf ta shigo tashin shi a bacci,
k'afarshi ta d'an tab'a tana kiran sunanshi,
a hankali ya bud'e idanshi ya sauke kanta,
murmushi tayi mishi tace " ka tashi kayi wanka lokacin office yayi,
murmushi kawai yayi mata batare dayace komai,
ta mik'e ta fita, bayan ta yabi da kallo cikin ranshi yaja tsoki had'i da cewa " no sexy words no dirty talk,
shi kanshi tashin miji daga bacci bata iya ba,
tsoki ya kuma ja yace " totally she's not romantic girl ,,,
haba ayi mace kamar ba mace ba,
wani namijin ma yafi ki sanin abubuwa,
ya fad'a yana shiga bathroom.
Kwance take cikin bedroom d'inta,
ta lula duniyar dadd'an bacci mai cike da dad'ad'an mafarkai iri-iri,
cikin sand'a ya turo k'ofar a hankali,
ya shigo a hankali ya rink'a takawa har ya isa bakin gadon da take kwance,
tsayawa yayi had'i da kafe ta da idanshi,
yayinda hawaye suka shiga ambaliya suna rufdugun zubo mishi,
saboda tsantsar bak'in cikin dayake ciki,
na abinda yayi niyyar aikatawa amma yasa hakan me kad'ai,
zai bashi damar mallakarta da kuma auren ta,
a hankali ya zauna bakin gadon yana kallan santala-santalan cinyoyinta,
ta inda 'yar yaloluwar rigar baccin ta tattare,
idanshi ya runtse da k'arfi while hawaye na cigaba da zubo mishi,
cikin kerrrrma da rawar jiki ya d'ora hannunshi saman fatar jikinta,
a hankali Sanah ta d'an motsa,
mik'ewa Aarib yayi ya kashe gaba d'aya fitilar d'akin,
d'akin yayi duhu sosai ta yadda koda ta farka bata tab'a ganin fuskarshi ba,
a hankali ya cire jallabiyar jikinshi,
ya rage daga shi sai boxer cikin sand'a ya lallab'a yahau sasan gadan,
had'i da d'ora bakinshi saman nata,
ya sanya hannunshi cikin rigarta ya soma.....................
MOMYN ZARAH
[7/7, 5:15 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
_Dan Allah muna barar addu'ar ku, anyiwa *AUNTY BATUL ADAM JATTKO* CS jiya dan Allah ku saka ta cikin addu'arku Allah ya bata lafiya ,Ubangiji ya tashi kafad'unta, an samu 'ya mace amma ta koma, Allah yasa mai ceto ce_
3⃣8⃣
Ya sanya hannunshi cikin rigarta ya soma k'ok'arin tab'a boobs d'inta,
da k'arfi ya dunk'ike hannunshi cikin rigar tata,
had'i da runtse idanshi da k'arfi,
kanshi ya girgiza yace " ya salam!....,
subhanallah!... innalillahi wa'innna ilaihirraji'un,
astagfirullah na wa'atubi ilaik....!
a hankali ya zaro hannunshi daga cikin rigar,
had'i da dafe kanshi while bai tashi daga kan gadon ba....,
idanshi ya kuma mayarwa kanta ya kafe ta da ido,
" no! no! I can't doing this, idan nayi haka ban kyautawa Abbu da Mamu ba,
ban kyautawa Dide da Juju ba,
zan lalata ingantaccen zumuncin mu,
idan ko nayi haka ban kyauwa kai na,
ban kuma tab'a yafewa kai na har abada,
ya akayi na bari shaid'an yayi tasiri kaina?
"Ya akayi har na bari wannan bak'in tunanin yazo kaina?
" Ya akayi na yarda na amincewa azzalumar zuciyata data sak'a man wannan bak'in aiki?
"Astagfirullah...! Astagfirullah...! Astagfirullah...!
a hankali ya mik'e ya gyara mata kwanciyarta,
had'i da ja mata blanket ya rufe ta ruf,
a hankali ta motsa ta juya had'i da gyara kwanciyarta sosai,
murmushi yayi hawaye na zubo mishi,
ya d'an duk'a yayiwa goshinta kiss,
had'i da shafa kanta yace " I really love you I can't hurt you anymore,
kana ya mik'e ya fita cikin sand'a ya koma bedroom d'inshi,
ya kwanta yana sauke nauyayyan ajiyar zuciya.
A weeks later
Yau Monday kuma yau ne hutun su Sanah ya k'are,
zasu koma makaranta dan haka tun da tashi sallar asuba bata samu damar komawa bacci ba,
ta shiga kitchen ta had'a breakfast ta jera saman dinning,
kana ta koma cikin bedroom d'inta ta fad'a wanka,
a gaggauce tayi wankan ta fita,
ta shafa mai ta shirya cikin riga da zani na shadda ta kafa d'aurin d'an kwali,
tayi make up ta fito d'as da ita tamkar ka sace ta ka gudu,
a tsaitsaye tayi breakfast kana tayiwa Mamu knocking had'i da yin sallama,
rik'e da canbi Mamu ta fito ta kalle ta tace " har kin gama shiryawa?
" Eh ban so nayi late ne muna da lectures 8:00am,
" kin dai yi breakfast ko?
"Eh nayi ga ku can kan dinning,
" to jira ni ina zuwa Mamu ta fad'a tana komawa cikin bedroom d'inta,
bata jima ba ta fito hannunta rik'e da 50k sababbi dal,
ta mik'a mata tace " gashi nan inji Abbu yace a baki na 1 month ne,
hannu biyu ta sanya ta amsa tana murmushi tace " thank you so much,
Allah ya saka da alkhairi Ubangiji ya bamu ikon yi muku muma,
" Amin ya Allah Mamu ta amsa cikin fara'a,
" Abbun ya tashi ne na shiga nayi mishi godiya?
" Bai tashi ba,
" please idan ya tashi ki mik'a man godiya ta,
"to zaiji in sha Allah,
tana isa harabar gidan Baba driver yayi saurin tasowa fuskanshi d'auke da murmushi,
yace " manyan gobe ina zuwa?
" Makaranta mana Baba...!
" au har kun koma?
"Eh!,
" ashe hutun bai da yawa sosai,
" a'a Baba kadai manta ne kawai amma ai mun dad'e sosai fa,
ta fad'a tana murmushi,
" to manyan gobe muje na kai ki ko?
" Yi zamanka Baba zan kai ta karka damu,
murmushi Baba yayi yace " nagode sosai Aarib,
murmushi tayi tace " Yaya Aarib bazaka makara a office ba?
" Badamuwa muje na kaiki,
" a'a Yaya Aarib please ka bari ya kai ni karka matsawa kanka,
k'ofar motar ya bud'e mata yana cewa " shiga mu tafi ban san jayayya,
murmushi kawai tayi batare datace komai ba,
ta shiga ta zauna , shima ya zagaya ya shiga,
tun da suka soma tafiya yake ta janta da hira,
bata wani amsa mishi sosai wani lokacin murmushi kad'ai take yi,
suna isa harabar makaranta shima yana k'arasowa,
tare sukayi parking motar shi tana kallan ta Aarib,
kishingid'a yayi cikin motar had'i da kafe ta da ido,
kwata-kwata bata kula dashi ba,
amma shi Aarib ya kula dashi,
tana k'ok'arin bud'e motar yayi saurin dakatar da ita yace " tsaya mana!
d'an kallanshi tayi batare datace komai ba,
yace " kin san me?
Idanta kanshi tace " a'a,
a hankali yace " kinyi kyau sosai,
murmushi tayi mishi tana kallanshi,
yace " yaushe zaki shirya na kai ku yawa ke da Khulud?
Ya fad'a yana k'ok'arin janta da hira,
dan ya d'auke mata hankali saboda ya k'unsawa Sir Moli daya kafe su da ido takaici,
sosai ta saki fuskarta tace " Allah da gaske kake?
" Seriously fa,
" to kayi magana da ita Khulud d'in ne?
" Eh itace ma tace na fara tambayarki,
cikin farin ciki da annashuwa tace " mu bari sai ran Saturday ko?
"Yadda zamu fita da wuri saboda kowa nada enough time,
" ok Allah ya kaimu princess,
" amin tace tana k'ok'arin bud'e k'ofar,
saurin dakatar da ita yayi yace " bari na bud'e miki mana,
ya fad'a yana fita, silent killer smile yayi idanshi kan Sir Moli,
kana ya bud'e mata motar ta fito,
zata tafi yace " sorry na manta ban tambaye ki inda zamu ba?
" Kai Yaya ai ka fini ganin gari,
kaga kayya kamata ka nemo mana inda zamu je,
ta fad'a idanta kanshi tana murmushi,
hannunshi sark'e a k'irjinshi yana murmushi,
yace " Ok to muje bakin bitch mu shiga jirgin ruwa ko?
" Ko muje Green park?
" Duk inda ka zab'ar mana yayi,
yadda suke tsaye suna facing juna,
fuskokinsu d'auke da murmushi,
idan ka gansu sai ka rantse tsofaffin masoya ne,
wad'anda suka shahara had'i da macewa,
wajen so da k'aunar junansu,
kwata-kwata hankalin ta bai kai kan Sir Aryan ba,
balle tasan kitimurmura Aarib ke shiryawa,
sallama sukayi kana ta juya ta fara tafiya,
sai da ya bari ta d'anyi nisa kana ya kwala mata kira " princess,
cikin nutsuwa ta juyo fuskarta k'unshe da murmushi,
murmushin shima yayi mata had'i da d'aga mata hannunshi alamar bye,
hannu ta d'aga mishi kana ta juya ta cigaba da tafiya,
duk abinda suke idanshi na kansu,
guntun murmushi yayi na gefen baki,
dan ya gane kitimurmura Aarib ke shirya musu,
kanshi ya shafa yace " kajawa kanka, dan ko daga yau bazata k'ara hawa motarka ba,
kaga kayiwa kanka kenan,
cikin isa, tak'ama had'i da izza ya zura k'afarsa,
k'asa ya taka k'asa kamar bayaso ya nufi office d'inshi,
k'amshin shi data ji ne ya tabbatar mata da yana gaf da ita,
a hankali ta d'ago kanta had'i da sakin kyakkyawan murmushi,
ido ta zuba mishi bata ko blinking,
har yazo gaf da ita ya wuce ta gabanta batare daya kalli inda take tsaye ba,
sosai yadda ya nuna halin ko'in kula kanta yayi masifar bata haushi,
fuska ta tsuke kana ta ida shiga class,
sau biyu tana ganinshi a ranar amma kwata-kwata baya kallan inda take,
har suka gama lectures tana fushi dashi,
suna gama lectures ta fito ta nufi get,
cikin nutsuwa take takawa harta fita daga cikin get,
yana tsaye yana magana da wani lecturer,
amma hankalinshi da nutsuwarshi basa tare dashi,
dan yaga fitarta,
Mutumin zai kuma yin magana Sir Moli yace " kayi hak'uri please gobe zamu k'arasa maganar,
ya fad'a still idanshi yana kan get,
murmushi Mutumin yayi danya lura koda sun cigaba da maganar ba fahimta,
zayyi ba, yace " ok badamuwa Allah ya kaimu goben,
" amin yace yana juyawa,
cikin nutsuwa yake tafiyar yadda kasan babu abinda ya dameshi,
ko ba sauri yake yi ba,
nan ko cikin ranshi ji yaje kamar ya tashi sama,
ko ya zunduma a guje saboda tsabar sauri ya tarar da ita,
a hankali ya bud'e motar ya shiga ya zauna,
had'i dayi mata key yaja ya bi bayanta.
Tsaye ya iske ta bakin titi tana k'ok'arin tsaida mai adai-daita sahu,
gabanta yayi parking tayi saurin d'auke kanta kamar bata ganshi ba,
ta taka ta matsa gaba tabar gurin had'i da fuke face,
gaba yayi da motar ya kuma komawa inda ta tsaya yayi parking,
baki ta murgud'a mishi had'i da k'ara takawa tayi gaba,
kai ya girgiza yana dariya kana ya bud'e motar ya fito,
inda take yaje ya tsaya had'i da langwab'ar da kanshi,
yace " I'm sorry K'albi ya fad'a yana rik'e kunnuwanshi,
d'an kallanshi tayi had'i da turo baki ta kuma kauda kanta gefe,
" ni ne na b'ata ran na sanya wannan kyakkyawar fuskar fushi ko?
"Gaskiya ya kamata a hukunta ni,
amma bari ni da kai na na hukunta kaina,
a hankali ya soma d'an marin kanshi yana murmushi,
" I'm sorry please ban k'arawa,
yadda yake yin abun in a funny way yasata dariya,
d'an tsalle yayi yace " good na sanya ta dariya,
baki ta turo tace " to ba kai bane,
" menayi...!?
Harararshi tayi,
yayi saurin cewa " au na sani ayi hak'uri,
dariya ta kuma, shima dariyar yayi gami da rik'o hannunta,
cikin motar suka shiga suka zauna,
kana yayiwa motar key yaja,
ya kalle ta yace " ke ma fa kinyi laifi....!
ido ta d'an zaro tace " menayi!?
"Shine har da wani zama cikin motar Aarib,
har da yi mishi murmushi, kuma bayan kin fito kika k'ara tsayawa kuna magana harda wani juyowa kiyi mishi murmushi ko?
" Dariya tayi sosai tace " to sarkin kishi,
ashe shiyasa aka d'aure man fuska akayi kamar ba'a sanni ba?
" Eh man!
" to ayi hak'uri ban k'arawa,
" ai baki laifi imma kinyi an yafe miki,
fuskarshi ta shafa tana murmushi jin dad'i tace " thanks Hub,
" yanzu ina zamu, naga kamar ba hanyar gida kayi ba?
" Park zamu je, mu rage tafash,
mu d'auke kewa!
har suka k'arasa suna hira da zuba love,
wajen mai kyau had'add'e sosai,
wajen gaba d'aya manyan yara ne,
' ya'yan manyan masu kud'i,
fili ne wajen an jera wasu irin table da chairs,
da ganin su daga turai akayi oder su,
kwata-kwata wajen babu rana babu kuma wanda ya damu da wani,
yawancin mutanen dake wajen fararen fata ne,
zama sukayi kan kujera gabansu da table,
suna zama wani matashin saurayi yazo yayi tsaye agabansu,
menu d'in Sir Moli ya d'auka had'i da matsawa kusa da ita yace " ga menu d'in me za'a kawo maki?
Kallan menu d'in tayi kana tace " akawo man coffee cappuccino ya isheni,
" kai K'albi wai meyasa baki san ci abinci ne?
" Kanta ta d'an karkatar gefe tace " Allah ya isheni,
" a'a gaskiya sai kin ci wani abun,
ya fad'a cikin damuwa,
ganin reaction d'inshi yasata cewa " ok to a had'o man da fruit salad,
dariya ya saka yace " kuma dai an k'ara kenan,
meye bambamcin su to?
" Abinci mai nauyi nake san ki ci,
rasa mezata ce tayi dan haka ta zuba mishi ido kawai tana kallanshi,
kallanshi ya mayar ga saurayin yace " bani Nigerian menu naku,
rusunawa yayi kana ya juya bai jima ba ya dawo da menu d'in Nigeria,
rusunawa ya k'ara yi ya mik'awa Sir Moli,
amsa yayi ya shiga dubawa kana ya d'ago kai ya kalli saurayin,
yace " ka kawo coffee cappuccino & Indian coffee,
sai ka kawo mana wainar shinakafa da miya da man shanu,
then naman kai, duk abinda Sir Moli ke fad'a yaran yana rubuwa,
" Sir drinks fa?
Kallanta yayi da alamar tambaya tace " ban shan lemo mai gas,
" na sani yace , kana ya mayar da kallanshi ga saurayin yace " ka kawo five alive na roba na pure orange,
sai energy drink,
"Ok Sir, saurayin yace had'i da rusunawa yabar wajen,
kallanshi tayi tace " ka kasan komai nawa!
" yes! yace yana kissing kumatunta,
" I love you ya fad'a yana kissing goshinta,
ture shi tayi had'i da kai mishi duka tace " I know...,
dariya yayi yace " kin san me?
"A'a..!
" please karki k'ara hawa motar Aarib,
duk inda kike san zuwa kiyi man waya ko ki saka driver ya kai ki,
amma dan Allah karki kuma hawa motar shi,
cikin mamaki tace " meyasa!..?
"Please ni dai ki amince idan har kina san kasancewa ta cikin farin ciki da walwala,
dan Allah please inba haka ba......!
" Inba haka me..!?
"In ba haka ba ya d'an fiddo harshenshi,
had'i da d'auke bak'in cikin idanshi ya karkata kai gefe alamar mutuwa,
dariya tayi sosai had'i da d'an dukan k'irjinshi tace " fanny guy,
" please kice man tom!
kanshi ta tallafo had'i da sanya hannunta wajen k'eyarshi,
ta d'ora goshinshi saman nata,
tace " okkkkkkk!!! in sha Allah ban k'ara hawa kaji my Hope,
light kiss yayiwa bakinta, tayi saurin ture shi had'i da kallan mutanen wajen,
taga babu wanda ya damu dasu balle a kula da abinda suke yi,
murmushi yayi yace " I love you..!
sexy eyes d'inta tayi rolling tace " I know...!
ba'a dad'e ba aka kawo musu abincin,
da kanshi ya rink'a bata a baki har suka k'oshi,
sai da sukayi 'yar hira kana ya mayar da ita gida.
_Abinda wasu mazan basu iya ba kenan, (b'oye fishi da danne shi), daga baya idan zuciyarku ta lafa kun samu nutsuwa sai ku magance matsalar cikin sauk'i, cikin lallami da rarrashi, wayo da dabara, amma basu mazan gani suke fad'a da masifa shine zaisa a gyara, ko a daina, abinda basu sani ba shine mace 'yar rarrashi da tarairaya ce, muddin kace zaka bita da yak'i da dole dole sai tayi abu, wallahi kana tare da bak'ar wahala, Allah yasa mu dace._
Washe gari Aarib na ganin lokacin tafiyar ta makaranta yayi,
yayi saurin gama shirinshi ya fita harabar gidan yana jiranta,
bai jima ba ta fito rik'e da waya da alamar ma waya take sai murmushi take yi,
ji yayi gabanshi yayi muguwar fad'uwa,
take yaji k'olulun bak'in ciki cikin ranshi da zuciyar shi,
dakewa yayi had'i da saita kanshi dan baisan kwata-kwata ta fahimci wani abu,
ita ko bama ta lura dashi ba,
balle ta kula da hidimar da yake yi,
ta gabanshi tazo zata wuce batare data kula dashi ba,
da sauri yace " princess ke nake jira fa..!
" au Yaya Aarib ka fito?
" Sorry ban kula da kai ba,
bak'in shi yaji ya k'ara k'aruwa,
amma sai ya k'ak'aro murmushi,
yace " eh na fito ke na tsaya jira ma,
shiga mu tafi,
" yau kam Yaya kayi tafiyar ka kawai,
driver zai kai ni makaranta,
kallanta yayi sosai yace " why!..?
" Murmushi tayi had'i da cewa " haka nan kawai,
ta fad'a tana tafiya,
bai kuma yi mata magana ba,
sai bayanta daya kafe da ido,
ya tabbatar Sir Moli ne ya hana ta k'ara binshi,
yasan kuma saboda abinda yayi jiya ne,
" oh God..! ya fad'a yana dafe kanshi,
duk abinda sukayi Sir Moli yana jin su ta cikin waya,
murmushi yayi had'i da cije lips,
yana kishingid'a kan sofa gami da lumshe idanshi.
Wayar na manne a kunnenshi yace " thank you my happiness,
shiga cikin motar tayi Baba driver yaja suka tafi,
Aarib yabi bayan su da kallo,
" for what!?
"For making my heart happy and shining,
murmushi tayi tace " kasan me?
"A'a K'albi,
" ka tuna mai gadin gidan Khulud da kayiwa alk'awari?
"Opssss....! OMG...! wallahi na manta ne,
ya akayi?
" Yayi man magana nima na manta ban yi maka maganar ba,
sai d'azu da ina shiryawa ya kira ni,
bai ma san ni bace number wani daban yake nema sai ya kira number ya zata number dayake nema ce,
" please ki kira shi yanzu kice mishi mu had'u a LAGOSA park k'arfe biyar na yamma,
" Ok to shikenan!
" ya dai san gari ko?
" Gaskiya ban sani ba amma ina zaton bai sani ba,
amma zance mishi idan ya fito ya tsaida mai napep yayi man plashing,
ya had'a ni da mai napep d'in sai na fad'a mishi indai zai kai shi,
" ok badamuwa ki kira shi yanzu ki fad'a mishi,
Allah ya kawo man ke lafiya,
"Amin...!
ta kashe wayar ta kira mai gadin ta shaida mishi sosai yayi ta godiya kamar ambashi abun,
a makare ta k'araso makaranta,
kuma shine dasu a lokacin gashi bayyin African time,
lokacin data zo har ya fara lectures,
kanta tsaye tayi niyyar shiga cikin class d'in,
fuska ya had'e sosai yadda kasan bai tab'a dariya ba,
yace " ke!.. ina zaki!?
Kallanshi tayi ido cikin ido tace " site...!
" amma kin san ba'a shigo man class late ko?
" Zatayi magana ya k'ara had'e fuska sosai yace " matuk'ar na riga na shigo class ba'a shigo man,
dan haka get out!
ya fad'a yana nuna mata k'ofa,
bata kuma yin magana ba ta fita cikin tsantsar bak'in ciki,
ita ta rasa dalilin dayasa yake yi mata haka,
matuk'ar suna cikin makaranta sai yayi ta d'add'aure mata fuska yana had'e-had'en rai,
ko magana bayyi mata a hankali,
a fili tace " ko dai yana da wata budurwar ne nan cikin makaranta shiyasa yake man haka?
Baki ts turo tana gyara zamanta kan step,
a k'agauce ya gama lectures d'in,
dan yasan yau yayi laifi akwai rigima,
tun daga bakin k'ofar class d'in ya soma kiran wayarta tana rejecting,
" tab..! yau kam ba kanta danna taro march,
har suka gama lectures kwata-kwata fuskarta babu annuri da walwala,
while har suka gama lectures yana ta faman kiranta,
had'i da tura mata sweet messages,
amma ko sau d'aya bata yi picking kota yi mishi reply ba,
zaune yayi cikin mota yana jiran su gama lectures ta fito,
yana ganin sun fara fitowa yayi saurin yiwa motar key ya fita,
yayi parking bakin get yana jiran ta fito,
a hankali take tafiya cikin nutsuwa,
tun da ta fito ya kafe ta da ido bai ko k'iftawa,
ganin ta kusa daf dashi ya sashi fitowa,
dan yasan yau akwai daru, tuni ta hango shi dan haka ta kauda kanta gefe tana niyyar wuce shi,
da sauri yasha gabanta had'i da kama kunnenshi yana up and down,
" I'm sorry K'albi ban k'arawa,
tsaye gabanshi tayi hannunta sark'e a k'irjinta tana kallanshi,
cikin shagwab'a yace " please a tausaya man mana Allah da wahala fa,
bata yi mishi magana ba ta bud'e motar ta shiga,
cikin murmushi shima ya bud'e ya shiga,
yayiwa motar key, " I'm sorry K'albi a yafewa miji mana....!
zatayi magana wayarta ta soma ringing,
kashewa tayi ta kira shi, tace " Baba kun k'arasa ne?
" Ok to gamu nan muma muna hanya,
d'an kallanta yayi yace
" kunyi magana dashi ne?
"Eh! tace tana k'ara tsuke face,
" please ayi hak'uri mana idan lectures ne ke da kike da Malamin ma d'ungurugun,
" ai banga alamar hakan ba!
" dan Allah ki hak'ura ki sakar man fuska,
Allah zanyi miki kuka idan bakiyi hak'uri ba,
murmushi tayi had'i da shafa fuskarshi,
tace " ka kware indai ta wajen bada hak'uri ne,
kayi laifi kazo kana ta magiyar ayi hak'uri,
to anyi hak'uri kuma dama ai kasan ba'a yin fishi dakai,
ta k'arasa maganar had'i da taja kumatunsa,
" ochhhhh da zafi fa,
ya fad'a yana yin parking,
bata yi mishi magana ba ta fito,
Baba mai gadi yana ganin su ya nufo su jikinshi yana kerrrma,
yana niyyar durk'uwa Aryan yayi saurin mik'a mishi hannu cikin fara'a,
batare da wani kyama ko kyankyami ba,
suka gaisa, sosai Sanah taji dad'i har cikin ranta,
ta kafe shi da ido, deep down kuma tana tunanin halaye da d'abi'un shi,
" hmmm shiyasa akace karka tab'a yankewa mutum hukunci,
ko kayi mishi mummunan zato,
matuk'ar ba mu'ala kayi dashi sosai kasan waye shi ba,
ta fad'a cikin ranta while idanta na kanshi,
iska ya hura mata yana murmushi yace " wannan kallan fa?
Murmushi tayi had'i da cewa " bakomai Hub!,
Baba mai gadi ya kalla yace " muje muci abinci ko?
"A'a ranka ya dad'e a k'oshe nake,
" ok tom, kasan yadda zakayi kakai takarda banki a baka kud'i?
"Eh nasani ai yallab'ai yana aike na wani lokacin,
" ok bawai yace ya juya ya koma cikin motar shi,
ya rubuta mishi check na 5 million naira,
ya dawo ya mik'e mishi yace " Baba ga wannan kaje kaja jari,
miliyan biyar ne, hannunshi na kerrrma ya amsa,
had'i da fashewa da kuka,
cikin tausayawa suka shiga bashi hak'uri suna rarrashinshi,
" nagode! nagode!! nagode sosai,
Allah ya k'ara bud'i da arziki ya inganta rayuwar aurenku,
ya baku zuri'a ta gari,
wacce zasu taimaki musulunci da musulmai da kuma al'umma gaba d'aya,
Allah ya kare ku daga dukkan sharrin masu sharri, daga dukkanin abin k'i,
ya d'ora ku saman mak'iyanku,
duk mai nufinku da mugun nufi Allah ya mayar mishi kanshi,
" amin suka ce cikin matsanancin farin ciki,
ya kalli Sanah yace " kibi mijinki kinji yarinya inayi bari na bari,
dan aljannarki na k'ark'arshin k'afarshi,
dariya suka yi dan sun fahimci ya d'auka su mata da miji ne,
ta amsa da " to in sha Allah,
dakyar suka rabu dashi, dan k'in tafiya yayi ya sasu gaba yana tayi musu ruwan addu'a da godiya.
Zama sukayi kan kujera suna facing juna,
fuskokinsu d'auke da murmushi,
" mai za'a kawo miki K'albi?
" Na ci abinci a makaranta drink kawai za'a kawo man,
" OK but ko a had'o miki da ice cream da shawarma?
" Banda shawarmar dai had'o da ice cream d'in kawai,
hancinta yaja yace " ba'a san cin abinci sai kayan kwad'ayi,
oder sukayi, ba'a jima ba aka kawo musu,
suka fara ci cikin nutsuwa, ido ya kafeta dashi yana kallanta,
da idanta tayi mishi wannan kallan fa " lafiya?
Shima da idanshi ya bata amsar " me kika gani?
" Gani nayi ka kafe ni da ido,
" in ban kalle ki ba wata kike san na kalla?
" Murmushi tayi had'i da jan hancinshi,
tace " a'a sani gaba kayi ta kallo har ka gaji,
" ban tab'a gajiya da kallinki K'albi,
baki ta turo tace " wai yasa idan muna cikin school sai kayi ta faman had'e ma rai,
kana muzurai had'i da ciccin magani,
kayi kamar baka sanni ba,
idanshi kanta ya shafo kumatunta yace " I'm sorry K'albi,
ban san cin amanar aiki na ne,
kuma idan nayi hakan tamkar na naci amanar aiki na ne,
na kuma sab'awa dokar aikin,
kinga idan nayi haka ban yiwa kaina da wasu adalci ba ko?
Ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi tace " I love you,
" if you're truly love me marry me!
I will...! but not now...!
kinga baki san nawa kenan,
" wallahi babu abinda nake so duniya sama dakai sai my Khulud kad'ai,
murmushi yayi yace " har Abbu da Mamu?
" Ai idan irin wannan maganar ba'a saka iyaye,
saboda su daban ne, idan ana dara fidda su ake gefe,
yaji murmushi had'i da d'aukar wayarta,
yayi dialing number shi yaga ta mayar my heartbeat,
d'ayan layin nashi kuma ta saka Hub!,
murmushi yayi yace " dama nace zan saka hannun daya saka da kanshi ya canja,
" me!?
Screen d'in wayar ya nuna mata,
duk sukayi dariya.
A week letter
Tafiya suke cikin mota da yamma around 5:00pm na yamma,
bayan sun gama lectures,
hannunshi rik'e da kwankwanin coke yana sha,
" Hub! Allah na gaji sosai ji nake kamar ana sassara man jikina,
" wayyo K'albi sannu kinji ko muje nayi miki tausa ne?
" Ido ta zaro tace " wai rufa man asiri,
dariya yayi had'i da kurb'ar lemun yace " meye abun zabura haka daga cewa zan miki tausa?
" Hmmmm bakomai, tace " tana mik'a mishi hannu,
lemun ya mik'a mata ta amsa ta kurb'a,
kana ta mik'a mishi tace " wai ga drinks d'innan aje amma kak'i yarda kowa yasha nashi,
dole sai musha d'aya,
" ni dake ba d'aya bane?
Ya fad'a idanshi kanta,
" ai idan akwai abinda yafi d'aya ma mu sune,
" good my K'albi,
ya fad'a yana sake mik'a mata lemun,
wajen amsa lemun ya sub'uce daga hannunshi ya zube mishi a jiki,
ido ta zaro sosai tace " I'm sorry,
ta fad'a kamar zatayi kuka hannunta na k'ok'arin goge mishi wajen daya b'aci,
hannunshi d'aya yasa ya tallafo fuskarta had'i da cewa " karki damu K'albi,
ki daina wahalar gogewa dan bai fita ki bari naje gida na canja kaya kawai,
" gida kuma..!?
" Gidan wa...!?
"Gidan ki mana, ya fad'a yana karya kan motar,
" a'a ni dai please ka fara kai ni gida,
in yaso kai sai ka wuce gidan gaba d'aya,
ganin yadda ta marairace fuska sosai,
yasashi yin dariya sosai yace " tsoran me kike ji?
" Baki ta turo had'i da cewa " ni ban jin tsoran komai, kawai dai hankali na ne yayi gida,
gefen fuskarta ya shafa yana dariya yace " matsoraciya kawai,
" kina tunanin zanyi miki wani abu ne, ko kina ganin zan iya cutar dake..!?
Ya fad'a hankalinshi nakan tuk'in dayake yi,
bata kuma cewa komai ba, har suka k'arasa gidan yayi parking,
bud'e motar yayi ya fito kana ya zagaya b'angarenta ya bud'e mata,
k'in fitowa tayi tace " shiga ka fito,
tuntsewa yayi da dariya sosai ganin yadda lokaci d'aya ta canja,
bai kuma yi mata magana ba ya sungume ta yayi cikin gidan da ita,
mutsu-mutsun direwa bisa k'asa tayi,
amma yak'i bata damar yin hakan,
cikin shagwab'a tace " Allah zanyi maka kuka idan baka aje ni ba,
bayyi mata magana ba sai dariya dayake ta faman yi mata,
ganin yana nufar bedroom d'inshi da ita yasata tsorata sosai,
gabanta ya shiga fad'uwa yana dukan uku-uku,
sosai tsoron da take ciki ya bayya a fuskarta,
shi kuma sosai yake yin dariyarsa kamar me,
saman gadon ya ajeta yana dariya,
dariyarshi ya k'unshe ya soma k'ok'arin cire rigar jikinshi,
cikin rawar murya tace " mezakayi?
Ta fad'a tana k'ifk'ifta ido,
dariya ya kuma sakawa sosai yace " sai baki caucau amma daga cikin muguwar matsoraciya ce,
ba tace mishi komai ba sai idonta data tsare shi dashi,
" ina zuwa yace yana fita,
ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi tana goge gumin daya zubo mata,
sai lokacin ta samu damar kallan bedroom d'in,
gaba d'aya bangon bedroom d'inshi pictures d'inta ne manne da kowanne bango,
anyi wallpaper dasu, a hankali ta mik'e tana bin d'akin da kallo sosai,
har gaban gadon pictures d'inta ne,
kan bedside & wardrobe ko'ina pictures d'inta ne,
tsaye tayi kawai cike da tsantsar mamaki tana bin ko'ina da kallo,
cikin ranta tana mamakin wanne irin mugun so Aryan keyi mata haka kamar hauka,
a hankali kwalla ta fara ciccika mata ido,
tana zubowa saman kwancinta,
saboda tsananin farin ciki,
yana gyara link d'in hannun rigarshi ya shigo,
yace " muje ko iya tsor...........!,
cak ya tsaya ganin hawaye saman fuskarta,
cikin tashin hankali yace " lafiya K'albi..?
Bata yi mishi magana ba , ta ruga da gudu ta fad'a cikin k'irjinshi,
ta rungume shi tsam..!
d'an kwallinta ya ture ya fad'i k'asa,
goshin kanta ya baje saman bayanta,
a hankali ya shiga shafa kanta had'i da d'an bubbuga bayanta,
cikin rawar murya tace " haka kake so na da yawa?
Ta fad'a tana d'agowa daga cikin jikinshi,
hannunshi ya sanya yana goge mata hawayen dake kan kumatunta,
had'i girgiza mata kanshi, cikin sanyin murya yace " karkiyi kuka please,
jikinshi ta k'ara fad'awa ta kanta saman k'irjinshi,
hannunta d'aya yana saman kafad'arshi,
while d'ayan yana bayanshi,
tace " ina sanka sosai Hub!...I really love you,
" idan da gaske ana so na a aure ni mana,
d'an dukan k'irjinshi tayi tana goge kawayenta,
tace " za'a aure ka in sha Allah,
"Yaushe?
" Ba yanzu ba..!
" wai mai yasa duk sanda nace miki muyi aure sai kice not now,
to sai yaushe?
" Sai na gama karatu....!
" what...!?
"Wai kina nufin sai kin gama BUK zamuyi aure!!!?
Ya fad'a yana tsuke fuskarshi sosai,
had'i da rabata da jikin shi,
" eh mana ..! meye naga ka wani zabura?
" Kallanta yayi cikin mamaki yace " anya kina so na kuwa Sanah?
" Sosai ma, meka gani?
"Ya za'ayi kice sai nan da 3yrs zamuyi aure,
" idan mukayi aure na san baka bari muyi planning,
ni kuma ban san haihuwa sai na gama karatu na kar yara su hana ni,
" tab!....! yace idanshi kanta yana yi mata wani irin kallo cikin b'acin rai,
" yanzu yaran ne baki so ko auren ko kuma ni!?
Ya fad'a cikin d'aga murya,
" relax mana Hub!!!
" ke dalla tsaya ban san rainin hankali,
me kike nufi?
" Kina nufin bazamuyi aure ba,
sai dai muyi ta yawo muna soyayya a titi ko me?
" Ko so kike har sharrin shaid'an yayi tasiri kan mu,
shaidan ya samu narasa akan mu,
muje muna aikata zina, bayan ke kanki kin san muddin muka ce zamu d'auki lokaci muna haka dole wata rana sai munyi aika-aika mun aikata abinda zamu rink'a yin danasani har k'arshen rayuwarmu,
zatayi magana yayi saurin d'aga mata hannu yace " meye amfanin soyayya?
Cikin rawar murya da kerrrrrrrma,
tace " aure!!?
saboda ganin yadda gaba d'aya yanayinshi ya canja ya koma mata asalin Moli,
" to mu tamu soyayyar ce bata cancanci aure ba ko me?
Ya fad'a idanshi cikin nata,
" ba wai ina nufin bazamuyi auren bane ba fa,
" to fad'a man ya kike san ayi?
" So nake sai na gama karatu...!
" ok so kike mu aikata zina?
Ido ta zaro had'i da cewa " a'a,
"Ok to so na ne bakiyi?
" A'a ta kuma cewa, idanshi ya runtse da k'arfi,
yace " thanks for the long time,
ya fad'a yana juyawa, cikin tashin hankali ta tari gabanshi tace " I'm sorry Hub!
na yarda muyi auren amma dan Allah ka bari sai bayan 10 months,
in yaso sai ka tura please,
" meyasa Sanah?
" Na lura neman jefa mu a halaka kike yi,
" a'a Allah ba haka bane, Allah na yarda first semester level 3 ayi auren mu,
" kinyi alk'awari?
"Eh Allah nayi, ta fad'a tana komawa cikin k'irjinshi,
hannu yasa ya k'ara matseta sosai da jikinshi,
tace " I love you, yace " I love you too...............!
_TAKE NOTE DEAR:- Duk yadda kike san namiji duk yadda zakuyi romance da shan minti (tab'e-tabe), karki sake ki bari ko kusa yakai hannunshi koda k'asan cibiyarki ne, balle cikin farjinki, har yayi fingering d'inki, karki sake hannunshi ko bakinshi ya tab'a nononki da farjinki, karki sake ki bari alk'alaminsa ya shige ki, wallahi Allah idan kika kabari sai kinyi danasani._
_Ehee idan kunne yaji jiki ya tsira_
MOMYN ZARAH
[7/7, 5:21 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
3⃣9⃣
After 1 year
Bayan shekara d'aya
Haka rayuwa tayi ta tafiya lokaci na wucewa,
kwanaki na gudu, while Sanah an shiga first semester level 3,
yayinda soyayyar su da Sir Moli sai abinda ya k'aru,
sosai suke matuk'ar so da matsanancin k'aunar junansu,
duk ahalin Hard'o family's sun san da zaman Aryan Moli,
kowa ya sanshi sosai dan baya da burki cikin gidan,
cikin ikon Allah,
Ubangiji ya yayewa Aarib matsananciyar soyayyar Sanah,
sakamakon addu'ar daya dage yana yi ba dare ba rana,
dayake Allah maji rok'on bayinsa ne ya amsa rok'onshi,
yanzu babu komai tsakanin shi da ita sai zumunci da 'yan uwantaka.
A b'angaren su Khulud kuwa abun ba'a magana dan sosai Jaddah da sako ta gaba kan rashin haihuwa,
ta musgunawa rauuwarta sosai,
kullum cikin kuka da k'unci take,
duk ta rame ta kod'e saboda damuwa,
damma tana samun sauk'i wajen Hanash,
dan tunda suke dashi bai tab'a nuna mata damuwarshi ba,
amma tasan shima yana cikin damuwa kan rashin haihuwarta,
dan lokuta da dama tasha shigowa d'aki ta iske shi yana kuka,
ko ta jiyo shasshekar kukan shi cikin bathroom,
amma duk da halin dayake ciki yake danne nashi bak'in ciki,
ya rarrashe ta, dan ta samu sukuni,
dan yasha yin fad'a da Jaddan kanta,
while kowa na gidan su yasan matsalar datake ciki,
amma babu yadda suka iya sai dai su tayata da addu'a.
Khulud na zaune cikin parlor taji an banko k'ofar da k'arfi an shigo
a hankali ta d'aga kanta ta kalli bakin k'ofar,
ganin Jaddah yasa gabanta muguwar bugawa,
da saurin ta mik'e jikinta na kerrrma da tsuma,
har k'asa ta duk'a cikin rawar murya tace " sannu da zuwa....!,
wani irin wulak'antaccen kallo ta watsa mata batare data amsa ba,
k'asa ta k'arayi da kanta cikin girmamawa tace " ina yini?
" Ke ni tashi kije ki kira man d'aya munafukin mad'aurin gindin naki,
kin dame ni da wata banzar gaisuwarki,
kanta k'asa cikin rawar murya tace " baya nan,
" a fusace tace " wad'ancan motocin da suke waje fa?
" Eh.! da d'aya ya fita,
kallan banza ta k'ara watsa mata tace " ina yaje?
" Ban sani ba ya dai fita ne kawai bai fad'a man inda zai je ba,
" da naso na same ku gaba d'aya dan ingano ta inda matsalar take kece ko shine,
amma tunda bai nan shikenan ke bari na fara ta kanki,
cikin d'aga murya tace " to nagaji da ga fara sa har yanzu banga k'aho ba,
nagaji da zamanki cikin gidan nan haka,
batare dana ga jikoki na ba,
so nake idan na shigo in fara jiyo hayaniyar yara tun daga waje,
ina jiyo hayaya-hayaya ana guje-guje da bari-bari,
ba wai kullum nazo gida na rink'a ganin fuska d'aya tak ba,
babu abin da kika iya sai dai ki ci kwanta,
idan kinji kashi kije kiyi ko?
Ta fad'a idanta kanta,
a hankali Khulud ta sanya hannu ta goge hawayenta,
" au kuku kike yi?
"Dan munafurci dukanki nayi ko zakinki nayi?
Shiru tayi bata ko d'aga kanta ba,
rankwashi Jaddah tayi mata akanta had'i da cewa " bak'ar munafuka,
wallahi ko kiyi ciki ki haihu ko kuma inyi mishi aure,
imma shanye shi kukayi kuka hanashi k'ara auren,
tunda dama naga alamar ba'ayiwa irinku kishiya,
to ni bazan d'auka ba dan bazan tsaya ina ji ina gani a mayar man da jikana juya ba,
eheee gwara ma kisan halin da kike ciki,
imma bak'in cikin kike man dan kar naga yaran shi to wallahi baki isa ba,
haba ace aure shekara biyu yanzu amma kwata-kwata babu wani motsi,
ko sau d'aya baki tab'a yin b'ari ba,
balle mu shaida kina haihuwa,
kin zauna kullum daga kici ki kwanta shikenan,
to wallahi baki isa ba, imma shi da kanshi bai iya nemo wata,
ni ina iya nemo mishi ehee, fa fad'a tana gyara mayafinta,
" shima zai iske ni ne har gida imma bai je ba zan dawo,
tana k'arasa maganar ta fita fuuuuuu,
bayanta tabi da kallo tana kuka mai cin rai,
saboda ba'a shafe sati d'aya sai Jadda tazo har gida taci mata mutunci san ranta,
bata tuna cewa Allah ke bada haihuwar da kanshi,
bata tunanin bata isa ta bawa kanta ba,
sai wanda ke bayarwa yaga damar bayarwa,
takai 1hr tana ruzgar kuka,
kwata-kwata bata ji tsayawar motar shi,
ko motsin shi ba sai ganinshi tayi kanta,
da sauri ta fara k'ok'arin goge hawayenta dan kar ya gani,
cikin sanyin jiki ya k'arasa inda take zaune,
ya zauna kusa da ita,
cike da tsantsar tausayawa ya kalle ta yace " yauma Jadda tazo ko?
A hankali ta d'ago jajayen idanunta ta kalle shi,
rasa abinda zai ce yasa shi yawo ta jikinshi ya rungume ta,
had'i da k'ok'arin maida kwallar dake shirin zubo mishi,
" wai meyasa Jadda ke yin haka ne?
" Meyasa bazata barsu suji da abinda yake damunsu kad'ai a rayuwarsu ba?
" Meyasa take k'ok'arin k'ara musu damuwa bayan halin bak'in cikin da suke ciki?
" Meyasa take k'ok'arin shiga hurumin Ubangiji ne?
Ya fad'a cikin ranshi,
a hankali ya shiga shafa bayanta zuwa kanta,
cikin sanyin murya yace " kiyi hak'uri komai kika gani daga Ubangijin talik'ai yake,
Allah mai kowa da komai shike da ikon yin komai a yayinda yaso a kuma inda yaso,
ba wayan mu ko dabarar mu bane zai bamu,
sai wanda yayi mu yaga damar bamu,
da zarar yaga damar bamu kum fa ya kum kawai zaice ya kasance,
kuma duk inda jinkiri yake to daga Allah ne,
gaggawace daga shaid'an, muyi addu'a Allah ya bamu,
idan har haihuwar alkhairi ce a gare mu,
idan kuma ba alkhairin bace Allah ya kawo mafita,
k'ank'ame shi ta k'arayi tsam-tsam had'i da fasa kuka mai cin rai,
mai ban tausayi, " kiyi shiru please,
ya fad'a muryar shi na rawa,
a hankali ta d'ago kanta tana kallanshi,
cikin matsanancin kuka tace " dan Allah ka yarda muje asibiti please,
dan mu gano inda matsalar take,
Allah da kanshi yayi cuta ya kuma yi magani,
amma kai kwata-kwata kak'i yarda muje asibiti,
balle a gano inda matsalar take har mu magance,
ta k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka,
jikinshi ya sake mayar da ita yana shafa kanta,
yace " yanzu abinda kike so ayi kenan?
Da sauri ta d'aga mishi kanta had'i da cewa " eh!,
guntun murmushi yayi yana goge mata hawayen,
yace " tashi muje ki shirya muje,
da sauri ta mik'e duk ilahirin jikinta na kerrrrma,
bathroom ya fara kaita ya taimaka mata,
ta wanke fuskata kana suka koma bedroom,
tana k'ok'arin saka doguwar riga,
yace " idan za'ayi scanning kuma fa?
Bata yi mishi magana ba, ta mayar ta d'auko riga da zani na atamfa ta saka,
had'i saka jihab da takalmi,
bata bi takan jaka da wayar ba ta fita,
a harabar Malam Aminu Kano Teaching Hospital yayi parking,
waya ya ciro ya kira Doctor d'in da suka zo gani,
yace su shigo ba matsala yana ciki,
wayar ya mayar cikin aljihunshi,
kana suka fita, koda suka je office d'in sai da suka tsaya bakin k'ofa sukayi knocking aka basu izinin shiga kana suka shiga,
haka nan Khulud taji gabanta na fad'uwa yana dukan uku-uku,
hannu Hanash ya mik'ewa Doctor d'in suka yi musaha,
kana Doctor yace " Bismillah ku zauna ga waje nan,
ya fad'a yana nuna musu sit,
sai da suka zauna kana Doctor ya kalle su fuskarshi d'auke da murmushi yace " Doctor Mujaheed _(Family Doctor d'in su Hanash)_ yayi man bayaninku amma ina san jin k'arin bayani daga gare ku,
a nutse Hanash yayi mishi bayanin komai,
numfasawa Doctor d'in yayi kana yace " shekararku nawa da aure?
" 2yrs kenan, Hanash ya bashi amsa,
a hankali ya mayar da kallanshi ga Khulud yace " zanyi miki wasu tambayoyi kicire kunya ki bani amsa sosai please,
dan su zasu taimake mu mu gano matsalar,
cikin sanyi ta d'aga mishi kai had'i da cewa " in sha Allah, while gabanta baibar fad'uwa ba,
" idan kuna sex kina jin zafi?
Kanta k'asa tace " a'a,
" kina zubar da wani irin ruwa mai launi daban ko wari?
"A'a,
" kafin ki fara period kin kai shekara nawa?
"16yrs,
" kina ciwon mara idan zakiyi period d'in?
"Eh..! ina yi sosai ma,
daga ina kike jin ciwon?
" Gefe cikina sai kuma k'asan mararta,
kuma ina jin ciwon harta wajen bayana da k'ugu na,
shiru yayi yana rubuce-rubuce,
kana ya d'ago kanshi ya kalli Hanash yace " kana tsagiya?
" D'an shiru yayi yana tunani kana yace " meye tsagiya,
" fitar da jini ta al'aurarka,
"a'a, Hanash yace,
" idan kuna sex kana jin zafi?
"A'a,
" kana jin wani lokacin penis d'inka na zafi, ko rad'ad'i ko kaji kamar bata aiki?
"A'a,
" bata baka matsala wajen sex, ko wani lokaci tak'i reaction?
"A'a batayin komai gaskiya,
wata 'yar k'ararrawa ya danna ba'a jima ba nurse ta shigo,
mik'ewa yayi ya nufi wajen scanning dake cikin office d'inshi,
nurse d'in na biye dashi,
" Bismillah,
Hanash da Khulud suka mik'e suka bi bayanshi,
labule yaja ya raba tsakanin gadon da scanner,
kana yacewa nurse d'in ta bud'e marar Khulud ta shafa mata scanning gel,
kamar yadda yace haka tayi,
duk iya scanning d'in da Doctor yayi baiga komai ba,
ajiyar zuciya ya sauke had'i da mik'ewa ya koma kan table d'inshi,
yayi 'yan rubuce-rubuce kana ya mik'ewa nurse
file yace " ki kaita lab,
a d'ebi jikinta, fitsarinta da sperm d'inta,
"amsa tayi kana ta kalli Khulud tace " muje,
Doctor ya kalli Hanash yace " muje ayi maka scanning,
"Ok yace yana mik'ewa,
kamar yadda Doctor baiga komai a wajen Khulud ba haka ma Hanash,
test d'in daya rubuta ayiwa Khulud haka shima ya rubuta mishi,
bayan kamar 15 minutes suka dawo office d'in bayan an gama d'aukar abinda za'a d'auka,
Doctor yace " sai kunyi d'an hak'uri dan result d'in zai kai 2hrs,
sai dai in zakuje ku dawo in kuma zaku jira ne to,
kafin Hanash yayi magana Khulud tayi saurin cewa "ok badamuwa zamu jira a waje,
dan bata jin zata iya tafiya ko'ina batare dataji result d'in ba,
murmushi Doctor yayi yace " badamuwa kuyi zamanku nan cikin office d'in,
dan nima fita zanyi yanzu, ya fad'a yana mik'ewa,
musabaha suka sake yi kana Doctor ya fita,
Hanash ya kalle ta yace " meyasa bazamu je gida mu dawo ba?
" Wallahi ban iya zuwa ko'ina a halin danake ciki yanzu,
dan Allah mu jira d'in kawai, lokaci bashi da wuya yanzu zaka ga har 2hrs d'in tayi,
ta fad'a cikin sanyinta,
murmushi yayi yana jawota jikinshi dayake akan sofa 3 sitter suke.
Cikin nutsuwa yakai kwalbar Dolomia natural mineral water,
(ruwan sayafi kowanne tsada) bakinshi ya kurb'a kana ya ajiye kwalbar saman table,
" Hub please kayi hak'uri mana,
bai kalle ta ba ya cigaba da latsa wayarshi,
a hankali takai hannunta zata shafa kwantacciyar k'asumbar dake kwance saman fuskarshi,
fuska ya tsuke had'i da buge hannunta yace " don't touch me again,
" haba my sweet Aryan na baka hak'uri fa,
Sanah ta fad'a cikin shagwab'a,
a fusace yace " ban hak'ura kuma All........! ,
da sauri ta sanya hannu ta rufe mishi bakinshi,
hannunta ya ture had'i da zafga mata uwar harara yace " ni daina tab'a, tunda na lura dama so kike yi mu lalace,
" please kayi hak'uri mana my Aryan,
hankalinshi ya tattara gaba d'aya ya mayar kanta yace " wai me kike nufi da nine Sanah?
Ido ta zaro tace " Sanah...! fa kace?
" Eh ko ba sunaki Sanah ba?
" Lalle yau ran maza ya b'aci,
bai kalle ta ba ya cigaba da latsa wayarshi,
" kayi hak'uri please..!
haba Hub..! ban sanka da dogon fushi bafa,
idanshi ya kafe ta dashi yana kallanta,
had'i da cizon lips d'inshi,
" please mana, ta fad'a tana shafa kwantaccen gashin kanshi,
" wai me kike san mayar dani ne Sanah?
" Ni na rasa me kike nufi, na rasa gane inda kika dosa,
kwata-kwata ban san me kike nufi da ni ba,
duk lokacin danyi miki maganar aure sai kiyi ta man hanya-hanya,
yanzu fa 1yr to above kenan muna dating,
kodan kinga ban tab'a attempting yin sex dake bane,
" am sorry Hub kayi hak'uri nesa ai tazo kusa,
cikin masifa yace " ban gane nesa tazo kusa ba..!?
Da sauri ta rufe mishi bakinshi tana kallan gefe da gefensu,
" kayi a hankali bamu kad'ai ne a wajen ba,
tsoki ya ja mtswwwww had'i da cewa,
" ni ban iya long relationship, ya fad'a yana mik'ewa,
da sauri itama ta mik'e ta tark gabanshi,
tana k'ok'arin rungume shi, hannunta ya rik'e idanshi cikin nata,
yace " kin san yadda nake daure sha'awata kuwa?
"Kin san taya nake iya yin controlling kai na wasu lokutan?
" Amma ke kwata-kwata baki tausayi na,
baki damu da halin danake shiga wasu lokutan ba,
ya k'arasa maganar yana shiga cikin mota,
tsayawa cak tayi tana kallanta,
motar yayiwa key batare daya kalleta ba,
yayi horn, cikin sanyin jiki ta taka ta shiga motar,
har ya isa k'ofar gidansu bayyi mata magana ba,
sai da ta sauka tana k'ok'arin shiga gida yace " daga yau bamu k'ara yin waya ko magana da juna,
balle ganin juna, duk sanda kika shirya aure na ki sanar dani,
ya fad'a batare daya kalle ta ba,
ta bud'e baki zatayi mishi magana yaja motarshi ya bar wajen,
bayan motar tabi da kallo har ya b'ace mata,
tunda ta koma gida take ta faman kiranshi a waya yana rejecting.
Doctor yayi knocking bakin k'ofar office d'inshi,
Hanash ya bashi izzinin shiga,
" kuyi hak'uri na barku kuna ta zaman jira ko?
"Ah ai ba damuwa yanayin aikin ne haka,
fuskar Doctor d'auke da murmushi ya mik'awa Hanash hannu had'i da cewa " congratulation,
duk gwaje-gwajen da akayi muku bai nuna kuna tare da wata matsala ba,
da nayi tunanin ma ko infection ne amma munyi muku test baku dashi,
ina ganin Allah ne kawai bai kawo lokaci ba,
ayi ta addu'a ana neman zab'in Allah,
murmushin jin dad'i Hanash yayi had'i da yiwa Doctor godiya sosai kana suka fita.
"Kin gani ko dama na fad'a miki babu mai matsala cikin mu Allah ne kawai bai kawo lokaci ba,
cikin sanyin murya tace " ni dai Allah ban yarda da wannan result d'in ba,
dan Allah mu canja wani hospital d'in,
" ban gane baki yarda ba...!?
" Bayan akan idanki akayi komai,
" please mu canja wani hospital d'in?
ta fad'a hawaye na zubo mata,
ido ya k'ura mata na d'an lokaci kana yace " yanzu wanne asibitin kike san muje?
" Muje Nasarawa please....!
batare da yayi mata magana ba yayiwa motar key yaja,
kasancewar a can family Doctor d'in su Hanash yake aiki yasa basu sha wata wahala ba,
akayi musu duk abinda ya dace,
amma still amsar dai d'aya ce basu da matsalar komai,
nan ma k'in yarda Khulud tayi ta marairaice mishi akan dole sai sun canja hospital,
Standard Hospital suka je nan ma akayi musu gwaje-gwaje nan ma ce musu akayi babu mai matsala cikin su,
ranar duk wani babban Hospital dake cikin garin Kano State sai da suka je,
still amma d'aya ake basu lafiyarsu lau basa tare da wata matsala,
basu koma gida ba sai around 12:25am na dare,
sosai Hanash yayi ta rarrashin Khulud yana bata baki,
had'i da k'ara tunatar da ita k'adddara da tawakkali.
A week letter
" Zohal zo ki raka ni gidan Hanash,
a hankali ta d'aga kanta ta saci kallan Mimmee,
cikin dabara Mimmee ta girgiza mata kai alamar a'a,
dan harga Allah babu wanda yake san abinda Jaddah keyiwa Khulud,
cikin sanyin murya tace " bani da lafiya Jaddah,
" baki da lafiya kike rik'e da waya..!?
Ta fad'a cikin rashin yarda da maganar ta,
" eh..! Doctor nake san kira ai,
" hmmm kedai kika sani, ta fad'a tana tab'e baki,
kallanta ta mayar kan Wajnah dake zaune kanta k'asa,
tana chart tunda Jaddah ta shigo bata ko d'aga kanta ba,
" ke..! zo ki raka to..!
yi tayi kamar bata ji abinda take cewa ba,
" Wajnah dake fa nake...!
" Au wai ni..!? me kika ce?
" Cewa nayi ki tashi muje gidan Hanash,
" ni zan raka ki gidan Hanash d'in?
" Dawa..! idan ba ke ba...!?
" Tab..! amma ai kin san ban shiga rayuwarsu da matsalar wasu ko?
" Ni bana d'orawa kai na damuwar wasu,
tawa ma ta isheni, jeki sai kin dawo,
" Wajnah ni kike fad'awa wannan maganar...!?
"Eh lalle ai kin girma kin isa aure kinga k'irjinki ya cika dole kiyi man haka,
ai dama an fad'a idan mace ta girma ta balaga ganin kanta take yi dai-dai da kowa,
to yayi yau bari na gama da wannan kafin na juyo kanku inga uban da ya d'aure muku gindi,
ta fad'a cikin masifa tana fita,
ganinta yasa gaba d'aya drivers d'in guda hud'u suka mik'e,
gudan kar suyi laifi dan sun san halin ta,
" da kuka tashi gaba d'ayanku ne zaku kai ni ko me?
"A'a suka ce,
bata kuma yin magana ba ta shige cikin mota ta zauna,
d'aya daga cikin su yayi saurin bud'e motar ya shiga ya zauna,
dukkan su shiru sukayi babu wanda yace k'ala,
ganin an d'auki lokaci yasa driver cewa " Hajiya ina zamu j.......!?
Bata bari ya k'arasa ba, tace " gidan Hanash,
batare daya kuma yin magana ba yaja motar ya fita,
bata bari ya k'arasa yin parking ba ta bud'e ta fito jikinta sai rawa yake saboda tsabar bala'i,
ganin ba kowa a parlor yasata d'aga murya tace " ke...! ina kike?
Khulud dake kwance saman bed,
jin muryar Jaddah yasata hantsulawa daga kan bed d'in,
jikinta na kerrrrma ta nufi parlor bakinta d'auke da " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
shek'ek'e ta kalle ta had'i cewa,
" uhnnn a kwana a hantse sai manyan mata,
hanshak'iya mandiyya masu kashin gold,
an iya nanik'ewa miji akai har yanzu ana bacci amma ba'a iya d'aukar ciki ba,
kanta k'asa tace " sannu da zuwa, ina wuni..!?
"Au ashe kin san an wunin amma kike lik'e da miji kuke bacci har yanzu?
K'ara sunkuyar da kanta k'asa tayi batare datace komai ba,
" ina ma yadda nazo yanzu yaran Hanash jikoki na ne zasu tare ni da gudu,
amma dayake juya muka auro shiru har yanzu aure shekara biyu,
to yanzu zuwa nayi kuyi man bayani daga inda matsalar take kece ko shine?
" Kece ba mace ba, ko kuma shine ba cikekken namiji ba?
" Idan kuma juya muka auro sai mu sani,
in banda hawaye babu abinda ke fita daga cikin idanun Khulud,
" uhnnn ina jinki bani amsa shi ne baya yi yadda ya kamata ko kuwa?
Hannu tasa ta toshe bakinta gudun kar kukan da take yi ya kwace mata,
ta sake yin wani laifin wajen Jaddah,
" dake nake ina jinki fad'a man dalilin daya hanaki d'aukar ciki?
" Kinyi shiru, yau ban barin gidan nan sai naji amsa ta,
meya hanaki yin ciki, shine ke da matsala ko ke?
Cikin kuka Khulud ta bud'e baki zatayi magana amma kuka ya hanata,
a hasale Jaddah tace " nace ki fad'a man dalilin daya hanaki d'aukar cik....!?
"Allah'n dayake bayarwa ne bai bamu ba,
Hanash ya fad'a yana fitowa daga cikin bedroom,
" ohhhhh ashe kai ma kana ciki?
"Eh..! yace yana mik'ar da Khulud tsaye daga durk'ushen,
" nagodewa Allah dayasa na same ku gaba d'aya,
dan haka kuban amsa yau, danna gaji..!
kan sofa ya zaunar da Khulud kana ya dawo gaban Jaddah ya tsaya yana kallanta ido cikin ido,
yace " uhmmm yi tambayarki me kike san ki sani..?
Cikin muryar kuka Khulud tace " please m.......!!
hannu ya d'aga mata ya dakatar da ita batare daya kalli inda take ba,
" ehhh ina san sanin daga inda matsalar take kai ne baka da cikekkiyar lafiya ko kuma itace juya?
" Kamar ya ban gane ba..!?
Ya fad'a still idanshi cikin nata,
" ina nufin bai ba cikekken namiji mai lafiya bane,
shiyasa baka yin abinda ya kamata ka kakasa yi mata ciki,
ko ko ita ce juya?
" Har yanzu ban gane badai,
" lusarin namiji ne kai baka yin abinda ya kamata ne, shiyasa har yanzu ciki bai shiga ba, ko kuma itace lusarar..!?
Mutun murmushin gefen baki yayi,
a ranshi yana jin inama ba Jaddah ce tayi mishi wannan tambayar ba,
a fili kuma yace " Ubangiji mai kowa mai komai,
mai yin yadda yaso a inda yaso,
wanda yayi saman bakwai da k'asan bakwai,
wanda ya halicci duniya da abinda ke cikinta,
mai bawa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, mai kwacewa daga hannun wani ya bawa wani,
wanda ya dai-daita wuta da k'ank'ara,
wanda ya sama da k'asa, ya kuma rik'e saman,
wanda bai haifa ba, ba a kuma haifashi ba,
wai zartar da hukunci akan kowa,
wanda yake azurta fak'iri ya talauta hamshak'i,
Ubangiji wanda zaice kasance ya kasance Allah mai " Kum fa ya kum,
wanda yayi ni yayi ki yayi Khulud,
wanda ke bada haihuwa shine bai bamu ba,
ya fad'a idanshi tarrr cikin nata,
kame-kame Jaddah ta farayi had'i da cewa " Hanash ni kake ciwa mutunci akan matarka..!?
" Cin mutuci ko gaskiya Jaddah?
" To yayi kyau ka kuma kyauta,
nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,
amma zanje na tadawa Ubanka hankali tunda shi bai isa yayi man musu da gardama ba,
balle ya sani gaba yana zani,
zanje na d'aga mishi hankali ta yadda shima zai d'aga maka naka hankalin,
shi ai baka isa kayi mishi haka ba,
tana k'arasa maganar ta fita fuuuuu,
Jaddah na fita Khulud ta fasa rikitaccen kuka,
bayanta Hanash yabi da kallo had'i da furzar da iska,
a hankali ya nufi Khulud ya zauna kusa da had'i da rungume ta,
batare dayace mata komai na,
sun dad'e a haka kana ya rabata da jikinshi yasa hannushi ya shiga goge mata hawayen ta,
cikin nutsuwa ya mik'e ya koma bedroom ya d'auko wayarshi,
kana ya dawo parlor ya kuma rungume ta yana dialing number family agent d'in su,
tana soma ringing yayi picking,
sai da suka gaisa kana Hanash yace " please zan iya samun visa America cikin kwana biyu?
D'an shiru yayi kana yace " wanne irin visa kake so yallab'ai?
" Ganin Doctor..!,
shiru ya kuka kafin yace " may be zamu iya samu cikin kwana uku,
" please kayi man k'ok'arin na samu d'in,
" haba yallab'ai idan kaga ba'ayi abuba to babu yadda za'ayi ne,
amma komai kuke so za'ayi k'ok'arin yi muku in sha Allah,
yauwa nagode sosai,
" haba yallab'ai meye na godiya kuma?
"Tsakanin mu ai ba godiya duk yiwa kai ne,
yanzu abinda ya rage ka fad'an inda zan karb'i passport d'inka?
" Oh..! Sorry na manta ban fad'a maka ni da Madam zamuyi tafiyar ba,
" amma yallab'ai idan dan wannan matsalar ce mai zai hana ku fara zuwa abuja da Lagos?
" Abuja da Lagos kuma...!?
"Eh akwai manyan asibitoci masu kyau,
wad'anda zasuyi maka tamkar kana American dan akwai asibitin wani ba'indiye daya bud'e Dr Hassan's Hospital iller crescent, 5 Katsina-Ala st Maitama, Abuja,
sannan akwai wani Primus Hospital Indian Hospital,
then..! a Lagos akwai Lagoon Hospital Apapa 8 marine road,
then...! akwai Lagoon Hospital Victoria Island 13 idejo,
sai Nicholas Hospital 7b etim crescent,
kaga wad'annan Hospitals d'in are the best hospital in Nigeria kaje ka gani daga can in baka samu abinda kake so ba,
sai ku wuce kawai ba ma sai kun dawo gida ba,
" Ok tom gobe zamu bi jirgi mu fara zuwa Abuja,
yanzu ma zanyi mana booking a Sheratoon Hotal,
" Allah yasa a dace..!
" Amin ya Allah..!
kana suka kashe wayar, kallansa ya mayar kan Khulud yace " tashi mu shirya kayan mu,
gaba d'aya daga can idan bamu gamsu ba,
sai mu wuce American kawai,
ya fad'a yana mik'a mata hannunshi,
hawayenta ta goge had'i da rik'e hannunshi,
suka shiga ciki.
Washe gari sai da suka biya suka kaiwa Agent d'in pastport d'insu kana suka wuce Abuja,
gaba d'aya hospitals d'in daya fad'a musu dake Abuja babu wanda basu je ba,
amma gwaje-gwajen da akayi musu ba'a gano wata matsala ba,
haka ma a Lagos haka sukayi ta yawon Hospitals amma duk inda suka je still dai amsar d'aya ce,
shine lafiyarsu lau basa tare da wata matsala,
bayan kwana biyu suka d'aga America,
bayan sunyi applied na ganin Doctor,
kuma an basu appointment,
k'arfe 1:43am na agogon America jirginsu yayi landing a America,
a Amsterdam Hotal suka sauka,
washe gari k'arfe 9:00am na safe suka je asibitin,
ba'a wani tsaya b'ata lokaci ba aka shiga duba su,
hmmm kayan company daban dana shago,
Nigeria anyi mana nisan nisa,
domin kayan aikin ma daban suke,
anyiwa su Hanash aune-aune,
da gwaje-gwaje an sanya su cikin machines kala-kala,
tun k'arfe goma na safe ake ta faman duba su,
ba'a gama ba sai 12:27am na dare, kana aka gama komai,
" zaku tafi masaukin ku ne ko kuma kuna san result d'in yau?
" Idan bazai d'auki lokaci ba muna san ji,
"ai yama fito, ku biyo ni, ya fad'a yana nufar cikin office d'inshi,
jikinta a sanyaye gabanta na dukan uku-uku ta mik'e,
ganin yanayinta yasa Hanash rungume cikin jikinshi kana suka bi bayanshi,
" zauna Doctor d'in yace yana nuna musu sit!,
hankalinshi ya tattara gaba d'aya kan Khulud yace " kin tab'a samun hatsari 8yrs back?
Gabanta na fad'uwa tace " a'a,
yace " baki tab'a fad'uwa daga wani waje mai nisa ko bigewa a cikin ki ba?
Sai da gabanta yayi muguwar bugawa kana cikin rawar murya tace " eh na tab'a,
ajiyar zuciya Doctor d'in yayi kana yace " a lokacin kinyi muguwar bugawa sannan abu mai nauyi ya danne miki ciki ko?
Tunowa tayi da lokacin da suke yin game a Roni,
Sanah ta buga mata ball kana ta kuma buge ta da k'afarta ta kuma taka ruwan cikinta da takalmin ball,
" eh tace duk ilahirin jikinta na kerrrrma,
" a lokacin kin suma?
"Eh..!
kuma an kaiki Hospital Doctosr sun duba ki a lokacin?
" Eh..!
sai da ya sake sauke ajiyar zuciya kana yace " I'm sorry daya kasance ni ne zan fad'a miki maganar,
numfashi ya kuma fitarwa kana yace " sakamakon wannan buguwar da kika samu a lokacin bazaki tab'a haihuwa ba har abada,
saboda an fasa miki mahaifa tun kina yarinya kafin ki balaga...................!!!!!!!
MOMYN ZARAH
[7/7, 5:24 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
~DEDICATED TO~
*🌈KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION✍🏻*
_(Sadaukarwa ga gaba d'aya Kainuwa writer's member's kunan cikin raina ban manta daku)_
4⃣0⃣
A matuk'ar razane Hanash yace " what..! ban gane ba?
"Eh...! kamar yadda kaji na fad'a muku haka ne,
bazata tab'a haihuwa ba har abada,
" shine nace maka ban gane ba?
"To yanzu Mr Hanash wanne irin bayani kake san nayi maka kuma?
" Bazata tab'a haihuwa ba kuma take period?
" Eh..! ai cewa nayi mahaifarta ta fashewa,
ba wai cewa nayi bata da mahaifa ba,
tana da mahaifa kamar kowacce mace,
sai dai ita tata mahaifar da ita da babu duk d'aya ne,
saboda tun kan tayi k'arfi (kwari) ta samu matsala,
so bata cigaba da girma tana k'ara k'arfi ba,
yadda take lokacin da abun ya faru haka take har yanzu,
kasan kuma bai yiyiwa mahaifar yarinya 'yar 10yrs kuma fashashshiya ta d'auki ciki har 9 months,
kamar ka d'aura ruwa cikin leda ya fashe ne,
kaga ai still ledar tanan kuma har sauran ruwa yana iya ragewa ciki ma,
to haka ne ya faru da mahaifarta,
mahaifarta bata da gwarin da zata iya d'aukar ciki balle harta d'auki d'a,
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
Allahumma ajirni fi masibat.........!
wata irin gigicacciyar k'ara Khulud ta saki had'i da zube k'asa a sume,
a kid'ime Hanash ya mik'e daga inda yake zaune ya ciccib'eta cikin tashin hankali,
shima da Doctor d'in mik'ewa yayi jikinshi na kerrrrma da tsuma,
kan gadon tura marasa lafiya aka d'orata aka nufi emergency room da ita,
duk iya k'ok'arin da Doctor sukayi amma abin ya gagara dan sun kasa dai-daita numfashinta,
in banda zarya a k'ofar emergency room d'in babu abinda Hanash keyi,
gaba d'aya yama rasa me zayyi,
bai yarda da abinda ake cewa idan damuwa da bak'in ciki sukayiwa mutum yawa bai iya kuku ba,
sai yau, dan wata dauriya Allah ya saukar mishi,
ko kwalla tak'i fito mishi, shi rik'on Allah ma yake inama zayyi kukan dan ya samu sassauci a zuciyarshi.
Kamar daga sama ya jiyo Khulud ta k'ara yin mahaukacin ihuuuu da tsananin k'arfi,
duk asibitin sai da ya amsa cikin tsananin tashin hankali ya danna kai ciki,
duk ilahirin jikinshi kerrrrma yake,
cikin tsuma ya k'arasa gareta had'i da rungume ta tsam cikin jikinshi,
gaba d'aya ta firgice take fita daga cikin hayyacinta,
ta koma cikekkiyar mahaukaciya taburan,
cikin matsanancin kuka tace " wallahi k'arya ne nasan my Sanah bazata tab'a yin abinda zai cutar dani ba,
bazata tab'a yin abinda zai haifar man da matsala ba,
bazata tab'a jefa rayuwata cikin k'unci da uk'uba,
bazata yiwa rayuwa ta illa ta kassara farin ciki na ba,
ka fad'a musu su k'ara duba ni dan Allah.....!
ta k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka,
k'ara matse ta tsam yayi cikin jikinshi,
yana sauke numfashi da sauri da sauri,
jikinta ta zame daga nashi had'i da cire d'an kwallin kanta tayi jifa dashi gefe,
ta sanya hannunta cikin gashinta kanta,
tana yi mishi wani irin kallo while hawaye na zubo mata tace " yanzu bazan tab'a haihuwa ba har abada....!?
" Yanzu shikenan bazan tab'a ganin d'ana na ciki na ba....!?
"Bazan tab'a d'aukar ciki na haihu ba....!?
" Bazan tab'a haihuwar gudan jini ba....!?
" Bazan tab'a ganin kwai ba kenan.....!?
" Bazan tab'a jin yadda mata keji lokacin rainan ciki da haihuwa ba?
" Sai da naji suna bada labari,
bazan tab'a jin da sanin zafin nak'uda da haihuwa ba....!?
" Yanzu da gaske na zama juya maganar Jaddah ta tabbata ni juya ce...!
na shiga uku naga ta kaina yanzu ina zan saka rayuwa ta naji dad'i.....!?
" Nasan shikenan kuma bani da sauran farin ciki har abada...!,
bazan kuma yin walwala da annashuwa ba..!
gefe ta kawar da kanta tace " nasan aure zakayi bazaka tab'a zama da juya ba..!
da sauri yasa hannunshi ya rufe mata baki,
" please kiyi shiru karki yi sab'o .....!
kamar mahaukaciya ta buge hannunshi,
kallanshi tayi ido cikin ido tace " aure zakayi ko...!?
" A'a bazan tab'a yin aure ba nayi miki alk'aw.......!
" a'a nasan Jaddah bazata tab'a kyale ka ka zauna dani ni kad'ai ba,
alhalin bana haihuwa, wallahi nasan sai Jaddah tasaka ka k'ara aure
wayyo na shiga uku ya Rabbi ka d'auki rai na na huta da wannan bak'ar rayuwar mara amfani.....!
bakinta ya rufe mata had'i da cewa " ki nutsu please..!
ya fad'a yana jijjigata,
" mutuwa zanyi Hanash wallahi mutuwa zanyi...!
ta fad'a cikin masifaffan kuka mai d'aga hankalin ma'abocin sauraro,
" aure zakayi nasan dole dole sai ka k'ara aure ...!
" nasan bazaka tab'a cutar kanka ka zauna babu yara ba...!
" nasan yadda kake bala'in san yara Hanash nasan kana san haihuwa sosai...!
" wallahi nasan sai ka k'ara aure,
ta fad'a tana dukan k'irjinshi while gashin kanta yayi buzu-buzu tamkar mahaukaciya,
hannunta ya rik'e cikin nashi cike da tsantsar tausayawa ji yake tamkar yayi ta ihuuuu yana d'iban k'asa yana zubawa kanshi da jikinshi ko ya samu sauk'i da sassauci cikin ranshi da zuciyarshi....!,
" Hanash mutuwa zanyi bazan iya cigaba da rayuwa ba,
dan Allah ka barni na mutu dan na gwammaci mutuwa ta akan rayuwa ta,
ta fad'a tana fad'awa jikinshi cikin matsanancin kuka mai firgita ma'abocin sauraro,
cikin raunananniyar murya yace " bazaki mutu ba Khulud,
in sha Allah muna nan yare har tsufa,
kuma har da mutuwa dan Allah ki kwantar da hankalinki,
karkiyiwa Allah mutulci, baki san me Ubangiji ya b'oye ba,
bamu san dalilin dayasa Allah yayi hakan ba,
Khulud ke ba jahila bace kin san Allah bai tab'a yin abu babu dalili duk abinda kika ga Allah yayi akwai dalilin yinshi,
babu abinda ya kamace mu sai addu'a mu dage muci jarabawar mu,
sai kiga Allah ya b'ullo mana da wata hanyar,
amma idan mukace zamu butulce masa sai ya barmu da azabarsa,
karki ce zakiyi yak'i da ikon Allah,
karki ce zaki shiga hurumin Ubangiji,
karkiyi haka please mu fa musulmai ne,
Allah ya koyar da mu abubuwa dama da zamuyi idan masifa ta fad'a mana,
ko muna cikin bak'in ciki da damuwa,
ki kasance mai yiwa Allah godiya a bisa ni'imarsa sai ya k'ara miki wata,
kiyiwa Allah godiya saboda ya barki da rai da lafiya, kinfi k'arfin abincin dazaki ci ruwan dazaki sha,
suturar da zaki saka, da wajen kwana,
ki godewa Allah dayaba ki komai a rayuwa kika fi k'arfin komai,
babbar ni'imar da Ubangiji yayi miki da yayo ki musulma cikin jinsin bani Adam,
Allah ya barki bai kuma tab'a jarraba imaninki ba,
Allah bai tab'a barin d'an Adam batare da jarabawa ba,
dole sai an jarrabi imanin mu,
ki godewa Allah abisa dukkan ni'imomin dayayi miki,
sab'anin haka kuma ki fad'a cikin fishi da azabarshi,
kamata yayi kiyi ta maimaita " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un a matsayinki na musulma,
dan Allah karki ban kunya Khulud,
kiyi ta maimaita innalillahi wa'inna ilaihirraji'un cikin ranki,
kinji my Khulud?
Hawayenta ta goge had'i da kama sumar kanta ta tufke ta sanya reborn,
cikin nutsuwa ta kalle shi tace " da gaske ne abinda Doctor ya fad'a ko mafarki ne nake yi...!?
Shiru yayi idansu sark'e cikin na juna suna kallan juna ido cikin ido,
hawaye ne suka kuma gangaro mata tace " yanzu da gaske bazan tab'a haihuwa ba har abada...!?
Still bayyi mata magana ba sai kallanta kawai da yake yi,
dan in banda baya san ya karya mata zuciya da babu abinda zai hana shi kukan shima,
" da gaske ni juya ce kenan...!?
Ji yayi zuciyarshi ta karye yana neman saka kuka,
dan haka yayi saurin rungume ta dan bai san taga d'igon hawayenshi,
dan ganin hawayenshi yana iya k'ara rud'a ta ya rikitata,
cikin kunnenta ya rad'a mata " duk abinda na fad'a ki maimaita,
idanta ta lumshe hawaye na cigaba da zubo mata,
batare datace mishi komai ba,
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
Allahumma ajirni fi musibati wa'akluflee khairan min ha,
muryarta na rawa ta maimaita,
ya kuma maimaitawa, itama ta maimaita,
sun dad'e suna maimaita addu'ar,
while tana sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali,
take taji ta nemi gaba d'aya bak'in ciki da damuwarta ta rasa,
lokaci d'aya Allah ya yaye mata k'unci da zafin zuciyar da take ji,
taji ranta yayi mata wasai, a hankali ta zame jikinta daga nashi,
cikin sanyin murya tace " mu koma masaukin mu, zuwa gobe ko jibi sai mu wuce gida,
ta fad'a tana mik'ewa da sauri Hanash ya rik'e ta yace " a'a ki bari sai kin warware kin k'ara samun sauk'i sai mu koma masaukin mu,
murmushin k'arfin hali tayi mishi had'i da cewa " lafiya ta lau babu abinda ke damu na mu tafi kawai,
" Ok to mu koma wajen Doctor d'in muji ko da wani abun da za'a k'ara yi,
" a'a mu tafi kawai ni na yarda da k'addara mai kyau da marar kyau,
ya yarda na amince Allah ne keyin komai shike da ikon yin komai,
wani abu mai tab'a faruwa face da iko da izininshi,
dan haka na d'auki hak'uri da dangana,
idan Allah yayi ina da rabon haihuwa zan haihu idan kuma bani da rabo komai za'ayi ban tab'a haihuwar,
ajiyar zuciya ya sauke cikin ranshi yana tunanin wani irin sanyi hali Allah ya bawa Khulud,
yana jin mutane masu tawakkali da hak'uri amma na Khulud daban ne,
murmushi yayi mata yace " eh amma dai mu koma muji mai zaice mana ko?
" Please Hanash I don't want argue with you,
so dan Allah mu tafi kawai,
langwab'ar da kanshi yayi gefe cikin alamar wasa yace " please mana dear,
d'an murmushi tayi kana tace " ok muje..!,
thanks yace had'i dayi mata light kiss,
" I'm sorry ban so haka ta faru ba,
please karki rik'e ni cikin ranki a matsayin wanda ya fara fad'a miki mummunan labari,
murmushi tayiwa Doctor d'in had'i da cewa " karki damu Doctor hakan Allah ya tsara man tun farko...,
sosai shi kanshi Doctor d'in yayi tsananin mamakin dauriya da juriyar Khulud,
ya kuma jinjina mata had'i da k'ara tausaya mata,
" please Doctor babu abinda za'a iyayi?
" Ko da wata hanyar bazamu iya bi ba...!?
" I'm sorry Hanash amma gaskiya duk inda zakuje cikin duniya kaf abinda za'a fad'a muku kenan,
idan har namiji yana iyayin ciki ya haihu to itama tana iyawa,
idan da zan baku shawara dana ce muku karma ku wahalar da kanku wajen neman magani ko neman wata hanyar dan gaskiya da kamar wuya...!
ajiyar zuciya Hanash ya sauke yana k'ok'arin yin magana tayi saurin cewa " shikenan Doctor mun gode..!
ta fad'a tana mik'ewa,
cikin mutuwar jiki ya mik'e had'i da mik'ewa Doctor hannu had'i da cewa " thank you Doctor...!
cike tsantsar tausayawa yabi bayansu da kallo.
Suna komawa masaukin su ta aje jakarta cikin parlor da hijab d'in ta,
kana ta shige bedroom, kayan ta cire kaya ta fad'a bathroom,
key ta dannawa k'ofar gudun kar Hanash ya biyo ta,
ta zauna saman WC had'i da fasa kuka mai cin rai,
zaune yayi a parlor ya had'a kai da gwiwa cike da tsantsar bak'in ciki,
ji yake tamkar anyi mishi bishara da ranar mutuwarshi,
ganin har wajen 40 minutes bata fito ba,
yasashi mik'ewa ya shiga cikin bedroom d'in,
shashshekar kukanta ya jiyo cikin bathroom,
idanshi ya runtse da k'arfi yana dayasanin zuwanshi America ganin Doctor,
dan ya tabbatar kafin ta koma normal za'a d'au lokaci kuma koda ta koma ma lokaci zuwa lokaci sai ta rink'a shiga damuwa,
idanshi da suka gama canja kala zuwa pure red ya bud'e kana ya nufi bathroom d'in,
murd'a handle d'in yayi yaji shi a rufe,
jin ya tab'a k'ofar yasata saurin mik'ewa ta kunna shower ta sakarwa kanta,
" bud'e yace yana knocking k'ofar,
" ina wankan zan bud'e..!?
" Eh....! shiyasa nace ki bud'e ai,
" wanka nake yi fa..!
" wankan ne kusan 1hr..!?
" Yi hak'uri yanzu zan fito..!
" a'a ki bud'e man na shigo muyi tare..!
saboda bata san yawan magana yasata bud'e mishi k'ofar batare datayi mishi magana ba,
a hankali ya taka ya shiga direct inda take ya nufa yana cire kayan jikinshi,
ta bayanta ya rumgumo ta ya had'a jikinta da nashi, dukkan su naked,
ta k'ark'ashin cikinta ya zagayo da hannunshi yana shafata gami da yin sama da hannunshi har zuwa kan boobs d'inta while shower na zuba saman su,
hab'arshi ya d'ora saman kafad'arta yana wasa da boobs d'inta,
had'i da cewa " muyi wankan tare,
ya fad'a yana k'ok'arin danne damuwa da bak'in cikin dayake ciki,
saboda ya kwantar mata da hankalinta ya kuma kawar mata da damuwarta,
murmushi tayi tace " aini na gama ta fad'a tana mik'a hannu zata d'auki towel,
hannunta dake k'ok'arin rik'e towel d'in ya rik'e yace " ayi man to ni ma,
" sallah zanyi..!
ganin yanayinta yasa bai k'ara yin magana ba,
ya sake ta gudun karya takura mata,
duk ilahirin jikinta kerrrrma da tsuma yake,
nannauyan fumfashi ya sauke had'i da bin bayanta,
batare data saka kaya ba tayi zaune saman bed,
a hankali ya zauna kusa da ita,
had'i da jawo ta jikinshi ya kwantar da kanta saman k'irjinshi,
yace " tunda nake dake baki tab'a ban labarin kin tab'a samun accident ba,
muryarta na rawa tace " ba accident bane..!
" to meye..!?
Ya fad'a yana runtse idanshi,
kana san kaji ne...!?
"Eh...!,
muryarta na rawa tace " kana san kasan abinda ya maida matarka juya wacce bazata tab'a haihuwa har abada ba ko...!?
Ta fad'a kuka na k'ok'arin kufce mata,
" ke ba juya bace Khulud dan Allah ne kad'ai yasan mai zai faru gobe,
" idan ba juya bace mecece ni...!?
Kanta ya shafa gami da cewa " matar Hanash uwar gidanshi kuma amaryarshi,
murmushin yak'e tayi wanda yafi kuka ciwo danta tabbatarwa kanta koda ace babu Jaddah sai Hanash ya k'ara aure,
dan ta san saboda ita bai tab'a yin rayuwa babu yara,
jin tayi shiru yasashi cewa " fad'a man meya faru meye sanadi da dalili....!?
Muryarta can k'asan mak'ogwaro tace " my Sanah...!,
cikin tsantsar mamaki yace " Sanah kuma..!?
"Eh my Sanah ce sanadi kuma dalilin faruwan hakan,
ta fad'a tana fashewa da matsanancin kuka,
kana ta shiga bashi labarin abinda yaru tun daga farko har k'arshe....!,
cikin jahilin kuka tace " nasan my Sanah bata san hakan zai faruwa ba,
nasan bazata tab'a iya cutar da ni ko tayi abinda zai cutar da ni ba,
nasan wacece my Sanah nafi kowa saninta,
bata da mugunta balle bak'in ciki tana da sauk'in kai batta dai da tsiwa,
nasan batayi hakan danta illata rayuwata ba,
asalima nina matsa mata muka je boarding school dan kwata-kwata bata k'aunar boarding school,
kuma nina matsa mata muka shiga game club & team,
sannan ranar da abun zai faru k'in yin ball d'in tayi dan sai da tace man jikinta yana bata wani abu,
ita baza tayi ball ba yau, amma na matsa mata dole dole sai tayi,
wallahi nasan ita kanta da tasan hakan zata faru dani sai ta gwammaci mutuwarta saboda nasan yadda take matuk'ar so da k'auna ta,
zan iya cewa Sanah tafi kowa so na a duk fad'in duniya,
ta k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka,
tunda ta fara bashi labarin ya kafe ta da daradaran idanshi,
shiru kawai yayi yana jinta amma Allah kad'ai yasan meke cikin zuciyarshi,
tunda Hanash yake a duniya bai tab'a jin tsantsar tsanar Sanah irin yau ba,
ji yake da za'a bashi free life babu ran wanda zai d'auka daya wuce nata,
bai tab'a sanin ashe da a baya ba k'inta yake yi ba sai yanzu da abinnan ya faru,
in banda rawa, kerrrrma da tsuma babu abinda jikinshi keyi,
ta ko'ina gumi keto mishi yake yi,
" tab ashe dama Sanah ce silar faruwan hakan...!?
"Itace tayi sanadiyyar rashin ganin d'anshi gudan jininshi a duniya..!?
" Duk matsololin dake faruwa ashe dama itace ta haifar da komai...!?
Ya fad'a cikin ranshi,
a hankali ya runtse idanshi da suka gama zama jajaye tamkar gauta da k'arfi,
saboda tsabar bak'in ciki bai san sanda ya fashe da fitinannan kuka ba,
had'i da rungume ta cikin k'irjinshi,
itama kukan take yi sosai, tamkar ransu zai fita haka suka rink'a kuka,
take suka ji gaba d'aya k'asar ta fice musu fit a ransu,
bayyi mata magana ba ya mik'e ya hau had'a musu kaya while yana kukan,
a daren yayi musu booking fly,
washe gari suka yo Nigeria cike tarin damuwa,
duk sun koma shiru-shiru dasu,
dama abinka da dukkan su ba maganarce ta dame su ba,
a Aminu Kano International Airport jirginsu yayi landing,
kasancewar bai sanar da driver dawowarsu ba yasashi,
d'aukar taxi zuwa gida,suna zaune a bayan motar ta d'ora kanta saman k'irjinshi yana shafa kanta,
cikin sanyin murya tace " please ka kai ni gida..!
kallanta yayi yace " wanne gidan...!?
"Gida mana, ta fad'a kamar bata san yin maganar,
" ai dama gidan zamuje ya fad'a yana cibaga da shafa kanta,
" no ba nan ba, gidan Mamu da Abbu..!
" nan kike san zuwa..!?
"Eh...!, tace a tak'aice, ido ya k'ura mata kana yace " please mu bar maganar nan tsakanin mu ban san 'yan gidan mu suji,
dan ban san Jaddah taji tazo ta k'ara tada mana hankali ta k'ara mana damuwa bayan wanda muke ciki...!,
" hmmm ai ko an b'oyewa 'yan gidanku ni dole na sanar da iyaye na halin da ake ciki,
ko ba komai sa tayani da addu'a kuma ma ai ya zama dole su san meke faruwa,
kuma suma su Mimmee koda an b'oye musu baki yak'i furta musu zasu gani a aikace...!,
bai kuma yi mata magana ba , har suka k'arasa gidan,
kayansu ya sauke daga cikin motar kana ya biya mai taxi d'in,
direct part d'in Mamu suka shiga,
a parlor suka iske Mamu da Abbu, Zafran, Ziyad da Aarib da Idrak zaune suna cin abincin saman dinning table,
dayake wani lokacin daga su har matansu part d'in Mamu ko Juju suke cin abinci,
wani lokacin ma har Dide da Juju duk had'uwa akeyi aci abincin tare gaba d'aya,
da sallama suka shiga parlor'n,
da sauri Mamu ta mik'e had'i da cewa " yau muna da manyan ba........!
bata k'arasa ba Khulud ta nufe ta had'i da fad'awa jikinta ta fasa rikitaccen kuka,
gaba d'aya parlor'n akayi shiru tsit tare da zubawa Khulud da Hanash ido,
cikin tashin hankali Mamu ta d'ago ta tace " lafiya Khulud..! meke faruwa...!?
In banda kuka babu abinda Khulud keyi,
cikin sanyin jiki Hanash ya nufi Abbu ya gaida shi kana suka gaisa dasu Zafran,
" Hanash lafiya kuwa..!?
Shiru yayi had'i da k'ok'arin danne abinda yake ji cikin ranshi,
" Zafran kira man Dide da Juju..!
amma karka fad'a musu Khulud ce tazo dan suna iya k'in zuwa...!,
cikin nutsuwa ya mik'e ya tafi kiran Juju da Dide,
cikin sa'a ya iske su cikin parlor,
sak'on Abbu Zafran ya isar musu,
da sauri Dide ya mik'e yana tambayar " lafiya Zafran..!?
"Nima ban sani ba, ya daice na kira ku yanzu,
jikinshi na rawa yabi bayan Zafran,
cikin sanyin jiki Juju ta mik'e dan takai 2days gabanta na yawan fad'uwa had'i da dukan uku-uku,
tare Zafran da Dide , Juju suka shiga parlor'n while duk ilahirin jikinsu na kerrrrma,
" lafiya...!?
Yace ganin kowa a parlor'n,
yana bin kowa da kallo,
idan Juju nakan Khulud danta tabbatar akwai abinda ya faru,
saboda jikinta ya dad'e yana bata wani abun,
kafad'ar Khulud Mamu ta girgiza had'i da cewa " kiyi magana mana Khulud,
ki fad'a mana abinda ke faruwa kin d'agawa kowa hankali..!
ta fad'a muryarta na rawa,
cikin mahaukacin kuka Khulud tace " Mamu na shiga uku...!,
duk wanda ke wajen sai da gabanshi ya yanke ya fad'i,
" Mamu bazan tab'a haihuwa har abada ba,
bazan tab'a ganin d'an ciki na ba,
cikin rashin fahimta Mamu tace " kamar ya..!?
" Mamu bazan haihu ba..!,
kallan Hanash Abbu yayi yace " Hanash meke faruwa ne..!?
Cikin nutsuwa muryarshi na creaking ya fad'a musu komai da komai,
ya sanar dasu abinda ke faruwa,
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
Allahumma ajirni fi musibati wa'akluflee khairan min ha,
Lahaula walak'uuwata illabillah,
La'ilaha illallahu Muhammad Rasulillahi (S.A.W.),
kowa a parlor'n da irin salatin da addu'ar da yake yi,
kuka Mamu ta fasa had'i da rungume Khulud suka cigaba da kukan,
aka rasa mai rarrashin wani, duk kara da kawaicin Hard'o family's ranar kawar da ita gefe sukayi,
sosai Juju ma ta sanya kuka,
da sauri Aarib ya fita ya kira Nisah,Gahez,Danish da Erum had'i dasu Hallan,
kowa da kowa aka hallara cikin parlor'n ana ta jimami masu kuka nayi masu jimamjin abun nayi,
Dide da Abbu kuwa sandarewa sukayi a tsaye dukkansu sai share gumi sukeyi,
bakinsu d'auke da addu'a, sosai Hallan ta tausayawa Khulud,
dan itama kuka tayi sosai,
cikin kuka Khulud tace " ina my Sanah..!?
" Tana makaranta..!
" dan girman Allah kar wanda ya fad'a mata abinda ke faruwa,
dan Allah karkuce mata saboda ball d'in data buga man a Roni ne sanadi dan Allah,
dan nasan saita fini shiga tashin hankali da damuwa,
wani irin kallan bak'in ciki da takaici Hanash yayi mata " ke da kike da matsalar ma aka fad'a maki balle wata banza,
ya fad'a cikin ranshi,
" dan Allah ko a fuska kar wanda ya nuna mata wani abu ya faru please dan Allah...!
ta fad'a cikin matsanancin kuka had'i da had'e hannuwanta alamar rok'o,
dan Allah ku taimake ni karku fad'awa my Sanah wannan magan.........!!
" meye kike cewa kar'a fad'a man Sanah ta fad'a tana shigowa parlor'n,
ganin idan Khulud yayi masifar yin jajir kuma tana kuka lokacin data shigo tana rusa uban kuka yasa Sanah sakin hand bag d'inta,
ta nufe ta da sauri, kwata-kwata bata lura da kowa dake parlor'n ba,
hannunta ta d'ora saman kafad'ar Khulud tace " lafiya my Ulud meke faruwa....!?
Ta fad'a muryarta na tsananin rawa,
da sauri Khulud ta goge hawayenta had'i da k'ak'aro murmushin k'arfin hali tace " babu komai my Sanah,
har kin dawo ne..!?
Cikin rawar murya Sanah tace " my Ulud dan Allah fad'an man abinda ke faruwa please,
wallahi tunda na kanki kina kuka kuma kina cewa kar'a fad'a man abinda ke faruwa nasan akwai wani abu,
san Allah ki fad'a man, ko kowa zai b'oye man wani abu nasan ke bazaki tab'a b'oye man ba,
dan bai kamata ki b'oye man ba,
" bakomai Khulud tace tana juyawa,
a fusace Sanah tasa hannu ya juyo da ita had'i da cewa " ban gane babu komai ba...!?
" Kinga please ki........!
bata k'arasa maganar ba saboda idanta daya sauka akan gaba d'aya Hard'o family's dake cikin parlor'n,
kuma harda kakaninsu, da iyayensu, then yayansu, da matansu,
kallan Juju tayi taga tana kuka,
a hankali ta fara bin gaba d'ayansu da kallo still Mamu ma kukan take yi,
Idanuwan Hanash sunyi ja sosai,
then Abbu da Dide sai gumi suke yi,
ga Hallan na kuka, Yayyansu kuwa kallo d'aya zakayi musu kasan suna cikin tsantsar tashin hankali,
hakan ne ya tabbatarwa da Sanah akwai babban abinda ke faruwa,
cikin tension ta mayar da kallanta kan Khulud tace " please my Khulud meke faruwa..!?
Ta fad'a muryarta na rawa,
" bakomai muje kiyi wanka ta fad'a tana rik'e hannunta,
Hanash dake zaune tsantsar mamaki ne ya kashe shi,
a fusace Sanah ta fusge hannunta,
ta mayar da kallanta ga jama'ar dake parlor'n tace " dan Allah ku fad'a man abinda ke faruwa mana,
kai Khulud ta girgiza musu alamar a'a,
kasancewar Sanah ta juya mata baya,
durk'ushewa Sanah had'i ds fasa rikitaccen kuka,
tana cewa " dan Allah ku fad'a man abinda ke faruwa,
ganin babu wanda yako kalle ta yasata mik'ewa ta nufi Khulud ta d'ora hannunta saman kafad'ar ta ta shiga jijjigata da k'arfi tace " nace ki fad'a man abinda ke faruwa...!
Tassssss!! kauuuuuuuuu Mamu ta maka mata gigitattun marika guda biyu,
cikin fad'a da kuka Mamu tace " bayan kin cuce ta kin illata mata rayuwa kashe ta kike san yi...!?
Cikin tashin hankali Khulud tayi saurin nufar Mamu tana cewa " a'a please Mamu no! no!! dan Allah,
a matuk'ar rud'e Sanah ta kalli Mamu had'i da maimaita kalamanta " bayan kin cuceta kin illata mata rayuwa kashe ta kike san yi,
shiru tayi tana tunanin wanda ta cuta ta kuma illata mishi rayuwa,
cikin ranta tace " mean KHULUD!!!,
da sauri ta nufi Mamu cikin tashin hankali tace " Mamu meke faruwa fad'an me menayiwa My Ulud..!?
" A'a please Mamu karki fad'a mata dan Allah, Khulud ta fad'a tana kuka,
itama Sanah tana kuka tace " please Mamu ki fad'a man,
cikin kuka Mamu ta kalli Khulud tace " komai daran dad'ewa dole wata rana Sanah zata sani,
da'a bari sai gaba ta sani lokacin abin ya lafa,
kema kin fara mantawa da abun cikin ranki,
azo a kuma tashi a dawo maki dashi sabo gwara a fad'a mata a taru ayi jinya lokaci d'aya
gaba d'aya,
tunda Mamu ta fara magana Khulud ke girgiza mata kai tana cewa" no! no! no please Mamu,
Mamu kallanta ta mayar ga Sanah kana ta fad'a mata abinda ke faruwa,
bata b'oye mata komai ba,tun daga farko har k'arshe ta fad'a mata komai tasssss.............!
MOMYN ZARAH
[7/7, 5:31 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
~DEDICATED TO~
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
```(GARKUWAR JIDDARH)```
4⃣1⃣
Tashin hankali wanda ba'a sa maka rana....!,
ji tayi tamkar an buga mata gudumar k'arfe cikin kanta,
dan wata irin k'ara taji " gannnnnnn...!,
cikin k'ok'on kanta, take ji da ganinta sukayi d'aukewar wucin gadi,
zuciyarta tayi bak'i k'irin mak'ogwaranta ya bushe rak'ayau,
k'irjinta ya soma yi mata zafi yana soya had'i da tuk'uk'in bak'in ciki,
sakwaf jiki ba kwari Sanah ta zame k'asa saman tails tayi zaman dirshan,
komai tsaya mata cak yayi, brain d'inta tayi hooking,
ta daina ji da ganin komai, ta d'auki tsayin lokaci a haka,
cikin kuka Khulud ta durk'usa gabanta,
gami da sanya hannunta tana jijjiga ta tare da kiran sunnata,
" Sanah...! Sanah..!
wani irin kallo Sanah keyiwa Khulud tamkar mai tab'in hankali,
bakinta na rawa tace " na cuci kai na,
bazan tab'a yafewa kai na ba,
hannu da k'afarta ta kalla had'i da cewa " ni da hannu na da k'afarta, da kai na illata my Ulud,
lalle *_RASHIN SANI...!_* yafi dare duhu,
ta fad'a tana kallan Khulud,
kamar zararriya tayi zumbur ta mik'e had'i sakin tijararran kuku mai cin rai,
gami da d'ora hannunta a ka tana ihuuun kuka,
tamkar wacce aka cewa uwarta, ubanta dama ahalinta gaba d'aya sun mutu,
sosai take kukan tana ihuuuu had'i da dukan kanta,
" wayyo na shiga uku na lallace,
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
wayyo Allah na ni Sanah wayyo rayuwa ta,
ganin yadda take ihuuu tana buge-buge yasa Aarib da Zafran saurin mik'ewa suka rik'e ta,
amma duk da sun rik'eta bata daina ihunnn da turje-turje ba,
sosai ta rink'a kokowar kwacewe tana ihuuuu,
" dan Allah ku barni na mutu ku barni na kashe kai na,
wallahi koda na rayu bazan tab'a rayuwa cikin farin ciki da jin dad'in duniya ba,
zan rayune cikin k'unci da k'unar rai,
ta fad'a tana kukan, sosai itama Khulud take kukan had'i da durk'ushewa a k'asa,
duk ilahirin jikinta kerrrrma da tsuma yake,
gashin kanta yayi buzu-buzu ta koma mahaukaciya tuburan muraran,
cikin kuka Khulud ta mik'e ta nufi inda Sanah keta saman yunk'oran kwacewa,
rungumeta tsam Khulud tayi a jikinta,
tun tana k'ok'arin kwacewa Khulud tak'i bata damar hakan ta rik'e ta gammm,
har ta gaji ta saki jikinta cikin na Khulud itama ta runngume dukkansu suna kuka,
cike da tsantsar bak'in ciki abin tausayi...!
Duk wanda ke wajen sai da yaji zuciyarshi ta karye,
" kiyi hak'uri my Ulud wallahi ban tab'a sanin hakan zata faru ba..!
" bani da masaniya, wallahi bada gayya nayi miki hakan ba,
ban san hakan zata faru ba, dana sani kin san ban tab'a yi miki haka,
dan Allah kiyi hak'uri my Ulud,
ta fad'a cikin matsanancin kuka,
" bakomai my Sanah nafi kowa sanin haka a duniya,
nasan bazaki tab'a yin abinda zai cutar da ni ba,
please ki bar maganar abinda zai faru ya rigada ya faru,
bamu san abinda abinda ya b'oye ba,
bamu san manufar Ubangiji nayin hakan ba,
sai dai muyi ta addu'a,
ta fad'a tana goge mata hawayen dake kan fuskarta,
" mai yasa ni abin bai fad'a kai ba...!?
" Mai yasa ni Allah bai jarrabe ni ba...!?
" Mai yasa ni k'addarar da jarabawar basu fad'a man instead of you ba...!?
" Mai yasa sai ke abin ya fad'a kanki...!?
" Mai yasa duk tarin students d'in dake wajen abun bai same su ba sai mu my Ulud...!?
" Why always us, why..! why...! my Ulud...!?
Ta fad'a cikin matsanancin kuka mai cin zuciya,
murmushi k'arfin hali Khulud tayi tana k'ok'arin danne damuwarta,
tace " karkice haka please, karkiyi sab'o mana, su sauran students d'in kin san kalar tasu jarabawar...!?
Cike da tsantsar tausayawa Dide ya rungume su had'i da shafa kansu,
cikin nutsuwa ya zame su daga cikin jikin shi gami dayin gyaran murya,
yace " wannan abu daya faru babu ruwan Sanah,
ba kuma itace ta d'orawa Khulud ciwo ba, ba itace ta hana Khulud haihuwa ba,
domin lokacin da akayi abun dukkan su suna yara k'anana,
a cikin su babu wanda ya haura shekara goma,
lokacin babu mai cikekken hankali ko wayo,
suna cikin d'anyar k'uruciya, ko ita Khulud d'in ce Allah ya k'addara tana iyayiwa Sanah haka,
idan ma da sanadi ko k'arar kwana tana iya mutuwa,
mu ahalinmu (Hard'o families) mun san k'addara, dangana, tawakkali da kuma hak'uri,
idan abu ya same mu bamu tab'a yin blaming wani muce shine sila,
domin muna da tauhidi, had'i da ilimi dai-dai gwargwado,
jahili ko mushiriki shine idan abu ya same shi bazai danganta al'amari ga Allah ba,
sai ya danganta abun ga wanin Allah,
bayan kowa yasan dai-dai da kwayar zarra bata da ikon motsawa face sai da izinin Ubangijin al'arshe,
tun farko Allah ya riga da ya tsara haka a cikin k'addarar Khulud,
babu kuma wanda ya isa ya kankare hakan daga cikin littafin k'addarar ta,
abinda ya kamacemu anan shine mu taya ta da addu'a bawai mu tsaya muna jimami ba,
idan rashin haihuwar shine alkhairi da kwanciyar hankaki a gare ta fa?
" Yaran yanzu wasu da haihuwar su gwara babu,
sosai Dide yayi musu nasiha mai ratsa jiki da ruhi gami da zuciya,
wanda har ita kanta Khulud da Sanah suka ji ransu da zuciyoyinsu sunyi musu d'an sanyi,
cikin sanyin jiki Sanah taje gaban Hanash ta duk'a while hawaye bai bar zuba daga cikin idonta ba,
tace " I'm sorry Brother kayi hak'uri nasan kaima na sanya ka cikin tarin bak'in ciki da takaici had'i da damuwa,
nasan zuciyarka tayi maka k'unci, zafi gami da rad'ad'i duk a dalilina,
please for gv me, I promise you nima bazan tab'a haihuwa a rayuwa ta ba,
ta fad'a cikin kuka,
take Hanash ya ji jikinshi yayi mugun yin sanyi,
zuciyarshi tayi sanyi, lokaci d'aya ya nemi duk wata k'una da rad'ad'in dayake ji akanta ya rasa,
karo na farko da yaji tayi abinda ya burgeshi,
cikin nutsuwa yayi mata murmushi tare da cewa " ba laifinki bane haka Allah ya tsara tun farko,
tun kan a haliccin duniya da abinda ke cikinta,
" thank you..!, thank you so much,
Mamu ta rungume Khulud tana share hawaye,
a hankali Khulud ta d'ago kanta had'i da mik'awa Sanah hannu alamar ta tazo,
jikinta na rawa ta mik'e ta fad'a jikin Khulud da Mamu,
dakyar Mamu ta lallab'i Khulud da Sanah suka ci abinci,
haka ma Hanash, daya tashi tafiya gida Khulud cewa tayi bata binshi ya barta anan,
dan tana san su d'eb'ewa juna kewa da damuwar da suke ciki..!
murmushi kawai yayi musu kana yayi tafiyarshi ya barta nan da sunan after 3days zata koma gida,
cikin ikon Allah da k'ok'arin Mamu, Juju Abbu da Dide suka fara mantawa da abun,
haka ma Halan ta dake tana kawar musu da abun daga cikin ransu,
aka kuma dage dayi musu addu'a da rok'on Allah akan Allah ya mantar dasu,
dayake Allah maji rok'on bayinsa ne ya amshi addu'arsu,
yasa suka manta suka shiga harkokin gabansu
yayinda yayyansu ma ba'a barsu a baya ba, kullum cikin d'aukar su suke yi suna fita dasu yawo,
sai da Khulud tayi 1 week kana ta koma gidanta.
2 weeks later
Tayi ta faman kiran wayarshi harta gaji, baya picking,
haka ma ko text ta tura mishi bayyi mata reply sosai hankalinta yayi mugun tashi,
haka ma a makaranta baya bari su had'u ko office d'inshi taje bai barinta ta shiga,
haka zatayi ta jiranshi bakin k'ofa amma yak'i bud'ewa sai ta gaji da jiranshi ta tafi,
kana ya bud'e,
yau kasancewar Saturday ce basu da lectures sosai,
da wuri suka gama, tun around 1:50pm na rana suka fito,
suna fitowa ta nufi office d'inshi directly,
batayi knocking ta rab'e daga gefe yadda bazai ganta ba,
tana jiran MD ya fito saboda taga sanda ya shiga,
batafi 10 minutes tana jira ba taji MD na cewa " ok to shikenan ba damuwa sai mun had'u goben,
da sauri ta fito daga inda take lab'e taje jikin k'ofar ta tsaya,
dai-dai lokacin MD ya fito, ganinta tana k'ok'arin shiga yasa MD bai rufe k'ofar ba ya fito ita kuma ta shiga,
kishingid'e ta same shi saman sofa idanshi lumshe jikinshi sanye da cot sai dai ya cire ta saman ya rataye ta,
daga saman bottles d'in gaban rigarshi b'alle kwantaccen gashin k'irjinshi ya fito luf-luf dashi abun sha'awa,
kwata-kwata bai san ta shigo ba, saboda lokacin da MD ya fita ta shigo,
so koda yaji motsin k'ofa ya d'auka na fitar MD ne,
ta d'auki tsayin lokaci tana kallanshi,
kafin ta taka zuwa inda yake ta zauna gefenshi,
a hankali ta sanya hannunta saman fuskarshi tana shafa sajenshi,
da sauri ya bud'e idanshi a d'an tsorace,
murmushi tayi mishi tace " na baka tsoro ko..!?
Sosai yayi murtuk da fuskarshi ya tsuke face, had'i da cewa " waya baki izinin shigo man office kai tsaye..!?
" Yadda akayi na shiga cikin zuciyarka kai tsaye batare daka sani ba, ka kuma shiga cikin tawa zuciyar batare da dana sani ba, ta haka na shigo,
ta fad'a hannunta saman face d'inshi,
hannunta ya ture had'i da nuna mata k'ofa yace " get out..!
" wai meyasa kake haka ne..!?
" Nafa baka hak'uri, please ka hak'ura mana,
" tashi ki fita, ban san magana dake please...!
bakinta ta rik'e had'i da cewa " nashiga uku yau Sir Moli ya kure ni wai bai san magana dani,
ta fad'a in a funny way,
" yes..! I said it again ban san magana dake get out,
" waii! in bi ina inga haske idan ka kore ni...!?
Ta fad'a tana k'ok'arin cusa hannunta cikin k'irjinshi,
da sauri ya rik'e hannun dan ya lura neman burkita mishi lissafi take yi,
" uhmmm idan na kula neman lalata ni kike yi, so kike yi ki lalata man tarbiyyarta,
shiyasa kika k'i yarda muyi auren ko..!?
Sosai abin ya bata dariya " wai neman lalata shi take yi ,
"Eh so kike yi ki iskanta ni ki...!,
" ok haka kace ..!?
"Eh...! hak.....!
jin ta had'e bakinsu yasashi yin shiru dole, had'i da zaro idanshi waje,
sai da ta tsotsi bakinshi sosai hana ta saki bakin,
ta d'ago ta kalle shi tace " uhmmm na lalata kan yanzu ko da saura....!?
"Ah inaga dai da saura..! ya fad'a yana sa hannunshi ya zame d'an kwalinta had'i da cire reborn d'in data d'aure gashinta dashi,
ya cusa hannunshi cikin gashin kanta,
ya karkata kanta had'i da had'e bakinsu,
idanuwansu duka lumshe duka suna sauke numfashi da sauri da sauri,
ta k'asa ya zura hannunshi cikin rigarta yana shafa bayanta,
while suna tsotsar bakin juna cikin shauk'i,
a hankali ya zagayo da hannunshi cikinta,
yana shafa cikinta da cibiyarta,
cikin dabara ya fara yin sama da hannunshi yana nufar boobs d'inta,
da sauri ta zame bakinta daga nashi had'i da saurin mik'ewa ta koma jikin bango ta jingina,
idanta lumshe tana fitar da numfashi a gaggauce,
ganin yadda k'irjinta ke yin sama da k'asa ya k'ara d'imauta shi,
a hankali ya mik'e ya nufi ta hannunshi ya saka ya dafe bangon ya sanya ta tsakiyarshi,
had'i da zuba matata jajayen idanuwanshi,
cikin salo yasa k'irjinshi saman nata,
ya matse ta da jikinshi sosai da bangon yadda bazata iya kwacewa ba,
sumar kanta data zubo ta rufe mata fuska ya sanya hannunshi ya mayar da ita baya,
had'i da zubawa k'irjinta saman boobs d'inta ido,
idanshi ya runtse da k'arfi kana ya sunkuyo da kanshi saitin kunnenta,
muryarshi na sark'ewa yace " why Sanah..!?
" Me yasa kike san jefa mu cikin hakala da tab'ewa had'i da fushin Ubangiji...!?
" Meyasa baki bari muyi aure muji dad'in duniyar ma'aurata ba...!?
" Why Sanah..!?
Ya fad'a yana lasar kunnenta,
a hankali ya shiga lasar kunnenta had'i da hura mata iska cikin kunnen,
idanta ta kuma runtsewa da k'arfi k'irjinta yana up and down,
cikin salo ya gangaro da bakinshi zuwa wuyanta yana lasar wuyanta,
zuwa saman boobs d'inta, hannunshi ya sanya yana shafa bayanta zuwa cikinta da cibiyarta,
cikin k'ank'anin lokaci suka rud'e hankalinsu yabar gangar jiki da ruhinsu,
jikinsu ya d'auki rawa, hannunta ta cusa cikin k'irjinshi tana shafa kwantaccen gashin k'irjinshi,
zuwa cikinshi da cikin kwarmin cibiyarshi,
take ya fara fitar da numfashi mai sauti,
cak ya d'auke ya mayar da ita saman sofa ya kwantar da ita saman 3 sitter had'i dayi mata runfa da jikinshi,
while bakinsu na manne cikin na juna suna ta faman shan lips da harshen junansu,
ta bayanta ya zura hannunshi yana b'alle bra d'inta ya sanya hannu cikin kwarmin bayan yana shafawa had'i da yin tafiyar tsutsa a gadan bayanta,
gaba d'aya sun gama rud'ewa sun kai k'ololuwa wajen buk'atuwa da juna,
sai aikin shafa k'irjinshi take yi,
tana k'ara ruk'unk'ume shi,
sun dad'e da tafiya cikin wata duniya ta daban,
sama-sama taji ana knocking k'ofar,
knocking d'in da aka cigaba da yine da yawo da ita cikin hayyacinta,
da sauri ta fara k'ok'arin tureshi,
had'i da k'ok'arin tashi, amma ina maza bisa kanta,
dan k'irjinshi ya sanya ya tokare ta sosai yadda bazata iya tashi ba,
while yana cigaba da abinda yake yi,
a hankali ya sanya harshe yana lasar saman boobs d'inta batare daya tab'a su ko fiddo su daga cikin riga ba,
cikin kunnanshi tace " please ka barni..!
ta fad'a maganarta na sark'ewa,
" ban iyawa yace while bai bar abinda yake yi ba,
" please ka bari ban so ana knocking k'ofa..!
" ban iya bari, idan na bari ina iya mutuwa,
ganin yadda duk ilahirin jikinshi yake kerrrrma,
yana k'ok'arin rabata da kayan jikinta,
yasa gabanta muguwar fad'uwa,
tasan kwata-kwata baya cikin hayyacinshi komai yana faruwa muddin tayi sake,
ga ta kasa yin koda kwakkwaran motsi,
cikin tashin hankali ta soma yin kuka k'asa-k'asa gudun kar wanda ke knocking yaji,
ta shiga yi mishi magiya had'i da bashi hak'uri,
amma ina yadda kasan cikin kunnen kurma take magana haka Sir Aryan ya koma,
ya birkice mata ya koma tamkar mayunwacin zaki daya shekara babu abinci,
sosai ta fara kokawa dashi tana k'ok'arin kwatar kanta,
danta lura muddin tayi sake yau sai buzunta hannunshi,
gaba d'aya k'arfinta ta tattaro ta sanya hannunta da gwiwarta ta hankad'a shi baya,
ya fad'a saman carpet tana ganin ya fad'i tayi saurin mik'ewa,
jikinta na tsuma ta koma can gefe ta rakub'e had'i da had'e kanta da gwiwa,
yakai 5 minutes zaune jikinshi ya mutu murus bai iya koda motsi,
ya d'an d'auki lokaci,
" Sanah gaskiya bazan iya wannan wulak'antaciyar kuma tab'abb'iyar rayuwar ba,
muddin kina so na ki bani chance na fito na aure ki,
idan kuma baki so na ki barni please,
Allah ya sani na gaji I'm very tired,
ban iyawa, kwata-kwata bana san zina, ban k'aunar koda kusantarta ne,
amma saboda wani banzan ra'ayinki na karatu kina neman jefa rayuwarmu cikin had'ari da bala'i,
ya fad'a muryarshi na creaking,
kanta k'asa tace " yanzu dana barka da sex zaka yi dani...!?
" Ka keta man haddi..! ashe zaka iyayin Zina...!?
" Waya ja..!, duk wad'annan abubuwan waye ya ja su....!?
" Wallahi Allah ko sex nayi dake kece kika ja mana,
" maiyasa bazaki tallafi rayuwarmu ba...!?
" Maiyasa bazaki barmu muyi aure ba please...!?
A hankali ta mik'e taje gabanshi ta zauna had'i da sanya hannunta ta shafo kumatunsa,
tayi murmushi tace " na baka dama ka tura gidan mu,
ina so a d'aura auren mu cikin satin nan wannan Friday mai zuwa,
nan da six days,
ta fad'a tana murmushi,
wani irin sanyin dad'i yaji ya lullub'e shi,
ya ziyarci dukkan jikinshi da zuciyarshi,
cike da tsantsar farin ciki ya mik'e da ita a hannunshi yana zagaya office d'in da ita,
thank you sweetheart..!, thank you so much K'albi I love you moreeee,
ya fad'a yana kissing goshinta,
I love you most, ya fad'a yana kissing kumatunta,
I love you madly and deadly ya fad'a yana kissing hab'arta,
dariya tayi tace " I love you too Hub..!,
muje na aje ki gida yau zan tafi Maiduguri gobe su Hilwa suzo,
idan ta kama ma a d'aura auren a goben,
ya fad'a yana d'aukar key d'inshi,
while tana rik'e a hannunshi,
da sauri Sanah ta ido tana k'ok'arin direwa,
" dani zaka fita a haka...!?
Murmushi yayi yace " to meye na tsorata..!?
"Bakomai ni dai aje ni ka shirya tsaf,
ji fa ko bottles d'in gaban rigarka baka rufe ba,
" kina jin tsoro kar a gane kinzo kinyi man fyad'e......!
ya fad'a had'i da kashe mata ido d'aya,
baki ta turo tace " nayi me..!?
Dariya yayi had'i da direta ya sanya 'yar saman cot d'inshi,
Sanah ta b'anle mishi bottle d'inshi,
kana ya kwashe wayoyinshi da key suka fita,
a bakin k'ofa suka iske labourer zaune yana jiranshi,
da alama shine yayi knocking,
da sauri ya mik'e yace " Yallab'ai dama nazo gyaran office ne,
murmushi yayi mishi gami da cewa " no karka damu bakomai ka barshi,
har ya juya zai tafi ya juyo ya sanya hannu cikin aljihunshi ya d'auk'o bandir d'in 1k gudu biyu na 200k ya bashi,
jiki na rawa labourer ya amsa had'i da zubewa k'asa yana godiya,
basu tsaya jin abinda yake cewa ba suka wuce, suka shiga mota,
sai da suka fita daga cikin makaranta,
kana tace " I'm sorry na manta ban fad'a maka ba,
gidan Khulud zaka kaini fa,
cikin mamaki ya kalleta yace " gidan Khulud kuma...!?
"Eh..!, zanje na dubo ta ne,
" lafiya dai ko..!?
"Oh...! ashe fa baka san meya faru ba,
d'an kallanta yayi yace " meya faru..!?
Cikin sanyin jiki muryarta na rawa ta bashi labarin abinda ya faru batare data b'oye mishi komai ba,
tamkar yayi kuka shima dan yaji abun har cikin ranshi,
sosai ya tausayawa Khulud had'i da kwantarwa da Sanah hankali da bata baki,
dayake sun sake sabon mai gadi,
dan waccan tun ranar da Sir Moli ya bashi 5m ya bar gidan ya kawo mak'ocinsa ya cigaba da aikin,
lek'owa mai gadin yayi had'i da cewa " waye..!?
Cikin nutsuwa Sanah tace ita yayar matar gidance,
batare daya kuma cewa komai ba ya bud'e musu get suka shiga,
murmushi Sir Moli yayi yace " hmmm uwar san girma ba rana d'aya aka haife ku ba,
kike cewa yayarta ce,
" eh man ai na bata 1hr kaga ko ai yayarta ce,
tunda na rigata shak'ar iskar duniya,
" eh lalle ke yayace ya fad'a yana dariya lokacin da yayi parking cikin gidan,
kallanta yayi yace " na jira ki ..!?
"A'a kaima kasan Khulud bazata barni na tafi yanzu ba,
" tom Maiduguri zan tafi ni,
a'a dan Allah ba sai kaje ba, kayi musu waya sai suzu nan su same ka,
idan ka tafi wa zai rako su gidan...!?
Ta fad'a tana langwab'e kai,
" hmmm ke dai kawai kice baki san na tafi,
" eh Allah ban san ka tafi, please kayi musu waya suzo kawai,
"tom naji na fasa bari zanyi musu wayar, as you said,
idan kin gama kiyi man magana nazo d'aukeki,
" Ok tace had'i da mishi light kiss ta shafa fuskarshi tace " I love you and I will never ever hurt you Hub..!,
kiss yayi mata yace " I know,
har ya fita tana tsaye harabar gidan tana d'aga mishi hannu,
sai da ya fita kana ya nufi cikin gidan,
tun daga waje ta soma jiyo tijarar Jaddah, tana ruwan bala'i da masifa,
da sauri ta k'arasa shiga cikin gidan,
tsaye ta iske Jaddah Hanash rungume da Khulud tsaye a gabanta,
Khulud nata faman kuka, Khulud na ganin Sanah tace " ya Salam!,
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
dan tasan Sanah dai-dai take da Jaddah,
jin salatin Khulud yasa Hanash mayar da kallanshi inda yaga tana kallo,
shi kanshi sai da yaji gabanshi ya fad'i,
da sauri Khulud ta zame jikinta daga na Hanash ta nufi Sanah ta fad'a jikinta,
" wacece..!?
abinda Sanah ta iya furtawa kenan,
" dan Allah karkiyi mata magana Jaddah ce mahaifiyar Papu Baban Hanash,
ido Hanash ya zubawa Sanah yana kallan abinda zatayi,
idanta ta runtse da k'arfi kana ta bud'e su,
ta sauke su kan Jaddah, abinda ya bawa Hanash mamaki yadda lokaci d'aya idanta ya canja kala,
" lalle yarinyar nan masifaffiyace,
ya fad'a cikin ranshi,
" hmmm munafuka ke mai 'yar uwa,
shine tsabar munafurci kika lallab'a kika kira ta,
to da tazo mezatayi min..!?
Jaddah ta fad'a tana hucin bala'i,
idanshi na kanta danya san hali,
da sauri Khulud tace " please for my sake dan Allah don't say anything,
" oho dai Jaddah tace tana mayar da kallanta ga Hanash tace " kai dakai nake nace alk'aminka baya motsi ne..!?
" Ko kuwa karanka ne bai isa tsaiko bo..!?
Ido Hanash ya zubawa Jaddah cike tsantsar bak'in ciki yake kallanta ido cikin ido,
" ka wani tsare ni da ido tunninka bazan iya magana bane, dan tsareni da wad'annan shayayyan idanun naka masu kama dana mashaya?
" Ka bani amsa juya ka auro wacce bata haihuwa data kasa haihuwa aure shekara biyu ko kuwa kai ne baka iya kwanciya da matar ba, baka yin yadda ya kamata..!?
Shi dai bayyi mata magana ba yadai kafe ta da ido tarrr cikin nata,
" bata tashi ne, ko kuwa motsi ne bata yi...!?
Ta kuma fad'a babu kunya balle kawaici da tsoran ido,
ganin baida niyyar bata amsa yasata mayar da kallanta ga Khulud tace " ke fad'a man mijikinki bashi da cikekkiyar lafiya ne, ko kuwa kwata-kwata alk'alaminsa ne baya aiki...!?
Ganin basu da niyyar bata amsa yasata zagewa tayi ta zazzaga ruwan bala'i da tijara,
san ranta kamar wacce ke shan kwaya,
takai awa d'aya tanayi musu bala'i kana ta kalli Khulud tace " banza juya mara haihuwa sai da aci a kwanta kawai marar zuci.......!
" ya isa!!, Sanah ta fad'a idanta tarr cikin na Jaddah,
" a'a please my Sanah dan Allah karki ce mata komai,
cikin zafin rai Sanah ta cigaba,
" idan kina tantamar lafiyar jikanki ne,
d'aki zaki kai shi ki duba shi ciki da waje,
ko kuma ki had'a shi da mace ki gani zata tashin ko bazata tashi ba,
bawai kizo ki tsare matarshi da tambayoyi ba,
ke wacce irin macece da zaki tsare mace matar jikanki kina tambayarta,
abinda ya shafi kwanciyar aurensu da azzakarin mijinta,
idan ni ce ke wandonsa zan cire na duba da kai na, ba sai na ba'tawa kai na lokaci wajen tambaya ba,
kin san ance gani ya kori ji,
haihuwa bata Allah bace, ni dai a iya sanina babu kasuwar da ake siyar da yara ko haihuwa bare suje su siyo,
Idan kuma akwai muje ki raka mu, mu siyo,
dan Allah idan Zohal ko Wajnah ake yiwa haka ya zakiji...!?
Tunda Sanah ta fara magana Jaddah ta kafe ta da idanta,
haka ma Hanash,
" haba ki barsu ma da abinda ya dame su ya ishe su, amma kinzo kina tayi musu ihuu aka,
cikin mamaki Jaddah tace " yanzu ki kalli tsabar kwayar ido na kice azzakari...!?
" Ke da kika ce bata tashi da motsi fa...!?
" Mu sai muce me..!?
"Tom yayi kyau Hanash daka tsaya kana kallan yarinya k'arama tana yi man tijira da rashin kunya a gaban idanka amma ka kasa d'aukar mata,
kana ta kalli Khulud tace " wallahi wallahi wallahi Allah,
na rantse miki da girman Allah idan bakiyi ciki nan da wata uku ba,
sai na aurawa Hanash mata biyu a lokaci d'aya,
cikin tsiwa Sanah tace " to ki aura mishi mana sai me ko ce miki akayi shi kad'ai ne namiji..!?
Bata ko kalli inda Sanah take ba,
" nan da wata wallahi ko tsafi kukeyi da bak'ar jab'a sai na yi mishi aure,
ta fad'a had'i da fita da sauri,
Jaddah na fita Sanah ta durk'ushe a k'asa had'i fasa rikitaccen kuka,
" na cuci ki Khulud ni ce naja miki dukkan wannan abun,
bayyi mata magana ba ya zuba mata uwar harara had'i da cifewa,
" I'm very very sorry har abada ban tab'a gajiya da baki hak'uri,
ta fad'a tana kuka, a hankali Khulud ta mik'e ta shiga cikin kitchen ta zubo mata drink mai sanyi cikin glass cup,
ta dawo ta tsuguna a gabanta had'i da dafa ta ta mik'a mata,
kai Sanah ta kawar gefe tana cigaba da kukanta,
tace " wallahi da ina da yadda zanyi danayi danna fitar dake cikin masifar matar nan,
da ace ina da hanyar da zan taimaka miki, na share miki hawayenki danayi,
da ace zai iya yiyuwa na haihu ba baki d'an danayi,
" karb'i ki sha Khulud ta mik'a mata glass cup d'in,
hannunta na rawa ta masa ta rik'e a hannunta,
yunk'urawa tayi da niyyar mik'ewa,
amma sai karaf kalaman Sanah suka shiga dawo mata,
da sauri ta koma ta kalli Sanah tace " me kika ce yanzu..!?
"Banyi magana ba, ta fad'a muryarta a shak'e,
" no abinda kika ce last yanzu,
" cewa nayi da zai yiyu dana haifa na baki d'an,
murmushi Khulud tayi had'i da gyara zamanta,
fuskarta d'auke da wani irin murmushi mai wuyar fassarawa tace " zayyiyo..!
cikin mamaki Sanah ta kalleta,
tace " kamar yaya...! ta wacce hanya..!?
" Kisha..! Khulud tace tana murmushi,
ba musu ta karb'a takai lemun bakinta ta soma sha, ajiyar zuciya Khulud ta sauk'e tare da fesar da iska mai zafi, zamanta ta gyara, tare da fuskantar Sanah cikin fargaba da taraddadin abinda ranta ya raya mata tace,
"Idan kina san ki taimake ni ki kuma rufa min asiri to kina da damar yin hakan".
cikin zak'uwa da son jin, wane abu zatayi ta fidda Ulud d'inta cikin wannan masifar rayuwar tace,
"Me zanyi miki Ulud in taimaki rayuwarki in rufa miki asirin gaya min shi yanzu zanyi?."
auren *RASHIN SANI.…!* da shi mijin ma da kanshi bazai sani ba,
cikin mamaki Sanah tace " Auren *RASHIN SANI..!* kuma.,! ta yaya da wa kuma?
Khulud tace " *HANASH.........!!!!*
cikin rashin fahimta Sanah tace " bangane abinda kike nufi ba my Ulud?
"Please ki fito a mutum sak kiyi man bayani sosai,
murmushi Khulud ta k'arayi idanta cikin na Sanah data zak'u taji abinda Khulud ke nufi,
numfashi Khulud ta kuma saukewa kana tace " *KI AURI HANASH........!!!*
MOMYN ZARAH
[7/7, 5:37 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
4⃣2⃣
Cikin muguwar zabura Sanah ta mik'e tsaye had'i da nuna Khulud da hannunta,
ta kasa furta koda kalma d'aya bakinta sai rawa yake,
tana yiwa Khulud wani irin kallo like monster,
mik'ewa Khulud tayi hawaye na zubo mata ta nufi inda Sanah ke tsaye,
baya Sanah ta soma ja, while Khulud na d'aukar step to her,
itama tana cigaba da ja baya,
har suka isa ga bango, a hankali Khulud ta dafa kafad'ar Sanah,
tace " dan Allah my Sanah kiyi man wannan alfarmar ki auri Hanash,
ai Khulud na furta Kalmar ki auri Hanash,
Sanah ta soma yin tari sosai tamkar ranta zai fita,
sunkuyawa tayi had'i da sanya hannunta ta dafe k'irjinta,
amai ta soma kelayawa ta hanci ta baki, while idanta na zubar da hawaye,
cikin k'ank'anin lokaci ta burkice ta fita daga hayyacinta ta soma fitar da numfashi kamar mai cutar asma,
tana daga sunkuyan ta d'ago red eyes d'inta ta kalli Khulud ta soma k'ok'arin yin magana,
amma ta kasa, a hankali ta koma kokawa da numfashinta,
har daga k'arshe numfashin ya d'auke cak, ta zube k'asa cikin aman datayi sumammiya,
bak'in cikin idanta ya d'auke sai farin kawai, idan ya kakkafe tamkar matacciya,
a haukace Khulud ta d'ora hannunta aka ta soma ihuuuuu tana kururuwa,
ta shiga jijjiga ta tare da kiran sunanta da k'arfi" Sanah!!!,
amma ko matsawa batayi ba, a d'imauce Khulud ta mik'e ta nufi fridge ta bud'e kamar zata b'alle murfin fridge d'in ta d'auko robar swan water,
jikinta na kerrrrma ta b'alle murfin ta shek'awa Sanah,
ajiyar zuciya ta sake da k'arfi had'i da fasa gigitaccen kuka mai cin zuciya,
cikin mutuwa jiki ta tashi zauna,
tayi zaman 'yan bori, had'i da gafe kanta da duka hannayenta,
gashin kanta ya zubo mata, yayinda duk ilahirin jikinta tsuma yake yana rawa,
yadda kasan ana buga mata gangi.
Itama Khulud d'in kukan take yi sosai tayi durk'ushe a gaban Sanah tana kuka wiwi,
" dan Allah ki taimake ni ki rufa man asiri my Sanah,
wannan hanyar ita kad'aice mafita,
kai Sanah ta d'aga ta zubawa Khulud jajayen idanuwanta,
ta dad'e tana kallanta kana tace " ashe duk ikirin soyayyar da kike man ba gaskiya bane Khulud...!?
" Dama ke da kanki zaki iya jefa ni cikin wuta...!?
" Zaki iya kai ni ga makasa ta..!?
" Ashe dama baki so na Khulud...!?
" Baki san farin ciki da kwanciyar hankali na...!?
"Duk so da shak'uwar dake tsakanin mu amma zaki yi min haka...!?
" Kin ban mamaki Khulud kin kuma d'aure min kai,
a tunaninki ko saurayin k'awata zan iya aura...!?
" Kin fi kowa sanin halina, kinfi kowa sanin wacece Sanah,
yanzu duk irin soyayyar da nake haka zaki yi min..!?
Duk iya k'ok'arina akan na faranta miki,
na sanya zuciyarki haske da farin ciki amma baki gani ba ....!?
" Yau ni kike zacewa na auri mijinki...!?
" Ni zan had'a miji dake, na had'a turaka dake....!?
"Mijinki na sunna wanda kika kwanta dashi, kuka had'a jiki da shinfid'a,
" Kina zatan ko saurayinki zan iya aura balle mijinki na sunnah...!?
"Wallahi ko maza sun k'are cikin duniya babu abinda zanyi da mijikinki,
ko kin mutu ko da baki raye wallahi bazan tab'a auren Hanash ba,
" Kin ban mamaki Khulud wallahi idan wani ne ya fad'a min bazan tab'a yarda ba zaki iyayi min hakan ba,
ashe dama baki so na duk abinda kike fad'a bai kai zuciyar ki ba iya bakinki ya tsaya...!?
Ta fad'a cikin matsanancin kuka,
" wallahi ina sanki ina matuk'ar k'aunar ki fiye da kowa cikin duniyar nan,
Khulud ta fad'a cikin kukan itama,
a fusace Sanah tace " k'arya kike Khulud baki so na wallahi,
ni dai ke sanki, amma ke baki so na baki kuma san farin ciki na,
" wallahi ina sanki my Sanah Khulud ta fad'a tana k'ok'arin rungume Sanah,
da sauri taja baya tana daga zaunen,
tace " kina san nawa zaki kice na auri mijinki..!?
" Baki tunanin kallan da duniya zatayi mana...!?
" Baki tunanin wacce irin fahimta da zargi mutane zasuyi akan mu...!?
" Khulud kinfi kowa sanin ina da wanda nake so,
finki kowa sanin irin mugun san da nake yiwa Aryan,
ke kanki sheda ce idan babu shi babu ni,
shi ne farin ciki da jin dad'in daniya da rayuwa ta,
matuk'ar bana tare da Aryan tamkar a raba gangar jiki da ruhinta me,
amma duk da kin san haka kike cewa na auri Hanash ba Aryan ba,
mutumin dako gani na bai k'aunar yi,
da yana da yadda zayyi da tuni yayi akai na,
mutumin daya tsane ni tamakar mutuwarshi,
ya tsani gani na, ga tsani kusanci na da ke,
wallahi nasan duk duniya babu abinda Hanash ya tsana sama da ni,
tayaya zanyi rayuwar aure da mutumin da bai ko k'aunar gani na....?
"Tayaya zan rayu da mak'iyi na wanda kwata-kwata babu so ko soyayya a tsakanin mu....!?
" Bayan ina da wanda nake so kuma bai fishi komai ba,
idan na auri Hanash in kai Aryan Moli ina..!?
" Inyi yaya da matsananciyar soyayyar shi...!?
" Wallahi idan na yiwa wanda yake min mugun so butulci kamar Arayan nasan Allah bazai tab'a bari na ba,
sai Allah ya hukunta ni, ya nuna min banyi dai-dai ba,
I'm sorry Khulud akan abinda nayi miki amma I can't betray him
I love him so much idan nayi mishi haka Rabbi bazai tab'a bari na ba,
sai Allah ya saka mishi,
ta fad'a tana fita daga cikin parlor mayafinta a hannu jikinta duk ya b'aci da aman da tayi,
da gudu Khulud ta biyo bayanta tana kwala mata kira amma bata ko juyo ba,
tayi ficewarta while tana cigaba da kukan,
kota kiran Sir Moli bata bi ba, ta tare mai adai-daita sahu ta shiga ya kaita gida,
part d'in Halan ta shiga ta zauna a parlor taci uban kukanta ta ,
Halan dake kitchen ta jiyo sautin kukan Sanah ta fito da sauri,
" lafiya..! meke faruwa dake ...!?
Halan ta tambayeta,
kamar zata gaya mata sai kuma ta fasa,
babu tambayar da Halan batayi mata ba,
amma batako tanka mata ba,
taci kukan ta san ranta kana ta shiga bathroom d'in dake parlor ta wanke fuskarta ta fita,
Halan tabi bayan ta da kallo,
luckily tayi sa'a parlor'n babu kowa tayi wucewarta bedroom d'inta ta fad'a saman bed,
idanta ta lumshe tana sauke ajiyar zuciya,
jin wayarta tana ringing ya sata bud'e red eyes d'inta dan tasan shine saboda ringing d'inshi is different,
sai da ta saita kanta kana tayi picking,
" I love you, ya fad'a yana kwanciya saman bed,
murmushi tayi batare datace komai ba,
" hello my K'albi, are you with me..!?
" Yes..! Hub...! I'm with you for ever an ever,
murmushin jin dad'i yayi yace " tom munyi magana dasu Hilwa sunce na fad'a miki ki sanarwa da Abbu jibi zasu zo...!,
muryarta na rawa tace " please su taho da sadaki da goro idan sun zo jibin a d'aura auren kawai please Hub..!,
ta fad'a muryarta na creaking,
mik'ewa yayi zaune da sauri had'i da cewa " me yayi miki..!?
" Wa..!?
Tace duk da tasan Hanash yake nufi,
" your monster ya bata amsa,
" hmmm even Aryan yasan he's my *MONSTER* amma Khulud want me to marry him...!,
jin tayi shiru yasa shi cewa " ya mare ki ko..!?
"Lah wallahi bayyi man komai ba,
kama ji na rantse maka kawai dai kai na ke min ciwo,
cikin tension yace " oh! no sweetheart,
kiyi hak'uri, sannu kinji,
ya fad'a kamar zai saki ihuu, at d same time,
" bari nazo yanzu na kaiki Hospital,
" a'a karka damu nasha magani,
" Ok tom ki kwanta kiyi bacci my life,
idan kina san wani abun ki fad'a min,
" I love you so much K'albi,
murmushi tayi tace " I love you more most heartbeat,
I will never ever hurt you anymore my hope,
ji yayi gabanshi ya d'an fad'i amma sai yayi murmushi yace " jibi su Hilwa zasu zo & u said a d'aura auren jibin ko..!?
" Yes I said it, kuma zan fad'awa Yaya Aarib ya sanar dasu Abbu a d'aura auren idan sun zo,
" nagode sosai Allah ya barmu tare my wife,
suna gama wayar ta lumshe idanta,
tana tunanin yama zata yi ta iya rayuwa da waninshi ba dashi ba,
mutumin dayake yi mata wannan mugun son, daga jin muryarta ta canja duk ya tashi hankalinshi,
a hankali ta furta I love you Aryan I can't do without you,
yadda Sanah taga rana haka taga dare bata koyi gyangyad'i ba balle bacci,
haka ma Khulud hankalin ta in yayi dubu ya tashi sosai,
ta kasa bacci sai kallan saman pop da take yi,
duk bayan minti biyu sai ta sauke ajiyar zuciya,
babu irin tambayar da Hanash bayyi mata ba,
amma tak'i ce mishi komai, har ya gaji ya kyale ta.
Washe gari tunda sassafe Khulud ta tashi ta tashi Hanash a hankali ya juyo had'i da kallan agogon bango yace " 8:15am na safe na,
" eh nasani please ka tashi ka kaini gida,
a d'an tsorace yace " lafiya...!?
Danshi yayi tunanin ba lafiya ba,
" a'a lafiya lau, kawai ina san zuwa ne,
agogon ya sake kalla yace " yanzu yayi wuri da yawa ki bari sai zuwa 12:00pm na rana,
" a'a ni dai please ka tashi ka kaini,
babu yadda ya iya dole ya sashi cewa " tom naji had'a min breakfast da ruwan wanka,
ya fad'a yana komawa kwancen,
" please ka tashi ta fad'a tana nufar bathroom da sauri,
bata b'ata lokaci ba, ta gama had'a mishi ruwan wankan,
bata bar d'akin ba sai da ta saka shi cikin bathroom kana ta fito ta nufi kitchen,
a gaggauce ta had'a mishi breakfast,
10:00am sukayi parking a harabar gidan,
da sauri ta fito jikinta na rawa ta shiga part d'in Halan dan zatonta Sanah na can,
sama-sama suka gaisa da Halan kana tace " ina my Sanah..!?
"Tana part d'in Mamu Khulud bata jira amsarta ba ta fice,
hakan ne ya tabbatarwa Halan ba lafiya akwai wani abu a k'asa,
harta mik'e zata bita bayan Khulud sai kuma ta fasa,
ganin safiya ce yasa Hanash juyawa batare daya gaida su Dide ba,
ya barshi idan ya dawo da yamma sa gaisa,
tayi sa'a parlor'n babu kowa kasancewar safiya ce,
dinning table ta kalla taga har an gama jera breakfast hakan ne ya tabbatar mata Sanah ta tashi,
direct bedroom d'inta ta nufa tayi knocking,
tana kwance saman bed, taji ana bugun k'ofar a gaggauce,
kwata-kwata batayi zaton Khulud bace ta tashi ta bud'e k'ofar,
had'i da juyawa batare data tsaya taga kowaye ba,
jin an saka key a k'ofar ya sata juyowa da sauri,
tsaye tayi cak ganin Khulud, cike da mamaki ta hard'e hannunta ta kafe da ido,
da sauri Khulud ta k'araso gaban Sanah ta zube had'i da dafa k'afafunta ta fasa rikitaccen kuka tace " dan girman Allah ki tsaya ki saurare ni,
kiji abinda ke cikin raina kafin ki yanke min hukunci please my Sanah,
na fi sabawa dake fiye da kowa,
nafi kusanci dake fiye da kowa a duniya,
ina tunanin sai lokacin da d'ayan mu ya shiga damuwa da matsala ya kamata mu nunawa junanmu tsantsar soyayyar da muke yiwa juna,
mu taimaki juna mu raba damuwa da bak'in cikin mu,
idan kika guje ni ko kika rabu dani a halin danake ciki yanzu,
ina kike san na saka kai na..!?
" Ina kike san na saka rayuwa ta naji dad'i...!?
" Dawa zanyi shawara, wa zai rab'e ni koya tausaya min ....!?
"Dan girman Allah ki tsaya ki saurare ni,
ta fad'a cikin kuka,
ajiyar zuciya ta a sauke hawaye na bin kuncinta, ta duk'a had'i da rik'o kafad'ar Khulud tana k'ok'arin mik'ar da ita,
" a'a ki barni a haka, ni dai dan Allah ki saurare," dan Allah ki tashi my Khulud
ta fad'a cikin kuka,
kamo hannunta Khulud tayi ta zaunar da ita a gabanta,
kana tace " ba wai ina nufin ki auri Hanash aure na har bada ba,
ina nufin *AUREN MANUFA*
zaki aure shi ne cikin *_RASHIN SANI...!_* ,
dan shi kanshi bazai san kin aure shi ba,
har kiyi ciki ki haihu saiki ban abinda kika fa,
idan Sanah na kanta tana yi mata wani irin kallo,
in banda tasan Khulud farin sani da sai tace mahaukaciya ce ko 'yar shaye-shaye,
" idan kika aure shi zaki rink'a shiga bedroom d'inshi a matsayin nice,
" hmmm kamar abin film to taya hakan zatayi...!?
" America zamu je wajen Chris shine zai kai mu inda za'ayi miki fuska irin tawa sak tamkar nice,
shine zai tsara mana sauran abubuwan,
duk sanda zaki je gare shi sai ki saka fuskar,
" first night fa!?
Sanah ta fad'a cikin rainin hankali,
zamuyi amfani da table ne, wanda zai kawar mishi da hankalinshi،
kuma duk duniya babu wanda zai san da auren daga ni sai ke sai Papu mahaifin Hanash,
"Tou 'yan gida ayi yaya dasu..!?
" Cewa zamuyi service zaki tafi,
ni zan shirya komai na tafiyarki service d'in sai ki dawo gida na da sunan kin tafi bautar k'asa,
"Ina level 3 d'in..!?
Sanah ta kuma tambayarta,
" eh..!ai nasan Abbu ya manta idan ma bai manta zan san yadda zan b'ullo mishi,
" tou wa zai d'aura auren..!?
"Papu ne zai d'aurawa Hanash d'in aure ke kuma Papun zayyiwa Dide wayau ya d'aura auren batare daya sani ba,
da real name d'inki,
murmushi tayi tace " tou Sir Moli fa..!?
Fuska Khulud ta k'ara maraicecewa tace " bafa auren zama bane just wata 10 ma ya isa in sha Allah,
kin haifa kin bani, sai ki koma mishi kuyi aure,
" budurci na fa..!?
" Zamu koma America a mayar dake cikekkiyar budurwa,
dariya Sanah tayi had'i da cewa " na gama jin tatsuniyar ki my Khulud,
amma hakan bazai tab'a yiyiwa ba dan ban tab'a jin hakan ba ko a film,
koma zai yiyiyu ni ban yi,
ta fad'a tana mik'ewa,
wani irin mahaukacin kuka Khulud ta saki had'i da durk'ushewa ta rik'ewa k'afafuwan Sanah,
tace " wallahi idan baki yarda ba mutuwa zanyi,
idan baki taimake ni kin rufa man asiri ba wa zai rufa min a duniya,
ki tuna kinyi min alk'awarin bazaki tab'a bari na cikin bak'in ciki da damuwa ba,
kinyi man alk'awarin bazaki tab'a bari na, na zubar da hawaye ba,
zaki kasance mai share min hawaye,
zaki taimake ni, zaki kasance kina rik'e da hannu na a kowanne lokaci bazaki tab'a sakin hannu na ba,
amma yau gani durk'ushe gabanki ina kukan,
ina kuma cikin damuwa da bak'in cikin,
ina cikin k'uncin rayuwa ke kad'ai ke da hanyar fitar da ni amma kink'i,
kin san girman alk'awari fa,
kai Sanah ta d'aga saman had'i da fasa kuka tana tuno abubuwa da dama,
da saurin Khulud ta mik'e ta kalli Sanah,
cikin kuka tace " shikenan tunda kin karya alk'awarirrikan da kika d'auka,
kin kuma kasa taimako na ki fidda ni daga cikin halin dake ciki,
bayan kina da damar yin hakan,
rayuwa ta bata da wani amfani,
dan haka wallahi! wallahi!! wallahi!! Allah!!! kai na zan kashe da wannan bak'ar rayuwar,
ta fad'a tana k'ok'arin fita,
da sauri Sanah ta rik'o hannunta ta bata batare data jiyo ba,
had'i da d'aga kanta sama hawaye na gangarowa kan fuskarta,
tace " *NA AMINCE!!!*,
saboda tasan babu yadda za'ayi hakan ta yiyiyo,
rungume ta Khulud tayi tana kuka tace " nagode sosai, Allah ya saka miki da alkhairi,
ya taimake ki kamar yadda kika taimake ni,
ya rufa maki asiri kamar yadda kika rufa man asiri,
yau na k'ara tabbatarwa bani da kamar ke duk duniya,
yau na k'ara tabbatarwa kina so na sosai zaki kuma sadaukar min da komai saboda farin ciki,
a hankali Sanah ta zame jikinta batare datayi mata magana ba ta shige bathroom,
kwata-kwata bata wani damu ba,
dan ta tabbata babu yadda za'ayi hakan ta faru ko a cikin film da novel ne balle a zahiri,
wanka Sanah tayi ta shirya kana ta kalli Khulud tace " muje parlor muyi breakfast dan na ji motsin su Mamu,
" ok to muje d'in amma damun karya fa gidan su Hanash zamu tafi muje muyi magana da Papu,
dan Hausawa sunce da zafi-zafi kan bugi k'arfe,
murmushi kawai tayi batare datace komai ba,
suna fita Mamu tabi su da kallo tace " ah ikon Allah Khulud yaushe kika zo..!?
Murmushi tayi tace " tun 10:00am naga baki fito bane shiyasa na wuce wajen my Sanah,
dama zuwa nayi ta raka ni kasuwa,
kallan fuskokin su Mamu tayi tace " kuka kukayi ne naga idanku ya kumbura yayi ja..!?
"Kuka kuma Mamu..!?
Khulud ta fad'a tana dariya,
ita dai Sanah batayi magana ba,
haka nan taji hankalin ta yak'i kwanciya gabanta na fad'uwa,
kallanta Mamu tayi tana nazarinta kana tace " meke damunki Sanah..!?
Da sauri Khulud tace " bakomai wai kanta ke ciwo,
baki Mamu ta tab'e had'i da cewa " kudai kuka sani,
sama-sama sukayi breakfast d'in,
ita Sanah ji tayi kwata-kwata bata san cin komai,
yayinda ita Khulud saurin suje wajen Papu ne ya hana ta ci,
suna gama breakfast suka fita bayan sunyiwa Mamu sallama sun biya sun gaida Juju da Dide,
k'in bari driver ya kai su Khulud tayi,
sai adai-daita sahu suka shiga, ya aje su k'ofar gida suka shiga,
a harabar gidan suka iske Jaddah tana k'ok'arin fita,
harara Sanah ta watsa mata had'i dayin kwafa,
da sauri Jaddah ta shige mota batare datayi musu magana,
Khulud ko tayi mamakin hakan dan tasan ko gidan bata da ikon zuwa saboda Jaddah,
basu iske Zohal da Wajnah ba sai Mimmee zaune a parlor,
har k'asa suka duk'a suka gaida ita,
ta amsa musu cikin sakin fuska da walwala,
anyi 'yan mintuna kafin Khulud tace " Papu yana nan..!?
"Eh yana parlor'n shi,
ayi mishi magana ne..!?
" eh amma parlor'n nashi muke san zuwa,
"tou bari na sanar dashi, Mimmee ta fad'a tana mik'ewa,
batafi 5 minutes da shiga part d'inshi ba ta fito tace " yace ku shiga,
ta fad'a tana fita harabar gidan,
jikin Khulud na rawa ta mik'e hannun Sanah cikin nata,
Sanah tayi murmushi kawai tana mamakin yadda akayi kwakwalwar Khulud ta toshe idanta ya rufe lokaci d'aya,
har take ganin abinda bazai yiyiyu ba a matsayin zai yiyiyu,
sai da sukayi sallama aka basu izinin shiga kana suka shiga bakinsu d'auke da sallama,
har k'asa suka duk'a suka gaida shi,
ya amsa cikin kulawa,
d'an shiru sukayi, shiko duk ya tattara gaba d'aya hankalinshi gare su,
Khulud tace " uhnnn dama....! dama....!,
murmushi yayi yace feel free daughter karki ji komai kiyi magana kawai,
cikin rawar murya tace " Papu dama so nake Hanash ya k'ara aure..!,
kallanta yayi cike da mamaki yace " aure kuma? " lafiya meya faru..!?
" Lafiya lau Papu kawai, naga ni har yanzu ban haihu ba kuma Jaddah ta damu sosai,
shiyasa nace mai zai hana ya k'ara aure,
idan Papu na kanta yace " uhmm ina jinki,
sai da tayi jimmmm kana tace " so nake ya auri my Sanah,
da sauri Papu ya gyara zanshi had'i da kallan Sanah,
yace " kamar yaya ban gane ba..!?
Bakin Khulud na rawa ta fad'a mishi tsarin da take san ya taimaketa tayi,
murmushi yayi irin na nutsatstsun daddatawa kana yace " hummm yaro dai yaro ne,
k'uruci dangin hauka kowa ya gama ki lafiya ya nad'e,
wannan maganar taku ai babu komai cikinta sai shirme,
abu kamar a garin gab'a-gab'a ko shirin film,
ina kuka tab'a ganin anyi haka..!?
" Dan Allah Papu ka taimaka min,
Khulud ta fad'a tana kuka,
murmushi ya kuma yi yace " hakan ba abune da zai yiyiyu ba,
zatayi magana ya d'aga mata hannunshi had'i da cewa " that's impossible tayaya hakan zai faru in real life...!?
" Idan dai kina da wani abun ki fad'a amma ba wannan ba,
" please Papu ka taimaka min,
" ban san gardama Khulud Papu ya fad'a,
ba musu Khulud ta mik'e ta fita jikinta a sanyaye,
yayinda farin ciki fal ran Sanah duk da tasan hakan bazai tab'a faruwa ba dama,
Papu yabi bayan su da kallo yana mamakin tsantsar k'uruciya da wautarsu,
haka suka koma gida jikin Khulud a sanyaye,
bedroom d'in Sanah ta wuce ta kwanta saman bed had'i da rufe idanta,
ta shiga tunanin mafita tasan dai dole sai Papu ya amince hak'onta zai cimma ruwa,
tunda dole shike da ikon d'aurawa Hanash aure,
ko da ace d'in Hanash bai sani ba,
da ya kira ta kanta shirya cewa tayi ya bari sai gobe yau bata tafiya,
haka ta kwana tana sak'e-sak'e,
har garin Allah ya waye bata runtsa ba,
a b'angaren Papu kuwa mamaki yayi tayi yana al'ajabin wannan abu,
minti d'aya zuwa biyu sai ya sauke ajiyar zuciya had'i da cewa hmmm,
ko da Mimmee ta dawo ta tambaye shi me yakawo su Khulud murmushi yayi mata yace " rabu da su shirme da k'uruciya ke damunsu,
" Allah ya kyauta Mimmee tace batare data k'ara neman k'arin bayani ba.
Washe gari tunda sassafe Khulud ta tashi, ta tashi Sanah,
bata ko bari sunyi breakfast da wanka ba,
ta uzzurawa Sanah suka tafi gidan Papu,
ko su Mamu basu san fitar su ba,
Sanah binta kawai take tayi tana dariya ciki-ciki dan tasan is so hardly Papu ya amincewa shirmen nata,
k'arfe tara na safe 9:00am suka isa cikin parlor'n,
babu kowa sai Wajnah da Zohal dake zaune suna k'ara kallan maimaicin film d'in da ake yi a MBC Bollywood,
" ah Sanah dama kina nan...!?
Murmushi tayi tace " ga tabbas,
tun ranar walimarku bamu sake had'uwa ba we missed you,
murmushi tayi tace " eh nayi busy a makaranta ne,
" Allah taimaka,
" Amin ya Rabbi,
gudun kar suja hirar Khulud tace " Papu na ciki..!?
"Eh yana ciki,
" Mimmee fa..!?
"Bata nan taje Da'awa kin san tun 8:30am na safe suke tafiya,
" yauwa Papu ya tashi..!?
"Ban sani ba bari dai na duba maki,
" Ok nagode sosai,
bata jima ba ta dawo tace " eh ya tashi yace ku shiga,
zaune suka iske shi ya d'an kishingid'a,
bai nuna musu komai ba, ya tare su faran-faran cikin fara'a,
gaida shi sukayi kana Khulud tace " please Papu taimake mu ni da Hanash dan Allah,
" Khulud abinda bazai yiyiyu bane,
tayaya hakan zata yi yu,ta yaya zan d'aura mata aure bayan iyayenta na raye...!?
" Kuma shi kanshi mijin bai sani ba, ta yaya za'ayi ta haihun..!?
Sosai Khulud ta saka rikitaccen kuka, had'i matsawa ta rik'e k'afar Papu tace " Allah Papu zai yiyiyu, nothing is impossible,
ni dai rok'a na kawai ka yarda ka amince ka d'aura musu auren,
sauran aikin kuma ka bar mana,
mu mata mun san duk hanyar da zabi hakan ta yiyiyu,
shekara d'aya kawai zasu yi kota haihu ko bata haihu ba shikenan sai a raba auren,
dan Allah Papu ka taimake ni ka rufa min asiri,
washe garin auren mu da Hanash,
kai da kanka fa kayi min alk'awarin duk abinda nake so zaka min shi,
kai kace man duk abinda nake so na fad'a maka zakayi min koma menene,
ku fa iyayen mu ne bai kamata ace ku ke karya alk'awari ba,
saboda kunfi mu sanin darajar alk'awari,
daga gare ku muke koyi dan Allah Papu karka k'i taimaka min,
idan kak'i wallahi mutuwa zanyi,
ta fad'a tana rik'e da k'afarshi,
cikin matsanancin kuku.
Kanshi ya girgiza cikin kokonta yace " kai..! hmmm uhunnnn!,
Khulud ina tsoran abinda ka iya zuwa ya dawo,
da sauri ta kuma k'ank'ame k'afarshi had'i da sanya gigitaccen kuka tace " Papu munje America ni da Hanash ganin Doctor an kuma tabbatar mana bazan tab'a haihuwa ba har abada!
zabura sosai Papu yayi yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
yaushe hakan ta faru Khulud..!?
" Wata d'aya kenan,
za kuma ka iya kiran agent da Doctor d'in family ka tambaye su،
duk suna da masaniya, nasan yadda Hanash yake matuk'ar san yara,
ni kad'ai nasan irin halin daya ciki akan rashin haihuwa ta,
wallahi nasha ganinshi yana kuka,
ya kuma yi rantsuwa da Allah har abada bazai tab'a kara aure ba ko me za'ayi mishi,
dan bai sha'awar mata biyu,
Papu kasan rayuwa kowanne d'an Adam kashe uku ce,
rayuwa ta farko hannun iyayenshi,
rayuwa ta biyu hannun matarka,
idan mace ce hannun mijinki,
(hannun abukanan zaman rayuwa)
rayuwa ta k'arshe hannun 'ya'yanka,
wanda daga k'arshe hannunsu zaka koma suci gaba da kula dakai da duk abinda ya shafe ka,
tun daga kan abinci, lafiyarka, suturarka da sauransu,
yanzu Papu idan mu bamu taimaki Hanash mun gina mishi rayuwarshi ta k'arshe ba wa zai taimake shi...!?
"Dan Allah Papu ka taimake mu ni da Hanash,
tunda ita Sanah ta yarda ta amince,
ajiyar zuciya Papu ya sauke cikin tsantsar tausayawa da karayar zuciya,
ya san duk maganar da Khulud ta fad'a gaskiya ce amma yana san ya tabbatarwa kanshi,
dan haka ya ciro wayarshi ya kira agent,
tana soma ringing yayi picking,
bayan sun gama gaisawa Papu yace " a cikin family akwai wanda yayi tafiya nan kwana kusa..!?
"Eh Sir..!,
" waye ..!?
" Hanash da Khulud sunje America last month,
" ok me sukaje yi..!?
" Ganin Doctor,
bai kuma magana ba, ya kashe ya kira family Doctor,
shima yayi mishi tambayoyi ya amsa mishi ya kuma tabbatar mishi Doctor John dake k'asar America yace har abada Khulud bazata tab'a haihuwa ba,
godiya Papu yayi mishi kana ya kashe wayar,
ya mayar da kallanshi ga Sanah da gabanta ke ta faman fad'uwa saboda tsoro da fargabar ganin Papu na niyyar amincewa,
duk ilahirin jikinta kerrrrma yake yana tsuma,daurewa kawai tayi,
cikin tausasa murya Papu ya kira sunanta,
"Sanah..!,
kanta k'asa ta amsa " na'am
" kin tabbatar kin yarda kin amince..!?
Shiru tayi batare datace komai ba,
zungurarta Khulud tayi, kanta k'asa hawaye na rubdugun zubo mata tace " eh...!,
" ba eh zakice ba, cewa zakiyi kin yarda kin amince,
cikin sanyin murya tace " na yarda na amince,
ya kuma cewa " kin tabbatar kin yarda kin amince?
" Eh na yarda na amince,
sai da Papu ya tambayi Sanah sau uku tana amsa mishi,
kana ya kalle Khulud yace " nima *NA AMINCE!!!* amma for just 1yr auren ba zai wuce shekara d'aya ba,
sosai Khulud take kuka tana yiwa Papu godiya,
murmushi yayi yace " tom ku fad'a min yadda kuka tsara abun,
" yanzu ta su Abbu zamu fara zamu yi takardar coppers na zuwa bautar k'asa akan Sanah,
tun yau zata yiwa Abbu maganar cewa takardarsu ta service ta kusa fitowa,
"ta yaya bayan sun san a level 3 nake..!?
Sanah ta fad'a cikin mamaki,
" Eh kokwanta zamu saka musu,
sannan Papu ne zayyi maganar takardar,
ta hanyar abokanansa duk da bamai kyau bace fake za'ayi,
sannan ranar da zaki kaiwa Abbu takardar zai kasance ni da Papu muna gidan yadda zamuyi karaf mu amsa,
ajikin takardar zamu saka an kaiki irin k'auyikan gudun nan masu nisa,
yadda dole sai kin gama kafin ki dawo,
then Papu zai bawa Hanash aiki ya zama busy ,
sannan dole fa sai dasa bakin Family Doctor,
dan shine zai sanar da Hanash cewa akwai wani Doctor a America dayake yin dashen mahaifa,
so idan yana busy kinga babu yadda za'ayi mu tafi dole ni kad'ai zan tafi,
idan munje sai muje wajen Chris shine zai kaimu inda za'ayi mata fuska,
sauran aikin kuma namu ne،
ajiyar zuciya Papu ya sauke yana tsantsar mamaki,
sauke cikin ranshi yace " lalle mata sai a barsu, ko shi kanshi bazai tab'a iya tsara wannan abun ba,
shiyasa akace duk abinda ya gagari maza a bawa mata su zasu iya,
a fili yace " tom yanzu ta maganar tafiya bautar k'asa za'a fara,
yanzu idan kun koma kuyi mishi maganar amma ku tsara abun yadda kokwanta bazai shiga ranshi ba,
suka amsa mishi da tou,
sun dad'e suna k'ara tautaunawa kan al'amarin kafin suyi mishi sallama har sun kai bakin k'ofa Papu yace " Khulud! Sanah!,
a hankali suka juyo yace " zanyi wannan abun ne saboda kun amince da kuma farin cikin Khulud,
amma duk abinda ya faru daga baya ba ruwa na,
duk abinda ya biyo baya babu ruwa na,
koda abu ya rincab'e ya cab'e daga baya karku yi kuka dani,
kun amince...!?
Sanah batayi mishi magana ba,
sai ido data zuba mishi,
Khulud tayi murmushi had'i da cewa " in sha Allah babu ma abinda zai faru ko ya biyo bayan sai alkhairi,
"Allah yasa,yace,
kana suka fita, suna fita wayar Sanah ta soma ringing da sauri tayi picking,
" hello Mrs Aryan Rayyan Moli,
murmushi tayi had'i da lumshe idanta,
yace " ya kika tashi..!?
"Alhamdulillah,
" ina busy ne kiranki nayi na sanar dake su Hilwa sun taho ki fad'awa Abbu suna hanya..............
_Who will win between ARYAN & KHULUD_
_Who is the winner and the loser ?_
MOMYN ZARAH
[7/7, 5:44 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
4⃣3⃣
Ido ta zaro cikin tsantsar farin ciki dan tasan matuk'ar suka zo shirin Khulud ya lalace,
tace " da gaske dan Allah Hub..!?
"Uhmmm wannan duk d'okin auren ne..!?
" Hmm bazaka gane bane,
" a'a zan gane idan an fad'a min,
Sanah tayi murmushi had'i da cewa " Hub seriously sun taho..!?
" A'a da wasa nake miki Hilwa bai nan sunyi tafiya da president sai bayan 3 weeks zasu dawo,
idan sun dawo zasu zo,
wata irin razananniyar fad'uwa gaban Sanah yayi tamkar an buga mata dalma haka taji,
cikin ranta tace " انا لله وانا اليه راجعون اللهم اجرني في مصيبتي واكلني خير منها,
ya Rabbi ka fitar da dani daga cikin tsaka mai wuya ka zab'a min abinda yake alkhairi a gare ni,
" K'ALB ya kika yi shiru..!?
Yak'e tayi wanda yafi kuka ciwo tace " ka rik'e a ranka ina matuk'ar sanka sosai,
ba kuma zan tab'a yin abinda zai cutar da kai da rayuwarka ina sane ba,
" I knew yace yana dariya,
"My life yanaji ki kamar a waje..!?
" Eh na raka my Khulud unguwa ne,
" ok take your time idan kun koma gida ki kira ni,
" ok badamuwa I love you so much,
" I love you too,
murmushi kawai Khulud tayi batare datace komai ba,
bayan sun koma gida sunci abinci,
Khulud tace " bari nayi wanka sai mu fita muyiwa Abbu maganar bautar k'asar..!
Sanah batayi magana ba, tayi shiru,
Khulud ta shiga wankan, safa da marwa Sanah ta soma yi tana tunanin mafita da abinyi,
tana cikin haka Khulud ta fito,
duk da ta lura da halin da Sanah take ciki,
amma sai tayi burus tamkar bata lura ba,
kayan Sanah ta saka kasancewar bata zo da kaya ba,
kallo d'aya zakayi mata ka fuskanci tana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa,
batayi mata magana ba, ta rik'e hannunta sukayi parlor dan taji muryar Abbu,
zama sukayi kusa da dashi suna hira sosai,
yana kuma basu lokacinshi sosai,
kallan Sanah Khulud tayi, tayi mata alamar tayi mishi maganar,
amma Sanah tayi burus tamkar bata san abinda Khulud ke nufi ba,
k'afa Khulud tasa ta tab'o Sanah had'i da motsa lips d'inta tace " talk..!,
ta fad'a yadda babu mai jinta,
still shiru Sanah tayi, ganin bata da niyyar yi mishi magana yasa Khulud,
cewa " hmmm Sanah ba tare kuka fara BUK dasu Wajnah ba ne..!?
"Eh..!, tace
batare data kalle ta ba,
" naga suna maganar tafiya service next week,
ya banji ke kina maganar ba..!?
" Eh..! so nake sai takardar ta fito sannan sai na fad'awa Abbu,
kallanta Abbu yayi kai badai har bautar k'asar tazo ba..!?
Karaf Khulud tayi tace " wallahi kau Abbu ai abun ba wuya,
gashi nima har nayi 3yrs da aure,
kuma tun kafin inyi aure ta soma fa,
" kai masha Allah, yanzu shekara ta zama kamar kwana,
babu wuya kaji ta zagayo,
" eh nima dana ji su Zohal na maganar nayi mamaki,
dan k'in yarda Papu yayi sai da yaje har makarantar ya tambaya,
murmushi Abbu yayi yace " ai ba'a k'arya da bautar k'asa,
kuma duk inda mutum yakai da wayo da lura akan yaran yanzu sai dai idan basu ga damar yin abun ba,
sai dai kawai mutum yayi iya k'ok'arin shi ya barwa Allah sauran,
ka kuma yi addu'a, ka tsarkake zuciyarka akansu,
shine kawai mafita,
ajiyar zuciya Khulud ta sauke cikin tsantsar farin ciki,
tace " that's why I really love you my Abbu,
kuma kasan our Sanah she will never hurt, chet and betray us,
murmushi yayi yace " haka ne kam Allah ya taimaka,
suka amsa da Amin,
ita dai Sanah shiru tayi har suka gama hirarsu,
suna komawa bedroom Khulud ta kira Papu ta sanar dashi yadda sukayi da Abbu,
yace " good in sha gobe zan kawo miki foam d'in,
ta amsa da to had'i da yi mishi godiya,
duk yadda Hanash yaso Khulud ta koma gida k'in komawa tayi,
dan gani take muddin tayi sake tabar gidan komai lalacewa zayyi,
akan dole ya hak'ura ya barta.
Tun a ranar Papu yayi duk cuku-cukun da zayyi akan ya samu fake copper foam,
washe gari cikin ikon Allah Papu yayi sa'a ya samu foam d'in,
dan sawa yayi aka buga mishi guda uku sak harda nasu Wajnah da Zohal duk da sunayen su jiki,
Khulud ya kira ya shaida mata cewar an samu foam d'in,
dan haka yau zai k'irk'iri zuwa gidan wajen su Abbu da Dide,
kuma idan ya tashi zuwa zai zo dana su Wajnah cikin aljihunshi,
dan haka su zo mu amsa amma ba gida zasu zo ba,
dan gudun kar Mimmee tayi wani zaton,
a bakin titi suka had'u da Papu ya basu foam d'in,
kana yace musu kar su bayar sai da daddare idan sun tabbatar da yazo,
suyi k'ok'ari su bayar a gabanshi,
Khulud ta amsa da to,
dan duk abinda ake yi Sanah bata cewa komai,
tun a gabansu Papu ya kira Dide,
bayan sun gama gaisawa Dide yace " kuna gida yau ni nazo zumunci tunda ku kun kasa...!?
Murmushi Dide yayi yace " ai ko muna busy dole muyi cancel d'in komai,
saboda muna da babban bak'o,
murmushi Dide yayi yace " tom yau zanzo bayan sallar ishsha in sha Allah,
kana sukayi sallama ya kashe wayar,
su kuma suka koma gida,
Dide ya kalli Abbu yace " wai 'yarka lafiya kuwa..!?
Cikin mamaki Abbu yace " wacce 'yar tawa..!?
"Khulud mana..!
" me ka gani..!?
Cewar Abbu,
Dide yace " gani nayi yau kusan kwananta uku a gida,
kuma mijinta kullum sai yazo d'aukarta tana k'in binshi,
yanzu kuma Alhaji Waseef ne ya kira ni, wai zaizo yau,
shiyasa nayi tunanin kodai akwai wani abu tsakaninta da mijinta،
k'in fad'a dai kawai tayi,
shiru Abbu yayi yana nazari kafin yace " to Allah dai yasa lafiya,
idan yazo zamu ji koma meye,
da daddare wajen 8:20pm na dare,
Papu yayiwa Abbu waya ya shaida mishi yana harabar gidan,
cikin fara'a Abbu ya mik'e yana wayar manne da kunnenshi,
Dide yace " ya k'araso ne..!?
Ya fad'a yana mik'ewa shima,
tare suka je suka, suka taro shi,
babban parlor'n gidan aka kaishi,
dama sun kafin yazo an gama cika wajen da kayan ciye-ciye da motsa baki,
hira suka shiga yi sosai cikin kwanciyar hankali,
ganin har 9:00pm na dare, su Sanah basu fito ba,
ya sashi yiwa Khulud text,
_"Na zo tun d'azu ina parlor'n k'asa_
Khulud kwance saman bed tana jiran Sanah ta fito daga bathroom,
taji k'arar shigowar text da sauri ta duba,
ganin Papu ne yasata saurin mik'ewa had'i da zumbula hijab,
" my Sanah yi sauri ki fito please Papu yazo tun d'azu mu yake jira,
ji tayi gabanta ya kuma yankewa ya fad'i,
cikin mutuwar jiki ta fito, a bakin k'ofar bathroom d'in ta iske Khulud rik'e da hijab & foam d'in,
tana fitowa ta mik'e mata hijab d'in ta sanya kana rik'e hannunta,
daga k'ofar parlor'n suka tsaya sukayi sallama aka basu izinin shiga,
kana suka shiga kansu a k'asa suka gaida iyayen nasu,,,,
cikin fara'a tamkar babu wani abu a tsakaninsu Papu ya kalle su yace " masha Allah manyan gobe,
Abbu yayi murmushi kana yace " ya akayi...!?
Shiru Sanah tayi batayi magana ba,
sai Khulud ce tace " Abbu foam d'inta ne ya fito,
ta fad'a cikin d'oki tamkar da gaske ne,
cikin mamaki Dide yace " foam d'in me..!?
"Service Khulud tace,
" service kamar yaya Dide ya fad'a idanshi kansu,
sai da gaban Khulud yayi muguwar fad'uwa kana tace " na bautar k'asa fa Dide,
Dide zayyi magana Papu yayi saurin cewa " ikon Allah ashe tare kuke dasu Wajnah...!?
"Eh ai makarantar mu ma d'aya class d'in mu d'aya, tare mukayi candy dasu,
Papu yace " nima sun kawo min foam d'in su yau da zan fito,
ni kuma ina sauri na saka shi cikin aljihu sai yanzu da kukayi maganar na tuna ya fad'a yana ciro foam d'in,
Abbu na murmushi ya amsa Dide kuma ya amshi na Sanah,
ido Dide ya zaro yace " tab Damaturo aka kaiki Sanah...!?
"Eh tace cikin rawar murya,
Papu ya amsa yana dubawa yace " ah ai kamar inda aka kai Zohal ne ma ko...!?
"Eh..! Dide yace, to amma mu da bamu da kowa a can bamu kuma san kowa ba,
ya za'ayi mu tura 'yar mu mace can...!?
Da sauri Papu yace " ai acan Yaya na yake aiki,
idan badamuwa sai su tafi tare da Zohal d'in zanyi mishi magana duk nasan babu damuwa,
in yaso sai Hanash ya kaisu tare idan sun tashi tafiya,
Abbu yace " Alhamdulillah ba damuwa ai,
ai an riga an zama d'aya koba auratayya tsakani akwai alak'a mai girma,
idan shi d'in ya yarda ya amince shikenan sai su tafi taren,
Dide yace " d'azu ma Alhaji Mudu yace min takardar yaran shi ta fito har su hud'u kuma duka kudu aka kaisu,
" eh dama na kudu suke kawo nan,
su kai na nan can,
a hankali Sanah ta mik'e had'i dayi musu sallama ta fita,
Khulud tabi bayanta,
sai da su Papu suka kuma shan hira sosai kana yayi musu sallama ya tafi,
duk wanda aka fad'awa Sanah zata tafi service a cikin gidansu sai yayi kokwanta ayi ta lissafin shekaru,
amma dayake ga foam kuma duk wanda aka tambaya sai yace eh foam d'in masu tafiya service na wannan shekarar ya fito,
still kuma ga su Wajnah da Zohal ma nasu ya fito,
ga na 'ya'yan abokanan su Dide da yawa ya fito yasa basu wani tsaya yin bincike ba suka yarda.
Da lokacin Dinner & convocation,
ana gobe za'ayi Sanah tayi kwace tana taita murk'ususu,
wai bata da lafiya cikinta ke ciwo,
ranar a hospital suka kwana, wata yarinya Khulud ta samu suka had'a baki ta kawowa Sanah irin ankon rigar da ake yi ta gama University,
har gida da sunan tata ce,
Ko da ranar tafiya tazo sosai Khulud ta rink'a kuka tana rungume Sanah tamkar ranta zai fita,
ita kanta tayi mugun mamakin wannan acting d'in na Khulud,
kasancewar Papu ya tsara komai,
dan haka yasa Mimmee da Jaddah da Wajnah suka tafi unguwa,
ya kuma cewa Zohal ta shirya kayanta zasu tafi Abuja,
a ranar yasa ta shirya tsaf ta fito da trolley d'inta harabar gidan,
kana ya saka Hanash yaja motar shi yana zaune a gaba,
Zohal na baya, suna isa gidan Papu ya kira Dide da Abbu ya sanar dasu sun k'araso,
gaba d'aya Hard'o family's suka fito mazansu da matansu aka rako Sanah har jikin mota,
Hanash ya fito ya sunkuya har k'asa ya gaida surukanshi,
Abbu yace " thank you so much Son,
Allah ya kiyaye hanya Ubangiji ya tsare,
Allah kaiku lafiya ya maido ku lafiya,
cikin rashin fahimta Hanash ya amsa da Amin,
Dide ya kalli Zohal yace " idan anje a dage please a kama kai a tsare mutuncinmu,,,
Zohal ta d'auka akan inda zasuje da Papu ne dan haka ta amsa da " in sha Allah,
Sanah da Khulud da Wajnah suka zauna a baya,
Papu da Hanash suna gaba,
Hanash yaja motar,
suna ta d'aga mata hannu,
duk wannan abun da ake yi babu abinda ya ragu daga cikin soyayyar Sanah da Sir Moli,
kullum sai sunyi waya kamar yadda suka saba,
sosai ya fuskanci tana cikin damuwa,
amma duk sanda ya tambaye ta,
amma amsa d'aya take bashi babu komai kanta ke ciwo,
daga d'aya b'angaren kuma ana ta shirye-shiryen tafiyarsu,
suna fita daga sashen unguwar su Abbu,
Papu ya kalli Hanash yace " muje gidanku ka d'auki motarka,
babu gardama Hanash yayi gidanshi,
cikin ranshi yana mamakin inda Papu da Zohal da Sanah zasu je,
suna isa gidan Hanash da Khulud suka sauka,
Papu ya k'arb'i tuk'in motar,
k'ofar wani gida Papu yakai Sanah gudan kar Zohal ta kawo komai cikin ranta,
yace " ki tabbata kin gama da wuri kin koma gida, kar Abbu yayi miki fad'a kinji,
ta amsa da " tou nagode sosai,
kana yaja motarshi,
da sauri ya k'arasa gidanshi,
ganin sun dawo gida Zohal tace " Papu mun fasa yin tafiyar ne..!?
"Eh wai ba jirgi sai next week dole,
baki ta turo cikin shagwab'a ta soma k'ok'arin yin kuka,
dakyar ya lallasheta suka shiga cikin gidan yasata dafa mishi coffee,
ya zauna a parlor, dan kawar da tunanin komai cikin ran Zohal yasa Papu bai fita ba,
Sanah kam kamar yadda suka tsara haka tayi Papu na ajeta,
ta tare adai-daita sahu, tayi gidan Khulud,
daga nesa ta tsaya had'i da kiranta,
dama tasan Sanah zata kira ta,
dan haka ta k'i shiga bedroom d'inshi ta zauna parlor,
da sauri tayi picking,
Sanah tace " na zo wajen,
"Ok Khulud tace kana ta mik'e,
harabar gidan taje ta bawa mai gadi 1k tace " please Yk siyo man credit mana ina cikin magana ya k'are,
jikinshi na kerrrrma ya amsa had'i da fita,
tana ganin ya fita, ta mayar da wayar kunnenta dan dama batayi dropping ba,
tace " ki k'araso,
umarni ta bawa mai dai-daitan,
ya kaita har k'ofar gidan ta bashi 1k bata tsaya karb'ar canjin ba,
ta shige,
da sauri Khulud ta kama jakarta suka shigar cikin gidan,
d'aya bedroom d'in mai Italian bed can Khulud takai Sanah,
dan kwata-kwata basu amfani dashi,
kuma tun ranar da aka kawo ta Sanah ke bala'in san kayan d'akin,
dan har cewa tayi idan ta tashi ko an daina yayinsu sai ita ta saka a gidan ta,
a saman bed duk suka zauna,
a hankali Khulud ta mik'e had'i da soma shirya mata kayanta cikin wardrobe,
tana jera kayan shafarta saman mirror,
d'aya bakin k'ofar parlor ta jiyo sallamar mai gadin,
da sauri ta fita,
" Hajiya gashi ya fad'a yana mik'a mata,
" ka barshi na siya ta banki,
sosai yayi mata godiya kana ya juya yacewa " aiko wallahi naidawa zanyi yaban kud'in dan ban iya saka katin dubu d'aya,
da sauri ta koma bedroom d'in Sanah had'i da danna key,
sai da ta shirya mata komai tsaf har bathroom sai da ta shirya komai,
shower gel, sponge, soap, towel da sauran kayan bathroom,
d'akin da ban d'akin sukayi d'as tamkar turai komai yayi luf-luf,
kasancewar Sanah bata san yin magana yasata kwanciya saman bed had'i da lumshe idanta,
zama Khulud tayi a gefenta tana ta bata hak'uri had'i da k'ara lallab'ata,
daga parlor ta jiyo muryar Hanash yana kiranta,
da alama ya shiga bedroom d'inta bai ganta,
da sauri ta fita ta same shi a parlor,
ya kalle ta yace " ina kika shiga ne ina ta faman kiranki shiru...!?
"Eh..! fita zakayi ne..!?
Ta fad'a dan kawar da wancan maganar,
" eh..! yanzu Papu ya kira ni yace yana san gani na yanzu,
yi tayi kamar bata san abinda Papu zai fad'a mishi ba,
tace " to Allah dai yasa lafiya,
" amin, ko zaki ne..!?
"A'a kaje baka san maganar da zayyi dakai ba,
Allah ya tsare..!
" Amin yace yana fita,
yana fita ta dannawa k'ofar key,
kana ta koma wajen Sanah,
kwance ta iske ta tana kuka mara sauti,
da sauri Khulud ta k'arasa gare ta,
cikin tashin hankali ta soma kukan itama tana bata hak'uri,
sai dakyar Sanah tayi shiru,
kana Khulud ta had'a mata ruwan wanka a bathroom ta shiga,
kafin ta fito ta had'o mata abinci a tray ta kawo mata,
sai da ta gama shiryawa kana Khulud tace " kici abinci..!,
" na k'oshi tace a tak'aice,
sai da taga Khulud na kuka wiwi kana ta d'anci,
babu yadda batayi da ita ta fito parlor ba amma fur tak'i,
tace bacci zatayi,
da Hanash ya dawo a parlor ya zube kusa da ita,
kallo d'aya tayi mishi tace " lafiya na ganka haka cikin damuwa..!?
" Ba dole ki ganni haka cikin damuwa ba,
wai Papu ne yace daga yau ni zan dama madadinsa a Dikko companies,
ni zan zama manager, wai daga gobe zan fara aiki,
yi tayi kamar bata san da maganar ba,
cikin tsantsar farin ciki tace " Alhamdulillah masha Allah gaskiya naji dad'i nayi kuma farin ciki matuk'a,
da Papu yaga magajinshi tunda ranshi,
ai dama kamata yayi yanzu Papu ya huta kai kuma ka karb'i ragamar komai,
" to amma aiki na fa..!?
" Ka rubuta resigning latter ta cewar ka aje aiki kawai,
ka cigaba da kula da dukiyar ku,
cikin lallami ta kwantar mishi da hankali,
kana ta bashi abinci ya ci yayi wanka,
yana yin bacci ta tashi ta koma wajen Sanah,
ta cigaba da lallaminta had'i da bata hak'uri tana rarrashinta,
har ta samu tayi bacci,
nan gefenta Khulud ta kwanta had'i da ja musu bargo,
tunda suka tashi sallar asuba Khulud bata koma bacci ba,
kasancewar yau Hanash zai fara fita office d'in Dikko companies a matsayin manager,
k'arfe tara dai-dai (9:00am) na safe ya gama duk shirin shi ya fita,
yana fita ta nufi bedroom d'in Sanah,
ganin bata tashi ba, yasata kwanciya kusa da ita.
Baya kwana biyu
Haka Sanah take rayuwa gidan Khulud,
cikin bedroom kullum duk nacin Khulud kan ta fito parlor bata fitowa,
haka zata zauna tayi ta kuka, wani lokacin tana kukan ma bacci yake d'auke ta,
a b'angaren Hanash kuwa sosai ya zama busy dan sosai Papu ke tula mishi aiki,,,
idan ya fita tun 9:00am baya dawowa sai 7:00pm wani lokacin ma har 9:00pm yake kaiwa,
daya dawo kuma sai wanka cin abincin da bacci,
ranar da akayi kwana biyu da barin Sanah gida Doctor ya kira Hanash ya shaida mishi cewar akwai Doctor d'in dayake yin dashen mahaifa a America kuma har a haihu,
sosai Hanash yayi farin cikin jin wannan labarin,
yasa Doctor d'in ya nemar musu appointment,
suna gama waya ya kira Agent ya sanar dashi ya nemar musu visa America,
kana ya kashe ya kira Papu koda ya gayawa Papu yana san zuwa America fir Papu ya hana shi yace bai san zance ba,
duk yadda Hanash yayi tayiwa Papu magiya yana rok'onshi k'in amincewa yayi,
jikinshi a sanyaye ya kira Khulud ya sanar da ita akwai Doctor d'in dayake yin dashen mahaifa a America,
sosai ta nuna tsantsar murna da farin ciki,
amma sai ya ce mata Papu ya hana shi zuwa,
tana jin yace Papu ya hana shi zuwa ta soma kuka sosai kamar ranta zai fita,
dakyar ya rarrasheta ya bata hak'uri,
kan idan ya dawo gida da daddare zasu yi maganar,
koda ya dawo gidan da daddaren yayi mata maganar sosai ta rink'a kuka tana rok'onshi ya kaita,
cikin badara tace " in banda nafi san nayi tafiyar dakai da saika saka Doctor d'in ya kai ni tun da Family Doctor ne,
an sanshi an san ahalinshi sosai,
kuma shine ma yasan Doctor d'in,
amma ni gaskiya nafi san nayi tafiyar dakai,
ta jefa mishi maganar cikin bashin shi da tunaninshi,
shiru yayi yana zanari kana yace " to mai hana ku tafi da Doctor d'in in yaso daga baya ni sai na biyo Ku...!?
"A'a ni dai nafi san nayi tafiyar dakai please,
dakyar Hanash ya rarrashi Khulud ta yarda zatayi tafiyar da Doctor d'in,
anan take Hanash ya kira Doctor ya shaida mishi shi bazai samu damar yin tafiyar ba,
amma shi da Khulud zasu je, kuma yana san ya kasance cikin sirri bai san kowa ya sani,
dan haka ya kaiwa Family agent passport d'inshi gobe dan yana san suyi mafiyar cikin satin nan,
Doctor ya amsa da to,
kana ya kira agent yayi mishi bayanin komai, shima yace " babu damuwa zayyi k'ok'ari ya samar musu visa cikin 2days.
Wasa-wasa k'aramar magana ta zama babba,
dan kwata-kwata tunanin Sanah bai tab'a bata faruwa wannan al'amari ba sai hau da taga visa su fito,
Papu shine ya nemar mata visa while Hanash kuma ya nemarwa Doctor da Khulud,
a yau k'arfe 2:10am na dare jirginsu zai d'aga zuwa Abuja daga Abuja kuma zasu je Addis Ababa dake k'asar Ethiopia,
daga can ne jirginsu zai d'aga zuwa America,
tun k'arfe 12:00am sukayi da Papu zai zo ya d'auki Sanah,
kasancewar Hanash ne zai kai Khulud zuwa Airport,
Khulud na ganin lokacin da suka tsara yayi ta shi,
ta tashi cikin sand'a ta fita daga bedroom d'inshi ta shiga na Sanah zaune ta iske ta,
tana sharar hawaye kamar yadda ta saba,
cikin rarrashi Khulud ta k'arasa gareta tace " I'm sorry my Sanah,
ta fad'a had'i da dafa kafad'arta,
batayi magana magana ba, ta mik'e ta fita,
da sauri Khulud ta ja trolley data shirya kayan Sanah ciki tabi bayanta,
sad'af-sad'af suka lallab'a suka suka fita,
cikin sand'a ta bud'e get d'in ta k'aramar k'ofa Sanah ta fita,
tana fita ta iske Papu yana jiranta,
ta shiga had'i da gaidashi ya amsa cikin tsantsar tausayawa,
kana yaja motar suka nufi Airport,
k'arfe 1:30 Khulud da Hanash suka isa Airport d'in dan matsa mishi tayi kan sai sun fito da wuri,
Doctor da Papu & Sanah na can zaune,
a reception suna jiran su,
text ne ya shigo wayar Papu yayi saurin dubawa,
_" mun shigo cikin Airport d'in yanzu gamu nan muna gaf da reception_
da sauri Papu ya mik'e had'i da jan trolley d'in Sanah yace " Doctor gasu nan zuwa idan Hanash yazo kayi k'ok'arin sallamarshi da wuri please,
"Ok Sir Doctor yace cikin girmamawa,
su Papu na shan kwana Hanash da Khulud na k'arasowa,
sosai take kuka tana marairaice mishi,
dakyar suka rabu ya tafi sukayi kamar sun shiga ciki,
yana juya baya Doctor yabi bayanshi,
sai da yaga tafiyarshi, kana ya sauke ajiyar zuciya ya dawo ya shaida musu,
sosai Papu yayiwa Doctor gargad'i had'i da dank'a mishi amanar su Sanah a hannunshi,
hannu bibbuyu Doctor ya amsa,
kasancewar yasan kome dan basu b'oye mishi komai ba,
dashi aka shirya plan d'in.
K'arfe 4:00pm na yamma na k'asar America jirginsu ya sauka a Airport,
bayan sun sauka a masaukin su,
sunyi wanka sunci abinci
basu wani b'ata lokaci na suka nemi Chris,
shine da kansa yazo ya d'auke su yakai su wajen da ake k'era fuska dama jikin mutum gaba d'aya idan kana so,
bayani sukayiwa shugaban company kan suna san ayi musu irin fuskar Khulud komai da komai,
in fact ma suna san a mayar da Sanah kamar Khulud a jiki,
batare da b'ata lokaci ba aka suka shiga gwaje-gwaje da aune-aune,
sai da aka d'auki duk abinda ake buk'ata ya kuma dace kana,
aka koma ga jikin Sanah, dan tafi Khulud 'yar k'iba boobs & hips,
sai da suka saka su a scale suka auna nauyinsu,
suka tabbatar dole sai Sanah tayi slimming ta rage k'iba kana,
kasancewar akwai issun kud'i enough yasa aka fara aikin,
cikin sati d'aya aka gama komai Sanah tayi slimming sosai ta koma tamkar Khulud,
dan sai da aka kuma auna nauyinsu aka tabbatar yayi dai-dai kana,
idan ka kalli fuskar da akayi ta Khulud sai ka rantse kan Khulud ne aka sare aka aje,
saboda babu abinda suka bari,
dai-dai da tauwadar Allah dake gefen hab'arta sai da sukayiwa fuskar,
fuskar robar tayi tamkar fuskar Khulud ta gaske,
kai idan ka gani sai ka rantse ba fuskar roba bace ta gaske ce,
lokacin da Sanah ta gwada fuska dan a tabbatar da tayi dai-dai sai da su kansu taurawan da suka k'erata sukayi tsananin mamaki,
dan koda Juju (mahaifiyar Khulud) za'a kawo ta fidda wacece Khulud d'in ainahi,
bazata tab'a iya banbancewa ba,
su kansu sai da kansu yayi masifar d'aurewa,
wajen muryarsu kuma sakawa akayi Khulud tayi magana mai tsayi sukayi recording,
kana sukayi wani d'an abu kamar d'an tsinke d'an k'arami,
suka ce ta rink'a mak'alawa a bayan kunnenta ko a wuyanta idan tana san tayi irin maganar Khulud,
shima sukayi kalar fatar Sanah,
yadda idan ta saka duk nacinka baka isa ka ganshi ba,
dan sajewa zayyi da jikinta,
data gwada saka shi tayi magana,
ni kaina Jiddarh sai da mamaki ya kusa kashe ni,
dan daga ni har su Khulud da Doctor sandarewa mukayi a tsaye,
saboda al'ajabi, dan irin muryar Khulud sak naji,
inda aka cigaba kamm an cigaba Nigeria anyi mana nisan nisa, domin akwai bambanci tsakanin technology d'in mu da nasu,
bayan an gama komai da komai,
komai ya kammala kana suka yiyo Nigeria k'asarmu ta gado,
koda suka isa basu sanarwa da Hanash ba,
sai da Papu yazo ya d'auki Sanah yakaita gidan ya aje,
bayan ya aiki mai gadin ta fito ta shige cikin gidan dan Hanash na office,
kana Khulud da Doctor suka sanarwa Hanash sun k'araso,
Sanah na shiga gidan ta wuce bedroom ta fad'a saman bed had'i da sakin rikitaccen kuka,
dan kwata-kwata bata tab'a tunanin hak'on Khulud zai cimma ruwa ba,
tun daga Airport suka rabu da Doctor shi yayi gidanshi Hanash da Khulud suka yiyo gida suma,
tana jin motsin su tayi saurin daina kukan dan kar Hanash yaji sautin kukanta.
Washe gari Hanash na tafiya aiki Khulud da Sanah suka fita suka tafi wajen Papu,
a parlor bak'i ya aje su,
kana ya fita ya kirawo driver shi da wasu mutane su shida ,
wanda shi kanshi Papun bai san ko suwaye ba,
bai kuma san daga inda suke ba,
driver shi yasa yazo dasu,
idan aka had'a da Papu da driver su takwas kenan...,
cikin sanyin jikin Papu ya kalli Sanah ya kira sunanta cikin nutsuwa,
Sanah..!,
kanta k'asa ta amsa cikin rawar murya,
duk ilahirin jikinta na tsuma na rawa,
yace " zan k'ara tabbayarki dan Allah ki bani amsa,
kin tabbatar kin yarda kin amince da wannan auren...!?
Shiru tayi ta kasa furta ko da kalma d'aya,
da k'arfi gaban Khulud ya fad'i,
Papu ya kuma maimaita mata tambayar still shiru tayi,
take gaban Khulud ya shiga dukan uku-uku saboda tsabar tsoran karta k'i amincewa,
cikin sanyin jiki ta d'ago kai ta kalli Khulud,
kallan da Khulud take yi mata ne ya tabbatar mata matuk'ar bata amince ba zuciyar Khulud tana iya bugawa nan take ta mutu,
a hankali ta lumshe idanta hawaye na zuba tace " eh na yarda na amince,
a fili Khulud ta sauke ajiyar zuciya had'i da fitar da numfashi da k'arfi,
hannu Papu ya saka cikin aljihunshi ya fidda bandir d'in 1k guda goma na 1 million naira,
ya mik'a mata had'i da cewa ga sadakinki,
cikin rawar murya tace " bandir d'aya ma ya isa,
shima kuma akai gidan marayu na yafe na yarda a bawa mabuk'ata,
ajiyar zuciya ya sauke had'i da jinjinawa jaruntarta yace " Allah yayi miki albarka,
ta amsa da amin,
shi Papun ne yayiwa Sanah waliyyanci,
driver shi kuma yayiwa Hanash,
sauran mutum shidan suka zama shaidu kamar yadda Allah yace,
anan take aka d'aura *AUREN HANASH WAEEF DA SANAH HAMRAZ*,
akan sadaki naira dubu d'ari.................!
MOMYN ZARAH
[7/7, 5:57 PM] +234 810 065 5176: _*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
4⃣4⃣
Kanta ta duk'ar k'asa cikin tsananin bak'in ciki da k'unar zuciya,
ji take yi dama mutuwarta tazo ta d'auke akan abinda take ji,
in banda ruwan hawaye babu abinda ke zubowa daga idanta,
cikin sanyin murya Papu yace " Sanah...!,
ya kira sunta cikin wata irin murya,
bata d'ago kanta ba ta amsa mishi da " na'am,
numfashi ya fitar had'i da cewa " ki kiyaye dukkan hakk'in miji da aurenki,
duk da shi mijin bai sani ba, amma ke kin sani,
duk abinda kika yi daya sab'awa dokar Allah,
Ubangiji bazai barki ba, idan kika sake kika sab'awa mijinki,
ko kika bujire mishi wallahi sai Allah ya rubuta miki alhaki,
kamar yadda yake rubutawa duk wata matar aure,
ko duk da kuwa shi mijin naki bashi da masaniya, ai ke kin sani,
dan haka ki kula sosai karki kai kanki wuta,
sosai Papu yayi musu nasiha mai ratsa jiki, zuciya da ruhi duk jikinsu yayi mugun yin sanyi,
cikin muryar kuka tace " in sha Allah zanyi k'ok'arin kiyayewa,
" Allah yayi miki albarka yasa ki gama da duniya da iyayenki lafiya,
" amin tace tana goge hawayenta,
kallanshi ya mayar kan Khulud yace " kiji tsoran Allah akan komai ki tuna Allah da mala'iku suna kallanki,
basa kuma bacci, ta sadaukar da tata rayuwar ne domin ke,
da farin cikinki, dan Allah ki kula da ita sosai,
cikin farin ciki tace " in sha Allah zanyi Papu,
kallansu yayi duka yace " tom ya maganar rabon kwana...!?
Yasan idan ya barsu ba zasu yi ba,
kuma idan akayi hakan ba'ayi koyi da cewar musulci ba,
kan Khulud a k'asa tace " zamu raba kwana bibbiyu in sha Allah,
" yauwa gwara kuyi hakan dan fitar da hakk'in junanku da kuma nashi mijin naku,
kana ya mayar da kallan shi ga Sanah yace " kina da abinda kike buk'ata....!?
" A'a tace kanta k'asa,
" kin tabbatar baki buk'atar komai Daughter...!?
" Eh tace still kanta k'asa,
" kina da account na bank...!?
"Eh...!
" bani account number zan tura miki 5 million naira na lefenki,
" nagode Allah ya k'ara bud'i da arziki,
amma dan Allah ka kabarshi bana buk'atar komai,
ido ya d'an tsura mata na wani lokaci,
kana yace " I'm sorry Daughter if I hurt you,
murmushi tayi dan karya ji babu dad'i tace " baka yi min bakomai ba Papu,
" tou idan banyi miki komai ba ki amshi kud'in lefenki tunda hak'k'in ki ne,
sai kiyi duk yadda kike so dasu,
" to nagode sosai Papu Allah ya k'ara girma,
" Amin yace,
kana ya mayar da kallanshi kan Khulud yace " ga sadakinta nan 100k, then...! ga wannan 900k d'in nan ki bata shima,
amsa tayi had'i dayi mishi godiya,
" ku tashi na maidaku dan naga yanzu 12:00pm na rana,
babu musu dukkan su suka mik'e suka fita،
bayan sun fita Papu ya kalli driver da sauran mutanen،
yace " dan girman Allah ka rik'e min sirri na,
yarda da nayi dakai shiyasa duk duniya cikin miliyoyin mutanen dana sani babu wanda na nema sai kai,
dan haka ka rik'e min alk'awari da amana ko bayan rai na dan Allah,
kanshi cikin girmamawa yace " karka damu yallab'ai idan har wanda ya mutu yana dawowa to wani zaiji maganar nan,
ni kai na naji dad'i nayi kuma alfari dana kasance ina d'aya daga cikin yardaddunka،
wad'anda ka aminta dasu har kake basu amana,
murmushi jin dad'i Papu yayi yace " nagode sosai,
kana ya mayar da kallan shi ga sauran mutanen,
yace " ku ban san ku ba amma dan Allah ku rik'e min sirri na،
suma cikin girmamawa suka amsa da " in sha Allah babu mai jin komai daga bakin mu..!
" nagode suma yace musu yana sanya hannu cikin aljihunshi,
bandir d'in 1k ya zaro ya bawa kowanne daga cikinsu bandir bibbiyu sukayi mishi godiya had'i da sallama suka fita,
shima fitar yayi yaje wajen su Khulud,
shiga cikin motar yayi kana yaja suka tafi,
tsayawa suka yi a bakin get Khulud ta fara fita ta shiga cikin gidan,
ta l'eka d'akin mai gadi taga yana sallah,
da sauri ta dawo ta rik'e hannunta had'i da yiwa Papu sallama,
ya ja motarshi yayi gaba, su kuma suka shiga cikin gidan,
suna shiga mai gadin na fitowa daga cikin d'akinshi da gudu jin an bud'e k'ofar,
ganin Khulud yasa shi tsayawa had'i da surunawa yace " ashe ke ce Hajiya...!?
Sai da gaban Khulud ya fad'i dan bata so mai gadin yaga Sanah ba,
amma sai ta dake bata bari ya fahimci wani abu ba tace " eh..!,
ni ce naga kana sallah ne,
" eh..! sallah nayi,
ya fad'a yana kallan Sanah،
kana yace " ranki ya dad'e bak'uwa kikayi ne..!?
Cikin takaici tayi murmushi tace " eh..!,
har sun juya zasu tafi yace " oh nama tuna ta ashe ba bak'uwa bace,
ai tace man 'yar uwanki ce ita,
tace yayarki ce ko..!?
A fusace tace " eh...!,
uban san jin gulma da tambayar tsiya yayata ce saura kuma naji ka fad'awa wani kaga wata,
kanshi ya sunkuyar yace " ayi hak'uri Allah ya huci zuciyarki,
" da ce maka akayi a zafafe take ta fad'a tana shiga cikin gidan rik'e da Sanah,
bayanta yabi da kallo cike da tsarguwa,
kasancewar yaro ne matashi dan bazai wuce 23yrs ba,
secondary school ya gama yana neman kud'in cigaba da karatu,
shiyasa yazo yake aikin gadi dan ya samu abinda zayyi karatu ya tallafi rayuwarshi....!
a parlor suka zube gaba d'ayansu,
karo na farko kenan da Sanah ta zauna cikin parlor tunda ta zo gidan,
kallanta Khulud tayi cikin sigar tsokana tana murmushi tace " Mrs Hanash Waseef,
sai da Sanah taji wani abu ya tsarga mata tun daga tafin k'arfata zuwa cikin kanta,
saboda dalilai biyu, na farko Sir Moli dan shi ke kiranta da Mrs Aryan Rayyan Moli,
na biyu kuma bak'ar k'addarar ta,
wato auran Hanash, cikin ranta tace " wato ruwa cikin cukali ya ishi mai hankali wanka har ya sha,
Allah mai yadda yaso mai tsarawa kowa rayuwarshi,
mutum bai isa ya tsarawa kanshi rayuwa ba,
bai isa ya kaucewa k'addarar shi ba,
duk abinda Allah ya tsara babu wanda ya isa ya hana faruwar hakan,
mutum bai isa yasan tsakiya da k'arshen rayuwar shi ba,
duk wad'annan abubuwan dake faruwa tsakaninta da Hanash amma yau itace ta zama matarshi halak malak...!,
itace yau suka had'a miji da Uludinta,
yau itake ke auran mijin her Khulud,
yau itace take tamkar matsayin *KISHIYAR KHULUD....!!!*
yau iatce zaune zaune gidan wani a matsayin matarshi ba Sir Moli ba,
tunda take a rayuwarta bata tab'a tunani ko tsammanin hakan a rayuwarta ba,
tasan kuma shima hakan ne,
yanzu tasan dole ne tayi nisa dashi far far away,
saboda kub'utar da kanta daga halaka,
da fad'awa cikin fushin Allah takai kanta da kanta wuta,
dan duk lalacewar aure, aure ne,
kuma bazata tab'a bari tayi sake wannan bazan auren dashi kanshi mijin bai san da ita ,
su kai ta wuta ba,
dan ita tana mamakin abubuwa biyu a rayuwarta,
na farko talakan da zai kai kanshi wuta,
shi a duniyar bai ji dad'i ya huta ya kuma more rayuwarshi,
yaci duniya da tsinke ba, amma kan wani d'an k'alilan abu ya tsaya ya kai kanshi wuta,
na biyu kuma matar auren da take bari aure da mijinta su kai ta wuta,
ita ba katuwa ba, ba fasik'a ba,
tana zaune cikin gidan aurenta da mijinta da yaranta ,
amma saboda tsabar san zuciya ta kai kanta wuta,
wannan abu yana matuk'ar bata mamaki sosai,
saboda daga mace har takala aljanna tana da bala'in sauk'in samu a wajen su,
ita mace idan ta kiyaye dokokin Allah,
ta kuma bi mijinta da iyayenta tayi musu biyayya shikenan,
then talaka Allah ya sauk'ak'a mishi rayuwarshi,
dan bashi da dogon hibasabi idan yabi Allah da manzonsa ya ki yaye sunnah,
ya rabu da iyayenshi lafiya shikenan,
amma saboda tsabar bala'i sai sun kai kansu wuta.
Jin tayi shiru tana tunani yasa Khulud tashi daga inda take a hankali,
ta koma kusa da Sanah ta zauna had'i da dafa ta,
cikin kwantar da murya tace " I'm very sorry My Sanah I knew I hurt you more,
dan Allah kiyi hak'uri nasan kina kallo na a matsayin mace mai matuk'ar san kanta ko...!?
Batare data kalle ta ba tace " ashe ke kanki kin san kina da san kan naki..!?
Murmushi yak'e Khulud tayi gami da cewa " nasan kuma kina tunanin saboda kece kika buge ni,
ko kamar kece silan faruwar hakan yasa nayi miki haka ko...!?
"Hmmm kawai tace had'i da k'ok'arin mik'ewa,
da sauri Khulud ta maida ta zaunen had'i da sanya kuka tace " dan Allah my Sanah karki juya min baya,
dan Allah karki bari shaid'an yayi tasiri akan mu,
yaci nasarar shiga tsakanin mu ya raba mu,
dan Allah kiyi hak'uri wallahi badan haka nayi miki haka ba,
nayi hakan ne saboda nasan duk duniya ke kad'ai zaki iya rufa min asiri,
ki taimake ni a lokacin dana fi buk'atar taimakon,
ke fa kikayi min alk'awari hakan tun muna yara,
" tunda kika fara kid'anki kina rawarki kinji nace miki wani abu ne...!?
Sanah ta fad'a tana kallanta,
" ai ko baki ce komai ba furkarki da yanayin ki sun nuna hakan koda bakinki bai kai ga furtawar ba,
ni dai dan girman Allah ki daure mu koma kamar da muyi zaman mu lafiya please،
" hmmm naji bari naje nayi wanka,
" da sauri Khulud tace " to ya maganar rabon girkin da Papu yace...!?
Ido ta k'ura mata na wani lokacin kafin tace " kiyi duk yadda kike so kamar yadda kika fara tun farko...!
Khulud na k'ok'arin yin magana tayi saurin mik'ewa ta shige bedroom had'i da dannawa k'ofar key,
dan karta shigo kwance tayi saman bed,
tana tunanin meyasa Aryan bai kirata ba yau wajen 10days kenan,
" anya yana lafiya...!?
Ta fad'a cikin ranta,
da k'arfi k'irjinta ya buga dan tasan matuk'ar yana lafiya babu yadda za'ayi ya shafe ko da kwana d'aya ne bai kira ta ba,
balle har tsayin kwana goma " anya lafiya kuwa..!?
Ta kuma tambayar kanta,
a hankali ta lalubi wayarta had'i da yin dialing number shi da sabuwar number ta data siya,
bata b'oye number ba dan tasan matuk'ar aka kira shi da no number bai tab'a yin picking ko waye,
sai da ta kusa tsinkewa kana yayi picking,
cikin sanyin murya mai tattare da tsantsar damuwa da zallar bak'in ciki yace " hello....!,
ido ta lumshe tana kwanciya saman bed d'in,
while hawaye na zubo mata,
" hello ya kuma cewa muryarshi na rawa,
still bata ce mishi komai ba,
jin anyi shiru yasa shi dropping wayar,
saboda yau kusan kwana goma kenan yana ta faman kiran wayarta,
amma not reachable kuma takai 3 weeks yanzu rabonta da makaranta,
sau uku yana zuwa gidan su yana tambayar mai gadin, amma duk sanda yaje ce mishi yake yi tayi tafiya,
sosai ya shiga matsananciyar damuwa da bak'in ciki,
ga Hilwa ya dawo yana yi mishi maganar ya sukayi da Sanah,
shi yama rasa amsar da zai bashi,
tana jin ya kashe wayar ta kifa kanta saman bed had'i da sanya kuka mai sauti,
sai da taci uban kukanta san ranta kana ta tashi ta shiga bathroom tayi alwala ta dawo ta shinfid'a sallaya had'i da tada sallah,
cikin sanyin jiki Khulud ta tashi ta shiga bedroom d'inta tayi alwala tayi sallah kana ta fito ta shiga kitchen ta d'ora musu abinci,
abincin data san Sanah tafi so a rayuwarta shi ta dafa,
shinkafa da wake da mai da yaji had'i da salad,
da soyayyan kifi,
sai da ta gama jera abincin saman dinning kana ta nufi bedroom d'in Sanah,
knocking tayi mata had'i da sallama,
a hankali ta mik'e daga kan sallayar ta bud'e mata k'ofa,
cikin fara'a Khulud ta rungume ta had'i da cewa " please tashi muje mu ci abinci,
bata kalle ta ba tace " na k'oshi..!
" please dan Allah, ki tashi muje,
Allah idan baki ci ba nima ban ci,
ta fad'a tana zumb'uro baki had'i da zama bakin gadon,
karo na farko da tun faruwar abun tayi murmushi had'i da mik'ewa tace " muje..!
d'an tsallan dad'i Khulud tayi tace " thank you..!
bata kuma yin magana ba har suka zauna saman dinning d'in,
bud'e food flak d'in Khulud tayi tana dariya tace " your favorite food na dafa miki,
murmushi ta kuma yi tace " nagode,
sai da suka gama cin abincin kana Khulud ta kalle ta,
tace " my Sanah yau fa ke zaki kwana da Hanash,
dan gwara muyi abinda zamuyi tun wuri kar wankin hula ya kaimu dare,
a matuk'ar tsoroce ta zaro ido had'i da cewa " in kwana dashi inyi mishi me...!?
Murmushi tayi ganin yadda tayi muguwar tsorata,
tace " haba my Sanah meye na tsorata haka...!?
" Calm down mana,
ke fa ba yarinya k'arama bace,
ba kuma jahila bace, ba kuma 'yar kauye wacce ke cikin duhun kai bace ba,
kin kuma san duk wasu hak'k'ok'in miji akan matarshi,
kanta ta shiga girgizawa tana cewa " Allah ban iyawa ba,
" tom idan baki je gare shi ba tayaya cikin zai shiga, kuma har a samu abinda muke so....!?
" Allah ban iyawa Khulud tsoro nake ji sosai...!,
" to amma dai kin san babu yadda za'ayi mace tayi ciki batare da tayi sex ba ko...!?
" Allah ni dai a'a please karki ce nayi sex wallahi ban iyawa,
" tou my Sanah so kike muyi ta zama haka batare da munyi mun gama abinda ke gaban mu kin komawa masoyinki ba...!?
" Dan Allah ko sau d'aya ne tak ki yarda kuyi sai kiga ma idan Allah ya taimaka an samu abinda muke nema,
kinga kar muzo muyi ta zama muna b'ata lokacin mu a banza batare da munyi abinda ya kamata ba,
idan ba haka ba meye amfanin auren to....!?
" Meye amfanin hak'ura da soyayyarki...!?
" Dan Allah ki yarda ayi yau kawai a wuce wajen,
sosai Khulud tayi ta lallb'ar Sanah tana rarrashinta,
had'i da nuna mata matuk'ar tana san ayi sauri a gama abinda ake yi ta komawa Sir Moli dole sai tayi sex,
har dai daga k'arshe ta yarda ta kuma amince,
" to shikenan na yarda, amma dan ki fad'a min da zafi....!?
" Ba wani zafi duk fad'ar mutane ce sai ma dad'i da zaki ji sosai da sosai,
ita dai Sanah bata yarda ba dan tasha jin mutane da dama suna fad'ar irin mugun zafin da ake ji da farko,
Khulud tace " kinga yanzu 3:20pm na rana,
muyi wanka muyi sallar la'asar sai muje kasuwa muyi siyayya,
" kasuwa kuma..! me zamu siyo...!?
Amma kin san dai dole muje mu yi siyayya kayan sawarmu ko...!?
" Shi ne nace mai zamu siyo...!?
" Kayan sawa dana bacci kin san yanzu dole kayan mu zai zama iri d'aya ne,
" ok kije ki siyo ba damuwa ba sai na je ba,
" a'a dan girman Allah ki tashi mu tafi tare please, dan Allah my Sanah,
" please kiyi hak'uri Khulud ban zuwa....!
" wai tsaya ya naji tunda akayi abunan kin daina ce min your Khulud ko Uludinna...!?
Murmushi tayi batare datace mata komai ba,
shagwab'e fuska Khulud tayi tace " dan Allah ki rink'a kira na kamar da,
" tom naji..!
"then dan Allah ki tashi mu tafi kasuwar please..! please..! karki ce a'a dan Allah,
nan ma murmushi tayi tace " tom tashi mu tafi idan muka dawo mayi wanka,
da sauri ta mik'e had'i da cewa " muje,
hijabai suka zumbula har k'asa,
Sanah ta sanya nik'ab suka fita,
driver yana ganin su ya taso...!
" ka barshi zamu je da kanmu,
bani key d'in ta fad'a tana mik'a mishi hannu,
babu musu ya bata key ta amsa,
ta juya ta tana bud'e motar zata shiga,
ganin Khulud ta tsaya baki bud'e batare data ce komai ba yasata cewa " muje ko..!?
" Mu je ina...!?
Khulud ta tambayi Sanah,
murmushi tayi had'i da shiga motar tayi mata key ta tadata tayi ribos tazo gaban Khulud ta tsaya tace " dan Allah ki shigo mu tafi kar muyi dare,
cikin mamaki da mutuwar jiki Khulud ta bud'e motar ta shiga,
Sanah ta ja suka fita, kasa hak'uri Khulud tayi dan haka,
tace " ke..! wai tsaya dama kin iya mota ne..!?
" Ga tabbas tace tana cigaba da tuk'in,
"a ina kika koya, waya koya miki...!?
" Tambai..! ta fad'a tana rolling idanta,
" please ki ban amsa waya koya miki..!?
" Sir Moli tace batare data kalle ta,
" wow..! gaskiya ya taimake mu daya koya miki motar nan,
murmushi tayi had'i da cewa " hmmm wancan d'an k'auyen mijin naki ya kasa koya miki kuna kusan 3yrs da aure,
dariya Khulud tayi sosai had'i da cewa " mijina ko mijin mu...!?