Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 6 of 7
Page 7
A cikin hoton zan iya gane Momah duk da ƙarancin shekarunta a lokacin,hannunta riƙe da baby girl an yi wa gashinta wani tozo daga gaba,gefenta kuma wani gawurtacen namiji ne dattijo amma ka na ganinsa ka ga jarumi.
Duk cikin hoton yanayin shigarsu ce ta fi ɗaukar min hankali,ba kaya ba ne irin wannan da muke saka wa ba.A'a nasu kamar fata ce aka sarrafa aka mayar da su kayan,su ma ɗin iya cinya ne a saman riga kuma wata rabaja ce kamar zaren kwakwa.
Kaina banda sarawa babu abin da yake,daga bayana na ji taku da sauri na mayar da hoton cikin akwati ina ƙoƙarin mayar wa.
“Ayodele mi kike a nan?”
Da sauri na miƙe na ce “babu komai Momah ” kallon tuhuma ta fara yi min amma na share tare da fito wa tsakar gida,zuciyata fal fargaba ‘wannan shi ne mahaifina? Wace ƙasa ce wannan ke shiga kamar ta arna? Sai yaushe Momah za ta kai ni gare shi? Ina son mahaifina’ duk a zuci na yi maganar kafin na zauna na kishingiɗa ga katanga.Wasu hawaye masu mugun ɗumi ne suka shiga sintiri a kumatuna, “na fita zuwa kasuwa sai na dawo” na ji muryar Momah ,na buɗe ido ina kallonta sarai ta ga ina hawaye amma ba ta tambaye ni ba ta fice.
Ko mi ta tuna oho,sai ga ta kuma ta dawo “tashi mu tafi tare ” na miƙe na ɗauko kallabina na saka takalmi,sai da na wanke fuska sannan na fito.Momah ta rufe ɗaki da gida mu ka wuce kasuwa,tun da mu ka shiga nake jin tsikar jikina na tashi.
Ina nan tsaye na ga wata yarinya na jaye da wani tsoho irin masu Bara a kasuwa,sai cewa take “a bamu sadaka saboda Allah da Annabi ” kafe su na yi da ido sun tsaya gaban wata mace mai sayar da busasar zogale.
Cike da azama na yi tako ɗaya zuwa biyu na damƙe hannunsa,cike da mamaki yake kallona idonsa da suke a rufe ƙarya ce ba makahon gaskiya ba ne.
“Mine ne za ka yi? Kan mi za ka saka hannunka cikin kwagirinta na kuɗi?” na tambaye shi,duk sai ya rikice ya ce “ki yi min rai ƴata,doli ce ta saka nake wannan ɗabi'ar ”
“Kake damfarar mutane ba! A yadda kake duk wanda ya ganka zai ji tausayin ka amma ka yi amfani da maganin rufa ido ka na cutar bayin Allah ”
Hawaye na ga su na zuba a idonsa ya ce “saboda na ciyar da iyalina ne amma ba da son raina nake hakan ba,amma na yi miki alƙawari daga yau ban sake wa”
Na sakar masa hannu,abu guda da na fahimta kaf uwanda ke kusanmu babu wanda ya gani ko ya ji tattaunawar mu.Dube-dube na fara can na hango Momah da ɗan saurina na ƙarasa gun ta.
Mun yi gaba kaɗan wani yaro ya faɗi gabana,cike da tausayi na miƙar da shi ina mai tambayarsa “mi kake ma kuka?” da hannu ya yi min nuni ya na magana amma ba ta fita saboda yadda kukan ya ci ƙarfinsa,hannunsa na ja mu ka shiga tafiya direction ɗin da yake nuna wa har mu ka isa wurin wani mutum.
Na buɗe baki zan ƙara tambayarsa kawai idona ya sauka kan ƴar ƙaramar baro mai ɗauke da doya.
Cikin dake wa na dubi mai sayar da doyar na ce “mi ka yi masa yake kuka?”banza yayi da ni hakan ya ban haushi na yi kururuwa duk mutane hankalinsu ya dawo kanmu wasu tuni sun zo su na tambayar lafiya.
“Faɗa masu abin da ya faru” na cewa yaron,cikin ikon Allah yayi bayani yadda kowa ya ji “mu na tafiya ne ni da twin ɗina sai wannan mutumen ya kira mu ya ce mu zo mu karɓi chocolat sai ni na ƙi zuwa Amra ta je ta karɓa shine ta zama doya”
“Laaaaha'ilah! ” duk kusan mutanen suka faɗa,amma mai doya ƙiri-ƙiri ya ƙaryata yaron ya ce “ka ji zai ƙulla min sharrin duniya,tun yaushe nake sana'ar sayar da doya a nan an taɓa kama ni ne? To nuna min ƴar uwar taka wacce na mayar”
Cike da yarinta yaron ya je ya nuna ɗaya da ke can ƙasa,shi kuma mai doyar ya ɗauki wuƙa ya yanka.
Da hannu na shiga taɓi na ce “a gaishe ka sarkin macuta na duniya,wato masanya ka yi to yanka wannan mu gani” na faɗa tare da nuna doyar da idona ƴar ƙaramar yarinya ce ƴar shekara huɗu.Muƙut ya haɗiye wasu yawu,cikin tsawa na ce “ka yanka aka ce ko kuma na kira ma ƴan sanda”
Ya ƙanƙance ido zai yi magana amma mutane ba su basa dama ba saboda hantarar shi da suka fara kan ya yanka ko kuma su kashe shi.Hannunsa na rawa yasa wuƙa zai yanka na ce “ba nan ba” sai dai tuni ya yi wulish ya yanka nan jini ya fara tsirta.Kawai sai ya fashe da kuka,wani ya kira ƴan sanda a nan cikin kasuwa ya mayar da ita mutum wurin da ya yanka kuma kusan idonta ne.
Ɗan kwalina na keta na ɗaure mata gun,ƴan sanda suka cabke shi kafin ƴan sanda su tafi da su suma don doli sai an kira iyayensu.
Neman duniya na yi wa Momah amma ban ganta ba ,a doli na dawo gida.
Bakin ƙofa na zauna ina zaman jiranta,kamar wacce aka mitsika na je na buɗe ramen da na saka Kambun Kunkuru.Har yanzu da ransa,sai dai ya ɗan gaji ya kuma ƙara girma.Na kuma mayar da shi a karo na biyu na rufe,ina nan zaune taxi ta tsaya .Momah ta fito,har muka sa kaya cikin gida ba ta ce min uffan wato fushi take da ni.
“Mom...”
“Yi min shiru! Wato ke ba za ki taɓa ganin abu ki yi shiru ba ko? Kaf kasuwa zancen ki ake ,ko kin yi tunanin ban san abin da kika yi ba? Na san yanzu zancen ya zo har nan unguwar shikenan sai a dinga kasa mu a faifai ana tallarmu duk irin gargaɗin da na yi miki amma kika yi fatali da shi kin kyauta!” ta na gama ta shige ɗaki.
Duk jikina ne yayi sanyi,a fili na furta “in sha Allah daga yau ba zan sake shiga sabgar kowa ba,ko da kuwa ace ni ce za su cutar zan yi shiru su kashe ni ”
Kamar yadda Momah ta yi hasashe kuwa hakan ce ta faru,zancen Ayodele ya cika unguwar tuni ma wasu sun fara zarginta da mayya.Dama ba su gama tantama akan al'amarin ceton Zeinab da ta yi ba.Yau kuma ta ceto yarinyar da aka mayar doya,tambayarsu ita ce inda a ce ba ta da ido uku ta ya aka yi har take fahimtar abubuwan da ke ɓoye wanda normal mutum bai gani? Wannan al'amari ya ƙara tunzura sauran Mayun da ke unguwar,tare da ɗaukar alwashin sai sun tozarta ta a bainar nasi.
★Washegari
Yau juma'a ce,da baƙin cikin abin da A'isha ta min jiya na kwana duk tun a jiyar na yi ƙoƙarin kiranta na wanke ta tasss amma ban same ta ba.
Ina isa asibiti na tarar da ita bakin ƙofa a tsaye jikin mota sai uban murmushi take zuba wa,da alamu sallamar Mansur ce za ta yi wanda shi kuma yake a zaune ya fiddo ƙafarsa ɗaya waje.
Na danne zuciyata na ce masu “sannun ku da hira” in dai ganye bedi na magana to su ma sun tanka ni,tunani na yi ba su ji ba sai na yi tsaye na ce “duk soyayyar ce haka?” Mansur kawai ya dube ni shi ma bai yi magana ba ,ita kuwa A'isha ko waiwaye .
Ganin irin cin kashin da suka yi min ya saka na shige cikin asibiti,na ja ƙyaci ina mai cewa “ai za ki zo ki tarar da ni ”
“Ayodele lafiya kike magana ke ɗaya” cewar Fatimah,na ce “ A'ishah ce wai don ta na gaban saurayi ta yi banza da ni ”
“Kai haba? Ni kuwa sai da mu ka gaisa har da shi Mansur ɗin”
“Hum!” kawai na iya yi bisanin na je na aje jaka na saka farar rigar likitoci.
Sai da mu ka yi nisa cikin aiki sannan A'ishah ta shigo,ina jin lokacin da Dr Jaleel ke yi mata faɗa kan ta zo lati sai haƙuri take basa.
Cikin sigar wasa na zo daf da ita ina mai cewa “na zata har shi Dr Jaleel ɗin banza za ki yi da shi,ko da yake yanzu masoyin naki bai nan” wani kallo ta yi min ba tare da ta ce komai ba.
Ni ma na kama gabana,ko lokacin cin abinci haka A'isha ta ware kanta duk yadda Fatimah ta so ta ja ra'ayinta amma ta ƙiya.
Tun daga wannan rana mu ka fara takon saƙa da ita,tun mutane ba su gane ba har suka fahimta.Dr Haleema har zaunar da mu ta yi ta yi mana nasiha amma a banza ,haka zan yi ma A'ishah magana ita kuma ta basar.In muna zaune cikin jama'a sai ta bai wa kowa hannu in ta zo gare ni sai ta tsallake,tun ina yi mata uzuri har ni ma na aro rigar rashin mutumci na yaɓa ma kaina don dama can ni masifaffiya ce ta ajin farko.
Yau saura kwana uku bikin ta,ina ji ta na bai wa Fatimah labari “Oga dai ya matsu a yi aurenmu,kin san a baya ya sha wuya sosai wurin soyayyata yanzu lokaci yayi da zai cika burinsa”
Fatimah ta ce “ai ke ma ga shi sai zumuɗi kike,na matsu mu miƙa ki gidan Mansur ko hankalinmu ya kwanta”
“Ai fa dai na matsu wallahi ”
“Ayodele kin ji yaran zamani ko?” Fatimah ta sako sunana,ina jin lokacin da A'ishah ta ja tsuki.
Ina cika takardu na ajiye na kalle ta na ce “da wa kike?” shiru ta yi ba ta ban amsa,na miƙe a hassale Fatimah ta sha gabana ta na cewa “don Allah ki yi haƙuri! Kin ga dai ba ta ce da ke take ba”
“To da uban wa take?”
“Ba ta dai ce ke ba, A'ishah don Allah tashi ki yi tafiyar ki tun da lokacin tashi yayi” cewar Fatimah,kamar jira take ta ɗauki jakarta ta fice.
Sosai Fatimah ta yi ta danna zuciyata tare da roƙona kan na je bikinta na nuna mata ba komai ba ce duniya,bisanin ita ma ta tafi.
Sai da na gama cika takardu sannan na fito. “Ƴan mata?”
Da mamaki nake kallon shi na ce “kai ne?”
“Eh wallahi na zo wurin abokina,ashe wannan asibitin kike aiki ?”
“Eh! Wurin wa ka zo?”
“Dr Jaleel mana,kin san abokina ne yanzu haka shi nake jira za mu wuce gidana”
“Ok yayi”
“Ba ki faɗa min sunan ki ba,tun ranar nan dai da na rage miki hanya na ji kin burge ni” karon farko da na taɓa jin haka daga namiji,sai abun ya ban dariya ban kai ga magana ba Dr Jaleel ya fito hakan yasa na yi tafiyata.
Tun daga nesa nake tsinkayen yadda mutane suka yi dandazo a ƙofar gidanmu.Gabana tuni ya fara dakan uku-uku,ina iso wa wasu suka fara faɗin “Ga ta nan!” can kusan ƙyauren gidanmu na ga Momah a rakuɓe idonta sun yi ja jawur,kallon mutane kuwa tuni ya dawo kaina......
Mai son complete 800 ne via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
[28/04 07:41] MRS SADAUKI: *FARAUTAR MAYU*