Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 3 of 7
Ci gaba da kiran sunan nawa aka yi,inda sautin ke fito wa na dinga bin direction ina ta tafiya har na ɓullo wata kwana.Nan na yi kiciɓis da allon sanarwa,sunan *GIDAN GAWA* ne ɓaro-ɓaro da manyan baƙi,a ƙasa kuma hoton gawa ne naɗe cikin farin likafani.
Waige-waige na fara ,har zan koma na ƙara jin sautin sunana,muryar ya ta namiji ce ba mace ba.Ɗakunan da aka tanada don ajiyar gawa na nufi na mazan,ƙofar da kanta ta buɗe hakan yasa na kutsa kai.
Ƙyalƙyal ! Aka kece da dariya,da sauri na fara dube-dube don tantance shin cikin wane akwatin ne ake dariya.
“Ga ni nan” na ji ya faɗa a bayana,na juya na yi tozali da mutumen da A'ishah ke ban labari an maido gawarsa.
Ido cikin ido muke kallon juna da shi,bisanin na ce “lafiya ka kira ni izuwa nan?”
“Kambuna nake so ki ban”
“Ba zan bayar ba doli ka mutu kamar sauran da ka kashe”
“Ki bani cikin lalama ko kuma na gayyato miki shugabanmu”
“Au! Har shugaba gare ku? Na tambaye ka mi yasa kuke son yin mugunta? Don me ba za ku zauna cikin duniya normal ba kamar kowa?”
“Saboda duniyar ɓoye ta matsafa ta fi daɗi,za ka sha jini ka yi ta siddabaru ka na tsoratar da mutane cike da nishaɗi ”
Hira ya fara yi min ta yadda suke kama kurwar mutum da kuma yadda suke yi in su na son bai wa mutum tsoro,hakan ya shagaltar da ni sosai sam ban fargaba sai mugayen esprit na ga duk sun cika ɗakin.
Ruhika ne na maras imani,wasu ma daga maƙabarta suka zo nan don taimakon ɗan uwansu.Kewaye ni suka yi,ba na ganin fuskokinsu.Wasunsu tamkar innuwa,wasu kamar dunƙulalen baƙin hayaƙi,wasu kuma cikin siffar fatalwa ne da farin likafaninsu.
“Auwushhh tangarrsinn,mahulujaaa.An yarhihum khaaaaa!” shi ne furicin da na samu bakina ya na furta wa,duk a tsorace suka ja ba shi kuwa tuni ya koma cikin akwatinsa.Idona na rufe na ci gaba da yin wani Yare ina yarfa hannu,a take wani haske duk ya game ɗakin wanda rufe wa idona bai hana ni ganin halin da suke ciki ba.
Tuni duk suka tsere suka bar ni da shi,akwatin da yake ciki na ɗora hannuna akai ya fara ihu ya na “cewa ki yi haƙuri zan tafi wallahi na yi miki alƙawari gobe zan bar gidan gawar nan zan je na kwanta kabar....” bai ida kai furucinsa ba wani haske ya fito daga bakina ya daki goshinsa tsit ya mutu a yanzu kuma na tabbata ko fatalwar ba zai iya yi ba.
Kaina yayi mugun sarawa,na dawo garas da sauri na fito waje sai kuma na ci karo da mai gadin wurin.“Wace ce ke?” ya jefo min tambaya,murya na ɗan rawa na ce “dama... Dama!”
Sai ya saki murmushi ya ce “yi tafiyar ki” ban san dalilin shi na yin haka ba amma sosai na ji,domin muddin maganar ta yi nisa ya tara min mutane dole a ɗora min Ayar tambayar mi ya kawo ni gidan gawa a wannan tsohon daren.
Ko da na koma ɗaki sai da na yi tunani bisanin bacci ɓarawo ya ɗauke ni.
Washegari bayan duk mun kimtsa na ga A'isha sai murna take,ban yi ƙasa da gwiwa ba na tambaye ta “wai farin cikin na mine?”
“Mansur zai zo ɗaukata,kin ga daga nan sai mu aje ki gida” ta ban amsa.
“Au haba? Fatimah ba ta zo da babur ba?”
“Ya samu matsala a jiya hanyar mu ta fiddo anko sai ta barsa wurin mai gyara”
Mu na tsaka da hira aka kirata,cike da murmushi ta ɗauka bisanin ta aje wayar ta ce “har ma ya iso mu je”
Sai da muka fito ne muka haɗe da Fatimah wacce ke zaune ta na shan love.Bakin ƙofar asibitin muka fita ,idona ya sauka kan wata ƙatuwar mota baƙa wuluk mai taya a baya.
A'isha ta buɗe mana gidan baya muka shiga ni da Fatimah yayin da ita kuma ta shiga gidan gaba.
“Baby ga ƙawayena da nake baka labari ka rage masu hanya” cewar A'isha .
“A gaishe ku fatan duk ku na lafiya?” ya faɗa cikin muryarsa irin ta siraran maza ,duk muka amsa da lafiya lau.
Ya dubi A'isha ya ce “ya maganar zuwa gidan abinci kenan?”
“Mu je mana ai su ma za su ji daɗi,ko ya kuka ce ƙawayena?”
Fatimah kawai ta amsa mata,ni kuwa na lula duniyar tunanin ta yaya ya samu kuɗi har haka cikin ƙanƙanen lokaci in dai yadda A'isha ta bamu labari ne Lagos ne ya je to tabbas akwai lauje cikin naɗi.
Ina cikin wannan tunanin har muka isa , restaurant ce ta sai wane da wane don ni ban ma san da zamanta ba.
Yadda aka tarbe mu kawai ya isa mu gane Mansur sananne ne a wurin.
Shi ya zaɓi abin da za a kawo ma A'ishah yayin da ya nemi mu zaɓa da kanmu,amma sai A'ishar ta nuna masa ko wurin aiki cikin plate ɗaya muke cin abinci don haka nan ɗin ma ba za a ware mu ba.
Shiru yayi ya na ɗan tunani,bisanin ya bai wa serveur ɗin umarni kan yayi yadda ta ce.Lafiyayen abinci ne,haka muka fara ci hankali kwance ba tare da wani tunani ba shi kuwa Mansur duk ya zama wani iri.
Tamkar wacce aka sa ƙugiya ana ƙoƙarin zaƙulo hanjin cikinta haka na fara ji cikina na min ciwo,da sauri na fidda hannuna na ce na ƙoshi.
Na tashi tare da tambayar masu kula da wurin ina ne toilet,aka nuna min na shiga.Amai na ta kwarara wa kamar raina zai fita,tsabar azaba har wata zufa ke tsatsafo min ina buɗe ƙofar toilet na yi kiciɓis da saurayin A'ishah...
[24/04 14:49] MRS SADAUKI: *FARAUTAR MAYU*