Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 5 of 7
Page 6
Kiciniyar fita daga cikin akwatin gawar na fara sai dai ga mamakina wata gawar na gani a tsaye kan ƙafafunta ta na ƙoƙarin danna ni ciki.Da dukkan alamu akwatinta ne,cikin wata irin murya ta maso duniya take cewa “ki zauna madadina don Allah na ga ke lamarin duniya bai sha maki kai ba,ban shirya zuwa can mazaunar fatale da ruhika ba”
Idona na ware sosai kan matar, datijuwa ce a ƙalla ta kai shekara hamsin da ɗoriya fara ce tasss sai tsagen fuskarta na kurmawanci da ya fito raɗo-raɗo.
Tabon goshina ne na fara jin ya na motsi,kamar almara sai gani na fito daga cikin akwatin na tsaya kan ƙafafuna.
Gawa ta fashe da kuka,cikin tsawa na ce “je ki koma makwancin ki,wato lokacin da malamai ke yi muku wa'azi kar ku biye ma ruɗin duniya ku na yawon dare amma kuka yi kunnen uwar shegu da su kuke fita cikin dare farautar bayin Allah.Yanzu kuma da zanzaro ya tonon gidan Rina gari ya kwaɓe miki za ki neman ki dawo duniyarmu?”
Idonta na zubar da hawaye ta shiga akwati ta kwanta wani haske ya fita daga goshina ya daketa tsit kake ji har esprit ɗin nata ya bar motsi,na maido dubana ga ɗayar wacce ke shashekar kuka na zuba mata Mayun idona masu masifar kaifi na ce “ ke kuma ina jin ki”
Cikin kuka ta fara yi min bayani “wannan da kike gani mahaifiyata ce,ta ja ni izuwa wani ƙauye ne don yin shagali ita da ƙawayenta a can suka nemi da ta bada jinina su sha da ta ƙiya ne hanyarmu ta dawowa mu ka yi hatsari.Kin ga ban mutu ba sun ɗaure ni da azargagi ne,shirinsu shi ne in an kai ni maƙabarta su je su haƙo ni su tsotsen jini”
A ɗan takaitaccen bayaninta na fahimci mahaifiyarta ta na cikin wata ƙungiyar Mayu ce masu shan jini,sannan duk shekara su na gudanar da bikin ƙara danƙon zumunci inda a dole wata za ta bayar da kyautar jini daga cikin ahalinta,kamar ɗa,jika ko ƙane.
Kallon tsaf na yi mata,sai yanzu na lura da goshinta da gefen bakinta duk a fashe suke alamun buguwa.Tunani na fara ta inda zan taimakonta,sai dai na kasa samun mafita don ban san fuskokin masu son kaita ƙasa ba.
“Ki taimaka min kar ki bari a kai ni maƙabarta da raina ban mutu ba sun juyar da hankulan mutane ne kawai ake min kallon gawa ” muryarta ta katse min tunani.
Na ja dogon numfashi bisanin na ce “ki na ji na,a halin yanzu banda mafita amma na yi miki alƙawari zan cece ki ko bayan an haƙa miki kabari ne an saka ki ci to zan zo gare ki”
Fararen idonta ta zuba min uwanda sam ba su da ɗigon baƙin ciki,na jinjina mata kai alamar tabbatar wa kan ƙudirina.Ban sani ba ko ta yarda da ni ɗari bisa ɗari,amma a sannu na ga ruhinta da ke dabaibaye da wasu Kambu ya ɗan samu salama.
Sai da na shafi fuskarta bisanin na fito,direct ɗakinmu na wuce sai na tarar da Fatimah a zaune.
“Kin tashi? Ya jikin naki?” na tambayeta.
“Da sauƙi alhamdullah! Na gode sosai Ayodele,haƙiƙa ke ƴar baiwa ce.Da ace musulma ce ke da tabbas ba ƙaramin gudumuwa za ki bayar ba”
Na sakar mata murmushi na ce “duk Ubangiji muke bauta ! Banbanci kaɗan ne,sannan shi ke tsara komai iyakacinmu mu yi aiki da baiwar da ya bamu amma komai daga Ubangiji yake”
“Zance na hikima! Anya kuwa ruhinki ba na Musulunci ba ne gangar jikin kaɗai ke ta Yahudawa?” Fatimah ta faɗa,dariya na yi na canza zancen “ai yanzu dai kin bar jin tsoron komai ko?”
Ta ja tsuki tare da cewa “shi ɗin banza Allah na tsane shi ,amma yanzu ban ji shakkar shi .Wai daga ina kike ko an kawo sabbin patients ?”
Na ja ajiyar zuciya domin tambayarta sai ta tuna min da danbarwar da na baro a can MUTUWARE.“Ki koma ki kwanta don kin galabaita sosai ,ni ma baccin nake ji akwai aikin da nake son yi cikin bacci” na faɗa tare da kwanta wa kan gado,Fatimah ta waro ido bisanin ta ce “kin san kuwa a jiya ne ko yaushe da kika yi bacci gidansu A'ishah wallahi sai da kika bani tsoro don ba zan ɓoye miki ba shi ne dalilin da yasa na sulala zuwa gida”
Na lumshe ido ba tare da na bai wa abin da take faɗa muhimmanci ba,nan take bacci ya ɗauke.Duk a mafarki aka nuna min maƙabartar da za a rufe wannan baiwar Allah,da kuma duk abin da zai faru da yadda zan kuɓutar da ita.
Washegari muka hau aikin safe bisanin mu sauka,tuni Fatimah ta yi tafiyarta A'ishah kuwa a gabana ta kira Mansur kan ya zo ya ɗauke ta.Na taɓe baki don na lura har wani rawar kai take wanda yawancin amare ko kuma wanda za su auri mai kuɗi suke yi.
Kafin ya zo ne na samu tsure A'isha da ido na ce “bayan Mansur ya dawo daga Lagos halan kasuwanci ya fara?” shiru ta yi bisanin ta ce “wallahi ban sani ba,kin san in mutum ya je neman kuɗi da zarar ya dawo to fa hutu ne kawai yake,ina ga shi ma bai komi”
“To in kuɗin suka ƙare fa? Ke dai ki tambaye shi ƙila ya na kasuwanci ya ɓoye miki ne” na faɗa cikin son jawo ra'ayinta,don zuciyata ta fara aminta kan na rusar maganar auren nan .
“Wallahi ba zan iya ba,ƙwarjini yake yi min ba zan iya tambayarsa ba.Kin san kuwa yadda nake jin mugun tsoron Mansur? Wallahi yau da ya zo ɗaukata kasa kallon ƙwayar idonsa na yi”
“Hum! Wai dama ki na sonsa ko kuwa yanzu ne da ya zama mai kuɗi kike ra'ayin shi?”
“Sosai kuwa! Dama rashin kuɗi yasa ba a bari muka yi aure ba.Abbana ya ce sai na ida karatu duk don kar ran Mama ya ɓace kin ɗan Yayarta ne”
Kai kawai na jinjina ina tunanin wani babban al'amari,bisanin na ce mata “okay ni zan tafi in ya zo ki gaishe shi”
“Ki jira mana sai ya sauke ki gida”
“A'a na gode!” A'ishah ta riƙe ni ta na cewa “ wallahi babu inda za ki je dole mu aje ki gida”
Muna cikin wannan yanayi motar Mansur ta tsaya,fito wa yayi.Sanye yake da baƙaƙen suit idonsa manne da baƙin gilashi,cike da ƙasaita ya iso kusa da mu.
A inda yake tsaye zan iya hango tsantsar mamaki kan fuskarsa,wanda tuni na fahimci na gani na a raye ne.“sannu angonmu” na faɗa cikin raha,sai ya ɗan daburce ya na mai cewa “oh! Na shagala da kallon amaryata ne shi yasa,fatan ki na lafiya?”
“Garas nake!” na basa amsa ina mai kallon tsakiyar idonsa don tuni ya cire gilashin,ya kawar da kai ɓangaren A'ishah ya na mai cewa “amarya ba kya laifi! Mu je ko? ” ga mamakina kamar raƙumi da akala haka A'ishar ta bi bayansa ko kallona ba ta yi ballantana zancen yi min sallama ko kuwa ta yi maganar sauke ni a gida da ta ce.
Na rumtse ido tsabar takaici,ganin Mansur ya ci taya ƙura ta tashi duk ta baɗe ni.A hankali na buɗe su tare da bin motar da idon har ta ɓace ma ganina,jiki a matuƙar sanyayye na je na tsaya bakin hanya.Tsabar yadda ruhina yayi baƙi har ban san lokacin da na tsayar da wata farar mota ba madadin taxi,sai da na ji muryarsa ya na cewa “hanya zan rage miki?”
Cike da masifa na buɗa baki na ce “aka ce ma banda kuɗi ko na yi ma kama da irin ƴan iskan ƴan matan nan?”
Ya waro ido ya ce “keee! To ce miki aka yi motata taxi ce?”
Sai a lokacin na farga da mota ce,na yi baya ina cewa “ka yi haƙuri ”
“Na ƙi ɗin dole ki shigo na kai gida”
Zan kuma ƙara yaɓa masa magana sai na ga yayi min ƙwarjini don babban mutum ne mai cike da kamala zai kai shekara arba'in da biyar.Na haɗe yawu na ce “na gode” amma fafur ya ƙi tafiya ya nace a ƙarshe dai na yarda na shiga.
Mu na tafe ya mayar da volume ɗinsa,ƙira'a ce ke tashi ana karatun Alkur'ani.Ban san mi ya shige ni ba,amma sauraren sautin ya saka na fara jin sanyi a raina .“Wace unguwa za mu je”
“Unguwar ƴan tsofi” na basa amsa don haka ake kiran unguwarmu.Ya ci gaba da driving,ni kuwa sai sauke ajiyar zuciya nake ina jin nutsuwa na daɗa ratsa ni har mu ka isa layinmu.A ƙofar gida ya sauke ni,na masa godiya ina mai ficewa.
A'ISHA
Yanayin kallon da Mansur yayi mata ya saka duk wata gaɓa ta jikinta ta yi sanyi.Tamkar za ta shiɗe haka ta ji,ga wani tsoronsa da shakkarsa da ta ji sun ƙara dirar mata.Allah na gani sam ta manta da Ayodele na kusa da ita,hakan yasa ta bi bayan Mansur da take jin ko yanka kanta ya ce ta yi to babu shakka za ta yi tsabar biyayya.
Su na shiga mota ya kamo tafin hannunta,cikin salon yaudara yake mata magana “na tsani arniyar can mi ma sunanta?”
“Ayodele” ta furzo lafazin dakyar.Ya ci gaba da cewa “yawwa! Daga yau ina so ki nisanta kan ki da ita,kar na sake ganin ku na ƙawancen na yanke shi kowa yayi harakar gabansa ki na ji na ko?”
A'isha ta jinjina kai ta ce “in sha Allah ko magana ban sake yi mata”
“Yawwa my Ayush! Kar ki sake ce mata ko kanzil! Ki goge lambarta daga wayar ki kafin nan ki tabbatar kin yi blocking nata”
“Yanzun nan kuwa Oga!” A'isha ta faɗa tare da fiddo waya ta aiwatar da duk abin da ya ce.Ya saki hannunta,ya na canza akalar motarsa zuwa restaurant ɗin jiya.
A'isha na zaune Mansur ke cewa “gishiri bai kama kaza ba yadda nake so,ka san a jiya wasu sun ci da rabonta shi yasa na kawota yau ta yadda komai zai tafi daidai”
Wanda zai kawo abincin ya ce “an gama ranka shi daɗe!” can ya tafi ya kawo,tsabar mugunta ta Mansur shi ya dinga bata abincin da Allah kawai ya san adadin tsafin da aka yi masa,ita kuwa sai ci take.Bayan ta gama ya kaita gida zuciyarsa fal farin ciki,“na tsane ki Ayodele! Daga yau dai na yi ma takalme tubkar hanci” ya faɗa a bayyane ya na wata irin dariya.
FATIMAH
Tunanin kar Mansur ya tarar da ita ya saka ta yi tafiyarta tun da wuri.Addu'a neman tsari take kar Allah ya sake haɗa ta da shi,duk da ta na jin cutar da ya bata ta ci duk ta zawayeta amma hakan bai hanata jin normal tsoro a kansa ba tun da shi ɗin mugu ne.Ta na zuwa gida ta samu tuni ƙanenta ya karɓo mata babur ɗinta daga wurin gyara,sosai ta ji daɗin haka don ta na tunanin ta kaucewa shiga motar mugun saurayin A'ishah.
AYODELE
Ina shiga gida na tarar da Momah zaune kan tabarma ga wani akwati a gabanta ,ta na gani na da sauri ta rufe shi ta shige ɗaki,na bi bayanta sai na ga ta tura shi ƙarƙashin gado.
Ban damu ba don ko magana ban yi mata ba,kayan jikina kawai na canza na fito.Jikina na bani kan na je maƙabarta hakan yasa na fito na samu wata taxi na masa kwantace da inda zai kai ni.Kamar dai yadda na gani cikin mafarki tun daga hanyar da aka bi da ni har izuwa maƙabartar.
Daga nesa na yi tsaye,mutane sai bisa suke ido kawai nake bazawa ko Allah yasa na ga kabarin wannan baiwar Allah.
Wani ihu ya ja hankalina,da sauri na juya ɓangaren haguna,sai na ga ashe akwai wasu kaburbura ma ta nan.Idona ya sauka kan gawarta,mugayen tsofin nan kuwa jira suke a rufeta su far mata.Ban buɗe bakina na yi magana ba,amma tabbas na kira su izuwa gare ni.Duk da alamun tsoro a fuskarsu yayin da kuma suke ƴar kallon-kallon,ban basu isasshen lokaci ba na dirar masu ko kuma na ce esprit ɗina ya shiga yin faɗa da su har na ci nasara a kansu duk suka gudu.
Daidai nan na dawo cikin hayyacina,wasu daga cikin mutanen da ke ƙoƙarin turbuɗeta suka ja baya su na kiran “wallahi da ranta” ina jin haka na yo baya na yi tafiyata.
Lokacin da na iso gida na Momah na banɗaki ta na wanka,hakan yasa na yi saurin shiga ɗaki na jawo akwatin ina buɗe wa na yi arba da wani hoto da yasa kaina yayi bala'in sarawa ya na daɗa juyawa......
Mai son complete 800 ne via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
[25/04 09:11] MRS SADAUKI: *FARAUTAR MAYU*