Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Farautar Mayu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 7
Page 4
Fuskar Momah sak ta tsohuwa irin uwanda sun ga jiya da yau.Tuni tsoro yayi min dabaibayi ya ɗaure min zuciya,cikin wata irin murya wacce ba tata ba take shaida min “wannan halittar da ke hannunki ta na da matuƙar haɗari ki yi gaggawa mayar masu ita kayar su.Kin san kuwa mi ake kira da Kambun Kunkuru? Maita ce mai shegen naci masu ita za ki ga ko mutuwa suka yi sun dinga yin fatalwa kenan domin son duniya ba zai taɓa gushe wa ba daga zuciyarsa” Momah na gama faɗar haka kamar ƙyaftawar ido ainahin fuskarta ta dawo normal.
Wani numfashi na ga ta ja ta na mai kafe ni da ido,da sauri na mayar da Kunkurun cikin jaka ina mai cewa “Momah ke ce?”
Maimakon ta ban amsa sai kawai ta fashe da kuka,hankalina ya ƙara tashi na shiga tambayarta can ta tsagaita da kukan tare da yi min umarni na je na kwanta.
Ban musa ba na kwanta sai dai fa ko kaɗan babu ɗigon bacci a idona.Tunani kawai nake,zuwa yanzu na fahimci akwai wani ƁOYAYYEN SIRRI(MRS SADAUKI) da Momah ke ɓoye min sai dai ban san shi ba.
Kamar wacce take karantar zuciyata na ji saukar furucinta “Ayodele ban ɓoye miki tarihin ki ba don wani abu ba,sai don kiyaye ki daga mumunar ƙaddarar da mahaifin ki ke son ɗora ki a kai”
Da sauri na yunƙura na tashi zaune na ce “Momah don Allah ki faɗa min wane ne mahaifina? Sannan ya na raye?”
“Da ransa duk da na fi shekara ashirin da baro ƙasarmu ta gado,amma ina ji a jikina bai mutu ba”
“Mine ne dalilin ki na guduwa to?”
“Zan faɗa miki sai ranar da kika cika shekara ashirin da biyu cicif”
“Nan da wata biyu kenan?” na faɗa don birthday ɗina ya kusa.Ta jinjina min kai alamar tabbatar wa,cike da farin ciki na kwana.
Washegari da zan tafi makaranta Momah ta jadadda min kan cewa na mayar da Kunkurun nan inda na ɗauko shi “to” kawai na ce mata ba wai don ina da niyyar yin haka ba.
Da na fito waje a ƙofar gida na yi rame daidai inda ruwa ke kwanta wa na saka Kambun Kunkuru na mayar da ƙasa,ina ganin yadda yake kallona da manyan idonsa amma Allah na gani ba zan barsa ba ya cutar da mutane.
Ko da na isa asibiti na tarar ana ta ɗaga ankon bikin A'isha ,ban ware kaina ba na shiga duba wa tare da tambayar inda suka fiddota.
Muna tsaka da aiki A'isha ta zo kusa da ni ta ce “Ayodele kin tuna mutumen da ya mutu jiya?” duk da na fahimci wanda take nufi bai hana ni neman ƙarin haske ba “wane fa?”
“Wanda kafin mu sauka ya mutu,gadonsa kusa da na yaron nan mai cutar sikila”
“Oh! Na gane shi”
“Hum! In faɗa miki an sake maido shi asibiti”
“Bai mutu ba?” na tambayeta da sauri,har sai da ta min wani kallo bisanin ta ce “ya mutu! ”
Na sauke ajiyar zuciya,ita kuma ta ci gaba da cewa “sai dai fa gawarsa ta ƙi shiga kabari ” A'ishah ta faɗa cikin wani yanayi.
Dukkan nutsuwata na bata tare da tambayarta “ban gane ba? To ya su ka yi da gawar?”
“Sun maido ta mana! Ta na can MUTUWARE cikin sanyi”ta ban amsa.
“Can shi ya sani! Mugun halinsa ne yasa Ubangiji ya nuna masa ishara” na faɗa zan ci gaba da aikin cika takardu don mun ɗan tsaya hutu ne .
“Amma Ayodele na tambaye ki mana”
“Ina jin ki” na faɗa ba tare da na dube ta ba.
Ta ce “mine ne haɗin ki da shi?” na ɗago na zuba mata na mujiya sai na ga ta ɗan rikice da sauri ta ce “ah! Ina nufin mi ya haɗa ku,jiya da ina ƙoƙarin taimakonsa na ji ya na cewa ki yi masa rai kar ki muzanta ni ban shirya zuwa ɓoyayyar duniya ba”
“Sai kuma ya ce miki da ni yake?”
“Sunan ki na ji ya faɗa”
“To ki je ki tambayesa” na faɗa cikin fushi tare da tashi na barta ma wurin.
Wunin ranar haka muka yi aiki sam babu walwala har Fatimah sai da ta lura kamar mun samu saɓani.Ta yi tambayar duk muka ce mata ba komai,wurin cin abinci ma haka A'isha ke ta min kallon ƙasa-ƙasa ban san mi take zargi a kaina ba har mu ka zo kwanciya.
Addu'o'i na ga ta na ta yi na neman tsari,sannan alamu sun nuna a tsorace take don motsi kaɗan sai ta zabura.Kasa haƙuri na yi na ce “ A'ishah ina son yin magana da ke”
Fatimah ta kalla wacce ta sharar bacci bisanin ta ce min “to”
Na saki wani murmushi sannan na ce “ki na tunanin ko wani na gani zai cutar da ke zan bari ballantana ni da kaina na cuce ki? Ban san zargin mi kike yi a kaina ba,amma ki sani ruhin Ayodele tsarkake ne .Burinsa kullum ya kawar da mugunta da masu yin ta,na san abin da ya faru a unguwarmu da kuma na mutumen nan sun saka miki shakku a kaina”
Ta ja wani dogon numfashi sannan ta ce “wallahi ni lamarin ki ne ya fara bani tsoro,abubuwa kike kamar ƴar autar aljan.Idonki fa har canza kala suke,kuma ba zan ɓoye miki ba wallahi na fara jin tsoron ki”
Na ƙyalƙyace da dariya na ce “wallahi ba muguwa ba ce ni ! Kuma ban san mike faruwa da ni ba.Abu guda nake so ki saka a ran ki shi ne Ayodele amanar A'isha ce”
Wani gamsashen murmushi ta sakar min ta ce “har na ji zuciyata wasai,yanzu kam zan yi bacci cikin aminci”
Sai da mu ka ɗan yi hira bisanin ta ɓingire bacci,na dube su cike da so da ƙauna irin ta jini.
Ina shirin yin kwanciya na ji an kira sunana “Ayodele?” na waiga ban ga kowa ba,sai na yi tunanin ko kunnena ne bai ji min daidai ba.Sai dai da mamakina haka aka sake kira a karo na biyu,kawai sai na fito.