Complete Hausa Novels

Fadeelah Complete Hausa Novel

Reading file: FADEELAH By Fadila Sani Bakori.txt

Chapter 8 of 12

Page 8

Haka aka yi zaman zana'idar mahaifin Fadila, Inda mahaifiyar Fadila da su Aisha sosai mutuwar mahaifin nasu ta tab'asu, dan gaba d'ayansu sun fita yayyacinsu ba kamar Fadila ba da take ganin kamar ita ta ce silar mutuwar mahaifin nasu , inda silarta ne zuciyarshi ta buga.

Haka suka kasance cikin jimamin mutuwar har aka yi addu'ar bakwai. Bayan an yi addu'a ne 'Yan'uwansu Fadila da suka zo gaisuwa da sauran mutane duk su ka watse, ya rage daga mahaifiyarsu Fadila sai su Fadila.

Daga Aisha har mahaifiyar Fadila babu wanda ke mata magana abinci ma babu mai ce mata ta ci ko karta ci. Abunka da mara lafiya hakan sai ya k'ara ma Fadila ciwo sosai.

Yau Aisha jin Fadila shiru ko sallar Asuba bata tashi ba hakan ya sa bayan ta je ta dama musu koko ta zo ta zauna bakin gadon da Fadila take tana Kiran sunanta, amma shiru . koda Aisha ta duba sai taga ashe Fadila asume take. Hakan ya sa Aisha cikin tashin hankali ta yi d'akin mahaifiyarsu da gudu ta sanar da ita halin da Fadila take ci.

Allah sarki mahaifiyar Fadila dake zaune tana kurbar kokan da Aisha ta dama musu cikin rud'ewa ta tashi har tana zubar da kokan bata sani ba.

Mahaifiyar Fadila koda ta je taga halin da Fadilar ke ciki, cikin tsananin damuwa ta ce " Aisha, Kira Napep mu kaita Asibiti "

Kacan cewar babu nisa tsakanin su Aisha da bakin titi hakan ya sa Aisha na fita ta zo da mai Napep. Da taimakon Aisha da mahaifiyarta suka sa Fadila acikin Napep d'in.

Wata k'aramar Asibiti da ke kusa da su suka kaita.

Suna zuwa ko aka fara ba Fadila duk wani taimako da ya dace.

Saida aka sama Fadila ruwa leda uku sannan ta fara dawowa hayyacinta. Likitar kallan mahaifiyar Fadila ta yi ta ce "Mama, gaskiya indai kina son yarinyarki da abun da ke cikinta to ku yi ma mijinta magana , tana buk'atar kulawa sosai idan ba haka ba zaku iya rasa abun da ke cikinta, sannan ta rik'a rage ma kanta damuwa , dan yanayinta duk ya bayyana ha...." Maganar da Fadila ke yi ce ta sa likitar ta yi shiru ,dukansu suka kai dubansu gareta.

Fadila cikin sanyi dan muryar tata ta yi k'asa sosai, ta ce " Mama, dan Allah ku yafe min kubar fushi da ni akan abin da nima bansan yadda ake ba. Mama dan Allah ku yadda dani Wallahi mama bansan ya akai nake da ciki ba, dan Allah ku yadda da n.." Marin da mahaifiyar Fadila ta yi mata ne ya sa ta yi shiru .

Mahaifiyar Fadila ta d'aga hannu zata k'ara ma Fadila wani Marin ne likitar take rik'e hannunta tana cewa " Ki yi hak'uri Hajiya k'addara ce , haka Allah ya k'addara miki " Likitar ta fad'i maganar tana rik'e da hannun mahaifiyar Fadila dan ta fahimci Fadila bata da aure.

Mahaifiyar Fadila ko cikin tsantsar takaici ta ce " Wallahi, indai kika kuskura kika k'ara yi min irin wannan maganar zaki ga abun da zan miki , wato har yanzu kina nufin ke ta kirkice kina da bakin kare kanki ko ? " Fadila dai ba magana sai kuka

Likitar nasiha ta yi ma mahaifiyar Fadila sosai ta ce " Hajiya mai faruwa ta riga ta faru saidai ki yi mata addu'ar Allah ya raba su Lafiya "

Mahaifiyar Fadila kasa jure zaman Asibitin ta yi ta koma gida, dan idan tana kallan Fadila ji take kamar ta shak'eta ta mutu ta huta, hakan ya sa ta dawo gida tabar Aisha. Kwanansu biyu Fadila ta warware baki d'aya.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya , yanzu haka an yi arba'in d'in mahaifin Fadila.Saidai ta b'angaran Fadila ta fara dangana da k'addarar ta ta farka ta tsinci kanta acikinta. Yanzu abu d'aya ke damunta fushin da mahaifiyarta take yi da ita dan ko gaisuwarta bata amsawa .Aisha ma sai taita yi mata magana ta yi banza da ita.

BAYAN WATA UKU

Yanzu kimanin wata uku kenan da rasuwar mahaifin Fadila , kuma har yanzu Fadila na gida bata koma aiki ba, haka 'yan wajan aikin nasu ma babu wanda ya k'ara tuntub'arta ya ji ya jikinta, garama Jamilu yakan kirata su gaisa .

Yanzu rayuwa ta fara sauya ma su Fadila, dan komai nasu kusan ya k'are, yanzu haka yau sun tashi basu da abin da za su ci.

Fadila yanzu cikinta watanshi hud'u kenan, saidai da yake ba mai girman ciki ba ce in ka ganta ba lallene gane tana da ciki ba, sannan kuma dama yanzu kullum da hijab take zama a jikinta.
Yanzu abu d'aya ke damun Fadila shi ne saurin jin yunwa gashi abun da za su ci yana naiman gagararsu . Hakan ya sa Fadila ta yanke ma kanta shawarar komawa ta ci gaba da aikinta .Fadila tashi ta yi ta je ta samu mahaifiyarta a d'aki zaune kan sallaya tana lazimi , dan tun da mahaifin Fadila ya rasu ta maye gurbinshi,dan shi mutum ne da kusan koda yaushe zaka ganshi da carbi a hannu yana lazimi.

Fadila cikin fargaba ta fara yi ma mahaifiyarta magana, dan ita kanta yanzu kusan bata son abin da zai had'asu magana da mahaifiyar tata. Fadila cikin sanyi ta ce " Mama, idan kin amince zuwa gobe ina so zan koma wajan aiki ? " Mahaifiyar Fadila kallan Fadila ta yi tana tab'e baki ta ce " Abun da ake gudu har ake hanaki ada ya riga ya faru , tom me ya rage ? , duk inda kika ga dama ki je ba aiki ba tashi ki bani waje " Fadila tashi ta yi a sanyaye dama tasan haka zata faru.

Fadila d'aki ta koma tasha kukanta ta gaji ta ba kanta hak'uri.
Bayan Fadila ta gama kukan ne Aisha ta shigo d'akin ,Fadila da sauri ta ce " Aisha, dan Allah ki tsaya mu yi magana " Aisha tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba ta ce "Ina jinki " Aisha, dama aiki na ke son in kama gobe dan Allah ki yi ma mama magana ko zata fahimce ni "

Aisha batare da ta tanka ma Fadila ba ta juya ta yi tafiyarta.

Fadila ganin yunwa zata kashesu dan yau kwana biyu kenan ba su yi girki ba sai 'yan dabe-bare da suke yi, hakan ya sa yau ta shirya ta nufi d'akin mahaifiyarta.

Duk da bata amsa gaisuwarta haka Fadila ta gaidata ,amma bata amsa ba, Fadila ta ci gaba da cewa " Mama, zani aiki? " Fadila ta fad'i maganar a tak'aice a hankali saboda yunwar da take ji. Mahaifiyar Fadila bata tanka mata ba haka ta gaji da tsugunno k'arshe ta tashi ta tafi dan bata da wata mafita wadda ta wuce hakan dan yunwa nagaf da illatata.

Fadila na zuwa office d'in MD ta fara shiga dan gani take ma kamar zai dakatar da ita , inda tun da suka rabu ma ko ya kirata ya ji ya jikinta.

MD da kallo ya bi Fadila ganin yadda ta rame ta yi bak'i , cikin tausayamata ya ce " Ya jikin naki ? " Na ji sauk'i na dawo bakin aiki ne? " Kai MD ya jinjina ma Fadila batare da ya tanka mata ba, sannan ya ce " Shi kenan , kima Jamilu magana "

Fadila ko yadda ta ga abokan aikin nata na kallanta tasan duk sun ji abin da ke damunta. Haka dai ta daure batare da nuna ta damu da kallan da aike mata ba suka gaggaisa, sannan ta nufi office d'insu.

Kasan cewar Fadila ta sanar da Jamilu dawowarta aiki ya sa bai yi mamakin zuwanta ba, saidai ya yi ta binta da kallan mamakin ganin ramar da bak'in da ta yi.

Fadila bayan ta zauna haka ta kwashe kaf matsalar gidansu da halin da take da mahaifiyarta ta sanar da Jamilu.

Jamilu sosai ya tausaya ma Fadila , kud'i ya bata ya ce ta je restaurant d'in kusa da su ta ci abinci.

Abin da ya ba Fadila mamaki lokacin da ta tashi aiki MD ya aiko mata da dubu daya (1000) kamar yadda ya sa bata ya ce ta hau Napep, sosai hakan ya ba Fadila mamaki.

Yanzu Fadila ta koma aiki, aikinta take kamar da , inda a hankaki-ahankali cikin jikinta sai k'ara girma yake. Sannan yanzu rayuwar tasu da sauki tana yin amfani da dubu d'ayan da MD ke bata suna yin cefane .

Saidai tsakaninta da mahaifiyarta har yanzu babu wani sauk'i. Dan har yanzu bata amsa gaisuwarta kuma so da dama sai taita yi mata magana ta yi banza da ita.

Haka rayuwa ta yi ta tafiya har cikin Fadila ya tsufa , yanzu kam duk wanda ya san ciki kallo d'aya zai yi mata ya gane tana da ciki, duk da ta kasance ba mai girman ciki ba.

Rahama TV yanzu hankalin su gaba d'aya ya koma akan taron da za su yi na murnar cikar gidan TV shekara goma da fara aiki. Sosai suke shirin taron wanda za su yi Ranar Asabar kamar yadda suka tsara.

ADAMAWA STATE

Muhammad yanzu rayuwarshi ya ke lafiya lau ya cire duk wata damuwa a ranshi . Yau Muhammad bayan ya dawo aiki ne yana zaune falon mahaifinshi suna fira, mahaifin Mahammad ya ce " Mahammad, yakamata dai wannan Karan ace ka k'ok'arta ka je murnar cikar shekara goma da Rahama TV za ta yi , kodan kasan cewarsa mallaki ga mahaifiyarka, Allah sarki lokacin ta yi k'ok'ari sosai ganin gidan TV ya fara aiki sai dai bai fara aiki ba har sai bayan ranta , dan idan ba zan manta ba sai ta ya yi shekara kusan koma cir da bud'eshi amma ba'a fara amfani da shi ba sai bayan kusan shekara koma, tun da kadawo karatu kullum nake maka magana akan kaje ka ganshi amma kak'i "Muhammad kai ya jinnina ya ce " Daddy, in sha Allah wannan Karan dai zan je, yaushe za'ai taron ? " This coming Saturday" Shi kenan zan yi k'ok'ari inga na je" Tom zan yi magana da Murtala Isa shi ne shugaban gidan TV "

KADUNA GARIN GWAMNA

Yaune ya kama za ai taron Rahama TV , inda Fadila ta shirya ta tafi da wuri duk da bata jin dad'in jikinta sosai , tun jiya take fama da ciwan mara haka dai ta daure ta tafi.

Taro ya yi taro inda taron ya samu halarta manya mutane da dama , daga ciki hadda Muhammad Sagir mai shadda da ya yi tattaki shima tun da ga Adamawa ya zo.

An yi taro angama inda sosai abun ya k'ayatar da Muhammad ,sai dai yadda ya ji ana bada tarihin yadda mahaifiyarshi ta shiga ta fita dan ganin ta bud'e gidan TV , sai dai Allah da ikonshi gidan TV bai fara aiki ba har sai bayan ranta, hakan ya sa Muhammad ya k'udirci taimaka ma gidan TV ganin ya d'aukaka yafi da haka.

Bayan an gama taron ne aka gabatar da Muhammad amatsayin wanda zai ba ma'aikatan gidan TV Frame na shaidar karramawa. Haka aka fara Kiran d'aya bayan d'aya ana basu har aka zo kan Fadila, wadda ta tashi duk a d'arare dalilin cikinta da ya fito.

Muhammad cikin fara'arshi ya mik'ama Fadila Frame d'inta inda aka d'aukesu photo dai dai zai mik'a mata.

Haka aka yi taro aka tashi, bayan taro ya tashi ne Muhammad ya yi ma MD magana akan yana so ganin lungu da sak'o na gidan TV. MD Fadila ya Kira a waya ya ce ta samai a office d'inshi, bayan ta zo ne ya ce " Fadila, ki zagaya da shi ko ina na gidan nan " Fadila cikin daurewa da ciwan marar da take ji ta tafi.

Muhammad tashi ya yi ya bi Fadila , duk in da suka je Fadila za ta yi mai bayanin wajan. Inda Muhammad ke jinjina kai kawai ba tare da ya tanka ba.

Fadila d'akin da suke gabatar da shirye-shiryensu ta kai Muhammad ta ce " Nan ne muke gabatar duk wani shiri da muke yi " Muhammad kallan Fadila ya yi yana mamakin yadda ba sai ya tambayeta ba take mai bayanin duk in da suka je kuma takan yi mai gamsassan bayani da ba sai ya naimi k'arin bayani ba.

Muhammad kallan Fadila ya yi ya ce " Ke awana b'angaran kike ?" Fadila shiru ta yi ,dan yanzu takan ji ma kunyar fad'in b'angaran da take aiki akai,haka dai ta daure cikin sanyi ta ce " Ni ce shubatar Shirin DARAJAR 'YA MACE " Wonderful " Muhammad ya ce , sannan ya ci gaba da cewa "Wata matsala ce kuke fuskanta ? Sannan me ye kike ganin zai k'ara d'aga darajar gidan TV nan dan na yi sha'awar bada gudinmuwata? " Fadila da mamaki ta d'aga kai tana kallan Muhammad , take kuma ta kauda mamakinta dan shi d'in ya yi kama da wanda zai iya hakan"
Fadila magana zata yi ta kasa jin yadda mararta gaba d'aya ta murd'a , dama kuma dauriya kawai take dan tun jiya take jin hakan. Fadila da sauri ta duk'e a wajan tana mai dafe mararta tana cije baki.

Muhammad da mamaki ya kalleta ya na tambayarta " Lafiya ? "Fadila da kyar ta iya bud'e baki ta ce " Cikina " Subhannallah baki da lafiya ne ? " Fadila zuwa yanzu ba ta iya magana , durk'ushewa ta yi awajan ta rik'e marar katakam.

Muhammad juyawa ya yi da niyyar ya yi ma MD magana, sai dai kafin ya d'aga k'afar Fadila tsabar azaba da ta ji ta rik'e mai k'afa d'aya katakam, tana jijjiya kai dan na kud'ace gadan-gadan ta taho ma Fadila.

Muhammad rasa yadda zai yi ya yi yana son zuwa ya Kira MD amma Fadila ta rik'eshi bada wasa ba. Muhammad Kiran MD ya yi awaya ya sanar da shi halin da Fadilar take.

MD da sauri ya nufo inda suke , yana zuwa ya kalli Muhammad ya ce " Da'alama na k'uda take aihuwa zata yi " Haihuwa kuma ? Shi ne ta zo aiki kuma ? "

Jamilu da yaga lokacin da Fadila da Muhammad suka wuce yanzu kuma ga tahowar MD da sauri tashi ya yi ya nufi inda suke dan shi gaba d'aya ya fara zargin MD akan cikin Fadila .

Jamilu koda ya je ya ga halin da Fadila ta ke ciki cikin rud'ewa ya yi kanta. Tsawar da MD ya yi masa ce ya sa ya fasa kamata d'in da ya yi niyya.

Muhammad kuma kallan MD ya yi ya ce " Ku kira mijinta mana ku sanar da shi halin da take ciki ? " MD shiru ya yi baitanka ba, sai zuwa can ya ce " Da akwai wata asibiti nan kusa bari in je in taho da d'aya daga cikin likitocin su dubata.

Muhammad da Jamilu nanan kan Fadila da ke ta cije-cije a wajan , kuma har yanzu rik'e take da k'afar Muhammad.

Muhammad da mutum ne mai tausayi sosai kallan Jamilu ya yi ya ce " Ku kira mijinta mana " Jamilu shiru ya yi dan bai san amsar da zai ba Muhammad ba, kuma hakanan ya ji baya buk'ar sanar da shi Fadila bata da miji.

Muhammad sunan tsaye MD ya zo da likitoci biyu mata.

MD da ya fara rud'ewa da yadda ya ga Fadilar ya ce " Ku kamata mu tafi asibitin mana " D'aya daga cikin likitocin ta ce " Nak'udarta ta riga ta kankama zata iya haihuwa a mota muna tafiya sai dai mu bari ta haihu a nan ✍🏻

SANARWA : Ba zan yi posting weekend ba , sai ranar Monday za ku jini in sha Allah.

📚 FADEELAH 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo musu na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH.

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.