Complete Hausa Novels

Fadeelah Complete Hausa Novel

Reading file: FADEELAH By Fadila Sani Bakori.txt

Chapter 6 of 12

Page 6

Fadila ta tashi yau bata jin dadin jikinta, hakan nan dai ta je aiki, koda ta je bayan sun gama gabatar da Shirin da suke yi ne ta kalli Jamilu ta ce"Jamilu, zan yi ma MD magana gida zani ba ni da lafiya. " Fadila tana fad'in haka ta tashi da sunan tafiya , saidai sakamakon jirin da take gani tana tashi ta yanke jiki ta fad'i"

Jamilu da sauran abokan aikinsu cikin rud'ewa su ka yi kan Fadila da ke kwance a k'asa a sume.

Jamilu fita ya yi ya je ya yi ma MD magana ya sanar da shi halin da Fadila take ciki.
MD Cikin mamaki ya kalli Jamilu ya ce"Jamilu, bata da lafiya ne dama?" Tom, ni dai ban sani ba, sai yau bayan mun gama aiki take sanar da ni bata jin dad'in jikinta za tafi gida, tom ta tashi ne ma da niyyar zuwa ta sanar da kai ta yanke jiki ta fad'i " MD cikin damuwa da halin da aka fad'a mai Fadila na ciki ya ce " Mu je akaita Asibiti a duba lafiyarta"

Da taimakon Firdausi da Ummi aka Fadila a mota, wa inda suma ma'aikata ne a gidan TV , suka tafi Asibitin.

Suna tafiya kafin su isa Asibitin Fadila ta farka , kallan Ummi ta yi wadda take kwance ajikinta, cikin k'asa da murya irin ta marasa lafiya Fadila ta ce" Ummi , Lafiya ? Ina Zamu? " Ummi cikin kwantar ma Fadila da hankali ta ce " Ba ki da lafiya ne shi ne za mu kaiki Asibiti a duba lafiyarki " Fadila shiru ta yi tana mamakin yadda akai haka , Sannan ta ce " Na ji sauk'i MD mu juya "

Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya ce" Ki bari mu je a duba lafiyarki hakan na da kyau"

Koda suka shiga cikin Asibitin Fadila saida ta dafa Ummi saboda tsananin jirin da take ji . MD Ummi ya ba kud'i ta sayi katin Asibitin sannan suka shiga wani Office. Likitar kallo d'aya ta yi ma Fadila ta gano abun da ke damunta, amma sai cewa ta yi" Me ke damunki ? " Jirine kawai sai rashin k'arfin jiki da ke damuna " Cewar Fadila. Kai likitar da jinjina sannan ta ce" Tun yaushe kike jin hakan ? " Tsakanin jiya da yau ne na fara jin hakan " Likitar laboratory Lab ta tura su Fadila blood test.

Cikin kankanin lokaci aka yi ma Fadila awon ta kawo ma likitar sakamakon .

Likitar na dubawa murmushi ta yi ta kalli Fadila ta ce " Kira min mai gidanki shi zan fad'ima ma wannan sakamakon " Fadila murmushi ta yi ta ce" Ba mujina bane Ogana ne , ki fad'in kawai "

Shiru likitar ta yi tana kallan Fadila, Sannan ta ce" Kina d'auke da cikin wata d'aya da kwana kai " Fadila zaro mayan-manyan idanunta ta yi tana kallan likitar ta ce" Likita ciki kuma ? , Kuma ni ? Kai ! ki sake bincikata dai ki gani , budurwa ce ni fa ba ni da aure ! " Likitar kara kallan Fadila ta yi da kyau sannan ta ce " 'Yan mata kina zuwa kallo d'aya na yi miki na gano abun da ke damunki "

Fadila tashi ta yi ta ce" Ina ban yarda ba Wallahi , ciki fa ? Kuma ni ?, to ,ta ya ya?"

MD jin alamun kamar hayaniya tsakanin Fadila da likitar , ya shigo office d'in yana tambayar Fadila Lafiya.

Fadila tsabar takaici kasa ba MD amsa ta yi , sai likitar ce ta ce " Ciki take d'auke da shi, shi ne ta tsaya tana gaddama wai in sake bincike , bacin tunda ta shigo kallo d'aya na yi mata na fahimci abun da ke damunta "

MD rasa abun cewa ya yi ya tsaya yana kallan Fadila kamar wani sakarai , Fadila kuma tsabar takaici kawai sai ta fashe da kuka ba wai dan ta yarda da maganar kikitar ba ne , tana kukan shairin da ta yi mata ne.

Likitar ko ganin haka kallan Fadila ta yi ta ce" Yi hak'uri 'yan mata share hawayanki idan biki yarda ba ko kina ganin shairi na yi miki za ki iya zuwa wani Asibitin a dubaki" Tana fadin haka ta kalli MD ta ce za ku iya tafiya "

Haka suka fito ba wanda ya tanka ma kowa. Ummi ko wadda ta ji duk abun da ke faruwa ita kanta ba k'aramin mamaki ta yi ba.

Fadila da har yanzu jiri take gani rik'e Ummi ta yi da sauri . MD kuma ganin haka ya ce " Kinga ma ko magani ba mu tsaya amsa ba , mu je wani Asibitin a dubaki a baki magani "

Innalillahi wa inna ilaihir raj'un , hankalin Fadila ba k'aramin tashi ya yi ba , lokacin da aka maimaita mata tana d'auke da ciki kamar yadda waccan likitar ta fad'a mata. Abun ka da mai ganin jiri Fadila yanje jiki ta yi ta fad'i wajan asume.

Take aka ba Fadila gado , in da MD kuma ya kalli Ummi ya ce" Ki kula da ita ina zuwa "

Ummi ko da dama ba wani shiri suke da Fadila ba ,ai abun yad'awa ya samu agareta , gefe guda ta koma , Jamilu ta fara kira ta sanar da shi Fadila na d'auke da ciki. Jamilu jin maganar ya yi wata iri ,sannan cikin b'ata fuska ya ce " Ummi , wannan kuma wata irin magana ce haka ? Idan ma wasa ne wannan ai ba wasa ba ne , haba ki rasa kan wadda za ki fad'i wannan muguwar fatar taki sai kan Fadila "Ummi da abun da ake so ya samu ta ce" Jamilu , Wallahi kar ka ji batun wasa Fadila ciki gareta ta , da aka fad'i ita kanta nunawa ta yi bata yarda ba irin borin kunyar nan , to shi ne MD ya ce mu je wani Asibitin a bata magani saboda wancan borin kunya ya sa ta k'i bari a bata maganin ma , aiko muna zuwa nan aka maimaita mata kamar yadda aka fad'i a d'ayan Asibitin"
Jamilu Allahhuma ajirni filmusibati kawai ya ke maimaitawa sannan ya ce" Ummi , kuna wana Asibin ne idan na tashi aiki in zo? " Muna nan Wisdom Hospital "

Ummi na nan zaune Jamilu na tashi aiki ya zo cikin k'osawa da ya ga halin da Fadila take ciki . Allah ya sa tana farkawa ya shigo. drip d'in da aka samata saura kiris ya kare .

Jamilu cikin sanyi ya ce" Sannu Fadila , ya jikin naki ? " Fadila fashewa da kuka ta yi ta na cewa " Jamilu , ka ji shairin da su ka yi min ko ?" Fadila ta idasa maganar cikin tsantsar tashin hankali da damuwa.

Jamilu shiru ya yi yana kallan Fadila ya ma rasa abin cewa.

Fadila tashi ta yi tana kallan Jamilu ta ce" Jamilu , dare ya yi za a naimeni a gida , gida zan tafi " A'a , Fadila ki yi hak'uri jikin ki ya yi sauk'i , Sai in je gidanku yanzu in sanar halin da kike ciki " Fadila kallan Jamilu ta yi ta ce " Me za ka ce musu yana damuna ? " Zan sanar da su ne cewa baki jin dadin jikinki" Kai Fadila ta girgiza ta ce " Karka fad'a musu komai , bari na ji sauk'i zan iya kowa"

Babu yarda Jamilu bai yi da Fadila akan ta kwana Asibitin zuwa gobe a bata sallama in da ance jikin nata da saura, amma tak'i .

An sallami Fadila suna bakin titi za su tari Keke-Napep motar MD ta tsaya .Bud'e ma Fadila ya yi ya ce " Shigo in k'arasa da ke gida " Fadila ji ta yi bata da wani zab'i wanda ya wuce ta shiga , in da dakyar take tsayuwar dan gaba d'aya bata jin k'arfin jikinta ,hakan ya sa ta shiga motar.

MD sai da ya kai Fadila har k'ofar gidansu sannan ya mik'a mata ledar maganungunanta ya juya ya tafi ba tare da ya ce mata komai ba.

Mahaifin Fadila ya fito kenan za shi masallaci sallar Issha'i aka sauke Fadila a mota akan idon shi, Mahaifin Fadila bin bayan Fadila ya yi da kallo ganin yadda take tafiya kamar wata 'yar maye.

Fadila ahankali cikin raunanniyar murya ta yi sallama ta shiga gidansu.
Mahaifiyar Fadila da kallo tabi Fadila ganin yadda ta shigo kamar wadda tasha ta bugu .Fadila na zuwa ta kwanta kan d'an madaidaicin gadonsu.

Mahaifiyar Fadila tashi ta yi tana cewa" Fadila , lafiyarki kuwa ? " Ban da lafiya " Fadila ta bata amsa a takaice.
Mahaifiyar Fadila shiru ta yi sannan ta ce " Shi ne dalilin dad'ewar taki kenan ? " A'a mun je Asibiti ne " Me ke damunki ? " Mahaifiyar Fadila ta tambayi Fadila.
Fadila cikin rashin sanin amsar da zata bata ta ce" Ban sani ba nima" Ta fad'i maganar tana goge hawayan da ke zubar mata.

Mahaifiyar Fadila ko da bata kawo komai aranta ba dan ita ta yi tunani ma kodan lokacin da mahaifinta ya bata yana gaf ya cika ne ya sa kila take son sa kanta cikin damuwa, hakan ya sa ta zauna bakin gadon da Fadilar ta ke, ta ce " Fadila , me ke damunki ne ? Lokaci guda haka kika rikice, In dan ma maganar mahaifinki ce ki kwantar da hankalinki shi aure ai lokaci ne , dan haka karma ma ki sama kanki damuw..."
Sallamar mahaifin Fadila ce ta sa Mahaifiyar Fadila ta yi shiru. Mahaifin Fadila ya ce " Fadila , wa ya kawo ki k'ofar gidan nan a mota ? " Fadila tana goge hawayan da ke zubar mata ta ce " Ba ni da lafiya ne ba na jin k'arfin jikina shi ne MD ya kawoni a motarsa " Shiru mahaifin Fadila ya yi dan sosai ya ke yabawa da hankalin ogan nata .
Ya san tabbas in ba rashin lafiya ba kodan munafukan layin nasu ya san Fadila ba zata yarda ta hau motar kowa ba ya kawoka har k'ofar gida , kuma a cikin wannan lokaci haka ba rana ba .

"Shi kenan, Fadila dan Allah a k'ara kulawa da kai , duk in da kike kisan in ba ma ganinki mahaliccinki na ganinki " Fadila dakyar ta iya bud'e baki tana mai k'ok'arin danne kukan da ke taso mata ta ce " In sha Allah, Baba "

Mahaifiyar Fadila da kanta ta sawo ma Fadila tuwon da ta yi ta kawo mata .

Fadila ko ba dan tana son cin tuwan ba sai dan kar a fahimci halin da take ciki ta daure taci kad'an , Sannan ta lallab'a ta yi sallah ta koma ta kwanta.

Kasancewar har washegari Fadila bata jin k'arfin jikinta hakan ya sa bata yi wani yunk'urin zuwa aiki ba.

Mahaifiyar Fadila na kitchen tana dama musu koka k'anwar Fadila wadda ke bi mata Aisha kenan wadda satin d'aya kenan da dawowa hutu da yake bording School take yi .Bayan ta gaida mahaifiyar tasu ne ta ce " Mama , anya kuwa ba akwai abin da ke damun Aunty Fadila ba ? Jiya fa kwana kuka ta yi ? Ko yanzu haka idan kika shiga d'akin za ki ganta tana kuka kad'an-kad'an " Mahaifiyar Fadila barin abun da take yi ta yi tana kallan Aisha ,sannan ta ce" Biki tambayeta me ke damunta ba ? " Jiya da daddare dai bayan kin fita na tambayeta ta ce min babu komai , daga nan ni kuma ban kuma tambayarta ba " Shiru mahaifiyar Fadila ta yi , sannan ta tashi ta nufi d'akinsu Fadilar.

Kwance mahaifiyar Fadila ta samu Fadila tana kuka k'asa-k'asa sosai , sai uban ajiyar zuciya da take ja .Mahaifiyar Fadila zama bakin gadon ta yi tana bubbuga k'afar Fadila , ta ce " Fadila , tashi ki zauna"
Fadila da sai yanzu ta ji alamun da mutun ad'akin goge hawayanta ta yi da sauri ta tashi ta zauna.

Mahaifiyar Fadila ganin yadda idon Fadila ya kumbura ya yi jajir tsabar kuka , cikin damuwa ta ce " Fadila , lafiya me ke damunki Wanda ya sa kika kwana kina kuka tun jiya har yau ?" Fadila k'asa ta yi da kanta tana mai goge hawayan da ke zubar mata.

Mahaifiyar Fadila ta kuma cewa " Fadila, me ya faru dake ne haka wanda ba zaki iya fad'imin ba? Idan ni biki fad'a min ba sai ki sanar da Aisha , kalli fa yadda idonki ya kumbura "

Fadila ci gaba da kukan ta yi kuma tak'i yin magana .Mahaifiyar Fadila kamar ta yi zuciya ta rabu da ita ,amma kuma ta kasa , hakan ya sa cikin damuwa ta kuma cewa " Ko wajan aikin naku ne akai miki wani abun ? " Kai Fadila ta girgiza. " Me a kai miki to? " Nan ma dai Fadila shiru babu amsa.

Atak'aice Mahaifiyar Fadila babu irin tambayar da ba ta yi ma Fadila ba akan abun da ke damunta amma shiru tak'i magana sai kuka. Suna cikin haka ne Aisha k'anwar Fadila ta shigo .Aisha cikin damuwa da halin da taga Fadilar ta kalli mahaifiyarsu ta ce " Mama, me ke damunta ne ? " Aisha ban sani ba , tak'i fad'a min , kira min Jamilu awaya mu yi magana da shi in ji ko wani abun ne ya faru jiya acan wajan aikin nasu "

Mahaifiyar Fadila Jamilu ta sa aka kira mata, bacin sun gaisa ne ta ce " Jamilu , lafiya ? Tun jiya Fadila da ta shigo gidan nan take kuka na yi na yi ta k'i fada min abun da take ma kuka , shi ne na ce bari in tambayeka ko ka sani ? "

Jamilu shiru ya yi dan baisan amsar da zaiba mahaifiyar Fadila ba , hakan ya sa ya ce "Mama, idan na tashi aiki zan biyo ta nan "

Mahaifiyar Fadila da Aisha tashi su ka yi suka bar Fadila anan tana mai ci gaba da kukanta.

Har Jamilu ya tashi aiki ya zo gidan idanun Fadila ba su bar zubar hawaye ba.
Mahaifiyar Fadila bayan sun gaisa da Jamilu ta ce " Jamilu, tun jiya Fadila ke kukan nan har yau , mun yi mun yi ni da 'Yar'uwarta ta k'i fad'amana abun da ke damunta , shi ne dalilin kiranka na ga taku ta zo d'aya ko kai ta fadi maka ? " Jamilu shiru ya yi ,ya ma rasa ta ina zai fara . Tabbas zuciyarshi ta kasa aminta mai da wai Fadila na da ciki .
Jamilu kallan Fadila ya yi ya ce " Fadila, ko dai ki fad'a mana damuwarki ko kuma ki yi hak'uri da kukan nan da kike yi , kina sa 'Yan'uwanki da mahaifiyarki cikin damuwa, dan Allah ki daure ki sanar damu gaskiyar lamarin abun da ke damunki ? ".

Fadila kai ta d'aga tana kallan Jamilu da idanunta wa inda har sun fara kankancewa tsabar kuka .Sannan cikin kuka ta fara magana kamar haka " Jamilu, nima bansan abin da ke damuna ba. Saidai ina jin rayuwata ta zo k'arsh..." Aisha k'anwar Fadila rufe mata baki ta yi ta ce kamar za ta yi kuka ,dan tabbas kome yake damun Aunynta mai girma ne, wanda har ta kasa fad'a musu.
Aisha da hawaye har ya fara zubo mata ganin yarda Fadila ke kuka ta ce " Haba, Aunty Fadila, dan Allah kar ki sa zuciyarmu cikin waswasi mana, kisa mu yi ta canke-canke abun da ba shi kenan ba , dan Allah ki fad'amana damuwarki ? Idan kuma kink'i zan je in kira Baba in sanar da shi abun da ke faruwa na san shi zaki fad'i mai " Aisha na fad'in haka jin Fadila bata ce komai ba ta tashi zata fita alamun zata kira mahaifin nasu.

Fadila da sauri ta kamo hanun Aisha tana mai k'ara tsananta kukanta ta ce " Mama , ku yi hak'uri zan sanar da ku ? Amma dan Allah ina rok'onku ku ban nan da sati d'aya sannan ✍🏻

*🤝 SDEEND MTN DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For

📚 FADEELAH 📚

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori.

SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki acikin wannan littafi mai suna FADEELAH.

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.