Complete Hausa Novels

Fadeelah Complete Hausa Novel

Reading file: FADEELAH By Fadila Sani Bakori.txt

Chapter 3 of 12

Page 3

Falon alhaji Sagir Suka koma suka zauna ,bacin sun zauna ne alhaji Bala ya kalli alhaji Sagir ya ce"Alhaji,ni fa ina ganin a yi ma Muhammad wani auran cikin satin nan ,kila a samu kwanciyar hankalinsa,dan gaskiya yanda na ga Muhammad abin ya tadamin hankali sosai"
Shiru alhaji Sagir ya yi sannan zuwa can ya ce"Ni ma na yi tunanin haka ,amma wa zan aura wa Muhammad ?Shi ne abun tunanin"
Maryam,yarinyar wajena ita za a aura mai cikin satin nan kuwa in sha Allah"
Mahaifin Muhammad hanun alhaji Bala ya kamo ya na cewa"Na gode sos...."Dakatar da shi alhaji Bala ya yi ta hanyar cewa"Haba ai yi ma kaine,babu godiya tsakaninmu dan na yi ma Muhammad wani abu"

KADUNA GARIN GWAMNA

Bikin Fadila yanzu saura sati shida inda har yanzu ta na kan bakarta na ba za ta auri Jamilu ba.Mahaifin Fadila ko ya ce babu gudu babu ja da baya aure kamar ma an yi sa ne.Haka aka ci gaba da shirye-shiryan biki.

Yau kwananan Jamilu goma kenan rabanshi da zuwa wajan Fadila,inda ko ya je shi ke kid'ansa shi ke rawar shi,Fadila ba ta tankamai.

Fadila na zaune ta yi shiru kamar kullum,k'anwarta ta zo ta sanar da ita Jamilu na d'akin Babansu wai ta zo. Tun da aka tsaida ranar auransu Mahaifin Fadila ya ce su rika shiga d'akinshi suna fira.

Fadila tashi ta yi ta sa hijab dinta ta nufi d'akin mahaifinta.
Fadila zama ta yi ba tare da ta tankamai ba.
Jamilu kallanta ya yi ya ce"Barka da zuwa malama Fadila,da fatan kina lafiya? Ina Kiran wayarki amma baki d'agawa,hankakina ya tashi na ce bari in zo in ji lafiya,daga nan inga kyakkyawar fuskarki"Ba na kusa ne"Fadila ta ba shi amsa a tak'aice,sannan ta d'ora da cewa"Jamilu,ina son in fallasamaka abin da ke cikin zuciyata,saidai babu lallai ba dole ka aminta da abin da zan ce,amma kuma duk abin da ya biyo baya ban yaudareka ba,kuma ban d'auki alhakinka ba.Magana guda d'aya ta gaskiya ita ce,Zuciyata ta kasa aminta da taka zuciyar,na yi iya k'ok'arin ganin na tursasata amma abin ya ci tura,atakaice har rauni na yi mata wajan jajircewa da bujire mata akan aminta da kai amma ta k'i,ina had'aka da girman Allah ka yi hak'uri ka hak'ura da zuciyar da ta kasa aminta da kai ka janye maganar da ke tsakaninmu,saboda ko ka aure ni zai zamana gangar jikina kadai zaka aura"

Jamilu shiru ya yi zufa na keto mai kota ina,daga k'arshe ma ba tare da ya tanka ba ya tashi ya tafi.

Yau sati d'aya kenan da Fadila ta sanar da Jamilu akan ya janye maganar auranta,saidai har yanzu ba ta ji wata magana ba mai kama da an janye
,saidai tun daga ranar Jamilu bai kuma kiranta a waya ba,saidai akwai abu d'aya da ta lura da shi mahaifinta kwana uku kenan baya amsa gaisuwarta,yau ne kuma ta k'udirci tuntub'ar mahaifiyarta dan jin ko ta yi ma mahaifinta wani laifi ne.

Mahaifiyar Fadila da daddare bayan ta idar da sallar magriba ta na zaune kan sallaya Fadila ta zo ta zauna gefan mahaifiyar tata,shiru-shiru kamar mai tunanin ta in da za ta fara,sannan ta ce"Mama,kwana biyu idan na gaida baba baya amsawa dan Allah ko na yi mai wani laifi ne Wanda ni ban sani ba?"
Mahaifiyar Fadila d'ago kai ta yi tana kallan Fadila,sannan ta girgiza kai ta ce"Tom,Fadila ni in kin yi mai wani abu ma ban sani ba,dan bai fad'amin ba,saidai in ya dawo ki je ki tambaye shi ki ji"
Fadila cikin marairaicewa ta kalli mahaifiyarta ta ce"Mama,dan Allah ki mai magana da kanki kin ga ni ba zan iya yi mai ba"Tom,shi kenan sai ki hak'ura ,dan nima ba zan iya yi mai ba."

Fadila haka ta hak'ura ta tashi.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya,in da ya rage har saura sati d'aya d'aurin auran Fadila kamar yadda mahaifinta ya sa.

Fadila ko yanzu abin da ke damunta bai wuce na gaisuwarta da mahaifinta ya bar amsamata ba.
Jamilu ko har yanzu tun da ta yi mai maganar nan bai kuma kiranta a waya ba.

Fadila har ya kama saura kwana uku biki bata ga ana wani shirye-shirye shirye na biki ba,haka ya tabbatar mata da babu bakin kenan,kuma dama ta dad'e tana zargin hakan.

Yau ne ya kama ranar da za'a daura auran Fadila kamar yadda mahaifinta ya tsaida,amma kuma shiru ka ke ji.

Fadila sosai ta yi murna da hakan,amma b'angare d'aya na zuciyarta cikin fargabar mahaifinta ta ke.

Da daddare Fadila na kwance mahaifinta ya aiko kiranta.

Fadila koda ta je ta dad'e a tsuk'unne ba tare da ya tanka mata ba,kamar ba zai tanka mata ba sai zuwa can ya ce"Fadila, kin maida ni karamin mutum, mutumin banza mai k'aramar magana,dama mutane na namin kallan wanda baisan abin da ya ke ba na je kamar ki a gida ba aure,idan an ce rashin mijine yanzu gashi mijin ya zo kin korai.Yanzu fad'amin me ye nufinki in ji?"
Fadila shiru ba amsa.Mahaifinta ko ya ci gaba da cewa"Fadila,Allah ya sa ni na fita hak'inki,na baki ilimin na addini da na zamani,na had'aki da mijin aure har uku duk kin k'i kin nuna min ke wayayyiyace ba aure ba ne a gabanki,dan haka ga mahaifiyarki nan ta zama shaida"Mahaifin Fadila dakatawa ya yi ya na kallan mahaifiyar Fadila,sannan ya ci gaba da cewa"Watan uku muke ko?"Kai mahaifiyar Fadila ta d'aga alamun haka ne. Ya ce "Kafin nan da k'arshan shekarar nan in dai Fadila ba ta kawo wanda take jin zata iya aura ba,Wallahi Allah d'aya na gama zama da ita acikin gidan nan,saidai ta san in da zata zauna amma ta gama zamam min a gida in dai wannan wa'adin ya cika"

Fadila shuru ta yi kanta a k'asa.Mahaifin Fadila kallanta ya yi ya ce"Idan har muka kai watan sha biyu ba tare da kin kawo daidai da ke din da kike jin za ki aura ba,karki kuskura in zo in iskeki a gidana ,ba dai gidana ba Wallahi saidai ki naimi wajan zama"

Mahaifin Fadila sai da ya kuma nanata ma Fadila akan karka kuskura ta k'are shekarar nan ba tare da wata magana ba,sannan ya ce ta tashi ta bashi waje.

ADAMAWA STATE

Alhaji Bala yana komawa gida ya sanar da matarsa hajiya Halima maganar ba da Maryam da ya yi ga Muhammad.
Hajiya Halima sosai ta ji dad'in maganar ,dan Alhaji Sagir mai shadda abin alfahari ne ka had'a iri da shi.

B'angaran Maryam ma ko da mahaifiyarta ta tareta da maganar take ta amince babu ja.

Mahaifin Muhammad ko da ya sanar da hajiya baturiya ta ji dad'in hakan,dan acewarta k'ila hakan ya kwantar ma Muhammad da hankali.

Da daddare alhaji Sagir ya samu Muhammed da maganar.Amma har ya yi maganar shi ya gama Muhammad bai tankamai ba.Hajiya baturiya ta ce"Muhammad,ba ka ji abin da daddynka ya ce bane,sun yanke shawarar had'aka da Maryam yarinyar alhaji Bala aure,saboda tunanin hakan ko zai sa ka kwantar da hankalinka"

Muhammad da ya rasa abin cewa,kuma baya son gwalishe mahaifinsa hakan ya sa ya ce"Tom,mommy"

Hajiya baturiya za ta sake magana alhaji Sagir ya d'aga mata hannu alamun ta yi shiru.

Kwana goma suka tsaida auran,hakan ya sa b'angaran amaryar suka ci gaba da shirye-shiryan biki,inda b'angaran alhaji Sagir babu wani shiri da su ke yi.Maganar lefe ma alhaji Sagir kud'i ya ba su ya ce su yi komai.

B'angaran Muhammad ko yama manta da maganar wani aure da za a yi mai.

Ranar da ta kama d'aurin aure ba wani taro a ka yi ba,garama gidan su Maryam d'in sosai su ke shirin auran.

Ranar Juma'a da safe aka d'aura auran Maryam da Muhammad,in da ba wani taro a ka yi ba na ku zo ku gani.

Lokacin da labarin d'aurin auran ya isa kunnan Muhammad,sosai abin ya d'aga mai hankali ,dan sai da a ka Kira alhaji Sagir aka sanar da shi halin da Muhammad d'in ya ke ciki.

Alhaji Sagir sosai hankalinshi ya tashi ganin yarda Muhammad ya ke kuka.Babu irin lallashin da alhaji Sagir bai yi mai ba,amma kamar ma ba da shi ya ke ba.

Alhaji Sagir ganin yadda Muhammad ya ke kuka ko ranar da Hafsat ta rasu ma bai yi kuka haka ba,hakan ya sa cikin tashin hankali da damuwa ya ce"Muhammad, ko auran ne ba ka so?"
Muhammad cikin kuka ya d'aga ma mahaifinshi kai ya ce"Daddy ,bana son auran nan dan Allah,mu yi alk'awari da Hafsat ba zan tab'a auran wata in ba ita b..." Muhammad ya karashe maganar cikin tsantsar kuka da bayyanar tsantsar ta shin hankali a tare da shi.

Mahaifin Muhammad cikin damuwa ya ce"Muhammad, ka yi hak'uri ,Hafsat ta mutu ta je in da dukkan mu za mu je,dan haka dan ka auri wata ba laifi bane"

Haka alhaji Sagir da hajiya baturiya su ka yi ta yi ma Muhammad nasiha da lallashi a haka suka sa mu ya yi shiru .

D'aya daga cikin gidajan alhaji Sagir ya ba Muhammad in da za su zauna,dan acewar shi ba za'akai Maryam in da akakai Hafsat ba,itama gidanta sabo za a kaita.

Usman abokin Muhammad shi ya jagoranci komai game da d'aukar amarya aka kaita gidanta.

Usman da sauran abokan Muhammad babu yarda ba su yi ba bayan sun kai amarya sun dawo akan Muhammad ya shirya a kaishi gidan amaryar amma ya k'i.Daga k'arshe sai da su ka fad'ama alhaji Sagir.
Alhaji Sagir babu yarda bai yi da Muhammad ba akan ya tashi abokanshi su raka shi,amma ya k'i.Da suka damai ma kuka ya sa musu,hakan ya sa dole suka rabu da shi.

Usman da d'aya daga cikin abokan Muhammad d'in suka koma gidan amaryar.Lokacin ko sun samu kawayan duk sun watse sun barta ita kad'ai.

Ita ko Maryam ta yi sunanin angon ne ma ya shigo,amma sai ji ta yi Usman na cewa"Amarya,ki yi hak'uri za ki kwana ke kad'ai, Muhammad ba shi da lafiya saidai zuwa gobe in sha Allah za ki ganshi.Amma idan kina jin tsoro sai in kai ki gidansu ki kwana "Maryam murmushi ta yi ta ce"Ya jikin na shi?" Alhamdulillah, da sauk'i"Shi kenan,karka damu kanka zan iya kwana ni ka dai babu wata damuwa"

Alhaji Sagir cikin fargaba ya yi barci,duk da ya sa ma'aikatan tsaro sosai a gidan gani ya ke kamar itama Maryam din za a iya yi mata abin da a ka yi ma Hafsat.

Cikin dare alhaji Sagir ya farka a furgice sakamakon mummunan mafarkin da ya yi.
Hajiya baturiya jin tarin alhaji Sagir ne ta farka tana tambayar shi "Alhaji,lafiya kuwa? yanayinka kamar a furgice kake?"Alhaji Sagir jan numfashi ya yi,sannan ya ce kamar zai yi kuka"An kashe Maryam kamar yadda a ka yi ma Hafsa.."Hajiya baturiya katse shi ta yi da cewa"Haba,alhaji mafarki fa ba gaskiya ba ne,na san mafarki ka yi,ka kwanta da tunanin haka ne a ranka shi ne hakan ya zo maka a mafarki, amma in sha Allahhhu babu abin da zai samu Maryam."

Shiru alhaji Sagir ya yi gaba d'aya ya k'osa gari ya waye dan ya je ya dubo 'yar mutane.

Alhaji Sagir na nan zaune har a ka kira sallar asuba.Ana Kira ko ya tashi ya d'auki key d'in motar shi zai fita.
Hajiya Baturiya cikin damuwa ta ce"Alhaji,in sha Allah babu abin da ya samu Maryam,ka daure mu yi sallah sai in raka ka mu je"

Da kyar hajiya baturiya ta shawo kan alhaji Sagir ya yarda su ka yi Sallah.Suna yin Sallah suka fita gidan zuwa D'an maliki road in da aka kai Maryam.

Suna zuwa ma su gadin suka bud'e alhaji Sagir ya shige cike da tarin fargabar abin da idonshi zai gani.

Sun dad'e suna bubbugawa,amma shiru.Hakan sosai ya d'aga hankalin alhaji Sagir da hajiya baturiya. Hajiya baturiya cikin fashewa da kuka ta ce"Mun shiga uku,alhaji kar mafarkinka ya zama gaskiya!"

Alhaji Sagir ya na son ya Kira mahaifin Maryam ya ce ya ba shi numberta ya Kira ya ji,amma kuma yana ganin kamar zai d'aga mai hankali.

Alhaji Sagir ci gaba da bugun k'ofar ya yi,inda kamar daga sama sai ji ya yi an ce"Waye?"Alhaji Sagir cikin jin sanyi aranshin jin muryar Maryam d'in ya ce"My daughter daddynki ne bud'e ko"

Maryam bud'ewa ta yi tana mamakin dalilin zuwan alhaji Sagir da asuba haka.

Alhaji Sagir da hajiya baturiya haka su ka bi Maryam da kalo.

Maryam wadda cikin barci ta ji yo bugun kofar falon,cikin sanyi ta ce"Daddy Allah ya sa dai lafiya na ganku da asuba ko jin Muhammad d'in ne?" Dan ita ta d'auka ko Muhammad ne ma ba lafiya.

Alhaji Sagir cikin sauke bayyanannar ajiyar zuciya ya ce"Maryam, Wallahi wani mugun mafarki na yi hankalina ya k'i kwanciya shi ne dalilin zuwanmu muga lafiyarki"

Murmushin jin dadi Maryam ta yi ganin yarda surukan nata suka nuna kulawa sosai akanta, ta ce"Ayyah,babu komai Daddy,in sha Allah babu abin da zai faru da ni,wancan ma wani rubutaccan al'amari ne"

Alhaji Sagir kai ya jinjina ya ce"Haka ne Maryam.Shi kenan bari mu tafi"

Hajiya baturi cikin marairaicewa ta ce"Ni dai alhaji duk da Maryam ba ita kad'ai bace a gidan hankalina ya fi karka ta akan mu tafi da ita,Allah bashi sai su dawo da Muhammad tare"

Alhaji Sagir cikin gamsuwa ya ce"Haka ne,Maryam d'akko mayafinki mu tafi ,kun dawo anjima da Muhammad tare"

Haka alhaji Sagir suka tasa Maryam su ka tafi da ita.

KADUNA GARIN GWAMNA

A yau jama'ar gasuwar magani ta Kaduna suka tashi cikin tashin hankali saboda rusan kasuwa da a ka yi musu,wanda abin ya had'a harda shagon mahaifin Fadila da ke saida kayan gwari.

Sosai rayuwa ta fara sauya wa su Fadila,inda dama kullum sai an fita kasuwa an nemo suke samun abin da su yi cefane.

Yanzu rayuwa ta fara tsananta wa su Fadila,Yanzu haka yau sun tashi babu abin da za su ci,ga shi kasuwar da aka dogara da ita wadda kullum sai an fita ake samo kudin cefanan abin da za su ci, gashi an rushe kasuwar.

Mahaifin Fadila kwance yana tunanin abin da za su ci,kallan mahaifiyar Fadila ya yi ya ce"Maman Fadila,na ce ko shinkafan nan za a auna a saida a samu kud'in cefanan abin da za mu ci?"
Shiru mahaifiyar Fadila ta yi,sannan ta ce "To,shinkafar ita kasan ta kare saura mudu uku ta rage mana,idan an saida mudu d'aya kaga saura mudu biyu kenan?" Tom,Ya za a yi haka nan za a saida in da za a zauna da yunwa ne?"

Mahaifiyar Fadila ba dan ta so ba haka nan taba yaro ya je ya saida mata mudu daya daga cikin shinkafar da ta yi ragowa,bayan yaron ya dawo ne su ka yi cefanan kayan mahad'in girkin shinkafar.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya,inda ya kasance komai nasu Fadila ya kare,duk wata dabara ta kare.

Yanzu haka tun safe har dare ba su ci komai ba.Mahaifiyar Fadila cikin taushin murya ta fara yi ma mahaifin Fadila magana kamar haka"Baban Fadila,dama cewa na yi inda dai ka ga in rushe maka hanyar da muka dogara da ita,wadda muke ci da sha a cikinta,me zai hana ka yi hak'uri Fadila ta koma aikinta kodan mu samu abin da za mu rik'a ci"

Shiru mahaifin Fadila ya yi kamar ba zai tanka ba sannan ya ce"Shi kenan zan yi tunani akan hakan ✍🏻

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori

SANARWA: Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban-daban da zan kawo muku na gyaran jiki a cikin wannan littafi mai suna FADEELAH .

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.