Complete Hausa Novels

Fadeelah Complete Hausa Novel

Reading file: FADEELAH By Fadila Sani Bakori.txt

Chapter 10 of 12

Page 10

Number Muhammad na shigowa Fadila ta Kira shi har kira uku bai d'aga ba, hakan ya sa Fadila ta mai text massage kamar haka : Assalamu alaikum. Da fatan ka je gida lafiya ? Na gode da sadaukar da lokacinka da ka yi agareni ka bani taimako har na haihu . Na gode sosai Allah ya sa ka maka sa mafificin alkairi "

B'angaran Muhammad ko lokacin da Fadila ta kira shi baya kusa , yana zuwa sakon text massage d'in ta na shigowa. Muhammad koda ya duba murmushi ya yi a zuciyarshi ya ce " Allah sarki tabbas ta cika mara manta halacci inda ga shi har ta amshi number ta ta kirani ta yi min godiya " Kasan cewar Muhammad mutum ne mai saukin kai hakan ya sa ya yi replying d'inta da " Ameen , ya jikin naki ? "

Fadila sosai ta kara ya bawa da kirkinshi da rashin kirman kanshi hakan ya sa cikin jin dadi ta mai da mai amsa da " Alhamdulillah. Na ji sauki "

B'angaran gidan su Fadila
Aisha sosai ta shiga damuwar rashin dawowar Fadila da bata yi gida ba.Hakan ya sa Aisha yau ta shirya da niyyar zuwa ta nemo in da Fadila take . Aisha koda ta gama shiryawa b'oye ma mahaifiyarsu ta yi inda zata, ta fita da sunan tafiya Islamiya.

Aisha bayan ta fito Kiran Jamilu ta yi a wayar mahaifiyarta da ta fito da ita bata sani ba. Jamilu na d'agawa bayan sun gaisa ne Aisha ta ce "Jamilu, zuciyata ta kasa jurewa da rashin ganin Aunty Fadila , dan Allah tana ina ina son ganinta ? " Jamilu shiru ya yi , sannan ya ce " Aisha, Wallahi nima takamaimai bansan inda Fadila take ba, ki kira numberta mana "A'a bana son ta san da zuwan nawa na fi son kawai ta ganni" Cewar Aisha.

Jamilu shiru ya yi sannan ya ce " Bari in turo miki number MD sai ki tambayeshi " Aisha ta ce "Ka tambayar min shi mana? " A'a Aisha ,da alama MD baya son in je in da Fadila take dan haka ki kirashi da kanki ki tambayeshi "

Aisha katse Kiran ta yi ta kira MD , bayan sun gaisa ne take sanar da shi tana son zata je wajan Fadila ne.

Shiru MD ya yi sannan ya ce " Shi kenan ki samu keke-napep sai ki had'ani da shi in ba shi Address d'in gidan "

Aisha mai Napep ta samu ta had'a shi da MD ya sanar da shi unguwar da zai kaita da number gidan .

Mai Napep d'in na aje Aisha ta fara nocking get d'in . Aisha na nan tsaye Baba Lami ta zo ta bud'e kasan cewar MD ya sanar da ita zuwan Aishar.

Baba Lami cikin fara'a ta ce " Sannu da zuwa , mu shiga tana ciki "

Aisha bin bayan Baba Lami ta yi har cikin d'an madai-daicin falonsu.

D'akin da Fadila take Baba Lami ta nuna ma Aisha ta ce " Ki shiga tana can "

Aisha da sallama ta shiga d'akin.

Fadila da ke zaune ta yi tagumi ta yi shiru ga yaron kwance kan katifar kusa da ita. Fadila da sauri ta kai dubanta ga k'ofar d'akin jin muryar Aisha.

Fadila tashi ta yi da sauri ta nufi wajan Aisha da niyyar rungumeta , sai dai da sauri ta tsuk'unna dan ta fama aikin da akai mata a ciki. Aisha da sauri ta k'arasa wajan Fadila ganin ta tsugunne tana dafe saman mararta .

Aisha cikin sanyi ta ce " Sannu ya jikin naki ? " Fadila ahankali ta matsa ta koma kan katifar ta zauna tana kallan Aisha, magana take son yi mata amma sakamakon kukan da ya zo mata ta kasa.

Aisha ko cikin sanyi ta ce " Aunty Fadila , sauri nake dan Mama bata san da zuwana ba , ki yi hak'uri ki bar kukan mu yi maganar da ta kawo ni " Fadila goge hawayan ta yi tana kallan Aisha alamun ina jinki.

Aisha kamar ba zata yi magana ba , sannan ta tashi ta d'akko jaririn da ke kwance kan makekiyar katifar d'akin irin gado huta d'in nan.

Aisha rungume jaririn ta yi tana kallo wanda ya sha tsadaddun kayan sanyinsa .Sosai Aisha ta yaba da kyawun yaron a zuciyarta .

Aisha kallan Fadila ta yi cikin sanyi ta ce "Aunty Fadila , wa ye mahaifin yaron nan ? " Fadila kallan Aisha ta yi da raunannun idanunta da yanzu ba su da wuyar fidda ruwa ta ce " Aisha, biki yadda dani ba ko ? " Aisha cikin alamun fad'a da kuma gajiya da rainun wayan da Auntyn tata ke yi musu ta ce " Aunty Fadila , me kike so ki ce min ne ? Haba Aunty Fadila, ki yi hak'uri ki bar yaudarar zuciyoyinmu haka nan mana, haihuwa fa kika yi ! Amma kike tambayata ban yadda da ke ba ? " Aisha ta fad'i maganar kamar ta rufe Auntyn tata da duka. Sannan ta ci gaba da cewa " Aunty Fadila , dan Allah ki bar yaudarar kanki damu kuma ki sanar damu mahaifin yaron nan ? "

Fadila kallan Aisha ta yi tana tashi da kyar dan ta fama ciwan ta inda aka yi mata theater . Fadila ta ce " Aisha , ina zuwa dan Allah "

Fadila toilet ta shiga ta yi alwallah ta fito, Aisha dai duk tana kallanta . Fita ta yi ta je d'akin Baba Lami sai gata ta dawo da Al'Qur'ani a hannunta .

Fadila kallan Aisha ta yi sannan ta ce " Aisha, zan miki rantsuwa da Qur'anin nan ba dan komai ba sai don bana son kina had'ani da abin da ban tab'a kusanta ba, na rantse da Allah da wanna Al'qur'anin idan har na tab'a kusantar zina Allah ya sa wannan al'wur'anin ya cine ,Allah ya nisanta ni da duk wasu rahamomin sa idan ha.... " Aisha da sauri ta rufe bakin Fadila tana kuka ta ce " Kin aika kuskure mafi muni Aunty Fadila, koda gaskiyarka baka rantsuwa da al'qur'ani, tabbas na yadda dake Auntyna ,hakan na nuni da cewa kenan Fyad'e akai miki ? " Fadila tana kuka ta ce " Ban sani ba Aisha , ni dai abu d'aya na sani ban tab'a aikata zina ba " Aisha kai ta jinjina, sannan ta ce " Aunty Fadila, idan haka ne ya tabbata jaririn nan MD ne ubansa , dan ni Wallahi shi nake kyautata zargina akan shi " Fadila shiru ta yi dan ita kanta lokuta da dama tana zargin MD d'in , saidai in ta tino ko sau d'aya maganar banza bata tab'a shiga tsakaninsu ba sai ta kauda tunaninta .

Aisha kallan Fadila ta yi da ta tsunduma duniyar tunani ta ce " Ki k'ara nazari sosai ki tuna ki yi tunani ki tuna abubuwan da suka faru a baya tsakaninki da shi ?, Ki yi dogon tunanin Aunty Fadila, na san za ki tuna " Fadila kai ta jinjina ta ce " Shi kenan Aisha zan yi"

Aisha kallan Fadila ta yi ta ce " Zan tafi " Fadila cikin sanyi ta ce " Aisha, dan Allah ki yi ma Mama magana indawo gida in zauna tare daku bana jin dadin zama nan da nake yi " Aisha kallan Fadila ta yi ta ce " Tom , ki yi tunanin abin da na ce miki ni na wuce " Aisha na fad'in haka ta juya ta tafi.

Aisha ko da ta koma gida bata sanar da mahaifiyarta ta je wajan Fadila ba.

BAYAN WATA UKU

Yanzu Fadila ta yi arba'in , inda Baba Lami ma tuni ta tafi tunda Fadila ta yi arba'in. Yanzu ya zamana Fadila ita kad'ai ce a gidan .

MD ko tunda Fadila ta zo gidan sau biyu ya tab'a zuwa shima duk abu ya kawo musu, ko d'akin Fadila bai shiga ba.

Yanzu Fadila ta gaji da zaman gidan dan kusan wata biyu kenan ita kad'aice a gidan sai yaronta da ya yi girma sosai tubarkallah .

Fadila so take ta koma gidansu da zama amma tana tsoran mahaifiyarta, haka dai ta k'udiri aniyar komawa dan tana ganin hakan ya fi mata mutunci . Ta kira MD ta sanar da shi k'udirinta amma ya ce ta jira tukun.

Yau sati d'aya kenan da Fadila suka yi magana da MD zai zo amma har yanzu bai zo ba . Fadila na zaune ta yi ma Ahmad wanka ta kwantar da shi saboda ya yi barci, ta ji shigowar MD bakin shi dauke da Sallama .

Fadila kai ta d'aga tana kallan MD sannan cikin jin dad'in zuwan MD d'in dan yau ta k'uduri barin zaman gidan ta ce " Barka da zuwa " MD kai ya jinjina ma Fadila sannan ya ce " Kin kirani akan zaki koma gida ? Kina ganin babu matsala ?, Mama ta hak'ura ne ? " Zan gwada in gani ne " Kai MD ya jinjina nan ma , sannan ya mik'a mata hollondia Yoghurt d'in da ya zo da shi ya ce " Ga shi ki sha wannan sai mu wuce " Fadila amsa ta yi ta sha dama yau ta kasa yin girki tsabar tasa ranta a tafiya gida .

Fadila na gama shan hollondia d'in take ganinta ya fara d'aukewa ta fara ganin duhu-duhu . Fadila cikin rud'ewa da yadda ta ji take ta sauya ga ganinta ya d'auke dishi-dishi take gani ta ce " MD, ba fa na gani duhu-duhu nake gani ? " Fadila ta fad'i maganar a rud'e

MD baitanka ma Fadila ba.

Fadila tashi ta yi ta fara laliban hanya sai ji ta yi an rungomata baki d'aya, daga nan jinta da ganinta ya d'auke bata k'ara sanin abin da ake ba.

ADAMAWA STATE

Yau ya kama Weekend Muhammad na gida, dama shi an fi samun shi a falon Hajiya Baturiya in dai yana gida. Muhammad zaune ya ke suna fira da Hajiya Baturiya Alhaji Sagir ya shigo falon wanda dawowarshi kenan daga maiduguri. Zama ya yi yana cewa " Tom , Alhamdulillahi. Yanzu dai muna sa ran komai ya kusa zuwa k'arshe ko ince ya zo k'arshe , Muhammad, wannan tafiyar tawa da na yi baki d'ayanta taka ce, wato wani abokina ne mu ka yi magana da shi akan mutuwar matanka, shi ne yake sanar da ni wai yawanci idan ana samun irin haka kuma har mun yi bincike babu wani information da muka samu to shairin iska ne , ya ce yawanci Al'jana ce ke aurar mutum haka ke faruwa, daga ya yi aure ta kashe matar , dan kamar yadda ya sanar da ni yarinyar abokinshi haka ta faru da ita , itama duk wanda ya aureta washegari za a farka a ga gawarshi, intakaice muku zance yanzu haka ya kaini har wajan shehin malamin da ya yi ma 'yarinyar addu'a yanzu haka ta yi aure har ta haifafa ma , tom sai dai malamin ya mutu amma akwai yaronshi babba wanda shi ya gadai , dan baka ga mutanan da ke zuwa wajan shi d'aukar karatu ba, Muhammad , yanzu haka a maganar da nake maka an sauke al'qur'ani har so uku , kuma gashi nan an rubuce shi ya ce a baka kasha , sannan duk gidan da zaka zauna a tabbatar an sauke al'qur'ani a gidan . Kai in tak'aice muku gaba d'aya yanzu haka shi wannan abokin nawa da nace muku ya kaini inda aka yi addu'ar nan yanzu haka ya ba Muhammad auran 'yarsa Kadija, dan haka duk lokacin da ka samu lokaci cikin Week din nan ka je ka ganta "

Muhammad da gaba d'aya yanzu babu maganar aure a gabansa sai be ji dad'in hakan ba , amma sai ya boye ma nahaifinsa ya ce " Daddy, duk da zuciyata har yanzu cikin fargabar abun da ya faru nake ba zan k'i na'am da duk abin da kuka yanke akaina ba , a koda yaushe uwarninku kawai nake jira , dan haka ba sai na ganta ba na aminta " Muhammad ya fad'i haka dan faranta ran mahaifinshi kamar yadda yaga shi ma akoda yaushe yana k'okarin ganin nashi farin cikin .

Alhaji Sagir kallan Hajiya Baturiya ya yi ya ce " Mommyn Muhammad , biki ce komai ba?" Hajiya Baturiya murmushi ta yi ta ce " Indai Muhammad ya amince nima a shirye nake da amsa tayin " Alhaji Sagir murmushi ya yi ya ce " Tom , alhamdulillah , yanzu zan samu mahaifin yarinyar mu tsaida magana inda ka yi na'am. Saidai kamar yadda nace maka ka shirya ka je ku ga juna , dan muna son yi abun cikin lokaci "

Bayan kwana biyu da maganar Muhammad ya shirya inda Jibirin d'an'uwansa ya yi masa rakiya suka je suka ga Kadija . Kadija ba wani yi ma Muhammad ta yi ba amma kasancewar ita d'in zab'in mahaifinshi ce sai ya hak'ura .

B'angaran Kadija ko take ta amince saboda Muhammad babu macan da zata gan shi ta k'i shi ,dan ya ji komai kota ina mutum ne .

Haka babu b'ata lokaci aka fara shirye-shiryen biki.

Ana gobe biki Malamin nan da aka had'a Alhaji Sagir da shi suka kwana karatun al'qur'ani a gidan da za a kai Kadija shi da d'alibanshi.

Washegari aka d'aura auran Muhammad da kadija.

Usman da sauran abokan Muhammad su suka kai amarya da k'awayanta har gidanta , wanda ya kasan ce shima sabo ne .

Bayan an akai amarya ba jimawa Muhammad bai tafi ba , Usman jin Muhammad shiru-shiru bai zo ba Alhaji Sagir ya Kira ya sanar da shi suna can suna jiran Muhammad ya zo kafin su wuce.

Alhaji Sagir d'akin Muhammad ya shiga zaune ya iske Muhammad da photon Hafsat yana kallo yana kuka. Alhaji Sagir fusge photon ya yi ya ce " Muhammad har yanzu ka kasa yadda wanda yafi ka son Hafsat ne ya d'auke abarshi , idan har ba kana son samun damuwa bane ko kasa ma kanka ka tashi ga su Usman can suna jiranka sai ka je su tafi " Muhammad goge hawan idonshi ya yi ya ce " Daddy, bana d'akko photon Hafsat ba dan in sa ma kaina damuwa na yi haka ne dan innuna ma Hafsat har yanzu tana raina ban manta da ita ba kuma ba zan tab'a mantawa da ita ba har ranar da numfashina zai bar gangar jikina " Alhaji Sagir goge hawayan Muhammad ya yi ya ce " Addu'a zaka yawaita yi mata ta haka ne kawai yanzu zaka nuna soyayyarka a gareta , jeka su Usman na jiranka "

KADUNA GARIN GWAMNA

Fadila tun safe ba ita ta farka ba sai a azahar

Fadila kwance ta ganta kan katifar d'akinta, jin jikinta take yi ya yi sanyi sosai kamar dai irin wanda ya tashi jinya .
Shiru ta yi tana tunani take duk abin da ya faru da ita ya dawo mata na zuwan MD gidan da kuma hollondia yoghurt d'in da ya bata ta sha daga nan ganinta ya d'aushe, shi ne fa bata sake sanin abun da take ba sai yanzu da ta farka ta ganka kwance.

Fadila da sauri ta tashi tana bin sassan jikinta da kallo, tashi ta yi da sauri tana duba kanta saidai ita bata ga wata alama ba a jikinta wanda zata shaida ko MD ya kusanceta , saidai tana jin gaba d'aya jikinta babu dad'i. Da sauri Fadila ta kai duba ga Ahmad amma bata gan shi ba.

Fadila tashi ta yi da sauri ta nufi falon nan ma babu Ahmad. D'akunan ta fara diddubawa nan ma babu shi . Ji ta yi hankalinta ya tashi sosai dan take jikinta ya fara rawa .

Fadila Kiran MD ta yi a waya sai jin wayarshi ta yi a kashe. Take ta rud'e hankalinta ya tashi , dan tunaninta ya bata MD ya bata abun da zai b'atar mata da hankali ne dan ya gudu mata da Ahmad , hakan ya sa Fadila jikinta na rawa ta d'auki hijab d'inta ta fit.✍🏻

Ku bar gaggawa za ku fahimta, ku dai ku biyoni a hankali , ku bar sani ina gudu kar in ji ciwo mana 😰

📚 FADEELAH 📚
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

Na
Fadila Sani Bakori.

SANARWA : Masu tambaya akan gyaran jiki akwai hanyoyi kala daban- daban da zan kawo na gyaran jiki acin wannan littafi mai suna FADEELAH .

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.