So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: SO DA ALƘAWARI.txt
Chapter 25 of 30
Da ire iren wannan Baba ya samu hankalin ɗan uwanshi ya kwanta koda suka fito innah da ƙyar taiwa Abbah sallama muryarta a shaƙe ranar anci sa'a domin a motar Abba suka fita Abba ya aje baba a kasuwa shi ma ya wuce tasa.
Iyaye mazan sun toshe kunnuwan su daga cece kucen matansu domin ita ma innah ta riƙe wuta sosai akan lamarin musamman da Anty nafi ƙanwarta ke ƙara rura mata wutar ƙin auren sai dai Baba da yake yafi ƙarfin gidan shi tara ƴaƴanshi yayi kaf yace bai lamunta wani ya ƙara sukar auren ba da wannan aka samu sauƙi.
Shiko Abba komai na shawarar biki baya tinkarar momi Iyah yake faÉ—awa hatta kayan lefen ma ya É—ebe su ya kai gidan iyah sabida haka koda biki yayi saura kwanaki bakwai iya ta sayi goron rabo ta saka Mariya ta kakkai gidan danginta sabida ganin take taken matan yasa Baba yace wa Abba ya tsaida ranar biki domin ko Saadik É—in ma baba bai faÉ—awa ba, sai da Bikin yayi saura kwanaki bakwai.
Baba ya kira saadik ɗin ya shaida masa duk yadda saadik yaso baba ya ɗaga masa ƙafa amman baba yaƙi yace ko bukka ce ya saka matar shi.
Da damuwa saadik ke shaidawa Innah wadda sam baba bai shawara da ita ba, cewa tai kada ya ɗaga hankalin shi abin da Allah ya hore mishi yayi ita kam ba taro zatai ba tinda abin yazo a ƙure iya ƴan uwanta kaɗai zata faɗawa.
Gaba ɗaya saadik ya shiga busy gidan daya kama suka shiga gyara shida su Nura ƙanin Nura yayi paint a gidan wanda Falo ne guda ɗaya sai ɗaki aciki sai banɗaki da Kitchen duk a falon.
Ɗan ƙarami ne gidan irin na zaman mutum ɗaya.
Bai sami nutsuwa ba sai ana saura kwana biyu daurin aure su Nura ne suka bugo katin É—aurin aure suka shiga rabo Babawo yayi musu É—inki shaddar É—aurin aure duk su huÉ—un.
Ana gobe ɗaurin aure Iya ta saka Abbas ya kaita gidan Momi wadda ta saki jikinta sam batai zaton da bikin bama sabida Abbah baya bibiyar ta akan lamarin shiyasa ta saki jiki akan aikin malam yaci maganar aure ta mutu zasu yi son ransu ita da lubna shiyasa suke ta ƙulla yanda za'ai Mahir ya turo manyan shi.
Ƙaramin hauka momi ta shiga yi sanda iya ke sanar da ita tazo tafiya da Rabi'ane sabida gobe za'a daura aure a wuce da ita gidanta.
Momi kuka Adaah kuka sai da Abba yayi jan ido sannan Adaah tabi iya domin ko kayanta ma bata haÉ—a ba, Abba yace a kai mata su daga baya.
Komai na momi ya tsaya cak sai faman zage zage take kuma tace ba zata taka ƙafarta gidan bikin ba Hajiya lubna tafi momi shiga tashin hankali data ji maganar amman data tina zagon ƙasan datai sai taji bata damu da auren ba tasan dole adaah zata fito ɗanta ya aure ta, domin ba burin ta auren adaah ba burinta dukiya.SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma 9022260850 Opay bank, Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
    Â
     *NA*
*AUTAR MANYA*
           *13*
Da tsananin ɓacin rai yake shiga cikin gidan nasu, yadda ya tarar da mutane a tsakar gidan nasu suna ta ɗaga kayan cikin akwatinan abin ya bashi mamaki ba kaɗan ba.
Ya tokare a bakin rijiya tare da zuba hannayen shi a saman ƙirjin shi sabida yadda ranshi ke ɓace baya tinanin ma na tsakar gidan sun ji sallamar da yayi.
Innah ce ta farga da tsaiwar ta shi ta taso ta iso inda yake tana cewa.
"Sadauki! lafiya na ganka a tsaye ka ƙaraso mana, Allah ya sa ƴan uwan naka basu tafi ba dama kai suke jira"
Ya É—ago tare da zuba mata jajayen idanunshi murya a raunane yace.
"Yanzu innah sai da kuka aika azo aga lefen nan fisabilillahi mai iyayen jiddah zasu É—auke ni?"
Sai ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana cije bakin shi, sauran maganar ta tokare a maƙoshin sa.
Innah ta zuba mai ido tana ƙara jinjina son da yake wa jiddah tinda har yana gudun ɓacin ranta da kuma na iyayen ta.
"To sadauki ya za'ayi da ƙaddarar Allah tinda Ubangiji ya ƙadarta ba Jiddah bace matarka a farko ba, yaya zamuyi gaba ɗaya haƙuri zamu yi tare da addu'ar alheri acikin lamarin"
Jinjina kanshi yayi tare da cewa.
"Tin da kika ce Allah magana ta ƙare"
Bai iya faɗa mata maganar da maƙocin nasu ya tare shi da ita ba sabida masifar zurfin ciki.
Ya na ƙoƙarin juyawa ya koma ɗakin shi su Ya minau suka ƙaraso wajan da shirin tafiya gida faridah sai tsokanar shi take yayi mata banza ya wuce ya barsu a wajan.
Innah tai murmushi tana kallon Aunty Hajjo tare da cewa.
"Yanzu goben ƙarfe nawa za a kai kayan? sai na kira Nafi kuje da ita amman ban da abinku da kun bari maza sun kai yanzu yaushe rabon da ku ga mata sun kai lefe?"
Da sauri faridah tace.
"Ban da abin Innah mazan su waye zasu kai? abu duk É—aya Mu dai ki bari Muje mukai"
Ba yadda Innah ta iya ta amsa musu kamar yadda suka buƙata Ya Minau ce tace.
"Innah ni naga Saadik na haÉ—e rai wai meke faruwa ne?"
Innah cikin basarwa tace.
"Ke rabu da shi ya ƙarata da Ƙuncin sa"
Har soro innah ta raka iyalan nata tana musu addu'ar fatan gamawa da duniya Lafiya suka fita titi ko wacce ta hau motar gida.
Ba jimawa da fitar tasu Baba shima ya shigo gida lokacin mutanen dake ganin kayan lefen duk sun tafi sai su Khadija dake tattare tsakar gidan.
Baba ya zauna a saman tabarma a rumfa Hasken farin ƙwan tsakar gida ya hasko har cikin rumfar da yake zaune yabi akwatinan da kallo Fuskar shi dauke da maɗaukakin farin cikin haɗin zumuntar da zasuyi da ɗan uwan shi ya dubi Innah dake haɗa masa abinci yace.
"Haƙiƙa Hafsatu naji daɗin wannan aure ina fatan Ubangiji yasa sai mutuwa ce zata raba su, tabbas Amadu ya wanke duk wani laifi da ya min abaya domin duk duniya ba wanda zai iya riƙe Ƴar amadu kamar Sadauki kinga munyi tuwo na mai na"
Ya faɗa yana sakin ƙayataccen Murmushi, Itama Innah Murmushi tayi tana cewa.
"Allah dai yasa ayi lafiya a gama lafiya niko burina na goya ƴaƴan ɗan auta tin da ƙwarina Kuma Allah ya cika min, sai batun kai Lefe kunyi magana da shi Amadun ne? waɗan nan yara fa sun kafe sun ce sai sune zasu miƙa kayan"
Baba ya É—aga kofin da innah ta cika mai shi da ruwan sanyin randa mai daÉ—i yace.
"Munyi waya ɗazu yace min Gobe da safe zai sauka kano Wajan yamma sai su miƙa abu duk na gida nida ma niyata ma a bata kayanta ranar ɗaurin aure, to tinda sunce zasu kai kar a katse su duk cikin murna ne"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.