Tsofaffin Hausa Novels

So Da Alkawari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: SO DA ALƘAWARI.txt

Chapter 13 of 30

Murmushi yayi.
"Kai Yaya nifa bashin ne bana so"
Ta kalle shi.
"Auta na baka kyauta tunda baka son bashi"
Da sauri yace.
"Wallahi ba zan amshi kuÉ—in kuba kowa yana fama da kanshi da É—anshi akan me"

"Saadik kenan ni na rasa irin zuciyarka Ubangiji ya sa kafi haka duk hidimar da kake mana kace kai taka tazo ba zamu taimaka maka ba, Bani manta Bikin jawahir kaifa kai mana kayan kitchen sannan Abbansu kasuwar bata garawa don Allah ka amshi kuÉ—in nan Saadik nasan rayuwar ana fama amman Allah zai warware"

Cikin son kauda maganar yace.
"Ki bani account ɗin sauri nake yi in yaso sai ki ma Yaya Hajjo waya ku tattauna nidai bana son ƙananun atamfofi gwara ko ba yawa a sayi masu aminci"

Duk yadda taso su sasanta ya amshi bashin kayan kona kuɗin yaƙi Sabida acewarsa kowa yana fama da kanshi ba zaka ɗora mai wahala ba.
Ya amshi Account Number ɗin nata ya saka mata Kuɗin da suka rage mai yayi mata sallama ya tafi gida duk da taso ya tsaya yaci abinci tinda an kusa gamawa amman fafur yaƙi tsayawa.

A bakin titi ya sauka ya shiga shagon mai fura da nono ya siyawa innah sanin tana son surki sannan ya saiwa Zarah alewa ya nufi lungun su.

Bai iya ɗakin shi dake soro ba sai da ya ƙarasa cikin gida ya sami su innah suna ƙoƙarin ɗaura alwalar sallar magariba da ake ƙoƙarin kira.
Ya miƙawa zarah alewarta wadda tazo ta ɗane shi yana kallon innah wadda ta zabga mai harara.
"Wai innah nikam mai nayi daga zuwana ga furarki na sayo"

Sai da ta É—aura alwalarta sannan tace.
"Ka kyauta ka bar Æ´ar mutane cikin wani hali kai tafiyarka"
Ya wani zaro ido waje.
"Inna itan ce tace nai mata wani abun nifa kawai biyoni tayi da kuka shiyasa na bar mata wurin"

"Oho ca nake kasan sanda ta faɗin, yanzu kayi sallah sai ka leƙa gidan nasu kaji yadda take nima danai sallar zan shiga"

Ya miƙa mata ledar furar tare da amsa mata da cewa.
"To"
Yana juyawa ya nufi ɗakin shi da fitilar ƙaramar wayarshi yayi amfani wajan haska banɗaki yayi uzirin gabanshi tare da ɗaura alwala, ya fita masallaci.

Bayan ya idar da sallar magariba, ya dawo É—aki yayi wanka Nura saiti ya kira a waya yana tambayar shi akan koya dawo Nurah yace mishi yana bakin titi yanzu zai shigo lungun da sauri yace masa inya shigo É—in ya biyo don Allah zai rakashi Gidansu Jiddah.

Zama yayi yana jiran Nuran bayan ya katse wayar jim kaÉ—an nurah ya shigo tashi kawai yayi suka fita.

A ƙofar gidan su Jiddah suka dakata yana tunanin ta yadda zai sami yaron da zai musu iso zuwa gidan dan shi yana jin nauyin kiran Umma a waya yace yazo.

Ana haka Fa'izu yayanta ya ƙaraso ƙofar gidan yana ƙoƙarin kashe babur ɗinsa ya ga su Saadik waɗanda suka ƙarasa gaban shi suna miƙa mai hannu.

Cikin mutuntawa suka gaisa yace.
"Kuma kunzo basa gidan kenan? nima sai da na zo bakin layin ummah ke faÉ—a min, suna asibiti Jikin Jidda babu daÉ—i"
Da sauri Saadik ya kalli fa'izun gabanshi ya faÉ—i tofa abin yayi zafi kenan harya kai da zuwa asibiti.
Cikin sanyi yace.
"Okay wane asibitin kenan bari mu ƙarasa"

Fa'izu yace.
"Nan asibitin Charity na bakin titi  ko wani acikin ku zai hau bayan babur ɗin muje tare?"
Saadik ya kalli nurah wanda shima ya kalli saadik É—in kafin Nuran yace.
"A,a bari mu tafi bibbiyun tafi daÉ—i"
Fa'izu yaja babur É—in nashi ya tafi su kuma su nufi bakin titi.

Gaba É—aya Saadik ji yayi garin yayi masa zafi fargaba ta cika zuciyarsa sai dai da yake akwai shi da dauriya yasa fargaban bata fito fili ba.

Duk Hirar da Saiti ke yi masa kawai jinsa yake a haka suka ƙarasa titi suka sami napep tafiyar kaɗan ce ta kaisu asibitin wanda yake ɗan ƙarami ne na kuɗi.
Suka sauka tare da bawa mai É—an sahun kuÉ—in shi, suka shiga cikin asibitin.
Suna shiga shima fa'izu na ƙarasowa sabida haka a tare suka ƙarasa cikin ƙaramin ɗakin da aka kwantar da jiddan bakin su dauke da sallama.

SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah.
[12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

                     *007*

Kwantaccen murmushi ya saki yana shafa saman kanshi da hannun shi guda ɗaya, haka nan ya ƙarasa gefen data mayar da kanta ya zuba mata ido tamkar ranar ya fara ganinta, Har Lokacin murmushin kuma bai gushe daga saman fuskar shiba.
Turo baki tayi gaba tana ƙoƙarin sake juya masa baya yayi saurin jan gefen Hijabin ta ya wani marairaice kamar wanda yake roƙar ta gafara tare da cewa.
"Haba Æ´ar aljannah, ban sanki da fushi ba haba Hauwa'na mai jiddana"
Yadda yayi maganar ba ƙaramar dariya ya bata ba, Seta sa hannu ta rufe baki tana dariya ƙasa ƙasa, ya wani gyara tsaiwa ya ɗan tsira mata ido kaɗan sannan ya kauda idon nashi.
"Yanzu dai ki wuce muje cikin gida Innah tace bakya zuwa kwana biyu sabida kin zama surukarta tace ko kin ganta guduwa kike yi"
Zaro ido tayi kaÉ—an cikin sanyin halinta tace.
"Wallahi ina zuwa kawai kwana biyun nan ne, Bana zama kaima ai kasani sauka ta sakoni gaba sai munyi zan sami sukunin zama"
Yadda tai maganar ya kwaikwaiya sai ta kawo masa dukan wasa tana shura ƙafafunta da gudu yayi soron gidansu ta bi bayan shi da wayo ya jata har Rumfar Innah wadda duk suna zazzaune an kunna Fitila mai farin ƙwai sabida babu nepa.

Su kansu su Ummi zuba masa ido sukai ganin yadda ya faÉ—o Rumfar yana dariya wadda tai mugun yi masa kyau don shi ba ma'abocin yin ta bane.

Inna ce tace.
"Lafiyar ka kaikam ka faÉ—o min É—aki kana faman dariya"
Muryar shi ce ta katse maganar Innah inda yake wa Jiddah magana yana waigowa wajan innah.
"Ki shigo mana kin wani raɓe to wai gidan baƙon kine?"

Sai lokacin Innah ta fahimci silar dariyar tashi wato tare da Jiddah suke.
Sai ta kada baki cike da Murnar Ganin Jiddan tace mata.
"Maza shigo Hauwa'u ni na rasa kwana biyu kunyar da kike ji tawa Ko a waje bana ganin ki ko wajan ƙawar taki bakya shigowa duk sabida Sadauki?"
Duk su Ummi dariya suka saka Banda Saadik daya É—aure fuska aiko ba shiri su Ummi suka kama kansu kowacce ta yi É—aki sim sim gudun Karsu jawa kansu masga.

Da sanyin ta tashigo ciki ta raɓe a gefe shiko ba kunya ya matsa wajanta Jug ɗin dake hannunta ya karɓa.
Yana ƙwalawa Khadija kira da sauri tazo gaban shi.
"Kawu gani?"
Umarni ya bata akan taje Kitchen ta ɗauko masa Kofi ƙarami ba jimawa ta kawo masa ya fara tsiyaya Kunun ayar aciki ya ɗagawa ya kurɓa ya wani Lumshe ido yana Murmushi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.