Complete Hausa Novels

√Shade Of Rufaida Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: √SHADE OF RUFAIDA book 1.txt

Chapter 46 of 50

Part1:chapter 46

Wajajen shida saura na yamma zarah ta farka a wahalallen baccin dayayi awon gaba da ita jitayi duk jikinta baya mata dadi,ga wani irin axaban tsamin da gabobin jikintan ta suke mata ta ciki ciki tanajin wani irin gajiya har cikin kasusuwan bayanta da cinyoyinta, bata iya yin komi ba wankan kawai ta sake fadawa ta dade a bathrum tana gasa jikinta cikin ruwan zafi wanda hatta wata nai jegon ma bata samu irinshi ajikinta ba..

rurin wayarta dayaki ci yaki karewa daga daki shi ya dameta wanda yasata fitowar dole daga bathrum din daure da karamin towel a kirjinta,gaban mirror tawuce direct ta dau wayar tahau dubawa as expected miscal din master kawai tacikaro dashi kwafa tayi dan tasan bazai wuce akan maganan su ba kiransa itama tahau yi ba a daga ba saita hakura.

Wani tafkeken ajiyar xuciya ne ya kwace mata cikin sanyin jiki batako yi yunkurin nemo man shafawar bama ta nemi waje agefen gado ta zauna ta kuma rabza uban tagumi acikin tsananin nisan tunani ta jefa kanta wani ajiyan zuciyar ta sauke sannan hummmmm kanaji kasan tayi nitso mai zurfi haka kawai ta soma sumbatu ita kadai tana cewa"Shegiya duniya, garin nemanki dole ne asha baqar azaba,Yo Mezai hanna in akasameki ayi yadda akaga dama dake..?gani take in Allah ya bata duniya kamar irin na Ainau toh wallhy sai dai ayi kallo dan ita kanta batasan kalar tsiya da tijarar da zata shinfida a doron qasa ba.

bataba kanta ansar tambyar ba ta miqe tsaye,kan screen din wayarta ta kalla a hnkli,snn taja wani kasalliyar tsaki wai mutumin da kake hauka akansa kenan shiru bai nemeka Ba?tsaki ta kumaja tuna yau ko nemanta ma imad baiyi ba bayn ko jiya cikin dare ma saida ta kirashi amma ya kashe mata waya.

Maida wayar gefe tayi kamar zata ajiye sai caraf ta kuma daukar waya tayi scrolling cikin contact cikin sauri har tazo dede kan number imad datayi serving da LOML. dialing ta shigayi kamar zaiyi ringing sai kuma ta katse cikin sauri ta aje wayar acan gefe,
Ajiyar zuciya ta sauke cikin tunani tace wakanta yau bazata ma fita ba dan bataso taje ta same imad adaidai lokacin da master zai iya kiranta agabansa cos she dont eva want to look suspicious gaban sa.

Bayan nan ta miqe tsaye ta isa gaban madubi mai kawai tashafa ta dan kikmtsa kanta xuwa shigar bacci dama can bata damu dayin wani ibada ba bokayen zee da suke bi kaf sun hanata yin sallah da azumi.

An riga an dasa mata aranta cewa yin ibada shi yake kara mata baqin jini da rashin sa'a a rayuwa kuma ta amince da hakan kwarai da gaske dan haka tana kammala kwaliyyarta tayi keys ma kofar dakinta batayi wata wata ba ta fada kan gadonta ta kwanta tayi lumui da wayarta a hannu dantasan dole ne master ya kira

Sai can around 12 kirar master ya shigo ta farka a gigice sukahau durama juna ashar
nan take tagaya masa cewa ita sai gobe zata iya zuwan masa,tamasa alkwari da sassafe
Abu daya yafada yasata yin murna sosai, da yace ya riga ya kada zee a abuja harta kwashe kayanta kaf ta koma Kano jiya cikin dare.
Tun da suka katse wayar take cikin jin dadi tabbas tasan yau da master bai bata hadin kai ba toh wallhy da tuni kashinsu ya bushe ba ita kadai ba harda Ainau dan babu abunda zai hana zee tayi watsi da sirrukansu waje,dan abu mai mugun saukine awajen xee musammn in ta debo kwaya har gidan nan zata iya zuwa ta tona musu asirinsu tas tass.

Yau Wani irin shiru gidan ya dauka da alamun kowa nata can sashen sa dan bakajin motsin kowa a sararin gidan kafafu ma duk sun dauke

Yau kwata kwata imad bai dawo gidan ba yana kammala tsabgar gabansa ya wuce wajen yaa sheik a cikin federal court Abuja

yawancin ayyukan documentation dinsa ne da sukaso su sha musu kai yasa basu samu sun kammala komi akan lokaci ba

mufrad ne kawai acikin gidan amma bazaka taba sanin hakan ba dan tun shigowar sa ya nufi dakinsa ya zauna akan couch dinsa yahau yar danne dannen sa a laptop as usual feeling so helpless and lonely sabida wani irin mugun shiru da koina ya dauka

Yau ko sanin inda matarsa Ainau take baiyi ba dan tun safe ta wuce office itama bata dawo ba,duk dama ya riga da yasaba da irin wannan rayuwar but he was nearly choke up today sabida baida wani aikinyi sosai agabansa da zaina dauke masa hankli,haka kawai saiya soma jin wani irin mutuwar jiki da kasala,yana jin haushin rashin tafiyarsan nan da baiyi ba dama kuma can tafiyar ne ke dan debe masa kewa da kaucar masa da tunani masu nauyi da kassara zuciya wanda ya tsane yinsu arayuwarsa wanda aganinsa babu amfanin ma yinsu tunda baiga alaman da akwai wani mafita ma rayuwar sa ba

...tun arond four oclk ya gama komi nashai ya zauna shiru shikadai a mugun takure dan baisan mema zaiyi ba,gashi inba aikin sa ko wani meeting ba shi bai iya zuwa koina arayuwansa ba, he is a chronic home addict,zan iya cewa arayuwar sa shi bai taba daukar kansa da kansa zuwa wani club ko wajen games ko wani wajje na shakatawar rayuwa ba,he neva care for that,tunanin hakan ma baiya yawan zuwa masa a duniyar sa sumtimes koyay tunanin zuwa ma ma baifi a kirga ba

Tashi zaune yy ya zauna da fillo rungume a kirjinsa kenan haka zaita zaman kadaici yau agidan?ders is No one to keep him company infact babu mai lekowa ta sashin ya dubasa bare aje ga kawo masa wani abun tabawa abaki shikansa yasan kowa ma shakkarsa yakeji,inbawai shine dakanshi zai kira a waya yace akawo masa abu to bamai lekowa nan har abada,abun haushi ma yake basa aransa cos baiga dalilin dan iskar tsoron sa da kowa yakeji ba.
Hours passs by
Yau a dakinshin kawai ya wuni trout bai leka koina ba banda sallah dayake saukowa yaje masallaci yayi,
Can dare Yana idar da sallahn ishai ya shigo gidan again ya rasa abunyi kuma yasan ba bacci zaiyi nan kusa ba,ba ama maganan zuwa wajen matarsa Aina'u yasan yadda yakejin ba dadin nan aransa hala inyaje ma bazasu kare ta dadiba.

Adakinsa ya shimfida sallaya ya hau sauke wasu dogayen nafilfilu raka'a sha biyu kamilallu yayi acikin kowani raka'a saiya karanta full surah mai tsayi daga farko har karshe cikin kyakywar nitsuwa,bayan nan zama yay kawai akan sallayarsa yahau bitar karatun qur'ani tun daga suratl nass danya dade baiyi karatun qur'ani mai tsaho da dadi kamar nayau ba,gaba daya shauqin karatun ta maimaiye fuskar sa da gangan jikin sa,shikadai ma kawai saikaga yana dan murmushi, sosai idanun sa suka cikke da ruwan hawaye saika rasa meke guduna acikin zuciyarsa,yau tun beyi wani nisa ba yahau jin fayau acikin zuciyarsa duk wani nauyin dayakeji aransa dayake saka masa yawan tunani da fushi sai yaji yadan ragu masa sosai

..,bayan ya kammala karatun zama yay yana studyng tafser din wasu ayoyi daga cikin suratul ali imran kamar yadda da can mahaifinsu ya dorasu akai.
Bayan ya gama hakan a nitse sosai ya maida qur'anin ya ajeshi a gefen gadonsa sannan ya zauna yana mai daga hannunsa duka biyu sama
addu'oi yahau yi kala kala yaname neman gafara akan tulin lokacin dayake daukawa awani wajen wanda yasan su suke datse masa saka himma akan harkokin addinin sa dana rayuwar sa,yay addua ma iyayensa da shikansa yaname rokon Allah daya basa y'ay'a na gari dan Harga Allah acikin ransa yana mutuwar son haihuwa abun na cikin ransa fiye da yadda ake tsammani,yana kammala adduar ya mike tsaye daga nan ya fada bathrum ya sakar makansa warm shower yay wanka
Within 20 mints ya dawo ya shirya kansa bai wani dade ba bacci yay awon gaba dashi.

Sassafe bayan ya dawo daga masjid bai wuce dakinsa ba ya nufi dakin Aina'u straight ya hau kwankwasa mata kofa amma sai shiru komawa cikin gidan yay ya gaida manyan gidan gani yay kusan kowa ya farka ana zazzaune a babban sitting rooms ana dan hira masu yin ibada har an gaggama ana shan coffe besides kusan al'adar gidan ne in har yaa sheik yana nan tofa tun asuba waje zaiyi lively da karance karancen littafai musamman na addini,ganin imad ne kawai ya dauke musu hankli anan yasa shi barin wajen ya koma sama direct dakin tan ya kara nufa yana buga kofar yana lura da agogonsa dake nuna 7:00am.
Kwata kwata baison yau ransa ya baci amma saiyaga kamar duk sanda yy kkrin danne fushin sa dmin yin hakqri to sai annemi a tunzura shi

Murda kofar yay da qarfi ji yay haryanzu a kulle yake da alama ma bata farka ba,kuma yasa muddin bata farka ba dawuyane inma ta farka tayi sallahn fajr,what d hell is this ya fadacikin jan tsaki,bai kara buga mata kofar ba ya bar wajen a kufule dakin sa kawai ya nufa yahau yin abubuwan da suke gabansa batare da yakarayin tunanin ta ba.

7.10am dot ainau ta farka daga bacci ta zauna turus akan gadon ta tana wani irin hamman gajiya dan jiya bakaramin gajiya tayi awajen aiki ba ko ayanzu bata ki ace mata ta koma bacci ba dan tamkar wacce tayi dambe a baccin haka bacin rai ya nuna boro boro ayanayinta ko salati bata yi ba ta sauko kasa ta rinka sheka tsaki ita kadai tana ball da duk abunda ya zo gabanta.

As usual Wanka ta fada within 10 min ta fito ta zauna agaban madubi dan yau by 9 takeso ta wuce office sanda ta gama kwalliyarta tsaf ta kyafu kafin ta tuno da cewa batayi sallah ba

Dogon hijabin data saba amfani dashi in zatayi sallahn ta bude wardrobe ta jawo ta kwama within 2mint ta idar without knowing what she did sabida tun farawarta take tunanin abubuwa dayawa aranta ciki harda kanwarta zarah dan jiya aiki ya sha mata kai basu hadu ba.

Sharp sharp ta kimtsa kanta cikin wata dan ubansun holland atamfa, red nd white colour mai bala'in tsada an mata dikin riga da skirt fitted wanda ya balain yin mata kyau ya haska tsayayyen dirinta,kwalliyar ma yau batayi wani na hauka ba,yau yaa sheik yana nan so zata iya yafa babban mayafi.

Ahaka ta futo tana takunta kwaras kwaras direct ta
Wuce dakin zarah ta turo kofar jin abude yasata shigo da kwanciyar hankli saidai abunda ta hango zarahn tanayi ne yaso ya katse mata hanzarinta.

Cikin sauri ta karaso ciki tana cewa"Mimi How far
Jiya da baki ganni agidan nan ba shine bazaki nemi ni ko awaya ba.

Da Wani irin munafikin Murmushin mugunta zarah ta juyo ayayin da ta dago kanta daga kan akwatin data gama cikawa da kayanta,tace hmm sis kenan kema kinsan in haukar aikin kin nan yana gabanki bana cika son takuraki

Zama ainau tayi idanunta da hanklinta gaba daya nakan kayayyakin zarah,sai dai aranta wani jin nauyin tambayar zarahn takeyi sabida tsabar girman kai dake damun zuciyarta.

Murmushi zarah tayi tace,yanzu kuwa nake shirin nemanki tun kan zarah ta karasa magana ainau tace yess yes meke faruwa zarah Tace hmmm babu sann ta riko hannun A'inau tana kallon ta cikin ido da ido"Sis im leaving.I have to leave right now,A Tsaye Ainau ta mike..tace mene? ina zakije akanme
To where nd why?
Mikewa zarah tayi Ainau ta hade rai ta mugun dakatar da ita da ido,tace
Ehm ehm zarah bana son wani case da safen nan,are u aware dat father inlaw na ya dawo ko?if u leave like this thy will definately ask questions.

Zarah tana murmushi tajawo hannunta ta zaunar da ita"..tace i know calm down ki saurareni nima bada son raina nace hakan ba,wani doguwar ajiyan zucya ta sauke dan already dama ta riga ta harhada maganganun da zata fada a zuciyarta zaunawa tayi ta soma fiddo su waje sosai ta tsara Ainau da cewar zamanta tare da su bazaiyu ba sabida tayi nazari da kasancewar zee a garin zai iya jawo musu mummunan matsala dukansu
Within no time ta hahhada karerayi ta tsara a'inau sosai ta kuma tsorata ta game da lamarin shedancin zee wanda ita kanta tasan ainau ta tsani harkoki da zee aganinta duk sanda aka gansu da zee hala shikenan kuma.

Gaskiya daya kawai ta fadawa ainau na maganan volunter out reach da zatayi,
Tacewa ainau duk wannan shirinta ne danta kore zee zee
Shiyasa ma bazata bar abuja ba,duk wayon ainau yau saida makircin zahara ya wuce mata yadda zatama yi tunanin komi.thy talk down with ain a daki sosai kafin nan zarah ta shirya tsaf cikin doguwar riga suka sauko atare hanunsu dauke da jakka da akwatina riki riki hakan ya jawo difernt sort of reactions inda kowa ya xuba musu ido a
A falon da sukayi sallama suka shigo

Gaban manyan gidan suka nufa direct suka rusuna har kasa mammane da junansu suna sadda kai kamar muminan kwarai,a ladabce sosai suka hau gaishe da kowa

imad ne sanye cikin suturarsa ta wata dakakkiyar brown colour shadda mai kyalli data mugun amshar shi tamasa kyau sosai,shima gaba daya ya maida hanklinsa kansu cikin nazari cos he tot wani abu ne ya faru irina wancan karon da ainau ta nemi guduwa bada sannin muff ba hka kawai saiyaji hanklinsa bai wani kwanta ba.

Qamshin turarukan jiki da girki kala kala na abinci d'adada su suka cike iskar wajen daga ganin yanayin su kasan zuwan su kenan kan dinning din hjy jasmine ce a tsaye ta sha purpl colour bubu gown kanta zagaye da wani hadadden silver veil tana ta kkrin dudduba abubuwan karyawa da aka jero!tun bayan amsa gaisuwa hajya adada bata kara maida hnklinta kansu ba tana aikin latsa wayarta,kallo daya hjy goggo ta musu snn ta mugun hade rainta dan harga Allah bawani son tarin jama'a takeyi ba musamman in yaa sheik yana kusa.

Ana zamnawa zarah tahau yin musu bayanin cewa ita zata wuce aiki,akan motar da zai kaisu kauyen ita kadai yake jira.

Yaa sheik na xaune a kujerar tsakiya baice mata uffan ba,he is unaware of anything dats going on acikin gidan musammn ma da shi ba mutum bane mai saka ido sosai.

sukan su hjya sunta mamakin sudden tafiyar da zarahn zatayi dan basuyi tsanmani da sassafen yau bane hidimar nata

Hjy jasmine ne tahau su da tuhuma tana cewa zarar "..meyasa baki gayamana zaki tafi sassafe ba?but sabida presence din yaa sheik zarah taki yin magana awajen dan gani take kamar zai iya ganesu,A'inau tahau kame kame banda titsiye su babu abunda hjy goggo takeyi da questions kamar wacce ta kama marasa gaskiya,hjy adada batace uffan ba sabida kwata kwata aranta bata kawo wani abu game da tafiyar zarah ba aganinta zarah mace ce mai son temako da tausayi ,mikewa tayi ta wuce daki ta dawo da wasu gifts bags harda cash ta debo tabawa zarah

Yaa sheik da baisan komi game da tafiyarba duk da haka saida ya dan mummusu nasiha sunata godiya

Mufrad da imad suna shiru basucei uffan ba har aka gama sallamar zarah, dakema driver gidan ne zai aje zarahn so Ainu ce kawai tafito har waje domin rakata

Suna ficewa a falon imad ya miqe a sadade yabiyo bayansu,a tsakar gidan ya cimma su zarah taja ta tsaya Ainau tayi saurin barin wajen ta koma ciki..
Kallonta yakeyi closely bcos he is soo inquisitive game da tafiyar da zatayi aransa kamar bai yarda da su ba.

Daga cikin falon kuwa yana barin wajen hjy adada tahau sauke wani makirtaccen murmushi tana qoda zarahr wa hjy jasmine,tana yabon halayenta azaton ta ficewa da imad yy yabi bayansu ko soyayyace ta riga ta kullu.

One time matan gidan suka hau yar zunde zunde ana hirar alakarsu da imad din kasa kasa burin su baifi yaa sheik ya dago kan zancen ba dan kowa ya matsu ayi biki a gidan,badon komi ba sabida hajy adada tanada mugun son nuna bajinta wajen biki musmmn ma ynzu da wani zumunci mai qarfin gaske ya kullu tsakaninta da hjy fulani, mufrad cud not stand it,sosai hirar tasu ya soma qona masa ransa sosai,shidai in za'a bude zuciyarshi baya sha'awar imad ya auri wannan marar kunyar yarinyar..tsanar da yyiwa halayen ainau gaba daya yasa yakejin aransa kamar zarahn ma bazata making good wife ma imad ba

dawowar Ainau kenan daga rakiyar zarah,tun kan ta ja kujera ta zauna mufrad ya mike tsaye suddenly ya droping spoon dinsa ahnkli ya juya bai kula kowa ba ya haura sama abunsa.
11/18/21, 5:50 PM - Buhainat: *™✓SHADE OF RUFAIDAH*

_BY_
_SURAYYAHMS_

_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.