Complete Hausa Novels

√Shade Of Rufaida Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: √SHADE OF RUFAIDA book 1.txt

Chapter 27 of 50

Part1:chapter 29

Malak tana ficewa a falon Shukra ta hau bin bayanta da Wasu muguyen harara daga nan itama tashi tayi ta fice fuu cikin jin haushinta tayi Sama can ta haura dakinta Wanda akayi sa da tulin kayan duniya tsarin sa tsarin Yan gata irin Disney princess din nan yasha ado harta jikin bango tana shiga dakin tayi super ta fado kan faffadan Italian bed dinta dayasha kwalliyar pink bed sheets da trow pillows,kwanciya tayi tana famar juye juye aranta feeling so annoyed and ashame dan kwata kwata Batayi tsammanin zatayi ta zuba farrr kamar ankunna engine agaban malak ba So Wat will dat girl think of her now?...

Ita kanta tasan Tana da zargi da son hada gurmi a zuciyarta game da mutum shiyasa gaba daya takejin kanta a matukar dore ynzu

Ita Gani take batayi daidai ba Cike da takaici ta cije labbanta cikin tunanin kalar fassarar da malak zatayi mata makira Magulmaciya,mai saka Ido ko cheap?Wani tsaki ne ya kufce mata tuna Wani uban Jan aji da shasshareta da malak keyi alokacin da Idonta ya rufe akan gulma tana famar xuba mata labarai babu tsayawa, Sosai ta soma Dan da nasanin tunkarar malak da hirar she tots ko malak zata biye mata ne su hada Kai yau agidan su kuntatawa Zarah but sanin cewa ta kwafsa yasa atake aranta ya cunkushe ta soma jin haushi da tsanarta arnta tana cewa halama Duk layinsu daya da Zarahn, Dan da alamar itama malak din son uncle mad din take,Wani dore fuskanta tayi aranta tana bambami tana cewa wallhy basu isa ba,mikewa zaune tayi tana huci "tabdi jam wallhi dukansu bazasu same uncle mad ba uncle imad yafi karfinsu shiba class dinsu bane wannan nazarin ne ya cigaba da huruwa yana zafafa aranta kusan shine ma ya dauke mata hankli ya dakatar da ita daga saukowa kasa zuwa waje.

Bangaren Aina'u kuwa tunda ta zame daga wajen cin abinci ta haura sama ta shiga dube duben dakin ko zataga muffy amma bata gansa ba,atake taji ranta yay mummunan baci zuciyarta yahau tafarfasa yana mata Kuna Wani irin gajiya da fushi ta soma Ji aranta game dashi

Cike da takaici take ciza yatsanta tana nazari ita kadai da zuciyarta,All this while mufrad yana Nan agarin abuja amma banda yawacen yawacen meeting dinsa acikin abujan Babu abunda yakeyi Kuma haka tayi haqri dashi dakema ta lura kamar dawowar su da Zaran yasa yake jajjan baya da ita a tunaninshi Hala zarahn tafi dauke mata hankli,hakan yasa sai yayi banza da ita baiya ma son kwana agidan and sometimes zaizo din but still acikin sauri zai Kara fita yace mata zaiyi wani abu awani wajen,abun mamaki sai gashi jiyan nan da imad ya dawo wai har yawaiwaye shi, ai tanajin hjy saddika da safe tana cewa ai tare ma suka kwana..

Cikin tsananin takaici take jeka ka dawo a coridor zuciyarta a cunkushe tarasa abunda yake mata dadi can saiga Zarah ta hauro sama cikin tafiyar yanga hannunta Niki Niki da kayan tsarabar su tare da yar fara'a akan fuskarta,Suna hade ido Zarah ta tsaya durus ta dan dakata tace "Sis ya naganki haka whats wrong?dada dore fuska ain tayi tare da sauke karamin Ajiyan zuciya tana kallonta tace Nothing, Muje tacan dakinki muyi magana banason magulmatan gidan Nan su jimu,atare suka juya suka shiga dakin Zarah dake ma Duk a waje daya ne,ko zama basuyi ba zarah ta hau nunnamata kayan tsaraba cikin rawan jiki gaba daya ta rasa nitsuwarta dake Duk designers ne wanda tabbas tasan da kudi mai yawa aka siyesu, bracelet na mandarina duck dats so shiny ta dauka ta makale a hannun ta tana murmushi, ita kuwa Aina'u tagumi ta rafka Dan damuwar ta mijinta ne ayanzu ,ynxu hakama haushin imad din takeji na balbaleta kamar ta kashe shi haka takeji,Wani tunani tayi saita juyo cikin sauri Tace zarah Kin lura da wata karamar yarinya datake wani mammakale ma saurayinki kuwa?cikin Jan aji ta tabe bakinta kamar ba zugi take so tayi ba..tace "Baifa kamata ace kina barinsu waje daya ba fa,wallh kwanan nan saikijii ana zancen laka masa ita ke kinsan munafurcin gdan Nan kuwa? tsaye Zarah ta mike a hujajan kamar an tsokanota tace "Ina yar waccan ficcikar yarinyar Wanda tasaka Wani abaya?tun kan ain ta dago taja Wani dogon tsaki "Mtchww ai nafiki ganin ta..you know wat sis ni bazanfa tsaya sanya ba,im so glad ur family are already pressuring him akan batun auren nan so kawai ya aureni mu huta"....tsaye ain ta miqe tun kan Zarah ta karasa magana ta tsare ta tace toh wat are you planning to do now?u have to act fast,ke wallhy daga yaa sheik ya dawo zamu bar gidan nan mukoma asokoro Kuma kema ai can zakibini tunda kowa yasan dai Waje na kikzo hutu,u have to speed up ur game fast zarah,tun anan kisamu ki ja hanklin sa or Did u think abubuwa zasu tafi miki daidai harya soma kulaki inmuna can su Suna Nan da irin wayannan Yan kusuri tsomen?
hmm jiya jiya yazo Amma har anbiyosa gida da yarinya..thy are just fooling us ingayamiki.

cikin nazari mai kama da rashin hankli Zara tace no way,no way bazai taba yuwa ba,kinga malam fa cewa yay abun nan zaidan ja lokaci kafin ya shigesa I have to get myself more close to him yana kallon cikin Ido na yana shaqar qamshi na,maybe in 2_3weeks sai kiga komi ya kammala Amma ai dolene in San nayi kafin Nan, tana gama Furta Hakan tana sauke Ajiyan zuciya fuuu ta wuce gaban wardrobe ta bude ta fidda Wani sabbin kaya,golden atamfa ce mai kyau da tsada wanda aka baza mata dinkin bubu tasha zaren design daga sama har kasa tana Wal wal tana sheqi da haske,ganin haka yasa Aina'u tayi saurin mikewa tsaye tana kallonta da mamaki"
Zarah wannan kayan Kuma fa?
Batare da kulawa ba zarah tace canza kaya kawai zanyi, Bata hankara ba taji har an fauce kayan cike da dore fuska ain tace 'whats wrong with kayan jikinki?..Zara xatayi magana ta tsareta a zafafe c'mon waike so kike kowa yasan kinxo neman namiji agidan Nan?dazu fa har dariya su nazli suke miki..hade ranta tayi cikin rolling eyes tace Aina'u pls spare me da maganan su nazlin Nan to in sunyi min dariyar saime?..damuwa ta batasu bane,hanklin gayen Nan nake bukata and you know kyakwar sutura itace hasken ya mace I want him to fall for me by simply admiring me..dariyan takaici ne mai karfi ya kufce ma ain batare da ta shirya masa ba, cikin dariyar tace ohh ahakan ne zai falling miki?tsaki mai kauri taja,Zara ki bude idonki ki dube shi da kyau acikin lawyoyin ma shina ajin farko ne gashi
kyakkwan namiji hadadde by now yasha arangama da irinki dubu Banda ma wayanda suka fiki a komi da komi Wani wawan suturanki ne zai sashi ya fallen Miki?c'mon In zakki kimtsa kawai ki kimtsa ki Dan kkakara turaren Nan naki kije waje ki same sa u can start a conversation or talk abt something else Zarah kada ki soma yarfa kanki agabansa pls know ur limits I beg you,ta karashe tare da hade mata hannun alaman roko..

Sauke Ajiyan xuciya Zara tayi cikin rashin sanin abincewa Nan dai ta sallame komi da alaman ta dauki shawarar ainaun altho ba a yadda taso kominta ya tafi ba,iya abunda ainaun ta kikkitsamatan kawai ta rike sannan ta hau kikkimtsawa can ta kama hanya tayi waje..

Anguwar bayan gari
Old maguwa site kano.

Karfe 1 da rabi bayan sallan azahar umma hadiza ne a kwance atsakar gidanta Inda ta baza babban tabarma a baranda kamar mai shan iska tana lura da masu shige da fice,yau takasa ta tsare ne danta dakatar da magulmatan anguwan su da suketa kaikawo tun safe a tsakar gidan kowa da kalar salon munafurcin sa suna famar mata tambayoyi akan kisan kai da sukaji ance yarta rufaida tayi..

Saidai wannan karon sun balain shan mamakin karfin hali irinna hadiza Dan kuwa bushe idanunta tayi tasss ta shiga bawa kowa amsa daidai da shi batare da nuna fargaba ko jin tsoro ba..
Hasalima in ga kalleta bazakace tana cikin damuwa ba,na ciki na cinta Amma haka tabi ta danne dukannin damuwar ta da kuncinta wanda har Yanzu tana jn zafi da radadin halin da rayuwar yarta rufaida ya shiga ciki

anan ma take dada Jin yadda labarin ya bazu aranta tana mugun shan mamakin yadda gulma ya karade gari cikin Dan kankanin lokacin da baikai ace har Yan nesa ma sunji ba..

Saidai ayau da Wanda take magana da shi da Wanda bata taba muamala dasu ba Dik sune agidanta,kusan kowa a anguwar saida ya shigo gidanta Jin Karin bayani akan zance
"Daga an shigo sai kaji ana sanya muryoyin tausayi na makirci "ayya hadiza Ashe auren dole akayi ma rufaida wannan mummunan al'amari yaje ya afku?Ai munji ance auren dole akayi mata shine taje ta kasa zama ta kashe mijinta,kwanaki yansanda aka zo aka tafi da yaa malam Ashe abun kenan?tou ita Kuma rufaida maiya kaita kisan Kai,au rayuwa ai yar haquri ce Kuma mai kudi kuka aura mata halan?

Umma Hadiza batacewa uffan saidai tajisu amma bata cika musu burinsu najn gulma game da abunda ya afku da rufaida,Abu daya kawai ta sani aranta shine ta Kare martaban yarta,Duk wanda ya kawo mata baqar magana acikin xancen sa itama takan tsayane ta dubi wani Abu mai muni daya faru dashi shima saita mayar masa da amsar sa daidai shi Inda zai masa ciwo da zafi wasu har sukan kasa yin haquri atake sai su nuna ransu ya baci suyita zage zage

Yanzun Nan ma rahamatu yar gidan malam dalhatu mai kantin breadi ta fice a zuciye tana zage zage tana kumfar baki,Kwata kwata yarinyar bata da mutunci,ubanta ne dillalin gulma uwar ta ma haka,kowa yasani gulma ne rayuwarsu, gaba daya lokutansu da karfinsu akan sakawa rayuwar mutane ido ya Kare,Wanda ake xargin tsabagen iya saka Ido da aibata yayan mutanen dasukeyi dinne ya jawo yarsu rahamatu ta lalace ta zama karamar karuwa a layi Amma Duk da haka basa gani Kuma basu fasa ba,a shekaru dai rahamtu bazata wuce ashirin ba Amma ayanzu haka aurenta biyu tana fitowa,ita tsaban son hada gurminta yau sawunta yafi kafa takwas a kofar gidan yaa malam tsaban sonjin rahoto but tunda umma hadiza ta gasa mata baqar magana ya mata ciwo saita ta fice a Gidan a zuciye tana karade anguwar Duk Inda ta zauna saita hau zage zage

"Ai kwara ni da kanin miji na ake zargina,zargina fa akeyi Wai nayi cikin shege ma kanin miji na ni ban kashe uban kowa ba
Amma yau har matar yaa malam ne zata cakka min baqar magana akan wata shashar yarta data dabawa miji wuka a ciki?..

"baqar zuciya da Muguwar tarbiyar data basu shine ya fito fili,yaran Dan sunga Suna da kyau sun bi sun debo kwadayin duniya sun daba a kokon zuciyansu,iyayen ma kwadayin abun duniya yasa sun sayar da mutuncin yayansu wa masu hannu da shunu hahahahaha ayyuriiiiiiii tooh ai sheikenan karyan kyau Kuma ya kare
Daga yau Zamuga uban da zai aura musu yarsu dataje ta kashe mijinta,Kai duniya ace yar yarinyar Nan har tasan tayi kisan Kai?Dama can ni ban yarda da shiru shirun rufaidan tan nan ba ai daga Ganin rufaida baqar mugunta da taurin zuciya ne da Ita irinna uwarta,ga jiji dakai haka zata wuce agaban babba bazata tsuguna tagaishe sa ba sunajin kansu yayan malami gasu waisu Yan boko,daga sun gama a aura musu masu kudi..
hehehehe yau munga karshen draman madalla da asirinsu ya Tono ga yarsu ta janyo musu abun kunya..

Aranar Babu wanda ya huta da wannan hirar musamman ma da umma hadiza taki Sam ta nuna damuwarta dan iya danne matsalarta tayi fuk danta Kare martaban yarta Wanda kwata kwata mutanen anguwa basuyi tsammani ba,lungu da sako zancen kenan wasu Sukace hadizar ce mai dore ma yayanta gindi suke tafka iya shege,ai hadiza shegen girman kai ne da Ita tanajin kanta matar Wani babban malamin tana so tayi ma mutane iyeyi da jan aji da walakanci,shirun umma hadiza akan zancen ya balain sosa ma magulmata rai bana wasa ba,barinma matar mai anguwar dake itace babban jakadar Duk Wani saka Ido da gulma Dan in anje an debo agidanta ake fara saukewa taji tanaji ta kushe Wanda Bai gamsheta ba,har karawa mata matsayi take depending on yawan gulman da kake kawo mata,yau da ba a samo mata cikakken rohoto akan case din rufaida ba har kukan takaici snda tayi,in aka tambayeta sai tace "hadiza ta rainata ne,bata darajata a matsayin uwa Kuma matar shugaba,gaba daya ta daga hankli ta da tsaban baqin cikin rashin samun cikakken rahoto akan batun rufaida,sonjin gurmi yabi ya hanata sakat,taso ace hadiza tayi magana Dan tabbas tasan lamarin Nan babba me, almajiri ya riga ya gaya mata cewa yau har fada umma hadiza sukayi da mijinta akan rufaida
Amma Wai har Yau itace zata sako hadizan agaba tana magiya tana son taji asalin Kan labari daga bakin matarnan ta rarraina mata hankli
Yo Inde batun kisa ne ai tuni sun riga sunji,dalilin yin kisan da sauran rahoton shi suke matukar muradin sonji Wanda har iyanzu Babu wanda yaji zancen daga bakin hadiza,Abun nan yana matukar Sosa musu rai..

Wasu ma gani suke kamar hadiza ba jinsu take ba,Amma inba haka ba wanni irin makirci da bugun ciki ne yau basu gani ba,mata sai kace dutsi
Daga anyi magana Iya kaci tace musu qaddara ne ya jawo lamarin Nan kuma Babu wanda yafi karfin qaddara
Daga Nan kuma saitaja bakinta tayi shiru bata kara ce masu komi,komin jidan makirici da iya shan ciki haka zaka gaji ka barta,Duk kokarinsu haka sukayi abanza suka kyale ta..

Bangaren rufaida kuwa yau Banda bacci da jinya Babu abunda jikinta yakesha gaba daya jikintan yayi lagwas Babu sauran karfi Dan ko taci abincin amai kawai takeyi..

Around 5 na yamma Ykmbo ne zaune a Tsakar gidan ta rafka uban tagumi ga tarin wanke wanke agabanta ta rasa ta Inda zata soma tunkarar yanayin jikin rufaida wanda haryanxu tausayi kawai yarinyar take bata Gani take ciwon Nan harda damuwa

Ta Dade awajen cikin tunani kafun ta kammala ayyukanta ta tashi takai komi kitchen ta kimtsa su,dakin ta nufa ganin rufaida nakan bacci yasa ta dau mayafin ta saba akai ana daf da gabanin magriba tayi ficerwata Dan dama akwai wasu abubuwan bukata datake so tayi amfani dasu .

Kiraye kirayen sallahn magrib yasa Da kyar rufaida ta bude lumsasshun idanunta da suka riga sukayi ja duk sun kumbura tsaban kukan datayi

Wani Nauyi idanun suke mata,ahakan dai ta shiga warasu ta shiga sauke su a hankli akan bugun kwanon dake dakin tana famar kallon sama can can tana sauke nishi mai zafi kamar wacce zata dauke ranta a take.

Wani kakkarfan Ajiyan zuciya ne ya kufce mata,a hnkli ta runtse idanunta tayi tsam da shi tana fesar da numfashi cikin dada son karfafa imanin dake cikin xuciyanta musammn game da hukuncin data soma yankewa ayanzun na dagewa da ibada dakai kukanta wajen Allah da neman sauki ta wajen sa Dan har yanzu ji take kamar bazata iya tattara pieces din rayuwanta ba

Ganin qur'ani acikin kayan da ummanta ta aiko mata ya jefa ta cikin shaukin jin cewa zata iya,da wannan tunanin ta miqe a sanyaye cikin layi Dan duk jikinta babu karfi,daga tayi Dan tafiya kadan saita tsaya,karshen ta haka ta shiga rirriike bango gudun kar jirin dake debarta ya zubar da Ita ga kanta dake mata nauyi da azaban ciwo da kyar take takawa har Allah yasa ta fito waje

dafa bangon kofar tayi sannan ta tsaya cikin karewa ko ina kallo ganin ko ina ya dau shiru Babu motsin kuwa sai rairayin iskan maraici

Sulalewa tayi a hnkli ta samu waje ta dofana daga jikin kofar tadan lafe jin yadda jiri da gajiyayyen numfashi ke kashe mata gabobin jiki..

Dan zaman datayi iska na shigarta yasata ta soma jin sanyi sanyi,Kanta hankara sai taji kamar sanyin yana kkrin shigarta sosai Daga idanuwanta tayi daga can kusurwa ta hango buta a kusa da randan kasarasu
saidai ayanzu haka Wani uban kasala da kwiyuwar takawa ta isa har wajen takeji..

Tafi minti biyar a haka iskan maraice na busota yana shigar jikinta tana danjin dadin shi wanda aranta harta yanke hukuncin ta tsaya a haka tana shirin aiyana Hakan aranta charaf ta soma tsinkayo muryoyinn mata daga can nesa ana ga gidan can Nan ne gidan,a hujajan ta mika wuyarta kadan sannan ta leka,Gani tayi ashe sune daga can nesa, muryan Maman Abdul ta soma tsinkayowa sannan na maman Iman da dayar matan alamn Nan gidan suka nufa

A hujajn ta daddafa isa harta bakin kofa tana leken su gani tayi su ukun sunsha manyan hijabai har kasa uwa manyan malamai gaba daya hirar da sukeyi ya sha musu Kai,tana tsaye har sanda ta tabbata Nan gidan suka dosa,gaban ta taji yana faduwa Sanin halinsu na gulma da son jin kwakwaf,aranta ta soma kawowa bai wuce suce sunzo ganinta ko suce sunzo jin ta bakin yakumbo akan lamarinta ba,Wanda kowa yasani dama can sun saba garzayowa tanan din in suka rasa makafa Duk dama basa cin sa'a da masifar yakumbo Amma haryau basu daddara ba..

Tun daga can nesa suka hau doka sallama asslamu ailakum Assalamu ailakum yakumbo?Wani shiru rufaida tayi bata amsa ba har suka iso daf

ganin zasu iya lekowa ciki yasata wucewa ciki da sauri ta dauki butar kawai ta wuce bayin daki..

Tana shiga ta aje butar ta wuce can cikin bayin ta boye kanta a Dan dungu daga Nan ma tana hangosu tana kumaj in Duk Wani sautin surutunsu,Labewa tayi a kangon karar tashiga lekewo ta waje ganin yadda sukayi tsege tsege a tsakar gidan da alama sunajiran suji Wani motsi ko sauti ne daga ciki
"Yakumbo?
Yakumbo bakin kirar su yafi na akirga Amma sai shiru

A haka saida sikaci kusan mintina goma rufaida bata fito ba Kuma bata amsa ba

sai can ta somajin sautin muryan Maman Abdul
Tace kunga banajin akwai mutum a gidan Nan kuzo mutafi kawai,cikin daka yar tsalle harda tuma maman Iman tace saidai ki leko mana ta cikin daki atake atake maman Abdul ta wuce har bakin kofar dakinsun bakinta dauke da sunan yakumbo Wanda har yanzu basuji an amsa su ba,Kai tsaye abunta ta tura kofar ta shiga,Nan ma sanda ta bata lokaci wajen kare ma koina kallo

Tasan tabbas suna Nan toh Ina kenan sukaje?ganan dai ko ina ba a kimtse ba

..daga Nan tsaye ta juya ta kalle su tace kai inaga fa yakumbo bata Nan kusa musamu waje kawai mu zauna kawai mujirata
,..daga can dayan matar dake ita tadan manyanta tace A'a kam dare fa yayi gaskiya tafiya zamuyi inyaso gobe da sassafe mwa taho,maman Abdul tace da safe fa kikace danke mijinki tsohon sojane baiya gari?toh ni wallhy
Zama daram anan har sai yakumbo ta fito,matar tace kikasan ko yaushe zata dawo darefa yayi,har yaushe wannan shegiyar magulmaciyar kinibabbiyar tsohuwa mai Dan uban warin talaucin ta Gama yawon baranta,mamn Abdul tace aikuwa
yanzu haka zaku samu tana can cikin anguwa ta hangame baki tana famar barbaden magana kwadayayya ce na karshe, ko kanzon abinci kika hadata dashi zaki kwashi labari,ahujajan maman iman tace to ko muma zamu zaga anguwar ne mu nemota?karde harta gaggayawa Wasu labarin rufaida mu muna Nan zaune min sake baki,gaskiya kawai kuzo mu bazama nemanta, ta karashe maganan tana jan tsaki Amma gaskiya bazan ji dadi ba in akace Wasu sunji labari nidake nake neman gindin zama Wajen matar mai anguwa?wallhi wannan labarin ne kawai zaisa ta dena raina min hankli tanai min kallon bitacan, dan dariya sauran matan suka kwashe dashi suka Tafa..maman Iman kenan ki kwantar da hanklinki ai inhar bamu samu labarin rufaifa ba to wallhy babumai samu..

Insha Allah Dole ne a bimu gobe Sau da kafa donjin sabon labarin rufaida,wani shiru rufaida tayi tana famar kallon yadda suketa nishadi suna maganganun su cikin raha da izgili suna kwashewa da dariya,wani Abu tadinga ji na toshe mata numfashi yana kkrin hanata Jan iska gaba daya sai taji hanklinta ya balain tashi kirjinta na mata zafi..

Saukar ruwan hawayen kawai taji akan fuskarta Amma harga Allah bata San lokacin taruwarsa ba..

Waje ta nema Adan gefe daf da Inda ake mata wanka akan dutsin ta zauna tuni Idanunta suka hau kallon bangon karan ta kure waje daya da kallo banda ruwan hawaye Babu abunda ke sauka daga cikin kwayar idanunta....

Muryan yakumbo ne ya dawo da ita,ta miqe tsaye tana tsinkayo shi daga waje ana rafka uwar masifa wa maman Iman,hakn yasata komawa jikin danga a bazata ta isa Inda ta lafe dazu ta Kara lafewar tana kan lekensu,ganin mamn Iman din tayi cirko cirko a hannun yakumbo tana masifa tana cewa "ke safiya Ina zaki shiga awajen Karki sake ki shigarmin bayan gida da daddaren Nan
"....saida gaban rufaida ya fadi yayi rasss tanajin bugunsa da mugun karfi,sai aynzu ta lura Ashe badon shigowar yakbo ba da tuni maman Iman ta kamata a bayan gidan tana ta kuka dan iya abunda suke cewa akanta kawai takeji kokadan bata ji karar tahowarta ba
Dan Bazata iya kayyade tsahon lokacin data dauka ahaka tanajin abunda suke cewa ba,duk taji Kuma ta fahimce su kowa dai so yake yaji meya afku da ita,labarin mumunan qaddarar ta kowa yake so yamaida abun wasa abun nishadi abun kodawa da cin zarafi Dan kawai a muzanta ta ahi dadi Wanda aganinta ko makiyinta bazata masa fatan ya shiga irin halin data tsinci Kanta a watannin da suka shude ba,
Aganinta ko mutum bazaice mata sannu ba ai Sam Sam Bata cancanci madallah ba kamar yadda taga suna dariya suna cewa kwadayin mahaifinta ya jawo mata Kuma uwarta bata bata tarbiya ba,cewa suke dama sune suka auri mai kudi wallahy da ko cin naman jikin su yake zasu zauna Dan haka ita rufaida datayi kisan Kai dama can girmai kaine da rikakken ra'ai ai dama tuntuni batasan maiya kawota duniyar ba ma
Maman Iman tace ai zamuga Wanda zai Kara aurenta
Ba ita Shasha bace kawai Dan an mata auren dole?yo ai mu irin auren da mukeso kenab in har da kudi Amma munafukar yarinya taje ta yayubo abun kunya ta dawo.
Dayan matar tace nifa mamaki yarinyar tabani
Kar cikin yayan yaa malam itace kamila shiru shiru bata da hayaniya Amma kiga Wai itace harda kisan Kai?toh gaskiya hadiza tayi mummunan sake ta bar yayanta suna abunda suka ga dama wannan ai iskanci ne da son zuciya,tabi ta sakalta yara ta barsu suna iyayi agari Wai gasu kyawawa masu diri matan alhazai hajiyoyin falo rayuwar carpet da tiles,har ana Wani kada mana duwawu in munje biki ana mana kallon kashi
Toh yau gata Nan dai mungani karshen alewa ai kasa ce sauran yaran tan ma kaf sai munga karshen su,muna anguwar Nan da ku wallhy hadixa saita dawo abar tausayi,nifa haushinta nakeji
Wawiyar mata mai mugun hali tabita ta kore kshiyoyinta kaf tayi babakere a gida ita kadai,ta dauki uban girman kai ta dorawa rayuwarta tanajin ita ishashiyace mai ilimi gata matar malami mswcheww
Wani uban shewa Mamn Abdul ta buga tace ihehehee anayi munajin dadi ana bari munajin haushi yo wani Matar malam?
Wani darene jemage Bai gani ba,kin manta maman Rashida makwabciyar su ne?
To wallhy Harta katanga takan leka cikin gdan taga me afkuea wallhi tallaho summa tallahi na rantse muku daxu tacemin dambe hadixa sukayi da yllll malam
Tana zaginsa yana zaginsa kaca kaca Wani shewa suka buga,mamn iman tace kice Allah?maman Abdul tana dariya tace ke dai rabu da makaryatan banza a fili saita rinka nuna mana kamar Babu komai tsakaninta da malam bayan mu munsan komi azabtar da Ita yakeyi,bakiga kwanaki yadda tabita kwanjame ba Kullum kafafunta abin layi neman maganin mata,
Hahahahahahaha

sosai rufaida taji zafi Kuma tasha mamakin wayannan bakaken magangnun su dake fitowa a tsakar gidan
11/18/21, 5:46 PM - Buhainat: *™✓SHADE OF RUFAIDAH*

_BY_
_SURAYYAHMS_

_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.