√Shade Of Rufaida Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: √SHADE OF RUFAIDA book 1.txt
Chapter 23 of 50
Part1:chapter 25
Daga ta bangaren su yaa sheik kuwa tunda ya idar da sallan fajr daga masallaci sai bai dawo cikin gidan ba ya tsaya a masjid din yanata karatun qur'ani wanda Duk da kasala da kwiuwa dayake neman shigarsa ya hanasa komi bai hanasa cigaba ba da aiwatar da karatun sa ba..
Sanda yay karatun sosai sannan yadan somajin dama dama Duk dama still kanshin bai dena masa nauyi sosai,anan ma baiyi kuskuren komawa cikin gidansan ba,jikin shi yanata basa cewa in har ya shiga ciki to tabbas kwanciya kawai zaiyi,da jallabiyar sa ajikin sa ya wuce direct sashen mahaifiyar sa..
Da kyakkwan sautin Sallamar sa mai cike da nutsuwa da Kamala ya kutso kansa ciki yanamai kalamshe idanuwan sa da mamakin abunda ya tarar da Ita tanayi..
Dan Murmushin gefen baki ya saki yana mai kada kansa wato haryau hjy bazata dena basa mamaki ba
Ita kuwa tunda ta daga Ido ta kalle sa bata kara kallon ko ina ba ta cigaba da abunda takeyi har ya karaso daf da Ita ya rusuna"..kin tashi lpya mama?..lpya kalau Alhamdullhi tace tana sauke wata nannauyan Ajiyan xuciya fuskarta tamkar Babu abunda yake damunta,Allon rubutun ta data gama wankewa ta daga tayi dashi can gefe ta jinginashi da kujera,tawadar da qur'aninta Duk ta Kau da su,u can tell dat ruwan rubutun ne acikin kwanon shan dake gabanta komai zatayi dashi oho yaa sheik dai binta da Ido yakeyi
Tana Dan tofe tofen ta,Yasan yanxu haka yana tsoma mata baki acikin lamarin xatace masa yay mata shiru Dan baisan komi ba,a Kullum acikin alfahari take da ahalinta,da kuma gidan da ta fito a matsayinta na yar gidan malamai,jikar malamai wanda kusan kaf zuriar mahaifinta da mahaifyarta malamai ne dan haka Babu Wani abun da bata iya ko ta sani gameda da malanta ba,duba da Ita kanta malamin zaure ta soma aura wanda zamanta a gidanshi kawao ya sata iya abubuwa Kuma tasan ta bambace gaskiya tsakanin malamai masuyi tsakanin su da Allah da masu saka son zuciya da asiri..
Shiyasa ma take ganin kamar a duniya babu wanda zai kaita sanin halin danta bukar dan kowa kwatankwacin halayyar sa kadan ne Babu acikin na mahaifinsa marigayi malam Amadu,.
Shiyasa tunda ya fita jiya cikin fushi ita sam hanklinta bai kwanta akansa ba,so bayan ta idda sallolintane ta fidda tsohon ajiya itama tayi yen rubuce rubucen ta da niyyar zata sha ta bawa danta zaidu yasha yauko yaki Allah saiya shi Dan yaa sheik bai yadda da irin abunsu na malantan Nan ba shidai yafi gane asibiti ko addua,Sam Sam baicika son shan Wani ruwan rubutu....
Bayan gaisawar su take cemai yakamata shima ya wuce can abuja yaga ya ake ciki dasu hajya goggo Kar suce ta ajiyeshi akan damuwar jikokinta,Murmushi kawai yay yace insha Allah zai je din,saita kafesa da Ido ganin yadda yake magana yana Dan yatsana fuska alamn kanshin har yanzu nadan damun sa yace mama ke yaushe kenan zaki taho?na dauka tare zamu wuce dake..
Tana lura dashi sosai tacce Ina zaidu,ai ku tafi can kawai inkaga nabar garin nan to komi ya daidata a rayuwar rufaida ne,Dan wayancan kam ban sansu ba..ji jikata ce damuwata...koya ma suke ciki oho?..tsaki taja cikin mita,tace awo ace mutum tsabar ya kashe xuciyarsa bazaima iya siyar Dan waya a hannun sa ana kiransa anajin abunda ke tafiya ba,zaidu ko kataba ganin hannun hadiza da wayar salula?nide ban taba Gani ba..
Kuma Duk wannan laifintane"abar bukar da jahilci amma ai shi ba matsiyaci bane..
Yaa sheik yace mama kamar tana da waya fa,cikin yar masifa ta juyo tace To daman kana sane kabarni inata kumfar baki,wayarta ta rarumo ta Mika masa tana miqewa sakamin lambarta anan,bai mata musu ba ya amsa lalubar aljihun jallabiyar sa yayi Jin ashe baifito da wayar bama yy fitar sauri gudun kar ya rasa salla atke ya maido mata wayar yanacewa mamma ki bari in nafito zan kawo miki kamar banfito da wayar ba,karban wayar tayi tana mita
O o nikam ma mairuwana da hadiza da ake min rowar lambarta
,badon jitakata rufaida bama Ina ruwana da wata hadiza,"..jingina Kai da yaa sheik yay a raunane yasata katse maganan cikin sauri tabishi da Ido Sam Sam bata fahimce yanayin sa bafa,sai tayi shiruuuu"can dai tace Kai zaidu?Wai meye haka kake narke min kamar Mai sabon ciki,ince dai ba sabon matsalar bukar ka dauko zaka yafamun ba?
Zaidu kafa kiyayeni
Kadauka ban fahimce ka bane
Anya zaidu kama runtsa jiya kuwa?
Wai Wai to ya naga idanunka sunyi Wani ciki ciki?
Ka dauko damuwar banza ka dorawa zuciyar ka..to kaima
Saika kashe kanka tunda bajina kakeyi ba,da sauri cikin dauriya yace a'a mama wallhy ba haka bane..
Tunda kince bakison maganan yaa bukar insha Allah bazan Kara kawo miki ba,ni damuwata rufaida ce,Wai naga ba lpya take dashi ba shine Nace toh ya za'ayi da Ita kenan?cike da yar hatsala Tace ohon musu,"..nide na hadata da uwarta,Kun dauka ko bansan abunda nakeyi bane?
Nayi Hakan ne Dan naga ko hadiza tana da sauran hankli,
Ni nana na haifi bukar,dukkan ku bazaku iya gayamin abunda bukar zai iya aikatawa,wato shi jahilin mutum yafi kowa gudun abun da zai rage masa kimarsa a idon mutane nasan bukar bazai taba yarda hadiza ta shiga masa gidansa tare da rufaida ba..
Nikuma burina kenan,nayi Hakan ne sabida hadiza ta shiga hanklinta ta zabi yarta rufaida ta rabu da bukar,zaidu Ina matukar tausaywa rayuwar yarnan hadiza,gashi bata da wani gata,banda azaba Babu abunda bukar yake gana mata a tarayyarsu,ita tsohuwar nata ma Duk talauci da ciwo ya nakasa ta bamai iya karban ma hadiza yancinta sai yarta rufaida..
Nayi musu Koran Kare ne sabida ta zuciya ta rabu dashi nahar abada itama ai tacanci taje ta kula da kanta....
Zaman gidansa zaman aljanna ne?
Inhar tayimin haka Nan ne zan iya kulawa da jikata rufaida acikin sauki batare da nama hadu da jarabar bukar ba..
Wallhy saida yaji anayi Wai kunu a Wani gida,Nan gaba in hadixa ta samu miji tayi aure nadan bazata hanani dauko rufaida gabana ba..yarinyar Nan tazo ta huta,dudu shekatun rufaidar nawa ne? Baifi acemin sha shidda ba fa,shukra anan saida aka haifeta kafin aka haife rufaida,kaga ai da sauranta,Duk karatun datake so inta dawo gabana saitayi shi,kamun ta Kara girma kadan sai in aurar da ita,insha Allah saina bawa bukar mamaki sai yayi nadamar abunda ya aikata min,...
Ajiyar xuciya Yaaa sheik dake kallo bakinta tuntuni ya sauke yace "Allah ya rufa asiri,Amma mama banso ace kinyi sanadiyar kashe auren yaa bukar ba,aure fa sunnan ma'aikin mu ne SAW,wanda a ranar karshe shida kansa zai kasance acikin alfahari da mu,bance shawarwarin ki basuyi kyau ba Amma nide Sam banji dadi daya jawo mutuwar aure ba,..
Mama kituna fa shaidan yakanyi matukar farinciki akan haka,nasan dai hadiz batajin dadin aurenta Amma ai qaddarar ta kenan,wanda inhar ta riqesa da Imani Sai kiga Allah ya dau mata mataki akansa dakansa..
Nide bazanso ace kece sanadiyar rasa auren hadiza ba.
Hjy mama dake harararsa tace eh ai dama nasan Hakan zakace shiyasa ma tun jiya nayi burus da qudiri ban saurareka ba..
Nima ai cewa nayi inason hakan ya afku bawai cemaka akayi har ya afkun ba,hmm zaidu?wato zaidu baka tashi yin wa'axinka sai akaina ko?yo ni meye nawa anan Dan Nace Ina neman wa rayuwar hadza sauki zaka wani fara lakamin tsiya kana hadani da shedan wai na kashe aure?..oh ni hasiya?karufamin asiri,basaima hadxar tayi wayau ba,kasanta fa saunace bana cire tsammanin bukar baiyi kwanan buzu akan yarnyar Nan ba ace mace Sam Sam ba zuciya?
Cikin sanyin Murya Yaa sheik yace insha Allah Duk zaa samu mafita..
Tace toh Ameen tana Satan kallon sa da gefen ido ganin yadda yake layi layin nan tasan bazai wuce yace mata zai koma can sashen sa ba
Caraf ta miqe tace jirani anan Ina zuwa
Bata jira mai zaice bama ta wuce sama cikin sauri tare da rubutun ta,kitchen ta nufa direct ta ajiye rubutun akan table,ta isa gaban Wani katoton microve ta dumama abincin dataci daxun yay saura Dan yau ko bacci bata samu tayi ba,so tuwon amala ne da miyan ewedu tana kammala xubawa a Dan plate ta debo hadadden miyar stew dinta dayaji barkwano qamshin atttarugun Duk ya buleta,dake kan gas yake haryanzu shima da zafinsa,nan ta yayyafa shi akan tuwon tare da namomin kaji daya cike ciki,ta dauko Wani katoton water flask da mug cup fari ta bude flask din ta juye rabin kunun daka dayakeci yana fidda uban qamshin kayan yaji,citta masoro,kajiji da sauran tarkace,ruwan rubutun ta ta dauko ta juye acikin kunun ta dama shi sosai yasan sake saida daga Gani zaka iya fahimtar Hakan sabida yadda kunun yaso yay tsololo.
Oho itadai bata damu badai aranta ta qudira cewa lallai zaidu saiyasha kunun na
Adan karamin tray tayi serving dinsa Kan kace kobo har ta sauko abu da bata taba ganinsa yayi ba takansa yanayi wato tagumi
Dan Kyabe bakinta tayi tana tahowa da mamakin yanayinsa aranta tana isowa gabansa ta aje tray din tace saika zauna kaci abinci ai tunda bakowa agidan daxai baka abunci Wayancan masu aikin naku dama ba iyawa sukai ba
Sanda Nace ma Jasmine ta tattarasu kaf suje can abuja Amma dake kunnen kashi ne da Ita sai ta kwashe su uwani da dayar mai dafa musu jagwlgwlen ta barni da maman Abdul,gyara zaman sa kawai yayi agabn abincin yanajin shirmentan danyasan bai isa yace mata bazaici ba,Alhalin ko kadan baijin sha'awar abincin Dan bakaramin ciwon Kai da bugun zuciya yake fama dashi ba..
Ayanzu Babu abunda yaketa bashi kamar kansa sanin komin kankanta ciwo yakan iya yin addua ya shafa awajen Amma yau saiyaga yakasa yin Hakan gaba daya,Wani irin muguwar axaban gajiya da kasala sun gama nakasa masa xuciyarsa taciki wanda kwata kwata baisan silarsu ba..
Arayuwa yakan going stress din daya ci uban na jiya shiyasa baiga dalilin da za'ace har jikinshi yana sacewa har haka ba,sosai yanayin sa yaso ya damesa aransa gudun ma kar ace masa Wani ciwo ne,Dan shi mutum ne wanda baison ciwo,tunda mahaifinsa alhj dikko yay ciwo agabn sa ya mutu saiya saka abun a ransa shisam baison yaga ana ciwo ko shikansa takamasa.
A hankli ya dau cup din kunun yay bimillah ya kurba yanata Jin surutan mahaifiyar sa dabaiya karewa sai hirar rufaida kawai take masa tana ta famar tsara kalar rayuwar da zata bata in ta dawo zama da ita..
Ayanzu haka burinta da zakuwarta baifi taji ance mata hadiza ta aikta abunda takeso din ba,inhar kuwa hadiza ta rabu da Auren bukar da ko itanan da zata iya bata tallafin kudi ta tada rayuwarta itama,,tace du du hadizar nawa take?ai ba Wani tsufa tayi ba,xaka samu dakadan ma ta girme jasmine in an bincika..Wani cak ta dauke hirar ganin ko kurba biyu masu kyau baiyi ba ya aje cup,ta juyo a tsime tana hararsa "waime haka zaidu?
Yace mama wallh banajin dadine
Tace A'a fito dai ka fadi gaskiya Jasmin ta fini iya abinci shisa Inna baka nawa kake cinshi kamar kana tauna kashi,baice mata uffan ba yay yar dariya,,abincin ya Kara jawowa gaban sa,yanata kallon abincin..
"kada kafarta ta ta shigayi ba kaga mahaukaciya tana tanata magana ba ai dole ne kayimin dariya,..cikin sa ne ya soma yin kugi Jin zafin kunun dayake ratsa hanjin sa,memakon ya rika Jin motsin acikin sa saiya somaji akansa kansan ya soma Wani irin juyawa yanajin jiri mai tsanani,can ya miqe a zumbur kamar an tsakure shi ya rike kansa cikin Wani yanayi hjy mama sanda ta razana itama ta mike,hankli tashe tace,"lpyarka kuwa zaidu?..yana kkrin daga hannun nasa kawai Taga xufa ya feffetso masa yuuu ata kansan kamar wanda aka watso masa ruwa.."Wani irin ihun ta fasa ta hau sauke salati tana kallon sa
abunda take ta suspecting aranta ya bayyana mata a filin,'..tace Wayyo Allah ni hasiya na shiga uku,bukar zai kashemin Dana..
Ta damkosa da uban karfi ta zaunar dashi"..jirani anan zaidu,karka yadda ka barnan maza jirani,bai ma gama tusa duwawunsa akan kujerar ba ta nufi kitchen da uban sauri jingina kansa yayi Dan baisan Meyake ji akansa ba alokacin,tsintar kansa kawai yayi yana fidda wasu ruwan hawaye ga kansa na masa Wani irin juyayi ga halin rudanin data tasomasa a bazata gaba daya sai yajishi a cikin rudani
A birkice Hjya mama ta isa kitchen din tana daga ruwan maganin ta tafashe da Wani matsancin kuka,cikin kukan dake fitowa harda sheshhka tace "Wato bukar saida yay kwanan buzu akan Dan uwansa zaidu ko?..Ashe bukar zai iya hallaka ni nima tunda ya iya yin Hakan akan Dan uwansa....
Toh bari zaidu yasha ya warke Duk Inda bukar yake a duniyan nan sainaje na same shi nima ya kashe ni...
Cikin wannan rudaddiyar yanayin ya shigo ta same ya sheik a gurfane a kasa yanata kakarin amai,da uban sauri ta fado gabansa tana dafa kafadun sa..tana cewa
Sannu zaidu yanzu zaka warke insha Allah,ni Nan da kake Gani nafi karfin bukar, wallhy karyan malanta yakeyi waye ubansa inba tsohon matsafi ba?
Yo ko ubansan ne ya taso bai isa ya kashe min kaiba.
Bukar bai isa yaymin asrar ranka ba zaidu..bai isa ba.
A sama sama yaa sheik yakejinta Dan bakaramin wahala yakesha da ciwon kansan Nan ba,a rikice ta dago fuskar sa ya durkusa gabanta yana fuskantar ta Babu jira ta bude kwanan shan ta soma kamfatar ruwan tana watsa masa tun daga tsakar kansa har fuskr sa..
Babu abunda yake saukewa sai Ajiyan zuciya,sanda ta jikashi tsaf sannan ta Kai masa ruwan har bakinsa cikin muryan tashin hankli da rikici tace "zaidu budemin bakin ka...yana kokrin kau da Kai ta daka masa tsawa a birkice tace wallhy Sai in faffala maka Mari anan zaidu, kasan dai ba tsoronka nakeji ba ko?,Wani Kukan ta Kuma fashewa dashi"..banda iskanci anmaidani bagidajiya an raina ilimi na,inba Reni ba
Inhaifeka aciki na sann kace zan baka abunda zai cutar da Kai?dakai da bukar din ma Duk halinku daya baku mutunta maganata,...zaidu ka bude bakinka ka amshe maganin Nan...kariya ne zai kareka daga sharrin bukar...ko sai ya kashe ka? Wayyyo Allah na shigga uku wayyo ni hasiya zaidu zaimin asarar haihuwa,Ihu kawai take,yaa sheik ya rasa abunda yake masa dadi baima San sanda ya dau maganan ya shanye Dukka ba,"..Wani cak ta tsayar da ihun ta tayo kansa tanai masa sannu kamar ba ita tagama masife shi ba..yana gyara zaman sa aksa ta yayumo kofin kunun tazo da shi gabansa
Gaba daya ta rikita shi saida ya shanye,
Tsaban ta rikita shi baima San Meyake ji ajikinsa da xuciyarsa ba kawai ya kwanta akan cushion ya lumshe Idanun sa yanata surutan datakeyi...
Wanda shi Sam ba so yakeyi ba,baison wannan dabiar nata na zargin mutum musamman inbataji ba batagani ba..
A lokacin ita kuwa Inda za'a bata qur'ani dafawa zatayi tace bukar ne yake taba mata da...
Har sanda jikin san ya lafa yay sauki sannan ta dena bambami,jinshi kawai take tana kwabarta akan ta dena irin haka,ta dena zargin yayan sa da wann sigar,yana cewa yasan yaa bukar bazai taba masa Wani abu mummuna kamar wannan ba, bama jinshi take ba banda takaici da jimamin baqar zuciya irinta bukar Babu abunda takeyi,to lallai ya zame mata tilas ta Kare danta zaidu,Dan tagaji da Jin wa'azukan sa da nasihohi sa masu kashe jiki,aranta tace ita ba Shashasha bace da har zata zuba ido wa katon jahili yana tsafe tsafen sa akansu har aje amata asarar da..
Yaa sheik ya gama mata nasiharsa tsaf Amma bata fasa kulla abunda ke zcyrta ba,Shiru dai ta masa Jin ya Nace da cewa baison ta kawo maganan zargin yaa bukar akan wannan abun kwata kwata ma ya hanata tunkarar sa dashi,yace mata inma gaskiya ne saidai ta Kara tunxirashi yay musu wanda yafi Hakan,yace kawai ta kyale shi..sunfi awa biyu ahaka har bacci mai Nauyi ya safce shi ta dade tana zaune a kusa dashi tanata kallon sa harsai da baccin nasa yayi nisa sosai
Tare da sauke Ajiyan xuciya ta miqe tsaye a gurguje ta haura sama ta dauko jakarta,ta sauko yauko jiran driver batayi ba ta rinka lallabawa har bakin titi ta tare abun hawa ba'a sauketa akoina ba sai gidan Wani boyayyen mutum daga cikin dangin mahaifinta wanda ya mutu tun shekarar da zaman Auren ta da mahaifin yaa malam ya kare..
Shima babban Malami ne wanda yasan addini bana wasa ba saidai shi a bilma ya zauna tare da kanurai yakan bada magani sosai Dan bazara taba mantawa shiya rinka kareta daga sharrin sihirin mijinta mahaifin yaa malam
Tunda ya rasu yayan sa suka dawo birni,dake a yanzu sune sukayi gadon abun sosai,gaba dayansu sun shahara sunyi suna sosai wajen bada maganin sihiri aljanu,jifa,karya kala kalan manakisa na aljanu Babu wanda basu iyaba..
Kawai dai wasu mutanen Sukanji tsoron zuwa wajensu sabida tsoron aljanun dake yawan mu'amala dasu,Duk dama tasan tun tale tale zuriar gidansu basa sihiri ko aikin bokanci..
HjyTana shiga gidan ta fashe ma yaran da kuka dakema sun manyanta sosai kuma suna sonta
Tace musu danta bukar ya haukace yana neman ya hallaka ta,kawai kuka takeyi tasan inbayi Hakan ba Hala sumadin hakuri kawai zasu bata suce tayi tawakkali,ita Sam bazata iya ba,so take ayi ma ahalinta
Katangar karfe da muguwar xuciyar irinta bukar,
musamman ma akan xaidu wanda ta bukaci ayi ma zaidun ta saukar qur'ani atayata da addoi da sadaqa..
Kudi mai uban yawa ta bude jakarta ta dire agaban su tace insun Kare zata Karo wasu,ita dai kawai atayata kare zuraiarta daga sharrin danta yaa malam..
Babu kalar nasihar da basuyi mata akan karta tsame yaa malam a adduar ba,kuka take ta tuma tace sammm Babu ruwanta dashi,ma duniya ta Mikasa sabida yaje ya ga Duk abunda take guje masa wanda shekara da shekaru tasan ta iya baqin kkrinta wajen jawoshi Amma yanzu jii take kokadan bazata iya ba...
Gudun kar zaidu ya farka yaga bata Nan yasa tayi maza ta sallamesu ta koma gida,samu kuwa tayi yanakan baccin sa,a sadade ta shiga ciki sannan ta dawo ta hau tattara wajen ta kimtsa tsaf ,daya daga cikin hayakin da aka bata ta zuba maza maza a kaskon wuta ta kawo Dede setin kujeran dayake kwancen ta ajiye masa shi yana hawa kanshi yana shaqa...
Haka ya rinka mafarkai Wai ana binsa da wuka za'a kashe Sa,acikin mafarkin ya rinka Kare kansa da adua ya shafi almost 2hrs yana baccin,sai can around 9:30am na safiya ya farka yanamai Jin kansa wasai,da guzarin sa wanda tamkar bashi bane dazu dayake Jin tsananin kasala da azaban ciwon kai..
Tashi yayi ya zauna Jin ko ina shiru ya saka Kai ya fice a falon ya nufi sashen sa,bai wata wata ba ya fada wanka
,fitowar sa keda wuya ya tarda tarin miss call of cause na can abuja yafi na ko Ina yawa,sai na imad guda daya,sauran Duk daga wajen aikinsa ne a gurjuge ya shirya kansa tsaf
Cikin wata dakakkiyar shadda dark blue colour ita bamai gare bace Dan haka asalin shape din jikinsa mai dauke hankli da nuna jarumtarsa a fili wanda tuni ta fallasa kanta wajen kara masa kyau da kima ta fito rass..
Cikin gaggawa ya koma sashen hjy mama ya same ta xaune agaban tv da waya akunnenta tana magana da hjy jasmine, Jin motsin sa yasa tayi saurin tura kullin magungunan data karbo yanzun Dan batama son ya San dasu,hayaki ne wanda za arika sakawa a sashen sa na can,wanda zaina kareshi daga sharrin Duk Wata muguwar halita musamman ma aljanu da mayu,sauran Kuma na yaransane,jira ma take inta fita ta aika sauran ma hadiza tsoronta Kar bukar wata rana ya kashe su..
Katse wayar tayi sanda sukayi sallama dashi Dan yace mata yana sauri Amma yau bazai dade ba zai dawo duba da Ita kadaice agidan sai yar aikin da aka barta dashi maman Abdul,datake Dan debe mata kewa,yana ficewa ta cigaba da shimfida ma hjy jasmine dokoki altho bata sanar da Ita komi ba,kawai dai umarni tabata akan tana da bukatar a tsare mata yayan ta da jikokinta daga sharrin mutum da aljanu...Kuma ta gargade ta da kyau akam maza ta gaya ma keeyan ya
nemeta awaya dake tasan shidin ya iya karatun qur'ani bana wasa ba,Dan shine yafiye yin saukar qur'ani agidan dama...but dake basu cika zama a Nigerian ba yasa abun baiyi Wani qarfi sosai ba..
Bayan sun gama discussing akan haka suka bingire da hirar dawowar imad,tanata bawa hjy jasmine dariya sabida kowa yasan yadda take da imad tamkar sa'oin juna komi saiyace ita,ita kuwa bata gajiya dashi ayi fada a shirya,kin dawowar sa Nigerian yasa tayi fushi tace bazata kara masa magana ba,Amma ayanzu Hakan ji take Inda zata so abuja da da mararin son ganinsa azuciyarta zata iso..
Sun dade suna hira Inda hjya jasmine ta zayyana mata dukkan abunda yake afkuwa a bangaren su hjy goggo a sabon gidansun...
Ajiyan xuciya hjy mama ta rinka saukewa Jin Wai harsuna shirya shagalin bikin murnan dawor su abujan,Duk sun gauraya da yara anata kashe kudade ana siye siyen banza da wofi,ga Aina'u ga kanwarta zarah data tsani yanayin rayuwarsu, ita sam ba irin rayuwar datake so ma yayan zaidu bakenan,son ranta ace su shikar kamilallun yarane maso son kiyaye addini kamar mahaifinsu..
Amma Sam Wai bazakaga sun nitsu Suna abu kamar na masu hankli ba sai in mufrad yana Nan ko mahaifinsu yana saka musu Ido?
Aranta tace toh lallai zata dau kyakkwan mataki Dan jiya taga illar zuba Ido kabar yara Suna tabewa awajen wanda baisan darajansu ba,sosai taga illar yin sanya a wajen hadixa.
Har suka kammala wayar bata dena mita ba,Wani haushin su hjy adadan take ta ji aranta tace"...Gaba daya sunzo sun dasa ma yayan zaidu kwadayin duniya,Suna cusa musu ra'ayin da bazai ficce su ba..
Da haushin haka aranta ta karace zamanta,sai can da ta idar da sallan azahar sannan ta Dan kwanta rama bashin baccin da ake binta wanda tun jiya batayishi ba...
11/18/21, 5:46 PM - Buhainat: *™✓SHADE OF RUFAIDAH*
_BY_
_SURAYYAHMS_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.