Trending Hausa Novels

Banana Island Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: BANANA ISLAND 2.txt

Chapter 2 of 16

Gabaɗaya gidan remoting system ne ,don haka komai da remote ake sarrafa shi daidai da labulai da ƙofofi . Ta wani ƙofa suka bi sai ga su sun ɓullo ta ƙafan benen da zai sadasu da ɗakunan ƙarƙashin ƙasa..Kenan gidan bayan bene kuma yina da under ground

Jikinta sanyi ƙalau yayi idonta suka fara cikowa da ƙwalla
Bakinta na rawa tace “Ina ne nan baiyi kama da asibitin da kace ba”

Murmushi yayi “Na hango tsoro a cikin ƙwarar idonki a kaina feel free ni Ba mugu bane”

Wayancewa tayi saboda kar ta bada kanta

“I do😁”

Haka ta cigaba da binsa har suka sauka a wani irin wargajejen falo wanda yafi na saman girma da tsaruwa ,wanda zai kwashe kujeru seti goma ,amma set ɗayan kujerune farare sol na leather seats sai manyan cup boards na littafai sai table ɗin tarkacen su desk top da laptops

“Zauna”

Ya bata umurni ,a ladafce ta zauna cikin sallamawa ,shikuma ya wuce wani ɗaki ,minti biyu sai gashi ya fito hannunsa da wani dogon bottle kamar na giya da cups guda biyu,gabanta yazo ya ajiye ya tsiyaya masu rabin cup

“Bissmillah”

Ƙiris ya rage ta fashe da ihu haka ta daure

“Menene wannan ,badai giya bane ko?”

Dariya yasoma ƙyaƙyacewa dashi har yana daga ciki,itakuwa ƙurr ta kafesa da ido ,ashe dama ya iya dariya har haka yake ɗaure fuska? Sosai taji yana ƙara burgeta

“Bana shan giya ,a normal drink ,haba If_babe😘bakisan drink din nan ba duk wayewanki? Kefa Lagos babe ne kuma University babe acan dinma hot cake🍰”

“Wallahi ni ba wayyayi bace kawai duk bugene ,so ban taba ganin drink din nan ba kar inje insha giya saboda kar ace mun ƴar ƙauye”

“Shikenan...shikenan your man baya shan giya da duk wani abu ma da bai dace ba ,amma zamu iya browsing sai mu bincika drink din a gabanki if you're doubting”

“No I trust you” ta amsashi da sauri tana ɗaukan glass cup din

Kafeta da ido yayi ,har saida takai glass din saman bakinta ta ɗago idanuwarsu ya sarƙe da na juna ,washe baki yayi

“Oh really ?”

Jinjina masa kai tayi
“Hmm” kawai yace ,shima ya dauki nasa ya ɗànyi sipping kaɗan ya ajiye

“Ina ne nan? Kuma meye dalilinka na baroni da Nigeria ba tare da consent ɗina ba ka kawo Ni nan ”

“Saboda Inyi building trust tsakanina dake ....yeah nan da kika gani gida nane ,shine karshen privacy na ,idan na gaji da mutane nan nike gudowa ,ba wanda yasan gidan nan dagani sai mamata sai ke yau”

“me yasa ni?”

“Kinada yawan tambaya ifty ,wannan tambayar naki shine abu na farko da ya jawo raayina akanki ...karki damu i love it.....Ammm kince mai ya kawo mu nan ? Saboda mu kwayewa junan mu hijabin da muka lulluɓe kanmu dashi ,abun nufi ,ki bani labarin ke wacece nima zan baki labarin kaina daga nan sai in fada maki matsayin tafiyarmu”

“Ba abu mai dadi da zakayi fatan ji a wajena ,in short Ni ƴar talakawane ,talakawan lilis mu barshi hakan”

“Hmm🤨kin manta naje har garinku na dauko mamanki still Baki yarda in na ga dama a rana daya zansan komai naki ba? So nike ki fada mun da bakinki

Gyara murya tayi

“Da fari sunana Iftihal_khair Mohammed ,Ni ƴar talakawane ,mamana maririya mara lafiya na fito daga maƙasƙancin family dake rugan bunzun jihar Gombe ,Ni kadai iyayena suka haifa, Babana makiyayine sana'arshi kiwon dabbobin mutane in ya kiwata ma masu hali dabbobinsu sai a biya shi guminsa ,haka dai rayuwa ta kasance har nakai shekaru takwas a duniya lokacin Babana ya hadu da wani mai gidansa a birnin Gombe ,ana kiransa Alhaji ɗan Nasi ,mutum mai kirki ya dauki Babana ya sashi a harkar nemansa ya danka masa dukiyarsa yina zuwa dasu fatauci yina saro masa raguna da shanaye ,Cikin ƙanƙanin lokaci Babana ya fara walwala bayida lokacin zaman rugan mu kuma ,don haka yazo ya ɗauke mu muka koma cikin gari muka zauna a bq ɗin gidan Alhaji Ɗan nasi

Buɗi ya cigaba da samun mu ,Mamata tana ma matar Alhaji aikin gida suna biyanta ,Ni kuma Alhaji ya sani makarantar da yaransa keyi saboda yace yina sona ,lokaci ƙalilan na sanu a makaranta saboda ƙwazo na ,gani dai baƙace amma kowa na sona.

Lokacin da nakai shekaru 10 lokacin babanmu ya gina mana gida a unguwar Alƙali amma bamu tare ba ,saboda wani fatauci da ya samu babanmu zuwa ƙasar Niger ,a wannan rutsutsin turawa suka kawo ma makarantar mu ziyara aka ɗauki hotuna damu yara ,shikenan bayan kwana biyu sai mukaji labarin hotona yina raining larabawa da turawa suna ta saka hotona a shafukansu ma sada zumunta wai nafi kowacce yarinya baƙa ƴar Afrika kyau ,sanadiyyar haka muka samu daukaka na ban mamaki .

Sai me?

Baƙin ciki da ƙyashi sai ya kama matar Alhaji ,ta koremu a gidanta ,muka koma gidan da babana,ya gina mana .mun koma da sati guda mummunar labari ya riske mu Babana ɓarayin shanu sun saceshi kuma mutanen da aka kama su tare sun tabbatar an kashesa .

Rayuwa tayi mana ƙunci ,bamu dakowa a Gombe sai Allah ,kullum kuɗin kyaututtukan da na sama sanadiyyar admiring din da larabawa da turawa sukayi a kan kyawuna shi mukeci muke rayuwa ,ba'a yi wata shida ba kuɗi ya tasamma ƙarayewa ,mamana ta fara sana'ar koko da ƙosai a tasha ,ta cireni a makarantan kudi na koma public school sbd alhaji yaki biyanmun matarshi ta zugashi

Takai ta kawo daƙyar nike zuwa makarantar saboda inataya mamata saida koko da ƙosai da safe
Na zama tantagaryar street child ,da taimakon Allah na gama makaranta na shiga Secondary shima tsintar karatun kawai nike har na kai SS3 lokacin mamata ta daina siyar da kosai a tasha tanayi a kofar gidanmu da yamma Ni kuma in saida awara ,rayiwa dai sai a hankali abu daya ke mun ciwo yanda kare bai taba tare Ni da sunan yina sona ba for that long ,kodon Ni baƙace?????

I dunno !

Har watarana muka kai ziyara rugar mu ,nan yaron mai unguwa ya liƙe zai aureni nikuma na daki ƙasa nace bazan auri jahili ɗan ƙauye ƙazami ba,a ƙarshe ma nace ma mamana mu tattara mu gudo ƙauyen bayan dangi sun mun caaa wai in gode ma Allah lamido yace zai aureni bayan na rigada nayi kwantai.

Mamana tabi raayina muka dawo Gombe ,sai me? Sai ciwo duniya ta tsaya mun cakkk

Tun ina tunanin sauki zaizo har mamana takai sai a kwantar a tayar daga ƙarshe ɓarin jikinta ɗaya ya shanye . A Lokacin nayi mock exams kuma nafi kowa ci a makarantar mu don haka gomnati ta biya mun waec da neco nikuma na siya jamb ,Kuma nayi jarabawa cikin nasara naci cleaned saidai duk jami'ar da nayi applying a arewa sun hanani Admission sai University of lagos.

Don haka na tattara harkar karatu na watsar tunda ba mai sponsoring ɗina ,abun takaici wai saiga ƴan ruganmu sunzo sun ɗauke mamana wai za ayi mata maganin gida tunda na gargajiya yaƙi ,da ban yarda ba amma sukayi mun ƙarfa ƙarfa .

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.