Complete Hausa Novels

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Babban Yaro Part 2.txt

Chapter 50 of 69

Duk wannan abun da ake gogon yana tsaye kusa da kan Mimi ya rutsawa fuskar ta kallo kamar wani maye gani a zaune bayan haka kuma ko kunyar su Umma baya ji.

Sallama Baban su Munnu yayi mana ya kama hanya ya futa Amjad din ya bishi a baya Umma kuwa zama tayi kan wata kujera tana fadin"Ni na manta shaf ban sanya kin kira Munnu a waya kin fada mata halin da ake ciki ba, in yaso ita sai ta fadawa Baban nasu."
Nace"Wallahi nima na manta shafa."!

Granny ce ta bude ido da sauri tana kallanmu ni da Umma tace"Kaddai bacci nayi a gurin nan."? Umma tayi murmushi tare da fadin"Bacci kika yi amma bai yi tsayi ba." Mayafin ta ta gyara tana fadin"Haba shiyasa kamar a mafar ki naji muryar k'ato ya shigo ko."
Nida Umma ka kalli juna wanene k'ato kuma."? Kafin muga tunani mu ya shigo dakin hannunsa rike da wasu manya manyan ledoji.

Kusa da Umma ya aje ledojin cikin nutsuwa yace." Umma zamu tafi gida. Ga abun bukata nan insha Allahu babu matsala."

Umma tace"Godiya muke Ubangiji Allah yayi albarka a rayuwa. "
Granny mik'ewa tayi tana wa Umma sallama, shikam tuni ya futa ko kallon inda nake zaune bai yi ba, Kai sai ince tun d'azu da safe da muka hada ido dashi ban kara ganin ya kalleni ba ko da wasa
Shige da fucen sa kawai yake.
Naji dadin Wannan sauyin da aka samu ta b'angaran shi.
Ya daina samun ido zan sake sosai dama idanunsa mugun dafi ne a tattare dani.

****

Alhmdullahi Mimi kullum samun sauki take yi yau kwannmu goma a sibiti kuma Alhmdullahi jikinta yayi sauki sosai tunda tana cin abunci Mara nauyi kuma tana zuwa ko INA, kwakwaran motsine dai Dr ya hanata

Amjadu kuwa kullum sai yazo shi da granny tare da kayan ciye-ciye hummm mu dake muke jinya maimakon muyi rama muka yi kiba ta sati biyu sosai na ware ganin baya shiga harkata ko yazo gaisuwace take hadani dashi, to shima tunda yaga jikin Mimi yayi sauki baya wani dadewa yake tafiya sabgoginsa, Kullum ina cikin Ac fatata tayi luwai gashi kullum muna tare da Mujahid muna shan soyayarmu ko Amjadu yazo ya tadda mu baya nuna damuwar komai karkari su gaisa ya wuce ciki.ko a fuska baya nuna Alamun wani Abu wai don ya fanni tare da jahid ni ni kaina yanzu tunani sauayrwa shi nace tafarar daya duk wannan rawar kan da yake akaina ya daina yi, ta lafiyar matar shi yake.
To nima hakan yayi mun dad'i yanzu zuciyata ta Riga ta tsayar min da Mujahid a matsayin miji maganar mu har gaban su Kawu Yunusa domun da suka zo duba Mimi sun gaisa da Mujahid din a matsayin sa na me Neman aure na.

*****

Kwanan Mimi goma sha takwas ta warware sosai ni kuma dama tuni na koma gida saboda makaranta, take Mujahid ya sanya ranar sallamar Mimi tare da tsauraran matakai babu yawan motsa jiki da cin abun mai nauyi babu kar zurga zurga tayi yawa, shima Amjad din banda tsawwala gurin yin sex wannan sune sharadan da Dr ya shimfid'a wa Mimi.

Granny itace ta dauki nauyi komai na gidan tunda anyi anyi dani kan na dawo gidan da zama har Mimi ta haihu naki ya Umma ma babu yanda bata yi dani ba, Amjad da kanshi ya turo Jahid gurina wai ya rarrashe ni naje na kula da Mimi fafar naki nace nima makaranta, lokacin mujahid har fushi yayi dani ya daina kirana a waya, kwana uku, nima shareshi nayi na cigaba da sabgata, da yaga Uwar bari ne yazo har inda nake ni kuma a lokacin na butsare masa sai ya dinga bani hakuri muka cigaba da sosyayar mu Cikin aminci da yardar juna.

****
Tun da watan azimi ya kama yake zurga-zurga har sai da ya tabbatar komai ya kammala ta fannin company shi sosai ake aiki tare da fidda kaya samfura iri-iri abun sai son barka sosai jama'a suke tsallakowa daga garuruwa suna zuwa d'aukar kaya.

Yaduka na mussaman ya sanya company ya shirya masa mai manyan zane ko wane kusan bandur dubu aka futa dashi gidanan yari(prison) bayan nan ya sanya aka futa da bandura na tampopi aka dinga shiga kauyi ka ana rabo, hatta da takalma sai da aka futa dasu aka rabawa mabukata.
Farkon wata kenan tsakiyar wata ma haka ne ya kasance, karshen wata ma haka.
Addu'a da fatan alkairi babu irin Wanda bai sha ba abakun mutanan gari

Yau saura kwana bakwai sallah.
Muna ta shirye-shiryen sallah. Lokacin Cikin Mimi ya futo sosai tunda yana matakin watanni shida tayi kiba sosai sa sosai kuma ta kwantar da hankalin ta.

TV muke kallo inda muke kallon tafsiri daga bakin Marigayi shak Isa Waziri Allah ya jikansa.

Kawai. Umma ta kunna redio murya wani shararan Dan jarida muka ji yana fadin"Salamu alaikum jama'ar jahar kano, labari da dumi-dumin sa, an yaka dai ta tashi yanzu-yanzu muka samu labari daga majiya me k'arfi shararar mutumin nan Wanda yayi suna a jahar kano, wato *Young millionaire Amjadu Abul Abbas mai nasara* wato mamallakin wannan shararan company me kawo muku nauin kayan sawa kama daga atamfoffi yadiga lesuka mayafai dogwayen riguna bulawus kayan yara hijab da sauran su, wannan company mun samu labari yanzu yanzu daga bakunan wadanda suke sari a cikinsa, cewa company ya hada baki da yahudawa nasara masu yak'i addinin musulunci masu adawa da fad'ar Annabi Allah wato Annabi Muhhamadu Slw a takaice dai an samu jikin takalman da company ya ke kerawa kasan takalmi an rubuta sunan Allah da manzon sa wato Allahu Muhammad, Jama'ar gari me zaku ce da wannan shirkar da wannan yaro da kuka amunce masa ya aikata.""

"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un shine abunda Umma take fad'a, take ta fashe da kuka tana gyda kanta take fad'in" Wannan zan sharri ne tswagaran sa na tabbatar yaron nan bazai aikata wannan danyan aikin ba."

Nima jikina wani irin shocking yake jin abunda Dan jaridar yaje fad'a, Cikin zuciya ta nace"Anya kuwa guy nan zai aikata Wannan Abu, duk da dai nasan Duk ak'idun shi na nasara ne kuma Duk yawanci abokan shi turawa ne, wata zuciyar tace min tabbas zasu iya rinyarsa dama ba wani tsoron Allah yake ba, tunda yana aikata zina." Kuka Umma take yi sosai da sosai Ya Aminu ya shigo gidan hannunshi rike da Leda me zane-zane da Lemo da a yaba a ciki.
Ganin Umma na kuka ya tabbatar labari ya same su
Umma tace"Kaji sharrin da jama'ar gari sukaiwa wannan yaron mijin Mimi ko."?
Ya Aminu ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya yace." Duk naji Umma gashi can ko ina ana surutu zancan ya cika gari.
Matasa sun fara gazgatawa domin wani Dan kasuwa ya futo da takalma na company an duba an ga gaskiya al'amarin.
Umma tace." Karya ne sharri ne aka shirya masa ni na tabbatar.
Ya Aminu yace." Umma sai ta iya kasamcewar gaskiya ne Wallahi mutane da basa tsoron Allah, ni dama wannan uban kud'in sa suna tsorata ni, akan ya samu duniya babu abunda ba zai yi ba."
Nace"Wallahi Ya Aminu nima na gasgata saboda d'abi'un sa duk na turawa ne.
Gaskiya gomnati ta shiga maganar kuma kamata yayi a dauki mataki akan sa, domin Allah da manzon sa ba abun wasa bane."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.